Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ita Siyama ɗin tare da shi, to a ranar tayi maganganu marasa daɗi akan sa, dan tayi alkawarin ɓatar da shi idan bai daina shiga sabgarta ba..."Ɓatarwa fa kace ɗan nan? Ɗan mutum din guda za'a ɓatar kamar ɗan kaza, kuma ita Siyama ɗin ce da kanta tace zata ɓatar da Ibrahim? Hajja ta katse Haladu cikin tsoro da jin wai zata ɓatar da Ibrahim. Haladu ya amsa da "Ai Hajja wannan ƙaramin aiki ne idan mutum yana da kuɗi, amma kuma ba wannan ne ya kawo ni ba. Hajja dai jikinta yayi sanyi tana kallon sa. Kafin yayi magana sai ga Nana ta shigo gidan da sallama. Suka amsa suna kallon fuskar nan tata a murtuƙe kamar kuturon da a kaiwa gorin hannu. Kallonta Hajja tayi bata bukatar ƙarin bayani domin babu komai a hannunta. Ganin Nana ɗin ta shige ɗaki yasa ta sauke ajiyar zuciya ta dawo da kallonta ga Haladu shima da yabi Nana ɗin da kallo ganin ko gaishesa bata yi. Ya ce "Hajja Siyama da kanta tace "Yaje ya rubuto duk wani abu da ya taɓa kashe mata zata ninninka masa ta biya sa. Kuma Hajja wallahi ko nawa yace zata ba sa, shine fa tun lokacin nake masa magana amma shi yaƙi ma ya saurareni, nace masa ko jari ai sai ya samu amma yaƙi. Shine nace bari nazo na sanar miki domin naga ai hakkinsa ne ba roka yayi ba. Hajja ta ce "To ai Ibrahim ɗin ne shifa yanzu damuwarsa yarinyar, kuma ai kaine zaka taimaka ka shawo kansa domin zaifi jin maganar ka. Ko kuma kawai kai ka zauna ka rubutu komai sai kuje da shi kasa ya bata. Haladu yayi shiru sai chan ya ce "To shi kenan Hajja in sha Allah zan masa hakan. Ya tashi zai fita sai kuma ya sa hannu a aljihu ya ɗauko dubu biyu ƴan ɗari biyar guda huɗu ya ajiye wa Hajja ba tare da yace komai ba. Hajja ta bisa da addu'a domin dama ya saba yi mata kyauta har fiye da haka ma, kasancewar shi Haladu shago garesa kuma babu laifi ana ciniki sosai. Yana fita Nana ta fito daga ɗakin. Kafin tayi magana Hajja ta ce "Ga kuɗi nan yayanki ya bani ɗauka kije kisan abun da zaki samo mana, kiyi sauri kuma tunda ga wuta sun kawo. Haka ta kwashi kuɗin ta fita Hajja ta bita da kallo. ****** *ADAWIYA* Wannan ba shine karon ta na farko da tazo ƙasar Ingila ba, amma wannan shine karo na farko da tazo a sa'a. Sosai komai yake tafiya mata kaman yadda take so, babban abun da yafi burgeta ma shine ganin manya-manyan salebiritis da kuma manyan Model's da bata taɓa tunanin zata haɗu dasu ba ta haɗu da su yau. Bata ƙara cika da mamaki ba sai da wani kamfani dage Ingila suka zo har Hotel ɗin da ta sauƙa suka kawo mata tayin yarjewa ta zama Models ɗinsu ta shekara ɗaya. Bata amince ba tace subata lokaci zata yi shawarwari. Bayan fitar su, ta kira Manager dinta yazo har ɗakin ya sameta, kasancewar tare suke tafiye-tafiye ko ina. Ta sanar da shi komai akan sun nemi da ta zauna tayi aiki dasu. Jin sunan Kamfanin yasa Manajan saurin kallon Adawiya ya ce "Madam Baki San wani kamfani bane? Ta ce "No ban san su ba, amma ina jin sunan su But ban taɓa bin aikin su ba, amma ina kallon fina-finansu ai. Manajan ya ce "Suna yin Really Video's ne na sex babu inda video ɗin su baya zagawa, kuma basa yi da kowa sai Model's, kuma kema ba wani aiki zaki musu ba sai shi wannan aikin. Adawiya ta dafe ƙirji tace kenan rom service and romantics Seex videos kenan fa? Ya ɗaga mata kai. Take ta sallamesa yana fita ta kira Badawiya Badau. Tana ɗagawa ta kwashe mata komai ta faɗa mata. Ai kuwa da sauri Badau ta ce "Ke ƴar sa'a da gaske? "Adawiya ta ce "Ban gane ƴar sa'a ba kin san wani kamfani nake magana ne? Badau ta ce "Yes ba VIP London ba ne? Cike da mamaki Adawiya ta ce "Wai dama sune? Badau tayi dariya ta ce "Shegiya ai dama nasan baki ma san suwaye suka zo gurin ki bane shi yasa kika tsaya wasa. Adawiya ta ce "Nashiga aljanna daɗi zai kashe Adawiya, VIP London ne wai dan Allah? Badau tace "Ke dalla tsaya, wai yaya ma akayi har suka ganki? Ta ce "Yau minyi aiki ne na taron salebiritis mawaƙa Model's ƴan Film da ƴan ƙwallo, ke duk dai wasu salebiritis, kuma nima na shiga inaga anan suka ganni. Badau tace "To zuwa gobe ki tabbatar kin kirasu kin yarda zakuyi aiki tare. Adawiya da har yanzu mamaki take ta ce "Yanzu zan ƙara duba shafinsu na gani. Badau tace "To sai kuma kiyi, mutanen da kullum sai na kallesu, ke zan iya lissafa miki ƴan team ɗin nasu gaba ɗaya musamman ma mazan, ke suna da wasu irin maza masu ƙirar jayent, Maza iya maza ga kyau ga lafiya ga iya aiki, nasha yin mafarkin su bayan na gama kallonsu, kema yanzu haka zamu fara kallonki a gurin fa. Adawiya tayi dariya tace "Wallahi har na fara tsoron wadannan mazan mazu ƙirar dakunan yaƙi, sai nake ganin kamar ban kai na shiga Team ɗin ba. Badau ta ce "Ai kuwa kece kika isa ki shiga VIP wallahi, to sauran matan finki sukayi ne, wai ke kamar ba ke ba, Please karki ba dani. Sai a lokacin ta ce "Yanzu to idan na yarda yaya batun kamfanin Magazin? Da sauri tace "Ke amma baki da hankali, ana maganar VIP kina zancen wasu talakawa, to bari kiji alawus ɗin VIP kaɗai ya kai fement ɗin Magazin na wata biyar wallahi. Ke ai idan kika shiga wannan team ɗin kinyi ban kwana da taulauci daga ke har zuri'arki. Adawiya dai ta saki baki tana mamakin a ina duk Badau tasan duk waɗannan. Haka suka yi sallama akan idan ta yarda da VIP ɗin zata juya conturak ɗin ta ya koma kan Badau na Magazing da take yi yanzu. Washegari kuwa shine zasu je su ƙarasa aikin da sukayi. Hakan yasa ta shirya da wuri cikin shigar wasu arnan kaya wanda kallo ɗaya zakaiwa kayan kasan dole sai dai Model's irin su. Doguwar riga ce mai adon duwatsu daga sama har ƙasa, kasancewar ita ɗin siririya ce yasa kayan suka fito da dirin ta, ga kuma gefe da gefen rigar a yage har cinyarta. Ta saka wani taƙami da tsininsa zai kai tsayin tsinken tsire, amma tsabar sabo da iya tafiya da shi ko alamar faɗuwa bata yi, hannun ta na riƙe da wata ƙaramar jaka kalar kayan wacce bata fi a saka waya kawai a ciki ba. Tana ƙarasowa aka buɗe mata motar mai buɗandan sama. Ta shiga ta zauna sannan aka ƙara gaba da ita. Suna tafiya Manager ɗinta yana mamakin yadda da akayi zata yi aiki da VIP domin tun da safe ta sanar da shi zasu je susa hannu, domin daran jiya ta gama shiga komai ta gani. Sai da ta shiga Magazin ta karasa aikin ta na ranar wanda hoto kawai ta ɗauka na wasu sabbin fantis da bra da aka kawo Magazin kuma ita aka zaɓa a matsayin wacce zata fara sakawa ayi tallan kayan. Sosai kayan suka mata kyau haka ta shiga saka su ɗaya bayan ɗaya duk wani color dake gurin sai da ta saka ana ɗau karta hoto dasu, duk wanda tasa zata tsaya ne tayi wani irin tsayiwa ta karkace gefe ko ta ɗan juya cinyarta ta baya, style dai kala da ban da ban har ta gama kafin ta mayar da kayan ta da tazo dasu, sannan ta ɗiɓi kayan da tayi talansu guda biyar domin sun mata kyau. Tazo zata fita wani daga cikin masu ɗaukar hoton ya sanar da ita Manaja na nemanta a ofishin sa. Haka ta tafi tana kwarkwasa kaman yadda ta saba. Tana shiga ta tarar da wasu matan a ciki suma a zaune suma duk Model's ɗin ne su Uku. Tana shiga tai musu Hai suka amsa kasancewar sun san juna. Bayan sun zaune manajan mai suna Alesx ya ce "Ku huɗu muka zaɓa zamu yi aiki daku karshen shekara, kafin lokacin zamu baku hutu na tsawon wata ɗaya, amma a cikin wannan watan babu sex koda kuwa da miji ne (Ma'ana ko kina da aure ne), ko da kuwa da Mace ƴar uwarki ce. Lokaci ɗaya matan suka kalli juna jin wani sabon iskanci. Duk da kuwa sun san haka aikin yake, amma mai ya kawo na cewa koda kuwa da Mace ƴar uwarki ne, ya ma raina musu wayo. Adawiya tace "Sabo da me? Ya ce "Saboda aikin da za'ayi yana buƙatar natsuwa da tabbatar da lafiyar Model's ɗin mu. Muddin wani abun ya shiga tsakaninsu da Maza to za'a gane kuma matsala ne, abun tsoron ma shine shigar ciki shine babbar matsalar, shine ma yasa ake kiyayewa. Adawiya da take jin ita da ta riga da ta gama aiki dasu muddin VIP London suka amshi komai nata, ta ce "Zanyi tunani akai" Alesx ya kalleta da mamaki ya ce "Ban gane zaki yi tunani ba kamar wacce aka bata shawara? Yaci gaba da faɗin Wannan dokar aiki ne ba wai shawara ake nema daga gareku ba, duk wacce taga bazata iya ba babu dole ta sanar tun da wuri mu nemo wata. Yayi maganar da ɗan ɓacin rai a muryarsa, kasancewar wannan dama ce da duk wata Model's ke fatan samu shiga a cikin wannan aikin na karshen shekara. Kafin kowa yayi magana wata daga cikin matan kai da gani kasan baturiya ce ƴar ƙasa ta ce "Yes mun yarda zamu iya, idan lokacin yayi sai a sanar mana sai mu kiyaye. Adawiya kuwa babu wani tunani tace bazata iya ba. She kansa Alesx ta bashi mamaki, amma bai ce mata komai ba har ta bar gurin suka bita da kallo. Wata daga cikin Model's ɗin ta ce Afirkan Model's. ta faɗa tana jan tsaki, sauran kuma suka kwashe da dariya...📝 Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza write [7/16, 3:54 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ _FCWA_ *My WhatsApp channel* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *Page 1️⃣0️⃣* Duk da Alesx yaji zafin rashin shigar Adawiya cikin tawagar aikin nasu amma haka ya haƙura suka fara neman cikon ta huɗun ƴar Afrika wacce zata wakilceta. Dama shi yarinyar na basa mamaki tun ba yanzu ba, tana yin wasu abubuwa kamar bata tsoro, amma a ransa ya yanke shawarar wannan karan zai koya mata hankali, sai tayi nadamar ɓata musu lokaci da tayi. Bayan ta fita ne ya sallami sauran ƴan matan shima ya tashi. Daga nan VIP ta nufa ranta fess tana jin ai ita dama ce mai kyau tazo mata kuma tabbas zata dama harda sikari tasha kayanta. Lokacin da taje get ɗin shiga VIP kuwa duk da cewar an ganta Model domin kallo ɗaya take buƙata duba da irin shigarta zaka gane ita ɗin Model ce. Amma hakan bai sa an barta ta shiga ba sai da ta nuna shaidar da aka bata lokacin da suka zo gurin nata. Lokacin da ta ƙarasa ciki sai aka tsayar da escort ɗinta (Mai tsaron ta) aka nuna musu hanya ita da manager dinta suka shiga ciki, shi kuma ya tsaya waje. ****** *SIYAMA* Yau kwana biyu da zuwan su Oga Fita gidan su, kuma har yanzu babu wani cigaba daga gurin Umma na amincewarta, hakan yasa tun jiya Siyama ta je gidan Kawu Inuwa da kuma Baba Hassan mahaifin Binta. Sosai tai musu ruwan ihisani da yasa kowa a cikin su sai da ya rikice. Shi Kawu Inuwa farko da taje kamar zai dake ta, domin haushi ta basa, amma lokacin da ta faɗa masa irin samun da ake yi, sai ya fara sakkowa. Bai sakƙo daga kan bishiyar kwakwan bama sai da yaga ta sauke masa rafar yan dubu-dubu guda biyar wato dubu ɗari biyar lokaci ɗaya ya duro daka saman, ya rikice har bai san lokacin da yake ce mata "To ai dama wannan aikin da moda shi ya dace da ke, yarinya fara kyakkyawar gaske, ai itama Umman taku wasa take, to wa zai ƙi nasa da abun arziki. Bari na shigar da su sai mu tafi gidan yanzu, to ai wannan sana'a ce ta rufin asiri, shekara ta nawa ban taɓa riƙe irin wannan kuɗin ba, amma ke daga rana ɗaya kawai kin riƙe, dama ana cewa wani lokaci idan kaga kana addu'a akan kayi arziki to kuma baka yi ba, to malamai sun ce tana komawa kan ƴaƴa ne, to babu shakka nawa kanki ya faɗa wallahi. Sosai ya shiga zaro zance ita dai Siyama tana sunkuye a ƙasa tana mamakin mai ya hana ta tun farko bata fara aiki da kuɗin ba, ai da tuni ba wannan maganar ake ba. Daga nan gidan Baba Hassan ɗan biyun mahaifinsu taje. Lokacin da ta isa gidan kasancewar shi yana da ɗan hali domin harda mota garesa dukda cewar tsohuwa ce amma dai yana da ita. Shima ganin ta a cikin wannan Motar sai da ya shiga boɗe baki. Bayan ta gama zaiyana masa komai ne ya shiga girgiza kai alamar tunani. Ganin kamar bai yarda bane yasa kafin yace komai ta sanar da shi irin alkarin dake cikin aikin nata, ta fara faɗa masa irin kuɗaɗen da zata samu, tana gamawa shima ta zaro guda shida ta ajiye masa, ta sanar da shi abun da take so yayi mata. Baba Hassan ya kalleta ya kalli kuɗin ya ce "Yanzu iya wannan abun da kika yi ne har kika samu wannan kuɗaɗen?" Siyama ta ce "Eh ai Baba wannan ma iya kyautar da na samu a gurin ne ba ma wanda aka bani na gasar bane". Jin haka sai yace "to shi kenan zuwa gobe zan je na sameta". Sai da ta shiga suka gaisa da Mommy itama ta bata rafa ɗaya kafin ta bar gidan. Tana fita Mommy ta dau waya ta kira Binta. Taso shiga gidan su Ibrahim lokacin da tazo wucewa, domin so take ta jawa tsohuwar sa kunne ganin shi baya jin magana. Amma ta bari har sai ta samu Umma ta yarda. Shi kuwa Nasiru babu wata-wata kuɗaɗe ya amsa daga gurin ta ya fara hutawa abun sa, har Allah-Allah yake ya warke ya ƙwace wannan motar ta zama tasa. Zaune suke a sashen Umma Kawu Inuwa da Baba Hassan sai wani abokin Kawu Inuwa da ya gayyato acewarsa wai Malami ne, zaiwa Umma bayani yadda zata fahimta. Sai yaya Bala da shima har yanzu yaƙi amincewa da wannan aikin a ransa. Bayan an gama gaisawa ne Kawu Inuwa ya fara da faɗin "Uwar yara gurinki muka zo akan yarinyar mu, izuwa yanzu dai kowa yaji abubuwan da suka faru da ita, to mun zauna munyi shawari nida babanta gashi. Ya faɗa yana nuna Baba Hassan. Yaci gaba da faɗin "To shine yasa nace a matsayin ki ta uwa shine muka ga ya dace musanar dake karmuyi gaban kanmu dukda cewar mun isa da yarinya, koba haka bane Malam Hassan? Ya karasa yana tambayar Baba Hassan da gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi ganin yanayin Umma da Yaya Bala. Baba Hassan ya ce "To dama ba komai bane sai kawai abar yarinyar nan tayi sana'ar ta, tunda dai ba zai hanata karatu ba, kuma wannan sana'ar sana'a ce ba mai muni ba. Umma ta ɗaga kai ta kallesa sai ta kawar da kai ganin sun haɗa ido. Ai kuwa shi kaɗai ya duburburce ya kasa ci gaba da jawabin. Sai Kawu Inuwa ya ɗora da "Yanzu muna so a matsayin ki ta uwa maba da mama, mai son cigaban ƴaƴanta kiyi hakuri kibi Siyama da addu'a akan aikin ta, kinga kema sai ku huta, nasan har gida sai ta sauya muku, dama gata yarinya ce mai kyauta da sanin yakamata, sam abun hannunta baya rufe mata ido. Umma ta ce "Yanzu tsakanin ku da Allah idan Siyama ƴarku ce ta cikinku zaku yarda tayi wannan sana'ar ta ƴan isa ta tallan jiki, ai duk kuna da yara mai yasa ba zaku tura su suma suje su samo abun arzikin ba kamar yadda kuka ce, to ni dai ban yarda Siyama ta ƙara aiki da wadannan mutanen ba, wanda tayi a baya ma kuskure ne kuma yarinta ne, amma in sha Allah ba zata ƙara ba. Ku kuma wallahi kun bani mamaki akan abun duniya zaku salwantar min da rayuwar yarinya har kuna iya kallon idona kuce wai na bar ta tayi talan tsaraici, A'uzubillahi-mina-shaiɗanunrajin, tuf da wannan tunanin naku. Kawu Inuwa ya ce "Yanzu mune shai ɗanunn kenan Aisha? Kuma mune kike wa gorin yarinya, shi kenan babu komai ba laifinki bane, ai mu ne marasa mutuncin da muka tako har cikin gidan ki, dole ki zagemu san ranki. Umma ta ce "Ni ban zageku ba, kuma babu yadda za'ayi nayi muku gurin aihuwa domin duk kun haifa. kuma Siyama ƴar kuce ban isa na shiga tsakaninku ba. Kawai dai abun da kuke nufi ne ba zan taɓa yarda ba."To me kike nufi da a'uziya da kika jawo mana yanzu na neman tsari da sheɗanu, ko ake ce miki bamu je islamiyya bane, to bari kiji babu wata addu'a da zaki yi wacce ban san ina ta dosa ba, dan haka karki ƙara mana addu'ar shaɗanu tun girma da arziki domin mu ba su bane, ya daga abun kirki a fara danganaka da jinsin tsinannu. Sosai wannan addu'ar ta ɓatawa Kawu Inuwa rai domin ji yake kamar shi ta kira da shaɗanin. Umma ta ce "Kayi hakuri ni ba nufi na kenan ba. Ta faɗa tana jin nauyin sa da take ji yana raguwa. Sosai take kunyarsu su duka su biyun amma wannan abun yasa take jin nauyin nasu na raguwa a ranta, dama shi Kawu Inuwa ya iya daukar abu da zafi kamar dai ita, shi dai Baba Hassan bai ma cika tsoma baki a lamarin gidan ba sai dole. Kawu Inuwa ya kalli Yaya Bala da yayi shiru yana ta tunani ya ce "Yanzu Bala a gabanka ina matsayin ƙanin ubanka kana ji uwarka na kirana da shaɗani amma kayi shiru ko? Kai Bala kana so ka gama da duniya lafiya kuwa. Sosai yaya Bala ya danne abun dake taso masa ya shiga basa hakuri har dai akayi sa'a ya tsaya da mitar kamar mace. Mutumin da suka zo da shi ne ya fara magana cikin natsuwa da dole kai mai sauraron sa ka tsaya ka ji abun da yake cewa domin ya iya magana. Ya ce "Duk na fahimce ku, kuma na gane inda zancen naku ya dosa. Yanzu ina so ku ɗan bani dama nace wani abu? Duk suka basa dama ya buɗe baki zai yi magana suka ji anyi sallama. Amsawa sukayi sai ga Hajja ta shigo ɗakin cikin sauri idanunta duk sun yi jaa, sai kuka take. Gata dai tsohuwa amma jikinta bai tsofe sosai ba, amma kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar da tana cikin wahala. Ganin mutane da yawa a palon yasa ta cire taƙalmi ta shiga gaisuwa da sauri-sauri. Kawu Inuwa ne ya fara faɗin "Baiwar Allah lafiya kuwa me kike buƙata gurin wa kika zo da zaki shigowa mutane cikin gida haka kamar sauƙar aradu babu neman izini?. Kallo ɗaya Umma tayi mata ta gane ta, ta ce "Sirikarku ce kakar yaron da yake zuwa gurin ita ƴar taku da kuka zo karewa" Da ƙarfi ya ce "Ita dai wannan ɗin, to wallahi wuce nan, ina dangin wannan matar ina Siyama da take shirin zama tauraruwa sha kallo. Hajja ta ce "Hajiya Aisha Ibrahim ne ba shi da lafiya kamar zai mutu sai sunan Siyama yake kira, dan Allah ki taimakeni Siyama tazo muje ko ganinta yayi dan Allah a taimaka. Da ƙarfi Umma take furta innalillahi tana faɗin "Mutuwa fa kike cewa Hajja? To meye ya sameshi haka? Umma tayi tambayar tana ƙarasowa gurin Hajja. Hajja tayi ƙarfin halin faɗin "Wallahi shida ita Siyama ɗin ce, wai inaga yanzu ta daina sonsa ne, shine ya shiga wani hali, yau kusan kwana biyar kenan mun kasa gane masa, dan Allah ku taimaka ko ganinsa tazo tayi zai samu sauki domin sunanta kawai yake kira. Umma ta kalli Yaya Bala da bai iya cewa komai ba ta ce "Kaji zancen da Nasiru ya gama faɗa jiya ko, dama nasan wannan yarinyar wallahi ba dan Allah take son wannan yaron ba, kawai tana so ta yaudaresa ne, kuma wallhi bata isa ba, muddin nine na haife ta to wallhi sai ta auri wannan yaron ai ita ta kawo mana shi akan shi take so, to dole ne sai ta aure sa. tace "Je ka kira min ita. Dama tana jin duk abun dake faruwa domin tun shigowar su Kawu Inuwa ta laɓe tana sauraron su. Umma ta ce "To ga kakar yaro ga ni uwar yarinya ga kuma iyayenta maza, sabo da haka a tsayar da magana yanzu, ni na yanke shawarar aurar da Siyama idan yaso ta ƙarasa karatun nata a gidan shi yaron, domin na gaji da wannan masifar da take ƙoƙarin tun karomu. Idan yaso ko bayan auran ne mijin nata ya barta sai tayi duk abun da zata yi, amma tana gabana dai ba zan yarda ba, Umma ta ce "Kuyi shaida ni Aisha na bawa Ibrahim auran Siyama ko bana raye. Da sauri Kawu Inuwa ya miƙe tsaye shima cikin masifa ya ce "Wannan wani irin rashin hankali ne haka Aisha? Haka ake aurar da yarinya dama, ko kin taɓa ganin inda mace ta bada aure ne? Cikin masifa da haushin da Siyama ta gama bata domin ta lura kamar kuɗi ta basu domin su zo su shawo kanta ta ce "To yaya zanyi da Siyama, so take sai ta kashe ni kuma in sha Allah bazata iya ba har sai lokaci na yayi, yaro kuma ita ce ta kawo shi ba dole za'ayi mata ba, kuma gata nan ku tambaye ta, har gida ta kawo shi a matsayin shi ne zabin ta. Lokaci ɗaya kowa ya kalli Siyama da ta sunkuyar da kai. Ita dai Hajja sai kuka take burinta kawai Siyama tazo suje tayiwa Ibrahim magana ko zai tashi ya samu ko abinci yaci. Cikin fushi Kawu Inuwa ya ce "Siyama wai da gaske ne kece kika kawo yaron matsayin wanda zaki aura? Kowa ya zuba mata ido, domin jin abun da zata ce. sai da tayi kamar baza ce komai ba sai cen ta ce "A'a ni ban turo kowa ba, kuma ai dama ba soyayyar gaskiya muke yi da shi ba ta wasa ce domin ai shima ya sa..."Bata ƙarasa ba taji sauƙar mari a kumatunta wanda yasa ta tsayar da maganar. Kawu Inuwa yace "Wallahi idan ka ƙara taɓata sai na rama mata babu ruwana da ciwon hannunka, yaya yarinya ba ƙarama ba da wayonta kuna so kuyi mata ƙarya a gaban ta. "Umma cike da mamaki kamar zata yi kuka ta ce "Siyama karya nayi miki kenan ko? Siyama ni kike ƙaryatawa? Siyama dai sai kuka take tana jin tsanar Yaya Bala a ranta na marin da yayi mata domin kuwa ya shige ta da kyau. Yaya Bala yaci gaba da faɗin "Ƙarya kike dan ubanki wallahi kinyi ƙadan Siyama yau she aka haife ki, kizo da yaro kice shi kike so yanzu sabo da wani dalilinki kece karya akai miki, to bari kiji wallahi Ibrahim shine mijin ki sai dai idan gidan nan zaki bari kije ki nemi wasu iyayen amma dai idai mune iyayenki Ibrahim zaki aura, wawiya sokuwa mai baƙin hali kawai. Ita dai Hajja tana tunanin waye zai yarda ya zama sirikar wannan mara kunyar da bata bar iyayenta bama bare na wasu,

Chapter 9 of 11