Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
is big for you dan crack can kill you wlh, oya let's see how many kalan buso hayaki kika iya let's play a game" yay magana yana bata mouthpiece din shishan, shima ya rike nashi mouthpiece din, yace "let's do it in one, two, annndddd three" atare suka zuko shishan kafin su janye daga baki, shiya fara mata alamu ta kalleshi hakan yasa ta kallai yawani irin huro hayakin daga hancin shi in style din circle circle, ware ido tayi kafin ta huro nata hayakin ta baki yay wani irin saman dakin kaman an bude teargas tafi ya shiga mata yace "yayyy beautiful u are really smart, ya kikaji shishan strawberry flavour ne yahadu ko" murmushi tayi bamata kulashi ba tsabagen yanda shishan yamata dadi takara kaiwa bakinta, murmushi yayi ya dauko kara daya na weed yaciro lighter daga aljihun shi ya kyasta sanan ya maida lighter yakai weed din bakinshi ya zuka hakan yasa ta kallai tana huro hayakin shishan, karan weed din yamika mata yace "zaki sha?" hararan shi tayi tace "give me a new one" dauko wani yayi ya kunna mata yabata karba tayi tashaka ta fuzar sanan tasha shishan tana murmushi today is just the best day of her life, inda ace su Ya Siddiqa sundan dadin abin nan da saisun saye duka weed da codeine din duniya gaba daya, lumshe ido tayi ta wani irin jingina da bango bacci nawani neman kwasheta dan abubuwan sun soma bugar da ita tun tana bashi amsar maganan shi harta zo bamataji da kyau, zata karakai dan gutsuren weed din bakinta Chris ya karba da sauri da mouthpiece din shishan ya ijiye su kan table yace "hey beautiful, you have had enough, don't want you to pass out is okay" dan turo baki tayi cikeda rashin jin dadi murya chan kasa da bata fita sosai, very slow tace "give me the shisha" hannunshi yasa ya shafa soft kumatunta yana kallon yanda take lumlumshe ido murya chan kasa cikeda sonta yace "you are the first Muslim girl I've ever loved in my life my god u are so beautiful, so pretty" dan bude ido tayi kadan ta hararai kafin tasa hannu ta kabar da hannunshi dake kan kumatun ta, cikin magagin bacci da maye tace "stop touching me" dan kara matsowa kusada ita sosai yayi yanajin tashin kida alamun mutane sun fara zuwa kenan dayake ansan yana tareda babe saisa ba'a zo an tadashi ba, matsowa kusada ita sosai yayi ya manna ma kumatun ta kiss ahankali yace "baby stand up mu kwanta akan gado, your Mum said we should have fun so let's have fun" yay maganan yana kokarin daga ta tureshi tayi batare data bude idoba tace "leave me alone" ganin tanada gardama and she is a lil bit stubborn yasa yawani irin fizgota jikinshi, da sauri ta bude idanunta dasukai jajir tana kokarin tureshi amma yaki barinta wani irin ihu ta kurma amma ko kadan ba'a jinta sabida karan kidan dake tashi agidan, kama fuskarta yayi tana kokarin kwancewa ya manna mata kiss abaki ya shiga laluban boobs dinta da tuntuni suke idanunshi baida burin dayawuce yaga yataba........ Wuraren four ya shigo Abuja hakan yasa yakara gudu sabida yakamata yay attending meeting dinan is his first meeting as lieutenant, kuma meeting ne da harda Chief of staff din Nigeria akan how to ensure security a Nigeria, yakai ta wuraren express road din Abuja wayarshi ya shiga kara, kallon wayan yayi while driving ganin Marshal barobaro kan screen yasa yarage gudun motarshi yagangara gefen hanya yay parking tareda daukar wayar yay answering call din tareda kamewa yace "Sir!" daga tachan bangaren Marshal yace "Lieutenant that meeting is not going to hold, am in the airport going out of country right now, until I get back" anatse yace "I wish you journey mercy sir" "thank you Lieutenant" ya katse wayan, ajiyan zuciya ya sauke tareda sauke ajiyan zuciya Allah nasonshi sosai dudda ya iso Abuja inda ace akwai meeting din babu yanda zaiyi yakai Barrack batare dayay latti ba, yin latti kuma is considered as unethical aspect of his profession, wani mahaukacin sauti daya daki dodon kunnenshi yasa yabude ido da sauri motace dake dauke da saurayi guda daya sai yan mata biyu akai dasuka sha attachment suna cikin wanan motar mara marfin sama, saurayin na driving da hannu daya yana shan shisha da hannu daya, bin motar yay da kallo hartai dan gaba kadan sanan tawani sha kwana, shi mutum ne dazaran mind dinshi yabashi yay abu yake, hakanan suna wucewa yaji kawai yanaso yabisu, tada motar yayi yakarasa har daidai inda yaga sunyi kwana ya kalli layin motoci yagani pake a wurin daban daban hakan yasa yay kwana ya shiga layin tayoyin motarashi sai taka kwalban su tutolyin yake, kashe motar yayi bayan yay parking abayan wata mota camry dayagani awurin yanajin tashin kida ga samari cike a awajen wasu kan saman mota suna zukan taba, wasu kuma na shan shisha ga mata gefensu, wasu rike da kwallaben giyoyi, ga ihu dayaji yana tashi tako ina, kashe motar yayi yana kallon yaran yace "why are all this Indomie generation so stubborn? Me sukeji a shaye shaye bayan clearly yana rubuce ajikin taba and other stuff cewa shaye shaye na kisa da wuri? Why are children taking what is harmful to their health" dan tsaki yaja yadau wayarshi ya shiga turama number dayay saving da NDLEA sako. _"am at kaduna-kano express road, some bunch of gang are partying with loud music on and using hard substances and other illicit drugs which according to constitutional law of Nigeria clearly state that they're illegal and as such anyone caught on such act must go for six month rehab, you need to invade into this premises and investigate properly with immediate effect, let's all come together and make Nigeria great again"_. *Lieutenant Sameer Simran Sameer* Ko minti daya baiyi da tura sakon ba sukayo reply "stay there lieutenant, we are on our way", gyara zama yayi yana kallonsu dudda su hankalin su bayama kanshi shaye shayensu kawai suke suna rawa suna wasa da yan matansu dabasu da banbanci da karuwai suna turenci.💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫 _CHASING THE HEART CRAVINGS_ Doesn't favor you always 💔 ✍️ M Shakur 1️⃣7️⃣ Tashi yayi yawuce bedroom dinshi ranshi abace wasu kananun kaya ya dauko, Black jean yasaka sai wata Ash color riga short sleeve mai gajeren hannu yasaka, rigan nada V neck daya bayyanar da kwantaccen gashin kirjinshi, rigan ta kamashi sosai, kaman rigan zata barke ajikinshi sabida yanda ta bayyanar da kiranshi na full packs man, Black jacket yadauka yadaura kan rigan yasaka wani boot baki yadau car key dinshi, kana ganinshi kaga soja yafito daga flat dinshi yaso ya shiga wajen Ummi but no Inya dawo yaje, he don't want to waste anytime, motarshi ya shige yaja tareda danna horn mai gadi ya budemai gate yabar gidan. Tashi Ummi tayi daga jikin window bayan taga taga fitanshi jikinta ya mugun yin sanyi takoma kan gado ta zauna ta buga uban tagumi cikeda damuwa ta daga hannayenta sama tace "wanan wani irin jarabawa ne Ya Allah meke damun Sameer ne dako kadan mace bata gabanshi?" tai dan shiru tasa hannu tai maza ta goge hawayen dake shirin zubomata, tasowa Nuru yayi yazo kusada ita yabata side hug cikeda damuwa yace "Ummi kidena damuwa okay, kidinga mai addu'a in sha Allahu har jikokin shi zaki gani nan bada jimawa ba kuwan" fuskar Nuru ta kalla tace "anya? Kaduba pa am sure sabida maganin dana gayamishi Baffa shi yakawomai ne yau da safe yasa yaki shigowa dan baisoma yasha, Noor ya zanyi da raina eh? Yayanku fa Noor duk ya girmeku nesa ba kusa ba, yabaka almost 8yrs but look at you now da Nabila batai having miscarriage ba da kanada yara biyu aduniya, I tot yanda na kawo maganan Asiya he will accept da gudu sabida cousin dinshi ce kuma naga suna shiri yarinyar na sonshi sosai, bazai wani sha wuyan neman aure ba dan da gudu Baffa zai bashi ita amma kalli abinda yama" ahankali Nuru yace "Ummi kibar maganan Asiyan nan, it won't work, ai dama tun kafin kiturani na gayamiki kice Yaya Sameer ya auri Asiya ai kaman kin kara koranshi daga zancen auren ne, Yaya Sameer dason girma tsiya inya auri Asiya ai kaman ya yankin ma kanshi ticket din raini ne, ni nasan dama bazai taba koda da wasa he will not accept maganan nan, kawai kiyitamai addu'a Ummi what goes around comes around, Yaya Sameer zaiyi aure one day one day" cikeda damuwa sosai Ummi tace "Ya Allah, Ya Allah kadubi lamarin nan nawa, Ya Allah ka karkata zuciyan Sameer zuwaga wata mace, Ya Allah kahadashi da wacce zaiso sosai, Allah ka aurarmin da yaron nan badanni ba badan halina ba" tasake share hawaye daya zubo mata rungumeta Nuru yayi yace "is okay Ummi ya isa hakanan" haka yacigaba da lallashinta har Muhammad shima yadawo duk suka taru suna bama maman nasu baki harsuka samu ta dawo normal tadan wartsake tabiye musu sunata hira. Tunda aka shigo dasu headquarter anan reception aka zubesu duk wanda zai wuce saiya kallesu, gabaki dayansu akasa suka zauna bama abasu kujera ba, Rahima tai kuka har idanunta sun kumbura kaman zaka taba jini yafito, daukan sunayen su akayi gabaki dayan su saiga wata mata ta taho da kayan first aid box a hannunta tareda daya daga cikin officers din dasuka kawo su suka taho gaban Rahima. Rahima yanuna mata yace "ga wacce batason ta mutun nan amma take shaye shaye, duba kafan Dr, tai targade Lieutenant ya gyara mata dazu" murmushi Dr tayi ta tsugunna a gabanta tana tattaba kafan ahankali kafin ta bude first aid kit din tadauko wani man zafi ta shafa mata sama sama tace "ya gyaru kamai muscles pain take having, wanan balm din kuma will kill it nan bada jimawa ba" sakin kafan tayi auduga ta dauka ta daura kan goshin nata tana share mata jinin wajen tace "what is your name yanmata?" shiru Rahima tayi batare databata amsaba tai banza da ita hakan yasa Dr din ta kalli fuskarta tacigaba da aikinta tace "young girls kaman ke always think shaye shaye is a gateway to having fun, inspiration, zero worries da sauran, aganinku shaye shaye wayewa ne irin kema kin isan na, but my dear is a lie bahaka abin yakeba, yes nasan shaye shaye nasa ka manta da matsalolinka, ka manta da bakin ciki da duk wata damuwa data addabi zuciyarka, kaji kaman kai kadai Allah ya hallita a duniyan nan, kaji yes a yanzu u can stand up to anybody kodakam babanka ne, inkayi you can stand up against anyone and anything in fact u can even stand against the world, shaye shaye nabaka wanan karfin da boldness din da jarumtar aganin ku but my dear is not true, duk ba hakabane, shaye shaye is mess with the heart and mess with your brain the IQ dinki, baya komi illa destroying dan Adam, tundaga na lafiyan shi harda sauran su and kill u wulakantaccen killing ma, but you know you still have time, u are young, you are too beautiful karki bata rayuwanki akan wanan shaye shayen da kikejin dadinshi nayan mintoci, see duk abinda dadinshi ba dawwamamme bane den babu amfani yi, dadin da last for few hours ko for a day dadi ne? Ki natsu kituba Allah zai yafemiki kisan me kikeyi kokya samu rabauta" tana maganan tana shafa gyaramata injury din goshin nata sanan ta shiga hada kayanta, ahankali Rahima tasa hannu ta share hawayen dasuka cika idanunta suka sake zubowa sharr, ganin Dr looks friendly yasa murya chan kasa tace "I want to use the restroom" dagokai Dr tayi ta kalleta jin tamata magana for the first time, murmushi ta sakin mata tace "stand up muje na kaiki" ahankali ta tashi tana dafa bangon wurin tanadan dingishi suka wuce itada Dr din, officer yace "kuma two minutes nabaki" da Dr suka tafi daidai sunkai wajen bayin wani yafito daga wani office ya kwalama kira yace "Dr you are needed here" da sauri ta kalli Rahima tace "shiga this is the rest room, zakiga ladies side inkin shiga" tai magana tana tafiya, bude kofan Rahima tayi ta shiga rest room din, dan passage ne awajen dakeda two pathways dama da haggu da akwai kofofi, ko kadan bata lura da sign din ladies da gentlemen ba take nuna Wannene bayin maza dana mata ba tabude kofar dama ahankali tanadan dingishi ta shiga, maida kofar tayi tarufe tai ciki, saida tai dan tafiya sanan ta iso main falon bayin wasu jerin bayi guda shida ne sai wash hand basin da manya manyan mirror a bangon, da sauri takarasa tabude bayin farko ta shiga ta mayar ta rufe, bayin so clean babu datti kodaya kodan bayin maza ne saisa oho, but bayin mata dai always yacika datti, mayar da kofan tayi tarufe tasa sakata sanan ta daga riganta sama tasa hannu a aljihun bayan wandon ta taciro wayarta da tuntuni take wurin Allah yaso ta babu wanda ya kirata da asiri ta yatonu sun kwace dan duk an karbe wayan sauran, maida wayan silent tayi da sauri sanan taciro number Mummy tana goge kwallan datake yi tai dialing number har wayan ya katse ba'a daukaba, haka tasake kira shima ba'a daukaba fashewa tayi da kuka tayi mara kara tana taushe bakinta, ba karamin tashi hankalinta yayiba takira mummy sau 17 times bata dauka ba bakaramin tashi hankalinta yayi ba yanzu kwana zatayi a wurin nan, gashi an fara kiraye kirayen sallan magrib, share hawaye tasakeyi, ahankali tasa hannu ta sauke cover bayin, zama tai kan sitter ta rufe fuskarta da duka hannayenta tana kuka tajima ahaka sanan tai shiru ta share idanunta tana kallon wayan sanan ta shiga saka wasu nambobi tadanyi jimm tana kallon number kaman mai tunanin wani abu kafin ahankali tai dialing number tasa hannu ta share hawayen daya zubomata takara wayan a kunenta, har wayan tagama ringing ba'a dagaba hakan yasa tasake dialing number akaro nabiyu, wayan na gab da tsinkewa aka dauka batare da ance komiba, ajiyan zuciya ta sauke mai kara kafin cikin muryan ta dake rawa sosai tace "h......he.....hello" hannu tasa tasake share hawayen daya zubomata tareda jan majina irin na wanda yaci mugun kukan nan, ahankali cikin kuka tone tace "In..i.....ina police station ankamani dazu, please come and get me Mama, am so scared, please come and get me kinji" tafashe dawani irin kuka mai tsuma zuciya, katse wayar akayi batare da ance komiba hakan yasa ta kifa kanta abangon bayin tafashe da kuka sosai, tai kuka na kusan minti biyar sanan tadago kanta tasake dialing number, ringing daya wayar tayi akai picking call din kafin ma tai magana muryan wata mata tarigata tace "I told you time without numbers karki kara kirana in your life, I don't have anything to do with you, an kamaki a police station what is my business with that? Mahaifinki judge ne so call him up not me, banda alaka dake or anything yarinya, stop calling me Mama mamaki kin barota achan gidan ubanki, in danta ninema rot a police station din ko agefen yatsana stupid girl, mtsww" ta katse wayan tareda jamata dogon tsaki, wani irin kuka tafashe dashi she is feeling kaman ta shake kanta ta mutu why did she even call this woman? takai almost 10min tana kuka kafin tadago kanta ranta yay mugun baci, cikin fushi tasake dailing number matar ringing daya aka dauka kafin matar tai magana tarigata tace "you know what calling you was the biggest mistake danayi sama da mistake din dayasa aka kamani aka kawoni nanma, how can I think a wicked woman like you can help me? Your heart is so black and dark da baisan menene help ba in this life, I hate you nima, I hate you with every single heart beat dina, My Mummy is better than you sau miliyan she can't never ever stand and watch me in pain, she is the best Mummy in the world, best Mummy, the absolute best, and I love her, I love her with all my heart, I can ever rot here saidai in Mummy na bata duniya, inhar nakara sa wanan hannun nawa nakiraki ba sunana Rahima ba, trust me inda ace Allah na laifi dazan iya cewa laifin dayayi shine yabama a wicked woman like you ciki harta haihu you deserve to be a barren cus you don't have soul saidai Allah baya laifi, I hate u, I hate......." katse wayan da akayi dip yasa tazare wayan daga kunnenta ta wurgar da wayan a kasan bayin ta shiga rera kuka tana kiran Mummy, she is so sad, she is so so sad, how can she even think if calling this woman mema yakaita eh? Mema yakaita, buga kofan bayin datake ciki taji anyi. "open the door" 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫 _CHASING THE HEART CRAVINGS_ Doesn't favor you always 💔 ✍️ M Shakur 1️⃣8️⃣ Muryan mace taji, azabure ta tashi tsaye ta shiga kalle kalle bayin tana neman inda zatabi ta gudu, dan karamin window dake wurin babub abinda zai mata dudda rashin kibanta bazata iya wucewa tawajen ba hakan yasa ta tsaya tana kallon kofan tana share hawaye batare data bude kofan ba, cikin tsawan matar tace "I said open the door Lady, da uban wa kike waya abayi haa, and maiya kawoki bangaren maza, open the door!" aka mugun daka mata tsawa da yasa ta matso kusada kofan tasa hannunta kan sakatan tabude, turo kofan officer tayi batai wata wataba ta dauke ta da mari tass! Rike kuncinta tayi tana dafa bango, tsugunnawa officer tayi tadau wayar data yar akasa tasa hannunta agaban riganta tawani irin finciketa tajata tareda bude bayi suka fita, suka fito main waje daidai lokacin Sameer ya shigo wajen shida wani dake rike da byro da wani paper dayake nunamai. Ganin yanda ake kallonta yasa ta hadiye kukan datake yi ta dage ta ture hannun officer data kama mata gaban riga tace "dalla malama kidena jana tunda ni ba akuya bace muguwa kawai" da hannu officer ta nuna kanta tace "ni kike cema muguwa?" hararanta tayi da idanunta dasukai jajir suka kumbura tsabagen kuka tace "eh ance muguwa azzaluma m....." tass! Officer ta dauke ta da mari saida Sameer dake duba list yadago kanshi ya kallesu, fashewa da kuka sosai Rahima tayi tana shafa inda ta mareta tace "ance muguwa azzaluma, uban mena miki zakiyi ta marina kina jana, what have I done, banza kawai wacce tai kwantai ba miji" wani dan gajeren murmushi Sameer yasaki da gefen baki, ya maida kanshi kan list din da aka bashi yana dubawa zagin ya mugun bashi dariya ne tayaya akai tagane tai kwantai batai aureba, ohhh this Indomie generation children are damn hilarious. Cikin fushi matar ta waiga ta kalli all the staff dake aikinsu abinsu dan irin wanan fadanne tsakanin yan shaye shaye dasu sun saba gani is not a new thing, hannu tasa tadau kulkin dake kan desk din Kusada su tace "zanci ubanki ne yau" cikin tsiwa tana kuka tace "ubana yafi karfin kicishi wlh, a inda ubana zai ubanki bai isa ya tsayaba saidai yazo bara" bugamata kulkin officer tayi a kafada hakan yasa tafasa wani wawan ihu da saida kunen kowa ya amsa, sake dago kai Sameer yayi ya kallesu ganin haka yasa officer dake nunamishi list din yajuyo yace "officer!" batare data kalleshi ba tace "officer I caught this gurl tana waya abayi shine on top of that takemin rashin kunya tana zagina, tana....." juyowa officer tayi zatai magana chairman yabude kofar office dinshi yafito yana kokarin sanya glasses dinshi a ido yace "Laraba enough! Lieutenant come with me please, officer give him the list" bama Sameer list din officer yayi yakarba yataho yawuce ta gabansu batare dayama kallesu ba yay upstairs, bude office din chairman yayi ya shiga, zama yayi akan kujeran da chairman ke nunamai yabashi hannu gaisawa sukayi, cikin harshen hausa Chairman yace "welldone Sameer am proud of you wlh, kasan mesa nakira ka, acikin yaran nan akwai mutum daya da I really don't know what to do about, am a leader you know Sameer and I don't want to be bias during the course of my work, bansan mezanyi ba I had to call you, kanada hankali sosai duk girman mutum sometimes idan zakadau hukunci dolene ka nemi shawara koda wajen dan cikin kane" yadanyi shiru kafin yamikama Sameer din hannu yace "kawo list dinan kaga" mikamai list din Sameer yayi ya karba yace "sunan yaran nan ne dakuka kamo, wanan yarinyar da officer ke bugunta yanzun nan she is the daughter of Chief judge of the federal High Court na nan Abuja, Rahima Sambo Rikadawa, da farko danaga sunan I was like maybe is just a random person dat happens tanada surname na judge din garin nan, saida na kira wani friend dina lawyer danasan yasan Chief Judge sosai and asked him about yaran Chief judge nawa yacemin four and call the names for me which wanan yarinyar dakake gani happens to be his last born, kana hango abinda nake hangowa Lieutenant?" ya tambayi Sameer daya natsu yana kallonshi gyadamai kai Sameer yace "a Chief Judge is someone that is very vulnerable, mutum ne da kusan idanun kowa na kanshi, aikinshi aikine dakesa kai makiya dayawa sanan kai masoya dayawa abin kanzama kaman 50-50, ko 60-80, cikin makiyan harda nakusa dashi wanda kawai neman abinda za'ai amfani dashine atunkudeshi wani ya gaje kujeran shi na Chief judge din babban birnin tarayya, inhar press zasu samu koda gutsuren information ne kan yarshi na shaye shayen illicit drugs abin can cost him alot to the extend da zai iya tarnishing image nashi and his reputation a society mu, bayan haka, yanadaga cikin mutane masu yankewa drug dealers hukunci yau ga yarinyar shi na drugs" dan ajiyan zuciya Sameer ya sauke ya gyara zama tareda ijiye hannayenshi akan table yace "me kakeso daga gareni Chairman?" ajiyan zuciya Chairman ya sauke yace "bakaga nasa akai yarinyar dinning ba, all the staff anan babu wanda yasan abinda nasani, I want to isolate the girl from the rest of the gang sainai contacting mahaifinta yazo dakanshi ya dauke ta kaita rehab yarage nashi, mun bashi itane yanzu dan kare shi dakuma aikinshi daga bakin Al umma amma in muka kara kama yarshi akaro nabiyu ni I will release d information nabar press suzo su gudanar musu da interview kafin atattarasu akaisu government rehabilitation centre koya kagani?" gyadamai kai Sameer yayi yace "sauran yaran fa?" cikin dan damuwa kadan Chairman yace "what do you think Lieutenant?" dan shiru yayi kaman mai tunani yace "they have to go for rehabilitation, rayuwan su zai taimaka, Nigeria muna so muyi eradicating shaye shaye idan aka samu yara kusan talatin suka dena shaye shaye cigaba da Nigeria ne sosai, yayinda idan ka barsu baka kaisu ba ka kaddara mutane talatin dinan zasuje su koyama wasu mutane talatin din shaye shayen ne, kaga rate of shaye shaye yasake increasing kenan" gyadamai kai Chairman yayi yana yaba fikran Sameer yace "hakane, za'a kaisu, bari na nemi mahaifin nata abokina yabani contact dinshi dazan iya samun shi" gyadamai kai Sameer yayi, dialing number

Chapter 8 of 15