rashin Anty Zainab. Bayan sun fito ne Nasiru yaje ya kira musu Siyama akan Ibrahim na waje yana jiran ta. A lokacin zuciyar Ibrahim kamar ta fita tazo gareta jin ance bata da lafiya sai yake tunanin kamar abun da tai masa ne yasa, yasan itama tana sonsa ba zata iya rayuwa ba tare da shi ba. Haka suka dinga tsayuwa zaman jira har dai Haladu ya fara magana, wasa-wasa sun kwashe kusan awa da rabi amma shiru. Hakan yasa Ibrahim sake kiran Nasiru yana ɗagawa ya ce "Har yanzu fa bata zo ba. Cike da mamaki ya ce "Wace ɗin?" Yayi tambayar da mamaki ganin kusan awa biyu da kiranta.
*SIYAMA*
Wayarta ta ɗauko ta jona a chaji tana jin yau dai ya kamata ta ɗan matsa ko Aida ta samu ta kira taji yaya a ke ciki a Team. Ita har ta manta da batun wani Ibrahim a waje, suma su Fati sun ma manta har sun bar maganar. Tana ƙoƙarin saka wayar a chaji sai ga Nasiru ya shigo hannu a saƙale ya na faɗin "Siyama wannan wani irin rashin hankali ne zaki bar mutum sama da awa a waje yana jiran ki, baki da hankali ne? Siyama ta ja tsaki a fili ta ce "Amma ai nace maka kace masa bana da lafiya ne ko? Kuma ai na sanar da shi babu ni babu shi to mai kuma yazo yi mini" Fati da Binta suka cika da mamakin jin cewar har yanzu Ibrahim na tsaye. Nasiru da ransa ya gama ɓaci, gashi dama cike yake da ita, jira yake kawai ya warke sai ya saita mata zama. Ya ce "Na tsare da Allah idan baki tashi kin fita ba sai na ɓata miki fuska da mari, dan ubanki waye ya kawo shi a matsayin wanda take so, na rantse kika ƙara magana a gurin nan sai na tar watsa miki baki wawiya kawai mara hankali. Jin haka yasa ta tashi ko hijjab bata tsaya ɗauka ba, kanta babu ko hula ta nufi hanyar fita. Sai dai ganin Umma zaune a palon ita da Kawu Inuwa suna tattaunawa ne yasa ta juya da sauri ta saka hijjab ta fito fuska a haɗe, babu wanda taiwa magana Palon ta sakai ta fita. A nesa ta hango su, hakan yasa ta nufe su da sauri tana aiyana irin cin mutuncin da zatai musu. Kallo ɗaya tai masa taga ramar da yayi harda wani dogon wuya kamar yaron raƙumi. Tana zuwa babu ko sallama ta ce...📝
Love all
One love
Comments
And shering
Love my fan's
By S-Reza writer
[7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*
_By S-Reza_
*FCWA*
*My WhatsApp channel*
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
*Page 7️⃣*
"Uban me ya kawoka ƙofar gidan mu bayan na maka iyaka da ni, na faɗa maka babu ni babu kai, abun da ya rage tsakanina da kai shine ka lissafo duk abun da kasan ka taɓa kashe mini zan ninka maka kayan ka, bayan haka karka ƙara nuna ka sanni idan kuma ba haka ba, wallahi Ibrahim sai kayi da ka sanin sanin Siyama da kayi a rayuwar ka, zan sa a ƙulleka har karshen rayuwarka. Siyama ta faɗa ranta a mugun-mugun ɓace, domin har ga Allah ya kaita bango, gara tai masa barazana ko zaiji tsoro ya rabu da ita ta sakata ta wala arayuwarta. Cikin karyewar murya Ibrahim ya fara faɗin "Siyamata karki min haka wallahi na yarda zan barki ki ci gaba da yin wannan aikin naki amma ba zan iya rabuwa da ke ba, wallahi da gaske ne ina sonki kuma na hakura da komai dan Allah karki min haka zan iya mutuwa wallahi" Ya karasa yana sunkuyawa har ƙasa. Wani irin banzan kallo tai masa kafin ta ce "Innalillahi wai nima mai ya kaini ai ga shi zan jawa kaina annoba. To bari kaji, na rantse da girman Allah ko mutawa zaka yi ka dawo duniya ka ƙara mutuwa ba zan ƙara bari ka ganni ba, na baka nan da kwana uku ka kawo min lissafin ka zan biya komai idan kuma muka wuce kwana uku to duk abun da ya same ka kai ka jawa kanka. Ta kalli Haladu da ya rakuɓe gefe ta ce "Idan shi wawa ne kuma dolo bai san abun da yake yiba, to kai ka sanar da shi, babu ni babu shi, idan kuma yaƙi ji ba zai ƙi gani ba, soyayya ce munyi a baya yanzu kuma nace na gama ba zanyi ba, kana dai ji ko?" Haladu ya ɗaga kai da sauri ita kuma ta juya zata shige gida. Da sauri Ibrahim ya kamo gefen hijjabin ta yana faɗin dan soyayarki da Annabi Muhammad s a w Siyama karki azabtar da zuciya da sanki, wallahi Siyama babu wasa a magana ta, zan barki kiyi komai ni Ina son ki a haka please. Siyama ta juyo a zuciye ta ce "Sakar min hijabi kafin na wanke maka fuska da mari, wai kai wani irin maye ne mara zuciya, ana soyayya dole ne. Ibrahim ya miƙe tsaye yana kallonta ganin yanda ta ɗanyi fari alamar rama sai hakan ya kara fito da hasken ta, ga wani kyau da tai masa fiye da kullum, jin sonta yake har wani fusgarsa yake kamar magineto ya ce "Siyama ke da kanki kika min alkawarin bazaki barni ba, kuma kince..."Kafin ya ƙara cewa komai ta fusge hijjabin ta ta juya zata shiga gida amma bata an kara ba sai jin ta tayi a cikin jikin Ibrahim kwance kamar ta samu gadon baccin ta. Sosai ya haɗe jikinsu a karo na farko yana sauke ajiyar zuciya har wani lumshe ido yake, yana jin ina ma zasu dauwama ahaka shi da Siyamar sa. Shi kansa Haladu ba karamin shok ya shiga ba ganin abun da Ibrahim ɗin yayi, sosai ya tabbatar da cewar Ibrahim baya cikin hankalin sa, idan kuwa ba haka ba tayaya zai rungumeta bayan nuna masa tsana da take yi har tana faɗin ko mutuwa ma zai yi sai dai yayi. Ita kuwa Siyama tsabar mamaki yasa bata fahimci komai ba, sai da taji yana ƙara kwantar da kansa a wuyan ta, har wani sauke ajiyar zuciya yake, idan bata yi ƙarya ba har wani wari yake yi na ƙazanta. Sosai ta dawo cikin hankalinta, ai kuwa da wani irin ƙarfi ta shiga raba jikinsu amma Ibrahim yaki bata damar hakan, tayi iya yinta amma ya manne ta sosai har neman ƙaryata yake yi. Ita kuwa ganin ta kasa kwacewa ga azabar ruƙo yasa ta fashe da kuka, amma ina Ibrahim bai san tana yi ba, sosai take kuka tana dukan sa ta ko inna amma shi sai lumshe ido yake ya faɗa duniyar tunani. Ganin dai kamar baya cikin hankalinsa ne yasa Haladu zuwa ya shiga ƙwatarta da ƙarfi, da kyar ya yageta daga jikin sa yana jan sa baya. Ita kuwa Siyama ganin haka yasa ta kwasa da gudu tayi cikin gida. Daidai zata shiga Palo shi kuma Kawu Inuwa zai fito suka haɗu. Ya ce "Lafiya ke kuma keda waye haka?" Siyama ta fashe da kuka mai ƙarfi tana nuna waje. Kawu Inuwa ya leƙa sai dai bai hango kowa ba, ganin ta shige ciki ne yasa ya girgiza kai ya bar gidan yana mamakin Siyama. Ko da ta shiga ɗakin su ta tarar da Fati da Binta kowacce na danna waya, bata ko bi ta kansu ba ta shiga rusar kuka kamar wacce aka yankewa ƙafa. Miƙewa tayi ta shiga toilel ta sakarwa kanta ruwa ba tare da ta cire kayan jikin ta ba, sosai Fati suka bita da kallo jin irin kukan da take, har Fati zata tambaye ta amma taga ta shige toilel hakan yasa ta fita izuwa dakin Nasiru. Sosai ta shiga wanke jikinta har lokacin tana jinsa a manne a jikinta, tana kuka tana tsine masa. Koda da fito Binta kawai ta gani a dakin bata ce mata komai ba ta kwashi kayan da zata sake ta komai toilel ɗin.
Tana gama shirya wa ta fito Palo domin ɗaukar a binci, amma tana zuwa taga Umma da Nasiru da yaya Bala da Kawu Inuwa Harda Fati duk sun saka waya gaba suna kallo. Gabanta ne ya bada wani rass domin jin ana kiran sunanta a cikin maganar da a keyi ta cikin wayar duk da cewar kuwa da turanci ake maganar. Kallon Umma tayi taga wani irin kallo da take mata, haka yaya Bala shima. Ƙamewa tayi a gurin ta kasa gaba ta kasa baya domin bata san kuma me ta ƙara yi ba. Umma ce ta ce "Haƙika samuwarki a cikinmu bai amfana mana komai sai masifa da tashin hankali, wato mu iyayenki mune abun cin mutumci har kina faɗa wa duniya cewar bamu da mutunci ko, yanzu Siyama mai muka miki a duniya da muka cancanci wannan abun, bayan zubewar mutuncin da kika jawo mana shine sai kin ƙara tozarta mu a cikin idon duniya. Yaya Bala ya ce "Umma kiyi hakuri duniya ce, wanda mai zo bama tana jiransa bare kuma wanda ke cikin ta, mu dai Allah ya gani wannan abun da ta faɗa idan Sherri tai mana Allah na gani, idan kuma gaskiya ne shima Allah zai saka mata. Umma ta fashe da kuka tana face hanci, gaba ɗaya lamarin Siyama yafi ƙarfin ta, bayan wannan abun da tayi shine bai ishe ta ba, har sai ta tabbatar wa da duniya cewar iyayenta mutanen baza ne. Kawu Inuwa ne ya iya faɗin "Haba Siyama Meya hakan kikayi, me iyayenki su kai miki mai suka rageki da shi a gidan duniya da zaki wulaƙantamu har haka, Siyama me duniya zata baki wacce baki samu tare da mu iyayenki ba. Yanzu wannan abun da kika fadawa duniya Kinsan iya lokacin da abun zai kai yana yaɗuwa. Siyama dai gaba ɗaya kanta ya ƙulle, to ita me tayi me tace! Ganin bata gane bane yasa ta juya da sauri ta ɗauko wayarta ai kuwa daga ɗazu da ta kunna wayar zuwa yanzu har ta samu kira sama da guda hamsin, Fita Aida ga kuma number Ibrahim ga Nusee. Sosai ta rikice har ma bata san wa zata fara kira ba. Kafin ta danna kira sai ga kiran oga Fita. Amma taji ba zata iya ɗaga kiran kowa ba a halin yanzu sai na Aida, ita ce kaɗai zata iya rarrashin ta har tayi shiru.
Kira ɗaya Aida ta ɗaga a ɗan rikice ta ce "Siyama kina ina ne kinga abun da ke faruwa kuwa?" Siyama ta ce "Please Aida wai menene, na kasa fahimta meke faruwa ne?" Aida tace "Karki damu nasan aikin waye, yanzu dai ki tabbatar kina gida, kuma idan Oga fita ya kiraki Karki ɗaga har sai na ce miki ki ɗaga, yanzu shiga WhatsApp zan turo miki da video ɗin. A kwai waɗanda nake zargi bari na tabbatar". Ita dai Siyama sai gyaɗa kai take tana sauraron ta. Dama tasan Aida itace komai nata, wallahi da babu Aida a rayuwarta da yanzu ta gama lalacewa. Suna gama wayar ta kunna data, kasancewar ta daɗe bata shiga WhatsApp ba, sai da ta tsaya sakonni suka gama shigowa kafin ta shiga sakon Aida. Kafin ta buɗe taga anyi rubuta a ƙasa sai ta karanta rubutan kafin ta shiga playing video ɗin. Cikekken labari akan Siyama Olusha tare da kafar yaɗa labarai na BBC. Sosai gabanta ya faɗi da sauri ta danna kan video ɗin kasancewar dama ya gama budewa.
Wannan mutumin da Oga Fita ya haɗa su da shi a matsayin ubanta na karya ne zaune a cikin gidan jaridar BBC yana basu labarin da bata san a ina aka kirkirosa ba. Sosai zufa ke karyo mata jin irin ƙaryar da mutumin ke shiryowa, harda faɗin wai iyayen siyama ɗin ne basa ko iya ciyar da ita, haka makaranta ma shine ya ɗauki nauyin biya mata, domin iyayenta sun ce bazasu iya ba. BBC su kai masa wata tambaya da tasa Siyama sakin fitsari a gurin domin jin amsar da Olusha ya bayar. Aka ce masa "Har yanzu kuma iyayenta basu nemeka ba ko dan ganin yanzu ƴar su ta samu abun duniya?" Olusha ya ɗan yi dariya ya ce "Yanzu haka halin da ake ciki kenan, ganin Allah ya ɗaukakata shine suka zagaya gefe suka lalaɓeta har yanzu tana nuna min cewar zata daina amfani da suna ta koma yi da na ubanta, sannan yanzu haka tun bayan faruwar abun tana gidan iyayenta ne, har yanzu bata ko zo gurin da nake ba, gaskiya nayi mamakin irin wannan butulcin da Siyam Olusha take son min. Sosai Siyama ta shiga tashin hankali mara misaltawa, domin kuwa Olusha cigaba yayi da bankaɗo abubuwa masu yawa, domin har mahaifin ta da ke ƙabari Olusha bai bari ba sai da yayi masa sharri. Daga karshe ya karasa da faɗin cewar, a lokacin da take hannunsa ta bar addinin Musulunci amma bai san yanzu ba ko iyayenta sun mayar da ita. "Innalillahi wa innalillahi raji'un! Shine abun da Siyama ke faɗa ta na zama daɓas agurin. Tana jin wayarta na ƙara amma ko ta kanta bata bi ba, ita tama rasa wani irin tunani zata yi. Ganin ana ta kira ne yasa ta duba wayar ganin Aida ce yasa ta daga ta kai kunne.
Aida ta ce "Kinga ki natsu kiji abun da zance miki... Kinsan su waye su kai wannan aikin? Siyama ta girgiza kai Aida ta ce "Adawiya da Badawiya ne, amma abun da nake so da ke Karki amsa kiran kowa, kuma ki zauna a gida yanzu haka Oga Fita yayi kiran gaggawa domin shima har yanzu bai gano gaskiya ba, nima bincike nayi, duk da har yanzu ban tabbatar ba, amma dai ina da tabbacin sune, yanzu dai idan na dawo zan kiraki, Karki amsa kiran kowa kinji? Batare da tace komai ba ta kashe wayar tana bin wayar da kallo. Daidai lokacin Nasiru ya shigo ɗakin ya bita da wani irin kallon tsana ya ce "Wallahi Siyama kinyi a sarar rayuwarki, da har ina tunanin butulcin da kikaiwa Ibrahim ashe harda iyayenki ma zaki sauya, wato kin ɗaukaka, kin samu abun duniya bari ki sauya kowa domin kar a dame ki ko? To gaki ga duniya da kuma Olusha, o! Sorry ashe fa kin koma Siyam Olusha Christa ko? Kallonsa take yi tana son ta ce masa wallahi ƙarya ne ake mata amma harshen ta yaƙi bata damar yin hakan. Nasiru ya ce "Kafin Umma tazo Gara ma ki tattara kayan ki ki tafi zuwa gurin ubanki da ya wadata ki da komai da mu muka kasa baki. Nasiru ya fita yana jin badan ciwon da hannunsa ke masa ba Allah da sai ya kusa ɓalla wannan yarinyar. Kuka take yi sosai tana tunano babban abun da zai sa Su Adawiya suyi mata haka. Dama har ƙiyayar da suke mata ya kai har haka.
******
*YAYA BALA*
Du ƙyar yayi sa'a Umma ta sakko daga fushin da take yi da shi, amma har yanzu taƙi yarda suya maganar Siyama. Shi kansa damuwar da yake ciki ce tasa bai ko zauna da ita ba, farko ya ɗauki abun da zafi, amma rasuwar matarsa yasa ya tattara komai yasa a gefe, yana so ya nusar da Umma cewar abun da Siyama tayi laifi ne amma yanzu tunda ya faru a jawota jiki domin kar ganin haka yasa ta fara tunanin yin abun da yafi haka. Amma ganin yadda Umma ɗin tayi ne yasa bai tare ta da maganar ba. Sai da a kayi sadaƙar bakwai kafin ya samu damar tunkarar Kawu Inuwa da maganar akan ya sanar da Umma ko zata hakura. Ai kuwa Kawu Inuwa ma ya fahimci sa hakan yasa ya samu Umma da maganar, sosai Umma ta shiga masifa akan sabo da me za'a jawota jiki bayan ta gama zubar musu da mutumci. Sai da akayi da gaske kafin Umma ta haƙura akan za'a raba Siyama da zuwa ko ina, sannan makarantar ta ma ta gama kenan, kuma ta sanar da Ibrahim ya turo ko baida komai a ɗaura auran domin dai shine kaɗai wanda ta bari yake zuwa gurin ta, har kuma ta tabbatar wa da iyayenta shi take so. Haka dai aka bar maganar akan gobe za'a zauna da ita aji yadda abun ya faru sannan a yiwa tufkar hanci. Washegari kuwa tun misalin takwas na safe Yaya Bala yaci karo da wannan sabon Video ɗin a Fecbok, ga kuma turo masa da shi da mutane ke tayi ta WhatsApp. Sosai ya shiga cikin tashin hankali ganin wata sabuwa. Farko yaso yaƙi yarda da abun amma idan yaga yadda mutumin ke magana kuma gashi tsoho, sannan kuma ai gaskiya ne, yanzu ta mayar da sunanta Siyam Olusha ba Siyama Al-Hasan ba. Daidai lokacin Nasiru ma ya shigo ɗakin nasa yana nuna masa. An taru akan a samo mafita sai taro ya dawo sabon tashin hankali, domin kuwa lokacin da Umma taga video ɗin kasa magana tayi, ai kuwa ana cikin haka sai ga Siyama ɗin ta fito. Sosai Umma ta shiga faɗin abun dake ranta, shima Kawu Inuwa zuwa yanzu yayi laushi da lamarin ta. Sosai yaya Bala ya shiga bawa Umma hakuri tana faɗin "Wallahi Siyama ba ƴar rufin asiri bace, mai muka mata a duniya da muka cancanci haka, aihuwarta da mukayi ne laifin ko rainonta da shayarwar da mu kai mata, rashin lafiyar ta da makarantar da ne ko dai menene. Sosai Umma ta basu tausayi har dai yaya Bala ya kaita sashen ta. Shiru yayi yana tunanin abun yi, anya kuwa wannan shirun da yayi ba matsala bane, to me zai yi shida baida lafiya, wata zuciyar ta ce "Kaje ka sami ita Siyama ɗin kuyi magana domin har yanzu baka san komai akan abun ba. Haka ya tashi ya nufi sashen su Siyama ɗin.
*****
*ADAWIYA DA BADAWIYA*
Adawiya ta ce "Ba wai shawo kan wannan tsohon ne matsalar ba, yadda zamu shirya zama da gidajen talabijin din shine matsalar. Shiru Badawiya tayi tana tuna cewar ai tana da wani saurayi mai aiki a BBC sannan kuma shi babba ne a gurin Badawiya ta ce "Wannan mai sauki ne, kawai dai amincewar shi mutumin ne matsalar. Adawiya da bata yarda ba ta saki tsaki tace "Wallahi duk kece kika ja mana wannan abun da yanzu ba wannan maganar ake ba. Ita Badau (Wani lokaci ana kiran ta Badau ne saboda a yanke sunan wato Badawiya ( tayi shiru domin kuwa tabbas tasan ita ce ta ja. Badau ta ce "Yanzu ke kiji da shawo kan sa, ni kuma zan haɗa musu zama koda da gidan radiyo guda uku ne ko biyu. Haka suka shirya kowacce ta fara gabatar da nata aikin. Lokaci da Adawiya ta fara samun Olusha da maganar bai yarda ba, domin ba karamin jan kunne Oga Fita da Siyama ɗin sukai masa ba, musamman ma bayan samun wannan nasarar tasu, domin kuwa har kuɗi suka ƙara masa. Babu yadda Adawiya bata yi ba, amma yaƙi yarda hakan yasa ta barsa harna tsahon kwana uku. Nan ma babu yadda bata yi ba yaƙi, sai da suka mallaka masa gida harda mota kafin ya yarda zai yi hira da gidan radiyo, farko yace sai dai ayi audio amma suka ce kar ya damu babu abun da zai faru, idan ma Oga Fita yace a biya sa komai da ya basa su zasu biya. Hakan yasa ya yarda, suka zauna suka shirya komai yadda abun zai tafi. Bangaren Badawiya Badau kuwa, dama suma BBC suna so zasu yi hira da ita Siyama ɗin, domin magana nata yawo akan ta, wasu suce musulma ce wasu kuma suce Christa ce, hakan yasa babu wata-wata suka saka musu rana.
Bayan fitar video ɗin kuwa sai ga abun da suke so ya samu, domin kamar dama abun da ake jira kenan labari ya yaɗu ta ko ina. Sosai abun yayi musu daɗi suna jira kawai suji labarin kwace aikin Baby and me da za'ayi da kuma rikici tsakanin iyayen Siyama da Siyama ɗin da kuma Fita da Olusha. Badau ce ta tura video ɗin cikin group ɗin su, duk da cewar kuwa wasu da yawa sun gani. Hakan yasa Oga Fita ya tara taron gaggawa. Adawiya da Badawiya ne suka fara isa gurin, kafin kace me kowa ya hallara amma babu Siyama. Cikin tsananin tashin hankali Oga Fita yake Tambayar Aida ina Siyama ɗin. Itama Aida ta ce bata san inda take ba. Nan fa Fita ya shiga faɗa yana zage-zage wai ita mai ya hana bata zoba. Adawiya ta ce "To tana ganin ita yanzu ta zama sele to mai zai kawo ta, yanzu ga shi irin abun da ubanta ya jawa mutane, kuma anyi taro domin a shawo kan abun ita da ya kamata ace tana gurin amma bata zo ba, to muma Meya amfanin zuwan mu, wa abun zai shafa idan ba ita ba. Aida ta kafe Adawiya da ido tana mamakin ƙarfin halin ta. Oga Fita ya daka mata tsawa yana faɗin "Kirufe mana baki a gurin malama" sosai kowa ya tsorata da tsawar da yayi. Shi Fita tunaninsa damar da suka samu karta kufce musu, sannan gashi yasan yadda Siyama take son iyayenta da tsoron su, tabbas idan har wannan abun ya baiyana zai iya rasa Siyama, domin yasan iyayenta zasu hanata kuma dole ta hanu. Tun ɗazu yake shiga da fita domin neman mafita, amma ya rasa. Ya taro wannan taron ne domin zai samu wata mafita guda ɗaya, shi har ga Allah baiyi zaton ko wasu daga cikinsu ne suka shirya ba, shi dai ya bari akan Olusha yayi halin su na ƴaƴan Adamu, kuma dole sai ya kai maganar gaba, dole sai ya sanar da shi waye ya saka shi wannan aikin bayan sun gama biyan sa.
Oga Fita ya ce "Kaman yadda kuka ji wannan mutumin ya faɗa cewar Siyama ba ƴarsa bace to tabbas haka ne, amma komai da ya faɗa bayan haka duk ƙarya ne, kuma koda za'a gaiyaci ɗaya daga cikin ku zuwa hira wani gidan radiyo ɗin to ta ƙaryata komai da yace. Badau ta ce "Yaya za'ayi mu ƙaryata bayan ita da kanta bata zo ta ƙaryata ba, Adawiya ma ta ce "Ai tun da kaji ya faɗa to gaskiya ne, dama haka halin matsiyata yake, daga lokacin da suka samu ɗaukaka babu wanda zasu fara wulakantawa sai wanda ya taimakesu, yanzu dai gashi, anyi mata abu har yanzu bata ce komai akai ba, yanzu kuma munyi taro amma bata halarci gurin ba. Sai a lokacin Aida ta ce "Duk abun da wannan tsohon ya faɗa ƙarya yake, kuma ko shakka babu saka shi akayi, ita kuma Siyama tana gida bata da lafiya yau sati ɗaya kenan, ko ƙofar gida bata fita, kuma wayarta a kashe sai ɗazu ta kunna, yanzu abun da ya dace ayi yanzu Oga Fita shine mu nemo su waye suka haɗa wannan munafuncin, kuma ko shakka babu suna cikin wannan team. Aida na faɗa gurin ya kaure da surutai, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Shi kuwa Oga Fita kansa ya dafe yana tunani. Adawiya ce ta mayar mata da amsa "Sai dai ko idan kece kika haɗa komai domin kuwa kece kika san duk wani sirrin ta a wannan team ɗin, domin mu sai yauma muka san ita ba ƴar gidan Olusha bace. Aida ta ce "Ko kuma kuda kuke bakin ciki da ɗaukakar da Allah yayi mata ba" Lokaci ɗaya Adawiya ta ɗauke wuta, tana kallon Aida. Oga Fita ya ɗago yana kallon su. Lokaci ɗaya ya ce "Kowa yayi shiru. Kuma kowa ya tashi ya tafi an fasa yin taron. Haka kowa ya tashi sai kallon-kallo ake kowa na jin kamar ya kaiwa ɗan uwansa duka. Sosai video ɗin ya ɗauki hankulan mutane ga shi har yanzu babu wanda ya fito yace wani abu akan maganar, sai yan