Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
Ya yi mana yatsu wani ya fi wani girma dan mu san ba daidai kowa ya ke ba, wani ya fi wani. Dan haka dan na raɓi mai kudi dan in sami danshin inuwa ban yi laifi ba." Shamaki ya damke hannu ya ji tamkar zai kai mata naushi, sai ya fasa saboda tsantsar takaici. Ya rasa amsar da zai bata, kwalla ta cika masa ido ya yi tsaye yana hangenta tana zaune a falo, ta dora kafa daya kan daya tana girgizawa. Yace "Malaika! ki je ki nemo maganin jahilci dan wannan ciwon yana damunki. Sau biyu ina sayo miki fom din makarantar matan aure sakandire ta ya ki da jahilci kin ki shiga. Na siyo miki na islamiyya kin ki zuwa. Kin gwammace kina ta yawo a gari kina kallon masu ilmi kina sha'awa." Ta murguda baki ta ce, “ka je ka nemo maganin talauci dan talauci na damunka kai kuma. " 26 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Yace "na godewa Allah a yadda ya bar ni dan na fi wasu, da yawa a jikina suke cin abinci. Ko a haka na dauwama Allah Ya yi min komai da Ya bani imanin sanin Sa da yarda dakaddara. A koda yaushe bakya taɓa kallon na kasa da ke sai wadanda suka fi ki dan haka ba zaki taɓa godewa Allah ba. Kin fi wasu, wasu kuma sun fiki." Ta ce "ko a layin nan ma kowa ya fi mu. Yanzu baka jiyo karar Jannareto a gidan Alh. Ayuba ba? Toda shi suke kwana da shi suke yini mu kuwa fa ko injin ba mu da shi. Gidan haya daki biyu kanana." "A'uzubillahi minal shaidanir Rahim. Innalillahi wa'inna ilaihi 2 raju'un. Allah Ya sa fada a lokacin da ya yi a gaban mahalaccinsa, dan abin na ta ya shallake tunanin mai hankali. Malaika ta murguda baki ta ce, "a kanka, ki gane. Shamaki saranda ya mika ya wuya dan ni ba shaidan ba ce.' Shamaki ya fada cikin sanyin jiki "zo kiyiwa Kasim tsarki, ga ruwan wanka nan na dora kiyi musu. Ni zan karasa dafa abincin." " 27 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Malaika ta girgiza kai ta ce, "wallahi a gajiye na dawo ga yunwa bazan iya ba, ai na sha cewa ka dauko min masu aiki ka ki. Ni ba baiwa bace, gidan kowa da masu aiki." Yace "Sai dai in auro mai kular min da yara tunda kin gaza.' " Ta zabura ta dire Ahmad a kasa akan leda a fusace, “garaka yi auren ma da ka taimaka min dan kana yin aure fitazan yi. Haka kawai da me zan ji da talaucin ko da fada da kishiya?" Shamaki ya shiga kicin da sauri ya gyara murfin tukunyar da take bori, ya fito da sauri ya dauko Kasim akan fo zai je bandaki ya yi masa tsarki, yayin da Aliyu ya calla ihu ya yar da taɓarya ya rike ido barkono ya fallatso masa a ido. Yara ukun gaba daya kuka suke yi. Shamaki ya zama kamar zautacce ya yi nan da gudu ya lallashi wannan ya dawo ya lallashi wancan. Malaika na zaune lambar tana ta kiran wayar Nasrin bata dauka ba, sai sake kira ta ke, gami da tura sakonni tana mai gabatar da kanta dan ta gane mai kira, duk da haka bata amsa ba 28 Jamila Umar Tanko (JUT). DA MA NI CE….. 1 alhali kuma wayar tana shiga. Ranta idan ya yi dubu ya ɓaci, ta rasa in da zata saką ranta. DA MA NI CE... 1 BABI NA BIYU BAYANKWANAKI UKU.... KANO a misalin karfe takwas da rabi na dare, Shamaki da matarsa ☐ Malaika suna zaune a falo, yana karatatun jarabawa yayin da ita kuma take cin soyayyen kifi tana kallon talabijin, yara sun yi bacci. Wayarta ce a caji take ta ɗau kara, da gangan ta ki ta dauka dan ko tantama babu ta san Saude mai siyar da atamfofi ceke kira, dan wata ya kare bata biya bashin da ta dauka ba. Shamaki ya kalle ta, ya juya ya kalli wayar, ya sake juyawa ya kalli matarsa. Malaika ta sha kunu ta ce, “Saude ce mai kayan siyarwa, ban biyata bashin dana dauka ba dan kudin da ka bani na kashe sai wani watan zan biya." 30 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE...1 Ya dauko wayar ya karanta sunan mai kiran a Abdul Nasrin. " duba sunan ya bayyane 'Nasrin Bai rufe bakinsa ba ta zabura ta kwaće wayar ta mike tsaye a gigice har da dukawa sannan ta danna. "Nasrin ta yi murmushi ta ce, "Kawata Malaika nice. Yi hakuri na ga sakonninki mu na ta aiki dare da rana sai yau da rana na dawo Abuja. Na kira in shaida miki yau za'a saka hirarmu da ke a labaran NTA na karfe tara, na faďa miki ne dan ki gani. " Lah kawata, Nasrin kece?" Malaika ta dinga tsalle tana murna tana godiya. Nasrin ta kashe waya, yayin da Shamaki ya rasa abinda su ke nufi, sai da ta wayar masa da kai sannan ya fahimta. Amma a zatonsa tatsuniya take ba gaskiya ba ne dan haka bai ce da ita komai ba, sai da aka fara labarai ya ga matarsa tsumu-tsumu cikin tsumma tana bayanai ga kyamusasshen ɗansa akan cinyarta yana kyallara ido sannan ya tabbatar da gaske take. Sai ya fara salati yana hada ta da Allah ya isa, ta cuce shi. 31 | Jamila Umar Tanko (JUT) ... 1 Bakinta baya mutuwa kuwa, sai kare kanta take har ma tana shaida masa in ya ga dama ya sake ta ta koma aikin jarida. Kan kace kwabo jama'a da dama sun ganta ana ta kiransu a waya ana sanar da su an ga Malaika. Murna take tana adarwa, ana ta taya ta murna. Yayin da shima 'yan uwa da abokai suke kiransa suna neman karin bayani, ya ma kashe wayarsa dan takaici. Suka yi ta musanyan yawu shi da ita, kai kace wuta zata fito daga bakunansu su kona junanansu. Sai dif aka dauke wuta ma,amma a haka cikin duhu suka ci gaba da yagar juna. Yau sai da ya ji a ransa da zai iya sakinta da ba zata kwana a gidansa ba, to Allah Ya hada shi da wani masifaffan ciwo wai shi So. Yana sonta a ransa, da kuma babu yadda zai yi da yara idan idan ta tafi ta barshi da su, mahaifiyarsa ta tsufa babu mai rike masa su. Ga aiki ga karatu ba zai iya zama da su ba da sai ya raine su har su girma. Ya ga da gaske Malaika hada kaya take zata tafi gidansu, ya shiga lallashi yana bata baki akan shi bai ce zai sake ta ba amma bata 32 Jamila Umar Tanko (JUT). DA MA NI CE... 1 kyauta masaba ne, tamkar bara take tana neman taimako alhali shi kuma bai gaza ba. Gashi yanzu ta jawo masa gori a wajen abokai, waɗanda basu santa ba zasu ga sunansa raɗai an rubuta kowa ya san matarsa ce. - Ta ce ita kawai ta gaji da zaman ne. kawai gara ta tafi, yanzu gashi ko gama nunawa ba'ayi ba aka dauke wuta, basu da injin da zasu kunna su ga haske. Sai da ya yi mata alkawarin Janareto wani watan, sannan ta hakura ta fasa tafiya. Yana kwance yana hawaye cikin dare ya ma kasa karatun jarabarwar da yake da ita gobe da sassafe. Asuba ta gari! 33 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... BABINAUKU: ABUJA Kwannan arfe huɗu da rabi na yamma, Nasrin ta jawo wayarta cike da sanyin jiki ta kira lamba mai matukar muhimmanci a wajenta. Bayan tsawon watanni biyu cur tana kiran lambar bata cin sa'a dan ba’a ɗauka kuma tana shiga, sai yau aka amsa mata. Ta ji farin ciki tamkar an jefa ta a gidan aljanna dan murna. Cikin zumudi ta yi salama, sautin wata kamilalliyar murya ce ta daki kunnenta. Ta gaishe shi cikin ladabi, ya amsa cikin mutuntawa gami da ambaton sunanta 'Nasrin'. Ta tambaya cike da mamaki "Dr.Jalo, daman kana da lambata amma na sha kira baka dauka?" Jalo ya yi sanyayyiyar dariya, yace, “tun ranar da muka yi musanyan lamba na ajiye ta da sunanki a wayata, amma ban cika amsa wayaba. 34 | Jamila Umar Tanko (JUT) () xTacos![] DA MA NI CE... 1 ne, ban ma cika bude wayar ba ma a rufe take yawanci." Ta lumshe ido ta ce, "sannu da kokari.Aiki ya yi maka yawa ko? Kana wanne gari ne?" Bai amsa mata ba sai ya yi shiru, nan da nan ta canja tambaya ta ga alamar ba shi da niyyar amsa mata. Ta lumshe ido, ta ce, "rubuce-rubucenka suna birge ni ina so in shahara in kware in zama kamar ka a harkar rubutu. 99 Ya yi murmushi yace, "ko? Allah Ya sa ki fi ni ma." Ta kyalkyale da dariya ta ce, “anya kuwa? Ban isa in kamo kaba ma, ranka ya dade." Ya yi sauri ya katse hirar yace, “to na ji dadi da kiran da kika yi min kuma na gode Allah Ya bar zumunci. Sai mun yi magana wani lokacin." Bai jira amsarta ba ya katse waya, yayin da Nasrin ta sankare a zaune nanike da waya a jikin kunnuwanta.Can da aka jima ta ajiye wayar cikin sanyin jiki, hakika ta ji ba dadi a 35 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 zuciyarta, amma da ta tuna babbar sa'ar data ci ta samu ma ya amsa wayar yau, sai ta godewa Allah. zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Ta jawo 'konfiyutarta' ta budo hotonsa a 'facebook ta daɗe tana kallon hotunansa shi da wani yaro dan kimanin shekaru hudu, kyakykyawan yaro da alama dai dansa ne dan suna kama kuma da shakuwar da suka yi. Ta daɗe ta na kallo kuma tana karanta rubutunsa (posts), hakika wannan bawa, Ubangijinsa Allah Ya cika shi da tsantsar basira da cikakken ilimi. Kalamansa yana nunawa tabbas tsantsar masani ne haka babu kalmar da bata da amfani a cikin rubutunsa. Idan kana biye da shi lallai zaka karu ta fannin addini balle a zamantakewa, haka idan kana da ra'ayin siyasa zaka ginu akan adawa mai maʼana da tsari, babu gaba babu cin mutunci. と 'Mu je Ta shiga cikin sharshin da jama'a suke rubutawa a kasan rubutunsa (comments). Da alama yawancin abokansa na facebook sun san shi a zahiri dan ta lura su kan tsokane shi shima ya tsokane su, suna kiransa da Dakta ko likita. 36 Jamila Umar Tanko (JUT) , DA MA NI CE... Daga nan ta tambatar da cewa da cikakken likita take tare, lallai dole Jalo ya yi tsada a waya ma balle a ido biyu. Ta ji ya daɗa kwanta mata a rai ba dan su yi soyayya ba tana sha'awar yin mu'amula da shi dan ta karu a harkar rubutunta na jarida. Ta nemo shi a ɓangaren watsappsda lambarsa, sai kuwa ta ci sa'a ta same shi da wannan lambar da suke magana. "Madalla da social Network".Nasrin ta faɗa a bayyane, yayin da take tsalle a kan gado. Wuyanta ya kage sai ta kwanta akan filo ta yi ruf da ciki ta ci gaba da kallonsa a hoto, sai dai taga ya ɗaɗe rabonsa da hawa watsapp tun watan jiya. Ko meye dalili? Oho! Data leka ‘instagram'ma ta haɗu da shi acan, amma fa mutumin akwai ruwan turanci, irin turancin da wata kalmar sai ka koma ka binciki ma'anar a dictionary.. Sai ga rubutunsa da larabci ma da yake ita ma gwanar larabci ce sai da ta karance tsaf, Ko a ina ya na magana ne akan ci gaban arewa, yana kira da musulmai 37 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE 1 su haɗa kawunansu,ya na magana akan a daina siyasar gaba da dabanci. Nasrin ta shiga mamaki tana tambayar kanta da kanta “me ya haɗa likita da rubucerubuce irin wannan? Tsabar kishin ' yarensa da Addininsane ko kuwa menene?" Bata tsahirta ba sai da ta ji an kira sallar magriba ta tashi ta shiga bandaki ta yi alwallah ta fito ta yi salla, bata tashi daga kan abin sallar ba sai bayan data yi sallar isha'i amma tana idarwa ta dawo kan laptop ta ci gaba da bibiyar Dakta Jalo. Karfe tara saura kwata ta ji ana buga mata kofar daki sai ta ji ranta ya ɓaci dan za'a katse mata hanzari, dan haka ta ki amsawa ta san yayarta ce Zainab zata dame ta akan ta fito ta ci abinci ita kuwa ba abincin dare take ci yanzu ba. Har yanzu ba'a daina bugawa ba sai ta ji muryar Dinah babbar kawarta kuma aminiyarta ce. Ta yi mamaki da jin muryarta a daidai wannan lokaci, ta yi sauri ta mike ta bude kofa, suka rungume juna suna murna, bayan sun shiga cikin ɗakin suka zazzauna a gefen 38 | Jamila Umar Tanko (JUT) NI CE... 1 gado.Dinah ta kalli laptop taga garjejen hoton Jalo ya cika allon, 'sceen' din. DA MA Ta zazzare ido ta tambaya cike da mamaki "Nasrin! Waye wannan?" Nasrin ta harare ta, ta ce, “dube shi da kyau dai. Ba ki gane shi ba ne? Jalo ne fa, mutumin da nake nuna miki rubutunsaa jaridu da facebook. Me Dinah ta gyada kai ta ce, “eh na tuno shi. ya faru kuma?" Nasrin ta yi dariya ta ce, “ba komai abokina ne kawai a facebook. Albishirinki! Yau kuma na ci sa'a ya amsa wayata, kinsan baya ɗaukar waya ran nan ba muna tare ba nayi ta kirabai dauka ba." mamaki. ah ta yi sororo tana kallonta cike da Nasrin ta daki kafadarta ta ce, “ke wai mamakin me kike yi ne wai?" Dinah ta yi ajiyar zuciya ta ce, "mamaki kike bani dai, wannan ba halinki ba ne. Yaushe kika zama marar aji har kike bibiyar mutumin da baki sani ba haka, har yake ja miki aji." 39 Jamila Umar Tanko (JUT) CE... 1 Nasrin ta yi dariya ta zungure ta da gefen hannu ta ce, “ke dalla ki kwantar da hankalinki ba wani abu ya hada ni da shi ba, nacin da nake yi masa dan in karu da shi ne kin san zama da irinsu akwai karuwa musamman ni da nake bautar kasa a harkar aikin jarida ina so in san makamar aiki.' " DA MA NI 66 Dinah ta harare ta, ta ce, ina joseph Bawa, ina Mathew Haris na ofis dinku? Ba tare ku ke ba kuma suna koya miki aiki yadda ya kamata ba? Ba sai wani a facebook wanda baya son yin mu'amula da ke ya koya miki ba, ba ki san ma in da yake ba. Ko ya fada miki?" Nasrin ta ɓata fuska da alama ta yi fushi. Dinah ta zabura ta mike gami da jan hannunta ta ce, “tashi ni ki raka ni zan tafi, tare da sweetheart dina nake ya kai ni Shoprite na siyo shafawar nan da nace zan fara shafawa wanda muka ga tallarsa a settlite. mans " Nasrin ta ja ɗankwali ta ɗaura suka fito falo suka iske Anty Zainab tana kallon talabijin. Dina ta duka ta yi mata sallama suka wuce har sun kai bakin kofar fita daga falo. 40 | Jamila Umar Tanko (JUT) Gy DA MA NI CE... 1 Anty Zainab ta ce, “Dinah! kin sami ladan kawarki da kika fito da ita daga daki, tun da la'asar ta rufe kanta ta ki ta fito gashi ni kadai Ogana bai dawo ba sai sha dayan dare." Dinah da Nasrin suka yi dariya. Dinah ta ce, "na ga alama bincikenwani abu aka bata a wajen aiki. Nasrin ta ce, “kada ki damu bari in raka ta in dawo. Antimi Zainaba kin ji?" Suka isa wajen dankareriyar motar, Adam yana ciki a zaune, bayan ya rage gilashi wundo sai suka gaisa da Nasrin, kowannensu cike da fara'a. 00 Nasrin ta yi dariya ta ce, "kuna son junanku kullum kuna tare a gida da ofis. Wai me zai hana ayi bikin nan a cikin shekarar nan daga mun gama bautar kasa." Adam da Dinah suka kwashe da dariya, da alama Nasrin ta soso musu in da yake yi musu kaikayi. Sai suka kalli juna daman kamar ta yi duba shawarar da suke yi kenan. Adamyace, “kamar kina duba yanzu fa maganar da muka gama kenan, amma tare da aurenku ke da Fu'ad za'a hada. 41 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Nasrin ta yi dariya ta ce, “sai ya koyi zaman Nigeria sannan za mu yi aure." . " Adam ya ce, "wallahi Engineer Fu'ad ya fi ki son zaman kasar nan amma ana bukatarsa a Embassy Amerika, shiyasa kullum yake bisa. hanya, shi yake taimakawa Daddy da aiki. To ke meye damuwarki tunda kin kusa gama bautar kasarki ba sai ku yi zamanku a can ba?" Nasrin ta taɓe baki ta ce, “Ba na son zaman Amerika,a tattakure na daure na yi shekaru ukun nan inagama karatu na garzayo gida, ni fa babu kasar da na fi son zama irin kasata Najeriya." Dinah ta yi murmushi ta ce, "uwar iya yi, Engr. Fu'ad yana hakuri da ke komai sai kin yi iya yi." " 916) 600 sa gilid ive bus. Nasrin ta harare ta ce, "au daman har na kai ki iya yi?" il refund emey aum sys denisb usbA Adam ya yi dariya yace, “za ku zo ɗaya dai, ai daman kawaye min kwainane da yawa. me mSIS SO ne. Kawai dai Engr.Fu'ad ya fi ni hakuri ne shiyasa ni ba'ayi " Iswede adub vs symsbA 42 | Jamila Umar Tanko (JUT) 8 ននមុន ม ถอus pe A DA MA NI CE... 1 Su ka yi dariya su dukka, ya ja mota su ka tafi. Nasrin tana daga musu hannu har suka fita daga get din gidan. Nasrin ta dawo gida cike da fara'a ta iske Yayarta Zainab har yanzu kallo ta ke yi ita kadai. Ta fara bawa Zainab labarin yadda suka yi da Dinah cewar sun kusa yin aure, Adam ya ce a hada bikinta da fu'ad. Zainab ta yi farin ciki da jin haka ta yi mata fatan Allah Ya sa ayi cikin shekarar nan ta 2011. Nasrin ta taɓe baki ta ce, “ba Amin ba, sai Fu'ad yagama yawon kasar wajen ya dawo gida ya zauna tukunna in za'ayi ayi, dan ni ba zan yi aure a turai ba rayuwar ba dadi." Zainab ta harare ta ta ce, "iyayenki suna can kina cewa ba zaki zauna a kasar ba, ke ai gida ne." Nasrin ta ce, "na fi sha'awar kasata Nijeriya." Ta tashi ta shiga daki tana tafe tana girgiza ko ba komai ta san ta bada haushi haka kuwa aka yi Zainab ta bita da harara. 43 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Tana shiga daki ta iske wayoyinta dukka uku an kirata, kuma da lamba ɗaya ce, tana dubawa taga Fu'ad ne, bata yi mamaki ba saboda yanzu ne daman lokacin da ya saba kiranta amma kuma ya kira da wuri ta san ba zai wuce maganar da suka yi da Adam ba ne har ya kyankyasa masa. Ta zauna a gefen gado tana duba wayoyin sai ya sake kira, nan da nan ta amsa. Ta yi fari da ido ta kashe murya ta ce, "Hallo darling." Ya lumshe ido yace, "Hi sweet." Kafin ta gaishe shi cikin zumudi ya fada "na ji sakonki." Ta yi dariya ta ce, "ya yi kyau. Ashe har an kyankyasa maka? Kai! Adam dan tsurku ne. " Fu'ad ya yi dariya yace, “tsurku ko gaskiya. Kawai dai na lura koda yaushe kina so ki yi ta tayar min da hankali. Amma yaya muka yi da ke? Ba cewa aka yi zaki gama bautar kasa ba ki dawo Amerika mu yi aure ba kiyi digiri na biyu 'masters ki nemi aiki ba?" 44 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Nasrin ta dafe kai ta ce, "Darlin! Na dawo daga aiki kaina ya yi min nauyi, ka bari za muyi maganar da week end ina son hutu yanzu. " Ya yi dariya yace, “ba damuwa gimbiya yau babu doguwar hira kenan?" Ta ce "kwarai ina son hutawa.' Ya ce "sannu kina kokari ma, dan ban zaci zaki iya ba." Su ka yi sallama suka kashe waya, ta tashi ta shiga bandaki, wanka da alwalla ta yi ta fito, ta yi sallar nafilfili sanna ta saka kayan bacci ta koma kan gado ta kwanta ta jawo laptop ta ci gaba da bibiyar Dr. Jalo. Sai kuwa ta ci sa'a ta gan shi akan layi (online)a facebook. Cika • Ta da murna cikin zumudi,hannunta na karkarwa ta rubuta sallamata tura masa, sai da ya dauki awa guda sannan ya ba ta amsa ya tura mata Wa'alaikissalam. Yana amsawa kuma ya fita, jikinta ya yi sanyi. Har yanzu tana ta karanta sabon rubutun da ya turo (post), ya yi magana akan illar 45 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE….. 1 almajiranci da maula a kasar Hausa wanda ya zama ruwan dare. Abokansa na facebook su nata ruwan sharhi (comments) sai ita ma ta tura nata dogon sharshin. Gogan na ta dai bai amsa musu ba, ya tafi abinsa. Ta kai karfe dayan dare tana karancekarance akan rubuce -rubucensa sannan ta kwanta amma ba dan tana jin bacci ba sai dan kada ta kasa yin sammakon zuwa ofis gobe, da tunaninsa ta kwana tana mafarkinsa domin hoton fuskarsa ya dasu a kahon zuciyarta. Asuba ta gari! Tana tashi da asuba ta yi sallah ta yi addu'a Allah Ya bata basira irinta Dr. Jalo tana so ta kware akan harkar jarida itama. "DA MA NI CE Jalo." Nasrin ta faɗa a bayyane yayin da take linke abin sallah. Bayan ta yi wanka, ta shirya cikin shigar riga da wando (Suit) sai dan gyale data ɗaura a kai shimaba yafawa ta yi ba, kamar kullum 46 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE 1 kamar yadda ta saba shigarta. Ko karya kumalloma yau ba zata yi ba ta dauki mukullin motarta ta rata yakar Laptop ta fito. Ta iske yayarta da angonta Salis a falo suna karya kumallo. Bayan ta gaishe su suka yi mata tayin abinci. Ta girgiza kai ta ce, “na makara ina da shirin da zan aiwatar (program) da sassafe.' " Zainab ta kalle ta ta ce,"ai kuwa daga ganinki bacci bai ishe ki ba, ga idanuwaki sun kunbura. Wannan wane irin sammako ne haka har zaki riga mai aikin banki fita?" Salis ya yi dariya ya ce, "wayar soyayya ta raba dare tana yi tare da Fu'ad." Suka kwashe da dariya su dukka yayin da Nasrin ta kara gaba dan taga alama zasu ɓata mata lokaci. Kai tsayc ta wuce wajen taron da 'yan majalissu tarayya zasu yid an dauko rahotanni, acan zata hadu da abokan aikinta. Tabbas taron nan ya caja kai dan ankai ruwa rana akan banbance-banbancen ra'ayi. Karfe biyu na rana ta samu ta fito daga 47 | Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 majillassa (House of reps) ita da abokan aikinta suka nufi gidan NTA dan mika rahotanni. DA MA NI CE... 1 BABI NA HUDU .KANO Zaman Malaika da mijinta ya faskara kowannensu ra'ayinsa ya banbanta, Malaika na kan bakarta na son masu kudi da tsanar talaka, haka Shamaki ya na ta nuna mata wannan hanyar ba mai bullewa bace gara ta dawo kan hanya. Zaman doya da man ja ake a matsayinsa na mijinta komai ya fada mata bata ji bai isa ya sakata ba ko ya hana ta ba. Haka bata kula da yara balle shi kansa. Wani abu dole sai ya yi magana, wani abu kuwa ya kawar da kai ya tashi ya yi abinsa da kansa. Tunda ta sami lambar Nasrin bata taɓa fashin kiranta ba, a kullum sai ta kira ta sau biyu ko fiye da haka a rana, sai dai a ki amsawa amma sai ta kira. Jifa-jifa dai Nasrin tana amsawa idan bata komai, amma ko Nasrin 49 | Jamila Umar Tanko (JUT) L DA MA NI CE... 1 bata fadaba daga yadda take amsa mata itama ta san ta gallabe ta. Sai lallaɓa Nasrin Malaika ke ta yi tana kwantar da kai akan ta yarda su yi kawance, har ma tana so ta kawo mata ziyara Abuja. Nasrin ta ce sai ta dauki hutu yanzu kullum a wajen aiki take yini. Nasrin ta na ganin kokarin Malaika na kiranta da take yi a kodayaushe, tana kashe kudin katin wayarta kullumgashi ba karfi gare ta ba, sai ta dinga turo mata katin waya na Dubu daya da dari biyar-biyar jifa-jifa, yayin da farin ciki ya lullube zuciyar Malaika ta ji ta kara son Nasrin, ta tabbatar mai kyauta ce kuma zata karu da ita. Shamaki ya zuba musu ido yana kallo kullum aka turo mata katin waya sai ta nuna masa gami da tsuyuwa ta tsawon awa goma a ranar, tana kiransa da wanda ya kasa. 50 jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 Wata rana Shamaki ya faki idon matarsa ya dauki lambar wayar Nasrin daga cikin wayarta. Ya laɓe ya yi ta kira tunda safe ba'a dauka ba sai cikin dare misalin karfe goma sha daya na dare ta ga missedcalls dinsa rututu sannan ta kira da sauri ba tare da ta san mai kira ba. Aka ci sa'a kuwa Malaika tana bacci, ya fito falo ya laɓe ya amsa wayar. Ranta ya ɓaci da ta ji muryar namiji ne kuma wanda bata sani ba. Ya gabatar mata da kansa sannan ta tsagaita, tana sauraronsa cike da mamaki kai tsaye ta zaci halin maza zai nuna mata, irin cin amanar matansu a bi kawa a ce ana so. Amma da Shamaki ya fara koro mata bayanai cikin ilimi da muryar tausayi sai Nasrin ta dakata ta nutsu tana sauraronsa. Shamaki yace, "a yanzu haka duk duniya Matata bata ganin daraja da mutuncin kowa sai ke, Nasrin ki taimaka min kiyi mata nasiha, akan ta yarda da kaddara, ta yarda da yadda Allah Ya ke son ganinta. Ta kula da ni ta kula da yaranta amma ko da yaushe so take ta ɓalle.. 51 Jamila Umar Tanko (JUT) DA MA NI CE... 1 auren ta fita gari neman kudi. Ita a dole sai ta yi arziki karfi da ya ji." Nasrin ta yi shiru ta kasa magana tana mai tausayin Shamaki, tabbas yana cikin masifa. Ta yi ajiyar zuciya sanna ta ce, “Ka yi hakuri da tambayata Shamaki, watakila ta ɓata maka rai. An ya matarka bata da taɓin hankali?" Nasrin ta tambaya cikin muryar girmamawa. Shamaki ya girgiza kai, yace, “ko ɗaya tana da cikakken hankali. Mace ce dai mai kwadayi da duban wadɗanda suka fita." Nasrin ta ce, "bata da ilimin addini da na boko ne?" Shamaki ya gyada kai yace, "zan iya cewa 'Eh' zan iya cewa 'A'a' saboda tana da shi daidai gwargwado dan tafi wasu da yawa amma basa yin irin halin da take yi. Kin ga kenan halinta ne ba jahilci ba." Nasrin ta yi ajiyar zuciya ta ce, “hakika na tausaya maka Shamaki kuma duk yadda ka fada na gasgata bazan musa ba, dan a yini daya 52 Jamila Umar Tanko (JUT) ... 1 nasan Malaika amma na fahimci da yawa daga cikin halayenta. Ka yi hakuri ka sake yin hakuri, da yardar Allah zan taimaka maka. Ada na yi niyyar sake lamba saboda da ita tana damuna ko in yi blocking dinta, dan ta daina samuna idan ta kira amma yanzu saboda kai zan jawo ta a jikina dan in fahimtar da ita rayuwa, da Izinin Ubangiji zata gyaru." Shamaki ya yi murmushin jin dadi, ya ce "Allah Ya saka miki da alkhairi, Allah ya sa ki fi haka. Wataran zan dauko ta mu je mu gaishe ki har gida. A wacce unguwa kike a Kano?" Nasrin ta yi dariya ta ce, "A Abuja nake zuwana Kano

Chapter 2 of 7