Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
kwana biyu kawai na yi, aiki ya kawo ni, ina bautar kasa a gidan talabijin ta taraiya NTA." Shamaki ya kama haɓa yana mamaki "lallai kuna shan aiki. Allah Ya taimaka, na gode." yace, Nasrin ta ce, "Amin. Sai da safe.' Suka kashe waya. " Shamaki a zaune Cur ya kwana yana mamakin yadda Malaika ta ke kokarin cusa kanta a wajen manyan mata irin wadan nan, 53 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 yadda ma Nasrin take magana Hausar ma tana kwące mata, turancin Amerika take yi, dakyar in ba girman can ba ce. Lallai Malaika da karfin hali take, ita da ta taso a kauye Allah ya rufa mata asiri ta dawo birni da zama amma tana hangen 'yan Abuja da 'yan kasar waje. Ya ci gaba da tunanin yadda rayuwarsa da ta matarsa zata kasance nan gaba, saboda a kullum kutsa kai ta ke, kuma haduwa da mayan mata take sake yi, tana sake taɓarbarewa a koda yaushe. Ya ci gaba da addu'a Allah Ya sa ta gane. Gari na wayewa Malaika ta tashi da fushi tana ta kunzumawa yara asharai KwandoKwando, wani ya yi kashi a kwance, wani ya yi fitsari, daya kuwa amai ya kelaya mata. Shamaki yana jinsu yana so ya fito ya taya ta yana tsoron masifarta. Ta taho a fusace ta daga labulen falon ta dube shi sama da kasa ta ce, "sannu hamshaki, Shamakin Muntsira wanda bai san wahala ba.Ka zo ka hakimce akan kujera an aura maka baiwa ko? To ka fito ka kula da yaranka gaskiya bazan iya ba da rayuwar talaucin nan, 54 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 dan tsiya ko me aiki ma ba zaka iya samar min ba." Shamaki ya yi murmushi ya fito tsakar gida, yace "ina jin ku ai ina so in fito ina tsoron masifarki." Ta fusata ta koma ɗaki ta kwanta akan gado ta ce, "ga su nan sai ka gyara su kayi musu wanka, kuma na gaji da wankin nafkin pampers zaka siyo min irin na 'ya'yan kowa su yini da ita su kwana da ita." aim 162 1 Shamaki ya gyada kai yace, "Cafdijam! Allah Ya hore." 99 multicl 90cm Ta zabura ta tashi zaune cikin tsiwa ta ce, "Daga anyi magana sai kace sai albashini wani watan. Wai kai nan dan albashi komai sai an yi albashi. Ni fa gaskiya bazan iya ba. Tam no " Yana jinta tana ta bala'i, bai kula ta ba, ya lallashin yaran, nan da nan suka yi shiru suna wasa da dariya ya wanke su tsaf ya shafa [ musu mai ya ɗora musu koko ya basu suka sha,se kanana biyu suka yi bacci ya je ya shinfidar da su sannan shima ya yi wanka zai tafi makaranta dan yana da lacca karfe sha biyu. wy 55 | Jamila Umar Tanko (JUT) (TU) 08 DA MA NI CE... 1 Ya tsaya akan Malaika tana ta danna waya bata kalle shi ba, ya mika mata kuɗi Naira dari biyu ya ce, “ga wannan a yi cefane a sayi ruwa." Ta daga kai ta kalla a shelake, ta ce, "dubu ce ko dari biyu?" Bai batakarɓa ba ya ajiye a gabanta ya fice, yana fita tsakar gida, ya ji ta a guje ta tare gabansa ta ce "wallahi ba in da zaka je sai ka kara min dari uku, kudin cefanena daga yau naira dari biyar ne kullum. saboda kowacce mace kullum sai mijinta ya saka mata katin waya. Idan da ka ce ba wandazan kira yanzu ina da manyan da nake magana da su kuma harkar karuwa ce harda kai. Sannan na gaji da cin mai da yaji miya zan dinga yi da nama kamar kowa. Kai hatta da kayan sakawata canjawazan yi, na gaji da atamfofi kanana, leshina masu tsada irin na su Nasrin zan fara sakawa." " Ya tsaya yana kallonta, yanajin abinda take fada tamkar almara, ko mafarki. 56 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE Ya ja hannunta suka shiga falo suka zauna ya jima yana kallonta ya yin da ita kuma take gatsine- gatsine. Ya fara magana cikin sanyayyaiyar murya. "Malaika! Shin ada a haka muke, ba a kauye muke ba gidan kasa da kara? Allah Ya daukaka mu muka dawo birni har na kama gidan haya na siminti. Da a kauye ba tallar goro kike ba ni nake sayar da rake daga baya na sami aiki har na samu na dawo jami'a? Kika san babban aikin da zan samu idan nagama karatun nan? Haba Malaika, Dan Allah ki nutsu ki yi hakuri na dan lokuta Allah Zai warware mana. Babban tashin hankalina ma shine yaran nan musaminan marar lafiyar nan. Malaika bakya kula da shi kin san yanayin ciwonsa sai da kula. Ki taimake ni Malaika ki taimaki yaran nan. Kin ga Aliyu ya isa shiga makaranta ko Nursery cikin unguwa ina so in saka shi amma asibiti duk ya cinye kudin. ', Yanzu kina maganar in saka miki kudi a waya ki dinga kiran manya. Su waye manya? Kada son zuciya ya kai ki ga fadawa ga halaka." " 57 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Ta zabura ta harare shi sama da kasa ta ce, "zargina zaka fara kuma? Ni Nasrin nake nufi da Dr.hala. " Shamaki ya gyada kai yace, "ba zarginki zan yi ba, Malaika ban taɓa zarginki ba. Amma bai kamata ki fi ganinsu da daraja ba fiye da ni, ni mijinki ne kuma aljanarki tana karkashin tafin kafata. Ban rage ki da komai ba, bakya raga min. Abin ya kai ma mun raba shinfida daga na doso ki sai tsaki da hantara. Menene laifina? Dan Allah Ya halicce ni a talaka? Malaika talauci ne laifina?" Sai hawaye ya surnano daga idanuwansa yayin da Malaika ta kura masa ido itama idanuwanta sun cika da kwalla, ta yi sauri ta mike zata fice daga falon. Ya jawo hannunta ya ce, "kiyi min alkawari daga yau kin daina duk abinda kike yi min. Kiyi min alkawari za ki gyara mu zauna lafiya. Ni kuma na yi miki alkawarin zan ci gaba da fada miki gaskiya da samuna da rashina. Albashin ma duk wata zan dinga kawo miki shi dukka kina kasaftawa, dubu goma sha takwas ne albashin." 58 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Malaika ta fisge hannunta ta fice da sauri ta koma daki ta kwanta. Ya fito yana goge hawaye da takardunsa a hannu, ya hau babur dinsa daya ajiye a zaure, ya tafi. Aliyu ne ya raka shi har kofar gida yana ta cewa “Baba ka siyo min alewa." *** Wayar Malaika ce ta hau kara jim kaɗan bayan fitar maigidanta, tana dubawa taga sunan Shamaki ne. Ta ki dauka gami da yin dan siririn tsaki ta ce,"me zai yi min kuma?" Ya ci gaba da kira sannan ta dauka a fusace ta san dai wani abu zai ce ta saya duk a cikin dari biyu kamar wani kayan gabas. " Ta fada a fusace “ina jinka." Ya yi murmushi yace, “ina cikin makaranta yanzu zan shiga Lacca nace bari in kira ki in ji muryarki gimbiyata." Haushi ya tokare ta, takaici ya baibaye ta yayin da dacin kunar zuci ya yi ta taso mata a makoshi.Ta yi tsaki ta kashe waya. 59 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Ta wurgar da wayar gefe ta kwanta tana takaici, ita fa duk wannan soyayar da zai nuna mata ba zata wadatar da itaba, ba zata zauna ta kare a cikin lungu ba bayan ga mata can suna fantamawa a cikin manyan motoci da manyan gidaje. Ta tuno yadda ta hango Dr.Hala a cikin motarta, ta hango Nasrin yarinya kamar furen fulawa saboda kyau da gayu, ga kamshi. Ta kalli kanta sama da kasa ta ganta kamar wata bushashshiyar bishiyar da ta sanadiyyar fari, wacce ba'a bata ruwa da taki, hakika wataran faduwa zata yi ta zama bushssheshan itace daga nan kuwa sai sara a kwasa akai gida a dafa tuwo ya kone, ya zama toka. bushe a Ta fada abayyane “ba zai yiwu ba wallahi.' " Wayarta ce ta ci gaba da kara ta ma ki kallon wayar balle ta dauka sai a karo na uku ta sa hannu ta ɗauka a fusace ta san Shamaki ne, ta faɗa cikin tsawa bayan ta danna “wai meye?" Sai ta ji wata sanyayyiyar murya mai kama da ta busar sarewa, aka yi mata sallama. 60 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Da sauri Malaika ta cire wayar daga kunnenta ta duba sunan mai kira. 'Nasrin Abdul Nasir' Wai! Rigijigafji!! Zo ku ga murna da ladabi gaba daya ta sauko daga kan gado ta durkusaa kasa. a Malaika ta gaishe da Nasrin. Ta yi mata kirari gami da addu'oin samun nasara rayuwarta. Sai Nasrin ta fara mamakin yadda Malaika ta iya kalamai haka amma bata yiwa mai gidanta. Ta gasgata Malaika tana da cikekken hankali babu taɓin hankali haka tana da ilimi da dubara ba gaɓuwa bace. Ta kudiri niyyar sai ta nemo daga ina matsalar ta ke. Yar jarida me neman labarai. Nasrin tana gyara zama tana juyi a kujerar ofis dinta ita kaɗai ce, dan yau gaba daya abokan aikinta sun fita aiki. Nasrin ta yi murmushi ta ce, "kawata, na kira in gaishe ki ne kuma in ji lafiyar yaranki da mai gidanki. Yaya kuma yaro mai sikila? Ina fatan ya ji sauki.' 99 Malaika ta washe baki ta ce, “lafiya kalau kawata, Allah Ya bar mu tare." 61 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Nasrin ta ce, "amin. Yau fa kira na yi muyi hira sosai dan ba ni da aikin yi." Sai Malaika ta dafe kirji, aka yi murmushi ta tashi bazar-bazar ta dawo falo ta zauna akan kujera aka yi bake-bake, jinta take tamkar da shugaban kasa ta ke magana, ita kuma ta zama minista. "lah dan Allah da gaske kike Nasrin? Amman na ji dadi, ashe kina sane da kiran da nake yi miki kullum? Wato aiki ne yake hana ki amsawa. Na zaci wulakanci ne ma dan kin ganni talaka." " Nasrin ta ce, "haba dai ai ke ma ba talaka bace kyakykyawa dake gashi sunanki mai dadi kuma naga alamar ke jinin sarauta ce ma 'Shamaki'. Ba ni tarihin rayuwarki Malaika." Dadi ya rufe Malaika, ta yi dariya ta ce, "Kwarai nice kuwa jinin sarauta. 62 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... LABARIN MALAIKA Sunana Malaika, sunan mijina Shamaki, sunan garinmu MUNTSIRA,a cikin karamar hukumar Bichi. Mahaifina attajiri ne, mai kudin gaske ga sarauta amma ya rasu, ni kaɗai ya haifa 'yan uwansa suka cinye min gado. Na zo na auri talaka yana ta gana min wahala ni da yarana. Shine nake so ki kawo min agaji nima in fita daga wahalar nan. " Malaika ta fashe da kuka. Sai Nasrin ta yi shiru hankalinta ya tarhi ta kasa tantance mai gaskiya a tsakanin mijin da matar.. Nasrin ta ce, "Malaika daina kuka ki faɗa min abubuwan da mijinki baya yi miki na hakkin aure.' " Malaika ta goge hawayen da daman bai zubo ba ta ce, "gidan haya nake ɗan karami 63 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... mai kunci, daki biyu kanana, idan zafi ya zo ba iska numfashinmu na cikewa, sai ayi wata ba'a kawo wutar lantarki ba, muna cikin duhu ba mu da jannareto, babu ci, babu sha, dari daya yake ba ni ko naira hamsin kudin cefane kuma a ciki zan sayi ruwa. Ga yara uku daya ba lafiya.Kayan jikina a yayyage, kamar almajira, makawabtana ma basa kawance da ni saboda duk sun fini." Nasrin ta girgiza kai cikin damuwa ta ce "bashi da shi ne ko yana da shi ya ɓoye?" Malaika ta cije baki ta ce, "yana da shi. ya ɓoye baya bani sai dai ya kashewa 'yan matan waje da danginsa." Nasrin ta dafe kai dan tausayi, ta faɗa a bayyane "me yasa mazan Hausawa suke da mugunta ne? Allah sarki Malaika, ki ci gaba da hakuri. Kin ji? Ita rayuwar aure lada ne kuma wannan jarabawar itace zata kai ki ga shiga aljanna, idan kika yi hakuri za ki haye.". Malaika ta fashe da kuka ta ce, “shiyasa kika ga ina ta binki rannan da muka haɗu, ko Allah Zai sanima ki samar min aiki a Abuja in samu in rike 'ya'yana. Auren nan ya ishe ni 64 Jamila Umar Tanko (JUT) - DA MA NI CE….. daman kullum cewa yake zai sake ni ya auro wata.' " Nasrin ta girgiza kai ta ce, “kada ki sake ki kashe aurenki, aure daraja ne da shi ki zauna ki rike ‘ya'yanki. Za ki iya sana'a a gida ba sai kin fito ba, Abuja kuma ta yi nisa, ke da kike Kano. Aiki a Abuja kuwa sai ka yi karatu mai zurfi kin ga ke ba kiyi ba." da Malaika ta zabura ta ce, “ai na yi karatu yawa dan nagama sakandire na yi diploma." Nasrin ta zare ido ta ce, “da gaske, ashe kawar tawaba sauki? To gaskiya ko koyarwa ce ya kamata a samo miki anan unguwarku bai kamata ya tauye ki ba.' Malaika ta ce, "ni dai gara in zo Abujar nan in same ki in ma ba aikin ba in kwana biyu nima in ga gari an ce kamar a turai garin yake, ban taɓa zuwa ba. Sai dai makwabciyata ce suke hutu acan idan ta je ta dawo sai ta dinga yi mana yanga, da jijji da kai. Ina so nima in je Abujar nan, Nasrin ki taimaka min.” Nasrin ta girgiza kai ta ce, "kullum ina fama da aiki amma karshen wani watan za mu shigo Kano aiki zan neme ki sai mu ga yadda 65 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 za'ayi. Yanzu zan turo miki da katin Naira dubu uku ki siyar ki rage wata matsalar, amma dan Allah kawata ki kula da hakkin aure, ki ci gaba da hakuri watarana Shamaki zai gane kurensa idan shi ya cuce ki, ai Allah ba azzalumin sarki ba ne.99 Malaika ta fara shshshekar kukan karya tana godiya. Suka kashe waya. Malaika ta daka tsalle tana rawa tana murna Aliyu ma ya taho da gudu yana taya ta suna ta rawa suna murna duk da bai san me yake faruwa ba, ya san tabbas yau Mamarsa na cikin farin ciki saɓanin kullum da ta ke cikin fushi tana kyararsu da zagi. Ba'a jima ba sai ga sako ya shigo wayar Malaika tana dubawa taga sakon kati daga Nasin, sai ta dauki mayafi ta fita wajen mai sayar da kati na kofar gidansu, anan ta siyar ya bata kudinta ta shigo gida tana ta fara'a, babu sauran fushi kuma ayau. Ta yini tana lissafin abubuwan da zata saya da kudin nan Naira dubu uku saboda bukatarta tafi ta dubu talatin ma. Tana son ta yi 66 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 dinkuna, tana son jaka, tana son takalma da mayafai, tana so ta fara saka tabarau (glasses) a fuska irin na Nasrin da Dr.Hala, itama ta zama 'yar gayu kamar su. .Da misalin karfe huɗu da rabi na yamma Shamaki ya fito daga cikin masallacin B.U.K bayan ya idar da sallar laʼasar, sai ya ji wayarsa na kara ya dauko ya duba lambar, lamba ce kayatacciya kai kace mai lambar tsarata ya yi da kansa,daga gani babu tambaya lambar ta daban ce, musamman daga kamfanin MTN, sai ya ga kamar ya taba sanin lambar amma ba zai tuna in da ya san ta ba. Gabansa na faduwa ya amsa yana mai addu'a ko waye mai kira Allah Ya sa alkhairi zai fada. A lokaci guda suka yiwa juna sallama cikin girmamawa. Shamaki ya yi shiru yana jiran mai kira ta gabatar da kanta, kuma ta fadi dalilin kiran. 67 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... Ta ce, "sunana Nasrin Abdul Nasir daga Abuja. Ina fatan ina magana da Shamakin Malaika?" Shamaki ya yi mamaki gami da farin ciki sai ya amsa "Eh nine." Yana tafe yana magana ya gaggauta barin jikin masallaci ya koma can gefe ya sami bishiya da kujerar zama ya zauna suka ci gaba da Magana, ya tabbatar tunda Nasrin ta kira shi da akwai wata magana mai muhimmanci. M ✓ Bayan sun gaisa Nasrin ta yi ajiyar zuciya ta ce "Jiya ka kira ni a da daddare na fara bacci, shiyasa na kira ka yanzu. Kafin in shiga cikin irin wannan magana musamman magana ta maʼaurata ya kamata in dan san wani abu daga cikin rayuwarku ko da kuwa kadan ne, ba sai dukka ba.” na 37 Shamaki ya gyada kai yace, "haka ne Nasrin. Ki saki jikinki mun baki amanar kanmu,mun yarda da ke ki tambaye ni komai da kike son sani in Allah Ya yarda zan amsa miki." Nasrin ta yi murmushin jin dadi ta ce, "na gode. Malam Shamaki zan so in ji 68 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 labarinka dana Malaika, da yadda ku ka hadu har ku ka yi aure. Shamaki ya ji dadin tambayar nan sai yace, "Malama labarin da tsayi sai dai in kin shigo Kano mu zauna saboda kudin wayarki zai kone da yawa." Nasrin ta yi dariya ta ce, "kada ka damu kuɗin wayata zai isa mu yi ta magana daga yanzu zuwa gobe da safe ba zai kare ba.” " Shamaki ya gyaɗa kai ya yi jinjina ya faɗa a ransa "babban goro sai magogin karfe, sama ta yiwa yaro nisa sai dai ya ɗaga ido ya hango ta. Allah Ya yi mana arziki ta hanyar halal. Amin.' " Shamaki ya yi ajiyar zuciya gami da gyaran murya, yaci gabace, “to ba damuwa bari ki ji cikekken tarihina da na matata Malaika. LABARINSHAMAKI: Yace "sunana Yusuf Muhammad Yusuf, sunan garinmu MUNTSIRA garinmu bashi da nisa da karamar hukumar Bichi, cikin jihar Kano. Na ci sunan Kakana Yusuf shi kuma 69 | Jamila Umar Tanko (JUT). CE... 1 yana da lakabi da ake kiransa Shamaki, Mafarauci ne kuma gwarzo a wajen sana'arsa. Shiyasa nima ake kirana da Shamaki karami,ko a makaranta Shamaki Yusuf Shamaki nake rubutawa. DA MA NI Na tashi a maraya mahaifina ya rasu tun ba'a yaye ni ba kuma nine ɗansu na fari, mahaifiyata ce kadai ke da rai, ana yaye ni sai Kakana Shamaki ya dauke ni, a wajensa na girma. Mahaifiyata ta je ta yi wani auren ta haifi kannena maza biyu, Kasim da Hashimu, da mace daya 'yar autarmu mai suna Sadiyalle. Babu abinda Kakana ya iya sai farauta abinda ya koya min kenan, da girmana na shiga makaranta boko amma na yi zurfi a karatun allo, babu wanda ya saka ni a makarantar boko,da naga abokaina suna zuwa nima abin yake bani sha'awa na ke binsu. Na gama firamare na shiga sakandire,daga garinmu da kafa nake zuwa Bichi makaranta, in je in dawo babu abinci, babu kudin tara, kayan makarantata ma a yayyage sai dai idan 'yan ajinmu sun tausaya min sai su bani tsohon 70 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 nasu, haka takalmana sun fatattake saboda tafiyar kafa. Cikin ikon Allah duk wadanda muka fara karatun tare tun ba'aje ko in ba suka watsar da karatun a takaice dai a wannan lokacin ni kaɗai ne nagama sakandire a kauyenmu. Nima sai na yi kamar zan bari Malamin ajinmu ya zo har gida yayi min nasiha dole in koma ba dan ina so ba saboda da ni ake ji a makarantar ina da kokari sosai. Kokarin da nake da shi ba irin wanda za'a ce na daya yake zuwa ba kullum, A' a kokarin da zan gagari Malamai ina kokarin kure Malam a aji, idan aka yi jarabawa babu dalibin da yake samun maki kusa da nawa sai dai can kasa dan ni a kowacce jarabawa casa'in zuwa casa'in da tara nake ci a cikin dari. Mutane har gani suke ko ni ba mutum ba ne ba ma. 29 Nasrin ta gyara zama ta ce, “dakyau shamaki ina jinka.' " Ya yi murmushi ya ci gaba da cewa, "Na fito da sakamakon jarabawa mai ɗankaren kyawun gaske. Malamin nan na ajinmu ya yi iya kokarinsa wajen ganin gwamnati ta dauki 71 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 nauyin karatuna zuwa Jami'a, Ciyaman din garinmu na wancan lokacin ya ce zai taimaka min amma basu mayar da hankali ba, sun yi alkawari ba su cika, ba har aka canja gwamnati. Na hakura da maganar karatu na ci gaba da sayar da rake a kofar gidanmu, sai daga baya ina ta fadi tashin neman aiki bayan shekaru sannan na samu aiki a sakateriyar Bichi, anan nake aiki har yanzu da satifiket dina na sakandire.' 99 . Nasrin ta gyada kai ta ce, “da kyau. Malaika fa? Wacece Malaika?" LABARIN MALAIKA: • Yace "Malaika Dahiru Muntsira, garinmu daya layinsu a bayan layinmu yake,tare muka tashi mun girme su amma dai dukka an yi wasa tare. Babanta Malam Dahiru shine mai garin garinmu Kuma yana da mata huɗu da yara da yawa, ko a ɗakin su Malaika ma su tara mahaifiyarsu ta haifa." Nasrin ta cika da mamaki ta bude baki ta kasa rufewa dan mamaki. 72 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya jikan Malam Dahiru." Shamaki ya zabura, yace, "ai bai rasu ba yana nan ya dai tsufa, ai ita ‘yar gatace da uwarta da ubanta a raye." Sai Nasrin ta zazzare ido tana mamaki dan ta fara jin banbance-banbance a tsakanin labarinsu, tabbas akwai makaryaci a cikin su biyun nan amma dai bari sai taga abinda zai turewa buzu nadi. Ta yi gyaran murya ta ce, "Allah na zaci ya rasu ne, Allah ya kara girma." Shamaki yace,"Amin. To kasancewar mu a kauye, dan sarki da talaka duk talawa ne kowa na yakin neman abinda zai ci, suma a gidansu akwai tsabar gero da masara ammafa mahadin dahuwa kowacce ita zata nema da yaranta. Haka muka taso kuma muna jin daɗin rayuwarmu kamar kowa, Allah ya jarrabe ni da son Malaika itama tana sona sosai har ma fiye da yadda nake sonta. Ban taɓa yin budurwa ba a rayuwata sai Malaika ita kadai na taɓa ji ina so har a cikin raina, haka itama ni kadai take kulawa. Mahaifinsu yana tilastawa 'ya'yansa sarki ai 73 | Jamila Umar Tanko (JUT) _ DA MA NI CE... 1 mata da maza su yi makarantar firamare kasancewarsa mai gari dole sai an ga yaransa suna zuwa makaranta sannan 'yan gari zasu yarda su bar nasu 'ya'yan su je, dan haka Malaika ta gama firamre tas, ni na je na sami babanta na bashi shawara ta tafi sakandire ni zan dinga yi mata siyayyar makaranta da yake Makaranta kwana ta ci. Ya amince Malaika ma bataso na lallashe ta, dan bata son ɓacin raina aka kaita makarantar kwana ta garin 'Dan zabuwa' nan kusa da garinmu.Garin kwaki, Kanzo, maggi, man gyada, gishiri sune dai siyayyar nake siya mata, idan ya kare ta yi min wasika wani Malamin makarantarsu ya kawo min in siya in bashi ya kai mata. Idan kuma ranar ziyara ta zo wato bisiting ni nake je mata, kawayenta kakaf sun san Malaika da Shamaki, dan soyayya ma haka ta mayar da sunanta a makaranta ba'a kiranta da Malaika Dahiru. A garinmu kowa ya san soyayyata da ita, samarin da suke sonta da yawa mun sha tare ni dambe a hanya suna ganin a dalilna ta ki su, haka itama ta sha 74 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 dambe da 'yan matan da suke matukar sona bana kula su. Ina sana'ar Rake bana tsinanawa kaina komai a jikin Malaika nake karewa, dangina suna ta zagina hatta mahaifiyata sai da ta fara jin zafin haka takan kira ni ta yi min fada, ina tabbatar mata wani abin ma karyar 'yan gari ne ba ayi ba. Sai da na zamar da Malaika abar kwatance a cikin kawayenta, ni ne dinkunan sallarta, ni ne ankon bikin kawaye da danginta, ni ne kudin kashewarta, ni na bata jarin da take sayar da wainar fulawa da awara a kofar gidansu idan tadawo hutu. Malaika tana da kokari matuka kuma na yi kokarin koyar da ita abubuwa da yawa idan an yi hutu, hatta turanci ni nake koya mata. Har ya zamanto ta fi kawayenta iya turanci, sai ayi ta mamaki idan aka ji tana turanci. Tana matukar jin maganata kasancewar tana da tsiwa da taurin kai dan wani lokaci sai mahaifiyarta ta kira ni a kawo min kararta in yi mata fada sannan ta bar abinda ta ke yi. Tana aji hudu na sakandire Mahaifinta yace ta isa 75 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 aure za'a cire ta in zo in aura idan kuma bana so zai yi mata miji, dan ya ji na fara rokarsa ya bar ta, ta kamala sakandire. akan A dole na fito aka yi aure daman na daɗe ina taron kayan auren. Dakin kasa guda daya jal Kakana yaba ni,anan muka zauna shi kuma da matarsa suna cikin daki daya. A haka muke zaune ban dade da yin aure ba na sami aiki a Bichi ake biyana albashi daga nan rayuwarmu ta dinga ci gaba. Mun fi karfin ci da sha da sutura sannan a hankali na yaɓe gidan kasarmu da siminti, na cire katagar kara na yi Katanga ta bulon kasa, muka ci gaba da zama na soyayya har Allah Ya ba mu haihuwa yaronmu na farko Aliyu, muka haifi na biyu na saka masa sunan kanina Kasim. A lokacin ne abokina yaba ni shawara muka je muka zana jarabawar Jamb, muka cike B.U.K. Abokina ya SO in karanci Likitanci(Medicine) na ki amincewa saboda shi ya san zan iya amma ni ina ganin ba ni da damar da zan jure karatun likita saboda ga iyali, ga aikina, zan fito in je neman abinda zan ci dole. Na cike kos din Biochemistry, Allah 76 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 cikin ikonsa ranar jarabawar Jambmuka je muka zana kuma na ci da yawa, abokin na kuwa bai ci ba. Nan da nan da gudu suka ba ni abinda na zaɓa daman sakamakona na sakandire ya yi kyau. Na nemi izini daga wajen aikinmu suka bar ni na tafi da albashina (inserɓice) ko da yaushe da babur dina nake zuwa daga Bichi zuwa Kano, in yi lacca in koma, da na ga da wahala sai na yi adashi na hada da rance na zo na kama mana gida anan Kano,a unguwar Dorayi akan Naira dubu talatin da biyar haya a shekara. Na dauko iyali muka dawo yanzu haka muna cikin shekara ta biyu kenan, anan aka haifi dan autan danmu Ahmad, kuma Allah Ya yi shi yana da sikila. Gashi dai ana ta faman zirga-zirgar zuwa asibiti.' Nasrin ta yi shiru tana mamaki wannan labari mai kama da almara, ta ji talauci tsantsa dan ita bata san irin wannanrayuwar ba. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “idan na lura Malaika na sonka kuma tana yi maka biyaya ko? Menene laifinta yanzu?" 77 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Ya yi dariya yace, "Jama'a da yawa tun a garinmu suna ta maganar cewa Malaika tana yi musu kallon banza, dan ta auri miji yana yi mata hidima, da na fara aiki ta fara miya da nama sai abin ya karu har 'yan uwana da 'yan uwanta suka shiga layi suna ta jin haushi wai Malaika na wulakanta su in an je gidan sai taga ḍama ta kalli mutum, in dai ba da kai zata karu ba bata kawance da kai. Ni dai ban gani ba dan bata yi a

Chapter 3 of 7