tasan ko giyar wake tashs ba zata iya duk wadannan abubuwan ba. Ita yanzu Babbar damuwar ta ma ta ƙarass gidan ko yankanta ne Yaya Bala yayi kowa ya huta. A haka Oga Fita ya kaita har ƙofar anguwarsu domin bata yadda yaga gidan su ba, Kallonta yayi ya sake cewa "Dubi unguwar da kike dan Allah Siyama, ki tsaya dai kiyi tunani. Yana faɗa ya mika mata wayar ta da take a kashe tun lokacin da ta isa gurin taron.
A hankali ta tura ɗan ƙaramin ƙofar gin nasu mai ɗauke da wani tsohon get ɗan ƙarami ta shiga, ta kalli gurin da yake ajiye tsohuwar Motar sa amma bata ganta a gurin ba, lokaci ɗaya gabanta ya fadi, basu dawo ba kenan, ta ci gaba da tafiya tana jin gabanta na ƙara faɗuwa. Kafin ta ƙarasa cikin gidan taji ana kiran sunanta. A ɗan tsorace ta juyo jin muryar Ibrahim, ai kuwa dai shine, yau ma dai kamar jiya ko wanka bai yi ba, waɗannan kayan ne dai na aikin sa, dukda kuwa yace yau basu da aiki domin yau Lahadi ranar hutu ce, amma gashi da kayan aiki, take ranta ya ɓaci. Ya ce "Zuwa na kenan sai kuma na hango ki zaki shiga gida shine na kira ki". Ya faɗa yana murmushi yana binta da kallo ganin yanda yau ta rufe gashin kanta, ga kuma wani irin kyau da tai masa, ga doguwar rigar ta tasa bai taba ganin ta da ita ba. Sosai asalin kyawun Siyama ya baiyana wanda shi kansa sai da ya ƙara tabbatar da cewar gaskiya Siyama matar manya ce, domin shi wallhi sai yaga yau ma kamar ba zai ma iya kallon cikin idon ta ba tsabar kwarjini. Sai kawai ya tafi tunanin shin me Siyama ta gani a tare da shi tace tana sonsa, gashi baƙi, talaka ƙazami,mara wayo kamar yadda ake cewa, anya kuwa bai yaudari kansa ba, to dama yana da kuɗi ne sai yace sabo da kuɗin sa ta ke sonsa. Ta ce "I B (Kasancewar wani lokaci bata ce masa Ibrahim sai tace IB)jiya fa na ƙara tabbatar maka da cewar ka daina zuwa idan baka yi wanka ba, kuma gashi ka ƙara zuwa haka" Ta faɗa da ɗan damuwa a muryarta. Wani suna da ita ta saka masa wanda yanzu kusan duk unguwar haka suke kiran sa da shi, duk lokacin da ta kira sa da I B wani irin farin ciki yake ji. Ya ce "Wallhi aikin motar jiya ne, sai yau muka ƙara sa ta, ina gida oga ya kirani wai dan Allah muzo mu ƙarasa masa yau zai tafi da ita ne, to shine fa naga yauma dare yayi, kin ga kuma idan takwas ta wuce bazan samu damar ganin ki ba shine yasa na ce ko ganin ki nayi. Ya ƙarasa yana ƙoƙarin ganin ta ina suka dace da Siyama. Ta ce "To sannu da aiki, yau dai an gama da wannan motar kowa sai ya huta ko? "Hamm sosai fa, ai gobe idan na fara hutu sai rana ta fito. Ya faɗa yana dariya. Kafin tayi magana wayarsa ta fara ƙara. Yana dagawa ya ce "Ina zuwa gani nan. Siyama ta kalli wayar hannunsa, a fili ta ce "Wannan wayar dai kai jin daɗin ta kake yi ko? Ibrahim ya ce "To yaya zan yi ko bana jin daɗin ta, bari dai kuɗi su shigo in sha Allah zan samu ƴar babba nima na siya ko fecbook da TikTok ɗin nan da ake faɗa nima na fara. Ya na faɗa ya miƙa mata ledar hannunsa yana fadin sai da safe. Karmar ta ce a'a, amma ta amsa tana masa sai da safe ganin yana ta sauri. Ya juya yana ɗaga mata hannu itama haka har ya tafi. Sai da taga ya fita kafin ta sauke ajiyar zuciya ta nufi ciki.
Da sallama ta shiga cikin falon, sai dai bata ga kowa ba, hakan yasa ta fara sanɗawa tana yin hanyar shiga ɗakin su. Har ta shiga babu wanda ya ganta. Tana juyawa ta ga Fati a gefen gado tayi kuka har idanuwanta sun yi jaa! Tana shiga itama Fati ta ɗago ai kuwa suna haɗa ido Fati ta ƙara fashewa da wani sabon kuka tana faɗin Aunty Zainab ta ta ta rasu! Cikin wani irin shok da faɗuwar gaba Siyama ta saki ledar hannunta tana tambayar ta wacce anty Zainab ɗin, mutuwa kamar yaya me take nufi? Fati ta ce "A hanyar dawowarsu daga gurin gasar ne sukayi hatsari shine wai ita ta mutu, yaya Bala kuma yana kwance rai a hanun Allah ga Nasiru shima ya samu karaya a kafaɗa da hannun". Siyama ta kurma wani uban ihu tana kiran sunan Yaya Bala da anty Zainab. Tashi tayi ta nufi sashen Umma tana tafiya tana kuka koda taje sai ta tarar da ƙofar Umma ɗin a rufe alamar bata gidan. Da sauri ta koma ɗaki tana tambayar fati wani asibiti suka tafi. Nan ta sanar mata da yadda itama taji wai kusa da gurin da aka yi taron ne domin waɗan da suka kira number Umma sune suka fadi sunan asibitin. Haka ta shirya ta saka hijjab ɗin ta ta fita, bayan ta sanar da Fati cewar ta rufe gidan.
Ko da ta fita wani asibiti da ke kusa da gurin da a kayi taron ta fara zuwa, ai kuwa tana ta tambaya aka tabbatar mata da cewar gurin ne. Koda taje asibitin ta tarar da Umma nata kuka domin da gaske anty Zainab ta rasu, sai yaya Bala da har zuwa yanzu bai farka ba. Umma tana ganin Siyama ta ƙara fashewa da kuka. Haka Siyama tazo suka zauna sai sharar kuka suke yi A nan asibitin suka kwana sai washegari Umma ta tafi gida ta bar Siyama a gurin, kuma har lokacin babu wanda ya farka.
Tana zaune a gurin kafin Umma ta dawo ita kuma ta ciro wayar ta. Ganin babu abun da take yi ne yasa ta kunna Data. Lokaci ɗaya ta dinga ganin saƙonni suna shigowa tako ta ina fecbook da TikTok da Whasopp. Sosai hankalin ta ya tafi kan wayar har bata san lokacin da likitan ya shigo ba. Har sallama yayi amma bata ko sani ba.tana kallon daga iya jiya zuwa yau ta samu mabiya a TikTok da fecbook na ban mamaki har yanzu ma ƙaruwa suke yi. Tana shiga Whasopp taga group ɗin su na ƴan team ɗin su, sai posting hoton ta na jiya a keyi, ga sitatus ɗin mutane ma, nan take taga message ɗin Oga Fita tana shiga tagan su da yawa, ta fara buɗe na farko taga saƙon magana ne yana cewa ta ɗora wannan bidiyo ɗin da hotuna a shafin ta na TikTok da fecbook tayi jawabi domin har mutane sun fara buɗe account da sunanta, duk da cewar dama tana da nata mai suna Siyam Olosha wanda babu wanda yasan ta da shi a gidan su. Ai kuwa nan take ta fara posting, kafin ta yi na biyu ta fara samun like da comments, bata da lokacin dubawa hakan yasa tana gamawa da fecbook ta koma TikTok, shima bayan ta gama sai ta fara shiga comments tana kallon masu yabo da zagi. Likitan ne ya ƙara faɗin "Madam kina tare da ni kuwa?" Sai a lokacin ta jisa. Da sauri ta ɗago a ɗan tsorace ta ce "Yes ina tare da kai". Ya ce "Ina ta magana kin mai da hankalin ki izuwa waya, alhalin zaman jinya kike yi. Kafin tayi magana taji kira na shigowa wayar ta amma ta share ta ce "Eh ina yin wani abu ne" Sosai likitan ya kafe ta da ido kamar dai itace yarinyar da tazo ta biyu a gasar jiya, kamar kuma ba ita ba, domin daga jiya zuwa yau indai kana yin media to zaka ci karo da hotunan ta. Siyama da ta lura da irin kallon da yake mata sai ta ce "Yanzu me ake buƙata?" Cikin diriricewa ya ce "Amm umm dama ɗaya ne ya farka daga cikinsu, kuma yana buƙatar abinci mai ruwa-ruwa kafin mu ƙara masa allura. Siyama ta kai kallonta izuwa gurin ai kuwa suka haɗa ido da Nasiru da ya buɗe ido yana kallon ta tun ɗazu ita bata sani ba. Ta ce "Sannu yaya Nass ya jikin? Me zaka ci? Ina yake maka ciwo? Nasiru ya lumshi ido ya buɗe yana jin jikinsa ya masa nauyi. Sallama suka ji anyi Umma da wasu daga cikin kawunansu suna biye da ita, sai Fati da ta ɗauko kwanukan abinci. Ganin haka likitan fita yana satar kallon Siyama. Daidai lokacin shima yaya Bala ya buɗe ido yana bin ɗakin da kallo. A hankali ya ce "Ina Zainab?" Kawunsu ƙanin mahaifinsu mai suna Kawu Inuwa ɗan bala'i ne na gaske, yana da faɗa sosai domin duk faɗan Umma tana tsoran sa, shine ke bin Gambon Hassan da Hussaini duk da ita Gambon Allah yayi mata rasuwa, shima Al-Hasan ɗin wato mahaifin su Siyama shima ya rasu, yanzu daga Kawu Inuwa ɗin sai Baba Husaini ɗin.
ya ce "Ka natsu tukunna Bala yanzu ta lafiyar ka ake yi". Ganin Bala yaƙi tsayawa ne yasa suka kira likita, nan ya sanar musu cewar babu abun da ke damun sa, kawai karya ce a hannun kawai, kuma an ɗaure. Shima ɗayan karaya ce hannu da ƙafaɗa shima an ɗaure. Sai da aka zuba musu abinci sukaci ƙadan kafin aka ƙara musu allura likitan yace zuwa gobe in sha Allah za'a sallamesu, sai suje su cigaba da jinyar hannunsu a gida. Sai da barci ya ɗauke su kafin kawu Inuwa da sauran suka koma gida aka bar Umma da Siyama da Fati.
Umma ta kalli Siyama ta ce "Jiya bayan fitar su Yayanki ina kika je? Umma tayi tambayar ne badan tasan komai ba, domin ita bata ko kalli shirin ba kasancewar babu wuta. Siyama ta ɗago daga chatting ɗin da take yi da Aida ta kalli Umma. Umma cikin faɗa ta ce "Ina miki magana kina danna waya tsabar raini ko Siyama" Ai da sauri ta kashe wayar tana dawo da hankalin ta ga Umma. Umma ta sake faɗin "Ina kika je baki dawo bar har wannan abun ya faru tun safe? Siyama ta kalli Fati taga itama ita take kallo sai kawai ta ce "Gurin taron nima naje". Umma da dama tasan dole gurin taje, domin yadda Siyama ta ƙwallafa wannan gasar a ranta tasan ko masu shiga gasar ƙare kenan. Umma ta ce "Amma ai Yayanki ya hana ki ko, kuma nima na hana ki, amma kin nuna mana cewar bamu isa ba ko? Siyama kibi duniya a hankali, yanzu gashi kina kallo yadda ake mutuwa cikin rashin shiri, yanzu da nice na mutu ina fishi da ke Siyama yaya zaki ji! Lokaci ɗaya gaban siyama ya faɗi jin kalmar mutuwa, ga kuma tunowa da yanzu fa da gaske Anty Zainab ta rasu ko. Umma ta ci gaba da cewa "Ki duba yadda yake fadi tashi akan mu, shi kansa ba wani samun kirki yake yi ba, amma haka yake kokari damu, yanzu ko wannan ba zaki duba ba ki riƙe maraicin kiba Siyama, yanzu ba kya tsoron wani abu ya dameki a hanya da kika tafi har gurin ke ɗaya bayan Uwar da ta haife ki tace karki je?. Daidai lokacin Siyama taji ƙarar shigowar message a wayarta hakan yasa ta kalli wayar ba tare da Umma ta kula ba, shigar kuɗi ne cikin account ɗin ta wanda tun ɗazu take jin shigar su. Haka dai Umma tai mata faɗa sosai wanda Fati dake kusa da ita tasha kuka ita kuwa rabin hankalin ta naga wayar ta ne. Haka dai Bayan farkawar su Nasiru Umma da Fati suka tafi gida. Har lokacin yaya Bala bai ko yi wa Siyama magana ba, yakan dai saci kallonta lokacin da take chatting yana ganin irin dariyar da take yi ko tayi murmushi. Sosai ya shiga tunanin meye laifin sa a riƙon da yayiwa Siyama, sannan tayaya har ta shiga team har ta samu damar halartar gasar batare da ta bar wata alama ko ɗaya da zai gane ba, ta yaya duk irin tsaron da ya saka mata, sosai wannan tunanin ke masa yawo akai.
Chatting suke yi a group ɗin su wanda ake sanar da ita dole sai tazo gurin aikin su wato shagonsu damin sa hannun akan komai nata, kuma ta warewa team nasu, kuma ga wasu manyan mutane dake son ganin ta. Ta ce duk Aida ta wakilceta amma Oga Fita yace, awa ɗaya aka bata ta shirya tazo, kuma ta tabbatar ta sha wanka domin ba ƙananan mutane bane zasu zanta da ita. Haka tace to zata zo.tana ɗago kai taga Yaya Bala yana kallon ta hawaye na zubo masa ta kumatu, ta kashe datar tana kallon sa, taje kusa da shi tana share hawayen ta kamo hannunsa, lokaci ɗaya ya dawo daga tunanin da yake ya riƙe mata hannun yana faɗin "Zainab baki mutu ba ko, kin dawo gare ni ko. Yana faɗa ya haɗa ido da Siyama ya sakar mata hannu ya juya kai gefe. Sai a lokacin Siyama ta ce "Dan Allah yaya kayi haƙu" Da sauri ya daga mata hannunsa mara ciwon ya juya baya. Siyama ta fashe da kuka tana toshe baki. Ta kalli Nasiru ta ce "Dan Allah yaya Nasiru" shima ya dakatar da ita. Ta juya ta fita daga ɗakin ta shiga Gurin likitan ta ce "Yanzu babu wani abu da ake binmu ko? likitan ya ce ba komai, sai maganin da zaki siya idan sun koma gida su dinga sha, amma sai zaku tafi za'a rubuta muku. Ta ce "Suma rubuta tun yanzu. Ai kuwa take ta fidda kuɗin maganin dama ita ce ta biya na komai, sannan ta kama hanyar gida. Ganin tana tafiya ana kallonta ne yasa ta samu wani guri a gefen asibitin ta tsaya ta kira Aida ta ce tazo da Mota yanzu ta dauke ta, bayan tai mata kwatancen gurin da take. Ai kuwa bata daɗe sosai ba sai ga ta nan da Mota, tana zuwa ta buɗe mata gidan gaba ta shiga. Aida ta kalleta ta ce "Ina muka nufa? Siyama ta kwantar da kanta a kujerar matotar tana tuna faɗan da Umma tai mata, ta ce "Muje gidan ki" Aida ta juyo ta kalleta bata ce komai ba har suka isa gidan Aida ɗin da ta kama take zaune ita da ƙanwarta da ƙanin ta Jamila da jamilu. Kana shiga gidan Aida kasan ka shigo gidan Model, hotunan ta ne ta ko'ina a cikin palon, haka cikin ɗakinta, hotuna dai irin na Model wasu doguwar riga wasu iya kayan barci.
Ganin Siyamar ta kwanta a kan gado ne yasa Aida faɗin "Amma kinsan awa ɗaya Oga Fita ya baki ko? Siyama ta ce "Ban san kayan da zan sa ba, kuma ni barci naje ji wallahi na gaji tun jiya ban huta ba, kawai kije a maimako na please. Siyama ta faɗa Domin tasan tabbas Aida ita ce komai nata, zata iya rantse wa da Allah akan cewar duk wani abu nata Aida ta fita sanin sa, haka zaluka wasu abubuwan ma duk Aida ɗin ce ke mata su, haka ko a team ɗin su idan kaji Aida na faɗa to an taɓa Siyam ne. Aida ta ce "To dama waye zai tsaya jiran ki yaji kunya, ai daga yau zuwa sati daya duk na tana di kayan da zaki dinga sakawa, ai ke sai dai a barki da halinki, Malama ki tashi ki shiga wanka ko wankan ma sai na miki ne? Ta faɗa tana sauko da wata akwati mai kama da Zakara. Take ta buɗe shi ta ɗauko wata doguwar riga jaa, mai adon duwatsu sai ɗaukar ido take yi, gefe ɗaya kuma ga taƙalmi da jaka duk irin ruwan riga, ga wata sarƙa mai tafiya da imanin wanda yasan darajar sa, kana ganin kayan kasan a haka suke zuwa a cikin wannan akwatin. Siyam na ganin haka ta shige toilet ta faɗa wanka tana tuno yadda suka yi da yaya Bala ɗazu. Koda ta fito ta tarar da matar da take musu kwalliya tana jiranta, ai kuwa nan aka fara mata, tana gamawa ta saka kayan sannan Aida tai musu hotuna, nan take suka dora a Fage ɗin su. Sai da suka gama sannan suka fita izuwa gurin aikin su. Ita dai Siyama duk rabin hankalin ta na ga asibiti, ga shi bata sani ba ko anyi jana izar anty Zainab ko sai yaya Bala ya tashi, ko dai ɗazu da ƙanin babansu ya tafi aka je akayi, sai take ganin kamar bai dace ta bar gida yanzu ba, amma wata zuciyar take sanar da ita cewar ai yanzu zata dawo. A haka suka ƙaraso Team ɗin nasu....📝
(Muna tare daku kuwa masoya? Kuzo mubi Siyama a hankali muga ina take son zuwa)
Love all
One love
Comments
And shering
Love my fan's
By S-Reza write ✍️
[7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*
_By S-Reza ✍️_
*FCW*
*My WhatsApp channel*
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
*PAGE 4️⃣*
Shiru Siyama tayi a cikin motar tana kallon shigar da tayi. A hankali Aida ta ce "Lafiya dai ko?" Siyama ta sauke ajiyar zuciya ta kawar da kai gefe, ita da kanta tasan shigar da tayi sam bai dace da itaba. Ta ce "Lafiya ina ɗan wani tunani ne" Ka she motar Aida tayi ta juyo ta kalleta da kyau kafin ta fara bata baki har dai Siyama ta sauƙo. Duk da hakan wata zuciyar na sanar da ita bata kyauta ba, amma ta danne suka shiga cikin group din da tun daga bakin get zaka fara cikin karo da manyan motoci na Medels ɗin dake gurin da kuma mutanen da aka ce suna san ganin ta.
***
*Yaya Bala*
Cikin tsananin ɓacin ran da ya sarƙe masa zuciya yake tuƙa motar kamar zai tashi sama, Anty Zainab kuwa sai kuka take duk ta rikice da ganin wannan sabon al'amarin. Sosai wata zuciyar tata ke ƙoƙarin ƙin yarda da cewar Siyamarsu ce haka. Shi kuwa Nasiru gaba ɗaya ma shi halin da Yaya Bala ɗin ya shiga ne yafi tashar masa da hankali gashi sai gudu yake yaƙi yayi magana da kowa. Daidai lokacin aka kirasa a waya ai kuwa take ya kai hannu da niyyar ɗauka kuma gashi sun iso kan jakshon, bai ma san sun iso ba hakan yaba wata babbar motar damar hawa kansu, lokaci ɗaya motar ta komatse ta baya, yayin da itama babbar motar ta dungura gefe ɗaya. Lokacin da mutane suka iso gurin Nasiru ne kawai ke motsi, kafin minti biyar har motar agaji ta iso aka kaisu asibiti mafi kusa da gurin. Take likitoci suka tabbatar da mutuwar macen cikin su, sannan suka naimi da a sanar da wani nasu. Cikin ikon Allah kuma waya biyu aka samu ta Yaya Bala da Nasiru, sai dai wayar Nasiru ta fashe hakan yasa aka duba number da ya kira karshe. Number yaran wajan aikin su ne wanda ya kira lokacin da suke tafiyar, koda aka kira aka sanar dasu shine suka zo gurin. Shine suma suka kira number mamar su suka sanar da ita. Koda Umma ta ƙaraso sai ta cika asibitin da kuka, tana kiran sunan yaran nata, sosai ta fita a haiyacinta sai faɗin dama ta hana su zuwa wannan gurin amma suka ce sai sunje yanzu ga abun da ya sake su, sosai take ta zaro magana harma bata san tana yi ba. Sai da likitoci suka tabbatar mata da cewar suna lafiya kafin ta ɗan rage kukan, amma duk da haka bata daina faɗa ba. Ganin halin da take ciki ne yasa likitan bai mata maganar macen da ta mutu ba, sai ma tabbayarta ko zata kira mahaifinsu ko kuma wani Namijin. Jin haka yasa ta bada number Kawu Inuwa wanda aka kirasa shima yazo cikin daren. Nan likitan ya sanar da shi cewar a kwai mace ɗaya a cikin su kuma Allah yayi mata rasuwa. Haka suka je ya ganta sannan ya dawo ya sanarwa da Umma wacce jin haka yasa ta ƙara dawowa da sabon faɗa. "Sai da nace masa kar ya je da ita amma yace yaji ya gani, yanzu dan Allah mai zai cewa iyayenta, wannan wacce irin masifa ce, wannan abun na arna da gaba ɗaya ma saɓon Allah ne, abun da babu wani ɗan musulmi kuma ɗan kirki da ya fito daga gidan mutunci zai bar ƴarsa tayi, shine har kuke ɗaukar iyalai kuje kallo to ga abun da ya jawo muku, ni dai sam ban ji daɗin wannan abun ba, Allah ma dai ya tarwatsa taron mutanen da suka ƙirƙiro wannan kafurcin Allah ya isa ban yafe ba. Sosai Umma take kuka tana face majina, sosai mutuwar Anty Zainab ya taɓa ta, samun sirika irin Zainab a wannan lokacin sai an tona, yarin ya ce mai kawai ci ga na tsuwa, duk da irin faɗan da Umma keda ita amma hakan baisa kana yawan jin kansu ba, gasu a gida ɗaya.
Haka ƙanin Kawu Inuwa ya fita da gawar Anty zaibab ɗin, basu Kaita gida ba sai suka wuce da ita babban masallacin domin tayi kwanan kaso a gurin. Acikin daren aka fara sanar da dangin ta da sauran abokon zama. Tun a daren likitan ya tabbatar da cewar karaya kawai suka samu ɗaya guri biyu ɗaya kuma guri ɗaya, sai kuma ɗan buguwa da suka samu amma ina sha Allah zuwa safiya zasu farka. Yana cikin barci yake mafarkin matarsa na cikin matsanancin hali, lokaci ɗaya ya buɗe ido da sauri yana bin gurin da aka kwantar da shi da kallo, ganin Umma da Kawu Inuwa ne yasa shi tambayar ina matarsa. Tun da yaga sun fara ce masa ya kwantar da hankalin da ya tabbatar da cewar ba lafiya ba, yana ƙoƙarin rufe ido ya haɗa ido da Siyama, wacce take zaune ta kusa da hannun sa mai karayar. Kallon ta yayi yaga komai na dawo masa. Haka dai bai ƙara cewa komai ba har suka ci abincin da aka kawo musu, sannan barci ya ƙara ɗauke sa bayan an masa allura. Lokacin da ya ƙara buɗe ido sai ya sauƙe a kanta ita kaɗai zaune a ɗakin tana kallon waya tana dariya. Sosai ya dade yana kallonta yana ƙoƙarin haɗa fuskar wannan ta gaban nasa da kuma wacce yaji jiya ana kira da Siyam Olosha. Sosai ya tabbatar da basu da wani banbanci sai dai wannan da take zaune a gaban sa yanzu hijabi ne a jikin ta waccer kuwa marabanta da tsirara babu nisa. A hankali yake lumshe ido yana budewa yana tunanin Allah yasa matarsa lafiya take. Yana cikin haka likitan ya shigo hakan yasa ya lumshe ido kamar mai barci. Yana ji likitan yana mata magana amma bata ji ba. Har sai da ya sanar da ita Nasiru ya tashi kuma abinci zasu ci kafin anjima. Likitan na fita ta shima ya sake buɗe ido.Yana farkawa itama tana satar kallonsa, ganin yana kallonta ne yasa ta fara masa sannu tana tambayar ina ke masa ciwo. Shi kuwa wani irin haushin ta da yake jine yasa ya juya mata baya yana ɗaga mata hannu yana kawar da kai gefe, sai yaga ta fashe da kuka tana wa Nasiru magana sai kuma yaji tabar dakin da gudu.
Bangaren su kawo Inuwa kuwa washegari aka shirya gawar Anty Zainab ƴan uwanta sukai mata addu'a harda Umma da itama ta zauna a gurin, nan dai ƴan uwanta su kai mata rakiya izuwa gidan ta na gaskiya. Lokacin da Kawu Inuwa ke sanar masa da rasuwar matar tasa sai kawai ya saki murmushi haɗi da hawaye duk lokaci ɗaya, dama ya ji a jikinsa hakan yasa ya kasa yin wani yunguri, amma zuciyarsa wani irin zafi take masa ga shi abun takaici