Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Socal media da aka bari da aikin yaɗa karya da gaskiya. Ana cikin wannan halin kamfanin Magazing wanda Adawiya take musu aiki suka sanar da ita cewar zasu yi aiki da ita na tsahon wata uku a Ingila zata je ta haɗu da sauran Models na kasashe daban-daban domin suyi aiki tare. Sosai murna ta samu team ɗin nasu Oga Fita duk da cewar yana cikin damuwa amma bai hana jin dadin abun ba. Washegari Adawiya suka tashi izuwa Ingila bayan ta gama shiryawa Badawiya komai. ****** *IBRAHIM* Haladu na jansa yana tirjewa kamar sabon mahaukaci, sosai yake tirjewa yana kiran sunan Siyama, shi dai Haladu abun da ya gani kuma yaji yafi karfin hankalin sa, sosai ya ƙara tabbatar da cewar tabbas Ibrahim yana son Siyama so ba na wasa ba, duk inda suka wuce sai an bisu da kallo domin kuwa Ibrahim buɗe baki yayi yake kiran sunan Siyama, duk wanda kuwa ya sanshi da Siyama dariya yake masa. A haka ya kawo shi har cikin gidan su kafin ya sanarwa da Hajja komai da ya faru tsakanin sa da Siyama. Ai kuwa Hajja ta fashe da kuka ganin yadda ɗan jikan nata ya koma kamar sabon mahaukaci a kan Mace. Sosai take kuka tana basa baki akan ya rufa musu asiri karya kashe kansa akan Mace, amma ina Ibrahim sunan Siyama kawai yake ambato. Ta shi yayi ya ɗauko wayarsa ya shiga gurin number ya latsa kira, amma bata shiga ba ita dai Hajja tana ta kallonsa. Ta ce "Ibrahim yanzu a kan Mace ka mayar da kanka haka, macen ma irin wannan mara tarbiyya da tunani, dan Allah ka yi hakuri ka samo wata ka cire tunaninta domin kaji tace bata sonka, dan Allah kaima kayi zuciya kaji ɗan ƙalilan?". Ibrahim ya ɗaga kai ya kalli Hajja sai kawai ya sunkuyar da kai ya fara ƙoƙarin tashi zai fita. Da sauri Haladu ya tare shi yana faɗin. "Wallahi Hajja a shiga tsakaninsa da wannan yarinyar domin tsaf zata iya aikata abun da tace, kin ga yadda take magana, harda cewa fa tayi zata sa a ɓatar da shi idan ya ƙara nuna ya santa. Ni Hajja shawarar da na basa ita ce, tunda har tace yaje yayi lissafin komai da ya kashe mata zata biya to kawai ya kai mata in yaso sai yayi amfani da kuɗin yayi wani auran". Hajja ta ce "Na yarda da maganar ka Haladu, kawai ta biya sa komai nasa. Haladu ya ce "Nifa na fara tunanin ma yarinyar bata da cikakkun hankula a kanta, domin irin abun da take yi kamar mara hankali. Ibrahim dai yana jinsu bai ce komai ba har suka gama Haladu ya bar gidan. ****** *SIYAMA* A hankali take tafiya domin bata bukatar kowa yasan da fitar ta. Ai kuwa cikin ikon Allah babu wanda ya ganta har ta bar cikin gidan. Tana tafiya kamar mara gaskiya sai juye-juye take tana kallon baya, gashi hijabi da tasa ya mata ƙadan, duk wanda ta wuce ta kusa da shi sai ya ƙara kallonta, wanda ya gane ta ya cigaba da kallo wanda kuwa bai gane ta ba ya girgiza kai ya ƙara gaba. Sai da tazo bakin titi kafin ta samu mai mashin tai masa kwatancen gidan Aida ta hau suka tafi. Suna zuwa ta sauƙa ta shiga cikin gidan domin karɓo masa kuɗin sa. Amma tana shiga gidan taga alamar babu kowa, sosai take mamaki domin kuwa tasan idan Aida bata nan to Jamila da jamilu koda yaushe suna cikin gidan a zaune. Dama ita har mamakin yaran take, domin zai yi wahala ka gansu a waje, kullum suna cikin gida kamar wasu amare, gasu da tarbiyya da ladabi, sosai take jinjinawa Aida akan tarbiyyar yaran duk da cewar yara ne amma dai tayi ƙoƙari, ƙarya ne tazo gidan basu gaida ta ba, gashi kullum kansu a ƙasa kamar wasu makafi, gashi basa da magana kwata-kwata ita dai yaran na burgeta. Haka ta shiga kiran sunan Jamila amma shiru sai kawai ta shiga ɗakin Aida ta kwanta domin kuwa wallahi bazata iya fita waje tace masa bata da kuɗi ba, sai dai ya tsaya har Aida ko Jamila da jamilu su dawo. Ta kai minti biyar a kwance sai taji kamar motsi a ɗaya ɗakin da yake jikin na Aida, hakan yasa ta sake saurara da kyau ai kuwa motsi ne harda ɗan ihu kaɗan. Hakan yasa ta tashi da sauri ta fita ta nufi ɗakin, a hankali ta tura tana raba idonta cikin ɗaki a ɗan tsorace. Gabanta ne ya fadi taji wani irin shok ya daketa lokaci ɗaya taji tana neman rasa tunaninta ganin Jamila da jamilu tsirara aihuwar uwarsu suna yin Seex. Innalillahi wa innalillahi raji'un! Take furtawa a ranta...📝 Love all One love Comments And shering Love my fan's By S-Reza writer [7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!* _By S-Reza_ _FCWA_ _My WhatsApp channel_ https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a *Page 8️⃣* Sosai gabanta ke faɗuwa kana ƙara kallon ikon Allah, azuciyarta tana cika da mamakin wai Jamila da jamilu ne ke aikata wannan ɗan yen aikin, ganin basu ganta bane yasa ta sake leƙawa, ta ja musu kofar ta koma da baya har zuwa cikin ɗakin Aida tana jin wani irin tsoro a ranta. Waya ta ɗauko ta kira number Aida tana ɗagawa Aida ta ce "Yauwa yanzu nake son na kira ki, ki duba Email ɗinki zakiga sako, sannan maganar aikin Baby and me ya taso, yanzu haka maganar muka gama yi da Oga Fita, kuma an yanke shawarar Fita zai zo gidanku domin yayi magana da iyayenki, ya sanar da su gaskiyar magana, domin sanadin abun da ya faru yana son kawo matsala a aikin da za'ayi, yanzu haka mutane sai ƙara rura wutar abun suke yi. Cikin wata irin murya ta ce "Aida ina cikin gidan ki kizo yanzu". Aida cike da mamaki ta ce "Wani gida kuma ba nace miki karki fito yanzu ba, Kinsan ilar take tattare da fitowar taki kuwa, mai yasa ba kya da tunani ne wani lokaci, sosai Aida ta rikice har tana masifa, ita dai Siyama tasan za'ayi haka. Siyama ta katse ta da faɗin "Na riga na fito kawai kizo. Cikin mamaki Aida ke tambayarta lafiya kuwa take ya taji muryarta haka. Siyama dai ta katse wayar tana tunanin abun yi, shin ta sanar wa da Aida ne ko dai ta bari babu ruwanta, ko kuma ta samu Jamila da jamilu ɗin tayi musu faɗa da nasiha, sosai take ta sake-saƙe har taji ana sallama. Amsawa tayi tana bada izinin a shigo. Jamila ce ta shigo tana ganin Siyama ta tsuguna har ƙasa tana gai da ta. Siyama ta amsa tana binta da kallo. Ta ce "Na shigo gidan ban ga kowa ba, kuma ga gidan a buɗe, shine nace bari nazo na huta kafin ku dawo. Jamila tace "Eh anty Aida bata dade da fita ba, shi kuma Jamilu baya jin dad'i ne, yana kwance shine naje kula da shi har barci ya ɗauke ne. Tun da ta fara magana Siyama ke ta kallon bakin ta, tana jin abun da take faɗa, a zuciyarta tana mamakin ashe dai yarinyar ta iya magana har haka. A fili kuwa ta ɗanyi alamar tausayi ta ce "Aiya to Allah ya bashi lafiya amma ai asibiti ya kamata kuje ko? Ta ce "Kawai fa ciwon ne kuma na ɗan lokaci ne, wani lokaci yana masa haka dama. Siyama dai ta amsa da to Allah ya sawaƙe. Haka Ta bar ɗakin bata jima ba sai gata da abun sha harda soyayyen nama da cincin. Siyama ta ce "Nagode. Har Jamila ta juya zata fita Siyama ta ce "Am Jamila minti ɗaya mana please? Jamila ta dawo ta zauna ba tare da tayi magana ba. Siyama ta kalleta sosai ganin ko Fati bata kai ba, sosai take tunanin anya kuwa wannan uwa ɗaya uba ɗaya suke da Jamilu da kuma Aida ɗin kuwa! Ita sai yanzu ma ta tsaya ta ƙarewa yarinyar kallo, gata dai masha Allah amma ta ɓata rayuwar ta. Siyama ta ce "Idan akwai kuɗi a gurin ki, please kije waje a kwai mai mashin da ya kawo ni, to ban fito da kuɗi ba kuma yana jira na. Da sauri ta miƙe tayi waje Siyama tabi bayan ta da kallo. Gashi dai bayan nata ma ba wani girma suka yi ba, domin irin dogwayen yaran nan ne, marasa jiki. Ajiyar zuciya ta sauke ta ɗauki nama ɗaya ta kai bakin ta. Lokaci ɗaya kuma abun da tazo yi ya dawo mata. Waya ta ɗauko ta buɗe data, sai ga sako daga email. Tana budewa taga daga campanin Baby and me ne, nan take ta shiga karantawa. Bayani ne akan sun shirya zasu fara aiki da ita, kuma ranar Laraba mai zuwa, kuma aikin na kwana uku ne, kwana ɗaya a kamfanin su dake Lagos, kwana biyun kuma duk a Maroco zasu yi, sosai take mamaki. A fili tace "Lallai baku da hankali wacce Siyama ce zata tafi har wani guri har kwana uku. Take taja wani gajeren tsaki tana ci gaba da kallon dokokin aikin nasu da suka turo mata, ita sosai take mamaki wai dama haka aikin Model ɗin yake ne. Ita fa a tunaninta kawai zaka je kamfane kayi musu hoton kayan da suke sai dawa sai kawai a sallame kane, amma shine harda kwana. Tana cikin haka taji sallamar Jamila ta ce mata "Anty yana ta zagi da kyar ya karɓi kuɗin ma fa" Siyama ta ce "Ai dole yayi faɗa yafa dade a gurin. Jamila dai bata ƙara cewa komai ba. Ganin haka yasa Siyama cewa "Dama kin ƙara masa kuɗi akan wanda yace ko? Ta girgiza kai! Siyama tace tom nawa kika basa tace "Yace wai ɗari huɗu shine na basa dubu daya ya bani ɗari biyar wai ɗari ladan jira. Ta faɗa tana miƙa mata canjin ɗari biyar ɗin. Siyama tace "Ai da kin bar masa gaba ɗaya kawai, to yanzu ai wannan naki ne ba nawa ba, sannan kina da account? Ta ɗaga kai. Siyama tace to bani sai na dawo miki da kuɗin ki harda kyautar da nayi niyar yi miki ko? Jamila ta girgiza kai ta ce "Wannan ma ai kuɗin ki ne, Anty Aida tace naki ne, shine yasa na baki chanji ɗin. Siyama da ta gano nufinta sai tayi murmushi tace "To kije na bar miki, kuma ki bani account ɗin naki kinji. Haka Jamila ta bata account ta tura mata dubu hamsin, tayi godiya ta bar cikin ɗakin. Sai a lokacin Siyama ta kalli uban kukadeden dake cikin account ɗinta. Ita fa sai ma yanzu ta tuna da cewar tun da aka fara wannan abun babu wanda ta bawa ko sisi, ita kanta bata samu natsuwar ci ba, kamata yayi ta fara siye bakin mutane da kuɗi, domin dai a kwai su, kuma sun fara zuwa ma kenan, domin ko ɗazu kuɗin da Baby and me suka rubuta na fement ɗin ranar ma kawai masu yawa ne. Da sallama Aida ta turo ƙofar ɗakin ta shigo hannunta rike da leda fara mai dan girma, sai Jamila da jamilu biye a bayanta kowa da reƙe da leda. Jamilu ya gaida Siyama sannan suka ajiye kayan suka fita. Aida cikin kulawa ta ce "Me ya faru naji muryarki alamar damuwa? Siyama dai sai bin Aida da kallo take bata ce komai ba har ta fara tsarguwa. Ta ce "Wai lafiya kuwa meye a jikin nawa? Ta faɗa tana bin jikinta da kallo. Siyama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Babu komai, ina so ne kawai na haɗu da wannan tsohon banzan Olusha, wallahi sai ya faɗa min a gidan oban waye mukayi haka da shi. Aida ta ce "Matsala ta dake kenan wallahi rashin nazari, ke yanzu idan aka ganki a gurin wannan mutumin me kike tunani zai faru, za'a ce kinje neman yafiya ko kinje ki masa wani abun. Kinga dan Allah bama wannan ba, yanzu wani kokari kikayi ta bangaren ki, yanzu fa kusan kwana goma fa. Bama wannan ba, kin duba sakon aikin naku ko? Kuma kinga lokaci kaɗan suka bayar hakan yasa Oga Fita ya yanke shawarar zuwa ya samu iyayanki da Umma. Domin nasan dai ke babu abun da kikayi. Siyama ta ce "Karki damu babu wanda zai zo gidanmu, nasan abun yi. Amma kuma Aida wannan aikin nasu kinji fa wai harda kwana, kuma harda barin ƙasa fa? Aida tayi dariya ta ce "To ke da meyi nufin ki, to ai ke dan ma a iya Afirka kika tsaya ne, bari ki fara aga aikin ki yayi kyau kigani har Jamani da Chaina da Faransa da Ingila za'a kiraki, yanzu Kinsan Adawiya ma tana Ingila kuwa? Siyama ta waro ido ta ce "Ingila dai? Aida tayi dariya tace "In sha Allah Siyama sai kin zama Model ɗin duniya ba iya Afirka ba. Siyama dai tayi shiru tana hango kanta tare da manyan Model irin su Razina da Alexander da Laila da kuma Oluwalu da kuma wanda take gani a matsayin madubi ko kuma tace yawan kallon aikinsa yasa ta fara sha'awar aikin Model, wanda take bin sa a duk wani kafa sadarwa da take yi Wato Adam Rezor. Sosai ta shiga tunanin Allah yasa watarana aiki ya haɗa ta da shi domin kuwa ita fan ɗin sa ce. Aida ta ce "Yanzu ga shawara? Kibi duk wani dankinki mai faɗa aji ki musu kyautar yanke talauci akan su zo su samu Umma su sanar da ita cewar Sana'ar Model sana'a ce kamar kowacce, kuma musulmai da Yahudawa da Kirista duk suna yi, kice su shawo kanta har ta yarda. Sosai Siyama tayi na'am da wannan shawarar haka ta kama hanyar gida tana tunanin rashin fadawa Aida halinda taga Jamila da jamilu a ciki, wata zuciyar kuma ta ce "To idan kuma ta sani fa! Daidai ta kusa fita Aida ta tsayar da ita tana zuwa ta ce "Kinga dan Allah maganar tafiya a ƙafa da wani boye-ɓoye duk ya ƙare yanzu. Acikin mutocinki wallahi sai kin ɗauki ɗaya kinje da ita gida. Wai ke an faɗa miki matsoraci na zama gwani ne, wa ya ce miki a haka zaki zama wata aba, kamata yayi ace izuwa yanzu sai abun da kika faɗa a gidan ku, amma kin tsaya kina tsoro. Siyama tayi murmushi tana jin wani ƙwarin gwuiwa amma gefe ɗaya tana cewa Aida baki san wacce Umma bane wallahi. Suna tsaye sai ga Jamila da jamilu sun fito da ledojin ɗazu sun bode wata arniyar mota sun zuba kayan a ciki. Aida ta ce "Waccer zaki ɗauka itace daidai ke. Siyama dai sai taji anya zata iya kuwa. Haka Aida tai mata dole har ta dauki motar ta fita da ita. Haka tana tafiya tana ƙara sakawa kanta ƙwarin gwuiwa, lokacin da ta shigo unguwar su ta New ariya dake Abuja, kasancewar unguwar dama ta yaku bayi ce, yasa duk inda ta wuce sai an ƙara kallonta, sosai ta dake tana kallon gabanta. Daidai tazo ta saitin gidan su Ibrahim zata wuce shi kuma ya fito, kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kai, shi kuma ya kafe ta da ido ganin ita ne yasa ya biyo bayanta da gudu. Ganin yana Binta yasa ta ƙara gudu hakan yasa mutane keta kauce mata, wasu na zagi wasu na Allah ya sawaƙe. Tana zuwa kofar gidan su ta sauƙa da kanta ta buɗe gidan kasancewar akwai gurin ajiye mota zai iya ɗaukar motoci uku, yasa ta shiga da motar, tana fitowa da niyar shiga gida sai taga Ibrahim yana haki na gudun da yayi. "Bani hanya na wuce? Ta faɗa tana harararsa. Ya ce "Siyama kashe ni kike son yi ne? Tsaya kiji abun da zance miki please? Lokaci ɗaya Siyama ta saki murmushi tunowa da tayi da shawarar ta ta ɗazu. Ta ce "Ina jinka" ya ce "Siyama dan Allah idan wasa kike min wallahi na horu haka, mutuwa kawai ya rage ban yi ba, wallahi ban san cewar san da nake miki har ya kai haka ba sai da kika fara min wannan wasan, dan Allah a tsayar da wasan haka, wallahi nayi alƙawarin idan har muka dawo kamar da zan zama miki duk abun da kike so. Kallonsa kawai take tana tunanin wai ita maima ya kaita fara wannan abun da wannan wawan ne. Ta ce "Yanzu da na baka miliyan biyar da mota da kuma na yarda na dawo soyayya da kai wanne ka tsaɓa? Lokaci ɗaya ya miƙe tsaye ya ce "Wallahi Siyama ke nake so ba kuɗin kiba, na zaɓeki, bana son komai naki sai ke ɗin. Lokaci ɗaya Siyama ta waro ido waje tace "Kai lallai na yarda kai wawa ne kuma dolo kamar yadda ake faɗa. To ni wallahi ko dubu biyar nafi so a kanka kaji ma da kyau kenan. Ta ce "Zan baka miliyan goma da mota kaima kaje ka gina kanka amma dan Allah ka barni nayi rayuwata please. Ibrahim ya ce "Wallahi Siyama ko duk abun da kika mallaka zaki bani akan na daina sonki ba zan iya ba, ni Ke ɗin nake so, kuma domin Allah nake sonki. Lokaci ɗaya Siyama ta zuba masa ido, sai kuma wani tunani ya ɗauketa na minti biyu, ta shiga tunanin ko dai wannan shine soyayyar gaskiya da ake cewa, ko dai ta yarda da shine in yaso ta gina shi sai kawai ta auresa ta dinga juyashi kamar ita ce matar, to ai kuma bata son sa, ina zata kai son mutumin da ta gama narkewa a cikin sa, duk da bai san tana yi ba, to amma idan ta yarda ta auri Ibrahim bata muzanta ba. Kuwa, kaman ita ta auri wawa. Lokaci ɗaya ta dawo tunaninta ta ce "Kai wawa ne, kaje gida ko ka samu abokinka kayi shawara da shi, ko kaje ka samu wannan tsohuwar kakar taka kayi shawara da ita, idan ka gama ina jiranka, domin dai na fahimci kai baka san me kake yi ba har yanzu. Tana faɗa ta kama hanyar gida ta barsa tsaye yana kallonta. Tana shiga cikin palon taga Umma da da Nasiru da Yaya Bala suna zaune sai Fati da take cin abinci. ****** *YAYA BALA* Lokaci da suka je ɗakin Siyama sai suka tarar bata nan hakan ya ƙara ɓata ran Umma sosai, ta shiga faɗin "Yanzu shi kenan Siyama tafi ƙarfinmu ko Bala, muna gidan nan da ita sai ta saka ƙafa ta fita nata gurin babu wanda ya sani ko, to wallahi na gaji ba zan iya ba, ka kira min ita yanzu duk inda take tazo gida ina son ganin ta. Sosai Umma tayi faɗa Yaya Bala dai sukai mata shiru domin shima harda shi take haɗawa. Haka Umma ta dawo Palo tana jiran a kira mata Siyama. Yaya Bala ya kalli Nasiru ya ce "Ɗauko wayarka ka kira ta" Nasiru ya shiga ɗaki da niyyar ɗaukar wayar, koda ya ɗauko baida kati a ciki, hakan yasa Yaya Bala yace a barta ai zata dawo duk ma inda taje. Yaya Bala ya kalli Umma cikin kwantar da murya ya ce "Umma magana nake so muyi akan karatun Nasiru da Siyama. Umma ta juyo ta kallesa har yanzu ranta a ɓace yake. Ta ce "Ita Siyama yanzu wani karatu kuma ya rage mata, yarinyar da tafi ƙarfin iyayenta, yarinyar da take da gaban kanta, kuma yanzu maganar aure zaka yi kawai ba karatu ba, ina so ka samu shi yaron da take tsayuwa da shi ya ruro idan da gaske yake kawai ayi mata aure mu huta, domin ni na gaji da wannan halin nata. Yaya Bala ya sauke ajiyar zuciya ya ce "To Umma shi kuma Nasiru fa, kinga yanzu suna shekarar karshe ne, kuma har yanzu hannunsa bai warke ba, gashi yanzu maganar kuɗi ne, bamu biya kudin jarabawar ba har yanzu kuma gashi ciwon nasa sai an ƙara komawa asibiti, ni dai nawa Alhamdu Lillah, shima sabo da yana da ƙanjiki ne ciwo ko yaya yake a jiki sai yaƙi warkewa. Umma tayi shiru tana tunanin lokacin da mahaifin su wato Al-Hasan shima haka yake da ƙanjiki koyaya yaji ciwo to ya fara ƙaruwa kenan ko yaƙi warkewa, sai sun sha fama sosai. Tabbas shi Nasiru da Siyama suka gado, itama haka ciwo yake mata ya bata wahala sosai. Umma ta kalli Yaya Bala ta ce "To ko shi Nasiru zai bar karatun ne har bayan shekara idan ya warke, kaga sai muji da kuɗin maganin ko? Domin kaga yanzu idan ba hakan a kayi ba zamu shiga cikin matsala. Yaya Bala ya ce "A'a fa Umma yanzu maganar barin karatu har sai wata shekarar ba dabara bace, domin idan shekarar ta dawo sai mun biya komai da muka biya a baya, kuma shi kansa ba zai ji daɗin karatun ba. Umma tayi shiru cen ta ce "To ko zaka je gurin masu gidan naku su bada kuɗin hayar wannan shekarar ne idan yaso kaga ko shekarar ta ƙare sun biya kenan ko? Yaya Bala yayi murmushi ya ce "Umma ko wata biyar bai yi bafa da suka bamu na waccer shekarar, kuma shima da yaya suka haɗa mana, yanzu kuwa muna zuwa zasu ce ai shekarar bata yi ba, kawai dai Umma bari na kira shi Nasiru ɗin muji ta bakin sa. Daga nan yaya Bala ya shiga kiran Nasiru sai gashi ya fito rike da waya a hannu, hannun ciwon nasa ya kumbura sosai babu ko kyawun gani. Bayan ya zauna Umma tace ya tashi ya kira mata Fati. Bayan sun zauna ta mayar musu da duk yanda sukayi, Nasiru ya ɗago da sauri jin abun da ake ciki. Ya ce "Yaya shekara mai zuwa fa cikin jiniyoyina fa zan shiga duk abokaina lokacin sun tafi sun barni, gaskiya Yaya a'a ba zan iya jira har wata shekara ba. Umma ta ce "To da wani hannun zaka yi karatun da rubutun ana magana kana faɗin ba zaka iya ba kamar wani karamin yaro, ko baka fahimci matsalar da ake ciki bane, duk akan maganar kuɗi ne, yanzu ma asibiti za'a koma a kan wannan hannun naka amma kazo kana abu kamar karamin yaro. Nasiru dai ya cuno baki ya shiga haɗa rai. Fati dai tayi shiru tana sauraronsu. Bayan kamar minti biyu Umma ta ce "To ko za'a saka wancen gidan a kasuwa ne, idan yaso sauran kudin sai ka fara wani kasuwancin da shi, tunda kaga aikinku ba kullum ake samu ba ko? Da sauri Yaya Bala ya ce "No a'a Umma ba zamu sayar da abun da muka mallaka na gado ba. Ya ce "Umma idan muka sayar da gidan zamu zo muyi da na sani, domin gidan Nasiru nake so idan Allah ya kai mu lokacin auransa sai kawai a gyara ya shiga. Cikin faɗa Umma ta ce "To Allah zai hore muku in sha Allah kafin lokacin ku siya wani, yanzu yaya kake so ayi, wannan dai gida naku ne, bayan shi baku da wani abu da za'a sayar asamu lafiya da kuma ci gaban karatun ku, to yanzu ni dai na gama magana aje a sayar Allah zai hore, lokacin da ka sayi wannan gidan kasan zaka samu kuɗin ne, Allah ne yaso kuma ya nufa har ka siya, sabo da haka ku dinga kyautata zato mai kyau ga ubangijinku shine ke yi a lokacin da babu mai baka. Sosai Umma ta shiga faɗa cikin na nasiha hardai suka yarda akan za'a sayar. Bayan an amince ne yaya Bala ya ce "To Umma yanzu mu sanarwa da Kawu Inuwa da Baba (wato Husaini ƙanin mahaifinsu shi suke cewa Baba) Umma ta ce "Eh ai dole zasu sani. Fati dai tuni ta tashi ta shiga cikin gurin Binta da ta bari tana ƙarasa abincin nasu, ganin bata gama bane yasa ta ɗauki kwano ta ɗebo kaɗan domin yunwa take ji. Haka ta fito palon

Chapter 7 of 11