Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
gabana, in na tambaye ta ta ce karya ne. Na yi faɗa da jama'a da yawa akan sukar Malaika a gabana. Abin nata bai giga ba sai da muka kauro Birni inda ta hadu da wayayyu, masu arziki sannan halinta ya fito fili karara, dan a kauye kowa babu, balle ta sami mai kudi ko 'yar gayun da zata makalewa. Idan dare ya yi sai taga kowa a unguwar yana kunna Inji, sannan ta lura ashe sai a haske ake rayuwa, taga kullum matan birni idan zasu fita kwalliya suke ci ba'a saka koɗadiyar atamfa ta ce itama sai ta yi haka, taga wasu motarsu suke shiga akai su unguwa ba kamar a kauye ba da sayyada ko da acaɓa ake fita, nan ma ta ce itama sai ta yi haka. Ta ga ana zuwa 78 | Jamila Umar Tanko (JUT) CE... Dubai da Saudia ayi sayayya itama ta fara DA MA NI sha'awar haka. Akwai wasu masu arziki a kusa da mu a gidan ta tare nan take ganin kayan kyalkyalin duniya, kafin aka yi faɗa kaca-kaca ta daina shiga. Ta koma gidan wasu masu kudi a tsallaken titinmu nan ma aka yi fada ta daina shiga, ni kuma ta zo ta sauke min kwandon masifa sai na yi kudi da karfin tsiya dan adaina yi mata gori. Tun daga nan nake yi mata nasihaamma tamkarzugata nake yi, yanzu data hadu da ke abin ya ci tura ta sake barkalewa.Nasrin ki taimaka ki nunawa Malaika yadda rayuwa take, na tabbatar ke kanki a danginku akwai talakawa dole wani ya fi wani. " *** Nasrin ta yi shiru tana tunani ta rasa abinda zata ce, bayanansa kamar da kamshin gaskiya na Malaika ma ta gasgata dan in har karya take yi ba zata dinga sharɓar kuka haka ba. Me yasa Malaika zata yi mata karya? Ko 79 jamila Umar Tanko (JUT). DA MA NI CE... 1 me yasa Shamaki zai yi mata karya? Dole a cikinsu akwai makaryaci. Nasrin ta gyada kai ta ce, “tabbas uwa ɗaya uba ɗaya ma dole a sami wani ya fi wani arziki, Shamaki ka ci gaba da hakuri. Kenan yanzu albashinka na can kauye da shi kadai ka ke cin abinci?" zama Ya gyada kai yace "Eh! Naira dubu sha takwas ne kacal kafin wata ya zagayo sai na ci bashi na bawa Malaika, gashi na koma makaranta siyan Handout, da yawa ma 'yan matan ajinmu da nake koyawa karatu su suka dauki nauyina ni kuma na bawansu, assignment da aattendance dinsu nine dan ba zuwa suke yi ba kullum, to a haka muke rayuwar gashi an hana Acaɓa a Kano balle in yi da babur dina, amma na kan fita wajen gari in yi acaɓa ma wataran. Ni dai fatana in kyautatawa Malaika kada ta tafi ta bar ni." Nasrin ta cika da mamaki ga shamaki ma yana kokarin kece mata da kuka kamar yadda Malaika ta yi mata. Ta yi tagumi ta yi shiru tana saurarensa wani abu take ji yana yi mata yawo a cikin 80 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 kwakwalwarta. Ta yi ajiyar zuciya ta ce,“kenan kai dalibi ne a B.U.K ba Malami ba?" alhali Shamaki ya fara mamakin tambayar nan ya fada mata komai. Ya gyaɗa kai, yace,"ai na faɗa miki in da nake aiki, anan kuma karatu nake." Nasrin ta gyara zama ta yatsune fuska ta ce "ka fara tunanin kara aure ne ya sa Matarka da rashin samun zaman lafiya a kishi junanku?" Shamaki ya yi dariya ya ce, "Aure? Ina ta kaina auren me? Ko kadan bana taɓa sha'war yiwa Malaika kishiya. Ina son Malaika har cikin raina bana son ɓacin ranta, ta kasa yarda. Da ina da kudin da ya kai cikin duniyar nan, da zan juyewa Malaika dan ta yi farin ciki." Sai Nasrin ta ji gabanta ya faɗi ta faɗa cikin firgici "Shamaki ka tabbatar abinda yake rankaka ke fada min?". Ya yi dariya yace, "Baiwar Allah baki san ni ba, ban san ki ba amma na kwashe sirrina kacokan na faɗa miki. Wallahi ban da 81 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 ke duk duniya ban taɓa irin wannan hirar da kowa ba dan ke ma na san zaki taimake ni ki fahimtar da ita. Kin ga yanzu ina Laɓel3, karatu ya yi nisa saura shekara daya in gama, gidana ba nutsuwa ina tunanin yara bana iya zama a makaranta in yini ina karatu, ba dan ma kwakwalwar mai dauka da wuri ba ce da tayaya zan din ga hayewa jarabawa, kuma ban taɓa samun carryoɓer ba, babu kuma dalibin daya fi ni ci a department dinmu." Nasrin ta gyada kai ta ce, “dakyau Shamaki na jinjina maka, in Allah Ya so zan taimaka maka cikin dabara zan fahimtar da matarka ba tare da ta san mun taɓa magana da kai ba." Ya ce "na ji dadi na gode." Nasrin ta ce,“tambayata ta karshe itace shekarun Malaika nawa? Naka nawa?" Ya yi murmushi ya ce, "Shekarun Malaika ashirin da shida, ni kuma talatin da biyu. Ke fa shekarunki nawa?" Nasrin ta yi dariya, ta ce, “ni saʼar Malaika ce shekaruna ashirin da biyar, gobe ne Birthday dina. Na gode sai anjima." 82 Jamila Umȧr Tanko (JUT) DA MA NI CE.. Nasrin ta kashe waya tabar Shamaki a zaune yana ta murmushin jin dadi shi kadai. Ji yake tamkar matsalarsa ta zo karshe, gyara ya zo Malaikarsa zata shiryu. Ya yiwa Nasrin addu'a Allah Ya bata dama da ikon shawo kan Malaika. Dan tunkarar Malaika da zunmar gyara abu ne mai wuya dan bata jin Magana. Ya isa gida da murna ya iske Malaika cikin farin ciki, hatta cimar gidan ta canza abinci da kaza ta yi musu, sai ya ji gabansa ya fadi ya tambayi in da ta sami kudi ta sayi kaza, ko zakka makwabcinsu ya yi musu daman ya saba basu? sai Malaika ta ce kawai ya ci ba sai ya tambaya ba. Shamaki ya girgiza kai ya ce ba zai ci ba ya sani.Ta gyara zama ta yi fari da ido ta dauko wayarta ta bude sakon Nasrin ta nuna masa. Ya kalla ya dubaba tare da ya gane ba. Ta yi masa bayani kati ta turo mata na Naira dubu uku. Sai ya ji jikinsa ya yi sanyi ya fara tunani aransa “anya Nasrin gyara zata yi ko kuwa ɓata min mata take? Na fara nadamar labarina dana 83 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 kwashe na faɗa mata ɗazu. Ashe ta turowa matata kati sannan ta kira ta ji ta bakina.' " Sai ya shiga zulumi yana mai tsananin takaici, yaga dakyar ya nemo Naira ɗari biyu ya bayar a yi cefane,yanzu ta zo ta turo mata da dubu uku. Yanzu ta ina Malaika zata ga mutuncinsa? Ta ina zata ji maganarsa? Ta ina zai hanata ta hanu ? Me yasa ba zata yi sha'awar ziyartar Nasrin a Abuja ba? Shiyasa ta fi sha'awar saki maimakon zama da shi dan ta koma ta zauna da Nasrin. "Malaika kada in kara ganin kin kira Nasrin balle ki roke ta kati." Shamaki ya fada a fusace. Malaiaka ta zabura ta taşhi tsaye cikin tsiwa ta ce "Lallai ma, au haka zaka ce? Bakin ciki ne abin dan kaga na sami mai taimaka min? Wallahi baka kaunata saboda baka kaunar ci gabana. Babu mai raba ni da Nasrin Aminiyata." Sai ya fusata ya kai mata hannu kamar zai mare ta, ya fasa.Tayi tsalle ta faɗa kan kujera tana makerketa ta zaci dukanta zai yi. 84 | Jamila Umar Tanko (JUT) CE... 1 Ya fice daga gidan a fusace, Malaika ta tashi tsaye ta tsaya a falo ta kama Rugu ta rasa abinda yake yi mata dadi zuciyar ta na tafasa ga tukikin masifa ya taso mata amma babu abokin fafatawa. DA MA NI Tsaki take tana kwafa tana fadin "cafdi jam! Ashe za'ayi ta yau a gidan nan. Daman ka mare ni da ka mari aurenka wallahi. Nasrin kuwa bazan rabu da itaba sai dai ka mutu. Shamaki bai shigo gida ba sai da daddare bayan Sallar isha'i, ya shigo da fara'a ya iske yara sun yi bacci sai Malaika a zaune a tsakar gida tana cin tsire. Ya yi sallama bata amsa ba, ya yi dariya yace, "kaga madam an sami kudi ana ta cin dadi bayan kaza ma kuma tsire ake ci, ai dadin zai yi yawa a rage na gobe mana. Ke kaɗai za ki ci dan rashin imani sai da kika bari yara sun yi bacci, ni bana nan?" Ta yi kamar ba da ita yake ba ta dinga kai tsoka lunkuma-lunkuma bakinta. Ya ga da gaskę cinyewa zata yi ya zabura ya kai hannu zai dauki yanka ɗaya, ta dɗauke namanta da 85 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 sauri ta juya baya ta cinye tas ta wurgar da takarda, ya zaci wasa ne. Ya ce ta dauko masa abincinsa na ɗazu zai ci. Ta harare shi ta ce "ai ka yiwa kanka wallahi mun cinye tas ka je ka nemi abincinka. Tunda kai ba'ayi maka gwaninta, kamar wacce ta samo kudin haram har da kin ci kuma wallahi duk ran da ka dake ni ka daki aurenka." Shamaki ya zauna ya yi shiru yana kallonta yunwa yake ji ta gaske kuwa, dan tun kokon safe ne a cikinsa gashi ba shi da ko sisi. Bashi da karfin yin magana ma balle fada, sannan ba ya son ma a kara tayar da zancen dan daga baya da ya huce sai ya ga bai kyauta ba kamata yayi ya yiwa Nasrin kyakyawan zato tunda taimakawa ta yi. Ya yi ta karanto istigfari a cikin zuciyarsa. Duk abinda Malaika take fada masa kalma daya yake faɗa yana ta nanatawa kamar karatu "yi hakuri, yi hakuri, bazan sake ba." Har sai da Malaika ta ji ya fara bata tausayi sannan ta daina tsigale shi. Ya tashi ya fitą kofar gida ya je wajen mai shayi da biredi na kan kwanar gidansu anan ya ci bashi ya cika 86 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 cikinsa ya dawo gida. A ranar dai Malaika bata kula shi ba, baya ta juya masa ya gaji da magiya ya rabu da ita. Asuba ta gari! *** Shamaki ya shiga cikin matsananciyar rayuwa, ko inaba dadi, can garinsu yana kula da mahaifiyarsa wacce bata da komai tana neman taimako, kannensa gaba daya babu mai shi babu wanda ya yi karatu a jikinsa ma suke nema, 'ya'yansa abin tausayi ya kamata an saka su a makaranta amma suna zaune a gida, ga marar lafiya kuwa wani lokaci sai dai a hakura a zuba masa ido yana ta kuka babu kudin magani, Malaika abar kaunarsa ta tsane shi ta juya masa baya, ya manta rabon da ta masa hira mai dadi. Baya gushewa da yin tsayuwar dare da addu'a yana kuka yana faɗawa Allah. Ya na nemawa Malaika gafara da shiriya dan baya fatan Allah Ya kamata da laifin kin yiwa miji biyayya da butulcin da take yiwa Ubangiji. 87 | Jamila Umar. Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Malaika kuwa ga ni take kamar duk rashin gata da rashin sa'a akanta ya kare, gani take tamkar ta rako mata duniya. Idan ta tsaya a titi ta hango mace ta na kotsewa a cikin mota mai kyau ta gani ta fada sai ta ji ta tsani kanta. Dan haka itama rayuwar ta yi mata kunci bata walwala ko kaɗan. Al'amarin Nasrin kuwa ta shiga rudani matsalar Malaika da Shamaki ta tsaye mata a rai, ta shiga aikin tunanin tantance waye mugu a cikinsu kuma waye ya yi mata karya, a haka dai kowa ya nuna mata shine abin tausayi dayan ke cutarsa. To Allah Shine Masanin badini da Zahiri. 88 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 BABI NA BIYAR ABUJA: Da misalin karfe goma na dare Nasrin tana sanye da kayan bacci tana kwance akan gadonta tana ta danna Computer ta har yanzu dai tana biye da Dr.Jalo mutuminta, ta ga ya yi sababbin rubutu ya turo. Tana ta bibiyarsa a hankali tana karantawa sai ta ci karo da wani rubutunsa wanda ta ke neman karin bayani akai, yadda ya yi rubutun ma kai kace da Shamaki da Malaika yake, ma'auratan da suka kasa fahimtar juna. Sai ta je ta yi comment a kasan posts dinsa. Bai bawa kowa amsa ba, dan ta iske dariruwan mutane da suka tofa albarkacin bakinsu, mata da maza suna ta mahawara. Gogan naka bai tanka ba shi dai ya zuba bayanai ya kara gaba, ya bar mutane da hayagaga. . Ta dubi lokacin da ya turo sakon, a ranar ne da safe.Ta dauko wayartą zata kira shi sai ta 89 | Jamila Umar Tanko (JUT) 1 DA MA NI CE... 1 kalli agogo ta ga dare ne bai kamata ta kira mai aure da daddare ba dan ta tabbatar yana da mata kada ta hada su fada.Ta dubo cikin hotunansa ta ga ya sake 'profilepicture' dinsa, tabbas ya yi kyau matuka kamar ka kira shi ya amsa. Idanuwan nan dara-dara, hanci doɗar, hakora a jere reras gwanin ban sha'awa ya saka wani farin gilashi wanda ya yi masa kyau, kana ganinsa kaga cikekken likita, likitan da yasan abinda yake yi. Ta dade tana kallon hoton nan a ranta tana mamakin yadda ta sami mutumin da yake birge ta. Dr.Jalo ne kaɗai mutumin data taɓa haduwa da shi take binsa ya ke ja mata aji. Shima babban abinda ya birge ta shine tunaninsa da fasaharsa lallai duk wanda Allah ya bawa fasahar rubutu ko ta magana lallai ya godewa Allah, ba kowa ne yake samu ba kuma ba'a saya a kasuwa, haka ba'a koyo a makaranata. "DA MA NI CE Dr.Jalo! Dr.Jalo." Ta fada abayyane a lokacin da ta ci gaba da kallonsa. 90 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Tana cikin wannan hali sai gashi ya hau facebook. Ta zabura ta bishi ta 'inbod' ta masa magana. Salama ce da gaisuwa ta tura masa, nan da nan ya amsa mata. Sai ta yi mamaki. Daga nan da kwarin guiwarta ta tura masa jinjina da yabo akan rubuce-rubucensa. Sai bai bata amsa ba kuma tana ganinsa 'online.' Ta sake tura masa cewar tana so su dinga gaisawa ya dinga bata shawarwari. Bayan ta jima da tura sakon bai bata amsa ba ma sai ya sauka daga facebook din ma. Ta san kuwa ba zai dawo a yau ba, ko ya dawo ba zai bata amsa ba. Ta ji kwallar takaici ta surnano mata ta fara tsanar kanta da kanta ma da ta ke jawowa kanta wulakanci, tana mamakin masu wulakanta mutane dan sunga mutane suna sonsu. A sanadiyyar Allah Ya yi musu wata baiwa, tabbas ita bata da wulakanci tun ma bata fara hulda da mutane haka ba, yanzu data fara harkar rahotannin nan ana nuna ta a talabijin ta samu masoya da yawa da suke turo mata da sakonni ta waya ko ta Email dinta. Tana kula 91 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 kowa yadda ya kamata shiyasa kula Malaika har sukasaba. ma ta tsaya ta Ta fara ji a ranta ba zata kara kula Dr.Jalo ba bare ya sake yi mata wulakanci, eh yana da kyau, yana da ilimi, yana da kamun kai , yana da aji, watakila attajiri ne ko dan gidan attajiri. Sai aka yi yaya kuma? Da me ya fita? Koda ace ya tara duk wadannan abubuwan da aka zano Nasrin tana da linkin nasa.Ta fara tunanin kai zuciyarta nesa ta manta da matsalar mutumin da bata sani ba. ** *** *** Washe gari da safe ta shirya zata fita wajen aiki ta jawo computer ta zata kashe saita iske amsar Dr.Jalo da asuba ya turo mata. Ta ji dadi a ranta harda rufe ido da budewa dan ta gasgata ba mafarki take yi ba ido biyu ne.Ya tabbatar mata yana farin cikin haduwa da ita kuma kada ta damu a shirye yake ya bata shawara koma wacce iri ce.Hannunta na rawa ta rubuta masa godiya da 92 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 nuna farincikinta. Baya kan layi amma ta san idan ya dawo zai gani. Ta fito falo tana walwala har sai da Salis da Zainab suka fahimce ta, yau tare da su ta karya kumallo saɓanin idan ta fito da fushi bata tsayawa ta ci abinci. Zainab ta harare ta, ta ce kin yi chats ko? Kin ji wani abu mai dadi dan nasan baki da abokai sai a socoalNetwork kullum kina kan computer, haka kawakenki mutanen ɓoye ne duk anan ku ke haduwa." 999 Salis da Nasrin suka kwashe da dariya. Nasrin ta ce, "ka ji wai muatanen ɓoye kamar wasu aljanu." Da suka gama cin abinci Salis da Nasrin kowa ya dauki jakar laptop dinsa ya fita, Zainab ta rako su har wajen motocinsu kowannesu ya shi tsaleliyar motarsa ya nufi wajen aiki. Sai yamma kuma ko da magriba, Zainab ita kadai ta ke yini kuma bata sha'awar 'yan aiki saboda matsalarsu ta ishe ta. Nasrin ta isa ofis, basu zauna ba yau, suka fita da motar ofis dauko rahotanni, acan ta yini basu dawo ofis ba sai da yamma likis 93 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE イ wayarta ma a ofis ta bari a caji, ta zo ta iske missedcalls Malaika babu adadi bata damu ta kira ba dan ta san kiran kawai take yi dan bata da abinyi. Kullum sai ta kira ta ta ishe ta da surutu marar maʼana. Dan haka ba zata kira ta ba itama sai ranar da bata da abinyi, sai su haɗu su yi ta hirar rashin abin yi. Kafin ta tafi gida ta bankaɗo Facebook dinta sai kuwa taga mutuminta yau 'yan siyasa ya ragargaza ya kawo musu misalai da manyan 'yan siyarsar kasashen da suka ci gaba wadanda suka san darajar bil'adama. Ya kawo misalai da 'Nafsin Mandela' da 'General Muhammad Buhari' zo kaga ruwan yabo da jinjina da ake yi masa. Nasrin ma ta shiga ta zankada turanci irin na su na gwanaye, ta yabi gwaninta Dr.Jalo, ta yaba masa akan fadar gaskiya komai ɗacinta. Tana shiga cikin inboddinta sai taga ya turo mata da sakon gaisuwa, daga nan dadi ya kusa tafiya da ita dan ji ta yi ta yi 'luuuu' kamar zata shide dakyar ta dawo daidai. Ta godewa Allah da Ya sa wannan hazikin bawan ya san da ita. Nan take ta bashi amsa tana mai 94 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 tabbatar masa tana nan lafiya cikin koshin lafiya tare da tambayarsa lafiyarsa shima. Tana turawa ta tashi rataya jakar laptop dinta ta fito daga ofis tana tafe tana rangwada, tafiyar ma yau sai da ta canja ta. Har sai da abokan aikinta suka fahimci yau nishadi take ji, masu gadi sun sha kyauta tunda daga reception take kyautar kudihar zuwa get. Ita a ranta sadaka take yi, da neman yarda Allah, Ya kara dorata akan miskilin hazikin nan, gwaninta Dr.Jalo. Ta iske yayarta Zainab a kicin bayan sun gaisa ta shiga daki ta yi wanka ta fito sanye da riga shimi da wando iya guiwa (Three Kuarter) za ta tayata abinda zata iya yi dan ita bata son aiki musamman na kicin, dan bata sababa. Nasrin ta na ta yiwa Zainab tsiya saboda bata daukar kuku da masu aiki, sai bayan kwana bibibiyu wata inyamura take zuwa ta kalkale mata gidan ta tafi ba zata dawo ba sai bayan wata kwana biyun kuma kullum, ita ke yin girki da kanta. Dan haka ne bata son ta yi aiki gwamnati alhali har masters gare ta. 95 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Zainab dai murmushi take tana aikinta Nasrin tana ta ɓaɓatun ta ita kadai. Nasrin ta yi fari ta zauna akan wata kujerar roba ta ce, "Antimi in baki labari?" Zainab ta ce, "Engr.Fu'ad zai zo ko?". Nasrin ta yi tsaki ta ce, “caf! wannan da zuwansa da rashin zuwansa ma duk daya. Wai fushi yake yi da ni,mutum ne mai yawan fushi da daukar magana. Ke ni ba zan iya ba. 99 Zainab ta ce, “ke dai na rasa mai Fu'ad ya yi miki bakya sonsa." 99 Nasrin ta ce, "kana son mace amma bazaka lallashe ta ba. Shi fa baya lallashi kuma baya bada hakuri sai dai a bashi, ya cika son kansa. " Zainab ta girgiza kai ta ce, "a'a haka ba zai yiwu ba aure ai dan lallashi ne da tausasa harshe, baʼace mace ce kadai zata yiwa namiji ba haka ba'a ce namiji shi kadai zai lallashi mace ba itama sai ta lallashe shi." Nasrin ta bata hannu suka tafa ta ce, "ina sonki saboda fahimtar nan tata ki Antimi. Labarin mutanen da suka san abinda suke zan baki, irin mutanen da suka yi karanci a 96 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 kasarmu, irin mutanen da ya kamata su mulke mu, wadanda Allah Ya yi musu baiwa ta iya tsara magana a rubuce." Zainab ta gyara tsayuwa ta ajiye cinyar kazar da take wankewa. Ta ce, "wannan wanene, daga Amerika yake shima? A ina kika sanshi,ko a gidan talabijin dinku?" Nasrin ta yi murmushi ta ce, “Ban taɓa ganinsa ba rubutunsa nake a gani a facebook kawai. Dr.Jalo sunansa, Dinah ta san shi, mu yi ta yi masa magana ya ki amsawa saboda jan aji. Amma yanzu kin ga yana kula ni har ma in tambaye shi abu ya ban amsa. " Zainab ta harare ta, ta yi tsaki ta juya ta ci gaba da aikinta. Nasrin ta ce "au Dr.Jalon tsaki?" kike yiwa Zainab ta ce “ke wallahi haushi kike ba ni. Daman har yanzu baki rabu da bibiyarsa ba. Ni da na karanta wani post dinsa bai birge ni ba, kawai dai ya iya turanci ina ga a turai ya yi makaranta.' " 97 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Nasrin ta mike ta fice daga kicin din cikin fushi, Zainab ta biyo ta tana kwala kira, Nasrin ta ki dawowa dan ta yi fushi, Zainab ta sha dariya ita kaɗai. Nasarin na shiga daki ta mayar da kofa ta rufe ta ci gaba da karatun rubutun mutuminta. Har yanzu dai bai hau ba. Ta ɗauko wayarta ta kira lambarsa, a kila-wakala take, zai dauka ko ba zai dauka ba. Sai gashi kuwa bai dauka ba. Bata ji dadi ba ta ji jikinta ya yi sanyi sai ta fara daina ganin laifin Zainab gaskiya ne mutumin da bai ma san tana yi ba har ta tsaya tana ɓatawa kanta rai. Bugun kofar da ake yi mata ta ɓaci, sai yi ake yi ana sakewa. Ta san Zainab ce sai bata amsa ba amma daga baya ta jiyo muryar Zainab da kuma ta kawarta Dina. Dan haka ta taso ta buɗe. Ita da Dina su ka yi tsalle suka rungume juna suna murna. Dinah ta ce, "kin huce? Aka ce fushi kike yi. Waya taɓa min ke?" Nasrin ta zunɓuro baki ta koma gefen gado ta zauna. 98 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Zainab tana ta dariya ta ce "wai dan na kushe wani abokinta a facebook take fushi. Ni da na ji tana yabonsa na zaci ma ta sanshi, ko cewa ya yi yana sonta. Saikawaina ji ta ce bata taɓa ganiusa ba haushi ya kama ni." " Dinah ta tsaya akanta tana harara ta ce "wannan dan wulakancin kika ci gaba da kulawa? Wallahi ke abin haushi ne da ke. " Nasrin ta ce, “ke ma ki biyewa Anti Zainab ki ci gaba da ɓata min rai. Ni fa ban ce wani wani abu ba fada mata zan yi in ce ya rage girman kai fa, yanzu yana ba ni amsa." Zainab ta yi gatsine ta yi zumɗe da baki ta ce "Ayyah kanwata yi hakuri, na zaci wulakancin ya yi miki kuma. Yi hakuri my sweetsister. " Gaba daya suka yi dariya, zainab ta fice. Dina ta zauna a kusa da Nasrin suka ci gaba da Kallon rubutun Jalo a Facebook, gaba daya suka hada kai suka rungumo Computer suna karantawa a tare suna shewa, suna tafa hannu suna jinjina. Suna fadin "Allah Ya taimaki likitan likitocin Naija." 99 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Dinah ta ce, "gaskiya ya birge ni gashi yaro bai fi shekaru talatin da biyar ba. A wanne gari yake ne?" Nasrin ta taɓe baki ta ce, “inazan sani ni da ba kula ni yake yi ba? Amma mu duba profile dinsa. 66 Suka dukufa suna ta bincike akansa sai bayanai suka nuna shi likita ne, mazaunin Lagos yana da mace daya da yara biyu maza. Matar tasa ma 'yar gidan Minister lafiya ce, sunanta Rayyana Abbas sun san sunan Babanta. Nan da nan suka koma neman Rayyana Abbas a Facebook, sai kuwa suka bankado ta. Tubarkallah! Masha Allah!! 'yar gayu ce matuka sai dai bata da kyau,baka ce kirin gajera mai kiba, amma akwai ilimi da kudi. Ita kuma cikekkiyar lauya ce. Dinah da Nasrin suka yi shiru suna kallon juna suna mamaki. Nasrin ta ce, "shege ai dole ya ja aji ya san yagama zabar mace. Ita kuwa ta yi sa'ar miji mai kwanya, sai ta godewa Allah kuma ta kula da shi dan idan ta yi sakaci mahara zasu 100 | Jamila Umar Tanko (JUT) _ DA MA NI CE... 1 kawo mata farmaki saboda mijinta kadara ne. Kin ji muryarsa kuwa . • • • Hmmmm, ba magana ke guy din ya hadu daga kafa zuwa tsakar kai.' " Suka sheke da dariya suka tafa hannu. Dina ta ce, "Nasrin kina son likitan nan ko?" Nasrin ta yi fari, ta dagaido sama tana tunani ta ce "not really but...." Dina ta katse ta, ta bangaji kafadarta ta ce "but me? Kawai ki fada min gaskiya kawata. Ina zaki ajiye Engr.Fu'ad?" Nasrin ta ce, "maganar gaskiya Dr.Jalo yana burge ni amma ba don kyansa ba, dan in karu da iliminsa kin san ni da son aikin jarida, bayan haka ina son mutum mai aji. Duk ya hada." Dina ta ce, “idan na kula kina son alaka da shi ta kurkusa bata nesa ba." Suka yi dariya suka tafa. .99 Nasrin ta ce, “ke muyi wata hirar mu share wannan da ma bai san abinda muke yi ba. Allah Ya bamu maza na gari muma. Dinah ta ce "da dai ya fi." 101 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Wayar Nasrin ceke kara Dinah ta miko mata da sauri, Nasrin ta na dubawa taga sunan Malaika, sai ta yi tsaki ta ajiye wayar a gefe. Dinah ta ce, "wacece Malaika?" Nasrin ta yi dariya ta ce, "sabuwar kawa na yi a Kano idan na baki labarinta zaki yi kwana uku kina dariya dan nasan halinki abu kadan ma dariyar awoyi ki ke yi kina yi." Dina ta tuntsire da dariya ta ce,"dan Allah ba ni labarin Malaika." " dauka. Malaika ce ta ci gaba da kira, Nasrin ta ki Dina ta ce "ki dauka dan Allah ki saka min ita a hand'sfree mu ci dariya." Nasrin ta ce, “dan Allah rabu da itaba zan dauka ba, surutu zata yi ta yi. Ke! zama ki santa. Ina wacce aka taɓa nunawa a labaraihar kika kira ni kina ta shan dariyar turancinta, sati byu da suka wuce? To itace fa. " Dinah ta yi tsalle ta dire tana ta dariya ta ce "Wallahi sai kin dauki wayarta, in ba zaki dauka ba ki bani lambarta ni in kirata mu gaisa." 102 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Nasrin ta hana ta, wayar dai har yanzu kara take yi, kira

Chapter 4 of 7