Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
" Gani durƙushe gabanki ina mai neman afuwar ki, na tuba nasan tabbas na miki laifi a baya, na kuma amshi kuskurena, ki taimake ni karki gujeni, Wlh kece Rayuwata rasaki tamkar rasa numfashina ne, ki taimakeni karki Auri wani ba niba Wlh ina sonki fiye da yanda nake son Rayuwata, ki taimake ni karki Auri wani ba niba nasan mutuwa zanyi muddun na rasaki." Ga baki daya jikin su yayi sanyi mussaman Indo wani irin tausayin sa take ji, sam Zuciyarta bata mata daɗi ba ganinsa a cikin wani mawuyacin hali, amma duk da haka sai ta daure zuciyarta ta ɗago cikin ƙarfin gwiwwa tace masa. " Ƙarya kake ya Mustafa baka sona da kana sona da baka wulaƙanta ni ba, da kana sona da baka kyamace niba da kana sona da baka dokeni ba. Shi Wannan ɗin duka a cikin Soyayya ce, baka taɓa nuna min hanya mai kyau ba duk kaucewar da nayi baka taɓa ajiyeni ka nuna min cewa ga inda zanbi rayuwata tayi kyau ba, baka taɓa ɗaukata a matsayin mutum sai ma dangana ni kake da suffar aljanu da dabbobi, idan ban manta ba akwai sanda ka ce min ( Allah ya sauwaƙa naso ƙazama Irin ki kazamar ƙauye, waima tukunna waye zai miki kiss da waɗannan yellow haƙwaran naki ɓace min da gani kafin na targaɗaki, mahaukaciya kawai marar lissafi, amma dai Wlh Allah ya isa tsakanina dake, ki rasa waye zaki ce kina so sai ni, to Wlh Allah ya isa kin cuceni) ka kuma cemin. ( Nidai wannan YARINYAR ta zamo min masifa duk randa zanzo ƙauyen Nan, da tsinkewar Zuciya nake zuwa, tunda nasan zan haɗu da bala'i) Kayi tunanin duk na manta da waɗannan maganganun naka ne, to yanzu kuma me zakayi da ƙaramar ƙauye mahaukaciya mai yellow haƙori marar lissafi wacce ka yiwa Allah ya isa, ka kirani da macuciya ka kirani da masifa da bala'i wanda har na zamo tsinkewar Zuciyar ka duk kawai dan nace ina sonka, meye laifina a nan ka faɗa min meye laifin Zuciyata dan ta ce kaine take so sai dai alhamdulillah ko yanzu na godewa Allah daya cire min Soyayyar ka cikin zuciyata, kaje ka riƙe matar ka ina ga hakan zaifi maka, nikam na riga da na yankewa kaina hukunci bana ƙaunar ka a yanzu." Ta ƙarasa maganar cikin zubar hawaye da rawar Murya, kallon tausayi Zarah take binsu dashi Tabbas tasan suna son junan su har gobe, sai dai ƙaddara ta gifta tsakanin su, wanda har ta kaisu ga rasa Aure tsakanin su, Tabbas wannan shi ake kira *SO BAI SAN JINI BA* domin kuwa da yasan jini bazai taɓa shiga zuciyoyin waɗannan ƴan uwa biyun ba, gashi har yana son shiga tsakanin *ZUMUNCIN SU* Shi kuwa Mustafa cikin mungun tashin hankali yake duban ta, jin maganganun da take tuna masa shi harga Allah ya manta ma da wannan maganar da take tuno masa sanda ta faɗa masa sannan ya tuna dashi ashe ita tana sane da shi cikin zuciyarta, Tabbas ya tafka babban kuskure, dubanta yayi tare da cewa. " Tabbas na aikata miki kuskure wai yawa na amshi laifi na, ina mai baki haƙuri da ki yafe min dan Allah komai ya wuce ki ceci Rayuwata karni bari Rayuwata ta lalace ta sanadin Soyayyar ki." Murmushi Indo Tayi mai cin rai kafin tace. " Lokaci ya riga daya ƙure maka domin kuwa nima bazan yarda nayi sanadin shigar wanda ya taimaki rayuwata ba ta lalace sanadin Soyayya ta, kayi hkr ka cire Soyayyata cikin ranka domin kuwa ba kai nake so ba ɗan uwanka nake so *YA HABEEB* shine zaɓin Rayuwata shine wanda ya cancanci nayi rayuwa dashi ba kai ba ka cire Soyayyata cikin ranka ko karka cire wannan damuwar kane ba tawa ba, domin kuwa son maso wani kake." Tana gama faɗin haka ta tashi tabar wajen cikin sauri jin kuka yana neman kwace mata Soyayyar sa yana son karya mata zuciya yasa har tausayin sa yasa ta kauce layi ta hanyar yiwa Habeeb butulci, kuma Abunda bazata taɓa yadda ya faru ba kenan. Runtse idonsa yayi cikin jin Zafin maganganun ta, wani irin ƙuna Zuciyar sa take masa, baisan ya zaiyi SHATUU ta fahimce sa ba, ta kasa gane kalar Soyayyar da yake mata, tausayin sa sosai Zahra taji, dubansa tayi tace. " Kayi hkr Mustafa na fahimce halin da kake ciki, ka daurewa Zuciyarka, ka cireta cikin ranka tunda kaga har iyaye sun yanke hukunci, nasan irin zafin da kake ji amma ya zakayi ƙaddara ta riga fata." Tashi yayi tsaye ba tare da cewa Zarah komai ba ya shige cikin motarsa yana layi, girgiza kanta Zahra tayi sannan itama ta tashi tabi bayan INDO, a Class ta sameta ta kifa kanta jikin kujera sai Rusar kuka take zama Zarah tayi tare da dafa kafaɗar ta tace. " Meye amfanin kukan? karfa ki sawa zuciyarki wani ciwo." Ɗago kanta tayi idanunta sunyi jajur tace. " Dole nayi kuka Zarah na rasa farin ciki na, gashi yana cikin wani mawuyacin hali, bana son ganinsa cikin damuwa Zahra ina son Ya mustafa bana son ganinsa cikin damuwa." " Idan ma kina sonsa ya kika iya tunda dai ƙaddara ta riga fata Daddy ya riga ya yanke hukunci, meye aibun Habeeb da kika kasa sonsa, meye banbancin Habeeb da Mustafa, basu da wani banbanci koda kuwa ta kama ce, kawai ki kalli Habeeb a matsayin shine Mustafa wala Allah zaki samu sassauci a cikin zuciyarki." " Ba zaki taɓa ganewa ba Zarah, ke bakya ganin banbancin su amma ni ina gani suna banbanci sosai, ki daina furta min kalmar na manta dashi bazan taɓa iya mantawa da ya Mustafa ba CIKIN RAYUWATA, ni kaɗai nasan Abunda nake ji akansa." Shuru Zahra tayi bata ƙara cewa Indo komai ba haka itama Indo har suka gama lectures suka tashi jikin Indo a mace yake murus tana tunanin wani Hali mustapha yake ciki. Bayan yayi parking ne a harabar gidan sannan ya fito ya dumfari part ɗin Habeeb yana huci kamar mayunwacin zaki babu ko Sallama ya faɗa falon Habeeb yana kwance bisa cinyar HASINA sukaji tsayuwar mutum a kansu da sauri suka ɗago idanunsu Mustafa ne suka gani tsaye, tashi Habeeb yayi ya zauna yana kallon Mustafa domin kuwa yasan ba Alkairi bane ya kawo sa, cikin sakin fuska yace. " Bros kaine bismillah ka Zauna mana kana tsaye.?" Wani irin mungun kallo Mustafa yake bin Habeeb dashi kafin yace. " Hmm!! Kana TUNANIN cewa akwai Abunda zai kawo ni ɗakin maci Amana irin ka har na samu wajen Zama Allah ya sauwaƙa ko yanzu ina jin takaici da baƙin cikin kasancewar ka ɗan uwa a gare ni, da ace ina da ikon sanja ƙaddara to Tabbas da saina cireka daga sahun alhalin mu." Sa ke baki Hasina tayi tana kallon sa domin kuwa Abunda bata taɓa gani ba kenan tashin hankali tsakanin su ikon Allah kawai ta tsaya kallo shi kuwa Habeeb runtse idonsa yayi yana jin Zafin maganganun ɗan uwan nasa, cigaba da cigaba da cewa Mustafa Yayi. " Nazo ne na sanarda kai cewa kayi gaggawan fita a harkar SHATUU domin kuwa SHATUU mallaki nace, idan kuma kaƙi to Wlh ka guji Abunda zai biyo baya dan bana tunanin zai maka kyau, maha'inci maci Amana dubeka ko kunya baka ji kana son BUDURWAR ɗan uwan ka, na dai sanar da kai ka fice daga harkar ta *IDAN KUNNE YAJI JIKI YA TSIRA*." Yana gama faɗin haka ya fice ba tare da ya saurari abinda Habeeb zai faɗa ba. Harya fice Hasina na binsa da kallon mamaki, kafin ta maida dubanta ga mijinta tare da jefa masa tambaya. " Meya haɗaka da ɗan uwanka, waye kuma SHATUU, naga ya Mustafa a fusace yana faɗin magana marassa daɗin sauraro pls meya shiga tsakanin ku.?" Ta ƙarasa maganar tana kallon idonsa, ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe tare da cewa. " Soyayya itace ta shiga tsakanina da ɗan uwana, ba wata dabam bace SHATUU INDO ce haka yake kiranta dashi, tabbas maganganun sa babu daɗin ji, amma nasan ɓacin raine ya jawo yamin haka karki damu komai zai wuce." " Idan har na fahimce ka dai-dai INDO kuke so dukanku, sannan kuna shirin wargaza zumuncin ku saboda Soyayya koh, yaushe ka fara son ƙanwarmu Indo, ban taɓa jin labarin ba, kuma baka taɓa nuna min ba ko a fuskar ka, wata ƙila zan kawo maka matsala ne cikin Soyayyar ku ko, meyasa ƙaddara ta haɗaku son abu ɗaya bayan tasan ƙarfin alaƙar jinin ku tabbas ƙaddara bata muku adalci ba, da ta zukatan *JINI ƊAYA* masu ƙaunar junan su meyasa so zai muku haka.?" Ta ƙarasa maganar ba tare ta nuna masa tasan Maganar ba zuciyarta kuma tayi sanyi, shuru yayi yana matukar jin nauyin matar tasa kafin ya kamo hanunta ya fara mata magana cikin sanyin murya da sigar rarrashi. " Ki gafarce ni matata, Tabbas na ɓoye miki damuwata ta Soyayyar Indo, badan komai nayi hakan ba sai dan nasan bazaki ji daɗi ba idan kika san ina sonta, ni kuma bana buƙatar na sanar dake Abunda zai ɓata miki rai, Tabbas Soyayyar Indo tayi nisa a cikin Zuciyata yanda bazan taɓa iya cireta ba, a dole zan miki kishiya badan kin gaza min ba ko kina da wani aibu, a'a ba haka bane duk abunda namiji yake nema wajen matarsa to nikam babu abunda baki min ba na samu jin daɗi da farin ciki marar misaltuwa a gareki, kawai zan ƙara Aure ne domin Soyayya ba don gazawar kiba, kimin uzuri ki fahimce ni, akan wannan Auren da zan ƙara, Mustafa ya shigo gidan nan ne cikin ɓacin rai badan komai ba, sai dan takaicin da yake ji Cewa nine wanda nayi nasarar samun Indo bashi ba, ma'ana ni aka yiwa baiko da Indo har Daddy ya bayar da kuɗin sadaki, kuma Aure bazai wuce nan da wata huɗu ba, kinji labarin.'' Ajiyar Zuciya HASINA ta sauƙe tana murmurshi ta furta cewa. " Alhamdulillah gaskiya nayi farin ciki sosai daya kasance mijina shine yayi nasarar samun ƙanwarsa a matsayin matar Aure nasan mijina mai Sa'a ne bai cika neman abu ya rasa ba, Indo ai mutumiyar kirki ce, gaskiya kayi sa'ar samun mata ta biyu, na kuma ji daɗi sosai domin kuwa ko ba komai ina son abunda mijina yake so taya hakan zai ɓata min rai, bayan kai ya faranta maka, ka sani cewa duk abunda yake farin ciki a wajen ka, to Tabbas nima abun farin ciki nane mussaman Indo wacce na mata farin sani wanda kuma nake da tabbacin cewa bazata taɓa cutar dani ba, na kuma ji daɗi da yabon da ka min nayi farin ciki sosai da zaka ƙara Aure badan na gaza maka ba, dole na fahimce ka MIJINA domin kuwa UBANGIJI shine ya halarta muku ƙara Aure, yace kuyi ɗaya, kuyi biyu kuyi Uku kuyi huɗu, amma idan zaku iya adalci, to me zai dameni nasan MIJINA mai adalci ne, Allah ya sanya Alkairi yasa ayi damu shine kawai fata na." Ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya, zuciyarta cike da kishin Indo sai dai tayi farin ciki da mijinta yayi nasarar samun Abunda yake so. Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Habeeb, tare da wani mungun Soyayyar matar tasa da ta ƙara ninkuwa a cikin zuciyarsa tabbas wannan itace ake kira da mata ta gari. " Tabbas ke abun alfahari ne a gare ni, bansan taya zan misalta miki irin farin cikin da naji ba, da kika fahimce ni har kika karɓi Abunda nake so da hanu biyu, Allah ya miki albarka." Da ameeen HASINA ta amsa kafin suka cigaba da zancen su, amma duk rabin hankalin Habeeb yana ga ɗan uwansa. Babu sallama ya faɗa falon nasa, RAUDA na zaune cikin tashin hankali, na rashin kwanan da mijinta baiyi ba a gida, gashi idan ta kira layinsa baya ɗauka da har ta fara tunanin zuwa ta sanar da su Momy sai kuma taga shigowar sa yanzu cikin sauri ta miƙe da kyar kasancewar cikin nata ya fara tsufa tace. " Ya Mustafa tun jiya hankalina yake tashe, na kasa bacci ina ka kwana Allah yasa dai lafiya." Tsuka Mustafa yaja yana ƙare mata kallo, cikin gatsali ya mayar mata da amsa daman da haushin sa ya shigo, dake ita ce ƙaramar katangar sa daɗin ƙetara yace mata. " Inda kika aikeni naje ni uwata, dake zaman ki nake ai dole na sanar dake duk inda zani Uwata." *Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻* *(Ummu Nasmah ce)* [5/1, 9:31 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘💘💘 *S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽* *Cigaban* *(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)* 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘 💘💘 *Na* *r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸* *(մʍʍմ ηαςʍα)* 👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻 *Marubuciyar* *Sauyin Rayuwa* *Nasmah ko Nasirah* *Sara da Sassaka* *INDO A BIRNI* AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*. *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ *D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞* *Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa* Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake. Allah yabar ƙauna. *S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢* *AUNTY HAUWA MAMAN USWAN* Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya. ________________________________________ *P*•••••••2️⃣5️⃣ ↗️ 2️⃣6️⃣ " Allah ya huci Zuciyar ka hankali nane ya tashi naga baka saba kwana a waje bane shiyasa hankalina ya tashi, amma Allah ya huci Zuciyar ka." Tsuka yaja ba tare da ya kalle ta ba ya shige cikin bedroom ɗinsa, zama RAUDA tayi zuciyarta na cunkushe duk da ta samu sauƙin Abunda Mustafa yake mata sosai amma har yanzu yakan mata wasu abubuwan da bata jin daɗin sa, tagumi tayi tana jinmamin halin da Mustafa, shi kuwa bayan ya shiga bedroom ɗin nasa kwanciya yayi tare da yin shiru damuwa na cinsa ya rasa ya zaiyi da Zuciyarsa babu abunda take masa sai suya, haka ya wuni kas cikin ɗaki har dare. Washegari da safe Indo ta sauƙo ta yiwa Momy duk aikin da ta saba bayan ta gama aikin ne ta ɗaura breakfast, shima da ta gama ta jera a daining tana shiga bedroom ɗin ta Momy ta bi bayanta, ta samu waje gefan bed ɗinta ta zauna tare da cewa Indo, ta zauna za suyi Magana, zama Indo tayi tana fuskantar Momy, dubanta sosai Momy tayi kafin ta fara magana. " INDO wai meyasa ke mayyace kam dole sai kin Auri ɗana ne, nace bana sonki na tsaneki amma ki dage dole sai kin haɗa jini dani, dan Allah na roƙeki ki fita daga harkar ƴaƴana kije ki sanar da Alhaji cewa kin fasa wannan auren, ni kuma na miki alƙawarin duk abunda kike so zan baki ko meye ne idan ma kuɗi kike buƙata ki faɗi ko nawa ne zan baki." Shuru Indo tayi tana al'ajabin ƙiyayyar da Momy take mata ta rasa me ta tare mata a duniya take gwada mata wannan baƙar ƙiyayyar kanta sunkuye tace. " Ki gafarce ni Momy gaskiya bazan iya tunkarar Daddy da wannan maganar, amma Momy idan babu me zai hana shi ya Habeeb ki sanar dashi ya faɗawa Daddy ni na amince zan haƙura da Auren ƴaƴan ki Idan har hakan zaisa ki sassauta ƙiyayyata cikin zuciyarki, bana buƙatar komai daga gareki domin kuwa babu wani abun duniya da nake buƙata a wajen ku, idan banyi addu'a Allah ya hore min na baku ba Ni ai bazan yi burin karɓar naku ba, kiyi hkr Momy idan maganganu na sun ɓata miki rai iya gaskiya ta na sanar dake." Wani mungun kallo Momy take bin Indo dashi na tsana kafin cikin ɓacin rai tace. " Lallai kin iya magana kam, kamar mutumiyar kirki, sai dai ki sani wannan daɗin bakin naki bazai yi tasiri a kaina ba, ni shawara na baki akan ki fita harkar ƴaƴana, amma tunda kinƙi ji to ki sani bazaki ƙi gani ba, domin kuwa bazan taɓa barin ki kiji daɗin Aure ba, muddun kika Auri ɗana." Tana gama faɗin haka ta tashi ta fice tana ƙwafa, hawaye ne ya ziraro daga idanun Indo, kafin ta goge ta kwanta ruf da ciki, ranar haka Indo taƙi fitowa falo domin kuwa itama yanzu ta fara jin Zafin Momy, ko ganinta bata son yi saboda tsantsar jin takaicin tsanar da Momy take gwada mata. A haka rayuwar ta dinga tafiya yayin da Mustafa ya daina koda kallon inda Habeeb yake shi kuwa Habeeb duk sanda suka haɗu sai ya yiwa Mustafa Magana amma ko kallon sa Mustafa baya yi, Mamy kuwa kullum cikin ruɗar Momy take da wajen bokan ƙarya, haka ta dinga ɓatar da ita amma Momy ta kasa ganewa. ********************************* Yau watan cikin RAUDA tara yayin da take cikin watan ta na haihuwa, sassafe ta shirya domin zuwa gida gaida Abbanta baida lafiya, Mustafa yana bedroom ɗinsa, kwance shima ba lafiyar bace dashi, dan harma ya ɗan rame, ciwon ƙirji ne yake yawan damunsa ga nauyi da ƙirjin yake masa yana kuma yawan yin tari bedroom ɗin nasa RAUDA ta shigo ta gaishe sa kafin tace. " Ya Mustafa baka da lafiya ne.?" Ɗago kansa Mustafa Yayi ya dubi RAUDA cikin sanyin Murya yace. " Lafiya ta ƙalau babu abunda yake damu na me kika gani kinga alamun rashin lafiya a tattare dani ne.?" Zama RAUDA tayi a gefan sa tace. " Eh mana naga alamunka duk sun nuna kamar baka da lafiya, PLS ya Mustafa ka sanar dani me yake damunka, hankali na yana tashi idan na ganka cikin wani yanayi na gwammace ni na kasance cikin wannan halin kai ka Zauna cikin farin ciki, dan Allah ka sanar dani me yake damunka." Wani irin tausayin RAUDA ya kama Mustafa, ta na yawan damuwa idan ta gansa a cikin wani hali tana lura da duk wani lamuran sa, amma sai dai shi ya kasa bata farin ciki, bazai iya sanar da kowa Abunda yake ji cikin zuciyarsa ba, ya gammaci ya mutu ko zaiji sauƙin Abunda yake damunsa baya ƙaunar Allah ya nuna masa ranar da zaiga auren Habeeb da SHATUUN sa, gara kawai yaga mutuwar sa da yaga wannan auren, duban RAUDA yayi yace. " Karfa ki damu babu abunda yake damuna, kiyi tafiyar ki kawai, ki gaishe da Abban nima zanzo na gaishe daga baya." Kaɗa kanta kawai RAUDA tayi badan ta yadda da Maganar Mustafa ba ta wuce abunta, bata juma da fita ba shima Mustafa ya fito yayi part ɗin Momy tana zaune ya sameta ta haɗa fuska, zama yayi yana cewa. " Momy lafiya naga kamar ranki a ɓace." Tsuka taja tana cewa. " Lafiya lau waɗannan yaran nake jira su sauƙo ƴan iska mayu tun ɗazu suka haura amma sunƙi fitowa ni so nake ma ta fito ta wuce ƙauyen nasu ko zan huta." " Wasu yara kuma Momy.?" " Waye kuwa bayan Habeeb da wannan baƙar mayyar Indo, kasan yau zata bar garin nan zai kaita ƙauyen su, gobe idan ta koma jibi kuma za'a kai kayan Auren nasu bazata dawo ba sai an ɗaura Auren naji Daddyn ku yana cewa Habeeb ɗin ne zai kaita." Dam ƙirjin Mustafa ya buga wani mungun kishin Indo ne ya daki zuciyarsa, hankalin sa ya kasa kwanciya mussaman da Momy tace suna ɗaki su biyu da Habeeb, tari ne ya sarƙe Mustafa sosai yake tarin sanda idanunsa sukayi jajur, hanunsa yasa yana tare bakin sa, ɗago hanun nasa da zaiyi sai jini ya gani, saurin danƙe hanun nasa yayi kar Momy ta gani Hankalin ta ya tashi goge bakin nasa yayi da ɗaya hanun yana ƙara ɓoye hanun nasa, Momy saurin duban sa tayi tana cewa. " Lafiya meya sameka yanzu? Tana buga masa bayan sa, ganin bai daina tarin ba ya sata tashi da sauri ta tafi ɗauko masa ruwa , ai kuwa Mustafa kamar wanda yake jira Momy ta tashi, shima ya tashi cikin sauri ya bar part ɗin, part ɗin su ya nufa ya faɗa cikin motar sa ya figeta da ƙarfi ya bar unguwar gabaki ɗaya, koda Momy ta dawo tasha mamakin rashin ganin sa inda ta barsa ƙwafa kawai tayi ta ajiye ruwan tana cewa. " Oh ni a'ishatu yanzu na barka zaune anan kana tari yanzu kuma na dawo ban sameka ba, sai kace wani aljani, ko ina kuma yayi sai Allah." Ta ƙarasa maganar tana taɓe bakin ta Tare suka sauƙo suna dariya, harda Zarah ma ashe suke cikin bedroom ɗin, Habeeb shine yake jan akwatin Indo, har suka sauƙo ƙasa, kusan tare suka fito da Daddy domin kuwa suna sauƙowa shima yana fitowa daga bedroom ɗin sa, murmurshi yayi yana tsokanar Indo. " Yau dai ƴata ana murna za'a gida, naga bakin yaƙi rufuwa yau za'a ga Mama da Baba." Dariya sosai Indo tayi sai kuma idanunta suka ciko da hawaye tana cewa Daddy. " Daddy ai dole nayi dariya, yanda na daɗe rabona da gida, sai dai kuma Daddy zuciyata sam babu daɗi sanda zan taho birni da *INNA* na taho sai dai kuma gashi yau zan koma ƙauye babu *INNA* ba kuma zanje can na ganta ba, hankalina yana tashi idan na tuno da wannan abun Daddy da wani ido zan iya kallon gidan Inna babu ita a ciki, Daddy........" Ringine ɗin wayar ta ne ya katseta tana duban wayar taga *SHARIFA* ce murmurshi Indo tayi tana goge hawayen fuskar ta tare da ɗaga wayar tana cewa. " AUNTY Sharifa kin wuni lafiya." Daga can Sharifa tayi murmurshi tare da cewa. " LAFIYA lau Indo, kwana biyu shuru matar ya Habeeb, shine Wato ko ki bani labarin cewa tsuntsun Soyayyar ya tashi daga kan ya Mustafa ya koma kan ya Habeeb, anya kuwa kin yiwa kanki adalci Indo Wanda kike so daban wanda kika zaɓa a matsayin miji daban, meyasa kika yanke wannan hukuncin.?" Runtse idonta tayi tana murmushin dole tare da duban ya Habeeb da Daddy sannan tacewa Sharifa. " AUNTY Sharifa Yanxu ina hanya ne zanje DASINA idan na ƙarasa insha Allah zan kira ki sai muyi Maganar." Daga can Sharifa tace " Shikenan Allah ya kaiku lafiya, ki gaishe da Mama idan kin isa." " Shike nan zataji insha Allah ki gaishe min da Ummi idan na ƙarasa zaki haɗamu." " Zataji " Sharifa tace tare da kashe wayar tana ganin tsantsar wautar Indo. Daddy ne yakai dubansa ga Indo yace. " Karki saka damuwar rashin Inna a zuciyarki, duk sanda kika tuno ta ki mata Addu'a, dukkan mai rai mamaci ne fatan mu Allah ya mata Rahma, gacan siyayyar da na miki nasa an haɗa miki a mota tare da na Habeeb wanda ya saya miki, idan kin ƙarasa zan kira ki, ki gaishe da mahaifan naki." " Zasuji insha Allah Daddy na gode Allah ya saka da Alkairi." Wajen Momy ta ƙarasa tare da sunkuyawa a gabanta tace. " MOMY zan tafi gida kimin addu'a idan kuma akwai Abunda na miki ba dai-dai ba ki yafe min Saboda bani da tabbacin cewa zan dawo ko bazan dawo ba, saboda halin tafiya." Taɓe bakin ta Momy tayi tana mata kallon tsana da ƙiyayya kafin tace. " Ni uwarki ce da zan miki addu'a, to bazanyi ba, idan kinga dama karki dawo idan kin tafi, ai dole ki roƙe ni gafara tunda kinsan kin cuceni kin liƙe min kin liƙewa ƴaƴana to wlh babu yafiya tsakanina dake, kawai ki rabu da ɗana sai mu Zauna lafiya idan kuma

Chapter 9 of 14