Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne yayi sosai, fuskarsa yaji danshin lema, koda ya kai hannu ya shafi sai yaji hawaye ne. Cikin mamaki Hajja ta ke faɗin "Kai Ibrahim meneke gani haka, wai dama kana nan ne ko dai yanzu kazo, tun ɗazu muna ta jiran dawowarka ashe ma kana gidan, me ke faru da kaine?" Hajja kenan kaka ce a gurin Ibrahim wacce ta haifi Babansa yanzu haka tare suke zaune shida ƙanwarsa da ita Hajja ɗin kasancewar iyayensa duk sun rasu, yanzu shi da ƙanwarsa Nana da Hajja suke rayuwa a gidan. Ya ce "Hajja Siyama ce" Cike da mamaki ta ce "Me ya sami Siyamar? ina ance matar Yayan nasu ce ta rasu, ko itama wani abu ya sameta ne? Lokaci ɗaya Ibrahim ya fashe da wani irin kuka wanda yasa Hajja kwaɗa wani irin salati haɗi da kiran sunan Nana wacce har barci ya fara ɗaukarta. Da sauri ta fito tana tambayar lafiya, haka suka kama shi har cikin ɗakinsa suka kwantar da shi kafin suka fara tambayarsa abun da ya sami Siyama ɗin, domin kuwa babu wanda bai san shi da Siyama ba, daga gidan su Siyama ɗin har gidan su da kuma mutanen unguwa. Ita kanta Hajja farko bata yarda da cewar Siyama tana son Ibrahim ba, domin babu yadda bata yi ba ganin ta raba su, amma ganin yadda ya dage, itama kuma Siyamar har gida take zuwa ta gaidata yasa ta hakura. Ita kuwa Nana dama basa shiri da Siyama kasancewar tana da girman kai ga raini, ko a hanya suka haɗu sai dai ta wuce ta wuce. Ganin yadda suka shiga damuwa ne yasa Ibrahim daurawa ya miƙe yace Nana ta dafa masa ruwan zafi zai yi wanka. Kasancewar akwai wutan nefa yasa ta miƙe domin jona masa. Babu yadda Hajja bata yi da shi ba amma bai ce mata komai ba hakan yasa ta hakura tana ce masa karya sa damuwar mace a kansa fa, ya rufa musu asiri dan Allah shi kaɗai ga resu. Hajja na fita ya ɗauko wayarsa ya danna kiran number Siyama, amma ya jita a kashe ya ƙara kira nan ma a kashe, take ya sauke ajiyar zuciya yana ɗauke babbar wayar abokinsa da ya nuna masa wannan video ɗin. Kunna wayar yayi yaga ta shiga ki, ya cire kin kasancewar yasan ki ɗin wayar, Yana budewa vedio ɗin ya shiga aki kasancewar dama a kai yake, sosai yake ta bin ta da kallo yana so ya gano tayaya haka ta faru, mai yasa bai taɓa lura da cewar Siyama tayi amfani da shi ne domin cika muradanta ba. Yana cikin haka Nana ta shigo ta sheda masa cewar ta shigar masa da ruwan. ****** *ADAWIYA* Kallon Badawiya tayi ta ce "Ni matsala ta dake kenan wallahi shegen jiji da kai, yanzu dan Allah meye laifin kamfanin Baby and me da zaki ce bazayi aiki da su ba, ai ko domin mu wulakanta wannan yarinyar ai kya karɓa. Badawiya ta ce "Ni kaina sai yanzu nake da na sani, domin na bibiyi aikin naga a kwai tsoka, kuma ba wai aikin Contract za'ayi ba, zaka iya haɗa aikin su da na wani ba kamar na Magazing bane da babu dama kayi aiki da wasu har sai lokacin da ka basu ya cika. Adawiya ta ce "You see ni wallahi lokacin da naji Fita na faɗin wai ke kince bazakiyi aiki da ƙaramin kamfani ba abun ya bani manaki domin Baby and me suna biya sosai kuma suna da costoma a ko'ina. "To yanzu yaya kike so ayi domin gaskiya ina son wannan aiki? Badawiya ta faɗa tana kallon Adawiya da ta cika tayi famm. Ta ce "Ai kin gama zubar da damar ki wallahi, amma bari zan samu Fita idan yaso sai a cire wannan Nusee ɗin dan nasan babu yadda za'ayi da zai sa Shara ta fita. Sai a lokacin Badawiya ta ce "To ko dai musan yadda za'ayi a cire ita Munafukar Siyama ɗin sai kawai a saka ni. Adawiya ta ce "Ta yaya? Tayi dariya ta ce "Olusha" Adawiya ta riƙe baki tana dube-dube ko wani ya jisu. Take suka tafa suna ganin ashe ma ga hanya mai kyau da zasu bi su rusa wannan banzar. ****** *SIYAMA* Duk da irin faɗuwar da gabanta keyi bai hana taji tsoron kar Ibrahim ya shaƙota ta baya ya fara dalla mata mari ba, sosai take tafiya ta ankare da shi, har sai da taga ta shiga cikin palon gidan nasu kafin ta sauke ajiyar zuciya tana jin in sha Allah ta rabu da ƙaya. A fili ta furta "Na tsallake ƙofa ta farko a cikin ƙofofin matsalolin da zan fuskanta. Tana ɗaga kai taci karo da matar kawu Inuwa wato mahaifiya Binta wacce suke kira da Momy. Kallo ɗaya tai mata ta kawar da kai gefe tana ƙoƙarin wucewa domin kuwa basa shiri da matar. Ganin tana ƙoƙarin yin hanyar ɗakinsu ne yasa ta faɗin "Ke Siyama dan ubanki bakya ganina ne da har zaki kama hanya ki wuce ni ko gaisuwa babu? To ke nake jira dama tun ɗazu nake zaune anan an kira number ki bata tafiya, idan har kina son kanki da arziki ki juya mu tafi gidana idan kuwa ba haka ba wallahi sai Ummar ku ta kusan hallaka ki, gata cen babu yadda ba'ayi da ita ba amma taƙi hakura, shi kan sa Bala da baida lafiya bata kyale sa ba, to sabo da haka ki juya yanzu mu tafi. Momy ta faɗa tana ƙarasowa gurin da Siyama take. Siyama da gabanta ya fara dukan goma sha tara-tara jin cewar yanzu kowa na gidan su yaji kuma ya gani kenan. Duk da cewa tana tsoron Umma sosai amma bata jin zata bar gidan nan ba tare da ta nemi amincewar ta akan fara aikin Model ba, ko da kuwa tsriranta zata yi ta cinye to wallahi sai ta tsaya ta ƙwaci yancin kanta. Momy ta ce "Wuce mutafi" Siyama ta ce "Babu inda zan je, yau ko soyani Umma zata yi sai dai tayi, aikin gama ne ya riga ya gama, kawai ki barni" Cikin tsawa da masifa Momy ta ce "Dan ubanki kin san halin da kika jefa ahalinki kuwa? Ina so na tafi dake domin zuciyarta tayi sanyi karta aikata miki abun da zai dameki keda ita amma kina cewa babu inda zaki, Siyama mai kike so ki zama ne, kije kina baiyana kanki a duniya akan kuɗi, to wallahi ina baki shawara akan karki yarda ki shiga cikin gidan nan har ki haɗu da Umma na faɗa miki. Momy na faɗa ta koma ciki ta bar Siyama tsaye idanunta na ta kallon mashiga sashen Umma ɗin...📝 Yanzu aka fara shiga labari, kudai kuci gaba da nuna goyon baya masoya. Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza writer ✍️ [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ _FCWS_ *My WhatsApp channel* https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *PAGE 6️⃣* A hankali ta fara nufar ɗakinsu tana tafiya kamar mai ciwon ƙafa, tana tura ƙofar ɗakin nasu sukayi ido biyu da Binta da take ta chatting abun ta, domin ita abun ma wani abun alfahari ya zama mata, sai posting hotonta da suka taɓa ɗauka da Siyama ɗin take yi tana faɗin ai ita ɗin ƙanwar Siyam Olusha ce. Tana ganin Siyama ta miƙe ta nufo gurinta tana kallonta itama sai binta da kallo take. Kafin tayi magana ta ce "Ina Fati?" Binta ta ce "Tana sashen Umma tun ɗazu" Tana jin haka ta sauke ajiyar zuciya ta zauna a gefen gadon ta sauƙe jakar dake jikinta sannan ta kwanta a kan gadon tana mai kallon saman rufin ɗakin. Ita dai Binta sai binta da kallo take amma ta kasa ce mata komai, ganin shirun yayi yawa yasa Binta faɗin "Anty Siyama ko zamu ɗanyi salfi guda biyu ne? Ta faɗa domin tambayar da ake mata na cewar tayi hoto da ita yanzu idan har da gaske ne ita ɗin ƙanwarta ce. Kafin Siyama ta bata amsa sai ji sukai an turo ƙofar an shigo da sauri. Da sauri Siyama ta miƙe zaune tana kallon Fati da take ƙoƙarin saka saƙata sama da ƙasa a ƙofar ɗakin. Siyama dai sai binta da kallo take. Itama dai Binta a tsorace take sosai ganin yanayin Fati ɗin. Fati cikin rawar murya ta ce "Anty Siyama Umma ce wallahi tace sai ta yanka ki, wai sai kin bar mata gida, ga cen Momy da Mama suna bata hakuri amma sai kuka take yi, shima Yaya Bala bata gyalesa ba, duk da ciwon hannunsa amma haka take ta dukan sa, shima Nasiru sai kulle shi akayi a ɗaki. Siyama ta ce "Buɗe ƙofar" Fati ta kalleta ceke da madarar mamaki ta ce "Baki da hankali ne, bakiji me nace ba?" Cikin zafin hannu Siyama ta miƙe ta shiga ƙoƙarin cire saƙatan da Fati ta sa, amma Fati ɗin tana hanata domin ita tasan abun da ta gani daga Umma. Kasancewar ƙarfin su ba ɗaya ba yasa Siyama ta tureta gefe ta cire saƙatan. Daidai lokacin kuwa Umma ta ƙaraso ƙofar ɗakin. Turus suka yi kowa na kallon kowa, lokaci ɗaya Umma ta tsaya da kukan da take yi tana ƙarewa Siyama kallo, ganin irin kayan dake jikinta. Itama Siyama kallo Umma ɗin take yi, tana ganin yadda ta rame lokaci ɗaya a cikin kwana ɗaya kawai, ga wannan kwarjinin da take mata yauma dai an ninninka shi, sosai take tsoron Umma domin mace ce mai zafin gaske, bama ita ba, dukkanin su suna taron ta sosai. Lokaci ɗaya Umma ta ɗauke fuskar Siyama da mari sannan ta kamo ta ta turo ta baya ta fara faɗin..."Siyama mai muka rage ki da shi? So kike Allah yayi fushi dani yace ban kula da tarbiyyar Kuba, duk irin ƙoƙarin da nake yi a kan ku amma Siyama sai kin wulaƙanta ni, Siyama ki fito bainar duniya tsirara Siyama, kina ƴar musulmai akan kuɗi, ko mun faɗa miki bamu gode a yadda Allah ya yimu bane? Sosai Umma ke kuka tana dukan Siyama wacce itama kukan take yi. Itama Fati kuka take yi kaman ranta zai fita. Umma ta ce "Faɗa min waye ya baki wannan shawarar kuma mai ya kaiki aikata wannan abun? Ganin taƙi yin magana yasa Umma ɗin ƙara mata mari ta na faɗin "Na rantse da Allah idan baki min bayani ba sai na yankaki kowa ya huta, ina miki magana kina kallona tsabar raini. Ana cikin Haka Kawu Inuwa ya shigo dalilin kiransa da Nasiru yayi. Ai kuwa yana zuwa ya hau Umma da faɗa kamar zai mareta, sosai yayi mata kace-kace ganin yadda duk ta bi ta ɗaga hankalin gidan. Sosai Siyama ke kuka Kawu Inuwa nata rarrashin ta. Haka dai Umma ta koma sashen ta Momy nata bata hakuri amma ina idan Umma ta tuno da yadda taga Siyama sai hankalinta ya ƙara tashi. Sosai Kawu Inuwa ya shiga lamarin har dai komai yayi sauki har akayi sadaƙar bakwai, har lokacin kuwa Umma bata ƙara bi ta kan Siyama ba, itama Siyama ɗin bata ko ƙara fita waje ba, haka zalika tun lokacin da ta kashe wayar ta a gidan Aida bata ƙara ko bi ta kan wayar ba, domin wani irin zazzaɓi ne mai zafi ya kamata tun lokacin da Umma ta jibgeta. Sosai Fati ke ta ɗawainiya da ita, shima Nasiru ya yi fushin ya haƙura yanzu har ɗakinta yake shigowa suyi hira, amma har yanzu basu magana akan abun da ya shafi matsalar ba, shi kansa yanzu Yaya Bala abun ya haɗar masa goma, ga rashin matarsa ga ciwon jikinsa ga wannan abun da Siyama tayi, yasa kowa sai kiransa yake yana tambayar sa, ga kuma fushin da Umma take yi da shi yanzu, ko yaje gaidata bata amsa wa babu yadda bai yi da ita ba amma taƙi sakar masa fuska. Washegarin ranar da akayi sadaƙar bakwai ne Fati da Siyama da Binta na cikin daki suna hira sama-sama sai ga Nasiru ya shigo ya kalli Siyama ya ce "Ina wayarki?" Siyama da har yanzu jikin nata baiyi daidai ba tace "Tana cikin jaka" Nasiru ya ce "Ibrahim ne ke ta kiranki yanzu haka yana waje, ya dade ki tashi kije. Yana faɗa ya juya bai ko bi ta kan maganar da take na cewar yace masa bata da lafiya ba. Fati ta ce "Ki tashi kije kice masa bakya da lafiya ne. Siyama ta kalli Binta ta ce "Binta fita kice masa bana da lafiya" Har Binta ta tashi Fati ta ce "A'a anty Siyama dan Allah kije da kanki please. Siyama ta miƙe zaune tana jin ai wallahi ba zata taɓa ƴarda ta ƙara haduwa da shi ba, ai tunda Allah ya taimake ta ya rabata da shi cikin ruwan sanyi to wallahi ta gode. Siyama ta ce "Ke wallahi ba zan iya fita a haka ba" Fati da ta cika da mamaki ta ce "Ibrahim ɗinki ne fa IB dai naki makaniki? Siyama ta ja tsaki ta koma kwanciyarta. Fati da ta buɗe baki da mamaki ta rufe ta ce "Ai wallahi anty Siyama bana tare da ke wajen yaudarar wannan bawan Allah ɗin, ai wallahi zunubin ki sai ya shafi mu muda muke kusa da ke, ki hana mutun kula kowa tsawon shekaru amma yanzu lokaci ɗaya kice zaki guje masa, dan Allah Karki fara. Siyama ta ce "To bari kiji wallahi ban taɓa son Ibrahim ba ko na minti rabi, dama nayi haka ne domin kar kowa ya gano shiri na, yanzu kuma na gama, abu ɗaya zan iya masa yanzu shine zan basa kuɗi masu yawa da zai ja jari idan kuma yaƙi ya fita a sabgata to Allah zan sa a ɓatar da shi. Yanzu haka saboda bani da lafiya ne yasa kika ga nayi shiru amma zuwa na warke komai zai cigaba, itama kanta Umma idan taji kuɗi duk wannan abun mantawa da shi zata yi, yanzu haka ina da Contract ɗin aikin Model da zan fara in sha Allah. Lokaci ɗaya Fati da Binta suka haɗa baki gurin cewa "Model" Siyama ta ja tsaki ta juya musu baya. Suka kalli juna suna mamakin Siyama. *IBRAHIM* Haka ya kwanta a wannan daren yayi barci rabi da rabi, ko da ya tashi da safe number ta ya fara kira amma dai har lokacin a ka she. Kamar da wasa ya tashi da ciwon kai mai zafi har baya ko iya magana sosai. Hajja dai gaba ɗaya ta rikice gashi ya ƙi sanar da su abun da ya faru. Haka tasa Nana ta je ta sayo musu maganin ciwon kai, bayan ya karya ta basa maganin ya sha, Ko da ya sha shine ya ɗan samu sauƙi, ganin barci ya ɗauke sa ne yasa ta fita ta bar masa dakin. Ita kuma Nana ta fara aikin gida. Hajja tana zaune Nana na kama mata kai shi kuma Ibrahim ya shiga wanka sai ga wata ƴar makwabtansu ta shigo da gudunta tana kiran sunan Nana. Har sai da suka tsorata bata ko tsaya wata-wata ba ta fara faɗin "Nana zo kika sirikarku ta zama tauraruwa. Tana faɗa tana turawa Nana wayar da har ta miƙe tsaye zata gudu, Hajja da kuwa tuni itama ta miƙe kasancewar har yanzu tana da ɗan kuzarin ta bata sakwarkwace sosai ba. Har Hajja zata fara masifa amma idanunta ya sauƙa a kan wata mai kamar Siyamar Ibrahim dinta sanye da wasu kaya komai nata a waje. Da dan mamaki Hajja ta ce "Me zan gani haka, wacce wannan ɗin jiki duk a waje? Yarinyar mai suna Fatima ta ce "Hajja ai Siyamar Ibrahim ce, ina wannan taron da a keyi na sarauniyar kyau, to shine fa ta shiga kuma gashi Alhamdu Lillah ta zo ta biyu. Fatima ta ƙarasa tana sakin murmushi. Hajja ta saki dogon salati har zuwa ƙarshe kafin ta amshi wayar daga hannun Nana da tayi shiru tana mamaki. Hajja ta ƙara kafawa wayar ido kamar zata shige ciki. Ta kai minti biyu kafin ta ce "Lala-lala wannan ba Siyama ba ce, Nana gane min wannan yarinyar da idanunta babu ko a lamar kunya, kalli yanda take abun fa da gani kasan ta saba, wannan ba Siyama bace. Ganin dai Hajja taki yarda yasa Nana faɗin. "Hajja ita ce mana ai shine dalilin da yasa Yaya wannan ciwon. Daidai lokacin kuwa sai ga Ibrahim ya fito daga wanka ai kuwa Hajja ta miƙe ta samesa ta na nuna masa wai da gaske Siyama ce wannan? Ibrahim ya kalli Fatima da ta sunkuyar da kai ganin sa ya fito, ya ce "Karɓi wayarki ki bar gidan nan" Hajja ta ce "Taje ina baka sanar da ni gaskiya ba? Ganin Ibrahim yana ƙoƙarin ajiye bokitin hannunsa ne yasa ta amshi wayar ta ta bar gidan da sauri. Hajja kuwa gaba ɗaya ta shiga ruɗani ita dai har yanzu bata yarda Siyama ce wannan ƴar duniyar da ta gani ba. Nana ma dai abun yazo mata a bazata, domin dai Siyama barta da iyayi da girman kai, amma sam halinta bana kwaɗayi bane, sannan a ɗan sanin da tai mata tun da suka dawo wannan unguwar zata iya tabbatar da cewar yarinya ce ba mai hangen nesa ba, to ko dai ɗan wannan kyawun da take da shi ne ya ruɗeta har ta shiga wannan harkar. Haka kawai taji ta fara tausayin Yayanta domin kuwa tabbas tasan ya rasa Siyama kenan kuma tasan irin son da yake mata. Ibrahim kuwa haka ya shiga ya shirya sannan ya fito da kayan aikin sa na zuwa gareji, kallo ɗaya Hajja tai masa ta tsorata domin kuwa tabbas ya rame sosai. Hajja ta ce "Ina kuma zaka je bayan baka da lafiya? "Hajja kirana a kayi wani aiki zamu karasa yanzu zan dawo " Ya faɗa yana ƙoƙarin fita. Hajja ta ce "To dan Allah dai karka dade idan kasan ba zaka iya ba ka dawo gida kaji?" Ibrahim ya amsa da tom kafin ya sa kai ya fita. Koda ya fita ya fara takawa a ƙafa har gurin aikin nasu. Yana zuwa ogan nasu ya fara tambayarsa lafiya yau ya makara Ibrahim ya sanar masa cewar baya jin dad'i ne shi yasa. Haka suka fara aiki amma ina wani irin sabon zazzaɓi ne ya rufe sa, ogan nasa da kansa ya tare masa mai mashin ya dawo da shi gida. Ko lokacin da ya dawo gida labarin Siyama ya gama yaɗuwa, izuwa yanzu Hajja ta yarda da cewa Siyama ce domin kuwa yadda mutane suka dinga kawo mata tsegumi kamar ba gobe. Nan dai Hajja ta shiga basa baki akan yayi hakuri ai tana sonsa wannan ma kuskure ne idan yayi mata faɗa zata bari. Shi dai Ibrahim babu abun da yake masa zafi sai idan ya tuno da cewar Siyama fa bata taɓa son sa ba, tayi amfani da shi ne kawai, a takaice dai yaudarar sa tayi. Idan ya tuna wannan shine ciwon ke ƙaruwa ga kuma wani irin sonta da yake ɗawainiya da shi, ji yake kawai ita yake son gani ko da kuwa zaginsa ne zata yi, gashi har yanzu bata kunna wayar tata ba. Wani abokinsa ne ya shigo gidan mai suna Haladu wanda ya bashi aron wayar da yaga video ɗin a ciki. Ya ce "Daga garejin ku nake aka ce ka dawo gida yanzu? Ibrahim ya meƙe zauna ya ce "Eh yanzu na shigo zazzaɓi ke damu na" Haladu ya ce "Ka dai saka damuwar wannan yarinyar kawai, ai dama kaga abun da nake faɗa maka, wallahi yarinyar nan ba dan Allah take sonka ba, amma kai kace ƙarya ne, to yanzu ka gani abun da nake so da kai shine wallahi tun wuri kayiwa kanka karatun ka natsu ka manta da wanzuwarta ka kama gaban ka, ka dai ga inda ta dosa harkar zubar da mutunci da wulaƙanta. Ibrahim da ya kafe Haladu da kallo har sai da ya gama kafin cikin ƙarfin hali ya ce "Haladu wallahi daga ranar da abun ya faru zuwa yau wani irin sonta ne ya ƙara ƙaruwa a zuciyta, wallahi ina son Siyama sosai, domin ina ji kamar zan yi hauka idan na rasa ta, please dan Allah ka bani shawarar da zata kaini ga samun Siyama please? Haladu ya ɗanyi dariya kaɗan kafin ya ce "Kaga IB karka ɗorawa kanka abun da Allah bai ɗora maka ba, tun wuri ka fita batun wannan yarinyar, ni dai ita ce shawarar da zan iya baka. Ibrahim ya ce "Wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba, domin ni sabo da Allah nake sonta, kuma itama tana sona inaga wani ne yayi wasa da tunaninta kasan mace kuma yarinya ce. Haladu ya ce "Ina waya ta? Ibrahim ya ce "Kasan me ya faru jiya tsakanin mu da ita? Haladu dai ya ce "Dan Allah ka bani wayata ana jirana. Ba tare da ya ɗauko masa wayar ba ya ce "Dan Allah ka kira min ita da wayar ka ni inaga tayi blocking dina ne. Cike da mamaki Haladu ya ce "Sabo da me? Domin kuwa shi kansa Haladu ya san da cewar Siyama tana nunawa IB so amma shi dai yasan ƙarya ne, babu yadda za'ayi mace irin wannan ta kamu da son mutum kamar IB wanda ko a cikin abokansu yafi kowa ƙazanta ga shi dai wani lokaci yana abu kamar mara wayo ko dolo. Amma kam tabbas idan baka san wacece mace ba tsaf zaka yarda cewar Siyama son sa take. "Ta ce wai daga yau babu ni babu ita wai tayi amfani dani ne domin cika burin ta kuma ta cika saboda haka karna ƙara nuna nasanta, Kuma tun juya ina kiran number ta bata shiga. Ibrahim ya faɗa hawaye na zubo masa. Haladu ya saki baki yana kallon ikon Allah. Ya ce "Ita ce ta kalleka ta ce karka ƙara nuna kasanta? IB ya gyaɗa kai. Haladu ya ce "Babbar magana wai kare da kiwon kura. Ya ce "Amma yarinyar nan ba ƙaramar jar wuya bace, wato anci moriyar ganga ko? To wallahi bata isa ba, ai yanzu ta zama sele kuma tayi kuɗi sabo da haka dole ta biyaka duk abun da ka kashe mata harda ƙari, kai nifa wallahi idan nine kai sai ta siya min gida da mota da kuma jari mai gwaɓi harda raran kudade a account, yo kai ai dama ce tazo maka mai kyau, kawai ka manta da ita. Ibrahim da ya gama zuwa ƙarshe ya ce "Haladu bana son zancen banza, wallahi ko kaɗan kudinta bai dame ni ba, ni ita nake so kuma wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba. Haladu ya katse shi da faɗin Ita dai sarauniyar kyau ɗin ko?. Sosai ran sa ya ɓaci har ya fito ya nunawa Haladu ɗin a fili kar she dai haka suka rabu. Da yamma ya tashi ya nufi gidan su Siyama ɗin amma haka ya ƙaraci zama bata ko fito ba, haka ya hakura zuwa gobe domin gobe ne za'ayi sadaƙar uku na Zainab, haka nan ma yanzu amma bai samu ya ganta ba. Sosai Ibrahim ya shiga damuwa babu yadda Hajja bata yi da shi ba akan ya hakura da ita amma ya kasa. Yau kwana takwas da faruwar komai kuma izuwa yanzu bai daina ziryar zuwa gidan su Siyama ɗin ba, hardai yaci karo jiya a gurin sadaƙar bakwai suka haɗu da Nasiru yake sanar da shi baya samun wayar Siyama. A nan dai Nasiru yake sanar masa cewar ai bata da lafiya ne, haka Ibrahim ya ƙarbi number sa akan idan yazo gobe zai kirasa sai ya turo masa ita. Haka washegari da kyar ya samu Haladu ya rakoshi akan zasu duba jikin Yaya Bala ne da Nasiru. Koda yazo ya kira Nasiru yazo ya shigar dasu har cikin gidan suka duba Yaya Bala sannan suka gai da Umma sannan suka sake yi musu ta'aziyar

Chapter 5 of 11