mata dan haka ba tayi mamakin Abunda Momy tayi ba yau.
Habeeb kuwa komawa yayi ya zauna tare da zuba tagumi yana nazarin maganganun Indo hankalin sa yayi mungun tashi da maganganun ta domin kuwa yana jin tsoron furucin ta hanunsa ya ɗaga sama sannan yace.
" Ya Allah gani gareka ya Allah ka zaɓa min abunda yafi Alkairi a rayuwata, idan har akwai Alkairi tsakanina da Indo Allah ka bani ƙwarin gwiwwar tunkarar Daddy, idan kuma babu Alkairi tsakanin mu Allah ka cire min Soyayyar ta cikin Raina."
Kwantawa yayi tare da yin shiru a haka bacci ɓarawo ya sacesa cike da tarin mafarkai ya kwana.
Mustafa kuwa yau cikin HAPPY yake ko masifar da yake yiwa RAUDA yau bai mata ba duk da itama fama take da kanta wani sa'in sai ta wuni a ɗaki bata fito ba gobe kam tayi niyar zuwa asibiti shiyasa tana jin shigowar sa ta fito falon sannu da dawowa ta masa bisa mamakinta sai taji ya amsa cikin sakin fuska, sanar dashi tayi cewa tana son zuwa asibiti gobe DAKATAR da ita yayi yace bari ya kira likita yazo dubata babu wani ɓata lokaci kuma ya kira doctor Sadiq cikin ƙanƙanin lokaci kuwa ya iso ya dubata sosai inda ya bata har gwajin fitsari, bayan ya gama dube-duben sane ya tabbatar musu da cewa tana da shigar ciki har na tsawon wata ɗaya da sati biyu, daga Mustafa har RAUDA babu wanda baiyi farin ciki ba, mussaman Mustafa har kyauta ya yiwa doctor.
MOMY kwana tayi ba tayi bacci ba tsabar tashin Hankalin maganganun Daddy wai Jinin ta ne zai Auri Wannan fitinanniyar YARINYAR INDO ina bazai taɓa yiwuwa ba, dole na wargaza Auren nan ko ta Halin yaya ne, da wannan mungun ƙudirin Momy ta kwana.
Washe gari da safe Indo ce ta haɗa breakfast cikin sauri domin kuwa tana da lectures 11:00am bayan ta jera komai a daining ne ta haura sama tayi wanka 10:30 dai-dai ta gama shirinta sannan ta sauƙo ƙasa Momy da Daddy sai su Ishaq ta samu a daining har sun fara breakfast zama tayi tare da cewa.
" Good morning Daddy"
Murmushi Daddy Yayi yace.
" Morning my daughter da fatan kin tashi lfy."
" Lfy lau Daddy" duban Momy tayi tace.
" Good morning Momy"
Inda Indo take Momy bata kalla ba bare tasa rai zata amsa mata, girgiza kansa kawai Daddy Yayi sannan yace.
" Allah ya sauwaƙa, Ci Abincin ƴata karkiyi let ɗin school."
Cikin sanyin jiki Indo ta ɗebi abinci muryar Sharif taji yace.
" Good morning Aunty Indo."
Murmushi Indo tayi domin kuwa Momy bata sonta amma ƴaƴan ta suna sonta dalilin daya sa take haɗiye duk wani Abunda Momy take mata.
" Morning Sharif, ba zaku school bane yau."
" Eh Aunty bazamu ba sai ranar monday yau Friday."
" To Allah ya kaimu."
Shima Ishaq gaishe da ita yayi, bayan sun gama breakfast ne Indo ta tashi ta haura sama ɗauko bag ɗinta, tana haurawa su kuma Mustafa da Habeeb suna shigowa, gaishe da Daddy sukayi ya amsa cikin sakin fuska, Momy suka juyo suka gaisar amma Momy bata amsa gaisuwar Mustafa ba, ta Habeeb kawai ta amsa nanma fuskar ta a haɗe zama sukayi Habeeb da zuciyarsa ke dukan Uku Uku yana son sanar da Daddy kuma ya rasa ta inda zai fara maganganun Indo ne suke faɗo masa cikin zuciyarsa tiryan-tiryan hakanne ya basa ƙarfin gwiwwar cewa.
" Daddy ina da Magana ne, bansan kuma yaya zaka kalli maganar tawa ba.''
Maida hankalinsa Daddy Yayi ga Habeeb yace.
" Umhumm ina sauraronka sanar dani menene.?"
Kauda kansa gefe Habeeb yayi sannan yace.
" *DADDY AKWAI ALAƘAR SOYAYYA TSAKANINA DA INDO MUN JUMA MUNA SON JUNAN MU, KUSKUREN FAHIMTA KAYI INDO DA MUSTAFA SAM BABU WATA SOYAYYA TSAKANIN SU DADDY NINE WANDA YA DACE NA AURI INDO BA MUSTAFA BA.*"
Wani iri Mustafa yake jin maganganun Habeeb ji yake tamkar kunnen sa ƙarya yake masa, domin kuwa yasan ɗan uwansa bazai taɓa son abunda yasan yana so ba sai Gashi yanzu yana jin kunnen sa yana masa ƙarya, Momy kuwa cikin sauri ta ɗago idanunta tana bin Habeeb da wani mungun kallo wani irin tsanar Indo ne ya ƙara ɗarsuwa a zuciyar Momy lallai YARINYAR nan ta cika mayya tunda gashi ta lashe mata Zuciyar ƴaƴan ta duban Habeeb Mustafa yake cikin ƙaraji yayi kukan kura ya tsakumi wuyan HABEEB yace.
" Me kake cewa ka faɗa min me kake cewa! Kuna soyayya da SHATUU oh kace kuna cin amanata, kai kai kai 👉🏻 kaine zaka ci amanata Habeeb, ɗan uwana ne fa kai wanda muka kwanta ciki ɗaya da kai aka haife mu rana ɗaya muka sha nono tare muka tashi tare har girman mu bamu taɓa samun saɓani ba, bama son abunda zai taɓa ɗaya daga cikin mu, shine yau zaka ci amanata na yadda da kai ban kuma taɓa tunanin cewa zaka taɓa yunƙurin rabani da farin ciki na ba sai gashi ka ɗauko hanya idan wasa kake Habeeb ka daina domin bamu saba Irin wannan wasan da kai ba kaji ɗan uwana." Ya ƙarasa maganar yana sakin wuyan Habeeb tare da ja da baya yana huci.
Sunkuyar da kansa Habeeb yayi ya kasa haɗa Ido da Mustafa kafin ya fara cewa.
" Banci amanar kaba Ɗan uwana, ka sani babu wasa a cikin soyayya duk maganar da nake faɗa gaskiya ne kuma har zuciyata nake faɗa maka shi, nayi duk yanda zanyi dan ganin na cireta a cikin raina amma na kasa sonta har barazana yake min da rayuwata, karka ga laifi na ɗan uwana domin kuwa shi *SO BAI SAN JINI BA* idan ya tashi shiga zuciya kawai yake ba tare da tunani ko lissafi ba, da so yana da lissafi da bai shiga zuciyar ɗaya daga cikin mu ba kamata yayi kawai ya tsaya a zuciyar mutum ɗaya Ni ko Kai amma tsabar rashin adalci Irin na SO shine ya shiga zuciyoyin mu duka biyu, *SO BASHI DA HANKALI ƊAN UWANA* ka daina ganin laifi na kaida kanka ka nuna cewa baka ƙaunar Indo kasha faɗa min da bakin ka, hakanne yasa nayi sakacin barin Soyayyar ta ta shiga cikin zuciyata komai ya faru laifin kane da tun farko ka amshi Soyayyar ta kamar yadda ta nuna maka da bazan taɓa yadda sonta ya shiga zuciyata ba, bare har yamin mungun kamu, kace min kana sonta tun tana DASINA idan har da gaske ka sonta a wannan lokacin to meyasa ka ƙita kake ƙyamar ta meyasa ka kasa kula da lamuranta meyasa kake zaginta a duk sanda kuka haɗu hakan duk yana cikin SOYAYYA ne? Ka bani amsar tambayata ."
Ja da baya Mustafa yake yana nuna Habeeb da hanu yana cewa.
" Kana jinshi ko Daddy kana ji fa daddy wai SHATUU yake so numfashina yake so Daddy kasheni yake neman yi rayuwata zai karɓa Daddy, anya kuwa shi ɗan uwana ne Daddy, daddy anya ɗan uwana Habeeb ne dana sani Daddy ƙarya yake baya soyayya da SHATUU nasan ni kaɗai take so nine kawai a cikin ranta kana ji Daddy har wani banzar tambaya yake min ."
MOMY da ta gama ƙula ne ta tashi cikin fusata ta ɗauke Habeeb da tagwayen mari, sannan ta taka har gaban Mustafa shima ta ɗaukesa da mari cikin ƙaraji take cewa.
" Meye a jikinta har kuke neman raba alaƙar dake tsakanin ku, me zakuyi da ita wannan tantiriyar data gagari iyayenta sanda suka haɗota damu me zakuyi da wannan taburmar ƙayar, to bari kuji idan nine uwar ku dana sunkuya nayi naƙudar ku na rabaku da wannan YARINYAR babu ku babu ita har abada domin kuwa bazan taɓa yadda ɗaya daga......"
Tsawa Daddy ya daka mata yace.
" Ya isheki haka A'ISHA ki rufe min baki karna ƙara jin maganar ki anan wai meyasa ne kike haɗa hankalinki da tuwo kike cinyewa ne, ki kama girman ki tun kafin ƴaƴan ki su daina ganin girman ki, ki kuma sassauta wannan munguwar ƙiyayyar da kike gwadawa yarinyar nan domin kuwa baki san gaba ya zata kasance ba wata ƙila ta amfane ki fiye da ƴaƴan ki da kika haifa ki sani cewa *ƳAƳA DA DUKIYA BA'A MUSU MUGUNTA* Saboda baka san wa zai taimake ka ba gaba, ki riƙe wannan a ƙwaƙwalwar ki ƙi kuma shiga hankalin ki."
A fusace Momy tace.
" Babu wata ranar da wannan YARINYAR zata min yarinyar da bata yiwa iyayen ta rana ba wa zata yiwa Rana, nifa Alhaji ina kan bakata Wlh babu ƴaƴa na babu wannan YARINYAR."
Tana gama faɗin haka ta ɗauki jakarta da hijab ɗin ta dama unguwa zata ta fice tana jefa yarannata mungun kallo, Daddy maida hankalin sa yayi garesu yace.
" Kowa ya shige ya tafi wajen aikinsa kun kusa kuyi let zan neme ku daga baya, kuma ban yafe ba idan kuka yi koda cacar baki ne a hanya kuje Allah ya muku albarka."
A fusace Mustafa ya juya ya fice daga falon Habeeb cikin sanyin jiki ya fita Indo dake tsaye a step ɗin falon ne ta sauƙe ajiyar Zuciya tare da ficewa tana kiran Zarah a waya, koda ta fito dukkan su sunja motar su sun bar gidan itama motar da driver yake jiranta ta hau suka kama hanyar makaranta.
MOMY DARECT gidan su RAUDA ta nufa wajen Mamy domin ta taya ta neman solution hon tayi mai gadi ya wangale mata get ɗin ta shige.
_______________________________________
Kuyi hkr da wannan yau ina cikin busy ne🙏🏻
*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah ce)*
[4/13, 8:29 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘
*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*
*Cigaban*
*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*
AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*AUNTY HAUWA MAMAN USWAN*
Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya.
_______________________________________
*P*•••••••1️⃣9️⃣ ↗️ 2️⃣0️⃣
Parking tayi sannan ta shige falon Mamy darect tana ɗauke da Sallama a bakin ta, tana zaune ta harɗe kafafunta ɗaya kan ɗaya tana danna waya, taji sallamar Momy tana dariya ta tashi tace.
"Ameeen Wa'alaikimussalam Hajiya A'isha yau kene tafe gidan nawa lale marhaba."
Murmushi Momy tayi tana zama bisa kujera tace.
" Nine tafe Hajiya Turai naga kin yafe gidana ne tunda muka Auri ƴarki ko gidan namu kin daina kallo bari muyi tunanin ganinki."
Dariya Mamy tayi tace.
" Kema dai kinsan halina ba son yawo gareni ba, jiya muke magana da Hajiya Hindatu akan cewa zamu je muga ɗakin RAUDA, ta kiran ma ta sanar dani bata jin daɗin jikinta ɗazun nan wai mun samu ɗan jikalle."
Dariya Momy tayi cikin farin ciki take cewa.
" Masha Allah! Kinga nida nake tare dasu ma bani da labari to Allah ya raba Lafiya shiyasa kwana biyu bata shigo min niko Hankali na baya kwance shiyasa ban leƙata ba."
Murmushi Mamy tayi tana ƙoƙarin tashi tare da cewa Momy.
" Bari naje na kawo miki ko ruwa ne kisha sai mu zauna musha fira kinga gashi an juma ba'a haɗu ba."
Dakatar da ita Momy tayi tare da cewa.
" Kibar ruwan nan yanzu muka gama breakfast so bana jin ƙishirwa, kinga nifa matsalace ta kawo ni gidan ki nazo wajen kine nasan ba'a rasa sulution a wajen ki."
Komawa Mamy tayi ta zauna cikin mamaki take cewa.
" Matsala kuma Hajiya A'isha sanar dani mu samo mafita yanzun nan.?"
Ajiyar Zuciya Momy ta sauƙe ta dubi Mamy tace.
" Eh Matsala Hajiya Turai babbar matsala ma kuwa ina cikin tashin hankali sosai Wlh."
" Kinga Hajiya A'isha kin kulleni a duhu fitar dani haske meke faruwa sanar dani.?"
" Hajiya Turai kin dai san akwai yarinyar da Alhaji ya ɗauko daga ƙauyen su ko? wannan fitinanniyar YARINYAR dana taɓa baki labarin ta, koda yake kin santa ma tunda kinsha zuwa ki sameta a cikin gida na."
" Eh na ganeta wani abunne ya faru da ita.?"
" Ai Hajiya Turai da wani abu zai sameta sai na fi kowa farin ciki musamman ma ace min ta mutu da saina zuba ruwa a ƙasa nasha, bana ƙaunarta ko kaɗan" labarin Abunda yake faruwa Momy ta bawa Hajiya Turai bata ɓoye mata komai ba har zuwa yau da Habeeb shima ya furta yana son Indo.
Shuru Mamy tayi tana sauraron Momy harta dasa aya kafin tace.
" Cap BABBAR MAGANA, yanzu ke Hajiya A'isha me kika yanke kin yarda ne? idan har ke kin yarda to ni bazan yadda a yiwa ƴata kishiya ba, ban zauna da kishiya ba kinga kuma ƴata bazata zauna da kishiya ba, sanar dani me kika yanke.?"
" Hmm Yanzu ke Hajiya Turai idan aka ce miki na yadda da wannan Auren sai ki yadda, kema dai kinsan na tsani YARINYAR nan to kuma taya kike tunanin zan yadda da wannan haɗin, nifa Abunda ya kawo ni gidan ki neman mafita ne, kinga Alhaji yana son Auren nan sosai har takai yana min barazana da kalmar saki nema fa take ta koreni daga gidan uban ƴaƴana kuma wlh bata isa ba."
Wani malalacin murmurshi Mamy tayi na mugunta tana duban Momy tace.
" Kwantar da hankalin ki ƙawata kamar kin kashe ɗan Mutum tunda kika kawo wannan matsalar wajena an gama da ita, kin gane, ki bari Ranar Lahadi, misalin ƙarfe 12:00am na rana kizo ina da inda zamuje a yi maganin wannan matsalar karki saka damuwa cikin ranki kar kuma ki sake yin faɗa na faɗa da mijinki kina shurun ki su da kansu zasu wargaza Maganar da kansu ta hanyar sa musu tsanar yarinyar a zuciyarsu badai Malam yana raye ba to kwantar da hankalin ki insha Allah komai yazo ƙarshe kamar anyi ruwa an ɗauke."
Dariya dukansu suka saka Momy ne tace.
" Shiyasa nake sonki ƙawata akwai ki da neman mafita, badai a kawo matsala wajen kiba sai kinyi maganinta, kice na kusa yarda ƙwallon mangoro na huta da ƙuda kinsan Allah yarinyar nan ta shige min hanci da ƙudunduno neman yadda zanyi na fyace ta nake yi ko zan samu sa'ida."
Dariya sosai Mamy take ta cewa Momy
" Ai kawai ki kwantar da hankalin ki ƙawata kin kusa fyaceta ki huta badai kinzo wajen Turai ba ai an gama kawai."
Dariya sukayi duka sun juma suna hira kafin Momy tayiwa Mamy sallama da alƙawarin cewa zata zo ranar Lahadi har parking space ta rakata sanda taga fitarta sannan ta koma falon nata, tana shiga ta sheƙe da dariya cikin salon mugunta take cewa.
" Alhamdulillah! Lokaci yayi da zan tatsi kuɗin uban mijina daga gareki Hajiya A'isha na daɗe ina jin baƙin cikin kuɗin da mijinki yafi nawa mijin gashi dai a ƙarƙashin inuwar uban mijina kuka tashi, Hajiya A'isha lokaci yayi da kuɗin ki zaiyi kuka zan tatseki kamar yadda makiyayi yake tatsar nonon saniya" waya ta ɗaga ta kira Malamin ta zance ko bokan ta, ringine ɗaya ya ɗaga.
" Cau cau dai Malam, mai aiki da aljanu malamin daya gagari manya bare kuma yara, ranka ya daɗe malam mai aiki da baƙin aljani."
Wani irin dariya tsinannen bokan yayi marar daɗin sauraro kafin yace.
" Faɗi menene damuwar ki, marar tsoron Allah, wacce kika kauce daga hanya maza yimin ƙarin bayani."
Shiga taitayinta Mamy tayi sannan tace.
Bayanin Momy ta masa sannan ta ƙarasa maganar da cewa.
" Mlm so nake muyi raba dai-dai da kuɗin da zata kawo ma'ana ka ninka mata kuɗi domin kuwa mijinta mai kuɗin gaske ne, sannan mlm bana so ka bata maganin da zaiyi amfani da wuri Saboda mu samu mu tatsi rabon mu, karka damu da ƴata da take auren ɗanta wannan ba ƴata bace ƴar tsintuwa ce a gidan marayu muka karɓo ta sanda bamu sami haihuwa ba, shiyasa kaga batayi halina ba, nima kuma ban damu ba ita da wahalar ta, nidai bana son ka bata sahihin magani gara muta wala gigi da hankalin ta, ka samu na samu."
Dariya ya sheƙe dashi yace.
" Baki da Matsala aike customer ce yanda kika ce haka za'ayi Lallai Turai kin cika baƙar munguwa."
Dariya ta sheƙe dashi tare da yi masa Godiya sannan ta kashe wayar.
Mustafa kuwa ikon Allah ne kawai ya isar dashi court ɗin nasu yau bai saurari kowa ba kamar yacce ya saba, office ɗinsa ya shige darect ya dannawa office ɗin key zama yayi ya kifa kansa a table ɗin wasu hawaye ne suka zubo masa masu zafin gaske shi kaɗai yasan abinda yake ji a cikin zuciyarsa wai yau shine yake hawaye akan mace RAUDA ce ta faɗo masa cikin ransa a fili ya furta cewa.
" Allah sarki ashe daman haka kike jin zafi cikin zuciryaki RAUDA, ashe daman haka zafin Soyayya take ban taɓa jin zafin ta ba sai yau, Tabbas na zalince ki sai yau nasan da haka dana ɗanɗani makamancin ɗacin da kikaji a cikin zuciyarki zan gyara zamantakewa ta dake insha Allah, meyasa zaka min haka Habeeb kafi kowa sanin nine a zuciyar SHATUU to meyasa kake ƙoƙarin shiga tsakanin mu, laifin mena aikata maka haka kake son cutar da rayuwata karka manta da kaifa ɗan uwana ne mafi soyuwa a gareni, karka cutar da rayuwata dan Allah na roƙeka."
Kusan Hauka Mustafa Yayi a wunin wannan Ranar domin kuwa ya kasa sukuni maganganun kawai yake shi ɗaya wunin Ranar baiyi aikin komai ba.
Shi kuwa Habeeb tun shigar sa asibitin aiki kawai yake amma baida nutsuwa ko kaɗan ji yake tamkar bai kyautawa ɗan uwansa ba Tabbas yayi sake da har ya bari Soyayyar Indo ta shiga cikin zuciyarsa, bai taɓa tunanin Mustafa yana son Indo ba domin kuwa shiya nuna cewa baya sonta abaya " ashe wai shi hakan sone a wajen sa, ada naso nunawa Mustafa kuskuren sa ta hanyar yiwa Indo Soyayyar ƙarya sai gashi kuma akasin haka ya faru nazo ina mata haƙiƙanin Soyayya, *SOYAYYAR GASKIYA* meke shirin faruwa tsakanina da ɗan uwana.?"
Ajiyar Zuciya ya sauƙe tare da zuba tagumi, sai kuma maganganun Momy suka faɗo masa a rai Zuciyarsa ce ta cinke cikin sauri ya ambaci sunan UBANGIJIN sa tare da tashi yayi office ɗin doctor Sadiq waiko tunanin zai ragu masa.
💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢
" Lectures ɗin yau gaskiya ban ganesa ba sosai."
" Ƙawata ina kuwa zaki gane lectures ɗin yau bayan kin shigo school da tunani, nifa yau tunda muka shiga Class nake lura da ke sam hankalin ki baya kan lectures ɗin nan, kinfi bada hankalin ki zuwa ga tunani."
Murmushi Indo tayi ta ɗaga kai ta kalli Zarah sannan tace.
Kedai Zarah bari kawai ina cikin tention Ina son Ya mustafa Zarah sai dai bazan iya Auren sa ba, na yanke shawarar Auren Ya Habeeb domin shine wanda ya dace da Rayuwata ina da tabbacin kuma zai koya min Soyayyar sa kamar yadda ya koya min shiɗin malami nane bazan taɓa manta alkairin sa gareni ba, Zarah kina ganin Abunda nayi kuwa nayi dai-dai.?"
Murmushi Zarah tayi tare da dafa kafaɗar Indo tace.
" Shawara mai kyau ƙawata, wannan shawara da kika yanke yayi dai-dai Tabbas kin cika ƴar halak da kika zaɓi Habeeb a matsayin wanda zakiyi Rayuwa dashi, nasan kina son ya mustafa Soyayya kuma ta gaskiya, sai sam bai dace da rayuwar kiba, kina da faɗa shikuma ya Mustafa yana da zafin zuciya kinga koda ace kin ɗaukesa bana tunanin zaman ku zaiyi daɗi domin kuwa biyu bata haɗuwa waje ɗaya dole ko wanne da lissafin sa, shi kuwa ya Habeeb mutum ne mai sauƙin kai zakiji daɗin zama dashi kuma ko ba komai shine wanda ya nuna miki Soyayyar gaskiya domin kuwa mutumin da bai taɓa kyamarka ba sanda kake cikin ƙazanta wannan shine masoyin gaskiya, ƙawata kiyi ƙoƙari kiga kin samu kin cire shi cikin zuciyarki ki Rungumi Ya Habeeb domin kuwa shine dai-dai ke."
Murmushi Indo tayi tare da kaɗa kanta tace.
" Anya kuwa zan iya ciresa a raina cikin sauƙi kin fa Soyayyar yarinta bana ji zai fita cikin raina nan kusa sai dai kawai zan danne zuciyata dan ganin na bawa ya Habeeb duk wani farin cikin daya dace."
Dubanta Zarah tayi tace.
" But amma ƙawata kina ga babu kuskure kuwa ga wanda kikeso kuma kice ga wanda zaki aura daban, a gani na cire Soyayyar Mustafa a ranki shine kawai mafita."
Murmushi kawai Indo tayi tare da ɗagawa Zarah hanu tana cewa.
'' times is off ya kamata mu shige Class kafin doctor Ahmad ya rigamu shiga."
Kaɗa kanta kawai Zarah tayi sannan ta tashi suka shige Class.
Da Sallama Hasina ta shiga falon RAUDA tana kwance jikinta duk a mace tun safe take amai duk abunda taci baya zama a cikin ta, ƙarasawa kusa da ita HASINA tayi ta Zauna tace.
" Baki da lafiya ne na ganki haka kwance, tun jiya banji motsinki ba, shiyasa na leƙo naga lafiya."
____________________________________
Gaskiya kuyi manage da wannan bana jin daɗi yau sorry for typing error🙏🏻 banyi editing ba.
*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah ce)*
[4/15, 3:42 PM] Ummu Nasmah: *_KU FITO MASOYA NA DOMIN NUNA MIN KALAR SOYAYYAR DA KUKE MIN TA HANYAR SAYAN NOVEL ƊIN MU, KUNDAI SAN KALAR RUBUTU NA KUN KUMA YANAYIN LABARI NA DAN HAKA KU GARZAYO DOMIN SIYAN WANNAN NOVELS ƊIN_*
*_INA KUKE MASOYAN KAINUWA WRITER MAZA KU GARZAYO KU KWASHI GARABASA DOMIN KUWA TAFE TAKE DA SABBIN LITTATTAFAN TA WANDA ZAKU AMFANA DASU KUMA KU NISHAƊANTU DOMIN KUWA MUNYI LALUBE MUN ZAƘULO MUKU FASAHAN MARUBUTAN ZAMANI WANƊA SUKA ƘWARE WAJEN KAWO MUKU TSAFTACACCEN LABARI MAI SANYA ZUCIYA SANYI_*
*_ZAKAƘURAN MARUBUTAN DAZA SU FADAKAR DAKU ACIKIN WAƊAN LITTAFAN NASU SUN HAƊA DA_*
*AISHA ABULLAHI FULANI*
Wacce ta nishaɗantar daku a cikin littafinta mai taken *MA'AURATA*.
Yanzu ma a shirye take tsaf domin ganin ta faranta muku rai tafe take da sabon salon labarin ta mai taken.
*RAYUWAR MU*
*RASHEEDAT USMAN*
*(UMMU NASMAH)*
Wacce ta nishaɗantar daku a cikin wannan shahararren Novel ɗin nata wanda yazo muku a cikin fittatu 15 daga ƙungiyar kainuwa Wato.
*INDO A BIRNI*
Yanzu ma dai tafe take da Sabon salon labari mai Ruɗa Zuciyar mai karatu kun dai santa bata wasa wajen zaƙulo muku daddaɗan labari mai cike da darasin Rayuwa tare da nishaɗi to yanzu ma dai gata tafe da sabon book ɗinta mai taken.
*RUƊANIN ZUCIYA BIYU*
*Haleematu Hassan Leemat*
Wacce ta ni shadantar daku acikin littafinta na ADALI'LIN DA NAMIJI
yanzu ma ta sake kawo muku wani sabon littafinta mesuna *LAIFIN WA?*
*(MAZAN KO MATAN)*
*FAUZIYA AUWALU ALIN BABA JINGAU*
*(YAR MUTAN JINGAU)*
Itace dai wannan shahararriyar marubuciyar da take nishaɗantar daku wacce ta jajurce wajen zaƙulo muku labari kan lamuran dake addabar mu cikin al'umma wacce ta kawo muku labarin.
*ABINDA KE FARUWA*
Yanzu mai dai tafe take da labarin da zai taɓa zuciyar mai karatu zai nishaɗantar daku ya kuma faɗakar daku mai taken.
*DAMUWA MUNGUN CIWO*
*NA'EEMA SULAIMAN*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 14