5️⃣ & 6️⃣
Wani babban bedroom ne hadadden da everthing looks absolutely neat dakin sai kamshin turaren wutan yan maiduguri dakin yake. Mata biyu ne sunci gayu sosai wearing wani material iri daya da aka musu irin gown dinan da ake kira da dinner gown mai ruwan gold sun daura head black shima sunyi kyau kowacce na sanye da makeup akan fuskarta. Tsaye suke kan wata magidanciyar mata dake zaune kan kujeran gaban makeken hadadden mirror kwalliyan dake dakin, daya daga cikinsu namata daurin kallabi, murmushi matar tayi tana kallon matan biyun ta madubi yanda suka dage dauri sukemata, daya daga cikinsu ne dake left side din matar tace "Ummi kinyi kyau wlh sosai" murmushi matar da aka kira da Ummi tayi cikin natsassiyar calm voice dinta irin na kamilallun manyan mata tace "nagode Nabila" karasa daurin dayan tayi ta kalli madubin tana kallon fuskan Ummi ta mirror tace "yauwa angama Ummi" murmushi tamata tace "angaida Yusra sarkin iya daura kallabi" dariya Yusra tayi cikeda farin ciki compliment from Ummi kaman kyautan kudi ne dan Ummi bata fiye surutu ba ko kadan, tashi daga kan kujeran Ummi tayi ta kalli kanta a madubi ba karamin kyau tayiba wani mahaukacin lace tasa mai bala'in tsada mai ruwan gold dakeda tiny zanen flower na Black, tasaka wani sarkan zinare daya dace da shape din wuyanta da warwaron shi a right wrist dinta, ta daura fine agogo mai kyau a left wrist dinta, purse dinta tadauka Black tazura takalmi na vinci irin mara takurawan nan mai dadin tafiya tadauko wani hadadden mayafin ta yafa tadaga kai ta kalli babban agogon bangon dakin cikeda dan masifa tace "me suke bata lokaci haka ba 9 za'a faraba this is past nine shine har yanzu basu fitoba, bari naje na tattaro su su fito mutafi" tai hanyar kofa harzata fita saita juyo ta kalli matan guda biyu tace "Nabila kun tabbatar kun fadama Nani komi banson jikokina suyi kuka, makesure you set everything and tell the Nani all she needs to know" gyadamata kai sukayi atare, Nabila tace "to Ummi, ba zasuyi kuka ba matar ta iya kulada su sosai, yanzun nanma na dubosu har sunyi bacci kuma basa tashi cikin dare in sukai bacci sai gab da asuba dinan" gyadamusu kai tayi batare datace komiba tafice, fita daga flat dinta tayi tai wani flat dake bangaren wanda tafito daga ciki, shiga tayi bayan tai sallama babu kowa a falon hakan yasa tai bedroom kai tsaye tun kafin ta shiga takejin hayaniya, muryoyin maza suna surutu, bude kofa tayi ta shiga da sauri, tsit sukayi kaman basu ke uban surutu ba da akejin hayaniyar su har falo, maza hudu ne adakin, uku ne atsaye duk suna sanye da Black suit da bakaken cover shoe sunyi masifan kyau da covers kaman wanda zasuje dai wani babban occasion, sai dayan dake zaune kan gado yana sanye da wani green wando dakeda layi jaa tagefe kafarshi sanye da farin safa sai jikinshi sanye da singlet. Agogon hannunta ta kalla kafin ta kallesu duka one after the other tace a"hiranku kawai kuke tayi daman ba shiryashi kukeyi kuda kuka cemin zakuzo tayashi shiri, kunsan karfe nawa? Oya kuwuce kufita kuje falo matan ku najiranku kufito dasu kuwuce mota gamunan zuwa" ta matsa daga jikin kofan ta nuna musu kofa alamun suzo su fita, sadaf sadaf sukazo suka fice one by one har dukansu ukun suka fita sanan ta maida kofar tarufe tayo inda dayan yake zaune yana kallonta murmushi shimfide kan fuskarshi, karasowa gaban gadon tayi tasa yatsa ta dungure mai kai tareda zubamai harara tace "biyema kannenka kayi kunata surutu instead of kashirya gashi lokaci yayi" murmushi yayi batare dayace komiba hakan yasa tasake watsamai harara taja ledan dake gefenshi wanda rigan sojoji ne keciki, hannu tasa ta zaro rigan tana balle maballin tace "oya stand up" tashi yayi ahankali dogone sosai dan yamafi mahaifiyar tashi tsawo, murdadde ne bana wasaba, ga wasu shati shatin six packs dayafito ta white singlet din dake jikinshi, baki ne shi very dark, yanada wani irin bright white idanu da gashin ido sosai bakake gasu dogaye yanada cikan gira gawani siririn hancin shi dogo dayakara ma fuskar nashi kyau, bottum lips dinshi is so so pinkish sai upper lips dinkuma baki hakan yabama bakin nashi wani irin alluring kyau baida gemu ko daya hakama saje baidashi kodan sabida anhana sojoji ajiyewane saisa oho. Yanada cikan jiki dan ko kadan he is not skinny one element dayasa aka dauke shi a soja shine tsayin shi dake karamai kyau koyana cikin mutum dubu zaka ganeshi sabida cikan haibanshi da kwarjini.
Ahankali yamika hannushi ya zura cikin hannun rigan kaman yanda Ummi tabashi sanan yamika dayan hannun yasaka yana kallon fuskanta yanda take rufemai boturan rigan, Murya chan kasa yace "Ummi yaushe zaki dena treating dina kaman baby wai?" batare data kalleshi ba tana sakanmai boturin tace "inka girma"
Dan turo baki yayi kaman zaiyi kuka yay exclaiming. "Ummi!" irin shine yaro dinan, murmushi tayi batare datacemai komiba har saida takarasa saka boturan rigan sanan tadago kanta ta kallai yanda yay da fuska yasa tadanyi murmushi taja hancin shi tace "inhar namiji baiyi aureba is always considered as yaro wanda bai girma ba bakaga yanda nake baka kaida Mu'az special attention ba why because bakuda mai kula daku, ni idan katambayeni wani zubin gani nake su Muhammad da Nuru sun girmeka dan sunyi auren su harda y'ay'a" tana karashe maganan tawuce abinta, wani clean takalmin sojojin shi dake kan shoe rag tadauko mai tana kallonshi yanda yadan bata rai tace "sa takalmin muje" tsugunnawa yayi yasanya takalman ahankali tareda kulle igiyoyin sanan yatashi yay gaban mirror shi yana takun nan daidai irin tafiyan maza dinan yaje yadau hadaddun turarukan shi ya fesa, sanan yadau wani black beret na sojoji yasaka ya gyara tama fuskarshi bala'in kyau, Ummi na tsaye sai kallonshi take tana murmushi juyowa yayi hakan yasa tai murmushi tace "har angama yaron kirki?" "Ummi!" yakara exclaiming sunan nata sabida baiso Ummi nakiranshi yaro, dariya Ummi tayi tace "to nadena sojana, mutafi" atare suka jera suka fice daga flat din nashi, ganin sauran har sun shiga mota already yasa suma suka shiga dayan motan kirar jeep, jeep din dayake ciki dagashi sai Ummi sun zaune abaya sai wani saurayi da shima ke sanye da suit baki kaman sauran mazan baikaishi girma ba amma sunyi kama yaja motar yana tuki yana tauna cingum. "yarda cingum dinan tunda kaiba mace bane Mu'az" Ummi tafada anatse kaman yanda tasaba magana, turo baki yaron datakira da Mu'az yayi yacire cingum din ya manna kan glass din motar yace "Ummi me cingum dina yayi? yau promotion night din Yayan mu amma am not still allowed to have fun, oh am tired Allah kaimu gobe nakoma wana school nabar muku gidan" bata kara kulashi ba dan rigiman Mu'az daban ce cikin yaranta, kodan yaga baida kani ne shine auta oho, tunda dai yacire shikenan aje ahaka. Hankalin shi nakan tuki yace "Yayan mu, Yayan mu" dagokai sojan yayi ya kallai yace "wat is it Mu'az, u are driving u need to be focus" kaman zaiyi kuka yace "ni dama nasani danabar Ya Muhammad ya tukoku this car is so boring duk kunyi shiru kuma nima sainai shiru, kullum kuyita shiru shiru kaida Ummi magana namuku wuya I don't know why, and magana is fun u know kasan mezan fadama ne" girgixa kai sojan yayi irin whatever dinan yacigaba da amsa sakonnin da aketa turomai na fatan alhairi da congratulations ta waya, agaban tangamemen checking point din Sani Abacha Barrack dake Asokoro Mu'az yay slowing down dan akwai motoci dayawa dake gabansu da ake dubawa kafin abarsu su shiga ciki, har aka kawo kansu, saukar da glass din motar kasa Mu'az yayi harda na baya ya kunna wutar motar hakan yasa motar tai haske wanda suka gani zaune abayane yasa suka wani irin kame mai tareda saramai. "Sir" gyada musu kai yayi yamusu alamu da hannu cewa su biyu ne da wanan motar data bayan su, da sauri sukama Mu'az alamu da yatafi motarsu Ya Muhammad ma haka tabiyosu abaya, agaban wani tangamemen Hall sukai parking inda aka tanada dan parking motoci sanan suka fiffito daga motar, da sauri Ummi ta shiga gyaramai kwallan riganshi kafin tai murmushi ta kalli sauran yaran nata tace "kumuje" Allah kadai yasan iya farin cikin datake yi yau, Ummi da shi sai Mu'az ne agaba, sai sauran yaran nata maza biyu da suma ke sanye da suit ko wanen su yarike hannun matar shi sunadan hira kasa kasa gwanin ban sha'awa suna biyeda su abaya, Ya Muhammad matar shi Nabila, sai Ya Nura dasuke cema Ya Nuru shine nabiyu agidan matarshi Nabila sai Ya Muhammad matarshi Fadila sai Mu'az auta yanzu yana 400 level mechanical engineering a ABU Zaria.
Gaban Hall din kadai zai shaidamaka cewa koma menene na manya ne, wajen yasha ado sojoji kota ina rikeda bindigogi, ga different families and friends na mutane sunata shigowa tundaga gaban Hall din aka shimfida wani hadadden red carpet da aka rubuta Nigeria is proud of you akai, shiga cikin Hall din sukayi looking compose sai kallonsu ake.
Babban Hall ne da mutane ke cike makil aciki, sojoji, Family, friends, government officials, and Media personalities.
💫 *_CHASING THE HEART CRAVINGS_* 💫
_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_
Doesn't favor you always💔
✍️ M Shakur
7️⃣ & 8️⃣
Anatse dukansu suke tafiya mutane sai kallonsu ake ana nunashi, ko kadan bai kalli kowaba gabanshi kawai yake kallo harsuka karasa chan wani table dake gaba da akasa name tag akan table din Maj. Gen Sameer Simran Sameer, table ne for almost 11 people, ahankali yasa hannu yajawoma Ummi dake gefenshi kujera yace "sit Ummi" zama tayi tareda shafa kanshi tace "thank you dan Albarka na" zama yayi kafin sauran su zazzauna suna kallon gaban Hall din inda lot of activities ke happening, daidai lokacin wani MC dake sanye da kayan sojoji cikin harshen harshen turenci yace "can we all stand for the national anthem" tashi tsaye dukansu sukayi, wasu sojoji da different uniform da trumpet 🎺 a hannayen su sukai layi agaban Hall din kan stage shiga busa trumpet din in national anthem tone ana raira national anthem kowa ya kame atsaye hall din bakajin ko hayaniya daya har aka gama sanan aka fara matching, different set of parade saida aka gama wani babban Field Marshal shine babban sojan Nigeria gabaki daya ya shigo stage din tafi aka shiga mai kafin a tsagaita yafara bayar da speech dinshi ta hanyar bayyana tsantsan farin cikin dayake ciki ayau banda haka yanama kowa barka da zuwa, yakara da cewa yau sun taru anan ne ba dan komi ba saidan karama some eloquent, magnificent and outstanding sojoji that put their lives on the line dansu kare this our blessed nation Nigeria, today we gathered here danmu karamusu girma badan komiba saidan yabama jarumta da kwazon su dan Allah atafa musu.
Tafi aka shiga yi pa pa pa, Nabila ce ta matse hannun Ya Nura murya chan kasa ta yanda su kadai zasuji kansu tace "Nooryluv" juyowa yayi yakalleta cikeda so yace "yes Nooryluv wife" murmushi tamai tareda dan sakinmai harara tace "kadenamin haka da idanu Ummi fa na nan" "tome ruwanta damu sonki yamaida danta haka ai" dariya tayi tadan tsunguli hannunshi data rike hakan yasa dukansu sukai dariya chan kasa atare, ahankali while staring at the stage yanda sojoji kekai komo sun bala'in burgeta tace "baby wai mesa baka zama soja ba kaima?" wani irin juyamata idanu yayi saikuma ya matso da bakinshi saitin kunnenta yace "banson soja saisa banyi ba, bakiga Yayan muba karfi yamai yawa, kullum cikin motsa jiki yake but I can make a deal for you" dan murmushi tayi looking excited tace "uu'hum" ahankali yace "wat about nai inserting my little soja a womb dinki tonight?" da sauri ta janye kunnenta jawota yayi da sauri yakara kai bakinshi saitin kunnenta yace "I promise idan nafara unzipping that your tiny hole baby har safe wlh bazan barki ba sallan asuba kawai zai dagani ina dawowa kuma zan cigaba, I will eat you to the extend sainai making sure my sperm are well placed and sitted in your womb" fizge kunenta tayi da sauri gabanta na faduwa, ganin yanda take zaro ido yasa yay murmushi da dan karfi yace "is a deal tonight" da sauri takai bakinta kunnenshi kaman zatai kuka tace "please baby kaga mubar maganan nibanyi accepting any deal ba wlh, beside our gurl is just 10 month old she is too small namata kani ko kanwa" tana maganan ta janye bakinta daga kunnenshi looking a bit sad, sa nashi bakin yayi akan kunenta yace "common gurl dat is not a problem, princess wurin Ummi zamu kaita inkin haihu" makemai kafada tayi tace "a'a niban yardaba banson gwaranni hakanan saitai 4yrs zamu mata kani gaskiya" "wlh baki isaba, namiki kokarin for good 10month dinan I've agreed namiki abinda kikeso no matter yanda nikeji haka zan hakura nayi withdrawing and release outside ni nigaji, I want to enjoy sex, your husband is good in bed why won't u have fun? Kuma children are blessing ko yara dari zaki haifamin inaso inada aiki da in sha Allah zan iya ciyar dasu, tonight zamu fara kinji" kaman zatai kuka ta kalli fuskanshi tace "agidan Ummi?" gira daya ya daga mata cikeda iskanci irin eh and so wat dinan, zatai magana sukaji an kira sunan Yayan su.
"Maj. Gen Sameer Simran Sameer, Maj. Gen Sameer Simran Sameer can we have you on the stage please?" tafi aka shiga yi, Mu'az harda buga table yana rawa yana ihu kallon Ummi dake gefenshi yayi yanda take tafi tana kallonshi, cike da farin ciki tace "tashi kaje Son" Nuru yace "yayan mu tashi kaje" ganin yaki tashi yasa Ummi tadafashi tace "tashi mana Son kaje ana kiran sunan ka sojana" ahankali yatashi daga kan kujeran tareda dan gyara riganshi wani irin ihu aka dauka a hall din ana tafi barinma yan uwanshi, tafiya yafara sojojin na saramai suna kamewa haryahau kan stage din sanan ya sarama Marshal dinsu kafin yay wani irin tsayuwa ya kame kaman zai hadiye numfashi irin yanda sojoji keyi dinan, cikin harshen turenci Marshal yace "Maj. Gen Sameer Simran Sameer has been promoted from Major General to Lieutenant General" wani irin ihu Hall din yadauka su Ummi da yan uwanshi suka tashi daga kan kujerun su suna tafi Nabila tafada jikin Ya Noor cike da murna suka rungume juna suna hamdala.
Vertical align emblem of cross sword and baton Marshal yadauka akan tray dawani soja yarike da aka shimfida red yafi haka akai, sai a star and Eagle duk ruwan gold ya makalamai su on both shoulder nan wasu sojoji sukahau busa trumpet na alamun ban girma, hawaye Ummi ta share tana murmushi she wishe his father was alive to witness this day jibi yanda ake karrama dansu, sai hotuna ake dauka ga yan news line awajen, an busamai sarewan na kusan minti biyar sanan aka gama, a ka'ida dama ana gamawa sojan da aka karama girman zai tafi yakoma wajen zamanshi yazauna, anatse cikin tafiyan shi na maza yafara tafiya zai tafi Marshall yace "not so fast Lieutenant, one more surprise for you" tsit kakajin Hall din, Ya Muhammad yace "Ummi kumu zauna ance akwai one more suprise" zama sukayi duk suna kallon stage din kaman suna kallon film. Anatse Sameer yakoma kan stage din tareda sake sarama Marshal ya kame, gyara microphone din bakinshi Marshal yayi yace "let's put our hands together for Alhaji Muhammad Mustapha Abdallah the chairman of NDLEA in Nigeria" Wani magidancin mutum ne sanye da bakaken suit sojoji biyu biyeda shi abaya suka taho sai tafi akemai yahau kan stage din yazo kusada Marshal ya mikamai hannu suka gaisa suna murmushi, Marshal yace "Muhammad Mustapha Abdallah was born November 13, 1954 in Hong, Adamawa State, He is a Nigerian Professional Security Officer who currently serves as the Chairman and Chief Executive Officer of National Drug Law Enforcement Agency after he was appointed into the post by President Muhammadu Buhari on January 11, 2016. He didn't just come here to grace this occasion No, he came for something even bigger amma karku manta ance waka abakin mishi tafi dadi ko" aka shiga tafi Marshal ya matsa gefe mutumin yana dariya yahau wajen tareda gyara 🎤 din yay gyaran murya yace "bakomi yakawo ni nan ba saidan muzo muyabama integrity, honesty dakuma jarumtar wani soja ba, da bai discrimination ta hanyar cewa ni soja ne wanan ne aikina wanan ba aikina bane a'a baya wanan, mutum neshi dat feels duk wata matsala data shafi kasarmu Nigeria inhar yagamu da ita zaiyi abinda yadace batare dayajira wasu ba ko ma'aikatan kan abinba, soja ne dat always put his country Nigeria first kafin kowani Al amari, soja ne daya tak amma tamkar sojoji dari, soja da sabida ayyukan shi ayau Nigeria zata buga kirji tace rate din production din kayan maye, kayan shaye shaye da yan shaye shaye sun ragu dakusan 30%, soja ne daya tak worth sojoji miliyan, I am here to present an honourable award of honor and recognition to non other soja than man of honor, man of the moment, man of integrity, a man that live for his country, can we all stand for Lieutenant General Sameer Simran Sameer!" yawani fadi sunan da karfi wani irin ihu aka dauka a hall din su Mu'az, Muhammad, Nuru da matayenshi tsalle suka shiga yi Ummu dai handkerchief tadaura akan idanunta tana share uncontrollably hawayen farin ciki dasuka shiga zubo mata non stop.
Dan Murmushi Sameer yayi tareda daga hannu dan he hardly smile, ahankali yakarasa har inda mutumin ke tsaye dawani hadadden award a hannunshi, hannu yamikamai suka gaisa, sanan yamikamai award din suka rike atare yan media anata musu hoto sanan Marshal ma yazo yabashi hannu yace "congratulations Lieutenant you deserve it" cikeda girmamawa yace "thank you sir" sai bayan sun gama hoton sanan Marshal ya karbi 🎤 din yace "hearty congratulations to you Sameer I must say, you deserve this, you deserve it Lieutenant" ihu Hall din yadauka da tafi saida aka dan tsagaita sanan Marshal yace "will you mind saying some few things? Come and say something about how you feel today, bazaka bar this stage without saying anything ba" ya matsamai aka shiga tafi sosai, takowa yayi yahau kan abin rikeda award din ya kalli dumbanin mutane dakenan makil a hall din ana kallonshi kafin yasaukar da idanunshi kan table din da yan uwanshi kekai yana kallon yanda bakunan su yaji rufuwa tsabagen farin ciki, ahankali ya saukar da idanunshi kan Ummi dake kallonshi tana share fuskarta da handkerchief tana murmushi, for the first time yasaki full smile dinshi a cikin Hall din cikin natsassiyar muryan shi yana daga award din yace "Ummi! This award is for you Mum" oh wow, oh wow, awwwn aka dauka a hall din ana ihu yayinda Ummi ta fashe da kuka sosai dan abin was so emotional da sauri Nabila da Fadila suka tashi daga kan kujerun su sukazo wurin ta suna lallashinta sukuma mazan suna murmushi. Anatse yacigaba yace "everything that I archive in this life is because of My Mum, My father died 25yrs ago, my Mother is an Iron woman, no she is my super woman she train 4boys and she thought us many many great things, part of it shine be truthfully Sameer, and everything you want to do in this life do it wholeheartedly, because anything that is worth doing then is worth doing well, give it your best my son" yay maganan yana kallon Ummi da Fadila ke pating shoulder dinta, murmushi yasake yi yace "this award is for you Ummi, and I love you, alot!" akahau tafi har Marshalsaida yamai tafi, Ummi kuma kuka, ahankali ya sauka yataho sojoji na kamemai ana saramai tashi Ummi tayi tawani irin rungume shi, rungume ta back yayi shima feeling calm and happy, dago kanta tayi tareda manna mai kiss a goshi murya chan kasa tace "am proud of you Sameer" mikamata award din yayi ta karba ahankali sai kallonsu ake ana daukansu hoto sanan suka zauna akan kujera, Ya Muhammad yamika mai hannu tareda saramai, Nur ma saramai yayi Mu'az kam rungume shi yayi cikeda murna yace "I love you Ya Sameer dina" kanshi Sameer ya shafa yace "love you too Kiddo" turomai baki yayi alamun baya so yana kiranshi kiddo hararan shi yayi, Nabila tace "congratulations Yaya Sameer" murmushi yadanyi yace "thanks Mum Princess" Fadila itama tace "congratulations yayan mu" itama dan murmushi yasakan mata dan baicika wasa dasu ba kuma yana mugun respecting nasu bamaya kirasu da sunansu yace "thank you Mum Little" shafamai kai Ummi tayi hakan yasa ya kalleta kafin ahankali ya rungumota suka cigaba da kallo program din har aka gama promoting sojojin dama su 18 za'a karama girma bayan angama akwai after party da su 18 din dudda Sameer baya ciki suka hada dan bai cika son hayaniya ba, yan uwansu suka hadamawa da abokan arziki, dudda yabasu kudi but ko kadan he's not interested, gamawa akayi tsaf sanan aka chanza wutan Hall din zuwa disco ball akai clearing babban stage din, sai wurin abincin serve yourself ne kawai akwai farin wuta aka fara rawa, tashi Nur yayi yamika ma Nabila hannu yace "let's go and dance baby" dan satan kallon Ummi Nabila tayi akunyace ganin hankalin Ummi baya kansu yasa ta tashi sukai gaba, Ya Muhammad ne shima yatashi yana daga Fadila sukai stage suma, kaman zaiyi kuka Mu'az ya kalli Sameer yace "Ya Sameer nima naje please?" dan hararan shi Sameer yayi kafin ya kalli agogon hannunshi shadaya da rabi yace "go but we all are leaving by 12, so you have 30min Ummi needs to rest and sleep" murmushi Ummi tayi she luvs it yanda komi Sameer zaiyi she is always first a lamuran shi, tafiya Mu'az yayi da gudunshi yarage su kadai akan table din, wayarshi yaciro daga aljihu dayaji tai vibrating sakonni ne keta shigowa Baffa yagani hakan yasa yabude sakon ya karanta sanan ya kalli Ummi dake ta kallonshi yace "is Baffa Ummi he's congratulating me, yace gobe shida family shi are coming over, bai dade da sauka ba" ahankali Ummu tace "kamai Allah huta gajiya ya gaida Maman su Aisha" gyadamata kai yayi ya shiga typing itakuma ta juyar dakanta tana kallon stage din yanda su Muhammad da matansu ke rawa irin couple dance dinan anatse gwanin ban sha'awa, juyoda kanta tayi ta kalli Sameer din dake shan bottle water, ahankali tace "Sameer kalli chan" ta nunamai kan stage, ajiye ruwan yayi ya kalli inda take nunamai, ahankali tace "basu burgeka ba? Kalli kanenka Sameer, inda ace Nabila batai barin cikinta na farko ba da yanzu yaran Nuru biyu, jibe Muhammad dat got married last year yanzu baby girl dinshi is 2month old, look at auta yanda yake girma yatasa shima, he is 25 now, Sameer so kake duka kannenka suyi aure subarka kosokake saiki tsufa tukunna zakai aure, bazakai aure ba tun da kuruciyan ka uhm Sameer....." "excuse please!" maganan dasukaji daga kansu yasa duk suka daga kai, wata doguwan budurwa ce tana sanye dawani red dinner gown dayamata kyau sosai, ta makala ID card awuya daya nuna ita media personality na NTA news ne, hannu tamika ma Ummi cikin harshen ta na turenci mai shegen dadi tana murmushi tace "congratulations Ma what an amazing son you have here, I must say you are bless Ma'am" dan murmushi Ummi tamata ta karbi hannun nata data miko mata tace "thank you" ahankali yarinyar ta kalli Sameer da yaciro wayarshi yacigaba da dannawa kaman bai gantaba, cikin harshen turenci yarinyar tace "please can I borrow your son just for few minutes, please Ma'am, plsssssss" taja
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 15