An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Adon Dawa Publishers
JAMILA
UMAR
TANKO
DA MA NI CE
DA MA NI CE... 1
HAKKIN MALLAKA(M): JUT
COPY RIGHT(C): JUT
SHEKARAR BUGAWA:
2015
NA'URA MAI KWAKWALWA:
JUT
DA MA NI CE... 1
FADAKARWA:
Wannan labarin na gaskiya ne, kuma an yi
shi ne da yarda wadanda abin ya shafa. Idan
waniya ji labarin ya yi kama da nasa/ko nata,
katari aka yi ba da shi/ita ake ba.
GARGADI:
Ba a yarda wani ko wata ya wanki wannan
labarinta kowacce siga ba, tawajen juya shi zuwa
fim haka ban yarda a rubuta wannan liittafin a
'social network'ba: face book ko whatsapp, ba
Duk masu tare rubutawa da baizinin da saninmu marubuciya suke yiba ba. makuma bada bada
yawunmu ba. Yin haka za'a fuskanci fushin
hukuma idan kuma aka yi a boye ban sani ba
Allah Ya na gani, dan ba karamin kashe mana
kasuwar littafi ake yi ba. Dan Allah jama'a a
dinga kula da hakkin mutane a kiyaye.
3 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE...
SADAUKARWA: BansW
chash on ide Amina Hassan Abdulsalam (AHA)del i svinsw
bed fy sie isted
TUKUICI: sw strays ad
Daukacin dukkanin'yan arewa masu kishin
arewa. Fatan Allah Ya bawa kasarmu zaman
lafiya.
GODIYA TA MUSAMMAN GA:
Sani Manaja Misau
Hauwa'u Umar Gajo (Yelleman)
Jibrin Umar Tanko
4 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MANI CE... 1
BABINADAYA:
LITININ KARFE TAKWAS NA SAFE
KANO
ata Zankaɗediyar mata ce ta
gifta a cikin wata tsaleliyar
mota, akan titin Nasarawa
G.R.A, Kano. Hakika matar nan ta hadu, ga
kudi, ilimi, ga kyawu duk daga Rabbil
samawati.
W
Malaika a zaune take donono a bayan
Babur ana ta zuga gudu da ita, amma bata cikin
hayyacinta, bata kara sanin inda hankalinta
yake ba tun sanda ta yi arangama da wannan
Zankaɗediyar matar da ta gifta ta gabansu a
cikin tsaleliyar mota.
Ta zama tamkar mutum-mutumi, ta daskare
kamar kankara, ji take tamkar ba'a cikin
wannan duniyar take ba. Tunani ya wurga ta
wata sabuwar duniya, dan haka bata sake
fahimtar abubuwan da suke faruwa a gabanta.
Jirgin tunani ya lula da ita duniyar gajimare, ta
5 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
hango ta har ta zama waccan matar itama ta
shige cikin tsaleliyar mota tana juya sitiyari.
Malaika bata farfado daga duniyar tunani
ba sai da ta ji muryar mijinta yana kwaɗa kiran
sunanta. Ta yi firgigit ta dawo duniyar da take
sai a lokacin ta ga ashe har sun shigo cikin
sibitin Nassarawa. Da ta ganta a bisa Babur
sai ta ja dogon tsaki, ranta ya ɓaci dan ita
tunani ya kai inda tayi male-male a cikin jirgin
sama ma ba a mota ba.
Kallo daya Shamaki ya yi mata ya
tabbatar ciwonta na tunanin‘kanzon kurege' ya
tashi.
Ya harare ta ya girgiza kai, yace "amma
kina tare da wahala in dai yanzu ma tunanin
nan kike mai kama da mafarki. Na yi miki
nasiha, na yi miki fada, na yi gargadi amma
duk a banza. Allah Shike azurtawa, Shine mai
talautawa, ki gode maSa da Ya baki lafiya Ya
rufa miki asiri, Ya baki miji mai zuciyar nema
dan ban taɓa barinki da yunwa ba. Ya baki
yara uku biyu masu lafiya daya ne mai sikila,
amma sai Ya bamu hali da damar jigilar kawo
6| Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE...
shi asibiti, Ya bamu kudin siyan magani. Ba
ma bara, ba ma rokon wani ya taimaka mana."
"
Malaika ta ji nasihar mijinta tamkar
zaginta yake, ranta ya ɓaci, ta turo baki gaba ta
kawar da kai gefe, sai kuwa idanuwanta suka
dira akan tsaleliyar motar Zankaɗediyar matar
nan data hango a kan hanya ashe itama asibitin
zata je. Sai Malaika ta shiga murmushi tana yi
mata kallo tamkar ta hadiye ta. Tuni ta manta
akwai wani bawa a kusa da ita yana yi mata
magana.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya
halicci wannan mata mai kyau da kudi.
Wannan idan ba minista bace to matar minista
ce. Zankadi! Ga kyan fuska, ga dirin jiki, ga
ilimi. DA MA NI CE...." Malaika ta faɗa a
bayyane ba tare da tasan zancen zuci ya fito
sarari ba. Yayin da take kallon matar tana
murmushin kauna.
barari ba. da take att
Sanda matar ta fito daga mota ta zo ta
gifta ta gefenaalaika, sai Malaika ta lumshe Laren jikinta. ido ta shaki kamshin
"Hakika
kudin mai
wannan mata a cikin masu
'yar gayu ce.
7 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
"Dama in zama kamarki." Malaika ta
fada cikin rada
Shamaki.
amma karab a kunnen
Sai ya ji tamkar ya dora hannu a kai ya
rusa ihu amma ya daure, ya girgiza kai ya saka
hannu a aljihu ya ɗauko kudi Naira dubu daya
ya mika mata, shima bata san yana mika
mataba har sai da ya nanika mata a hannu, tana
can tana kallonMatar nan.
Ya fada a fusace “ki je ki bi layi da sauri,
da na yi niyyar jiranki har ku gama in mayar da
ke gida, amma naga alamar kin shiga layin da
zaki ci gaba da ɓata min rai gara in kin kin gama ki
hawo adaidaita sahu ki dawo gida.
"
Ta kalli kudin ta jujjuya ta yamutse
fuska ta ce "a dubu zan yi kudin adaidaita, in
sayi magani in yi cefane? Cafdijam."
Yace “kada ki sayi magani ki kawo min katin
da daddare zan saya a kemis din unguwarmu,
muna saka ran karɓar albashi yau."
Malaika ta wuce a fusace tana zunkuda
goyo tana gunguni, ta ce "Allah Ka raba ni da
auren talaka, komai babusai kullum an jira
"
albashi.
8 Jamila Umar Tanko (JUT)
"
DA MA NI CE... 1
Shamaki ya daɗe a tsaye yana kallonta
cike da takaici. Ji yake tamkar ya dauko
hankali da tunani ya cusa a cikin kwakwalwar
matarsa. Yana kallonta bata nufi layin mararsa
lafiya ba, ta nufi ofishhin da wannan matar ta
nufa. Ya san magana zata je ta yi mata idan
taga fuska sai ta tambayi lambar waya da
adireshi.Ya san ko ya bi ta, ba zai iya hana ta
abinda ta yi niyya ba, dan bata ganin girmansa
saboda shi talaka ne.Ya ji kwalla ta cika masa
ido ya hau kan babur dinsa a sanyaye ya burga
ya yi gaba.
da Gudu yake ta shararawa a hanya dan
tafiyar ta sa da yawa daga nan zuwa Jami'a
(B.U.K) ba karamar tafiya ba ce, ga go slow a
hanya kasancewar yau litinin maʼaikatada wa 'yan
makaranta sun firfito. Tabbas ya san ya rasa
laccar karfe takwas zuwa tara sai dai ya sami ta
karfe tara zuwa goma shima sai ya yi da gaske
sannan zai samu.
ph
9| Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MÁ NI CE... 1
MALAIKASHAMAKI
Zuciyar Malaika cike da fargaba ta nufi
ofishin da haɗaddiyar matar nan ta shiga amma
sai ta tsaya a bakin kofar ta kasa shiga don ta
na jiyo muryarta ta na magana da maza likitoci
cikin harshen nasara, nan ma suka tafi da
imaninta dan tana so ta ji ana ragargazaryaren
Nasara abin yana bata sha'awa.
Kwatsam! sai ga wata burdurwar yarinya
mai dankaren kyau, ilimi da gayu, ta ci ado da
dankareren leshi ko gyale bata yafa ba tana
tafe, tana rangwada tamkar ba zata taka kasa
ba. Da alama a cikin hutu ta taso, dan babu
alamar wuya a tare da ita. Ta na rataye da jakar
'lap-top' a kafadarta, tafiya take ta na amsa
waya, wayar ma abar kallo ce, ta zamani.
Da ta zo daf da Malaika zata wuce sai
Malaika ta zabura ta dafa kafadarta, ta ce
"sannu kawata. Dan Allah ina da tambaya."
Kyakykyawar budurwa ta yi mamaki
bata san sanda ta katse wayar da take yi ba, ba
tare da tayi sallama da shi ba.Ta zubawa
Malaika ido tana jiran ta ji tambayar.
10 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE T
Malaika ta yi murmushi ta ce, "sunana
Malaika Shamaki. Ke fa, yaya sunanki?"
Ta kalle ta, amma bata yi mamaki da
yawaba kasancewarta 'yar jarida watakila ko ta
santa a talabijin ne.
hakoranta
Budurwar ta yi murmushi fararen
suka bayyana, ‘yar siririyar
wushiryarta ta haska ganin Malaika, ya yin da
gefen kuncinta dukka biyu suka loɓa (beautiful
points), Kamshin cigam din bakintamai
kamshin minti ya buso cikin hancin Malaika.
Malaika ta ce, Sunana Nasrin Abdul-
"
66
Nasir."
Malaika ta zabura ta ce, “cancandi!
Sunan ma irin na ku na 'yan gayu. Kina aiki
anan ne? Ko mahaifiyarki ce naga ta wuce
yanzu? Dan kuna kama wallahi."
Tabbas Nasrin ta ga rashin kamata a
wadannan tambayoyi amma ta daure
kasancewar ta san darajar dan Adam, bata
wulakanci.
Sai Nasrin ta yi murmushin karfin hali ta
girgiza kai ta ce, "aiki na zo yi daga NTA
11 Jamila Umar Tanko (JUT)"
DA MA NI CE
talabijin Abuja, ni ‘yar jarida ce, zan yi hira da
wannan bakuwar ne da kike fada.
"
"Ita wacece a kasar nan? Ta yi kama da
Minista ilimi." In ji Malaika.
Nasrin ta yi dariya ta ce, “ministan ilimi
ai namiji ne. Wannan babar likita ce, 'yar
Nigeriya ce amma a Amerika ta fi zama. Me
kike nema ne?"
Malaika ta yi murmushi ta ce, “Yarona
sikila ne jiya ba mu bacci ba, ki rokar min ita
ta duba shi, ke kuma ki dauke mu a jarida ki
yadawa duniya ko za'a bamu taimakon kudi in
kai shi turai, na ji an ce ana zuke jininsu a zuba
wani saisu warke gaba daya."
29
Dariya ta subucewa Nasrin ba tare da ta
yi shirin yinta ba.
Ta dafa kafadar Malaika ta ce "kawata,
ki je wajen likita ya duba shi wannan bakuwa
ba mararsa lafiya ta zo dubawa ba. Ta zo ne
akan binciken makasudin ɓarkewar cutar
sakarau data bulla a wasu wurarena garin nan.
Daga America aka turo ta."
99
Malaika ta ji dadin da ba zai masultu ba,
yau 'yar gayu ta dafa kafaɗarta.
12 | Jamila Umar Tanko (JUT)
NI CE... 1
Sai ta washe baki ta ce, "cafdijam! Ashe
babba ce sosai, likitan likitoci za kice min. ki
yi min hanya in ganta mana."
"
DA MA
Nasrin ta fara fahimtar cewa bada me
cikakken hankali take tsaye ba, sai ta girgiza
kai ta fara tafiya.
Malaika ta zabura ta rike hannunta ta ce,
"yah ke ma'abociya kyau da ilimi! Ki saurare
ni mana, ki fahimci in da na sa gaba. Ki yi hira
da ni a nuna ni a talabijin nima, dan duniya ta
san mu talawa muna shan wuya.
99
Dariya ta kwacewa Nasrin ta kama haɓa
ta fada a bayyane cikin mamaki "ikon Allah,
Allah mai halitta kala-kala. Ke kuma hira kike
so ayi da ke duniya ta ganki. 66
Dai-dai lokacin wasu maza biyu suka
tunkaro su dauke da manyan kyamarori,
Usman da Ishak, da alama abokan aikin Nasrin
ne. Su ma suka ja suka tsaya a in da suka ga
Nasrin, suna tambayárta meyasa ta tsaya anan?
Nasrin ta yi dariya ta ce, "kawa na yi
yanzun nan tana so ayi hira da ita, ɗanta yana
da sikila."
13 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Usman ya girgiza kai, yace “ba da masu sikila
za muyi hira ba da masu sankarau ne.
"
Ishak yace,
hira da ita mana.'
"
"ai duk ciwo ne za mu iya
Nasrin ta ce, "hakika mun yi babban
kamu dan wannan matar zata iya magana sosai,
na ji muryarta da zaki kamar ganga. Hajiya
Malaika kin iya turanci?"
Malaika ta yi dariya ta gyada kai ta ce,
"zan iya, irin na mu na Hausa dai."
Gaba ɗaya suka tuntsire da dariya.
Nasrin ta dafa kafadarta ta ce,"ki jira ni
to in shiga in gama hira da Dr. Hala Hamma
Yaro. Dan kada ta tafi kin ga takanas dan ita
muka zo Kano."
"
Malaika ta yi musu jinjina da hannu, ta
yi dariya ta ce, "Allah Ya tsare min ke. Sai kun
fito, ki gaishe min da ita sosai."
Nasrin da abokan aikinta suka tura kofar
ofishin suka shiga gami da yin sallama.Fiye da
mintina talatin basu fito ba Malaika kuwa na
nan a tsaye akan baranda bata tafi ba, haka ta
ma manta da abinda ya kawo ta asibitin.
14 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Da ta ji shirun ya yi yawa sai ta tura kofa
ta shiga ofishin kanta tsaye, tana tafe tana
sanda har ta isa wajen wata kujera,Likitoci
biyu su na ta yi mata nuni da hannu ta koma
amma ta ki, babu wanda ya yi magana saboda
an ɗora kyamara akan Dr. Hala tana bayani,
yayin da Nasrin na kusa da ita tana mata
tambayoyi.
Malaika ta sami waje ta zauna bata damu
da hararrar da likitocin nan suke yi mata ba.
Ta na zama ɗanta yace bai san zance ba,
ya fara yunkurin kuka, nan da nan ta sauke shi
ta kafa masa nono a baki. Ita fa a dole sai ta ga
kwakwaf.
Tana kallonsu tana murmushi abinda ta ke gani
a talabijin yau gashi a fili.
Da aka kammala hira da Likita kafin a
rufe kyamara Nasrin ta taso da sauri ta ce da su
Usman masu dauka su juyo su dauki hirarta da
Malaika. Har za su yi mata musu, Nasrin ta ce
su dauka kawai zata fada musu dalili idan an
gama.
15 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Malaika aka gyara riga da mayafi aka juyo da fuskar tamushashshan jaririnta ana
murmushi.
Dr. Hala ta gyara gilashi ta zubawa
Malaika ido tana kallo cike da mamakin yadda
ta shigo ofishin ba da izini. Sai taga kamar da
akwai alamar sanayya a tsakaninta da 'yan
jaridar, dan haka ta rage mamakin.
Turancin dai ba laifi, ta yi kokari ta yi
bayanai akan ciwon ɗanta, ta kara bayanai
akan gwamnati ta shigo cikita taimaka.
Da aka gama sai Dr. Hala ta kira Malaika
kusa da ita, tana mata tambayoyi akan ciwon
danta cikin rada. Gami da karbar dan ta
dudduba shi, ta bata shawarwari.
Malaika fa ba sauraron abinda Likita
take fadaba take, sarka, dan kunne da zobunan
lu'u lu'u (Diamond) din jikin Dr.Hala kawai
take kallo, har da bude baki, suna ta walwali
suna haske saboda kyau. Da likita ta gama
bayani sai Malaika ta nemi data bata lambar
wayarta.
16 | Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Likita ta girgiza kai ta ce bata da
takamaimiyar lambar waya guda daya,kullum
canja layi take yi.
Malaika bata ji dadi ba, ta tashi ta goya
ɗanta ta karasa wajen Nasrin, wacce ke zaune
tana ta rubuce-rubuce akan tebur,Malaika ta
tambaye ta lambar wayarta, Nasrin ta yi ta
hanya-hanya bata so ta bayar amma da ta ga
Malaika ta dage har ta fito da kujajjiyar
wayarta zata dauki lamba sai Nasrin ta bata,
burin ta kawai Malaika ta kara gaba dan ta bar
su, su yi aikinsu.Farin ciki ya cikawa Malaika
kalbi, ta tafi tana godiya.
Har ta jima da fita sai gata ta dawo, daya
daga cikin manyan likitocin daya jima yana jin
haushinta sai yanzu ya sami damar more
bakinsa. Dr.Gumel ya yi mata tsawa gami da
balbale ta da fada har da kunfar baki.
ya ce, "Malama! Kina
damunmu mu na aiki sai shige da fice kike yi.
Wai shin waya baki izinin shige da fice a cikin
ofishin nan?"
Dr.Gume]
Malaika ta fusata ta harare shi, ta yi
gatsine ta ce, "Malam, ba wajenka na zo ba,
17 | Jamila Umar Tanko (JUŤ)
DA MA NI CE... 1
manyan ma basu yi min magana ba, 'yan kasar
waje wadanda Amerika da Obama su ka san da
su, sai kai da kake tare da ni a Kano."
Gaba daya aka yi carko-carko ana kallon
Malaika. Tabbas bata san da wa take magana
ba, da ta san ko shi waye ba zata faɗa masa
haka ba. Dr. Gumel likitan da ake ji da shi ne a
kasar nan,ta fanni dashen koda.
Sai ya kasa magana ya ci ganba da
karatun jarida.
Nasrin ta ji kamar ta barke da kuka dan
Malaika ta dame ta, ta fada cikin shagwaɓa da
takaici, "Malaika me zan yi miki kuma?"
Malaika ta washe baki tayi dariya ta ce,
"yaushe za'a saka hirar da muka yi? Dan in
gani, kuma awacce tasha za'a nuna?"
Nasrin ta ce"hunda kina da lambar
"
wayata za mu yi magana a waya.
Malaika ta gyada kai ta ce, "zan kira ki
idan na fitazan saka katin Naira dari biyu dan
mu dade muna hira. kin ji kawata."
Malaika ta juya ta nufi kofar fita, har ta
isa bakin kofa ta juyo ta harari Dr.Gumel ta ce
18 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
“ɗan bakin ciki sai ya mutu, Allah ne Ya hada
ni da haɗɗun 'yan gayu babu mai raba mu.”
"
Sai kowa ya bude baki yana kallonta
cike da takaici, Usman ya zabura zai yi mata
magana, Dr. Gumel ya yi masa nuni da hannu,
alamar ya yi shiru ya kyale ta. Bayan ta fita
suka tuntsire da dariya gaba dayansu, sun yi
Amanna tana da taɓin hankali, dan haka sun yi
mata uzuri.
MALAIKA SHAMAKI
Sai yanzu Malaika ta tuna abinda ya
kawo ta asibiti, rashin lafiyar ɗanta. Ta ɗauko
katinta daga jaka ta tafi da sauri tana ta salati,
tabbas ta san ta makara dan karfe takwas ake
gama karɓar Katina, gashi yanzu karfe goma
daidai. Tana isa ta iske dandazon mata suna
tsaye a layi, wajen babu masakar tsinke.
Dakyar ta kutsa ta cusa kai cikin ofishin
duk da carin da mata na kan layi suke yi mata
bata kula su ba. Ma'aikaciyar jinya (Nurse) ta
tare ta da sauri ta tambaye ta, ina zata je? Sai
Malaika ta mika mata katinta wai a taimaka
mata.
19 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Ma'aikaciyar jinya ta harare ta sama da
kasa ta watsar, gami da yi mata tsawa ta
ce,“Sannu isasshiya, sannu shafaffiya da mai,
sai yanzu za ki zo? To an rufe karɓar kati sai
gobe, idan goben ma baki zo da wuri ba sai
wani satin. "
Malaika ta harare ta,kama kugu ta
murguda baki ta ce, "Toh mai gadin kofa ke ba
likita ba kin fi likita zakewa. Da irinku ne
likitoci da karasa marar lafiya za ku yi saboda
babu imani da tausayi." • 99
Wata mata dake kan layi ta zabura ta
dafa kafadar Malaika ta ce, "haba baiwar
Allah! Yaya zaki dinga zagin mata akan
aikinta?"
Malaika ta juyo ta sauke kwandon
masifa akan matar da ta yi magana. Nan da nan
waje ya hargitse aka dinga hayaniya, gaba ɗaya
Malaika aka bawa rashin gaskiya sai kadan ne
suka bi bayan Malaika, su ma irin matsalarsu
daya da ita sun zo a makare an ki karbar
katinsu.
Malaika ta hada hayaniya har likitocin
da kansu suka firfito suna bada hakuri.Daga
20 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
karshe dai aka tantance Malaika ce ta hada
rigima, amma dan a zauna lafiya aka karбi
katinta tare da na sauran amma da sharadin ba
za'a gansu ba sai bayan azahar. Su ka yi
amanna suka koma gefe suka zauna, har yanzu
bakin Malaika ya ki mutuwa.
Fadi take ita ba talaka ba ce, wata talaka
bata isa ta taka ta, ta kyale ta ba. Mamaki ya
kama jama'a suna ta kallon koɗaddiyar
atamfar da ke jikinta amma tana fadin ba su
san ko ita wacece ba, ita da manyan likitoci ta
ke kawance ba da Nurses ba.
Ma'aikaciyar jinya 'Nurse' dai ta
fahimci Malaika ba sa'ar yinta bace, taga
alama ta dame ta, ta shanye ta a fagen tsiwa da
zakin murya, da alama 'yar ta kife ce. Ta fara
zargin ko tana shan benelyn dan yanzu an ce
har da matan aure ma sha suke, dan haka duk
wanda ya kula ta ma zai zama mahaukaci.Ta
kyale ta, tama daina kallon inda take, dan har
yanzu Malaika harararta ta ke tana nuna ta da
hannu tana murguda baki.
Nasrin, masu kyamararta, Dr.Gumel da
Dr. Hala ne suka biyo kan barandar da su
21 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA
Malaika ke zaune zasu wuce da alama dakin
kwanciyar mararsa lafiya suka nufa. Da suka
hango Malaika ta tunkaro su cike da fara'a,
gaba ɗayansu babu wanda gabansa bai fadi ba,
suka yi turus. Musamman Dr.Gumel yana
tsoron kada ta tara masa jama'a.
NI CE... 1
"Lah kawata Nasrin Abdul Nasir."
Malaika ta faɗa gami da rungume Nasrin.
Nasrin ta yi murmushin karfin hali ta ce,
"sannunki. Kin sami ganin likita?"
Malaika ta ce, "Eh an shiga da katinmu,
dan da har waccan 'yar bakin cikin zata hana
mu ganin likita wai mun makara."
Ta nuna Ma'aikaciyar lafiya 'Nurse'
yayin da Nasrin da Nurse suka haɗa ido, sai
kunya ta sa Nasrin ta sunkuyar da kai
kasa, kuma ta gaggauta barin wajen kamar
yadda Dr.Gumel ya yi gaba da sauri bai tsaya
ba.
Nasrin ta na tafe tana magana ta ce,
dawo wajenki anjima.99
"zan
Dadi ya kama Malaika ta koma wajen
zamanta ta zauna tana murna tana korawa
jama'ar wajen bayani, tana mai gabatar musu
22 | Jamila Umar Tanko (JUT)
.
DA MA NI CE... 1
da su Nasrin har da karin karya wajen
gabatarwar. Ta tabbatar musu da su kunna
labaran tara yau zasu ġa hirarta a talabijin din
NTA.
Ma'aikaciyar jinya 'Nurse' ta juyo da
sauri tana kallon Malaika kan ta ya ɗaure.
Malaika aka harari ta,tamurguɗa baki ta
ce "kalle ni da kyau ni ba karamar mace bace,
kin dai gani da idanuwanki ko ni wacece.
Kuma idan karya nake ki kunna talabijin yau
ko gobe idan baki gan ni a labarai ba ki kira ni
makaryaciya. Ni talaka baya yi min raini, dan
shi ba koman-komai ba ne."
Malaika dai bata kara ganin Nasrin
ba,sai bayanla'asar sannan likita ya ganta. Ta
je har ofishin bata gansu ba, ofishin ma a dates.
Ta karade asibitin nan kakaf tana nemansu bata
gansu ba. Ta je wajen da Dr.Hala ta ajiye
motarta ta ga wayam babu mota, sannan ta
tabbatar sun shanmace ta sun arce.
Shamaki ya kira wayarta fiye da sau
ashirin bata dauka ba, ta ga kiran ta ki ɗauka
dan bata san me zata ce masaba. Ta tari a-daidai-ta-sahu (Napep) ta tafi cikin fushi dan ba ta
23 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
ji dadin rashin yin sallama da su Nasrin bad an
tana saka ran samun kudi a wajensu. Unguwar
Dorayi ta nufa anan take da zama, sai da suka
yi faɗa da mai adaidaita sahun a hanya dan
yace ta koma tsakiya tayar gefe daya bata da
iska. Ta fara fada wai ita bata son harkar
talauci yana neman kudi amma ya kasa canja
taya.
Mai a-dai-dai-ta-sahu (Napep) ya ji
lafazan Malaika suna yi masa shawagi a
kwanya, sai ya saita mudubi ya kara kallonta
dan ya tantance mai kudi ya dauko wacce
motarta ta sami matsala a hanya ta rufe ta hau
babur dinsa, ko kuwa talaka ‘yar uwa ce take
kasassaɓar magana?Ai kuwa daga dukkan
alamu 'yar uwa talaka ya hanga, kososuwa
irinsa. Bai san amsar da zai bata ba, suka ci
gaba da tafiya yana jira ya ga ta nuna katon
get, sai gashi ta ce ya ajiye ta a kusa da bola, ya
kaita har kofar gidanta ta shiga, nan ma ya sake
gasgatawa 'yar gidan malam shehu ce dai.
Ko ba komai ta barshi da zulumi da
sunbatu.
Yana ta ambaton "Allah mai halitta!'"
24 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
Ta na isakofar gida tun daga kofar gida
ta fara jiyo ihun karamin ɗanta yayayyen
'Kasim' ta shiga da sauri ta iske shi a zaure a
zaune akan foh, yayin da babban ɗanta'Aliyu'
dan shekaru biyar yana dakan yaji a turmi a
tsakar gida.Shamaki ya yi dagaje-dagaje da
bakin gawayi yana dafa wake da shinkafa.
Malaika ta dora hannu aka tana shirin kur❜ma
ihu, ta daure dai ta fasa, ta sauke hannun.
Ta fada a bayyane "wallahi talauci bai yi
ba."
Shamaki ya fito daga kicin a sukwane yana
nuna ta da hannu,
".
'ina kika tsaya kika ki dawowa gida?
Dan na san ba ganin likita ba ne ya tsayar da ke
ba. Na kira wayarki kin ki ki dauka."
Malaika ta harare shi ta yi tsaki ta ci
gaba da kutsawa cikin gida, yayin da take
kokarin kwance goyo shima na goyen Ahmad
kukan yake yi, ga gajiya ga ciwo.
balbalin fada,
Shamaki ci gaba da binta a baya yana
bar yara a makwabta ba
wanka, babu abinci, na zaci zaki riga ni
dawowa har na yi lacca biyu na dawo ba ki
25 Jamila Umar Tanko (JUT)
DA MA NI CE... 1
dawo ba. Ba dai a wajen masu kudin kika
zauna ba."
Malaika ta fada cikin gadara da tsiwa
"kamar ka sani kuwa acan na ɓata lokaci. Allah
ma