Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels **DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA BIYAR 5 PART A ✍️ ✍️ ✍️ NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI👮 TYPING:-UMAR FAROUQ ZANGO✍️✍️ POSTING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 ASLM, bayan tsokacin da dakatawar posting din Dakarun Musulunci insha Allah a yau zamuci gaba, Muna fatan Allah ya taimakemu 🙏🥰♥️♥️ Duk sa'adda Huzaifa ya sami nasarar saran jikin katon mutumin ko ya sokeshi da takobinsa sai yaji kamar dutse ya doka ko kwarzanewa jikinsa baya yi sai dai kaga tartsatsin wuta na tashi. Wannan barandami na mutumin kuwa, duk abinda ya sama dashi sai ya rabe gida biyu walau dutse ko karfe. Duk irin zafin naman Huzaifa da tsananin jarumtakarsa sai yaga duk sun zama na banza domin katon ya ninkashi a komai. In ba don ma yana da mutukar kwarewa ba da iya yaki da tuni katon yayi masa kwaf daya. Suna cikin wannan bakin gumurzu ne katon ya shammaci Huzaifa ya gabza masa naushi fuska. Saboda karfin naushi sai da Huzaifa yayi sama ya gwaru da jikin bango a lokacin da wani gudan jini yayi fitar burgu daga cikin bakinsa ya fado kasa a mutukar galabaice takobinsa ma sai ta subuce daga hannunsa ta fado kasa. Koda ganin abinda ya faru sai aljani huraisul Marwas ya fusata ainun ya bude fuka fukansa ya kawowa katon mutumin suka a kirji da wani mashinsa na yaki. Kawai sai katon ya tare sukar da tafin hannunsa. Take mashin ya narke ya kama diga kasa tamkar ya kwana dari a cikin wuta yana damuwa. Cikin zafin nama katon ya kaiwa hurusul Marwas mangari da hannunsa guda, ai kuwa sai yayi Saar samunsa a fuka fukinsa na hagu. Kamar an cilla tsakuwa haka hurusul Marwas ya fada can baya ya gwaru da bango ya fado kasa sumamme sakamakon karyewar fuka fukinsa. Koda katon ya ga wannan nasara da ya samu sai ya bushe da dariya mugunta sannan ya juya izuwa kan yarima Huzaifa yaje kansa ya tsaya ya raba kafafunsa kuma ya sunkuyo da nufin ya kama kan Huzaifa ya murde masa wuya. Ashe a dai dai wannan lokaci hunzalu na ta yiwa Allah kirari yana neman ya karfafeshi da karfin da zai iya taimakon su Huzaifa. Ai kuwa nan take yaji wani gagrumin karfi ya shiga jikinsa, kawai sai gani yayi ya daka tsalle daga inda yake ya dira akan wannan garjejen kato. Kafin katon ya kamo kan Huzaifa da hannayensa tuni hunzalu ya naushi gadon bayansa. Saboda tsananin karfin naushi take gadon bayan katon ya burme, sai ga hannun hunzalu ya Faso ta cikin katon. Yana zare hannunsa sai katon ya sulale kasa matacce, ji kake Tim! Tamkar giwa ce ta fadi. Shi kansa hunzalu bai san saadda ya kame ba kamar gunki saboda tsananin mamaki bisa ganin wannan gagarumar jarumta da yayi. Kawai sai yaji tsoron Allah da kaunarsa sun karu ainun a cikin ransa, bai san saadda idanunsa suka ciko da kwallah ba suka fara zubar da hawayen murna. Huzaifa da aljani hurusul Marwas kuwa, kasa motsawa sukayi saboda tsananin alajabi sai bayan yan dakiku sannan Huzaifa ya mike tsaye ya dubi hunzalu cikin murmushi yace, ya kai hunzalu kayi sani cewa wanda duk ya yi imani da Allah kuna ya dogara da shi bisa dukkan lamuransa to fa babu abinda zai gagareshi a doron kasa. Tabbas imaninka da tsoronka ga Allah ne suka sa ka sami wannan gagarumin karfi har ka sami nasarar kashe wannan katon ka ceto rayuwarmu. Ni da hurusul Marwas kuwa ajizanci ne irin na dan Adam yasa muka shaafa da ci gaba da neman taimakon Allah, a lokacin da muke yin yaki da wannan kato, shi yasa muka masa samun nasara a kansa. Koda Huzaifa yazo nan a zancensa sai yaji ana ta kiran sunansa a bayansa. Koda ya waiga da sauri sai yaga ashe ba wasu bane face dakarun garinsu wadanda ke cikin wannan daki a kulle, su duka sun zo bakin kofar dakin sun tsaitsaya wacce take a kulle da katon kwado kuma an yi tane da sandunan karfe mai kauri. Nan take Huzaifa ya sunkuya ya dauki takobinsa ya tofa mata wata addua sannan ya dagata sama ya sare kwadon mukullin da aka rufe kofar da shi. Take kwadon ya fadi kasa kofar ta bude, sai dakarun suka fito waje gaba dayansu cikin tsananin farinciki suna yiwa Allah godiya gami da yiwa Huzaifa jinjina. Nan dai aka dunguma da nufin a fice daga cikin kurkukun gaba daya amma sai Huzaifa ya tsaya cak! Sakamakon aljani hurusul Marwas a kwance yana nishi ya kasa tashi. Cikin kaduwa Huzaifa ya ruga gareshi ya durkusa a gabansa yace, ya kai dan uwanavv menene ya sameka ka kasa tashi kana ta nishi haka? Hurusul Marwas ya budi baki da kyar yace, shi baka ganin yadda fuka fukina na hagu ya kumbura bane? Ai na karye ne kuma ba zan iya koda motsawa ba daga nan face an gyara mini wannan karaya. Koda Huzaifa ya dubi fuka fukin ya ga yadda ya karye kuma ya kumbura sumtum! Sai hankalinsa ya dugunzuma domin bai san yadda ake DOA aljanu ba yayin da suka karye. Huzaifa ya dubi aljani hurusul Marwas yace, yanzu menene abinyi? Kaga dai inda zamu taru mu duka nan ni da dakarun nan da muka ceto rayuwarsu ba za mu iya daukarka ba sannan kuma bamu san yadda ake gyara karaya ba irin taku ta aljanu. Koda jin wannan batu sai aljani hurusul Marwas yayi murmushin karfin haki yace, ai batun gyaran karayarmu iri dayane da naku, kawai yanzu ku garzaya ku samo itatuwan bishiya masu kauri gami da danyar jijiyar bishiya kuzo ku gyara karayar da sauri kafin abokan gaba su zo su afka mana domin na san cewa nan da zuwa wani lokaci akilin sarki shaaran zai iya samun labarin halin da kurkuku ke ciki aboda tsegumi irin na yan uwana aljanu. Yanzu ma karfin addu'armu ne ya hana aljanun dake yaso munafunci zuwa kusa da nan bare su san halin da ake ciki. Koda jin wannan batu sai Huzaifa ya umarci wasu daga cikin dakarun na musulunci da su ruga suje u samo manyan itatuwa da danyar jijiyar bishiya. Nan da nan kuwa dakarun suka cika umarni. Lokacin da aka zo da abubuwa biyun sai aljani hurusul Marwas ya dubi yarima Huzaifa yace, ina mai baku shawara daku samo murtukekiyar sarkar karfe ku fara daure hannayena, kafafuna da wuyana kasa cikin dirkoki in ba haka ba kuwa gyaran karayar nan ba zai yiwu ba. Koda jin wannan batu sai yarima Huzaifa yayi murmushi yace, hakika aikin mai shawara baya baci. Aaje a samo irin sarkokin da ake daure fursunonin aljanu a gidan nan, sannan vkuma ina son muci gaba da yin adduoi gaba dayanmu domin Allah ya hana abokan gabarmu zuwa nan harmu kammala duk abinda muka zo yi. Nan take kuwa akayi amfani da wannan umarni. Bayan an samo wata murtukekiyar sarkar karfe an daure hanaye, kafafu da wuyan aljani hurusul Marwas a jikin wadan su manyan dirkokin gini, sai hurusul Marwas ya sake bayar da shawara a toshe bakinsa da tsummokara a daureshi tamau. Wannan shawara ma ba ayi biris da ita ba,, koda aka fara gyara karayar fuka fukin nasa kuwa yaji wani irin mugun radadi da zugi sai ya yunkura cikin azabbaben karfi, ya kwarara uban ihu. Da yake bakinsa a toshe yake sai ihun ya zamo kamar an busa bututun algaita, amma duk da haka sai da karar sautin ta cika birnin shumbul gaba daya ta firgita komai da kowa. Motsawar da yayi kuwa, sai da gaba dayan ginin gidan kurkukun yayi girgiza kamar zai rushe. Cikin hanzari Huzaifa da sauran jamaarsa suka daka tsalle suka dira akan hurusul Marwas suna kokarin danneshi. Duk da haka sai suka kasa ladaftar da shi domin da zarar ya yunkura sakamakon zafin da yake ji na gyaran karayar sai kaga ya watsar da su kasa tamkar busassun ganyayen bishiya na zubowa kasa. * * * * * * A can gidan sarautar sarki shaaran kuwa, lokacin da wakilin sarki da sauran jamaar asa suka jiyo sautin ihun aljani hurusul Marwas dai suka rude kuma suka cika da tsananin mamaki domin basu taba jin wani sauti ba makamancinsa a cikin garin. Nan take wani babban badakare ya dubi wakilin sarki yace, ya shugabana anya kuwa ba abokan gabarmu mune suka shigo cikin garin nan bamu sani ba suka fara yi mana yakin sunkuru? Koda jin wannan tambaya sai wakilin sarki shaaran ya dakawa badakaren tsawa yace, hana wannan wacce irin maganar banza kakeyi ne haka? Ta yaya abokan gaba zasu iya shigowa cikin garin nan ba tare da mun sani ba alhalin ka san cewa a ko ina kuma dare da rana aljannunmu masu gadin birnin nan suna sintiri suna kewaya garin? Badakaren ya numfasa yace, ya shugabana ni fa alamarin mutanen nan maabota addinin musulunci yana bani tsoro saboda suna da matukar karfin sihiri. Ka tuna cewar bamu taba jin irin wannan sauti ba a garin nan sai wannan karon, kuma mutum ba zai iya fitar da wannan sauti ba sai dai gawurtaccen jarumin aljani kamar irin aljanun da suje gadin kurkukun sarki da gidan gonarsa. Ni dai ina mai bayar da shawara ka tura dakaru suje su gano halin da kurkukun yake cikin da kuma gidan gona don kada makiya su zo su shammacemu. Saadda wakilin sarki yaji wannan batu sai ya gyada kai yace, hakika aikin mai shawara baya baci, amma ai na san cewa babu ta yadda za'ayi makiya su iya shigowa cikin garin nan ba tar da asirinsu ya tonu ba saboda irin kwararan matakan tsaron da sarki ya dauka. Koda gama fadin hakan sai wakilin sarki ya dubi wannan badakaren yace dashi yayi sauri ya hau dokinsa ya tafi izuwa kurkuku ya gano halin da yake ciki, sannan kuma ya wuce izuwa can gidan gonar sarki can ma ya gan ko akwai wata matsala. Nan take kuwa badakaren ya hau dokinsa ya zabureshi da gudu ya nufi hanyar da zata kaishi kurkukun. * * * * * * A can kurkuku kuwa, cikin gaggawa su Huzaifa suka gama gyaran karayar aljani hurusul Marwas sannan Huzaifa ya bayar da wata addua ta musamman yace kowa yayi ta biyata a cikin zuciyarta sannan ya umarci humzalu da yayi musu jagora izuwa gidan gonar sarki. Nan take kuwa suka hau dawakansu su duka suka fice daga cikin gidan kurkukun suna ta karanta wannan assay addua da Huzaifa ya basu suna ta wuce gawarwakin dakarun dake tsaro gaba daya. Sai a wannan lokacine ragowar dakarun kurkukun da ke can kofofin farko na shigowa suka ankara da abinda ke faruwa, suka ruga da gudu izuwa kan su yarima Huzaifa da nufin su kashe su. Nanfa aka rugumtsume da sabon azabbaben yaki. Da yake wannan karon su Huzaifa na tare da dakarun musulunci sai nan da nan suka sami nasarar yakin. Koda tsirarun dakarun suka ga saura su yan kadan sai suka zubar da makamansu suka fara yunkurin guduwa. Cikin daga murya Huzaifa ya bayar da umarnin kada a bari dayansu ya tsira ya gudu daga cikin kurkukun. Aikuwa sai dakarun musulunci suka rinka kurewa dakarun kurkukun gudu suna rafkesu. Nan da nan aka karar dasu gaba daya. Faruwar haka ke da wuya sai aka sake hawa dawakai da nufin a tafi izuwa gidan gonar sarki. Har an iso baki kofar fita daga kurkukun sai wani tunani ya fadowa Huzaifa kawai sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak sannan ya dubi hunzalu da sauran dakaru na musulunci ya ce, ba zamu iya tafiya ba izuwa gidan gonar sarki a haka ba dole ne mu yi bad da kama muyi shiga irin ta dakarun sarki shaaran yadda ko akan hanya babu mai taremu. Wasu daga cikinmu kuma dole ne su yi shiga ta bayi sannan ina son mutum hudu daga cikinku wadanda zasu iya kundunbala su tsaya a bakin kofar kurkukun nan a matsayin masu gadi a cikin shigar masu gadin domin jikina ya bani cewa a ko Yaushe wakilin sarki shaaran zai iya turo mutanensa domin su zo su ga halin da kurkukun nan ke ciki. Yanzu su waye zasu iya yin wannan kundunbala mu barsu anan kofar kirkir koda dai sun mutu sun san cewa shahada sukayi? Kafin Huzaifa ya rufe bakinsa tuni gaba daya dakarun sun budi baki cikin hadin murya kowa dacewa shi ya amince. Koda jin haka sai Farin ciki ya kama Huzaifa ya dubesu yace, hakika duka imaninku ya inganta domin dukka musulmi na gari yana da burin shahada. Koda gana fadin hakan sai nan da nan aka shiga shirye shiryen sauya tufafi. Cikin kankanin lokaci kowa ya gama komtsawa. Aljani hurusul Marwas ne kadai bai yi shiga irin ta dakarun shaaran ba a matsayinsa na aljani. Take aka bar mutum hudu a bakin kofar kurkukun suka yi tsayuwa irin wacce masu gadin kurkukun ke yi koda Yaushe. A sannane Huzaifa da sauran dakarun suka tusa keyar dakarunsu da suka yi shigar bayi suka gaba, hunzalu ne akan gaba cikin shigar dakarun birnin yana yi musu jagora, Huzaifa na daga can bayan karshe. Suna cikin wannan tafiya ne suka yi kicibus da wannan badakare wanda wakilin sarki shaaran ya turo shi kurkukun domin yaga halin da kurkukun ke ciki. Koda ganinsa sai wani daga cikin dakarun musulunci ya yunkura zai zare wuka ya kasheshi, amma sai Huzaifa ya yi masa inkiyar ya kyaleshi. Lokacin da badakaren ya karaso dag da su ya ga ashe hunzalu ne ke jagorantar wadannan bayi sai ya risina cikin girmamawa ya gaisheshi yace, ya shugabana daga ina kuke haka, kuma ina zaku kai da wadannan bayi haka? Koda jin wannan tambaya sai hunzalu ya dubi badakaren yace, daga kurkuku muke kuma gidan gonar sarki zamu kai wadannan fursunoni domin su canji maaiakatan can kamar yadda aka sabayi kullum. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama badakaren yace, haba ya shugabana ta yaya zaka debo fursunoni daga kurkuku ka kaisu can gidan gonar sarki alhalin kafin sarki ya taci yaki ya kafa doka mai tsauri cewar babu mahalukin da zai sake shiga ko fita daga cikin kurkuku da gidan gonarsa? Yanzu haka ma wakilin sarki ne yace na zo na ga halin da kurkukun ke ciki sannan na wuce izuwa can gidan gonar tasa, can ma na ga lafiyar sa. Saadda badakaren yazo nan a zancensa sai yaji hunzalu ya bushe da dariya. Lokaci guda kuma ya turbine fuskarsa ya daka masa tsawa yace, ina hankalinka ya taci ne? Shin kana zaton zan aikata abinda zai bata ran sarki ne alhalin na san cewa ko yaya nayi wani kuskure sawa zaiyi a kashe dana guda daya dake tare a inda ban sani ba? Ka sani cewa ni ne mai kula da aiyukan gidan gonar sarki idan aikin gonar sarki ya tsaya ko aka sami wata matsala yana dawowa zai hukuntani. Ka ga ni yanzu kana bata mini lokaci kuma kana batawa kanka lokaci gwara ka tafi izuwa Aiken da aka yi maka. Koda gama fadin hakan sai hunzalu ya bangaje wannan badakaren ya wuce gaba ayarin su Huzaifa suka take masa baya. Da yake duk u Huzaifa suna sanye ne hulunan karfe ne badakaren bai ga fuskar dayansu ba bare ya gane cewar ba dakarun kasar bane, amma sai ya tafi yana waigensu cikin alamun mamaki da rashin yarda. A wannan lokaci aljani hurusul Marwas na can sama cikin gajimare yana bin su Huzaifa kuma yana karanta dduar da Huzaifa ya bayar dalilin da ya sa sauran aljanun dake shawagi a sararin saman garin suka kasa ganinsa ke nan kuma suka kasa ganin su Huzaifa. Lokacin da su Huzaifa suka ci gaba da tafiya sai wani badakare dake kusa da Huzaifa ya dubeshi cikin girmamawa yace, ya shugabana me yasa ba ka barni na kashe wancan badakaren ba dazu? Kayi sani cewa barinsa a da rai a garemu ba karamin ganganci bane domin ga dukkan alamu bai yarda da mu ba, kuma zai iya zuwa ya kai labarin mu ga wakilin sarki shaaran can fada a turo mana mayaka masu yawa su kawo mana hari. Saadda Huzaifa yaji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya sannan yace, tabbas abinda ka fada gaskiya ne, to amma kuma kashe shin shine abu mafi hadari a garemu domin idan wakilin sarki ya ga ya dade bai koma ba zai turo abu sawunsa kuma idan aka zo aka ga gawarsa za'a gane cewar mun shigo cikin garin sai abi sawunmu har can gidan gonar a tarfa mu. Yanzu kuwa idan yaje kofar kurkukun yaga dakarunsu a tsaye babu alamar wata matsala zai juyo ne ya biyomu izuwa can gidan gonar sarki, kafin ya riskemu kuma tuni mu munje mun dauko luhaira. Koda Huzaifa yazo nan a zancensa sai gaba daya dakarun suka gamsu da bayaninsa kuma suka cika da tsananin mamakin irin basirarsa da yadda akayi ya shirya wannan dabara. Alhamdulillahi nan zan da kata sai Allah ya kaimu sati mai zuwa zaku jini dauke da ci gaban wannan labari. Sunana Umar Farouq Zango nake muku Fatan alkhairi sai mun hadu a ranar jumaa idan Allah ya kaimu.🙏🙏🙏🙏**DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA BIYAR 5 Part B ❤️ ♥️ NA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI👮👮 Typing:- UMAR FAROUQ ZANGO.✍️ Posting:- Najibullahi Muhammad 🥷🥷 Haka dai suka ci gaba da tafiya har tsawon kusan rabin sa'a sannan suka iso kofar gidan gonar sarki. Tun daga mesa gabansu ya fadi sakamakon hango irin tsananin tsaron da ke gidan gonar, wanda ya ninka na kurkukun sau goma. Nan take zuciyoyinsu suka karaya suka tabbar da cewar babu yadda za'ayi su shiga cikin wannan gidan gona cikin irin Saar da nasarar da suka samu a can kurkuku kuma komai zai iya faruwa ko dai su rasa rayuwarsu ko kuma a dade ana gumurzu har wakilin sarki ya san da zuwan su azo ayi musu rubdugu. Koda yarima Huzaifa ya gama aiyana wannan alamari sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi ya fara shawara da zuciyar sa. Abin da ya fado masa a rai shine, idan har basu sami damar shiga cikin gidan gonar ba kai tsaye har su gano inda Luhaira take a cikin kankanin lokaci ba duk shirin su ya wargatse. Har suka karasa daf da kofar gidan gonar Huzaifa bai sami wata mafita ba. Da isowarsu sai dakarun dake tsaron kofar suka dakatar dasu. Shugaban masu gadin ya dubi Hunzalu a fusace yace, menene ya kawoka nan tare da bayi kalilan da kuma dakaru masu yawa haka? Koda jin wannan tambaya sai zuciyar sa ta buga da karfi, tsoro ya baibayeshi ya firgita ainun domin yana ganin cewa asirinsa ya tonu amma sai ya yi ta maza ya dakawa shugaban masu gadin tsawa yace, shin ka manta da wanda kake maganane? Ka manta da cewar nine mai kula da dukkanin bayin dake aiki a cikin gidan gonar nan fiye da shekaru talatin baya har ma sai da dana yazo ya gajeni? Koda jin wannan batu sai shugaban masu gadin ya bushe da dariyar mugunta, lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa yace, ai duk maganar da kake yi alamarin ne na da wanda ya wuce. Shin ka manta ne da cewar dan naka daya gajeka Yanzu haka baya kan aikinsa kuma an sare masa hannuwansa da kafafunsa kuma antsire idamunsa sakamakon laifin da ya aikata na kusantar amaryar da sarki zai aura. Kai kanka yaushe rabonka da shiga cikin gidan gonar nan, a kallah ankai sati guda. Kuma sarkine da kansa ya dakatar da kai don tabbatar da tsaro a gidan gonar gaba daya bisa barazanar abokan gaba. Ina mai tabbatar maka da cewa idan ba sarki shaaran bane ya zo da kansa nan yace mu bude maka kofa ku shiga ba babu yadda za'ayi ku shiga cikin gidan nan. Koda jin wannan batu sai hankali su yarima Huzaifa ya dugunzuma ainun suka rasa abin da ke musu dadi. Shugaban masu gadin ya sake duban hunzalu ya daka masa tsawa yace, ya kai

Chapter 1 of 6