ta shiga ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa hakan yasa ta sakar masa cizo amma ko a jikinsa, sai ma ƙara matseta da yake yi yana ƙara tabbatar mata da cewar yana sonta. A haka Haladu da Nana da Hajja suka zo suka samesu, Siyama tayi-tayi har ta haƙura ta fara kuka domin ta matsu sosai. Shi kuwa wani irin sanyi da natsuwar zuciya ya samu kansa a ciki har yake nema ya shagala barci ya ɗauke sa. Yana jin an shigo ya saketa yana miƙewa. Ita kuwa da kuka ya cika mata baki ta fashe da shi tana gyara rigar ta da ta tattare. Hajja ta ce "Ibrahim ka fara hauka ne, meye wannan ɗin kayi, ko ka zama mahaukaci ne. Ta faɗa tana kallon Siyama da ta miƙe tsaye tana gyare-gyare. Ta juyo ta kalli Ibrahim ya sakar mata murmushi ta ce "Zaka san ka haɗa jiki dani, ba dai kai wawa ɗan iska dole shege ba ka jira dawowa ta" ya ce "Dan Allah ki dawo da wuri please Siyamata" ya faɗa da dan ƙarfi domin har ta bar gidan.
Suna fita Hajja ta ɗauke shi da mari ta ƙara masa tana faɗin "Yanzu kasan me zata aikata mana ne, me yasa baka da tunanine Ibrahim yaushe ka zama ɗan iska a cikin gida zaka kama musu yarinya haka ake so ɗin" sosai Hajja tai masa kace-kace, kuma tace karya kuskura ya leƙa ko waje. Tana gamawa ta kwashe kuɗin tana nunawa Haladu da yake ta kallonsu tun da yazo. Hajja ta ce "Haladu yanzu nawa kenan wannan kuɗin. Ya ce "Hajja guda biyar ne sun kama dubu ɗari biyar kenan" Hajja ta waro ido tana kama baki ta ce "Ɗari biyar dai Haladu? Haladu yayi dariya ya ce "Allah ne ya baku" "Yanzu zamu iya taɓawa nifa ina tsoro karta dawo tace a bata kayanta? Kafin Haladu yayi magana Ibrahim ya wafce kuɗin ya saka a ƙarƙashin katifarsa ya ce "Babu wanda zai taɓa mata kuɗi mayar mata da shi za'ayi. Haladu ya ce "To wallahi baka isa ba, ina ruwanka kai ne ka bayar, kai dai kaje da rashin zuciyarka yarinya ta zageka ta zagi uwarka a gaban ka, ai ni wallahi ka bagama bani mamaki. Ibrahim ya ce "To ko kaima zaka zaga ne ka gani? Haladu ya ce "Ba zan zaga ba domin nasan illar hakan amma kuɗi ne dai sai ka bayar anbawa masu hankali su hajja. Ibrahim yace "To zoka ƙwata. Haladu ya ce "Yanzu kuwa" Haka suka shiga dambe har sai da Haladu ya ciro kuɗin ya mikawa su hajja raba ɗaya ya ce zai ajiye musu sauran sabo da kar ya zo ya kwashe. Hajja dai sai godiya take duk da har yanzu tana tsoro, ita dai Nana har ta fara lissafin abubuwan siya.
******
*AIDA"
Sai da ta tabbatar da duk wata shedar ta da yake nuna cewar Adawiya da Badawiya ne suka saka wannan tsohon banzan Olusha yayi wannan aikin hakan yasa ta samu Oga Fita ta sanar masa, shima yayi mamaki ai kuwa nan take ya haɗa mintin aka taru ya tambayi Badau kasancewar ita Adawiya bata nan. Farko tayi musu amma ganin shedar da Aida ta kawo yasa ta tabbatar. Nan take Oga Fita ya wanketa tass akan yanzu gashi sun jawo mata zagi agurin iyayenta da jama'ar gari. Sannan yace "Zasu yi vedio su ƙaryata kansu. Nan fa Badawiya tace ba zata iya ba. Haka zaman ya watse akan ita dai wallahi ba zata yi video ba. Ai lukacin da Adawiya ta samu labari daga gurin Badawiya, lokacin har ta sa hannu a VIP London, dama tana neman yadda za'ayi ta bar team ɗin su na Farin gida, kuma dama sunyi magana da shugaban Magazing akan zata mayar da Badau taci gaba da aiki a tare da su a matsayin ta, ita ta samu wani aikin. Alesx da haushin ta yake ji tun lokacin da yayi mata maganar Aikin karshen shekara tace ba zata yi ba. Bai nuna mata komai ba yace ta kawo hotunan ƴar uwar tata.
Sosai Adawiya ta kira Oga Fita suka yi kace-kace har tana ƙara sanar da shi cewar zata ƙara yin wani sabon Video ɗin akan shi Oga Fita ɗin yana kwanciya ne da duk members ɗin team ɗin su kafin ya ɗauke su harda ita Siyama ɗin, kuma harda ita kanta Adawiya ɗin. Sosai Oga Fita ya shiga tashin hankali domin shi ba rabuwar da sukayi da su bane matsalar ko faɗin cewar zata ce yana kwanciya da su ba, a'a shi abu biyu yake tsoro, na ɗaya Siyama da iyayenta, domin ya tsorata da Umma da ya ganta. Na biyu kuma jin cewar Adawiya ta shiga VIP London, sosai yake mamaki da tsoro. Haka dai a ka rabu tsakanin team da Adawiya da Badawiya. Haka kuwa ta tattara komai nasu sai England London tarar da ita a cen.
Hakan yasa sunan Aida ya shiga cikin waɗanda zasu yi tala ga Baby and me. Yanzu haka ita da Nusee da Sarah ne zasu fara zuwa gurin domin saka hannu kuma a ƙara koya musu duk wasu abubuwan da zasu yi. Ganin har lokacin da aka bawa Siyama ya wuce ne yasa suka ce kawai a fara aikin da sauran Medels ɗin, idan yaso duk lokacin da ita Siyama ɗin ta shirya zasu yi aiki da ita. Akan haka aka tsaya, Aida tana ta kiran Siyama domin ta sanar da ita amma bata amsawa, sai kawai ta tura mata message. Da sauri ta fito Palo tana kallon Jamila da ta fito daga kicin riƙe da kofin shayi tana sha. "Kar dai kice min baki gama girkin ba? Jamila tayi dariya ta ce "Harma munci namu ke kawai ya rage" Ta ce "Ina Jamilu? "Ya shiga wanka tun ɗazu nima shi nake jira" Da mamaki Aida ta ce "Ina zaku je da kike jiransa? Jamila ta buɗe mata kanta ba tare da tace komai ba. Sai Aida ta ce "Auf sorry ni bama Na manta munyi maganar wankin kai daku ba. Ta ce "Yauwa zan bar muku wannan farar motar, kuma karku tsaya a ko'ina, kuna gamawa ku dawo gida, zan kara muku kuɗi yanzu, karfa ku tsaya a ko'ina" Jamila ta amsa da tom. Haka ta shiga cin abincin tana sauri, kafin ta gama Jamilu ya fito cikin shirin sa na kayan ƴan kwallo yana kallon Aida ya ce "Anty baki tafi ba har yanzu ƙarfe tara saura fa?" Haka ta gama kafin ta wanke hannu ta ƙara jaddada musu cewar karsu tsaya a ko'ina ana gama gyara mata kan shima yayi askin su dawo gida, suka amsa da to kafin ta rungume su ɗaya bayan ɗaya suka rakata har gurin motarta ta shiga ta nufi team ɗin su. Tana barin gidan Jamila da jamilu suka koma ciki. Bata fi minti biyar da fita ba motar Siyama ta shigo gidan. Bata tsaya komai ba ta shige cikin ta nufi ɗakin Aida duk ranta a ɓace. Tun daga palon take jiyo Nishi a ɗakin Jamila, hakan yasa abun da ta gani ranar ya fado mata, take ta nufi ɗakin tana tunanin wai kullum haka suke yi ne, anya kuwa Aida bata sani ba, da mamaki taga ɗakin a buɗe, ta leka ta samesu kamar ranar yau ma dai sex suke yi, sosai wannan karan ta tsaya tana ta kallonsu har ta manta da abun da ya kawota, sosai taji tana neman rasa control ɗin ta, hakan yasa ta ciro wayarta ta shiga camera ta fara ɗaukarsu vedio. Haka ta juya ta fita ganin haka tasan Aida bata gida, hakan yasa ta bar gidan itama.
Aida kuwa tare suka tafi su uku kowacce da motarta. Bayan sun isa gurin ne, aka tabbatar da cewar zasu iya, nan suka saka hannu, kafin aka shigar dasu wani ƙaton abu mai kamar irin abun gurin wanka, amma wannan a zagaye yake kamar saiko. Da mamaki sukaga ruwan zafi ne a ciki sai tururi yake yi, gashi ruwan kamar yalo kamar kore. Haka dai Nusee ta fara shiga sai Sarah sai ita Aida ɗin. Jin ruwan ba zafi sosai ne yasa suka sake. Sunyi a ƙalla minti talatin kafin aka ce su fito. Nan ma aka basu wani ruwa mai kaman mai aka ce su shafe jikinsu, su dai komai aka ce sai yi suke, suna sanye da bra da banti kawai a jikinsu. Lokacin da suka kalli jikinsu suka ga sun kara wani haske da kyau. Bayan sun gama shafe jikinsu aka basu wani ruwa irin na da suka shiga ciki amma wannan normal ruwane su shiga ciki irin dai na ɗaxu. Bayan sun fito aka basu wasu kayan suka saka, aka fara yin hotuna. Ita Sarah tallan fauda suka ɗauketa wanda uwa da ƴarta zasu iya yin amfani da shi a lokaci guda, za'a dinga ɗora hotonta a jikin fauda ɗin. Ita kuma Nusee tallan man shafawa ne nata itace za'a dinga ɗora hotonta a jikin man ita da yarinyar da aka bata mai kyau da ita suka yi hoton yarinyar sai dariya take yi. Ita kuma Aida turare ne shima duk na kampanin Baby and me ne, wannan shine karo na farko da suka fito da turare na Baby and me hakan yasa suka zaɓi ita Aida ɗin ganin ita ba fara mace. Nan aka shiga nuna musu yadda kowacce zata tsaya a dauki hoto, sannan sati mai zuwa kuma za'ayi vedio domin fara haɗawa, kasancewar tallan nasu yana shiga gidajen talabijin da na rediyo harma online da dai sauransu. Haka dai kowacce ta dawo gida cike da farin ciki.
******
ADAWIYA
Duk da yadda take kallon haɗuwar gurin amma hakan bai sa ta shagala da kallo ba saboda karma a raina ta. Sunyi tafiya mai tsayi a linta kafin suka isa wani ɗaki, suna shiga ta ga ɗaya daga cikin mutanen da suka zo gurin ta. Tana shiga ya miƙe tsaye suka yi hannu da manager ita kuma ya ɗaga mata hannu. Kallon ɗakin take ko tace ofishin da ya cika da hutunan fina-finai na batsa wanda wasu daga ciki ma duk ta kalla. Sosai sunan wani fim ya ɗauki hankalin ta ganin hoton wani saurayi Model ɗan ƙasar Faransa. Tasan yaron sun taɓa yin aiki da shi a nan Ingila a Magazing, amma bata san ya shiga VIP London ba, kallon hoton tayi taga a she ma film ɗin sabo ne, domin ba'a sake shi ba. Maganar da mutumin yayi ce ta dawo da Adawiya cikin tunaninta ya ce "Ga dokokin aikin VIP" Ya faɗa yana turawa manager ɗin wata zungureriyar takarda. Manager ya shiga karantawa yana yi yana kallon Adawiya da mutumin cike da mamaki. Sai da ya gama kafin ya share zufar da yayi ya ce "Zamu iya yin magana da ita mu biyu? Mutumin ya ce *Yes don't worry" Yana faɗa ya nuna musu wani ɗan Ƙaramin daki gefe da su. Adawiya ta ce "No ba sai munje ko ina ba, nasan komai game da aikin kawai asa hannu" manager ya kalleta da kyau ya ce "No Madam ki dai ƙara ki sake dubawa yanzu da kanki. Haka ta ƙarɓa ta shiga dubawa sama-sama ta karanta abun da idonta ya kai wanda bata kalla ba kuma ya wuce. Nan take ta saka hannu shima manager babu yadda ya iya ya saka hannu. Take aka bata wasu takardu akan taje ta ƙara cike su. Bayan sun gama mutumin ya ce ta biyo shi ita kaɗai. Nan suka shiga tafiya saida suka yi nisa kafin suka iso gurin ɗaya mutumin. Ya bata wasu kaya ta saka. Nan ta saka kayan wanda basu da maraba da tsirara. Wani dakin hoto ta shiga, ai kuwa tana shiga ta tarar da mata da maza sun kai goma ana ta hoto, yanayin shigar dai ba'a cewa komai. Domin dama haka shigar Medels yake musamman ma yan VIP. Ba'a tsaya da ita a nan ba suka shiga wani ɗaki bayan mata da mazan sun gama mata barka da zuwa. Suna shiga wani na miji yabi bayan su da abun ɗaukar video. Suna shiga taga ɗaki ne harda gano da komai. Kwanciya ya ce tayi, ta kwanta tana kallon namijin da shima ya zagayo kusa da ita babu komai a jikinsa sai ƙaramin wandon maza. Mutumin da suka shigo tare ya ce "Sau nawa kika taɓa yin sex? Ta haɗiye yawon tsoro tana tunanin to ina ruwansu da sanin wannan tace "Bata sani ba" Kallon Namijin yayi ya ce "Zata iya yi kuwa? Ya ce "Eh zata iya. Ya kalli mai ɗaukar video ɗin ya ce muje zuwa. Ya fara ƙoƙarin cire mata ɗan fanti dake jikinta sai ta riƙe, domin har ga Allah ta tsorata da namijin ganin sai jiki duk a murɗe kamar ɗan dambe.Wata tsawa mutumin ya daga mata yana cewa zata ɓata musu aiki gwaji za'a kawai idan har ta iya cin gwajin to za'a fara aiki da ita kwanan nan, idan kuma bata ci gwajin ba za'a ci gaba da bin ta a hankali har ta saba. Sosai ta tsorata a fili ta ce "Sex ne gwajin?" Ya ce "Yes baki gani a jikin takardar da kika sa hannu bane? Gabanta ya ba da wani rass...📝
_To masoya S Reza, wannan shine karshen free page Kaman yadda nayi alƙawari. Nera ɗari biyar kawai zaki biya a saka ki a cikin group aci gaba da posting. Kuma yanzu haka ba tsayawa zan yi da posting ba, domin wasu sun fara biyan nasu, idan kin biya sai na tura miki wanda akayi ba kyanan sai kuma a ci gaba da ga inda aka tsaya. Ba sai na ce muku komai akan wannan labarin ba kunsan za'a samu darasi mai muhimmanci, sanna akwai aikin da na sani a ɓangarorin cikin labarin kaman yadda kuka gani, Jamil da jamilu abun da suke yi Aida ta sani, Adawiya da Badawiya sun samu madafa, Siyama da Ibrahim me zai faru, Hamm ba sai na cika ku da surutu ba mu haɗu a VIP. Ga account number da za'a biya ɗari biyar 8100785178 Opay Adam Salisu. Sai a tura da shedar biya ta wannan lambar 08100785178. Idan ma katin waya zaki turo shima kiyi magana wa wannan number. Idan kika biya kudi akan wannan littafin wallahi ina sheda miki cewar baki faɗi ba domin zaki kwashi ruwan darasin rayuwa. Sai na ganku ƴan amanar S Reza_ 🥰
Love all
One love
Comments
Ana shering
Love my fan's
By S-Reza write
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels