Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Abba chairman yayi harta gama ringing ba'a dauka ba, hakan yasa yacigaba da kirashi har sau biyar ba'a dagaba, knocking kofar akayi hakan yasa ya ijiye wayan yabada izinin shigowa, wanan officer data daddaki Rahima ne ta shigo rike da wayan Rahima dake ringing tace "Sir wayan yarinyar chan ne her Mother has been calling, I want to ask for your permission idan na amsa na sanar da ita mun kama yarta kokuma na kashe wayan" hannu chairman ya mikamata alamun tabashi wayan hakan yasa ta mikamai ta juya tafita, sake daukan ruri wayan ta shiga yi ganin Best Mum akan screen yasa Chairman yay pikin tareda sawa a speaker kafin yay magana Mummy tariga shi. "Autana where are you, sorry dakika kira ina kitchen dasu Siddiqa, wai har yanzu baku gama birthday party bane da Chris I think I asked you to come back kafin 6 gashi yanzu ana kiran magrib......." dan gyaran murya Chairman yayi yace "this is Alhaji Muhammad Mustapha Abdullahi the Chairman of National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) in Nigeria, please madam is your husband there I will like to speak to him" sosai gaban Mummy yafadi hakan yasa tace "innalillahi Malam please ina y'ata take? Ina Rahima na? Ina Autana? Yarinyar dataje birthday maiya badaku da ita kuma?" yanda duk take maganan a hargitse yasa yace "calm down madam, I asked is your husband there I want to speak to him" arude tace "no, no, bayanan yay tafiya yace port Harcourt this morning, please ina y'ata? Me takeyi awurin ku?" shiru Chairman yayi yana sauraron yanda Mummy tarude ahankali yace "I am sorry to announce this sad incident like this Madam, but your daughter Miss Rahima Sambo Rikadawa has been caught taking Illicit drugs, Codeine, Crack, Tramadol, Weed, and shisha, she has been detained here according to the constitutional law, after some inevitable steps da we must carried out akanta, we are going to hand her over to rehabilitation centre inda zatai spending period of 6 months, thank you Madam for your time and do have a wonderful night rest" ya katse wayan tareda kashe wayan gabaki dai ya ajiye kan table Tareda danjan tsaki yace "mahaifinta yay tafiya Yaya kenan? Kaga tashi muje muyi salla" tashi sukayi suka fito daga office din suka sauka kasa inda suka tarar su Chris duk nacin abinci anbasu abinci a takeaway faran shinkafa da stew da dafaffen kwai, duk sunyi zuru zuru sunaci kaman ance in basuci ba za'a kashe sune. Magrib sukayi suka fito daga masallaci suka shigo cikin premises dinsuna dan tattaunawa, reception suka shiga wata mata suka hango sanye dawani bakin dogon riga dayaji stones tayafa wani mayafi milk color na manyan mata akai tarike wani handbag na LV tana magana da receptionist din wurin tana fada tace "ina kuka kaimin y'ata where is Rahima? Kubani y'ata natafi da ita shairi ake mata Rahima batashan komi saidai in wanchan yaron Chris shine ya koyamata taga yanasha ta dandana dan dama shiyay inviting nata to birthday party shi" cikin masifa Chris yace "No dey lie Madam, your daughter sabi everything so tey she dey carry for bag go school, no dey lie for my head ha'a see me see gbese o" cikin fushi Mummy ta juya zatai magana taga wani magidancin mutum tareda wani cikakken dogon bakin yaro dake sanye da jacket baki dabai ja zip dinba, rigan dayasaka mai ruwan toka ya bayana da kirjinshi hartana hango kwantaccen gashin kirjinshi baki sidik, dan girgiza kanta tayi ta saita idanunta kan Chairman kafin ta kalli wasu manyan hotunan frame dake jikin bangon reception din na president, da vice president saikuma hoton shi da aka rubuta chairman NDLEA, cikeda masifa tace "good ka iso Chairman, I guess you are the one I spoke to a while ago, ina y'ata take? Kubani y'ata natafi gida, shairi kuke mata Rahima babu abinda tasani, she is my last born, yaushe na haifeta duka duka da zaku kamomini yarinya daga taje birthday coursemate dinta kucemin shaye shaye take? How on earth is this possible?" anatse Chairman yace "Madam until your daughter's father is back and come here dakanshi I'm not releasing Rahima nor giving her to you" yana maganan yay hanyar office dinshi binshi Mummy tazo zatayi security suka tareta hakan yasa ta tsaya daga wurin, ganin bala'inta bazai yi komiba burinta shine tasamu su saki Rahima su koma gida asirinsu arufe batare da Abban su yasani ba amma taga ina wayan nan basuda mutunci hakan yasa ta shiga rokon security su barta taje taga Chairman sukaki. Shiga office din sukayi daidai wayar chairman yahau ruri karasawa table din yayi yadau wayan ganin Mahaifin Rahima ne yasa yay picking yasa a kunne ya nemi waje ya zauna yace "good evening to you Sir, this is Alhaji Muhammad Mustapha Abdullahi Chairman din NDLEA, I've been calling you na sanar dakai wani muhimmin abu, mun kama yarka awani gida nan hanyar Kaduna kano express road ita da wasu yara maza da mata su talatin da daya da sunan birthday party tana shaye shayen miyagun kwayoyi da gwamnati tabada umarni duk randa muka gani yanayi mu kamashi sanan mu aika dashi rehabilitation centre, ganowa damukayi Rahima yarka ce mukuma dan matsayin ka akasar nan munkuma san yanayin matsaloli da fitintinu dazaka fuskanta in duniya tasan me ake ciki yasa mukace bari mu maka alfarman kiranka mu sanar dakai shima badan komi ba saidan labari dakuma yanda ake yabata akan aiki bisa gaskiya dakake yi ne" shiru Abba yayi na kusan minti takwas tunani yake Rahima shaye shaye, party da maza ahanyar wajen gari, shaye shaye, innalillahi wa innailaihi raji'un, Chairman ne jin shiru yasa yace "kana jina" ahankali cikin murya datai rauni sosai Abba yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un" saida yafada sau uku yasake yin shiru yama rasa maizaice, Murya chan kasa data nuna karara alamun bacin rai da tsantsan damuwa yace "Chairman banda abinda zan cemaka sai Allah nasaka da alkhairi, wlh bazan maka karyaba wutan kaina ta dauke dib I don't know wat to think, alfarma daya zakamin kawai yanzu zan kira mahaifiyar ta tazo ta dauke ta sutafi gida, first flight zan biyo nadawo garin nan gobe dasafe zanzo har office dinka nasameka zamuyi magana da kyau, nakumayi alkawari binciken case dinan da kyau nagode" ahankali Chairman yace "mahaifiyar yarinyar is already here badai mubata yarinyar bane daman munce dole sai munyi magana dakaine, yanzu kuma tunda munyi zamu sa abata ita sutafi gida" ajiyan zuciya Abba yasauke yama kasa magana hakan yasa Chairman ya katse kiran yana girgiza kai yace "rayuwa kenan saikaga a good man ya haifi boka, jarabawan Allah kanzo tako ina, please Lieutenant help me tell them sukaima matar yarinyar nan sutafi gida" tashi Sameer yayi yafita daga dakin ganin babu kowa a upstairs din yasa yay dining din dayake anan sama dama dining din yake yasaba zuwa NDLEA din so ba bakonshi bane babu inda baya shiga saidai in baisoba, bude kofan dining dinyayi tana zaune kan kujera ta kifa kanta kan table tana kuka ga takeaway din rice da stew dinta agefe ko kallonshi batayi ba, hannayenshi yazuba a aljihun wandonshi yay wani irin tsayuwa irin na sojojin nan yace "Ke!" da kakkausar muryan shi da sauri ta dago kanta gabanta na faduwa sabida yanda ya kirata, dauke kai tayi daga kallonshi ganin wanan mugun bakin sojan nanne daya mata wankan ruwa dazu. "zoki fita ur Mum is waiting at the reception" dawani irin mugun sauri ta juyo tareda ware jajayen kumburarrun idanunta tace "Mummy na kace?" shiru yayi bai amsata ba sai zubamata manyan idanunshi masusa mutane shakkan shi dayayi yana kallonta, dawani irin sauri ta tashi gabanta nafaduwa ta taho tana dingishi tabi ta gefenshi tafita da sauri tai hanyar stairs, ahankali yajuya yafito shima ya tsaya a daidai bakin benen har lokacin hannayenshi na cikin aljihun wandonshi yana kallon yanda take tafiya tana dingishi da sauri tana sauka, saida tagama sauka daga benen sanan tafashe da kuka sosai tana yarfe hannu kafin ta kwalama Mummy data juyama stairs din baya tana waya kira. "Mummy!!!" da sauri Mummy dake waya tajuyo ganin Rahima ga bandeji a goshi tabi tai daka daka kaman ba yarinyar data bar gida fess fess ba yasa ta zare wayan daga kunnenta tana kallonta, dawani irin gudu Rahima ta taho tana dingishi takarasa tawani fada jikin Mummy tareda fashewa da kuka sosai mai tsuma zuciya, bayanta Mummy ta shiga shafawa tace "ya isa, ya isa, am here now stop crying" dagota tayi tasa hannu tana sharemata hawaye tareda shashafa goshinta inda taga bandeji tace "maiya sameki anan maisa kike dingishi" cikin kuka tanuna Chris ashagwabe tace "wanchan matsiyacin ne Mummy mai kama da jaririn kunkuru shine ya fesamin goshi" wani mugun kallo Mummy tamai batason tai magana dan tasan yariga yasan few things gameda Rahima batason ya tona musu asiri hakan Yasa tace "barshi yama kanshi, let's go" security ne suka tare musu kofa bazasu barsu su wuce ba, Sameer dake gaban stairs a sama yana kallon komine cikin husky voice dinshi yace "let them pass" da sauri Mummy ta dagokai tareda juyowa hada ido sukayi da Sameer wani wawan faduwa gabanta yayi, chak ta tsaya tana kallonshi harsaida Rahima ta kalleta cikin muryan kuka tace "Mummy mutafi" ajiyan zuciya ta sauke takalleta tace "okay Auta muje" fita sukayi daga wurin security zasu maida kofan su rufe takara juyowa ta kalli Sameer daya fara tafiyan shi nan dai dai yay office din Chairman. 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫 _CHASING THE HEART CRAVINGS_ Doesn't favor you always 💔 ✍️ M Shakur 1️⃣9️⃣ Mota suka shiga Mummy taja motar suka tafi, saida suka shiga titi Mummy tace "what kind of matsala kika sani Rahima yanzu? Yanzu wani irin karya zan shiryama baban ki dazai yarda eh? Mezan cemai, kai! Innalillahi wa innailaihi raji'un, wanan Chris anyi dibabben yaro mai bakin jini da badluck mtsww" taja tsaki tana gudu ahanya, Rahima ba tace mata komiba gabanta faduwa kawai yake babu abinda take tsoro aduniya yanzu haka kaman haduwanta da Abban ta ahaka suka kai gida, su Siddiqa duk suna daki, dakin Mummy suka tafi direct wanka Mummy tasa tayi tabata abinci, kasaci tayi tace "Mummy bazan iya ciba, in Abba yadawo gobe kasheni zaiyi ko Mummy?" zama Mummy gefenta kanta takama ta daura akan kirjinta ta rungume ta tace "Hey am ur Mum ko, so kibar komi a hannuna, now eat ko kadan ne saiki sha paracetamol dinan karkiyi zazzabi kije ki kwanta kinji" gyadama Mummy kai tayi tasa chokali cikin abincin zata kai baki ta yatsine fuska tadago kanta ta kalli mummy, murmushi Mummy tayi tace "ina zuwa" tashi tayi tai wurin safe ta bude kara daya na wiwi ta dauko tazo ta juyemata a abincin juyawa tayi ta shiga ci da sauri dan yunwa takeji rabon ta da abinci tun rana, tana gamaci Mummy tabata paracetamol tasha ta kwanta ba'a wani dau lokacin ba bacci yay awon gaba da ita, tsayawa Mummy tayi tana kallonta barinma goshinta dake sanye da bandeji har lokacin da kafadarta dayadan kumbura sabida kulkin da matarnan tabuga mata sai wrist din kafarta, wani irin murmushi tayi ta tashi daga inda take tadau kulan tajuya tafita daga dakin. Sai wuraren 10 yakoma gida sabida tsareshi Chairman yayi sai hira yakemai, shidai chairman arayuwanshi starting from rana na farko daya fara ganin Sameer yake bala'in sonshi, gabaki daya yama maida Sameer din wani abokinshi dudda ya girmeshi amma yana son yaron, jan Sameer din yayi har zuwa gidan shi sukai dinner mai rai da lafiya sanan wuraren 10 Sameer yamai sallama yarakoshi waje saida ya shiga motarshi yafita daga gidan sanan yakoma cikin gida yana murmushi. Wuraren 10:30 ya isa gidansu Gate aka budemai yay Parking yafito, flat dinshi yawuce direct dan yasan Ummi tariga ta kwanta, sabida hawan jini dakuma matsalan kafanta yasa Dr yace tadinga kwanciya da wuri, yasan ta kwanta saisa bayason yaje yatadata, part dinshi yawuce ya shiga ya maida kofan ya rufe bathroom ya shiga yayi wanka yafito daure da dan towel a waist sanan yadawo falo agogo ya kalla so yake yakira Mu'az he has been busy da tubda yadawo daga zaria baisamu ya kirashi ba, sanin yay bacci yanzu yaja ya kunna laptop dinshi ya shiga yin some work da yakamata ace yayi, almost 1hr yabata sanan ya kashe ya ijiye agefe yay addu'an bacci ya kwanta. Aka'ida dama ana kiran sallan asuba yake tashi, tashi yayi yashiga bayi brush yayi yay wanka tareda dauro alwala yafito jallabiya yasaka ya feshe kanshi da turare yafito, mai gadinsu yatada sanan yawuce masallaci. Wuraren 6 na safe ya shigo gidan flat dinshi yawuce ya shirya cikin wasu sport wears, bubu short ne daya tsayamai iya gwuiwa sai wani riga mai kama da singlet da wani karamin towel a wuya na goge zufa ya saka sport sneakers dinshi na Nike yafita gudu haka daily routine dinshi yake kullum ka'idane saiya motsa jiki da safe na 1hr, da yamma inya dawo daga aiki dawuri saiya shiga gym dinshi yay work out har zuwa gab da magrib sanan yay wanka yatafi masallaci. Around 8 na safe ya shigo gidan, shashin shi yawuce yay wanka ya shirya cikin uniform tsaf sai uban kamshi yake yafito yay flat din Ummi, tana zaune kan dogon kujera sanye da dogon riga tana lazimi, tana ganinshi ta zuba mai harara hakan yasa yay dan murmushi yakarasa inda take, kusada ita yazauna yace "good morning Ummi" addu'a ta shafa sanan ta kalleshi tace "Sameer dama ido kanga ido" kaman zaiyi kuka yace "Ummi am sorry nowww please kidena magana haka" dan tabe baki Ummi tayi tace "toya kakeso Sameer kanunamin kafi karfina" da sauri yace "Ummi dan Allah kiyakuri please forgive me, I've been busy jiyan nan koda nadawo was late saisa ba shigo ba banso natade ke, am sorry kinji Mamana" yanda yay magana cikin kwantar da murya danko kadan baiso yaga Ummi na fushi dashi yasa tace "to shikenan yawuce, tashi muje kaci abinci". Tashi yayi sukai dining, kunun gyada Ummi ta zubamai da kosai da aka soya sanan tawuce dakinta, faracin abincin yayi dan he loves all this natural local food, he is not a fan of all this abincin yan gayun, bai wani jima da faraci ba Ummi tafito dawani 5liter jarka dayake cike da ruwan rubutu akan dinning table ta ijiye tadau cup ta bude ta tittila ruwan ta cika ta ijiye a gefe sanan ta rufe jarkan tace "maganin da Baffan ka yakawoma ne, ruwan rubutu ne akama na ayoyin Allah koma menene ajikinka dake hanaka aure zai kone ne da izinin Allah, ungo karba ka shanye" tamikamai cup din, dan murmushi yayi dan baiso yasami matsala this early morning hakan yasan ahankali yamika hannunshi ya karba yay bismillah yakai bakinshi ya shanye yabata cikeda murna tace "yauwa ko kaifa, Allah yamaka albarka soja na, Allah kuma yahadaka da matarka kwanan nan" baice mata komiba yacigaba dacin abinci dan bai wasa da cikinshi yanada ci sosai dama ance dogo nada dogon ciki, sanan duk soja nada ci , saida yagama ci tass sanan yatashi tareda goge bakinshi da tissue yace "thank you Ummi na koshi, natafi" kanshi ta shafa tace "adawo lpy, Allah yabada sa'a Allah ya tsaremun ku duka" ahankali yace "Ameen" sanan yawuce yafita saida ya tsaya yabiya mai gadinsu salary shi dan on 25th of every month yake biyansu sai murna Gate man yake yanamai godiya sanan yawuce ya shiga mota yatada yatafi office. Karfe sha biyu da minti ashirin jirgin su Abba ya sauka a Airport din Abuja, yariga yafada driver yakawo mai mota, key motar kawai ya karba yabama direba kudi yahau taxi yakoma gida shikuma ya shiga mota yatafi kallo daya zakamai kagane yanada damuwa sosai, a parking space din headquarter NDLEA yay parking yafito, ya shiga ciki Chairman yariga ya sanar dasu zuwanshi hakan yasa cikin girmamawa sukamai iso har office din Chairman shiga ciki yayi cikeda girmamawa Chairman yatashi kan kujeran shi tareda bashi hannu yace "barka da zuwa Alhaji" karban hannunshi Abba yayi cikeda murmushi yace "barkan mu dai ya aiki yakuma fama da jama'a" "Alhamdulillah please sit" Chairman yanunamai kujera hakan yasa ya zauna ahankali tareda sauke ajiyan zuciya yace "bakomi yakawo ni nanba nazo namaka godiyan karamcin dakamin ne nagode Allah ya rufa naka kaima haka" girgixa kai Chairman yace "wlh is all thanks to Lieutenant Sameer, konima jiya kaina ya kwance he was the one that advised me akan yanke wanan decision din, Nigeria is just lucky to have that guy" "are you talking about Lieutenant Sameer Simran Sameer dana karanta a news an karamai girma?" da sauri chairman yace "shine, shine ma yagano yaran anan Abuja express road yana dawowa daga zaria shine ya gansu suna shaye shaye awani gida cikin daji suna raye raye yasanar damu, all the children are student babu wani tsayayye mai aikin yi Allah dai yakawo mana karshen shaye shayen nan na yara matasa" shiru Abba yayi kafin ahankali yace "Alhaji Rahima, Rahima na that is just 20 itace aka kama tana shaye shaye?" dan murmushi Chairman yayi ya gyara zama yace "I know yanda kakeji yanzu haka I understand you, Rahima da aka ganta ita tama gama buguwa saida aka kwara mata ruwa sanan ta farka, yaron ma da ya gayyace ta wurin sunanshi Chris birthday dinshi ne anyway is a long story basai kasan komi ba kawai ka kula da yarka Alhaji karabata da abokanen banza dansu ke batama yaranmu tarbiya ayau kadage kanama yaro tarbiya agida wani nachan awaje yana batasu, kawai ka tsaya tsayin daka akanta, karabata da yaron dan yace waishi saurayinta ne soyayya suke dan makarantan sune ajinsu daya, karabata dashi dan Allah dan he will only cause more harm to her life, Allah ya shirya mana iyalinmu gabaki daya" ahankali Abba da jikinshi yay wani irin mugun sanyi yace "Ameen" duk shiru sukayi Chairman na kallon Abba ba karamin tausayi yabashi ba sai zufa yake kana ganinshi kasan yadamu toyama za'ayi bazai damuba yarshi na shaye shaye ga yawo da abokan banza, ahankali Dady yasauke ajiyan zuciya yamikama Chairman hannu yace "I will not forget this, nagode nagode, yau dinan zanje har Barrack na nemo Lieutenant namai godiya duk wanda keson cigaban ka sanan duk wanda yarufa naka asiri a lokacin da u can't do anything mutum ne daba zaka taba manta wa dashi arayuwaba, dan Allah karkace a'a am inviting you for a dinner a gidana gobe dakai da Sameer shima yanzu innaje mai godiya zan gayamai hakan" washe baki Chairman yayi a whole Chief justice na Abuja High Court is inviting over to his house for dinner this call for celebrating, cikeda murna yace "that will be an honour sir, nagode zaka ganmu da izinin Allah, Allah kuma yanuna mana goben, this mark the beginning of amazing friendship anzama daya da izinin Allah, and karka damu komi will be fine kadage da mata addu'a kaida mahaifiyar ta she will change" ahankali Abba yace "Allah ubangiji yasa" atare suka fito har wajen motarshi chairman yarakashi sanan sukai sallama yatada mota yawuce Barrack. ID card dinshi kawai yanuna cikeda girmamawa sojoji suka barshi ya shiga Barrack din tareda hadashi da wanda zai kaishi har office din Sameer, parking yayi bayan sun iso suka fito suka shiga, lift sukahau, sanan suka sauka a 4th floor sukai office din Sameer, knocking sojan yayi daga taciki akace come in, bude kofan soja yayi ya shiga Abba biyedashi Sameer ne zaune kan kujeran shi yanama wasu sojoji guda shida dake tsaye a office dinshi magana, sojan dake tareda Abba ne ya saramai tareda kamewa. "Sir, someone is here to see you" tashi Sameer yayi daga kan kujera dan kallo daya yamai yagane shi yasan chief judge sosai kawai ne wani abu baitaba hadasu bane, karasowa yayi har gaban Abba inda yake tsaye tareda bashi hannu yace "you are welcome sir" sanan yajuya ya kalli sojojin dakin yace "you guys can go" saramai sukai suka fita sanan ya nunama Abba kujera yace "please sit" zama Abba yayi tareda yin murmushi ganin yanda yakemai magana cikeda girmamawa yasa ya zauna, komawa Sameer yayi ya zauna akan kujeran shi, ahankali yace "ina yini Sir" murmushi Abba yamai cikin natsuwa yace "barka da ware haka Lieutenant, daga wajen Chairman nake, I went there to thank him, I came here to thank you as well, thank you so much Lieutenant Sameer" cikin dan kunya dajin nauyin mutumin Sameer yace "but why sir? You don't have to thank me am only doing my job, dan Allah kadena min godiya" wani irin burgeshi Abba yaji yayi ganin yanda yake da hankali ga natsuwa, murmushi yayi yace "I have to, chairman told me everything, duk wanda yamin abin alkhairi koda kankani ne saina mai godiya that is the policy dana dauka tun ina yaro Sameer hakan yasa Allah ya albarkaci rayuwana, kuma darajan hakan nakeci haryau, thank you so much Sameer Allah yamaka albarka" dagokai da sauri Sameer yayi ya kallai yanda yace Allah maka albarka saiya tunamai da baban su kafin yarasu, ahankali yace "Ameen nagode" ahankali Abba yace "am inviting you over to my house for dinner gobe kaida Chairman don't say no please son, ina jiranku gobe," wani kati yaciro ya ijiye mai akan table yace "this is my address, ina jiranku, sai anjima" yajuya yafita binshi da kallo Sameer yayi sunan son da yakira shi dashi namai yawo akai ahankali yadau katin ya kalla kafin ya ijiye agefe yacigaba da aikin dayake yi. 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫 _CHASING THE HEART CRAVINGS_ Doesn't favor you always 💔 ✍️ M Shakur 2️⃣0️⃣ Bayan yabar Barrack office dinshi yaje yay failing 1week leave daga aiki he want to stay at home yasama Rahima ido dakanshi. Tunda garin Allah ya waye Rahima tarasa natsuwa tayi zuru zuru duk idan anbude Gate sai gabanta yafadi dan tasan Abba zai shigo in any moment, Mummy tayi tayi tai calming dinta down amma abin yaci tura tsoron mahaifinta da Rahima takeji dabanne dan ba yamata wasa ko kadan, kosu Siddiqa sun gani akwai wani abu akasa tunda suka tashi sukaga bandeji a goshinta gashi tana dingishi kuma tai zuru zuru ko kallon banza bata musu ba ma ranan dan ta gaishe dasu duka, tai salla kuma sanan ta shigo kitchen dudda babu wani abun kirki data iya amma saida ta taya Zeena aiki Zeena na wanke wanke ita tana dauraya, bayan sun gama kuma ta kwashe bawon doyan da Siddiqa ta fere ta zuba a bola, duk tanayi ne sabida batason akai karanta koda guda dayane wurin Abba, Mummy tai tai taida ita tazo taje ta kwanta ta huta taki yarda saiyi take. Bayan Magrib Abba ya shigo gidan da sallama su Siddiqa ne kawai a falo da Mummy dataci gayu sosai suna kallon dan makaho a arewa 24 Mummy tayi tayi da Rahima tazo ta zauna suyi kallo taki, jin sallaman Abba yasa da gudu yaran sukaje suka rungume shi. "oyoyo Abba" tasowa Mummy tayi ta watsama yaran harara tace "sai asakan mini mijina" dan dariya Abba yayi yana kokarin danne bakin cikinshi yace "a'a bazaki koramin yarana ba, zodai tanan" yadan jawota da hannun dakanshi dat is free hakan yasa ta taho ahankali tana murmushi duk ya hadasu duka ya rungume he feels better his family is just his everything, sakinsu yayi ya zauna akan

Chapter 9 of 15