takama bayan huta ba ta rukunkumeshi, shi kuwa sai ya mike tsaye a hankali yana mai kurawa kurar idanu, itama kurar ta kura masa idanu tana gurnani shi kuma yana ta karanta wata addua a bakinsa don kada kofinta ya kamashi.
Huzaifa yana so ya daki idon kurar ya zare takobinsa amma sai ya ga itama kurar tana yunkurin ta shammaceshi tada ka tsalle ta diro kansu.
Nan dai aka ci gaba da kallan kallo tsakanin kurar da Huzaifa har tsawon yan daki. Daga can sai kurar ta dako tsalle a sama cikin shammace domin ta turmushesu a tare shi da Luhaira ta tafi can gefe daya kurar ta fado kansa shi kadai suka kacame da kokowa.
Su fada nan, su fada can, suka rinka dudufniya a kasa, kurar na kokarin kafa masa hakoranta a jikinsa shi kuma sai ya rinka gabza mata naushi a fuskar ta yana kawar da kanta.
A lokacin ne kurar ta rinka yakusar jikinsa da faratan hannayenta da kafafunta.
Nan fa duk su biyun shi da kurar suka fara gane kurensu domin ya hada nata jini da majiya a bakinta, idanunta da hancinta, ita kuna ta kakkarce masa sassan jikinsa jini na ta zuba.
Duk wannan abu dake faruwa Luhaira na zaune a kas gefe daya tana kallonsu kuma tana ta faman rusa ihu da kuka amma ta kasa tashi ta gudu saboda tsananin tsoro da firgitar da tayi.
Sai da aka shafe sama da saa daya ana wannan bakin gumurzu tsakanin Huzaifa da wannan kura, ya zaman cewa duk su biyun sun galabaita ainun amma saboda naci gami da Taurin zuciya kowannensu na kokarin hallaka dayan.
Koda kurar taga tayi iya kokarinta akan ta turmushe Huzaifa ta cinyeshi domin ta kawar da muguwar yunwar data addabeta sai ta sakeshi ta juyo izuwa kan Luhaira ta dako wawan tsalle a sama da nufin ta dira amanta ta turmusheta gashi a wannan lokaci Huzaifa ya galabaita ainun ya kasa mikewa da sauri ya ceci rayuwar Kuna Luhaira.
Koda Luhaira ta ga kurar nan ta dako tsalle zata dira akanta sai ta sulale kasa sumammiya saboda tsananin tsoro.
Ai kuwa sai Huzaifa gani yayi wata irin katuwar kibiya ta taho da gudu ta soki kirjin kurar ta bullo ta gadon bayanta.
Take kurar ta fado kasa Tim! Matacciya ko motsawa batayi ba.
Koda Huzaifa ya daga kansa sama ya dubi saitin da kibiyar tafito dai ya kame saboda tsanin mamaki wanda ya gani rine da kwari ya tunkaro inda yake.
Ba wani ya gani ba face gimbiya lafirat yar sarki shaaran ta kura masa idanu tana murmushi.
Cikin tsananin Farin ciki Huzaifa ya mike tsaye da sauri ya tareta ya budi baki da nufin yayi mata magana.
Koda taga yawan raunikan da ke jikinsa sai ta dimauce, bata san saadda ta kama kafadunsa ba ta zaunar dashi a kasa ta sa hannunta ta yage rigar jikinsa wacce dama tuni ta gama yayyagewa ta yi kaca kaca da jini.
Cikin hanzari lafirat ta dauko battar ruwan Shanta ta wanke duk jinin dake jikin Huzaifa sannan ta dauko garin magani ta fara shafa masa a jikin raunikan nasa.
A dai dai wannan lokaci ne Luhaira ta farfado daga sumun da tayi.
Koda ta bude idanunta taga Huzaifa zaune tare da lafrirat tana taba jikinsa tana shafa masa magani sai kawai taji kishi ya turnuketa, a sannane taji wani irin bau ya shigeta wanda ba ta san ko menene ba, kawai sai ta kurawa Huzaifa da lafirat idanu ba tare da su lura da cewar ta farfadoba.
A wannan lokaci ne Huzaifa yayi gyaran murya yace, yaje jarumar jarumai, yanzu ina kika nufa ne, kuma me kika sani dangane da abin da ya faru a filin yaki?
Koda jin wannan tambaya sai lafirat tayi murmushi tace, ai ni bani da wajen zuwa face farautar ka domin a halin yanzu bani da kowa cikin duniya sai kaitunda na rabi da ubana da yar uwata kuma na tsanesu kamar yadda na tasani mutuwa ta.
N hakura da kasaita ta haihuwa wato birnin shumbul, bani da sauran buri a duniya face na koma birninku na Darul Husuf inda zan karasa sauran rayuwata na bude sabon shafin rayuwa na yi aure na sami tawa zuriyar.
Bayan lafirat ta gama wannan jawabi sai ta kwashe labarin duk abinda ya faru a filin yaji ta zaiyane masa sannan tace, dama saboda na gamu da kai shi yasa na biyo wannan hanyar ta birninmu amma ko kadan bani da shaawar komawa cikin birnin shumbul har abada.
Lokacin da lafirat tazo nan a jawabin ta sai Huzaifa ya cika da tsananin Farin ciki bisa jin nasarar da suka samu a filin yaki.
Nan take shima ya ba ta labarin irin bakin gumurzu da sukayi a kurkuku kafin su fito da Dakarun musulunci daga kurkuku da kuma yadda aljani hurusul Marwas ya sha bakar wahala wajen kokarin dauko Luhaira a cikin gidan gonar sarki inda ya fafata kazamin yaki da wadansu mugayen zakwakuran aljanu guda dubu daya da dari daya da kyar ya samu ya hallakasu bayan ya kusan rasa tasa rayuwar.
Koda gimbiya lafirat taji wannan labarin sai ta kamu da tsananin Farin ciki bisa jin yadda aka tarwatsa mugun nufin mahaifinta akan dakarun musulunci da ya kama yatsare da kuma kyakkyawa Luhaira wacce yaci burin aurenta bayan ya kawar da birnin Darul Husuf.
Lafirat na cikin wannan Farin ciki sai kuma fuskarta ta juye izuwa tasananin damuwa ta sunkuyar da kai kas tayi shiru batace komai ba.
Alamarin da ya dugunzuma hankalin Huzaifa kenan ta dubeta cikin alamun tsananin damuwa yace, yake lafirat menene ya faru na ga kuma fuskarki ta sauya yanzu take cikin yanayin damuwa?
Koda taji wannan tambaya sai lafirat tayi ajiyar zuciya tace, wani labari mara dadi na samu a bakin wadan su fatake wadanda na hadu dasu a hanya a lokacin da na biyo hanyar zuwa birnin shumbul.
Naji wadannan fatale suna cewa sarki shaaran ya samu nasarar shiga har cikin birninku na Darul Husuf yaci shi da yaki.
Koda jin wadannan bayi sai Huzaifa ya mike tsaye zumbur a dimauce yace, kai karya ne abin ba zai taba yi yuwa ba ke nan domin na sam.cewa katangar birninmu tana da wani asiri na musamman tun zamanin iyaye da kakanninmu wanda babu wani kafiri sa ya isa ya shiga cikin birnin.
Lafirat ta gyada kai tace, ai bisa labarin da naji daga bakin fataken sun ce mutanen ku ne suka cire tsafin da ke jikin katangar birnin taku da hannunsa amma mahaifina ne ya yaudaresu yace yaci birnin shumbul da yaki kuma saboda murna ba zai shigo cikin birnin ba har sai ancike wadannan layu wadanda aka binne a karakshin katangar.
Ai kuwa ana cire layin ne shi da dakarunsa suka afka cikin birnin suka hau mutane da sara da suka.
Ance ankashe sama da mutane dubu dari uku da hamsin kuma gaba daya malaman garin da manyan fadawan sarki an kullesu a kurkuku.
Koda lafirat tazonan a labarinta sai Huzaifa ya murna uban ihu Kuma ya fashe da kukan bakin ciki yace, Lallai mahaifinki ya cutar da duk wannan nasara da nasamu ta karbo dakarunmu da dauko Luhaira sun zama a banza.
Ya zama wajibi yanzu mu garzaya mu tafi neman su sarki a duk inda suke domin mu san hanyar da zamu bi mu karbo birninmu.
Koda bama fadin hakan Sai Luhaira ta mike tsaye ta karaso gabansu ta dubi irin kibiyoyin da ke cikin kuttun da lafirat ta rataya a bayanta sai taga iri daya ne da kibiyar da ta soke wannan kurar da ta yi yunkurin kasheta, take ta gane cewar lafirat ce ta ceci rayuwata saboda haka sai dubeta tayi mata godiya sannan ta kama hannun Huzaifa akaron farko a rayuwarta ta jashi izuwa gefe ta dubeshi tace, ya kai wannan babban jarumi, kayi sani cewa ni yanzu na aminta da kai kuma nayi imani da duk abubuwan da kafada mini, amma taya ya kake tsammanin cewar zan ci gaba da da aminta da kai a cikin wannan hali kana tare da yar abokin makiyinmu wanda ya jefa rayuia cikin duhu ya rabani da komai da kowa nawa?
Menene ne tabbacinka cewar itama ba zata yaudareka ba, ta cutar da kai kamar yadda mahaifinta ya yaudari mutanen birninku ya cutar da su.
Ka tuna fa cewa karewa bata tayi gudu ba danta yayi rarrafe.
Lokacin da Luhaira tazo nan a zancenta sai hankalin Huzaifa ya dugunzuma ta rasa irin matakin da ya kamata ya dauka domin ya kasa tantancewa a tsakanin lafirat da Luhaira wacce ya kamata ya rike hannu biyu kuna yayi amfani da maganganunta?
Kawai sai ya dubesu duk su biyun yace, ku zo mu koma izuwa masaukinku domin mu yi shirin tafiya izuwa birnin Darul Husuf.
Ba tare da gardama kuwa Luhaira da Lafirat suka bi Huzaifa a baya da sauri suka nufi sansanin nasu inda suka ya da zango.
Da zuwansu sai Huzaifa ya bayar da umarni a kwashe kaya domin a ci gaba da tafiya.
Koda Humzalu da aljani hurusul Marwas suka ga Huzaifa ya dawo da gimbiya lafirat sai suma hankalinsu ya dugunzuma, haka ma sauran dakarun musulunci.
Yayin da Huzaifa ya fahimci halin da kowa ke ciki sai ya dubesu gaba daya yayi murmushi sannan yace, Yaku yan uwana kuyi sani cewa yanzu lafirat ba abar kyama bace a cikinmu domin kuwa yar uwarmu ce addinin musulunci.
Ta hakura da iyayenta, da danginta da kasarsu kuma ta zabi takoma cikinmu inda zata karasa sauran rayuwarta.
Ina mai tabbatar muku da cewa lafirat bayar da gagarumar gudunmawa a yakin da muka fafata da mutanensu kuma yanzu ma ta ceci rayuwarmu ni da Luhaira a cikin dajin daga sharrin wata muguwar kura tafin da muke yin farauta.
Bugu da jari kuma tazo ta sanar da ni halin da birninmu yake ciki na Darul Husuf wanda shine dalilin da yasa yanzu na ce mu gagauta shirin tafiya.
Nan dai Huzaifa ya zaiyane musu duk labarin da Lafirat ta zo musu da shi.
Koda jamaa suka ji wannan batu sai hankalin kowa ya dugunzuma, wasu suka fara kuka da bakin ciki, wasu kuma suka kama yiwa yan uwansu adduar Allah ya jikansu domin sunji a jikin su cewar mutuwa ta dauke su.
Haka dai aka shirya aka kwashe kaya gaba daya aka ci gaba da tafiya cikin sanyin jiki, rashin kuzari da alhini.
Ana fara tafiyar ne Luhaira ta kama yin hamma sakamakon yunwar da take ji. Shi kuwa Huzaifa saboda yana cikin tsananin bakin ciki da har zuciyar sa ji yake tana tafarfasa kamar zata kone ya ma daina jin yunwar, yayin da lafirat da lura da halin da Luhaira take ciki sai ta matso da dokinta kusa da na Luhaira sannan ta bude jakarta tafiddo gasasshen nama n wani tsunsu ta miko mata.
Ciki matukar murna gami da godiya ta karba. Har ta yagi naman zata kai bakinta sai ta tuna cewar Huzaifa ma bai ci komai ba kawai sai ta raba naman duka kaso biyu tamikawa Huzaifa.
Huzaifa ya kau da kai yace, bazan iya cin komai ba har sai na sadu sarki naga lafiyarsa.
Koda jin haka sai itama Luhaira tafama cin naman ta daureshi taje fashi cikin jakarta da ke bisa kan dokinta. Ashe lafirat ta lura da ita, nan take itama taji kishi ya turnuketa tace, a cikin zuciyar ta.
Yanzu kenan itama wannan yarinyar tana kaunar yarima kamar yadda nake sonsa har ma ta kai cewa ba zata iya cin abinci ba saboda shima bai ci ba?
Ni kuwa zan zuba ido na ga iyakar adalcin Huzaifa.
Ni dai nasan cewa dani ya fara yin soyayya to yanzu zai rabu da ni ne ya kama Luhaira ko kuwa ni zai kama ya rabi da ita?
Tana cikin wannan Hakane taga aljani hurusul Marwas ya saki fuka fukinsa ya sauko kas kasa dag da Huzaifa ya dubshi yace ya shugabana kayi sani cewa idan kai zaka iya jure yunwa ta Tsawon lokaci to wadannan yan matan biyu bazasu iya ba. Saboda na lura duka su biyun suna cikin yunwa amma kuma saboda kaki cin komai suma sunki yadda suci komai.
Koda jin haka sai Huzaifa ya dube su duka su biyun ya danyi jim daga can kuma sai ya bada umarnin a tsaya aci abincin kowa da kowa.
Alhamdulillahi anan zan dakata sai kuma Allah yakaimu sati maizuwa inda zakujini da karshen wannan Littafi wanda Insha Allahu nake sa ran cewa a rana itayau zamu kawo karahensa gaba daya.
A madadin mutanen wannan gida mai albarka muna mara yiwa Safyanu Abban yara gaisuwar mahaifinsa bisa rashin lafiyarsa duk da cewar mun hadu da shi a ranar laraba ya shigo unguwar mu wajen yayarsa mun hadu da shi kuma ya fada min cewa ai an sallamesu a asbitin sun koma gida.
Don haka a madadin sa ina yiwa mutanen wannan gida godiya bisa addu'o'i da kuka dinga masa muna godiya ubangiji Allah ya bar zumunci kuma Allah ya kara hada kawunan mu.
Allah kuma ya kara masa lafiya da sauran mutanen da ke kwance a gida ko asibiti.
Ni UMAR FAROUQ ZANGO nake muku Fatan alkhairi sai Allah ya hadamu a sati mai zuwa inda zamu karkare wannan Littafi kuma Insha Allahu kawai tambayoyin da zasu biyo baya, idan mun kammala shi wannan Littafi ina muku Fatan alkhairi.**DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA BIYAR 5
PART LAST CHAPTER ✍️✍️🙏
NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI👮👮
TYPING:-UMAR FAROUQ ZANGO✍️✍️
POSTING:- Najibullahi Muhammad 🥷🥷
KARSHEN LITTAFIN 👇👇👇
Tsayawarsu ke wuya sai aka zubawa Huzaifa da lafirat da Luhaira abinci a kwano guda koda fara cin abincin sai ke da wuya sai Huzaifa yayi shiru ya kasa ci gaba da cin abincin, yayin da ya fada cikin kogin tunani, koda lafirat ta dago kai ta lura da halin da ya shiga sai ta dan girgiza kafadarsa, koda ta girgiza kafadar tasa sai yayi ajiyar zuciya, cikin damuwa ta dubeshi tace, ya kai gwarzona shin wanne irin tunani kake haka wanda har ya hanaka ci gaba da cin abincin.
Koda jin wannan tambaya sai ya sake yin ajiyar zuciya a karo na biyu sannan yace, ki sani yake lafirat cewa ni yanzu gaba daya babu abinda ke min dadi, babu abinda nake tunani face halin da jamaar birninmu suke ciki sannan kuma ga tunanin halin da sarki da kuma dan uwana ukashat yake ciki, tabbas mahaifinki ya cutar damu matuka sosai, yayi mana babbar illa mai wuyar gyarawa.
Koda jin haka sai tayi ajiyar zuciya tace, tabbas abinda ka fada hakane, amma kada ka manta da cewa a kullum ubangiji yana bayan gaskiya, kuma komai daren dadewa gaskiya itace take yin nasara kuma mai gaskiya shine yake yin nasara matukar yayi hakuri kuma ya jure duk wata musiba da wata jarrabawa data fado masa.
Yayin da shi kuma ramin karya kurarrene, kuma mulki da Zalunci baya dorewa, wata rana sai an wayi gari babu mulkin kuma babu mai mulkin, haka zalika kuma karyar itace zata kaishi kasa kuma ta zamo abokiyar gabarsa.
Koda jin haka sai Huzaifa yayi ajiyar numfashi yace, tabbas zancenki gaskiya ne. Sai ta kuma kallonsa cikin damuwa tace, ni Yanzu gaba daya nasan cewa mutanen ku ba lallai su yarda dani ba kasancewar ni yar babban makiyinku ne. Amma kuma basu san cewa ma tsani mahaifin nawa ba kamar yadda na tsani mutuwata, tabbas ina cikin fargaba domin kuwa gabana tsinine bayana kuma siyaki.
Koda jin haka sai Luhaira ta ce to ai nice babbar abar tausayi tunda ke kin san asalinki da mahaifarki, to ni fa ban san kowa ba sai haidaman da suke hidima a cikin gidan gonar sarki.
Kuma ban san komai ba na alamuran rayuwa, wai shin mai wannan kalmar take nufi da kikace gabanki tsini bayanki kuma siyaki.
Koda jin wannan tambaya sai ta doka mata harara tace ai dama ke jahilace rainon gidan gona shi yasa bazaki san abinda ake nufi da hakan ba.
Koda fadar hakan sai lafirat ta mike tsaye ta barsu a gurin. Tabbas kishi ne yasa ta fadar hakan, kuma shima Huzaifa ya lura da hakan, sai dai kuma abinda ta fadawa Luhaira bai masa dadi ba, haka itama Luhaira kalmar ta yi mata zafi.
Haka dai aka gama cin abinci sannan aka kwashe kaya aka kimtsa sannan aka ci gaba da tafiya a wannan karon ma babu wani mai yin magana ko surutu, saboda gaba daya kowa ka ganshi hanlinshi ya dugunzuma kawai so ake aje birnin Darul Husuf domin a ga halin da birnin ke ciki, kuma aga lafiyar sarki.
* * * * * *
Al'amrin sarki shaaran da gimbiya Sazirat da tawagarsu kuwa, tunda suka fito daga birnin Darul Husuf suka nausa cikin daji basa tsayawa sai idan sunji yunwa ko kuma idan dare yayi, kai koda daren yayi indai ansamu hasken Farin wata to fa basa tsawaya. Haka suka ci gaba da tafiya ba sassauci su kwana nan su tashi can har sai da suka karaso kofar birnin shumbul.
Tun daga nesa sarki shaaran yaga wasu alamomi wanda bai saba ganinsu ba a cikin birnin yayinda yayi tafiya ko kuma yaje yaki ya dawo.
Kawai sai ya kalli Sazirat yace shin baki ga wasu bakin lamura ba daga cikin birnin mu ba?
Koda jin wannan tambaya sai Sazirat ta daga kanta sama ta kalli cikin birnin sannan tace, na lura da cewar kamar tutar dake kan tsakiyar ginin kurkukun birnin babu ita. Tabbas akwai wani babban alamari da ya faru a bayan baka nan.
Koda jin haka sai sarki shaaran ya bayar da umarni a tsaya da tafiyar.
Sannan sai ya sauka daga kan dokin sa shi da Sazirat suka ci gaba da tafiya a kafa har suka kusanci kofar birnin shumbul sosai amma kuma sai ya zamana cewa sun buya a cikin duhuwar ciyayin gurin ta ta yadda babu mai iya ganinsu.
Sannan sai sarki shaaran ya fiddo da mudubin tsafinsa ya shafeshi da hannunsa na hagu, yana mai karanta wasu dalasiman tsafi, take kuwa duk abinda ya faru a cikin birnin ya bayyana a cikin mudubin tsafin, tun daga lokacin da aka kai Huzaifa gaban wakilin sarki a matsayin tsohuwar mata, har zuwa lokacin da suka sami nasarar shawo kan tsoho Humzalu, da kuma shiga gidan kurkuku da nasara da suka samu a gidan gonar sa har hurusul Marwas ya dauko Luhaira. Kawo izuwa fitowarsu daga cikin birnin.
Koda gama ganin wannan alamari sai nan da nan sarki shaaran ya kamu da bakin ciki mai tsanani, bai san saadda ya mike tsaye da gudu ba ya durfafi masu gadin kofar birnin ya hausu da sara da suka. Da kyar Sazirat ta dakatar da shi sannan ta dubeshi cikin takaici tana cewa, ya kai abbana saboda me zaka huce haushinka akan dakarunmu.
Cikin fushi sarki shaaran ya dubi Sazirat yace, ai kwada ki barni na karar da wadannan marasa amfanin, tunda har zasu iya barin abokin gabarmu ya shiga cikin birninmu yayi mana barna ba tare da sun iya dakatar da shi ba.
Koda jin haka sai Sazirat ta kamashi ta jashi gefe daya, suka bar bakin kofar birnin suka yi tafiya mai nisa har aka daina hangosu.
Sannan suka samu guri suka zauna, tsawon yan dakiku dayansu bai ce komai ba.
Daga can sai sarki Shaaran ya dubi Sazirat yace, yake yata Yanzu menene abinyi, tunda kinga dai yanzu makiya sun sami nasarar shiga birnina kuma har cikin kurkukuna da gidan gonata sun sami nasarar kubutar da dakarunsu da kuma yarinyar da nake ta kwadayin na aureta.
Koda jin wannan tambaya sai Sazirat ta sake fadawa cikin kogin tunani, daga can sai ta dago kai ta kalli sarki shaaran tace, ina da wata dabara ko shawara guda daya.
Cikin sauri sarki shaaran yace fadamana ita muji kafin nima na fadi abinda nayi tunani da kuma hukuncin da na yake a raina.
Koda jin haka sai Sazirat ta sake ajiyar numfashi tace, ni a ganina kada mu shiga cikin birnin nan yanzu, mu koma da baya cikin daji mu sami nutsuwa daga nan sai mu aika da gorin gayya izuwa kasashen wannan nahiya tamu musamman wadanda sukayi imani da tsafi, mu nemi taimakon dakarunsu, kuma muyi musu romon baka muce duk kasar da ta bamu Aron dakarunta kuma mukayi nasara a wannan yaki to duk zamu hada kai mu yaki duk wata kasa da take irin addinin mutanen birnin Darul Husuf, kuma kowanne sarki zai samu kaso mai tsoka a cikin birnin zama a iya bashi mulkin rabin birnin.
Ina ganin idan mukayi hakan zamu samu damar tara dakaru masu tsananin yawa sannan kuma mu hada da namu na cikin gida ka ga babu ta yadda sarki uwaisul karni da jamaarsa zasu sami nasara akanmu.
Koda jin wannan shawara sai Farin ciki ya lullube sarki shaaran ya buhse da dariya, sannan yace, tabbas tunanina da naki sunzo daya, nima irin abinda na yanke kenan tabbas idan har muka sami wannan nasara to birnin Darul Husuf nakine.
Koda gama fadin hakan sai ya rungume Sazirat cikin tsananin Farin ciki, nan ya kuma tarawa da ita sukayi lalatar su.
Suka tashi suka koma can inda suka baro sauran dakarun da suka taho da su daga birnin Darul Husuf bayan sunci birnin da yaki kuma sun bar jiran gari a hannun mahaifiyar ukashat wato gimbiya muzaira.
* * * * * *
A can kofar birnin Darul Husuf kuwa, bayan gari ya waye sai sarki uwaisul karni ya tattara gaba daya dakarunsa guri daya, sannan ya dubesu cikin kwarin gwiwa yace, yaku dirkokin birnina hakika an samu maci amana a cikin birnina wanda aka hada kai dashi aka zubar da jini a cikin birninmu. Dole mu dage da addua kuma mu jajurce wajen ganin mun kwato birninmu daga hannun makiya, don haka na bayar da umarni kowa ya gyara damararsa domin kuwa gobe ne zamu je izuwa cikin birnin don kwatar birninmu a hannun makiya Allah.
Babu gudu kuma babu ka da baya koda kuwa za'a karar damu gaba daya.
Koda jin haka sai aka shiga kwalla kabbara, sannan aka shiga shirye shiryen fara yaki.
Kashe gari kuwa da safe kowa ya shiriya akayi sahu sahu ana jiran fitowar sarki uwaisul karni, ganin ya dade bai fitoba ne wakilin sarkin yakin Darul Husuf ya tafi izuwa ga tantin sarki uwaisul karni, yana zuwa yayi sallama ya shiga ciki ai kuwa da shigar sa sai yaga sarki uwaisul karni ya kalli gabas yayi sujjada yana tayiwa Allah kirari akan ya basu nasara akan abokan gaba.
Bayan wasu yan dakiku sai sarki uwaisul karni ya dago daga sujjadar sannan ya kara daga hannu nanma yayi addua sannan ya shafa.
Sai ya juyo ya kalli wakilin sarkin yaki, sai wakilin sarkin yakin yace ya shugabana dakarunmu duk sun shirya kai kadai ake jira.