Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jefa mutum halaka koda kuwa shi mai imani ne. Kiyi hankli da rayuwa karki jefa kanki a tsabgar da bazaki iya ficewa ba. Karkiga waike yarince nitsuwa da sanin yakamata shine kadai girman ba yawan shekaru ba,yakamata kisani ke marainiyar Allah ce wasime kiji tsoron Allah mahaliccin ki kiyaye dorawa zuciyanki kwadayin abun hannun wani.. Wani Shiru wasimen tayi cikin yanayin nitsuwa tanajin abunda din biltin take cewa dan bada wasa taga tanayi mata maganan ba,sosai bilti ta gargade ta ta kuma ja mata kunne sosai musmn akan ƙarban abun duniya a hannun mutane musmmn ma shi saheeb. Atake Jikin wasime yay sanyi har bilti ta gama maganganunta ta fita bata dago kanta dake kallon ƙasa ba..ajiyar zcya kawai ta sauƙe zcyarta cike da fargaba ta mike tsaye ta cire kayan jikinta snn ta shiga bathrum tay wanka tare da yin alwala,sharp sharp ta idar da sallahnta wanda bawai ta gama iya shi bane,yau kam ma kwata kwata zcyarta da mind dinta gaba daya sun raja'a ne akan kayan wasa. Tana idarwa ta kimtsa dakin tsaf, snn ta kwaso su teddies da barbie dolls dn ta jerasu akasa daganan kuma ta tsunduma wasan baby bataji bata gani. A fannin saheeb kuwa fitarsa a gidan ya same su tolu da malam musa awaje sun kasa sun tsare a bakin motarsa suna jiran fitowarsa, haka ya ciro sabbin kudade ya rarraba masu goron sallah kowa yana washe baki, a bakinsu yakejin labarin cewa Taheer yy tafya baya gari,Perfect oppurtunty for him ya gayyace wasime zuwa asalin gidan iyayen sa domin suganta cos in two days time za'a ayi big birthday party blast ma kanwarsa anisa duk dama abun na gidane kawai so shiga wajen sai wane da wane sabida a cikin family house dinsu za'ayi. Burinsa ayanzu baifi yakai wasime wajen mahaifyarsa ba kodama zasu soma sabawa da junansu, ta inda xata nan gaba zai iya dogara da cewa mahaifyar tasa zata taimaka masa wajen yaƙin kwato ragamar kulawa da rayuwar wasime daga wajen familynta, danso yake ta girma tasan cewa shi yay mata komi na rayuwarta kafin suyi aure. Mahaifyarsa hajiya mufidat Garba bakare babban jamiar kare hakkin dan adam ce,snn ta karance fannin lauyanci tana da doctorate degree dinta. Tana kuma bada gudumawa mai matukar Muhimmanci wajen taimakawa marayu da marasa galihu (humanatarian)a reshen ƙasar amurka. Washe gari da safe wasime tana farkawa a bacci ta soma lalubar ababen wasanta sanda tay wasa iya isarta snn ta tashi tay sallah Ahakan ma Saida bilti ta tsawatar mata snn ta aje taje tayi sallahn a nitse,kayan datay fitsarin dasu ma yau kasa wankesu tay ta dukunkuna su kawai ta aje a bayan gida,yau hatta abinci shareshi tayi koda bilti ta tursasa mata a gaggauce taci dan kadan snn ta koma kan ababen wasanta ranan gaba daya bilti bata gane kan wasimé ba. Washe gari da safe ma hakan abun ya kasance saidai sukayi fada sosai da bilti snn ta nitsu tay ababen dake gabanta wasan sosai ya shige cikin ranta, Duk abun duniya ya dame zucyar bilti ,at around 12am lkcin bilti ta kammala dukkan wani ayyukanta ta fito kenan tana zaune a falo akan kujera riƙe da remote din tv a hannunta tana neman tashar arewa tanata famar scrolling har tazo ta wuce kan tashar bata lura ba saboda harga Allah babu wani cikakken nitsuwa atattare da ita,tunanin rayuwar wasime tasaka agabanta tun jiya,da shi ta kwana dashi ta kuma farka,kuma haryanzu tana kai bata fasa ba. Tunani kashi biyu ke wanzuwa a kwakwalnta har yanzu dai itama hanklinta bai wani kwanta sosai akan tarayyar wasimé da saheeb ba,koda ma ace babu wani cutarwa acikin tarayyar nasu, amma dai tasan dolene salonshi na kashe mata kudi da bata ababen duniya yaxo ya gurbata mata rayuwarta na nan gaba. Takanyi duba da yanayib bambaci dake tsakanin su da saheeb,shifa dan gidan masu shine masu fada aji..anan kuma su basu mallaki arzikin komi ba face iya wanda Allah ya basu na rufin asiri. Toh ta ina kenan zasu iya da wasime nan gaba inhar ta kyaleta ta saba da kalar rayuwar da batata ba?yarinya marainiyar Allah kuma ga igiyar Auren wani akanta. Kamata yay wasime ta zamto killataciya tun yanzu,ita kanta tarasa dalilin dayasa taheer yaki cewa komi akan tarayyar wasime da saheeb aganinta sam sam bai dace ba, duba da yadda sabo na yau da kullum daa kuma shaƙuwa da juna yakeson ya soma yin tasiri a zukatansu. Bawai iya nan ne ciwon nata ba,hatta sauyawar halayyar wasime yana daya daga cikin abunda yake tada mata hankli. Lokacin da anono ta kawo wasimé ko kara kasaka abakinta bazata tauna ba,amma yanzu gabaki daya ta sauya ta dawo wata marar da'a gashi bata son girmama na gaba da ita. Tasan hala dan bata taba haihuwa ba batasan zafin ɗa ba amma rayuwar taheer da na wasime tamkar wani babban responsibilty ne akanta tunda amana iyayensa suka damka mata,bazata ce tayi nasarar rayuwarta ba inhar ta kyale tarbiyan dayan su ya gurbace. aynzu kam taheer ya dan girma,tasan ba lallaine ya bata ciwon kai mai yawa ba,duk dama yakan dan taba yarintar,amma aynzu batashi take ba yazame mata dole tasaka ido akan rayuwar wasime,dole ne tasan yadda zatayi ta saita tarbiyanta dan kwata kwata wnn sabbin dabiu da halayyar nata sam basu dace da ita ba. Tana cikin wannan tunanin wayarta ya soma ringing saheeb tagani akan screen da kamar bazata dauka ba can dai ta hakra ta dauƙa gameda kara wayar a kunne..babu yabo ba fallasa tace "salamu alaikum saheeb? As usual da fararsa ya amsa suka gaisa..kai tsaye ya tambayeta ko zai iya zuwa ya dauƙi wasime izuwa birthday partyn sistersa yau.."tace a'a saheeb kasan dai wasime bata fita acikin gidan nan saida umarnin taheer kuma kaga taher din bayanan kabari mana sai wani lokaci inyaso by then taheer ya dawo amma ynzu kam baya gari. ..,yace eh nasan da hakan shiyasa ma nake neman alfarman ta wajenki dan Allah bilti,namiki alkwarin baxata jima ba zamu dawo,taheer dont even need to knw this, ana yanka cake akayi dan hotona shikenan saina dawo da ita,it wunt take dat long...please kitemaka min . ya karashe maganan cikin magiya..dan shiru bilti tay sabida rashin sanin hukuncin da zata yanke Wasime ne ta dosu falon Goye da white teddy bear a gadon bayanta tana tafiya tana wasa da wani abu mai balls balls aciki. Bilti bilti doramin abuna ya tsinke... Saheeb yana tsinkayo muryanta yace 'Is that beauty?bilti bata amsa ba,yace bilti dan Allah hadani da ita.. Mika mata wayar tayi kiyi magana saheeb ne,"da uban zumudi ta amsa taa kara a kunnenta tace "Alo?yeeeeyyy yaa saheeb...dariya yay beauty beauty..beauty na kitayani rokon bilti mana tabari in zo in dauƙeki kije kiga mummy na. Wani daka tsalle tayi cikin murna tace haba? Kace Allah zan ganta? Dariya yay sosai snn yace eh mana amma ai sai bilti ta amince...dan shiru tay tana mai satar kallon biltin da gefen idanunta,gani tay kamar bilti ta hade fuska. Gaba daya zuciyar bilti bai wani kwanta da abun ba amma dai zata kyalesu din suje kawai da sharadin saheeb zai cika alkwarin sa na dawowa da ita akan kari. Tunda ta basu go ahead dukansu suke cikin halin murna at arnd 3 na yamma saiga saheeb ya shigo,yau half jumfa yasaka ajikinshi ta masa cas cas dake bugun kamfani ce ya sako hularsa mai shegen tsada. Riga da zani na leshi wasime ta saka sky blue in colour shima duk acikin sabbin dinkunan da akayi mata ne,saheeb yana isowa tay gudu taje ta hau jikinshi tanai mai oyoyo.Duk dama yau bataga wani sakewar fuska awajen bilti ba Da zasu fita bilti ta kirawo saheeb gefe "Dan Allah karku dade dayuwar taheer ya dawo yau kuma kasan dai bazaiji dadi ba inyazo ya tarar da cewa bata nan. Cike da assuring dinta yace insha Allahu zan cika alkwari. 40min drive yakaisu makaken gidan su saheeb ko ina a shirye yake tsaf da kawatattun decorations wanda akayi su musamman don shagalin partyn,kusan rudewa wasime tayi ganin wnn gidan ma yafi wancan wanda sukaje shekaran jiya girma Surutu kam yau yashata harsaida yaji babu dadi. Everything went well,saidai plan din saheeb na bayyana wasime ma mahaifyarsa bai samu yay aiki akan tsarinsa ba.. muhimman baki ne suka tsareta a babban falon gidansu cikin wata muhimmiyar zantawa ta kasuwanci.,tunda aka yanka cake da ita suka dan daddauki hoto shikenan bata ƙara samun daman lekowa wajen ba,su wasimé kam tuni ta saje cikin yan uwanta yara,saidai kaf cikinsu itace tay daban sabida yanayin suturarsu yasha bambam da nata. Kusan kowani yaro awajen dan masu shine kuma ancan caɗa ma kowannen su kwalliya da hadaddun ready made gowns nd expensive suits, amma ita kam riga da zani nema ajikinta wanda a kiyasce kudin leshin bazaifi dubu takwas ba. While da party is going on kowa yanata enjoying kanshi da abinci kala kala ana rawa ana games amma gaba daya hklin saheeb baya jikinshi,baida wani abunyi a zcyarshi face sake sake,And zee was there to annoy him more, dan tunda taga zuwansa wajen tareda wasime take famar tsine masa albarka duk inda ya zauna haka zata bishi ta nanike mishi Snn bata da wani magana mai armashi sai Aibata alakarsa da wasime. Aranta ta tsane Duk wani abunda ya shafe taheer. Ayanzu sosai take nuna adawarta da shi. Da abun ya ishe sa ne yay zciya ya tashi yabar mata wajen yabarta a zaune ita kadai akan table a tsakiyar idanun mutane, Hakan dayay sosai ya bata haushi,aftr like 2 mint tana kkrin latsa wayarta zata turawa kawarta eesha text messg caraf sai idanunta suka sauka akan wasime. Tun daga can ta zuba mata ido tanamai hararata, wucewar ta ta gani ta hanyar guest washroom tana doka uban sauri,mammtase kafafunta datakeyi ya nuna alaman fitsari ne ya matseta. Wani Dariyar mugunta zee tay snn ta tashi tsaye a gaggauce cikin satar idon mutane tabi bayanta washroom din ahnkli take lekawa cikin sanda a Lokacin data shigo lkcin har wasime ta kammala yin tsarki tana kkrin maida panties dinta bata hankara ba taji an wani fincikota tayi baya,wani irin bugawa da karfi kirjinta yay acikin yanayin firgita da tsoro har ta karkace baki zata saki ihu Da ƙarfi zee ta buge bakinta sanda jini ya tsittu..,bata jira ba ta fixgo ta ta cakume mata wuya ta shaketa sosai tanamai hadeta da jikin bango" tuni hancin cikin wasime ya cure, cikin nata ya duro ruwa tanajin kamar zata saki fitsari ajikinta ,"ihu tayi niyyar sakawa...zee din ta zare mata ido tare da daka mata tsawa "kiyimin shiru da bakinki,kikq yadda kikayi ihu anan saina kasheki,mayya kawai shahsha yau saina kasheki,in kashe banza. Kukan bazata wasimevta barke dashi wani mari zee ta dora mata snn ta turata ta fada akasan toilet din cikin ruwan datti,karkar jikin wasime yake rawa jin kanta kamar wata mutacciya Kuka takeyi mai tsananin nuna firgita saidai marar sauti sabida toshe bakinta da zee din tayi.."wato ke bakiji ko?Uban wa yace miki kizo nan...uban wayace miki kinabin saurayina?zare mata ido take kamar zata hadiyeta cikin masifa Da baya baya wasime takejan kanta hawaye sungama wanke mata fuskanta tana famar girgiza kanta alaman ta balain jijjiga da tsoro. Toh Daga yau saiyau Naƙara ganin ki a inda saheeb yake saina yanka ki...saina hallakaki kin bar duniya.. kina ji ko bakiji?Wasime Bata iya daurewa ba ta saki kuka mai firgitarwa.Au baxaki yi min shiru ba munafuka?Janta tayi akasa tanamai wurgi da ita..ajijjiya take ya soma rufewa wasime ido,cikin kokawa da numfashinta ta soma cewa cikin kuka"..anty anty anty dan Allah dan Annabi kiyi hkri bazan ƙara ba waayyo Allah na kasheni zakiyi anty? kallo daya kay ma wasime zaka tabbatar da cewa bata cikin hayyacinta dan bakaramin raxana tayi ba Haka zee ta bushe idonta ta cakumo ta kamar yar tsana ta mikar da ita tsaye tana kallonta babu ko digon tausayawa a idanunta taja tsaki mtsww"bangama dake ba"..wani janta tay izuwa bakin water flush system suna kaiwa wajen ta danna kanta acikin bututun kashi ta murda flush ruwa ya rinka zuba akan fuskar wasime yana suffocating dinta,numfashinta ta dinga jaaaa da ƙarfi tanajin kamar ranta zai fice ajikinta,yarinya sai bari take tana tsananta kuka mai ban tausayi amma zee bataji kamar zata dena muguntar ta ba. Daga waje kuwa saheeb ne yaketa neman ta bai ganta ba,duk saiyaji hanklnsa ya tashi sabida biyar da rabi ya gauce yana matukar son ya maishe ta gida kamar yadda yay ma bilti alkwari... Da kyar wani basira tazo masa ya fara bibiyar yara yaran yana tuhumarsu ko sunganta daya daga cikin kannen zee din ne ya ce masa ai yaganta dazu tabi nan..sai ya masa nuni da hnyar washroom. Cikin gaggawa ya doshi wajen,yana shiga kuwa yasoma tuamali da ihun wasime,a guje ya isa kofar inda ihun yake tashi yana bankadewa daidai lokacin zee ta cakka kan wasimen acikin latrine ta danna mata ruwan flush akanta data wani fixgo ta sai gani tayi Yarinya ta sanɗare bata numfashi,...... Na kudine 300 naira,subcribe via 0152983148 Mohd sule surayya Gtb send ur evidence to 08060712446. 7/25/22, 19:19 - Kawata: FITAR RANA 16 Da wani irin zafin nama saheeb ya karaso wajen Jikinshi har na rawa ya saka hannu ya finciko wasime a hannun zee snn ya juya yanamai dora ma fuskan zee din wani gawurtaccen mari mai saurin rikitar da kwakwala.. tattaba fuskan wasimen ya shigayi ganin batako motsi hanklinsa tashe ya runtse idanuwansa snn ya bude, yana cewa"oh my gosh,zainab What did u do?..tsawa mai cike da kufula ya daka mata,kuka zee ta fashe dashi snn ta koma gefe ta rakubu da jikib bango sosai tay narai narai da idanunta Cikinta duk ya gama durar ruwa a tunaninta mutuwa ma wasimen tayi. Tattaba fuskan wasimen ya rinka yi hanklinsa a mugun tashe jikinshi gaba daya na rawa duk ya rude yabi ya rasa ta inane ma zai fara tunkarar abun,shimfidar da wasimen yay a kasa yana kkrin tabbatar makansa cewa ba mutuwa tay ba,wayarsa ya lalubo daga cikin aljihun wandonsa snn ya danna kirar gaggawa ma emergency,Acikin yanayin raxana sosai zee ta matsa kusa da su jikinta na rawa sosai ,leken fuskan wasimen takeyi a sace cikin ranta tana cewa wayyo Allah na na shiga uku shikenan yau nayi kisan kai, muryanta na rawa rawa sosai tana sauƙe hawaye tace "babe pls ishe alive..,wayyo ni na shiga uku, anya kuwa ba mutuwa tay ba? Tsabar fushi saheeb baisan sanda ya tureta tayi ƙasa ba"...get the hell out of here you witch"..abun bai masa bama,tashi yy ya soma dukanta da kafarsa yana takata cikin tsananin fushi da harzuka .. Yana cewa "Zainab mekika aikata min? Har muguntan naki yakai ki kashe yar mutane akaina?...wani maraitacen kuka ta rushe da shi acikin yanayin rudani tana cewa "wallahy sharrin shedan ne,saheeb dan Allah ka fahimce ni..I didnt mean for this to happen,nifa tsoro kawai naso in bata danta dena shiga harkanmu.Ba kasheta nasoyi ba....i swear to u.. Ko kulata baiyi ba domin kuwa hnklinsa ya mugun tashi ganin yadda wasime take kwance akasa almost lifeless bata ko fidda gudan numfashi. Jim kadan saiga team din emergency sun shigo wajen hilimi guda, acikin gaggawa suka daga wasime suka jefata a motarsu ta emergency atake atake aka sankaya mata engine din taya numfashi emergency nurses dake tare da ita suka shiga kkrin bata taimakon gaggawa. wani makaken private hospital suka wuce da ita wanda yakasance mallakin mahaifyar saheeb din ne dan haka likitoci har biyu ne suka amshe case dinta Akayi marmaza akayi da ita ciki ana duddubata . Ciwon Asthmanta ne ya tashi but in xtreme conditon,sukansu likitocin sunsha mamaki yadda take kkrin fighting. Ziriya kawai saheeb yakey shikadansa a bakin kofar inda aka shiga da ita yana salati a zucyarsa duk yarasa abunda yake masa dadi Can saiga shigowar anisa tare da zee suna karasowa cikin asibitin suna tahowa cikin sauri kowannen su hanklinta a tashe ,zee harta bawa anisa labarin duk abunda ya afku tsakaninta da wasime, saidai bata nuna mata cewa abisa qudirinta na mugunta lamarin ya afku ba,sai tay manipulating mind dinta kamar yadda ta saba da cewa sharrin shedan ne ,Ayanzu zee tasani sarai bata da wani makama face anisa,sabida bukatun anisa awajen saheeb kamar yankar wuka ne,inhar tace ya yafe mata toh fa komin girman lefin dolene ya hkra ya yafe dan bakaramin son yar uwansan yakeyi ba... Cirko cirko sukayi a bakin ward kowa yay zugum ana jiran sakamakon jikin wasime daga bakin likitoci. Shiru shiru har sukaci kusan mintina arba'in a tsaye amma babu wanda ya leko Wayarsa ce ta dinga ringing yay banza da ita bai daga kirar kowa ba dan koda bai sani ba yasan cewa bilti ce kawai zata iya nemansa a wannan lokacin. Agogon hannunsa ya duba hanklinsa a tashe yaga wai har karfe bakwai shaura gashi har yanzu likitoci basu ce komi akan condition din wasime ba. Gaba daya sai yabi ya rude mancewa ma yay da cewa bai gabatar da sallahn magrib ba. Anisa ce ta matso kusa dashi ta dan rugumesa tanamai comforting dinshi cikin yanayin nuna tausayinta agareshi wanda hakan ne yasaka ya dan ji dama dama. Tashi yay ya dan fita snn yaje yay sallahn magrib din, har ya kammala ya dawo wayarsa baidena ruri ba,Anisa ta kallesa "big B..Wai meyasa bazaka dauki wayarka ba ne..Tun dazufa naga anata kirarka what if its important...nannauyar ajiyan zcyace ta kufce masa yanamai shafe fuskansa datayi jaaa da tafukan hannayensa cikin jann numfashin sa sama sosai. Muryansa cike da amon damuwa Yace "I dont knw how to start explaining to u,Inna dauki wayar nan ma bansan mezance ba...am fucked up right now..duk wancan yarinyr ce tajawomin...ya furta hakan yana aikawa zee wasu matsiyatan harara. A mamaknce Anisa tace toh who is calling you kode iyayen yarinyar ne?shiru taga yay, ta damko hannayen sa cikin son ta tursashi tace karkayi haka yaa saheeb they need to knw ai, this is serious fa.. saheeb Zaka aje musu yarinya acikin wani mayuyacin haline batare da ka sanar dasu ba? This is btwn life nd death...inta mutu daureka ma zasuyi ko suce basu yadda ba Bro u have to let them know right away.... Juyowa yy idanunshi cike da damuwa yanacewa "I know...i knw anisa...but you have no idea how we got here.Saida fa na roke alfarma awajen bilti kuma namata alkwari before 6pm yarinya tana gida but just look at what happen now.. Cikin sauri bai hankara ba anisa ta kwace wayar dake hannunshi tana cewa nikam bani lambar ta toh ni zan kira ingaya musu gaskiyan abunda ya faru,ita biltin batada fahimta ne Aiba lefinka bane...its an accident fa..kuma babu wanda yafi karfin hakan tafaru dashi. Ransa a hargitse yace Anisa give me that phone u wont understand me. Boyewa ta dadayi ta matse wayar da rigarta cikin bijire masa, a bayadda ya iya haka ya kyaleta dashi. Kwafar lambar tay awayanta snn ta kira layin bilti Tana karawa a kunne taji service provider tanacewa the number ure trying to call is curently switched off pls try again or call back later... A Lokacin numfashin saheeb kamar zai tsinke yabar jikinshi tsabar fargaba,"ganin anisa tayi shiru da waya a kunne bata kuma ce komi yasashi yace "Did she pick up?Ajiyar zcya ta sauƙe snn ta Sauke wayar a kunnenta cikin girgiza kai tace "the line is swichd offf.... Ajiyar zcya ya sauƙe feeling relieved yana dan lekawa,yace nidama likitocin nake jira sufito inji ta bakinsu tukuna kafin sai in nemesu on sanar dasu. Anisa batace mishi uffan ba tay wucewarta wajen zee data manne da bango tana matse idanun karya,dan harga Allah bawai nadaman abunda tayi wa wasime ya sakata damuwa ba,damuwarta shine kar ace tayi kisan kai ko saheeb yace zai guje ta,duk damuwarta kar ace wasime mutuwa tayi azo ace za'a kamata. Gashi mahaifyarta irin mata masu daukar zafin nan ne...dama can ubanta ne kawai yake daure mata gindi kuma ahalin da ake ciki ynzu uban nata yy tafiya izuwa europe baya ma ƙasar. A fannin bilti kuwa tun ficewarsu a gidan baifi da awa guda ba saiga taheer ya dawo daga tafiyarsa. Bata ma sanda shigowar sa gidan ba tana can cikin kitchen tana yan aikace aikace. Dakinshi kawai ya nufa direct yaje yadan huta gajiyar da ya debo ajikinshi sabida kwana sukayi a mota suna tafiya tsakanin adamawa da cameroun,sai can snn ya tashi da kyar jikinshi duk yay tsami,haka ya lallaba kansa yaje yay refrshing kansa a bathrum ya fito yay glaming kansa acikin wata simple polo shirt light yellow in colour da bakin wando,da soft sneakers shima baki Turarensa mai sanyin qamshi ya fetsa yanamai Lura da time a agogon guccin dake sakale da tsintsiyar hannun sa Wajajen biyar da rabi lkcin ana neman shida saura taheer ya samu saukowa,a bkin kofar kitchen din ya tsaya snn yay gyaran murya,dan raxana bilti tayi musmmn data gansa gatsau haka acikin gidan duk dama tasan hakan zai iya yuwa tunda yanada personal keys dinshi.. murmushi mai sanyi ta sakar masa shima ya mayar mata a takaice, cikin kulawa tace"Taheer yaushe agari?Looking really stressd up cikin kyabe bakinshi yace "ai nafi awa guda agidan nan kawai dai nagaji ne shiyasa naje na dan kwanta danna huta...bilti da akwai abincine?wallh yunwa nakeji...tun safe fa banci komi ba,.. da mamaki ta dubesa tana wondering tace"akanme toh? Shiru yay mata bai amsa ba..tace toh zauna nan bari dai naje na kawo maka dan abunda ya samu sai samu kaci. Waje ya samu ya xauna a falo snn ya dauki remote din tv yana danne danne Bilti kuwa tunda ta shige kitchen take dannawa saheeb ƙira amma bai daga ba,gabaki daya saitaji hanklinta bai kwanta ba. ranta sai ya soma harzuka,bacin rai na neman ya rufe mata ido, acikn zcyarta tana cewa yaya yaron nan zaimin haka..toh ga taheer dinma ya dawo niyanzu mezanje masa gameda fitar wasime? Duk fargabanta kada Allah yasa su shigo su iske shi a falon. Harta kammala hada masa abincin saheeb bai daga wayar ba.haka ta basar da lamarin ta danne fushinta ta fito fuska ba yabo ba fallasa ta kawo mishi abincin acikin yanayin dubara tace "inkai maka dakinka ko inaga can dinma ai zaifi..Nan wajen duk yay kura bari inzo indan goge Kai saika shiga daki karna takuraka duk salon wayon waidan ta koreshi ne ya shige room dinsa karyaga shigowarsu wasime cos at any moment tana tsammanin jin sallamar su... Haka taheer yay taurin kai shima yaki tafiya dakin duk wayonta baihau kansa ba.. Yace kibarshi anan kawai bilti"Ni anan kawai zanci" Bilti bata taɓa kasancewa a halin baraxana da razana irin na yau ba sai cizan yatsa takeyi a zucyarta tana mita "kassh amma yaron nan baimun adalci ba...ziriya takeyi ita kadanta a kitchen da waya a hannunta tana mai dada neman layin saheeb din Taheer nadaga falo yanacin abincinsa hanklinsa kwance. Duk A tunaninsa wasime tana can daki a kumshe kamar dai yadda ta saba. Bilti ta kira saheeb yafi sau hamsin amma shiru bai daga wayar ba,kowani dakikanin wucewar scnds na agogo saita kirga Hanklinta bakaramin tashi yake dadayi ba Musamman dataga har an kusa a kammala sallahn isha i bai daga kiraba kuma basu dawo ba... Wani zucyar nata tunzirata akan taje kawai ta gayama taheer komi iyakaci ne yay fushi ai ba dukanta zaiyi ba. But dat isnt fair to him Matarsa ce fa wasime, nd she rmbr how he gave her Strict oders akan kar abarta tafuta taje koina face inshi ne ya bada izinin yin haka. Ganin takwas yay har yana shirin gaucewa yasaka bilti ta cire ranta da tsumayin fushi da bacin rai ayanayinta Fitowa tay jikinta a mugun sanyaye da niyyar kawai zata fallasawa taheer abunda ake ciki,tana isa falon ta samu taheer din bayanan da alaman sallahn ishai yaje gabatarwa a masjid. Kwanukan dayaci abincin ta tattara takai cikin kitchen ta zuzzuba su a sink ayayinda wani tukukin ajiyan zuciya ya kufce mata..wanke wanke ta hauyi kodama zai gushar mata da tashin hanklin datake ciki amma ina abun saima karuwa yakeyi acikin zcyarta..tambayar kanta takeyi "meyasa saheeb zai mata haka? Kallon agogo tayi taga Har karfe takwas da rabi shaura Wayarta ta kama ta kashe ranta a mugun bace snn ta fito da niyyar dauƙo hijabinta zata je har gidan su saheeb din kawai dakanta. Agaggauce ta haura sama ta sauko cikin shigarta na doguwar hijabi dark green in colour duk fargabanta kar Allah yasa ta gamu da taheer,ai gwara taje sharp sharp taji meke faruwa koma minene zai farudin yakasance dai ta dawo da yarinya gida. Tana saka hannu a door handle din falo zata ja ta fito waje sai taji alaman kmr ankama ne ta waje da alaman ana kkrin shigowa ne ciki. Bugawa da

Chapter 10 of 15