Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da zani na atampa, bude kofar dakin Rahima tayi ahankali ganin tana bacci har lokacin yasa tasake yi murmushi tawuce dakinsu Siddiqa, bude kofar dakin tayi duk suna kwance suna bacci, maida kofan tayi tarufe ta karasa ta bubbuga musu gado. "Siddiqa, Luba, Zeena, oya kutashi kutashi la'asar tayi aje ayi salla azo ai abinci" tashi ahankali Lubabatu tayi tana turo baki zama Mummy tayi gefenta tace "yan matan mummy ta" da sauri ta kalli Mummy tadan harari Mummy irin hararan nan na ban yardaba tace "yan matan ki dai na dakin ki tana bacci yar gaban goshinki, mu ai bakison mu, Rahima dabake kika haifeta ba kikeso ita kadai" da sauri Siddiqa data karasa tashi zaune tace "Luba banhanaki irin wayan nan magangan....." hannu Mummy ta dagama Siddiqa tace "leave her, gaskiya tafadi, but am sorry kinji y'ata kema kinsan ina mugun sonku ko, me kikeso yanzu?" dan murmushi tayi tace "Mummy wanan dubai gowns dinan dakikasa kawarki tasayoma Auta" da sauri Mummy tace "angama zan sa akawo muku guda biyar biyar each, oya yanzu atashi ayi salla kuzo mu shiga kitchen yan albarka" da sauri Siddiqa tace "Auta, bari naje nakirata Abba yace mudingayi tare" hararanta Mummy tayi tace "agulma'u bil kisira, Ke kinmafi mai kisiri mai dummataini ce, to bazakije ba, wuce kije kiyi alwala kuyi salla mu shiga kitchen inta tashi zatai nata" wani kallo Siddiqa tama Mummy najin haushi saikuma ta tashi ya wuce bayi abinta, Mummy tana zaune tareda su duk sukai salla sanan ta tattara su sukai kitchen saida tasa suka fara shirye shiryen hada sanwa sanan tafito tai dakinta, wayarta dake kan mirror ta dauka tai dialing number Abba, ringing daya ya daga. "Wifey" "na'am Alhaji, nace ba" anatse Abba yace "uhum ina jinki" kashe murya tayi tace "Abban su nace anjima da daddare Lieutenant zaizo wajen Rahima ne? Naga dazu yazo dama inaso nasani ne danna sashi a abinci zamu fara girki ne" daga tachan bangaren Abba yace "yeah I think tarema zamu dawo, dazu dayazo yana shigowa aka kirashi, shida Marshal ogansu sukaje supervising posts, so yacemin zaizo da night, kisada shi, tare zamu shigo, nima I thought bazan dadeba, anyway lemme just tell you abinda nazo yi a office kinsan menene" da sauri Mummy ta gyara zama tace "no Alhaji menene, bani insha? Wani contract kasamu ko mene?" dan dariya Abba yayi yace "No ba contract bane, dama nayi ordering wata mota ce" da sauri Mummy tace "mota Alhaji? Mezakai da mota gala da uban motoci" ahankali yace "ki rage murya kar yaranmu suji" da sauri MUMY ta kwantar da murya tace "na rage" Abba yace "actually Rahima nama ordering mota, so ya iso shine aka kira naje nai signing ne, luxus ce motar yar babba hakanan but ba chanchan ba anjima zamu dawo da ita" yay maganan sounding so excited, wani irin faduwa gaban Mummy ya shigayi ranta yay bala'in baci wani baki ciki yataso mata, jin tayi shiru yasa Abba yace "ya kika gani? Naga tai bala'in kokari duk tabi tadawo wani iri, ta lalace ta rame, ta kode kinga yau kwananta 5 batasha komiba, so I thought of lemme buy car for her hakan zai sata murna, murnan kuma zai mantar da ita komi yasata dawo normal, su Siddiqa kuma nasu motan in sha Allah kowaccen su duk ranan daurin aurenta ranan da za'a kaisu gidan miji da sabuwa motarsu za'a kaisu, kinsan yanzu abun zaiyi wani irine natara yara duk nabasu motocin kansu tun kafin suyi aure kaman batasu ne, ko Rahima ma wanan ne dalilin bata mota bawai dan shagaltarwa ko sangartarwa ba, akwai many ways dayakesa yaron barin hallaya marasa kyau, inhar kasamu yadena koda na kwana uku ne tokabashi tukwuicin dazaisa yaron yaji zaima iya barin dabi'un marasa kyau har abada kin gane wife" danne bakincikin da Mummy takeji tayi tai murmushin yake tace "wow Abban mu mungode, yau zakasa baby girl dina farin ciki, u have no idea yanda kasani farin ciki, thank you Alhaji, Allah yamaka albarka" har cikin zuciyanshi Abba yaji wani irin sanyi yanda Mummy tai farin cikin abinda yayi batare data batarai kota nuna wani irin haushin akan yasaima Rahima mota baisaima yaranshi ba, ahankali yakira sunanta. "Maryam dina" murya chan kasa tana danne duka bakin cikin datakeji tace "na'am Alhaji na" murya chan kasa Abba yace "I love you so much Maryam banjin akwai mace mai irin hallaiyan ki aduniyan nan ba, ni karan kaina nasan nayi dacen mata, nagode miki and I know I always promise you this, yanzu ma still zan kara promising naki, listen Maryam kome kikeso aduniyan nan, komeye shi, gida, kudi, fili ke koma menene inhar baifi karfina ba wlh saina miki shi you deserve this and even more, Ke mace ta gari ce" dan dariya tayi tace "haba Alhaji ni kadenamin godiya please, kake cewa komenakeso to mema bakamin ba, Alhaji kabude min manya manyan super market guda hudu anan Abuja, ka zuba ma'aikata kullum kudi shiga account dina yake, ka budemin spa, banda all this duk wata ana maka salary zaka bani kudi nima kyauta mekuma nake nema inhar am not greedy, indai nice I will always support you mijina, kaga kar yaran nan suyi shirme a kitchen nabarsu su kadai, bari naje saika dawo" katse wayan tayi da sauri ta jefar da wayan man gado ta kife kanta zuciyata na wani irin kuna kaman an watsa garwashi, tadade ranta bai baci hakaba, mikewa tayi tsaye tace "aiko I promise you yau zaku iso gidan nan ku tatrar da bakin cikin da baku taba tunani ba, wlh sainasa murnan ka takoma ciki" tai maganan tana bude kofa tafita, sake bude kofar dakin Rahima tayi ganin har lokacin bacci take yasa ta kalli agogon bangon dakin biyar saura ahankali tace "by 6" tawuce tai falo tsabagen bakin ciki kasa shiga kitchen din tayi tawani kwanta akan dogon kujera tana kallon agogon bango tana jiran 6 yayi. Wuraren 5:50 Rahima tabude idanunta ahankali dasuka sanyi ja sabida baccin datashi, tashi ahankali tayi ta zauna tana yatsine fuska kaman zatai kuka tace "uhmm" daidai Mummy tazo wajen zata bude kofan ta shiga jin muryan ta yasa tai wani irin murmushi tareda taune lips tajuya ahankali sadaf sadaf takoma falo ta zauna. Hannu tasa ahankali ta zare hijabin jikinta tanaji ko ina na jikinta namata ciwo, tashi tayi ahankali daka kan dadduman tadauke dadduman da hijabin nata ta wurgasu kan madubi tawuce ta shiga bayi fitsari tayi tai tsarki ta wanke hannunta sanan tasa toothpaste a toothbrush dinta ta shiga wanke bakinta dan ta tsani ta tashi daga bacci taji bakinta namata wani iri, wanke bakin tayi tsaf sanan ta debi ruwa ta wanke fuskanta taja towel ta share ruwan fuskan nata sanan tabude kofa ahankali tafito feeling headache kanta yawani saramata, hannu ta daura kan goshin nata tareda lumshe ido tana tsaye daga bakin bayin saida kan yadan lafa sanan tabude idanunta ahankali ta daga kafafun ta zata fara tafiya idanunta suka sauka akan kwalaban codeine guda uku dake kan side drawer gadonta an ajiyesu gasunan acike tap bawai empty bottles ba, ga karan weed guda uku gakuma light, wani irin racing heart dinta yayi she can't believe wat she is seeing, tsabagen mamaki da rudewa kulle idanunta tayi sanan tabude da sauri tasake kallon saman side drawer taga still dai suna wurin dawani irin sauri takarasa wajen wani irin zama tayi dirzhan akasa tana kallonsu kaman mai daukan karatu agaban Malam tana bude baki har wani yawu take hadiyewa kaman wacce aka gabatar mata da farfesun kan sa, hannunta har rawa yake tamika tadau kwalba daya na codeine din tarike a hannu jikinta har bari yaje bar bar kaman irin yaron daya ga abinci for the first time after like a whole year of starvation, kanta gabaki daya ya kwance kaman wacce akama baki ko kadan bata tunani all abinda zuciyanta idanuwanta gangan jikinta da ruhinta ke gani dakuma tunani shine wayannan kayan mayen, dawani irin sauri ta shiga bude codeine din wani irin cillar da marfin tayi ta daga sai bakinta tana sha tana nishi tana lumshe ido kaman yaron karami da akabama bobon dayagama kuka abashi, saida ta shanye shi tass sanan tawani irin cillar da bottle din tadau na biyun da gudu tana sauke ajiyan zuciya tabude ta yarda marfin takafa abaki saida ta kwalkwale tass sanan ta wurgar da bottle din vamatare da tasan inda take wurgawaba tadau 3rd bottle takafa abaki, harwani lumshe ido take tana sauke ajiyan zuciya gwanin ban tausayi tsabagen yanda tai kewansu fess ta shanye na ukun sanan ta cillar tawani irin yin doguwar gyatsa tana murmushi tai maza ta kwaso duka karan wiwikan tana kallonsu, kallon dakin nata tayi ganin babu komi na sha yasa tasake kallon side drawer, ganin lighter akai yasa tai shiru to kodai ta gwada smoking nashi ne ai taga Chris yay smoking nashi ranan yana shan codeine yana zukanshi wai mugun dadi kakeji, da sauri tamika hannu tadau lighter ya kyasta na wiwi wuta yakama ta yarda lighter takai wiwi baki ta zuko ahankali sanan ta fuzar tana lumshe ido tawani mike kafafu akasa tanajin dadin da bata tabajin irinshi ba. Fitowa su Siddiqa sukayi daga kitchen rike da kulolin abincin dasuka dafa suka shiga jerawa kan dining, wani irin strange wari Siddiqa taji daya gauraye da kamshin abincin daya cika falon hakan yasa Siddiqa ta kalli Zeenatu dake kara rufe kulan abincin da kyau tace "Zeena bakiji wari ba?" da sauri Zeena ta dago daga abinda take tace "wari Ya Siddiqa? A'a ni banji wani wariba" da sauri Luba tawani yatsine hanci tana huroshi tace "huuuu nima naji warin wlh, kaman warin taba" Mummy dake kan kujera tana kallo tai kaman bataji suba tace "me haka? Astagafurullah lafiyan ki kuwa Luba kike kira mana sunan taba agida? Baku kukagama girki ba yanzu? Halama kun kona tukunya ne, ko wani abun barinma ke Luban nan mai shegen cinne cinne awuta, Common kuzo nan kusa mana zee World mu kalla Mahek" da sauri suka taho falon suka zazzauna dudda warin sai cigaba yake da damunsu amma Mummy tahansu magana sai labarin Mahek din take basu. Yarda kara dayan wiwi data gamasha tayi, dukta bata carpet din dakin nata da tokan wiwi, lighter tadauka ta kunna na biyu ta shiga sha idanunta na mugun juyawa, jikinta nawani irin saki, tanajin ta a sama, sama kaman tana tafiya akan ruwa kifaye na lasan diddigen ta, silin din dakin take kallo tana zukan wiwi sai taga Maman ta sojoji sun sata kneel down, jikinta sai rawa yake wai tana tsoron bindiga tafashe da kuka, kyalkyacewa da dariya tayi tana zukan wiwi cikin wani slow murya tace "sooooja ci ubanta muuuguuuwaaa ceeeeee, batada imani kusada tsinto duwatsun kwata" takara kyalkyacewa da dariya ta mugun buguwa to the extend da bamata duniyan nan she is high.... An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 15 of 15