Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
Koda jin haka sai sarki uwaisul karni ya dubeshi yace, kaje ka shaidawa dakarunmu cewar ganinan fitowa na tsaya nema mana nasara ne a wajen ubangiji, sannan ka isar musu da sakona cewar suka kasance masu addua, duk rintsi kada sun manta da neman taimakon ubangiji. Koda jin haka sai nan da nan wakilin sarkin yaki ya juya ya tafi izuwa ga rundunar tasu kuma ya sanar da su sakon da sarki ya fada masa. Ai kuwa bai dade da fada musu wannan sako ba, sai ga sarki uwaisul karni ya fito daga cikin tantinsa ya nufo inda dakarun suke. Nan da nan gurin ya kaure da kabbara ai kuwa babu wani jira sarki uwaisul karni ya hau dokinsa ya zabureshi da gudu yana mai kwalla kabbara aikuwa sai suma dakarun suka rufa masa baya kamar kaza da yayanta. Suna zuwa tun daga nesa suka fara yiwa masu gadin kofar birnin ruwan kibiyoyi, ba sassauci suna zuwa baki kofar birnin suka banke kofar birnin suka shiga da karfin tsiya. Nan da nan garin ya hautsine da yaki, aka fara cinikin rayuwaka, cikin izinin ubangiji kuwa dakarun musulunci suka fara samun nasara a hankali sarki uwaisul karni suna kutsawa har suka dan gana ga fadar birnin, kafin kace wani abu tuni an karar da dakarun dake gadin gimbiya muzaira. Kawai sai sarki uwaisul karni ya sauko daga kan dokinsa ya nufi inda muzaira take nan da nan cikinta ya duri ruwa idonta ya zazzaro alamun rashin gaskiya suka bayyana akan fuskarta. Kawai sai ta sulale kasa aumammiya, sai sarki uwaisul karni yace, akaita kurkuku. Sannan ya dubi wani ba fade yace, ina sauran hakimaina waziri da kuma malaman wannan gar, kawai sai yace ai duk makiya sun kaisu kurkuku sun kulle. Koda jin haka ai sarki uwaisul karni yayi umarni da aje a fito da su. Daga nan sarki yayiwa jamaar gari bayanin duk abinda ya faru da su, aikuwa sai wasu suka hau jimami wasu kuma suka hau hailala. Daga can kuma bayan an kawo su waziri da hikamai da kuma sauran malaman garin sai sarki ya kuma yin jawabin wani mafarki da yayi. Yace a cikin mafarkin nasa an nuna masa cewa dan sa yarima Huzaifa ya sami nasarar ceto dakarun da sarki shaaran ya kulle a kurkuku kuma ya sami nasarar dauko Luhaira yar gidan likita abi sharhaz. Koda jin wannan labari sai mutane suka hau kabbara da murana, sarki ya daga hannunsa kowa yayi shiru sannan kuma yace, an nuna min cewa makiya sunan suna yin mugun tanadi akanmu don haka daga yau na umarci duk wani badakare ya kasance cikin shirin yaki domin bako wanne lokaci zasu iya kawo mana harin sumame, haka zalika na umarci dukkan malaman mu da mutanen dake cikin wannan birnin su dukufa da addua domin Allah ya karemu daga sharrin abokan gaba. Nan dai sarki ya sallami kowa yace gobe za'a kuma haduwa a fada. Nan dai kowa ya tafi yama fadin albarkacin bakinsa, kashe gari da safe kuwa fadar birnin Darul Husuf ta cika makil, ko inaka duba ba abinda mutum zai hanga face kawunan jamaa ko ina, bayan kowa ya gama hallara sai daga can sarki uwaisul karni ya fito, cikin kashin lafiya, koda jamaar gari suka rude da kabbara har sai da sarki ya zauna akan karagar sa daga can sai sari ya tashi yayiwa jamaa sallama sanna ya fara da cewa, ya ku jamaar birnin Darul Husuf mai albarka, ku sani cewa lokaci yayi da zamu farka daga barci mu tashi tsaye mu zage damtse d addua, domin kuwa abokan gabarmu suna nan suna yi mana mugun tanadi na zuwa su yakemu, duk da irin nasarar da muka samu a kansu a can filin yaki, da kuma nasarar da Huzaifa ya samu na shiga birnin su tare da ceto rayuwar dakarun mu a cikin kurkukun birninsu da kuma dauko Luhaira yar likita abu sharhaz, sanin wannan nasarori da muka samu akansu dole ne su fusata kuma suyi babban shiri na ganin sun dauki fansar abinda muka yi musu. Duk da cewa suma sun shigo namu birnin sun kashe mana jamaarmu, amma kuma cikin nasarar ubangiji gashi birninmu ya kuma dawowa hannunmu. Wannan ba karamar nasara bace daga ubangijin mu, don haka dolene mu gode masa bisa wannan nasara kuma mu sake rokonsa akan samun nasara a akan abokan gabarmu anan gaba. Domin kuwa naci alwashin cewa wannan yaki da zamu sake yi da mutanen birnin shumbul shine yaki na karshe tsakanin mu, Kodai mu karar dasu mu mulki birninsu ko kuma su karar da mu su mulki birninmu, abinda nake so da ku shine ku dage da addua sannan kuma ina mai jan hankali ga dakarun mu su mai da hankali wajen ganin munyi shiri mai kyau don tabbatar da nasarar mu a filin daga. Haka kuma kuma malaman mu na umarceku da ku Shiga halwa ta tsawon a kalla kwana uku domin kara roko nasara akan abokan gabarmu. Da wannan nake muku Sallama sai mun sake haduwa nan da kwana uku wanda shine lokacin da zamu koma bayan gari domin tarbar abokan gaba. Koda gama wannan jawabi sai sarki ya tashi ya shiga gida, shigarsa gida ke da wuya bai zame ko ina ba sai turakar gimbiya shulaifa wato mahaifiyar Huzaifa. Koda shiga sai ya tarar da ita cikin damuwa zulumi da fargaba, idanunta sunyi jajawur alamun ta dade tana kuka. Lokacin da sarki ya shiga cikin turakar tare da yi mata sallama sai ta mike tsaye ta tareshi tare da amsa sallamar tasa. Koda sarki uwaisul karni ya ga halin da take ciki, sai ya kama kafadunta yace yake matata ina dalilin shiga wannan yayi naki. Koda jin wannan tambaya sai shulaifa ta dubeshi a lokacin da hawaye ya subuto mata tace, ya kai mijina hakika na shiga fargaba da tashin hankali a lokacin da ka tafi wannan yaki kai da su Huzaifa, har na dinga wasu irin munanan mafarkai na tashin hankali, ko da yaushe bani da nutsuwa kuma bana iya cin abinci. Lokacin da sarki shaaran ya shigo birnin nan na gama saddakarwa cewa na tasaka kai da da na Huzaifa, ta tabbata cewa zan zama bazawarar kuyanga ko baiwa mara da. Lokacin da na samu labarin shigowarku cikin birnin nan bayan tafiyar su sarki shaaran ina gidan kurkuku nayi Farin ciki tare da yi muku Fatan nasara, yanzu kuma gashi kana cewa nan da kwana uku zaku sake fita wani yakin, wanda kai kanka baka da tabbacin cewa zaka rayu. Baya ga haka ga Huzaifa bai dawoba ba musan halin da yake ciki ba. Koda jin wannan batu daga bakin shulaifa sai sari uwaisul karni ya dubeta cikin murmushi sannan yace, ki kwantar da hankalinki da izinn ubangiji zamuyi nasara a wannan yaki, haka kuma ina mai yi miki albishir da cewa danki Huzaifa yana nan cikin kashin lafiya, don ya sami nasarar abinda ya je aiwatarwa a birnin shumbul, ya ceto rayuwar dakarun mu da sarki shaaran ya kama, haka kuma ya sami nasarar dauko Luhaira yar likita abu sharhaz dake tsare a can gidan gonar sarki shaaran tare da taimakon wani aljani. Don haka ki kwantar da hankalinki Insha Allahu mune zamu sami nasara a wannan yaki. Haka kuma abinda baki sani ba shine, dan Huzaifa wato yarima ukashat ya dawo bangare mu domin ya gane gaskiya kuma ya nemi afuwarmu baki daya. Koda jin wannna batu sai ta fashe da kukan Farin ciki tare da yiwa Allah godiya, nan da sarki uwaisul karni ya ci gaba da kwantar mata da hankali har ya samu ta saki ranta daga nan yayi mata sallama ya tafi izuwa turakarsa. * * * * * * A can bangaren su Huzaifa kuwa bayan sun kammala cin abincin sai Huzaifa ya bayar da umarni a kwashe kaya a ci gaba da tafiya, haka suka ci gaba da tafiya ba sassautawa sai idan lokacin cin abinci ko kuma loakcin sallah ya riskesu ko kuma idan dare yayi kuma babu hasken farin wata, su kwana nan su tashi can har tsawon kwana uku. A kwana ukun ne suka fara shigo wannan daji inda kwafsa yaki tsakanin su da mutanen birnin shumbul, anan aka yada zango sai da fair ya waye sannan aka ci gaba da tafiya. A can bangaren su sarki shaaran kuwa, bayan sunya da zango a cikin dajin da ke bakin kofar birnin shumbul sai suka kafa tantuna anan suke wana kuma anan suke tashi, kuma sai ya zamana cewa suna masu baiwa kansu horon yaki a wannan guri, har tsawon kwana hudu a kwana na hudun ne dakarun agaji suka fara zuwan wannan sansani na su sarki shaaran, aikuwa rana da suka fara zuwa sarki shaaran yayi Farin ciki sosai haka zalika ya samu kwarin gwiwa tare da cikakken yakinin cewa shine zaiyi nasara wannan yaki. Haka dai yaci gaba da baiwa wadannan dakaru horon yaki ba dare ba rana, haka kuma kullum sai dakarun agaji sunzo daga kasahse daban daban dake nahiyar gaba daya. Kafin cikar kwana bakwai sai da sarki shaaran ya tara dakaru sama da guda dubu dari hudu. A rana da kwana bakwai ta cika ne ya tara gaba daya dakarun sannan ya sanar musu da cewa a gobene zasu tunkari birnin Darul Husuf domin yakin karshe tsakaninsa da mutane wannan birnin. Sannan yayi sanarwar cewa duk mutumin da ya ya ko masa kan yarsa Lafirat yayi masa alkawarin babbar kyauta, haka zalika wanda duk ya ya ko kan Huzaifa da kuma kan ukashat shima akwai kyauta ta musamman, wanda duk kuma ya sato Luhaira daga cikin gidan sarautar birnin Darul Husuf ya kawo masa ita to tabbas daga ranar zai bashi babban matsayi a cikin fadarsa. Koda jin wadannan alkwura da sarki shaaran yayi sai kowa ya cika da buri da kwadayin ganin ya samu wannan dama duk da sun san cewa ba abune wanda zai faru cikin sauki ba. Kashe gari tun da dukun safiya dakaru suka tashi suka fara shiri masu wasa makami na yi masu gyaran sirdi nayi kowa da irin abinda yake gyarawa dan shirya wa tafiyar. Sai da rana ta fito gari yayi haske sosai sannan kowa ya gama shiryawa akayi sahu sahu ana jiran sarki shaaran da gimbiya Sazirat. Su kuwa naso fito ba sai da rana ta take sosai sannan suka fito cikin shigar bakin sulke na yaki, wohoho duk wanda ya ga wannan shiga da sarki shaaran yayi da yarsa gimbiya Sazirat sai ya firgita kuma sai yayi tunanin su kadai ma zasu iya yakar duk biranen nahiyar su cisu da yaki saboda shigar ta fito da kwarjinin su da kirar su ta sadaukai musamman ma shi sarki shaaran. Ba tare da jiran komai ba kuwa sarki shaaran da Sazirat suka hau dawakansu, suna hawa dawakannasu sai dawakan suka daga kafafunsu na gaba tare da yin haniniya a dai dai lokacin da sarki shaaran ya kwarara uban ihu tare da zare takobinsa ya nuna hanyar da za su bi dan komawa izuwa birnin Darul Husuf. Ai kuwa dokin yana dire kafafunsa a kasa sai sarki shaaran ya zabureshi da gudu izuwa cikin daji aikuwa sai wadannan dakaru suka rufa masa baya suna masu ihu da kururuwa kai kace mutanen duniya zasu je yaka. A can bangaren sarki uwaisul karni kuwa yana kwance yana cikin barci a cikin turakarsa kawai sai yayi wani mummunan mafarki. A cikin mafarkin annuna masa cewa amfani gonaki na wannan birni sun kone haka kuma jini sai kwarara yake a cikin wadananna gonakai. Koda gama wannan mafarki sai sarki uwaisul karni ya farka yana mai yin hailala, kawai sai ya sakko daga kan gadonsa ya fito daga ciki dakin nasa, kawai sai ya kira wani hafiminsa yace masa, yaje gidan babban liman maza maza ya kirashi, kuma sannan ya biya ta gidan sauran malaman garin su taru a fada da anyi sallar asubahi. Ai kuwa ana idar da sallar asbahi sai fada ta cika makil da jamaar gari tare da manyan malaman fada da kuma hakimai da sauran fadawa. Nana sarki ya tashi yayi sallama sannan akayi addua bayan anshafa ne sarki yayi jawabin mafarkin da yayi jiya da daddare koda jin bayanin wannan mafarki sai wani babban malami wanda ya kasance dattijo kuma masanin fassarar mafarki ya tashi ya fassarawa sarki wannan mafarki nasa inda yake cewa hakika abinda mafarkina ke nuni da shi shine makiya na dab da shigowa cikin birnin nan namu mai albarka, koda jin wannan fassara daga bakin wannan makami sai mutanen dake fadar suka rude da hayaniya da salati. Koda jin haka sai sarki ya daga hannunsa sama kowa ya sake yin shiru, kawai sai sarki uwaisul karni yace, daga yanzu zuwa rana ta fito kowanne badakare ya je ya shirya a hadu kofara fada haka zalika ya umarci duk mutanen gari da su zauna a gida kada wanda ya kuma fitowa waje har sai suna dawo daga wannan yaki da zasuyi ya umarci malaman garin cewar gaba dayan su su hallara a masallaci su dukafa da addua haka suma mutanen gari sauran dakaru kuma dasu za'a fita wannna yaki. Koda gama wannan jawabi sai sarki uwaisul karni ya juya ya shiga gida domin shirin yaki, sa da aka shafe sama da sa'a hudu ana shirin fita yaki sannan kowa ya kammala dakaru sukyi sahu sahu a bakin kofar fada ana jiran fitowar sarki, jima kadan sai ga sarki uwaisul karni yvta fito cikin shigar Kayan yaki na fararen sulke, tabbas shigar da yayi sai da ta kara masa kwarjini sosai. Aikuwa yana zuwa ba wani jira ya kama dokinsa ya hau sannan ya zaburesi da gudu izuwa kofar birnin. Anan aka kafa tantuna aka zauna ana jiran isowar abokan gaba. Alamarin su sarki shaaran kuwa suma haka abin y kasance sun kwana nan su tashi can har tsawon kwana takwas, a kwana na tara ne suka iso bakin kofar birnin Darul Husuf, kasancewar a lokacin duhu ya fara bisa dole suma suka ya da zango kuma suka kafa tantuna suna jiran gari ya waye domin a gwabaza wannan yaki. Kashe gari kuwa tunda fukin safiya dakarun kowanne bangare suka hau sahu sahu, kowacce runduna ta na jira shugabanta ya fito, domin a bayarda umarni. Can sai ga sarki uwaisul karni da sarki shaaran sun fito gaban jamaarsu, kawai sai aka ga wani daga cikin dakarun sarki shaaran ya sukwano dokinsa izuwa sansanin su sarki uwaisul karni. Har wani badakare ya zare takobinsa da nufin yata tareshi kawai sai sarki uwaisul karni ya dakatar da shi. Da zuwa sai wannan badakare ya sauka daga kan dokinsa, ya zo Har gaban sarki uwaisul karni ya mika masa wata wasika, sai sarki ya karbi wasikar, sannan ya fara karantawa kamar haka. *sako daga sarki mai cikakken ikon zuwa ga abokin gaba ta, ina mai yin umarni a gareka da ka janye dakarunka daga wannan filin yaki, domin kuwa babu ta yadda za'ayi kuyi nasara a wannan yaki domin kuwa sarki yawa yafi sarkin karfi, sannan kuma ina so kazo har gabana ka fadi bisa gwiwarka ka nuna cewa kayi mana mubayaa, wannan shine kadai abinda zai sa na yafe maka zunubin da kuka aikata min, idan kuma ba haka ba to ina mai yi maka rantsuwa da girman kujerata sai na mayar da kasarka birnin nakasassu.* Koda gama wannan jawabi sai ran sarki uwaisul karni ya baci, sai yasa aka rubuta martanin wasikar kamar haka. *karyar ka ta sha karya kai gafalallen sarki ka tuba ka karbi addinin Allah sannan kuma ka koma ga Allah ka nemi afuwarsa gareka, sannan kuma kayi alkawarin cewa bazaka kara zubar da jini ko zalunci a bayan kasa ba, idan har kayi haka tabbas zan Barka da ranka idan kuma baka tuba ba to tabbas a yau daina shafe tarihinka a doron kasa* Koda aka wannan badakaren ya kaiwa sarki shaaran martanin wannan wasika tasa sai ran sarki shaaran ya baci, aikuwa nan take ya bayar da umarni da a afkawa su sarki uwaisul karni. Aikuwa sai gaba dayan dakurun sarki shaaran suka zare makamansu suka zaburi dawakansu izuwa kan su sarki uwaisul karni suna masu kururuwa da ihu, kafafuwam dokin su na karyar kasa nan da nan kura ta turnuke sama kasa ta dinga girgiza kamar zata tsage. Koda sarki uwaisul karni yaga dakarun sarki shaaran sun durfafosu cikin mugun nufi sai shima ya bawa dakarunsa umarni da atare su tun kafin su karaso, aikuwa sai suma suka zaburi dawakansu suna masu zare takubba tare da kabbara, suma suka kai dauki kan dakarun sarki shaaran, aikuwa ana haduwa a tsakiya sai aka gwamutse kirazan dawakai suka fara bangazara na yan uwansu Nanfa aka fara cinkin rayuka. Komai kallon kurallar mutum bai isa ya banbance bangaren da ke samun nasara ba. Domin kuwa kare jini biri jini akeyi, nanfa maza je suka fara kwamarzuwa babu sassauci ana kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama juraya da jarumata. Duk inda sarki uwaisul karni yasa gabansa sai dai kaga dakaru na zubewa a kasa kamar sassabe a gona, hakama a bangaren sarki shaaran wato dai sai yiwa dakarunsu suke sarki ya hana dawa tsaiwa. Koda ganin irin barnar da kowa ke yiwa kowa sai sarki uwaisul karni da sarki suka tarwatsa dakarun dake gabansu suka zaburi dawakansu suka nufi kan juna cikin mugun nufi da zakuwa. Ai kuwa suna haduwa suka fara kaiwa junan su sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bakinta da jarumta cikin salo da kwarewa irin ta manyan mayakan da suka ga jiya suka ga yau. Haka dai aka ci gaba da wannan yaki, to amma kasancewar dakarun sarki shaaran sunfi dakarun sarki uwaisul karni yawa sai ya zamana cewa an fara cin karfin dakarun birnin Darul Husuf, haka dai aka ci gaba da dauki ba dadi har tsawon sa'a hudu, koda ganin cewa wankin hula zai kaisu dare sai dakarun sarki shaaran suka fara amfani da karfin tsafi domin su karar da dakarun sarki uwaisul karni, koda ganin haka sai dakarun sarki uwaisul suka fara karanta wata addua ta musamman ai kuwa duk tsafin nasu sai ya tashi a banza, haka dai aka ci gaba da yaki har ya zamana cewa an karar da kaso biyu cikin uku na dakarun birnin Darul Husuf, su kuma dakarun sarki shaaran an karar da kaso daya cikin ukunsu. Koda fahimatar hakan sai sarki uwaisul karni ya dan ka da baya kadan ya tsaya yana mai gyara tsayuwa koda ganin haka sai shima sarki shaaran yayi koyi dashi. Sannan sai sarki shaaran ya dubi sarki uwaisul karni cikin murmushi mugunta yacena fada maka wannan yaki na mune kuma dolene muyi nasara akanku kana da dama har yanzu lokaci bai kura maka ba, indai har zakayi abinda nace maka tunda farko to zan yafe maka. Koda jin haka sai sarki uwaisul karni ya dubeshi cikin fushi yake cewa, kai Munafukin Allah kayo sani cewa har abada babu sulhu tsakanin da makiya addinin Allah ni dasu sai kaifin takobi kawai. Kuma idan har na mutu ina da yakinin cewa nayi shahada kuma zaa tashe mu a wata rayawar daban a ranar alkiyama don ayiwa kowa hisabi bisa abinda ya a doron duniya, wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiki na kwarai zasu samu babban rabo, wadanda kuma suka bijire suka aikata zalunci irin ka to zasu sansani azaba mai radadi. Sai ka fadamin menene ribarka anan, kodajin haka sai sarki shaaran ya bushe da dariya sannan yace, ai ku kukayi imani da wannan zancen mu kam sam zamuyi imani dashi ba, kaicho kaji rashin rabo. Hakika wanda yayi nisa baya jin kira. Ana cikin wannan haline sai su sarki uwaisul karni suka jiyo takun sawayen dawakai daga cikin daji, ba kowa bane face Huzaifa tare da dakarun musulunci wanda sarki shaaran ya rufe a gidan kurkuku. Ai kuwa tuna kafin su karaso filin yaki suka zare makamansu ai kuwa sai filin ya kuma hargitsewa da zazzafa kuma mummunan yaki, ana cikin haka kuma sai ga dakarun ukashat nan suma sun nufo filin yakin aikuwa sai musulmai suka kara samun sabon kwarin gwiwa, nan da nan aka sa dakarun sarki shaaran a tsakiya. Sarki uwaisul karni ya tari sarki shaaran, ukashat ya tari sarkin yakin birnin shumbul, Huzaifa kuma sai ya tari mai bakaken kaya, Lafirat ta tari yar uwarta Sazirat, uwar mayu da hirama suma suka afka cikin wannan yaki. Kowa na kaiwa kowa mummunan hari cikin mugun nufi. Haka dai akayi ta dauki ba dadi har tsawon wata sa'a ukun a sannane aka fara cin karfin dakarun sarki shaaran koda suka ga an kusa karar da su sai suka fara guduwa daga filin yakin koda ganin haka sai sarki shaaran ya dinga yin tsafi duk wanda zai gudu sai ya kama da wuta ya kone kurmus. A lokacin da sarki uwaisul karni yayiwa sarki shaaran munanan sara har guda uku daya a gadon bayansa daya kuma a kan dantsensa na dama sai kuma cinyarsa ta hagu, gurin ya bude sai jinine ke zuba. Shi kuma sarki uwaisul karni ya sami raunika har guda biyu daya a cinyarsa ta dama daya kuma dantsensa na hagu aman ranuni baiyi zurfi sosai ba. Ana cikin haka ne sarki uwaisul karni ya shammaci sarki shaaran ya dan kara masa sara a kasan cibiyarsa, kawai sai ji akayi sarki shaaran ya kwarara uban ihu sannan ya durkushe bisa gwiwowinsa, ana cikin Hakane itama Lafirat ta shammaci Sazirat ta dan kara mata naushi a cikin tana durkusawa tayi mata mugun duka a gadon baya, aikuwa sai ta kife kasa tana mai aman jini cikin galabaita gashi duk sunyi wa junan su munanan rauni ka alamun karfi yazo daya. Kawai sai Lafirat ta taka kafafunta tana mai tafiya da kyar tazo kan Sazirat a lokacin da hawaye ya zubo mata tace, yake yar uwata kiyi sani cewa bani da wani sauran da uwa na jini a wannan duniya sai ke, ina mai baki shawara daki tuba ki koma ga ubangiji musulunci, ki karbi addinin gaskiya. Koda jin haka sai Sazirat ta takarkare ta bushe da dariya tace, kiyi hakuri yake yar uwata bakin alkalami ya riga ya bushe, nikam da nayiwa iyayena da kakannina butulci gwara na mutum a cikin addinina. Koda jin haka sai Lafirat ta sa takobinta ta sare kan yar uwarta Sazirat. Hakama a bangaren su Huzaifa ta ukashat kowa ya kashe abokin gwaminsa. Ya zamana cewa saura sarki shaaran kawai a kwance ya kasa tashi, a haka sarki shaaran ya ci gaba da kakarin mutuwa har rantsa ya fita idanunsa suka kakkafe harshensa ya zazzago kasa. Tur Allah wadai da irin wannan mummunar mutuwa. Daga nan aka dunguma aka koma cikin birnin Darul Husuf. Ukashat ya dubi Huzaifa ya bashi hakuri abisa abinda ya faru tsakaninsu a baya ya nemi yafiyarsa cikin Farin ciki da murna suka rungume juna, sannan yarima Huzaifa yace da ukashat ga babbar kyauta nayi maka kawai sai ya nun amsa gimbiya Luhaira. Ana cikin haka sai gimbiya Lafirat ta zai gaban sarki uwaisul karni tace itama

Chapter 5 of 6