Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
umarnin mahaifiyata akan auren mahaifiyar ka. Ka saurara da kyau kaji labarin da zan baka watakila kaima ka samu wani darasi daga tarihin rayuwata kuma ya aa daga aikata irin kuskuren da na aikata. * * * * * * A Lokacin da nake kamarka na kasance dan guda daya da Allah ya bawa mahaifina, na taso da ilimin addini da hikima gami da gagrumar jarumta, na kasance a wancan lokacin mai dakawa maza gumba a hannu, amma kuma sai ya zamana cewa yan mata basa gabana, Ma'ana bana soyayya kuma bani da wani shaawa akan soyayya da kuma aure, saboda ni burina kawai shine na kasance ko da yaushe cikin jihadi da daukaka Kalmar Allah da kuma tallata addinina zuwa sauran kasashen dake makwabtaka. Ina cikin wannan hali ne iyayena suka fara min maganar aure, sai nace ai da sauran lokaci. Haka dai tun suna lallabani har ta kai cewa sun fara fusata, ganin hakan ne yasa na Fara tunanin macen da ya kamata ace na aura. Wata rana naje cikin gari ina rangadi sai kwatsam na ci karo da wata kyakkyawar budurwa, koda muka hada idanu da ita take naji gabana ya fadi. Haka naci gaba da tafiya ian satar kallonta, daga can sai na lura ashe itama satar kallona take, koda na fuskanci hakan sai tsayar da dokina har suka zo zasu wuce ta gabana. Sai na tsayar da su na musu sallama tare da gabatar da kaina a gareta, itama ta sai ta gabatar min da kanta lokacin da naji daga inda take sai nayi mamaki, ba daga ko ina take ba face ta fitone daga gidan likita abu sharhaz wato likitan gidanmu. Nayi mamaki matuka saboda ni a sanina likata abu sharhaz bashi da da ko ya. Lokacin da na gabatar mata da abinda ke cikin raina nayi tunanin ko zata ki amma bisa mamaki sai ta karbi tayin soyayya ta, ta karbeni hannu bibbiyu. Lokacin da muka fara soyayya mun kasance ko da yaushe cikin shauki da son ganin juna, har ta kai cewa bama iya sa'a hudu ba tare da mun nemi juna ba. Lokacin da shakuwarmu ta kara nisa sai na gabatar da abinda ke raina ga mahaifina, sai yayi farin ciki, ita kuma mahaifiyata sai abin ya faskara daga gareta. Tace ita bata amince da wannan hadin ba saboda ita yarinyar bani take so ba mulkin da nake ciki take so. A lokacin soyayya ta rufe min idanu bana ganin laifin muzaira ko kadan. Haka mahaifiyata taci gaba da nusar da nai akan auren muzaira amma ina na rigada nayi nisa a cikin gokin sonta. Bayan anyi auren mu sai Allah ya dauki ran mahaifiyata, lokacin da takwanta rashin lafiya sai ta min wasiyya da na kara aure domin kuwa Matar da nake tare da ita ba sona take mulki na take so, idan har ka samu wata mace mai tsoron Allah mai cikakken imani to tabbas zata iya kareka daga sharrin wannan Matar taka. Lokacin da na jewa matata da batun Karin aure ta nuna kishi da damuwa sosai, amma kuma daga baya ina mata nasiha sai ta daina, nayi tunanin hakan so ne daga gareta ashe ita akwai manufarta, wadda gashi yanzu ta nuna ta a fili. Tabbas mahaisfiyarka babu irin son da ban nuna mata ba amma sai gashi yau tana neman rayuwata da mulkina. Wannan shine babban kuskuren da na aikata a rayuwata. Koda sarki uwaisul karni ya zonan a zancensa, sai hawaye ya zubowa ukashat, yace yanzu duk akan neman duniya da kuma mulki ta hada duk wannan fitinar. Tabbas sharrin mace yafi ga haka, ya kai Abbana ban taba ganin mutum mai hankali, ilimi da hangen nesa ba kamar ka a wannan nahiya tamu gaba daya. Lallai zan kasance mai bin dukkan umarninka ba zan saba maka kuma zan ci gaba yiwa mahaifiyata addua akan Allah ya shiryeta, ya sa ta gane gaskiya. Ina so ka sani cewa a halin yanzu babu abinda na ke so sama da na sake saduwa da dan uwana Huzaifat domin na nemi gafararsa kamar yadda na nemi taka bisa abubuwan da na aikata. Haka kuma begensa da tunaninsa sun addabi zuciyata fiye da yadda nake yin na mahaifiyata saboda na gane cewa bani da wani dan uwa kuma masoyi sama da shi a wanann doron kasa, don't haka kusa bana son naga ya sauka a jikinsa bare ya taba lafiyar sa. Lalli ina bukatar na je duk inda yake a cikin gaggawa domin na ga halin da yake ciki kuna na kai masa dauki. Ya kai Abbana ka yi min izini na kwashi dakaru mu tafi izuwa hanyar birnin shumbul domin kaiwa Huzaifat dauki. Lokacin da ukashat yazo nan a zancensa sai hankalin sarki uwaisul karni ya kara dugunzuma ya dubeshi cikin firgici yace, ta yaya kake tsamamnjn zan iya barnka ka tafi inda dan uwanka ya tafi bayan bani da tabbacin cewar shima yana raye? So kake na yi biyu babu kenan yazamana cewa babu kai babu shi? Ka tuna fa cewar haryanzu hankalina ya rabu gida biyu. Ina tunanin jakin da jamaata ke ciki a cikin birninmu kuma ina tunanin halin da dan uwanka ke ciki a can birnin shumbul. Idan kaima ka tafi ka barni wane irin hali zan shiga kenan? Saadda ukashat yaji wannan batu sai yayi murmunshi ga sarki uwaisul karni yace, Haba ya kai Abbana, shin ka manta ne cewar tun muna yara ka koya mana rashin tsoro akan tukarar makiya Allah? Shun ka manta ne cewar ka koya mana mu yi imani sa cewar babu Mao kashe wa da rayawa sai Allah, kuma duk abinda muka ga ya samemu kaddarace daga Allah? Saboda me yanzu kake tsoron 'ya'yanka su mutu alhalin ka tabbatar mana da cewar matsoraci bashi zama Gwanin har abada? Ka tuna da irin labaran da ka bamu irin na jarumatakar da kayi a zamaninka da irin tsananin wahalar da kuka shafa kau da iyayenka da kakanninka kafin ku sami nasarar tsare addinin Allah a cikin birnin darul husuf daga sharrin kafiri har kuka zami gagarabadau a filin fama, sunayenku suka daukaka a nahiyar ku ma zami dodanni ga kafiri masu son rushe addinin karya. Shin ba ka so ne muma 'yayanka mu sami irin wannann daukaka ko kuwa ba ka son mu dace da samun babban rabo na kadan yada addinin Allah a doron kasa? Koda ukashat yazo nan a zancensa sai jikin sarki uwaisul karni yayi sanyi ya sake rungumeshi a kirjin sa yana mai cewa, na yarje maka ka tafi izuwa wannan babban aiki ya kai dana kuma zan kasance mai yi maka adduar samin nasara har Allah ya dawo mun da kai lafiya. Koda jin haka sai farin ciki ya kullube ukashat ya kama yiwa sarki godiya. Ba tare da bata lokaci ba ukashat yayiwa sarki sallama sannan ya kwashi dakarun yaki mutum dubu dari biyu da hamsin ya tafi da su. A cikin su har da habibullah, hirama da uwar mayu, manya dakarun yaki na birnin darul husuf. *Wannan shine abinda ya faru ga su sarki uwaisul karni bayan sun baro sansanin yaki sun dawo gida sun tarar da cewa tuni abokan gaba sun kama birnin nasu na darul husuf* Alhamdulillahi anan zan tsaya sai Allah ya kaimu sati mai zuwa idan da rai da nisan kwana zamu sake haduwa a cikin wannan littafi na DAKARUN MUSULUNCI dan jin yadda zata kaya...**DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA BIYAR 5 PART D ✍️ ♥️ NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI👮 TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO✍️✍️ POSTING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 SANARWA!! Bayan gaisuwa d fatan Alheri GA mutanen wannan gida, Ina so na sanar da ku cewa yakamata ku sauya akan abinda ya shaf cigaban wannan gida.. *COMMENTS * LIKES * SHARE wadannan abubuwan guda uku suna da matukar muhimmanci wajen Karawa MARUBUCI karfin gwiwa. Abin mamaki shi ne, duk lokacin da aka dakatar da posting na tsawon kowa 1 week ne, sai kaga mutane sama da 200 suna maka magana akan dalilin dayasa aka dakatar. Amma Kuma idan ana typing da posting din littafin, Bai wuce mutum 10 ko 20 ba suke comments da likes, Daman haka ake nuna son Abu? Daman idan aka baka abinda kake so baka iya yin godiya sai dai kayi shiru? A Gaskiya muddin kuna son cigaban wannan gida to yakamata bayan Karanta wannan sakon to ku ware lokacin comments da likes. Muna fatan Allah ya taimakemu ✍️ ✍️ ✍️ 🙏 * * * * * * Al'amarin su Huzaifat kuwa, tun da suka baro gidan gonar sarki shaaran dauke da Luhaira bisa aljani hurusul marwas sai suka ci gaba da tafiya a cikin daji ba sassauci suna kept kwazazzabai, koramai da duwatsu da bishiyoyi har izuwa tsawon saa uku basu ya da zango ba kuma basu hadu da komai ba. Suna cikin wannan tafiya ne suka iso cikin wani daji mai yawan sarkakiya, duhuwowi da dogayen biahiyoyi masu wadansu irin siffofi na ban tsoro. Koda Huzaifat ya ga sun shigo wannan daji sai ya bayar da da wata adduar ta neman tsari daga sharrin aljanu da dukkan mugun abu aka yi ta karantawa. A dai dai wannan lokaci ne magriba ta riskesu din haka sai aka ya da zango a cikin wannan daji aka kafa tantuna aka shiga kokarin yin alwala. Duk wannan tsawon lokaci da aka shafe ana tafiya Luhaira nata farka ba daga barcin da take ba don haka ma aljani hurusul marwas na sauka kasa sai Husain ya dauketa daga kansa ya kaita cikin tantinsa ya Kwantar da ita bisa shimfida yayi juyi kuma ta ci gaba fa barcinta. Sai da su Huzaifat suka idar da sallar isha, aka fara hada hadar cin abincin dare, sannan Luhaira ta farka daga barcin. Koda ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin tanti kuma a dokar daji cikin dare sai ta kwalla ihu da karfi cikin tsananin razana. A wannan lokaci Huzaifat yana zaune tare da sauran dakaru suna tulawar karatu alkurani. Koda ya jiyo ihunta daga cikin tantinsa sai ya mike tsaye zumbur a firgice ya ruga izuwa cikin tantin domin a zaton sa macijine ya shiga cikin tantin ya sareta ko kuma wani mugun kwaro ne ya cijeta. Da shigar sa cikin tantin sai ya iske Luhaira tsaye jikinta na karkarwa. Koda tayi arba da shi sai ta koma can baya jikin karshen tantin ta dubeshi a firgice tace, wanene kai, kuma Yaya akayi kuka daukoni daga gidan gonar sarki kuka kawo ni nan? Shin baku san matsayina bane? To nice amaryar sarki shaaran ta nan gaba. Ina mai shawartarku daku gaggauta mayar dani inda kuka daukoni in ba haka na kuwa gaba dayanku kun sayi ajalinku da kudinku. Lokacin da tazo nan a zancenta sai ta ga Huzaifat ya duneta cikin nutsuwa ba da tsoron komai ba yayi murmunshi sannan ya budi baki yace, an gaya miki cewa kowa ne yaje tsoron sarki shaaran? Akan wane dalili zan ji tsoron mutum dan uwana wanda bai kasance ubangiji ba? Koda jin wannan batu sai jikin Luhaira yayi sanyi ta cika da tsananin mamaki domin ita a iya tasowarta daga kuruciyarta har izuwa girmanta ba ta taba ji wani mahaluki da ya ambaci sunan sarki shaaran ba haka karara sai Huzaifat, kuma kowa yana tsoron sa yana yi masa biyayya an daukeshi tamkar wani ubangiji domin babu abin da ake bautawa a cikin wanann gidan gona sai shi. A zatonta sarki shaaran ubangijine abin bautawa, amma sai gashi yanzu taji ana kaskantar da shi an fifita wani ubangiji sama da shi. Cikin alamun tsananin mamaki da tsoro Luhaira ta kurawa Huzaifat idanu cikin nutsuwa tace, ya kai wannan saurayi maabocin kyawu da kwarjini, wai shin wanene kai kuma anya kuwa kai mutumin kasarmune shumbul? Koda jin wannan tambaya sai Huzaifat ya sake bushewa da dariya yace, sunana yarima Huzaifat, daga sarki uwaisul karni na birnin darul husuf. Luhaira ta gyada kai cikin dadin mamaki tace, ni kam ban tana jin sunanka ba bare sunan mahaifinka dana kasarku. Ban san ko ina ba face gidan gonar da aka haifeni a ciki, kuma ban san kowa ba face hafiman da suke yi min aiki sai sunan mai girma shaaran ana gaya min cewar shi ne mijin da zan aura nan da zuwa karshen wanna shekara. A iya sanina ban taba fita ba daga cikin harabar wannan gidan gona kuma kullum sai naji ana kirana da sunan mai tsarki Matar mai sarki sha'aran. Koda jin wannan batu sai Huzaifat yayi hailala ya fubi Luhaira ya daka mata tsawa yace, kada ki kuskura ki kara yin irin wannan furuci domin sabone mai girman gaske, domin babu wani mahaluki da ya cancanci a ki rashi da mai tsarki face Allah da mazaonsa Annabi Muhammad S A W. Sarki da shi ne ya halicci komai da kowa, kuma ya aiko manzonsa Annabi Muhammad a garemu domin ya sanar da mi shi da yadda zamu baiya masa. Sarki sha'aran ba komai bane face azzalumin sarki daga irin sarakunan da suke mulkar biranen duniya. Ya ke wannan maabocoyar kyawu ta ban alajabi, shin kin san iyayenki ko kuwa kin san yadda akayi kika taso a cikin gidan gonar azzalumi sarki sha'aran? Koda jin wannan tambaya sai nan take idanun Luhaira suka ciko da kwallah har hawaye ya subuto mata sannan tace, ai ni ban taba sanin wacece ni ba kk asalina. Ni dai kawai na taso na tsinci kaina a cikin kasaitaccen gida mai dauke da komai na nin dadin duniya a cikin wannan gida na gona tare da hadimai maza da mata wadanda adadinsu ya kai dubu masu yi min hidima iri iri. Hatta wanka, cin abinci da sanya tufafi ban taba yi ba da kaina. Ba san bakincikiba bare wani abu da ya dameni a cikin zuciyata har sai da na cika shekara goma sha takwas sannan wata rana a boye kuma a sirrance na yi hirar kusan rabin sa'a da wani hadimina wanda ya kasance saurayi kamarka maabocin kyawu mai suna shukairu. Shukairu ne ya sanar dani cewa dukkan dan Adam yana da iyaye, uwa da uba, kuma shine ya gaya mini cewa babu wanda ya san iyayena ko asalina domin tin ina kankanuwa aka kawoni cikin wannan gida aka ci gaba da rainona har na girma a matsayin Matar da maigirma shaaran zai aura. Koda Luhaira tazo nan a labarinta sai idanunta suka ciko da kwallah ta ci gaba da cewa, daga wannan lokaci na ci gaba da hira a boye da shukairu ba tare da kowa ya sani ba har muka shaku ainun. Kwatsam wata rana sai tsautsayi yasa shukairu ya taba jikina a lokacin da na fadi kasa ya kawo mini dauki. A dalilin haka ne maigirma sha'aran yasa aka tsire masa idan uwansa biyu kuma aka yanke masa hannaye. Daga wannan rana ban sake ganin shukairu ba dai dai duk saadda na tuni irin wannan hukunci da aka yi masa sai na yi ta kuka kamar bazan daina ba. Koda Luhaira tazo nan a zancenta sai kuwa ta fashe da kuka. Bisa mamaki sai tagga Huzaifat idanuna sun kama zubar da hawaye. Al'amarin da ya bata mamaki ke nan har tayi shiru ga barin nata kukan ta dubeshi tace, ya kai wannan dan sarki kai kuwa menene dalilin zubar wannan hawatue naka? Shin tausayin ajima ne ya kamarka ko kuwa tausayi nane? Saadda Huzaifat yaji wanann tambaya sai ya sa hannu ya share hawayensa sannan ya dubi Luhaira cikin nutsuwa yace, shin shukairu bai baki labarin cewar yana da mahaifi wanda ake kira da humzalu ba? Cikin mamaki Luhaira tayi farat tace, tabbas ya bani labarinka mahaifinsa kuma sunan da ma fadi yanzu shi ya ambata kuma na fuskanci cewar yana son mahaifinsa fiye da komai a doron kasa. Kai kuwa yaya akayi ka san Mahaifin shukairu alhakin ka gaya mini cewa kai ba haifaffen birnin shumbul bane? Koda jin wanann tambaya sai Huzaifat yayi murmunshi yace ai kema na san usulunki kuma na san ko suwaye iyayenki da yadda akayi aka kawo ki gidan gonar sarki shaaran tun kina yar karama. Ke na takaice miki labari ma babu abinda ya kawo ni birnin shumbul daga birninmu na darul husuf face domin na kubutar da rayuwar wadansu dakarunsu daga cikin kurkukun sarki sha'aran sannan na dauko ki daga gidan gonar sarki sha'aran na mayar dake mahaifarki inda iyayenki na jini suke. Koda jin wannan batu sai Luhaira ta kwallah ihu mai tsananin kara ta dubi Huzaifat cikin alamun rashin yarda tana mai kara ja da baya tace, ta yaya zan yarda da kai na gamsu cewar duk abinda ka gaya mini yanzu gaskiyane? Huzaifat yayi murmushi yace ai ita gaskiyane guda Dayace, kuma shi ramin karya kurarrene. Idan har satoki nayi daga gidan gonar sarki sha'aran saboda kawai son zuciyata ko don son biyan wata bukata tawa sai asirina ya tonu kin gane hakan. Idan kuna gaskiyane kina da haifa da usuli duk ranar da kika hadu dasu sai kin ji a jikinki cewar lallai nakine. Koda gama fadin hakan sai Huzaifat ya juya ya fice da ga cikin tantin ya bar Luhaira a tsaye cikin tsananin damuwa, rudewa famj da wasi wasi. Abinda ya far fado mata a rai shine, yanzu kuwa shin gaskiyane inda da iyaye, kuma ina da usuli? Idan har hakan ne lallai sarki sha'aran satonj yayi daga wajen iyayena saboda kyawuna domin ya mallakeni kawai. To tayaya wannan matashi saurayin yasan duk wannan lamarin , haka dai taci gaba da wannan tunani har izuwa tsawon wani lokaci daga can kuma sai ta fito, tadubi Huzaifa tace ya kai wannan saurayi shin bazaka taimakeni da abinci ba ina Nin Yunwa. Sai Huzaifa ya mika mata naman wata dabba koda ta kai bakinta sai ta furzar ta kasa ci, sai ta dubeshi tace, bazan iya cin wannan naman ba. Sai yace to shine da mu idan zaki ci kici idan kuma bazaki iya ba to I kwana haka. Haka ta tashi ta koma cikin tantin tana tunani har dare ya raba, barci ya saceta bata sani ba. Bayan su Huzaifa sun gama hira sai ya shiga cikin tantin, a lokacin iska na kadawa sosai a cikin dajin, yana shiga sai ya kura mata idanu, koda yaga irin tsananin kyawun da Allah ya bata, ya kwatantata da gimbiya Lafirat da kuma Sazirat sai ya ga banbancin tamkar fari da baki ne. Nan da nan sai yayi sauri ya dauko wani mayafi mai kauri ya lullubeta da shi dan kada shedan ya rinjayi zuciyar sa, Ya fita ya kyaleta ita kadai. Kashe gari tunda dukukun safiya iskar da taje kadawa mai karfi da sanyi ta tasheta, sai tunanin jiya ya fado mata. Kawai sai tace tabbas idan har Hakane sarki shaaran ya ya cutar dani da ya boyeni a cikin waje daya Tsawon shekar da shekaru. Tana cikin wannan hali ne tama dube dube a cikin sansanin ai ta hago Huzaifa a can gefe daya yana gyara kwari da bakansa. Kai tsaye Luhaira ta tunkareshi. Da zuwamta dag da shi sai ta dubeshi tace dashi, saboda me zaku barni da Yunwa alhalin na saba cin abincin safe da wuri? Ko kallona Huzaifa bai yi ba ce, ai mu ba bayinki bane da zamu je mu kai miki abinci mu zauna muna jiran ki tashi daga barci. Duk wanda kika ga yana cin abinci yanzu guzurinsa ne ke kuma baki da guzurin nima bani da shi. Yanzu haka da kika ga ina gyara kwari da bakana cikin daji nan zan shiga na farautar sai ki zo muje kiyi domin ya kamata ki koya tun yanzu. Koda jin wannan batu sai murmushi ya kunucewa Luhaira taji wani dadi a rantsa bisa jin cewar za'a tafi farauta da ita. Ita dai ta sha jin hirar farauta a bakin hadimanta har ana bata labarin irin na manyan jarumai masu kama manyan dabbobi a daji ko suyi gumurzu dasu amma ba ta tana ganin alamarin ba da idanunta. Luhaira ta dubi Huzaifa cikin murmushi mai tashi wanda ya kara matso tasananin kyanta tace, ina fata zaka koya mini yadda ake amfani da kwari da baka kuma zaka koya mini yadda ake yaki da takobi? Maimakon Huzaifa ya baiwa Luhaira amsar wannan tambaya da ta yi masa sai ya kasa sakamakon bugawar da karfin gaske kuma ba komai ne ya haddasa hakan ba face take yaji kiniyar son Luhaira ta sokeshi a kirji. Kawai sai ya kauda kai ga bari kallona ya mike tsaye ya nufi cikine daji da sauri, itama sai ta bishi da gudu don kada yayi mata nisa. Huzaifa da Luhaira suka ci gaba da nausawa cikin daji, duk inda ya kurda sai itana ta shiga. Abinki da wadda bata saba shiga daji na sai ta dinka faduwa a duk saadda take taka cikin kwazazzbai. Da zarar tanadi sai ka ji tayi dan ihu amma sai Huzaifa ya juyo ya dubeta ya dauke kai kawai ba ya kokarin taimakonta. Alhamdulillahi nan zan dakata sai Allah ya kaimu sati mai zuwa Insha Allahu za'a jini da ci gaban wannan Littafi. Bayan haka ina so nayi amfani da wannan dama na sanar da yan uwa kuma abokai aminai na wannan gida cewar mahaifin daya daga cikin dan uwan mu kuma abokin wato Safyanu wanda aka sani da Abban yara shine mahaifinsa bashi da lafiya yanzu haka an kwantar dashi a nan asibitin Nassarawa muna rokon yan uwa da kusa shi a cikin adduar ku. Muna fatan Allah ya bashi lafiya yasa tazama kaffara. Wadanda suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansu da rahama, wadanda kuma suke tare da mu Allah ya bamu ikon kyautata musu kuma ya rabamu da su lafiya. Ina yiwa kowa Fatan alkhairi. Wassalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuhu.**DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA BIYAR 5 PART E ✍️ ♥️ NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI🪖 Typing :- UMAR FAROUQ ZANGO✍️ Posting:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 Comments da likes da share... Haka suka dai suka ci gaba da yawo a cikin dajin Huzaifa na neman dabbar dajin da zai harba ko tsuntsu amma bai gani ba har ya zamana cewa duk su biyun sun gaji ainun kuma gashi rana ta kara takewa yunwa taishesu. Bisa dole suka sami wuri duka zauna suna hutawa da nufin koma da baya izuwa sansaninsu bayan sun huta din domin aci gaba da tafiya. Suna cikin wannan hali ne kwatsam! Suka hango wata katuwar kura a gabansu ta dira akan wani katon dutse wanda tazararsu da shi ba ta wuce taku goma ba. Kallo daya suka yiwa kurar suka gane cewar Lallai a cikin tsananin yunwa take domin sai haki take tana zazzago harshenta waje. Koda kurar ta dago kai tayi arba da su, su ma sukayi arba da ita sai Luhaira ta kurma uban ihu, saboda tsananin tsoro bata san saadda

Chapter 3 of 6