Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shigo sannan kowa ya nitsu aka dan sarara daga nan Wani shiru gidan ya dauƙa, dan Kaf yaran gidan sun watse kowa ya fita neman nakai,aka bar manyan sukadai agida tareda wasimé data laɓe agefen innono tayi shiru tanajin tattaunawarsu wanda mafi akasari akanta ne. Ta gama lura kamar aure ake shirin yi mata ba itama,ita ko ajikinta dan bayau ta soma ji ko ganin aure ba,zaman su a sansanin fulani yasata fahimtar komi,daga ya mace takai shekaru 9 xuwa sha 11 to a al'adance ma ta isa ayi mata aure,halan itama takaine,taga duk kawayenta nacan ma an bijiro da maganan aurensu duk dama bata san menene shi auren ba amma haka dai suke cewa. Dattijon dayake bayani bazai wuce shekaru 60 ba, yace wa matayen sa da suke zazzaune agefensa akan da su shirya tarban ɓaki dan Lokacin isowar waliyann angon kawai ake jira angama shirye shiryen komi afannin amarya,Innono tacigaba da masa godiya tana saka masa albarka da tare da danta Qasimu daya amince a aurawa jikarta dahiru aure da wasimé," Dama can angaya mata danta Qasimu yay sa'ar aure duk dama tasan ƙabila ya auro amma ta lura kamar matarsan tana iya bakin kokarinta wajen yin musu adalci,sosai innono taji dadi da suka bata hadin kai ta bawa jikarta dahiru auren wasimé badon komi ba kodan sabida ta inganta rayuwrta na nan gaba. Around 3pm na yamma saigasu kuwa sun iso,danta qasimu da matarsa da dansu taher wanda a shekaru bazai wuce ashirin ba,yaron kyakkawane na bugawa a jarida yafima iyayen nasa muhibba,yanada sigar mulki da kuma ƙasaita irin na wayayyu yan birni,shi tunda yaxo baiyi magana da kowa bama, Hannu bibbiyu iyayensa suka amshe zancen aurensa wanda aka ƙullasa bayan sallahn la'asar ranar jumu'a.a bakin masallacin Kofar mai kasuwan anguwan mahuta .."Taheeeru Elqasim junaid da matarsa wasimé Aliyou denge Akan sadaki dubu dari da hamsin lakadan ba ajalan ba.,aure yaci darajar dumbin jama'ar gari sabida ranace ta cin kasuwar kauyen,da wanda yasansu da wanda baisansu ba kaf an halarta ankuma sakawa auren albarka. Nan danan mata suka tada Yan raye raye da kade kade na al'ada guda ya cikka tsakar gidan kamar dagaske,kan kace kobo auren da akayi tsammanin yinshi cikin sirri da tsagaitawa saigashi yayi armashi har andanyi wasanni na al'ada antarawa amarya da ango kudi,Matsala daya aka samu kasancewar wasimé yar karamace batasan ma me akeyi ba,shekarunta tara ne kacal,shima taheer sam baiji dadin hakan ba a xuciyarsa dan baisan yaya xaiyi da wannan premature auren da aka musu ba,shikansa he is not ready to be a husband yet musmn ayanxu daya saka zancen karatunsa agaba, toh inaga kuma yarinya ƙarama yar nine years wacce batama san zancen me akey ynzu ba,yasan wannan wani nauyi kawai aka dora masa,da kuma rainon ƴa wanda aka laƙa masa akansa,saidai shi mai tsananin biyayyane ga iyayensa, shiyasa bai nuna komi a yanayinsa ba,kuma yake biye musu a duk da wayewarsa da ajinsa hakan bai hana ya amshe batunsun hannu bibbiyu ba..besides kawai auren aka daura musu ,ba'ac su zamto tamkar mata da miji aynzu ba,saidai yasan ixuwa wani lokaci inta Girma hakan zai iya faruwa,Nasiha kam sunshata awajen su innono da mutanenta da ta bawa waliyayyancin wasimé. Yaga ba'aje koina ba har iyayensa sun kwallafa yarinyar aransu, jin cewa ita marainiyace babu uwa ba uba babu dangi sai innono.,innono tasa a hada auren da jininta ne sabida gudun hannun da wasimé zata iya fadawa ciki inta tafi ta barta awani wajen. Yanzu da akay mata aure tun tana yar ƙaramanta ai zata iya zama a karkashin surukunanta harsai ta girma snn ta tare a dakin mijinta, Sannan shima dahiru zai iya cika duk wani burinshi nayin karatu da zamowa duk abunda zai zamo kafin wasimé ta gama balaga ta mallake hanklin kanta,Koda bata sani ba, tasan dai rayuwar wasime na nan gaba bazai sangarta a hannun wani jininta ba. Washe gari sassafe suka bar garin suka doshi hanyar cikin garin kaduna bayan an kammala komi na al'ada. Innono da danta Qasimu da matarsa sai amarya da ango wanda haryanxu acikinsu wani baice uffan ma wani ba,ya zamewa taheer jiki shi baiya saƙe fuskansa da kowa,da wuya kaga dariya akan fuskansa ko murmushi zaiyi baxai wuce na gefen baki ba. Shi wani irin murdadden mutum ne dabaison cikia magana bare zancen shirme,yana da ƙarfi da izza,shiyasa Arayuwansa Yake mutuwar son yay millitary school ya dawo land army amma haka firrr iyayensa suka hanashi. alhj Qasimu da matarsa Sun nuna kamar likita kawai sukeso ya zamo,amma son da sukeyi wa dansu yasaka suka ƙasa yankemai babban burinshi na sob zama soja dan wani son zuciyarsu,Shima anashi fannin son dayake ma iyayensa yasaka ya ƙasa yankewa kanshi hukunci Dan a duniya babu wani abunda yake tsananin ƙauna yake kuma darajawa kamar iyayensa Kaunar da yake musu yasashi yafara pursuing careersa ta zamowa likita, amma likitan sojoji. Wanda Yana kammala sec schl 'dinsa at age of 16yrs ya samu scholarship mai kyau bisa kwaxonsa a NEET exams da suka zana na xuwa military school india,HPSP wato health profession schorlaship program ita ta dauki nauyinsa tana biya masa kudin makarntarsa harya kammala cos is just 4yrs alkcin,ynzu haka baifi wata biyu da dawowarsa ba,ynzu haka Mahaifinsa yana kkrin nema masa wata dama A "NAMC" nigerian medical millitary corps service,dan yayi 2yrs medical functions, wanda daya kammala zasu turashi can USU (uniformed service university of health) dats the national medical center is bethesta maryland,acan washintong D.C,inda zai ƙarkare karatun nasa sann ya dawo gida. Dukkan wani jajircewa da tanadinsu arayuwa wa dansu taheer kawai sukeyi shima dukkan soyayyarsa da biyayyarsu naga iyayensa,sunada burin bashi ingatacce kuma tsaftacacciyar rayuwa dake shine kadai Allah ya azurtasu dashi a duniya ,Mahaifinsa al'Qasim baida wani sana'a face saida siyarwan motoci, ita mahaifiyarsa kuma malamar jamia ce amma yanzu tanata kokrine domin shiga matakin farfesa a fannin mecha-tronics and electrical engineering. SHARE PLEASEEE👏🏽👏🏽💘💆🏻‍♀️🤌🏻 7/25/22, 19:19 - Kawata: *FITAR RANA...* _......faduwarsa_ BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM. 3️⃣ Saican wajejen bayan magrib suka iso cikin garin kaduna,lkcin kowa ya gaji,wasime kam tanata sharban baccin ta A kofar gate din babban gidan qasimu sukayi horn mai gadi ya taho ya bude musu ƙofa, tunda sukayi parking taheer ya sabule jikinshi ya haura sama can dakinshi babu abunda ya kuma sauƙowa dashi,yana shiga dakinsa ya fada akan gado yana maida gajiyayyen numfashin shi dayake fitowa daga can ƙasar huhunsa a hankli. kirjinshi da zuciyarsa sai racing sukeyi yabi ya rasa kwakkwaran dalilin faruwar haka,duk yadda yaso ya mance da zancen auren a zcyarsa ya ƙasa,ynzu shknan fa yay aure..kwantaccen gashin kanshi ya shafa ahankli cikin jan numfashi ya furta"what the fuck,wani irin mixed feelings na i cant believe this shi ya mamaye sigarshi wanda yy kama da kamar zai yi murmushi kamar kuma zaiyi kuka a lokaci guda,daga nan miƙewa yay gaban wani dan mini freezer ya buɗe ciki,2 rows ne mai dauƙe da chilled bootle water sai chapman ansha rabi an bar saura,Ruwan kawai ya dauƙa ya bude ya kurɓa kadan yana lumshe idanunshi after each sip snn ya mayar ya ajiye ya mike ya shige bathrum,wanka yy yabiya sallolin dake kanshi,tuna wayarsa a kashe yasashi kunnata,dan kadan yay scrolling baiga wani abu intresting ba ya ƙara kashewa,da kyar yau yay bacci dan aranshi babu abunda yake face juye juye da tunanin auren da aka dora masa,a bangaren wasime kuwa saiyau taga babban gida ƙere tunaninta,yo duk kauyensu bataga i irinsa ba,da xuciyarta kawai taketa shagalin hira tana maganganu kai kace nazarin wani abu muhimmi takeyi ,gidane irin na zamani yasha interlocks ga motoci a parke 1,2,3 saida ta tsaya kirgawa tass acikin zuciyarta,motoci guda uku ne harda wanda sukazo aciki making 4cars,sai kuma jincheng rubber rubber da tagani agefe,baki bude tace"laaah gidanma harda Achaba? Bakinta ta washe a tunaninta ai zatana xuwa gida tunda a machine kawai taga ake shiga kauyensu data fito,...sai kalle kalle kawai take abunta tana leken wajajen da suka burgeta kamar wawiya,da alama tamance wai yau an dora mata wani abu akanta waishi aure Hahaha inza a yankata aynxu ma bazata iya tuna komi ba . karshe babban mai aiki kuma nannyn gidan wanda suke ambata da suna Bilti ita ta riƙo hannunta tajata izuwa ciki tayi mata wanka fesss ta shafa mata mai tasa kaya nan danan bacci mai nauyi ya saceta danko abinci bata iyaci ba,washe gari da asubahin fari taheer ya farka ya fice sallahr fajr shikadai danyau bai jin zai iya jiran dad dinsa kamar yadda ya saba dan harynzu basuyi wani dogon hira akan lamarin aurensan ba,kuma yasan da maganganu sosai a bakin mahaifin nasa,shidai baison yay tattaunawa maizurfi, he dont really care inde hakan zabinsu ne shimai musu biyayya ne ako wani irin hali so long as dis marriage bazai hanasa cika burikansa na rayuwa ba.guntun ajiyar zciya ya sauke ayayin dayake sauƙa ahankli daga kan matakala,jallabiya brown ce ajikinshi tasha karin guga ta masa damas ,a hnkli yake takawa alaman baison kowa yaji motsin fitarsa daga gidan,tunda yy alwala ya zauna cikin masallaci bai ƙara fitowa ba,yau sai wajajen bakwai saura ya dawo cikin gidan sallama yy a kofar falonsu, Abbansa na zaune da jarida a hannu ya amsa,waje ya nema ya zauna a kasa sai ynxu ya lurada innono data fito ta shirya tsafff tana zaune a falon itama tana kallon tv tare da mahaifinsan bazaiwuce suna tattaunawa akan lamarin aurensa ba,wani haɗe ransa yay tamau kmar bai taɓa dariya arayuwarsa ba,mentally ya datse zcyrsa daga bugun datake snn ya dan cixa labbansa a asirce,idanunshi yay rolling snn yy ƙasa dasu a miskilance "Anono kintashi lpya? Da sauri ta amsa shi...lpya lau dahiru Angon jiya har anhito kenan,ajiyar zciya ya sauƙe irinta cikin wuyar nan baice uffan ba Tahau bada labarin shagalin jiya,da yadda aka tara musu kudi wajen gasar rawan ango da amarya da akayi,amarya ta samu dubu uku cas cas ango ya same dubu biyu da dari biyar,tace Sai dai fa kuyi hkri dashi na sallame yan biki kunsan abun bawai na shirya masa bane,alhj Qasimu yanata murmushi uffan taher baice ba,shikansa yasan jin sallamar san yasata ƙara himman maimaita maganar da sukeyi na batun auren na sa,hirarsa ma a sama sama takomo amsawa tana jaddada masa cewa tabar musu yarinya marainiyan Allah .tace"nide ba zama zanyi anan ba saiku riƙeta amana inmakun zalunceta Allah na kallonku, nide zan tafi tasha can anjima motar shayibu zaibiyo tashar sai kacewa danka daheru ya ajeni can.,alhj qasimu dake satar kallon dan nasa yaga ya sunkuyar da kansa can ƙasa ya bata shiru,yace babu damuwa mama ai gashi nan yanajinki,"my son kanajinta ko?kau da kai Taher yy baice uffan ba ya gyara zamansa, suna cikin tattauna haka saiga shigowar matar gidan hannunta dauƙe da flask din ruwan zafi da wainar kwai da kayan karyawa ...ferfesun kan ragone cikin cooler da kayan tande tande an naɗe shi a babban leda wanda innono xata wuce da shi sabida yunwa dan sukansu basu san inata dosa ba zama innono tayi ta ƙarya sann Ta sassaka musu albarka,tare da zuriarsu. Ƙarfe Takwas saura wasimé ta farka bacci hannunta bisa baka tana kkrin tare wagegen Hamma daya taso mata hartakai hannunta baki saikuma ta firgita ta sauƙe tahau tattaba jikinta jin duk ta jiƙe da fitsarin datayi a kwance,subuhanalillah!! da mugun gudu ta sauƙa akan gadon ta riƙe kirjinta dake bugawa da karfi fuskanta tamkar zatay kuka ta doƙa salati" innallahi wa inna ilaihi rajiun na Higa uku !!fitsari nayi,ta tattaba gadon sann ta tattaba jikinta"ayyy ashe fitsari nayi..yau na higga uku,a hargitse ta juyo cikin magagin bacci Da muryan tsoro tana neman innononta.innono Ano..Cin karo da idon mutum akanta yasata yin tsit ta koma baya a tsomare kamar wata barauniya,"wata mata tagani agabanta sanye da riga da zani da wani baƙin hijabi,gashi Allah ya xuba mata ruwan ciki gaba daya sai taji hanjinta na curewa tsabar tsoro,suna hade ido taji gabanta ya fadi rass duk sai taji ta rude,duk damuwarta fitsarin datayi musu akan' gadonsu tanayi tana waiwayen wajen,wayyo Allah rabonta datay fitsarin kwance fa yau yakai shekara guda kenan amma meyasa yau taga tayi kuma a gidan mutane?sai satar kallon jikakken gadon take da gefen idanunta da suka firfito tanayi tana damƙe zaninta da hannunta dake karkarwa, kiris ya rage Bilti ta fashe da dariyar yanayinta dan sosai ta bata dariya. Cikin gyaran murya tace yan mata harkin farka?..zatayi magana bilti ta katse ta cikin sauri "natasheki kiyi sallah kince min toh ko harkinyi sallahn kenan?kanta ta sauƙar ƙasa kirjinta na bugawa fat fat,ta rasa mema zatace daga nan wani shirune ya dauƙe Wajen,murmushi kawai bilti tay snn tajanye hannun ta tay da ita bathrum,"Cire kayanki, ta umarceta sannan ta soma hada ruwan wanka mai dumi a bath,da kyar wasime ta kammala cire kayan nata ta tsaya daga ita sai pants,duk ta kame jikinta waje guda sabida tsoro da kunya jikinta duk rawa yake,haka ta dunkula kayantan a hankli ta ajesu kusa da wani empty bucket tana ta kallan inda tajikasu da fitsarin cikin nisan tunani,"Uuhum uhnmmm Gyaran muryan matan ya ƙara firgitata ta dago kanta a firgice tace naam 'brush ta gani a hannun matar sabo dal a ledansa aka budesa,a hnkli tace,"xo nan kiyi maza ki goge bakinki saimu tafiko?tune din lallami datasa yasaka wasime gyada kanta batare da tay niyya ba, Ƙarasowa tayi kamar mai tsoron wani abu ta tsaya agefenta,Sink bilti ta kunna ta mika mata brush din tana kallonta harta kammala yi dakanta,She was bit relieve dataga ta iya batayi wani kuskure ba,bayan nan tayi mata wanka suka jajjaba alwala,.dan karamin towl ta dora mata sann ta jawota dakin ta koma ciki after like 5mint ta dawo ta sameta a inda ta barta tana tsaye,Batace mata uffan ba ta kalli gaban madubi "mikomin vasaline"babu musu maza taje ta dauko ta kawo,tana ajewa bilti ta dan jawota kusa snn ta soma tsantsane mata jiki ahankli snn ta shafa mata mai ta mulƙe ta tass ta gyarata..ganin ta runtse idanunta tana kakkame jikinta yasata sakin numfashi ta kyaleta mamaki da fargaba duk ya cika kirjin wasime,a nutse bilti ta kammala mata komi ya rage saura saka ƙaya saiga sallamar innono ta fado dakin fusknta murtuke,tsaye bilti ta miƙe da dan fara a a fuskanta tace "Kaka karde har an fito,kiyi hkri saura kiris inkammala shiryata,ganin wasime fess fesss yasa innono sakin fuska tana washe baki.."lahhh baiwar Allah harkunyi wanka.. kai sannunki da aiki,karki damu wallh dama ainice mai tafiyar ita kuma wasimé inazata ai tazo gidanta kenan, nima zuwa nay nan indan jira anan,ina ni ina kallon kayan takaici,mtsew Allah yabaka jika mai shegen mulki,".kinga na shirya zan tafi dayakaini tasha in samu shayibu shine wai saina jirashi yay wanka kuma fa fess jikinshi yake,aikoda na shunshuna dandamalin rigarsa da zai wuceni harwani qamshin inibi yakey,yo saide in hammatar sa ne bai wankeba,kenifa na lura dahiru fa dan walakanci ne dama shide akomi sai anjirashi..neman yayi' mun kora da haline kawai A gidan nan..nide ina ƙara baku amanar ƴata yannan kusamin ido sosai akansa karyaga kamar sadaqa aka basa ya wofantar da ita da jan fuskarsa awajen fatashhh kamar anja baya an kalli agogo.. hahahaha Bilti ta kyalkale da dariyar yanayin maganan nata dayazo da yanayin barkwanci tace "kai kaka toh karki damu da wannan indan wannan ne ai zamu kula miki sosai da wasimé surutai innono ta cigaba dayi abunta,daga nan bilti batace komi kawai tajanye zanin gadon da wasime tay fitsari ta wuce bathrum dashi,ganin anbarsu su biyu ta riƙo kafadun wasimê data cuno bakinta gaba tanajinta tamkar wacce zata sakar mata kuka, "kema sai sime sime kike ban kayan toh in saka maki,tasa hannu ta fauce kayan,Riga da sket ne mai kyau na back of fish Amber colour dinkinsu na karkara ba amasa style din komi ajiki ba,Sosai wasime ta tsane Saka sket a rayuwanta,ita tafi sabawa da riga da zani galau galau taganta Kamar yadda ta saba acan kauyansu a jos,wani langwame wuya tayi ta larne kamar zatay kuka,"Innono wannan matsatsen abun kika samin?,keyanta taji an dungure ta baya"ke kinci uwaki,ki tsaya ingama sakamiki tukun zaki gani bazai matseki ba,tafin hannunta takai saman fuskarta tana turo bakinta a shagwabe har innono ta gama sakamata kayan yai mata rass kuwa sabida tanada ginannen jiki ba ita tsiririya sosai bace" "yawwa baga ki nan kin fito ba,innyeeeee gangariya tsiren mangu..wazai ganki ahaka fess yace katuwa irinki kina fitsarin kwance?,cikin gatse innono ta furta hakan tana hararta sabida ta tsare farfarun rikicinta dantasan wasime da naci akan abunda bataso yanzu saitasa acanza' kayan nan,shiru wasime tay tana wasa da yatsun hannunta,kan gadon innono ta kalla snn ta kalli idanunta sai tafara mata magana ahankli Kuma cikin sigar lallami,yanzu fisabillahi wasimé saiki rasa abunda zaki kawo tsaraba a gidan surukanan naki sai fitsarin kwance?garinya akay haka..shiru tayi daga bisani idanunta ya cikko da ruwa ta dago muryanta a sanyaye tace "Innono..ba laifina bane nifa Wani abu na dingaji yana fifitani cikin dare,sai naji kamar ana watsamin ruwa toh dana farka sainaga har waje ya jiƙa" Wayyooo ahhhshh inno..no ..Kunnenta taji anƙama, sai kuma aka sake aka rungumeta sosai,ajiyar zuciya ta saki tanamai ƙara sakejikinta a kirjin innononta data kwantar da muryanta ƙasa kasa ta dada mannota da jikinta sosai,'"kinaji na ko?..toh karki ƙarayi ina gaya miki nan ba inda ya kamace ki da kiyi fitsarin kwance bane..nan fa gidan surukunaki ne kiyi musu biyayya kinji?..lafewa tay tanamai gyada kai childishly,jinta kawai take amma batasan komi ba, "ga nan BILTI zatana miki dukkan abunda kikeso,bance kuma ki sake jikinki ba,yadda kike aiki a gida can nan ma ki saki jikinki kiyi,nan ma gidane,inkina bukatar abu ki tambayeta kada kuma inji anyi kuka dake. Ruwane suka cikko idanunta muryanta na rawa tace"innono wai barina anan zakiyine komi?ina zakije Ano?nide wallhy bazan zauna ba zan biki ..Ayanayin tausayawa tana kuma hararata tace "Sau nawa zan gaya miki da kizauna anan?hannu tasa a fuskanta snn ta fashe da kuka ni yaushe kika fadamin Kawai cewa kikay inshirya zamuzo binni Jiya naji kina cewa anmin aure,yau kuma shine zaki tafi kibarni anan wajen yoo akanme?ƙara sautin kukan tayi,innono cikin kyabe baki ta miƙe tsaye ta doshi kofar fita dan tasan batada amsar wannan rikici"ai saikiyi Ni kinga tafiya,harta fara takawa sai kuma ta komo ta leka bayi lkcin bilti harta kammala dauraye bedding din ta fito dashi a bucket zatakai waje rana ya bugashi ya bushe,innono ta washe baki..."baiwal Allah bilti ni na wuce saduwar Alheri nagode nagode da dawainiya Allah yamiki albarka Allah yajikan magabata ,bilti tana murmushi tace karki damu kaka ai aikina ne. Allah kaiki lpya ya kareki Innono tace ameen,tana juyawa ta kalli wasime harta kammala hada jakarta ta runguma asigar bori,da sauri ta dauƙe ido kamar bata ganta ba tayo waje Wanii fuuuuu wasimên ta biyo bayanta tafin hannunta bisa kan fusknta tanajin aranta kamar bazata ƙara ganin inonon ba,wani jan zuciyarta take dagske kamar wata mai aljanu idanunta na tara kwalla har ƙasa suka sauƙo cikin babban falon gidan,lokcin babu kowa a falon face Alhaj Qasimu da matarsa duk sun miƙe tsaye da shirinsu zasuyi rakiya wa innono,"matar gidan ne ta jawo hannunta tsakiya kowa na mata barka da safiya Har suka kammala maganansu batace dasu uffan ba.Tana hankare da inononta,tana fita itama tabita kafa da kafa"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un innono dan ALLAH karki tafi kibarni anan wajen.ni wallhy saina biki,ni wallh bazan zauna ba. Wayyyo Allah na na sshhiga uku ta tumu aƙasan tiles ta dora hannunta aka,innono na innono na wayyo innono nikam saina biki ..Acikin rudani da firgici ta furta hakan tana tsananta kukanta daya kufce mata bazata.Kuka kawai wasimê take babu kakkautawa kowa na kkrin rarrashinta Innono kam ko ajikinta danko kallanta batayi baretaji tausayinta, zamanta anan din shiyafi,dan wannan shine rayuwa mafi daraja da inganci data bawa wani wanda ta taimakawa arayuwanta,ta haɗa jininta da wasime aganinta tayiwa iyayen wasimé dukkan halacci da amanan daya dace ace tayi musu izuwa ynzu,acikin zuciyarta tana matkar kaunar wasimenta amma haka tayi kamr batasan anayi ba Allah Allah ma take tabar wajen "Suna fitowa waje wasimé ta bude sabuwar shafin kuka "wayyo Allah na,innono innono,innono zanbiki dan Allah zan biki,wayyyooh Allah na kaf gidan saida ya dauƙa da ihun ta tana bubbuga kafafunta a ƙasa tana kuka sosai.,kusan hanklin kowa awajen saida ya tashi banda innono data cure bakinta sama tayi gum,tasan sukam sabone basuyi dajin kukan yaro ba barinma yaro mai rikici,a sace ta kalle wasime da' gefen idanunta aranta ta kyabe baki ganin yadda ta turje ana fama da ita,dan kada kanta tay tace "zataxo ta saba ai,"danta Alhj qasimu ne ya riko hannunta cikin lallami kiyi shiru mama na,baya taja tace o o o o cikin sheshehka, kanta take girgizawa tana rabza ihu tana kiran innonon da ƙarfi,hanklin matarsa ya tashi ta rirriko kafadunta tanata lallashinta amma duk hakan baisa tay shiru ba,sunai mata kallan yarinyane amma basusan aranta tasan mame takeyiwa kuka ba. Duk sanda innononta tace zatayi tafiya wani wajen dabaida suna toh tasan zata iya daɗewa sosai bata dawo ba. Wajajen goma shaura anakan rikici da ita saiga taheer ya fito daga cikin gidan yana tfyarsa cikin sauri, murmurarren jikinshin nan yasha kwalliyar kananan kaya blue shit da black trousers data amshesa tamasa kyau, wani Sassanyar Qamshin bold rasasi da ck shiya mamaye iskan wajen wanda ya sakasu duka suka maida hankulansu kansa,wasimé ce kawai batako kallesa ba dan bakaramin ihu takey ita kawai a kyaleta tabi innononta ba,tun daga stairs yakejin ihun nata wanda hakan ya dada sa stern mood dinshi dada harzuƙa yabi ya ƙara harɗe fuskanshi tam yanajin haushin yarinyar aransa,wajen da akayi parking motar da zai kaita ya dosa,Innono da tayi tsinin baki taja ajiyan zuciya dataganshi,gyara tsyawurta tayi tana matsowa kusa da inda yake,toh Alhamdullh gama daheru ya samu fitowa ni kunga tafiyata,qasimu sai anjimanku,sauri tayi ta haubinshi abaya baya Alhaj Qasimu ya fidda kudi mai dan yawa dayakai dubu biyar ya damƙa mata a hannu nashan ruwa,matarsa ma haka ta bata gashi suma sauri suke zasu fita,hannunta ta rike tam duk dama sai dukan hannun take tana ihu tana firgici,innono ta soma ƙirar "bilti, bilti,.,bilti tana isowa ta dauke wasimen cak ta miƙa mata ita sabida cikamasu kunne da takeyi,cikin masifa tanacewa"marar kunya kawai,ki wuce cikin gida da ita Intagaji zatayi shiru,da kyar bilti ta kamota ta riketa tana fifficikewa"innono tana ta sassaka musu albarka wani horn ya danna da mugun ƙarfi kukan nan kam ya isheshi da gudu wasime ta hargitso wajen motar itama zata shige cikin motar aikuwa tana dososu,tsigar jikinta ya wani tashi sakamakon wasu dararan idanuwan sa masu ban tsoro da taga sun tsareta masu mugun firgitarwa,"kibace min anan wajen, a mugun razane taja da baya kamar an hanƙadata ta tsomare waje guda tana gunjin kuka tana kallon bakinsa daya furta mata hakan wnda kamar bada ita yay ba.Tunda suka hade ido dashi sai yanxu wata kalma ta shiga tsakaninsu,wani irin muguwar tsoronsa taji ya shigeta a take. Wani shiru wajen ya dauƙa Baice mata uffan ba ya rufe motarsa a mugun fusace sanda ta razana ta ƙara ja baya a firgice..innono ta harareshi sabida sam batason rashin mutunci irin nashi,itade taja Allah ya isa in Advance dan bazata lamunci adaka mata yarinya ba mahaifyarsa tana dan murmushin yanayinsu "Allah ya kare,Alhj qasimu duk suka daga musu hannu,innono tahau matse idanunta tana daga musu hannun itama, dan ita saiyanzu ma taji tausayin wasime ya shige zuciyarta,Allah sarki wasimé,gashi basuy wani doguwar xama ba,kwata kwata shekarun nata tara ne kacal tayi mata aure,murmushin tasu ta tsoffi ta saki tana goge idanunta da bakin zaninta,"tasan hala kafin ta dawo hala harta ƙara girma daheeru ya maidata matarsa,yoo ko zataxo ma ta girma taso shi?inshi yaxo baisonta fa!!..kai duk dai tunanin shiirme suka soma dagula mata kwakalwa sun bar gidan da kamar minti tara baice mata uffan ba ya kunna music a motar,biltice tay kkrin janye hannun wasime suka nufi cikin gidan wanda bacin razana datayi wani sabuwar shafin kuka da bori ta ƙara budewa, tun suna rarrashinta har suka gaji suka kyaleta,haka kowa ya fice akabarta agidan daga ita sai bilti, ƙarshenta basuji sakat a kunnensu ba,har saida wasime ta samu tayi bacci danko abinci taƙi sam tasaka abakinta. Bagaren su innono kuwa har suka isa kai tasha bata dawo daga tafkin tunanin shirme data shige ciki ba,wani irin horn mai ƙarfi yay sanda ta firgita taja innallalhi sann ta dawo hayyacinta Babu halin yin masa magana sabida waƙar daya cikama

Chapter 2 of 15