Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"school fine Yayan mu, kullum akemana C.A, kullum" batare daya kalleta yace "that calls for working hard more right?" washe mai baki tayi cikeda jin dadi ganin yau yana mata magana sosai tace "right Ya Sameer" murmushi maidan sauti yayi yacigaba dacin abinci ahankali sai kallonshi takeyi yanda yake kurban tea din kadai is breathtaking, yanayin komi da aji bada garaje ba, ita kanta batamasan mesa take kallonshi hakaba kaman zata cinyeshi, juyowa yayi ya kalleta sabida yanda jikinshi yabashi ana kallonshi hakan yasa tai murmushi tareda wayancewa da sauri tace "Ya Sameer kaga my friend is getting married ending of this month kuma wai Mummy bazata mini ankon ba, Ya Sameer zakamin plssss" gyada mata kai yayi hakan yasa tai ihu tareda tashi daga kan kujeran tana rawa, murmushi yayi yatashi daga kan kujeran plate din abincin ya nuna mata yace "take those to the kitchen kizo side dina later" da sauri tace "to Yayan mu nagode" karasowa cikin falon yayi yana kallon Mu'az dake buga game awaya, kafin yakaraso inda yake yace "Mu'az" da sauri Mu'az ya ijiye wayan dan duk in Ya Sameer ya kirashi har cikin ranshi yakeji da sauri yace "na'am" karasowa gabanshi yayi hannunshi daya cikin aljihu yana kallonshi yace "what time did you suppose to leave for school?" cikeda dan yanayin tsoro Mu'az yace "by 3 yayan mu zantafi" ka wuce kaje kafara shiryawa, tashi Mu'az yayi da sauri yay hanyar dakinshi daidai lokacin Princess tararrafo tazo har inda yake tsaye ta kama kafanshi tanaso ta mike tsaye, murmushi yayi ya tsugunna ya dauketa yaja kumatun ta ahankali yace "princess" kyalkyace wa da dariya yarinyar tayi tana shafa dogon hancinshi hakan yasa su Nuru dukansu suka kwashe da dariya, hararan su yayi kafin ahankali yace "let's go out they're watching us princess" _Dear VIPs na_ _this book is combination of storyline 2&3 which most of you chosen, when most of you keep selecting 2 da 3, i was like what is VIP if I can't give my VIP what their heart yearns? I was like okay 2 and 3 u guys are up, that's all what VIP is all about grant them what heart dinsu yearns for and liked._ _Dear VIPs na_ _life is all about making your Very special people(VIP) feel special, feel involve, feel worthy and feel muma munada daraja, treat them with respect and take them on a cruise of nishadi da farinciki, this book *chasing the heart cravings* kunshi komi, dan kowa na book din yabi abinda zuciyan shi keso, e.g ni yanzu nabi abinda zuciyana keso nake muku book ko? Haka kuma kunbi abinda zuciyan ku keso kukai joining VIP dan bakusan jira right? So come with me lemme give u on a journey of an unbeatable experience, and feelings that is mind blowing and out of this world cus this novel is blockbuster_ _subscription is 2k ba dan komi ba, I buy data, I sit and type always, power bank for always having chargi for regular updates and other pete pete matsala that your 2k can help me taushe it. I love you VIP na, and I am forever grateful of your support 🙏🏽 cheer to good live, endless friendship and love!!_ _pay 2k into my account 3107021073 aisha Muhammad first bank, send evidence of payment to my watsapp number 07012181461 so I can add you to VIP group, as of now this is VIP comment section_ _Happy Salla VIPs 🥂_ 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫 _CHASING THE HEART CRAVINGS_ Doesn't favor you always 💔 ✍️ M Shakur 1️⃣1️⃣ ********* Wuraren 9:30pm Mummy ta shigo flat din nasu tana kallon ko'ina na falon dan daga study room din Abban su take tamai rakiya sukadanyi hira kafin tabarshi sabida yasamu yayi aikin gabanshi, ganin su Siddiqa sunriga sunyi clearing falon wurin dasukaci abinci yasa tai corridor, ahankali tabude kofar dakin su Siddiqa, kwance tagansu dukansu ukun kan gado suna kallo da laptop din Siddiqa, ganin Mummy yasa Siddiqa tai pursing film din tace "Mummy" murmushi Mummy tadan sakar musu daga bakin kofan tace "na leko naganku ne, zanje na kwanta baban ku na study room dinshi sai chan tsakar dare zai shigo inya gama aiki, gud night girls" atare dukansu sukace "good night Mummy" gyadamusu kai tayi tace "adai tofa addu'an bacci kafin ai baccin" tajawo kofar su tasa hannu kan switch ta kashe wutan corridor sanan tai dakinta, bude kofar dakin tayi, hango Auta datayi zaune akasa chan karshen gado hannayenta na rawa sosai, ta sosa kai, ta sosa wuya da baki kaman wacce sabon hauka yakama yasa da sauri ta shiga ciki ta maida kofar ta rufe tasaka key sanan tasaka duka sakata biyu kofan na sama dana kasa sanan takaraso ciki da sauri tana kallon kulan abincin data kawo mata dazu kafin tawuce study Abban su, da sauri ta zauna a gabanta tadan balla mata harara tace "keme haka wai?" kaman jira take fashewa da kuka sosai tayi tana sosa kunnenta kaman an zuba wani abu a kunne tace "Mummy please kibani abin am not my self again, kaman zan mutu nakeji" cikin dan masifa Mummy tace "so kike kitonamin asiri baban naki na nan eh Auta" girgixa matakai tayi tama kasa magana sai kara rungume jikin nata tayi dake rawa sosai kaman mai farfadiya, dafakai Mummy tayi tana kallonta ga shegen kukanta damunta yake, tsaki tayi ta tashi daga wajen tai hanyar wardrobe dake dakin dakenan fari design dinshi irin na yan Italian, bude wardrobe din tayi saiga wata yar babbar safe a upper layer wardrobe din na chan saman, safe dinne kadai kawai awurin sauran kasan ne kayanta ke jere awurin, ga wani small circular keyboard a marfin safe din dake dauke da numbers ajiki dakuma alphabets, juyowa tai ahankali ta kalli Rahiman data dauke kai da sauri ganin Mummy ta juyo jikinta na rawa kaman yanda ta barta tana sosa kafadan ta wanan karan, ganin ba wurin take kallo ba tana fama da kanta ne yasa da sauri Mummy ta juya ta shiga danna numbers din wajen danta samu tai unlocking locked safe din. "GG879G" shi ta danna sanan tabude kofar safe din aiko yabudu, dawani irin gudu Rahima ta zabura ta mike tsaye kaman mahaukaciya tayo wajen Mummy na shirin kai hannu tarigata kaiwa, the fastest abu da hannunta zai iya grabbing tai grabbing kwalba biyu tajuya da sauri Mummy tabiyota tace "Mehaka auta eh? Bani nan, karkisha abin nan dis night kibari babanki yay tafiya, baninan nace" ayanda Rahima keyi ita kanta Mummy ta tabbatar cewa bamatasan metake yiba, juya marfin bottles din hannunta tashiga yi all the two at the same time hakan yasa daya ya sabule yafadi kan gado, da sauri takarasa bude dayan ta kafa zata kafa abaki Mummy ta fizgota luuu tayo baya da sauri takuma tareta dan tasan Rahima ba karfi fess zatai kasa tace "bani nan, that is too strong for you banriga na sirka mikishi ba, give it to me" kokawa da Mummy suka shiga yi ta ture Mummy tareda kafa kwalban abaki tana kwalkwala kaman numfashinta depend on it, tana gab da shanyewa Mummy tai nasaran fizgewa daga bakinta ta kalli dan wanda yarage aciki da baida wani yawa ta kalleta yanda ta cigaba da sosa wuya tana lashe lips dinta dake kyallin maganin tajuya tana kallon budaden safe din da akwai kwalaben almost 8 an rubuta benylin codeine ajiki, sai kuma wasu wrap takardu dayawa da aka musu nadi kaman na madaran kuka, da wani leda irin wanda ake sa counting paracetamol and other drugs aciki wani white yan fici fici dasu kananu, ganin yanda take kallonsu kaman wata mara hankali yasa Mummy tai tsaki tareda tsugunnawa tadau marfin datayar akasa ta mayar tana rufe bottle din tace "gobema ranace fitsararriya kawai, kozaki mutu ban kara baki" tadau dayan bottle din tajuya ta maidasu cikin safe, sanan tadau takarda daya da aka nannade kaman madaran kuka ta maida kofar safe din tarufe da karfi tsabagen haushin data bata sanan ta maida wordrobe din tarufe ta dawo ko kallonta batayiba tadau kulan abincin ta dauka tareda zama abakin gado, da wani irin sauri Rahiman ta taho ta zauna agefenta kaman zata shige jikinta tana kallon kulan abincin, ahankali ta bude kulan marfin ta cire ta mikamata da sauri ta karba ta yar akasa yay kara, cikin fushi Mummy tace "wai bazaki natsuba kosai kintaso kowa na gidan? Wlh zan fasa bakifa tom" maida hankalinta kan yar takardan tayi ta shiga warwarewa, wani irin bude baki Rahima tayi tana kallon takardan kaman idanunta zasu shige ciki, warwarewa tass Mummy tayi wani dagargajajjen ganyen weed ne ya bayyana, dan murmushi Mummy tayi takai hancinta ta shinshina kafin tasa yatsunta tadan debo tana murzawa feeling the texture tace "kin ganshi very fresh from farm wlh mai kyau daga wani kauye a yola nasa aka kawomin, inda kinsan kudin danake kashe miki da zaki dingajin magana na jibi yanda kikama CODE9 sha daya dan Allah bayan kinsan jinin ki baida karfi, uhmm nama fasa baki gwara na sayar nasan sayarwa nayi" da sauri kanta kaman zai cire tace "n......no p....l...." tama kasa magana miyau har fitowa yake daga bakinta tsabagen yanda take kwadayi, dan murmushi Mummy tayi tace "always do as I say kinji, kema kinsan duk randa Dady bayanan har ci kike kisha kiture dan kanki, karki karamin abinda kikayi dazu kinji" gyadamata kai tayi da mugun sauri tana kallon abun burinta kawai Mummy tajuye mata a abinci dan yunwa takeji sosai, ganin yanda ta kosa yasa Mummy ta shiga zazzaga mata akan abincin white rice da stew da plantain din, saida tajuye tass dawani irin sauri ta fizge abincin tazauna akasan dabas, hannu tasa tajuya abincin kafin tafara debowa cikin hannu tanaci, hannu baka hannu bisa kwarya kaman wacce tai shekara uku bataci abinci ba, Mummy sai murmushi take tana kallonta tadau bottle water gefen gadon ta tana budemata, in less than 2min ta cinye tass ta yarda kulan awurin da sauri Mummy ta mikamata ruwan, karba tayi ta kafa abaki saida tai kusan rabin ruwan sanan taja wani irin gyatsa, dariya Mummy tayi tace "yauwa Alhamdulillah, su yarinyar Mamanta ankoshi, yanzu anci abinci, jebayi ki wanke hannu kidawo sai bacci ko naga idanunki harsun chanza kala" gyadamata kai tayi tanaji duk wata matsalanta yakau hankalinta ya kwanta ta tashi bayi tayi feeling super happy, ruwa tabude a bathtub din Mummy ta tsaya tana kallon ruwan da idanunta dasuka fara wani irin lumshewa, saida ruwan ya cika tap yafara zuba sanan ta washe baki kafin tawani irin fada cikin bathtub din da kayan jikinta tai resting head dinta a inda akesa head ta lumshe ido tasa hannu tana wasa da ruwan kanta nawani irin juyawa, she is feeling happy, she is feeling exotic, feeling exceptional, feeling out of this world, shiru tayi tareda dena wasada ruwan tana lumshe idanunta da sukai fici fici tana budewa har na kusan 2min sanan tai murmushi daya bayyabar da white teeth dinta cikin wani slow voice and in a very slow tone tace "nima I hate you, you are a bad person, kuma bazan kara kiranki ba wicked kawai" shiru tayi kafin ta ciko hannayenta da ruwa takai bakinta tai kururururu da ruwan tana wasa kaman yanda yara sukeyi tawani irin fuzar da ruwan akasa cikin fushi tana kallon towel din Mummy dake ahange kan hanger tace "I hate youuu!!!" jin ihunta yasa Mummy tawani zabura tareda buga salati tace "innalillahi yarinyar nan zata tonamin asiri" da sauri Mummy tafada bayin salati tayi ta kashe tap din dahar lokacin ke zuba da gudu tawani jawota daga cikin ruwan hakan yasa ta bude ido kadan tanadan turo bakinta zatai masifa ganin Mummy ne yasa tawani irin rungume ta tace "Mummy naaaaaa, Mummy you are the best Mum, Ke kadai kesona, su Abba su Ya Siddiqa da wanan wicked din are all cruel people, Mummy na I love you sosai sosai" tadago kanta daga jikin Mummy ta kalli fuskarta tanadan lum lumshe ido tace "I love you Mummy naaaaaa" dan murmushi Mummy tayi tace "naji to cire kayan ki daura towel kije ki kwanta banson drama" Mummy tai maganan tana zage mata zip din bayan rigan tasake ta tareda jawo towel, sanan taja mata rigan kasa ta daura mata towel din kafin ta kamo hannunta sukafito, kan gado ta kwantar da ita tace "oya sleep now don't make anymore mess, am tired jiki da jini" tajuya zata tafi hannunta takama cikin tsantsan maye tace "Mummy tell me what you use to tell me" shiru Mummy tayi tana kallonta saikuma tadawo kan gadon ahankali ta zauna hakan yasa da sauri Rahima ta daga kanta ta daura akan cinyarta tareda lumshe ido tana sauke ajiyan zuciya, ahankali Mummy take shafa kananun kitson dake kanta murya chan kasa tace "Autana I always give you what you want for that sake no one should know our little secret koda za'a kasheki ne right?" da sauri ta gyadama Mummy kai tace "ri..........ght" murmushi Mummy tayi tace "nasanki Rahima na kuma San duk cikin yarana babu wanda yakaiki rike amana da keeping secret, nobody should ever know that you and Mummy use to smoke kinji" da sauri ta gyadama Mummy kai tana murmushi, Mummy tace "always keep it cool, I will always give you what makes you happy and painless, in the night but during the day time babu shan komi so that nobody will know at home dan mutane suna ganin abun baida kyau, but mu munsan anything that makes you happy ai yanada kyau ashashi ko Auta?" gyadama Mummy kai tayi tace" yes Mummy, murmushi Mummy tayi sosai tace "salla inkinga dama kiyi inkinga dama karkiyi am an advocate of kowa yay abinda ke sashi farin ciki, live your life to the fullest kome kikeso let me know okay, I will give u har rayuwata ba duniya kadai ba, am your best friend kome zai sameki kome zakiyi let me be the person you will always meet first and tell kome zakiyi aduniyan nan bazan taba miki fadaba daidai ne awajena kinji" gyadama Mummy kai tayi kafin tajuyo ta bude idanunta da sukai danja ta kalli Mummy da itama ita take kallo, cikin murya yar kankanuwa tace "Mummy wanan powder white dinan kaman dakakken chalk yaushe zaki banishi?" dariya Mummy tayi tace "in an kawomin" shiru tayi tana lum lumshe ido hakan yasa Mummy batasake cemata komiba, ahankali bacci yay awon gaba da ita hakan yasa Mummy ta kwantar da ita tareda tashi ahankali tawuce bayi inda tabata ta gyara sanan tai wanka tafito tana kallon Rahima datai dai dai agado tana tikan baccin ta, shiryawa tayi cikin kayan bacci tawuce tafice daga dakin tai dakin Abban su dudda yana study but inya dawo zai samsta anan dan batason anything dazaisa yaje dakinta. Around 5:02 ta tashi jin muryan Abba na kiranta, a firgice ta bude idanunta dasukai jajir dan kowani gaban jikinta najin kiran Abba ta kallai tanadan sassauke kai, babu alamun wasa kan fuskarshi yanuna mata kofa yace "wuce kije ki dauro alwala kiyi salla" gyadamai kai tayi ta tashi ahankali dan jiri take gani sosai bacci bai isheta ba, ganin tayi hanyar bayi yasa yajuya yafita dan sauri yake antada salla, bayin ta shiga ta wanko fuskarta tadauro alwala tafito tana kallon ko ina na dakin tadanji dama dama dan jirin yaragu sabida wanke fuskar datayi, wurin wardrobe din Mummy tayi tana kallon kofa da sauri tabude wardrobe din, hannunta tamika ganin hannunta baikai safe din dake chan sama ba yasa da tai wajen mirror, kujeran wajen ta dauko tahau kai ta tsaya hakan yasa takai safe din, password din da taga Mummy tasa jiya ta shiga sawa dan tana gani ta haddace shi tsaf akanta, bude safe din tayi jikinta har rawa yake, one bottle of codeine ta dauko gudun kar Mummy tagane sanan tasauko kara daya na wiwi tana waigen kofa, gyara zamansu tayi tsaf gudun kar mummy tagane sanan ta maida safe din tarufe tasauko tadau kujeran ta maida inda yake gaban madubi, sanan tadawo tarufe wardrobe din taboye abubuwan a jikin towel dinta sanan tabude kofa tafita tai dakinta, da sauri ta maida kofar tarufe jakar makarantan ta ta dauka ta zuba su aciki sanan ta rufe ta ijiye tana murmushi har wani murna takeyi kafin tai bayin ta, brush tayi sanan tai wanka tafito daure da towel, mai tadauka tafara shafawa saida tagama tsaf sanan tasake fadawa kan gado taja bargo ta lumshe ido ko minti biyu ba'ayiba bacci yasake awon gaba da ita. Cikin bacci taji ana shafa mata fuska bude ido tayi da kyar tana turo baki ganin Mummy ne yasa ta mirgino ta daura kanta kan cinyar Mummy cikin muryan bacci tace "Mummmmm niban tashi ba" dagata Mummy tayi tace "tashi kafin Abban ki yakara tambayan ki, kinyi salla?" girgiza ma Mummy kai tayi ashagwabe, hakan yasa Mummy tace "toki barshi basai kinyiba, tashi ki shirya school, kinga yau zaku riga baban ku fita saisa naciro miki wanan abayan da gyalenshi ki saka banso kisa jean baban ku yahau miki fada" saukowa daga gadon tai da sauri tadau doguwan rigan da Mummy ke nunamata data ijiye kan kujeran mirror ta warware doguwan rigan tana daure fuska, hadadden doguwan rigane mai bala'in kyau na Dubai bakine complete babu kwalliya ajikinshi sai hannun doguwan rigan da aka bishi da wasu silver kullatai da akai musu design din flowers yay mugun kyau rigan. Cikeda rigima sosai ta kalli Mummy tace "Mummy nine zan sa kayan nan? Ni wlh bazan saba so ake zafi yakasheni eh" cikeda lallabawa Mummy tace "haba Auta na, Ke kinfiso ayita miki fada na yaune kawai gobe baban ki zaiyi tafiya yabar mana gida zakiyi yanda kikaga dama kinji" wurga rigan tayi chan wajen kofa tace "wlh ni banaso ni english wears zansa" dafakai Mummy tayi ta kalleta yanda ta zauna akan kujera ta juyamata baya tana kumbure kumbure, tasowa Mummy tayi takaraso har gaban madubin ta bayanta ta tsaya ta dafa kafadarta tana kallon fuskarta ta madubi tace "haba my fine princess, Princess Rahima na, yar lelen mamanta, duk gidan nan babu wanda zai nunamiki kyau wlh kai duk Abuja ma, beauty yar gidan Judge, yarinya inba dandan president ba sai rijiya adanmini murmushin nan mana" Mummy tadan chakuleta hakan yasa tafashe da dariya, ganin tafara dariya yasa Mummy tadauko rigan tace "imaza shiryo kici gayu kifito ina jiranki kizo kiyi breakfast kinji" gyadama Mummy kai tayi Mummy tawuce tafita. Shiryawa tayi cikin dogon rigan tadau gyalen ta yane kanta dashi tadau wayarta tajefa cikin jakanta sanan ta giya jakan tabude kofa tafito tai falo, zaune taga duka yan gidan nasu a dinning, tunda tafito Abba ya tsareta da idanunshi dake cikin fararen glasses hakan yasa takaraso ahankali tayi kusada Mummy, da hannunta shiga wasa kafin murya chan kasa tace "ina kwana Abba" tea Abba yakai baki ba yabo ba fallasa yace "lpy" juyawa tayi ta kalli su Siddiqa da suma duk sun shirya zuwa makaranta dan hararan su tayi ta gefen ido sanan tace "ina kwanan ku" Siddiqa ce kadai ta amsa dan sauran basuda lokacin dan iskan gaisuwanta. "kin tashi lpy Rahima" ko amsawa batayiba tazauna kusada Mummy suka faracin abinci, tea kawai ta iya tasha dan ko kadan bata iyacin abinci inba Mummy ta samata abinda tasaba samata ba, batajin dadin cin normal abinci saida suka gama tsaf sanan suka tashi, 5k Abba yaciro daga pocket yamikama Siddiqa yace "gashi nan dukanku, adawo lpy" sanan ya kalli Rahima da nugayen ido yace "kibari akawomin karanki kiga abinda zai faru yau, kuwuce kutafi" wucewa sukayi suka fita, gaba Rahima tayi fuu tabarsu tana zuwa tabude gaba ta shige ta rufo kofar da karfi, da sauri Luba tace "iyye Ya Siddiqa bakene ke zama agaba ba, bari naje nafadama Abba" hannunta Siddiqa tarike da sauri tace "kubarta, muje inada hot presentation this morning, banda lokacin Rahima yanzu" duk shiga bayan motan sukayi direba ya shiga yajasu har zuwa University of Abuja, Siddiqa yafara saukewa agaban department dinta na Accounting tana 400 level, dubu dai dai tabama Zeena da Luba, duk suka mata godiya sanan tajuya tagaba tabama Rahima nata 1k din ta hanyar ajiye mata akan jiki, cikeda tsiwa Rahima tadau kudin ta jefar ta window tace "mezanyi da kazamin kudin ku? Mummy na tabani ☓2 of your chicken change, 10k dan haka banso" cikin tsananin fushi Siddiqa ta kalli kudin data jefo mata akasa tace "ni kika jefa da kudi Rahima?" "baki fasamata baki bane saisa har yanzu take mana iskanci" cewan Luba, ganin abin na neman zama rigima yasa Idris direba yace "dan Allah ayahakuri, bakuyi fada agida bane zakuzo kuyi a makaranta gashi anata kallonmu, kinga Siddiqa wuce ajinku kiyakuri yarinya ce" cikeda tsiwa Rahima tace "wlh ka kara cemin yarinya saina katsama mari hala nama kala da yarinya" bude marfin gaban motan Siddiqa tayi ta fincikota waje ta bala'in tsorata hannu tadaga zata wanketa da mari da sauri tarufe fuskarta tafashe da kuka jikinta na rawa tace "wlh kika dekeni saina gayaki da Mummy" sakinta Siddiqa tayi ta matsar da ita gefe ganin duk yanda ta tsorata sanan ta kalli direban tace "kaisu Lubabatu department katafi tajama kanta da kafarta zata taka tundaga nan har Vet wlh" tai maganan tana rufe marfin motan, direba yaja yay gaba, buga kafa ta shiga yi akasa tana kuka sosai Siddiqa tai tsaki tace "sai girma ba hankali, katuwa dake kina kuka cikin makaranta gashinan sai kallonki ake, ki kwana anan" juyawa tayi tai tafiyanta cikin department dinsu tabarta awajen sai kallonta ake. Sauke jakanta tayi daga baya tana kuka tabude ta ciro wayarta ko tsayawa rufe jakarma batayiba tarike adayan hannun ta shiga neman layin Mummy, horn taji an danna mata da sauri ta daga kanta da idanunwanta dasuka rine da hawaye, kallo daya tamishi ta dauke kai wani shegen yaron ajinsune Chriss sunanshi Christian ne dayasamata ido, ajinsu daya shima Veterinary medicine yakeyi, duk inya ganta saiyace Hi beautiful amma ko kulashi batayi, fitowa yay daga motan da sauri hadadden guy ne yaci gayu sosai da wandonshi dayay ass down gawani hadadden sneakers akafarshi da katon sarkan cross yakaraso gabanta, cikeda damuwa yace "Hey Beautiful what happen? Why are you crying like this? Who was that Goddamn gurl that drag you out of the car?" yay maganan cikin fushi, daure fuska tayi tasa hannu tana share hawayen daya gama wanke mata fuska, cikin bala'i tace "is none of your business, leave me alone" "noo I can't, I can't leave you alone, u don't look good beautiful, let's go we have class by 9, and is to 9 now" kallonshi tayi da dara daran eyes dinshi, murmushi yamata yadan daga mata gira daya tareda cije lips dinshi yace "please beautiful let's go, I know u can't walk from here to our department, so let's go okay, plsss her majesty, plssss " yawani ja please din, dauke kai tace "okay" murmushi yayi cikeda jin dadi yana bala'in son Rahima tun rana na farko data fara attending lectures, batama uban kowa magana a ajin dudda yanda kowa yake shigemata gashi sai mahaukacin kokari da inba kaga tana amsa tambaya ba baxaka taba cewa tanada kokarin ba. Hannu yamika yace "lemme help you with the bag beautiful" murmushi tadanyi dan haka takeso ana treating dinta kaman sarauniya ta mikamai karba yayi da sauri yataho yabude mata shiga tayi sanan yarufe yazagaya ya shige shima yatada motar. 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫 _CHASING THE HEART CRAVINGS_ Doesn't favor you always 💔 ✍️

Chapter 5 of 15