Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a matukar sanyaye ta ƙaraso gefen sa ta zauna, cikin sanyin murya tare da ƙunar Zuciya ta furta masa cewa. " Ya Mustafa ashe daman Indo kake so, ka dinga wulaƙanta rayuwata, ya Mustafa meye laifi na danna soka? Meye laifin mutumin daya soka tsakani da Allah ya yarda ya zauna da kai cikin tsananin wahala domin ban taɓa jin daɗi koda na sakan ɗaya bane a cikin gidan nan, *SABODA ITA DAMAN KAKE WULAƘANTA NI* ni bazan hanaka Auren Indo ba, haka kuma bazan ɗaga hankali na ba, tunda nasan baka sona kaga babu wani amfani nayi kishi a kanka kuma bana tunanin zaka soni ko nan gaba bazanyi yaji dan zaka ƙara Aure ba, bare har na tona asirin aurena a gidan muba, sai dai ina son ka sani cewa zalintata da kake akwai Allah yana ji kuma yana gani shine kuma mai sakayya, ina maka fatan Alkairi game da neman aurenka Allah ya baka Sa'a." Cikin kuka ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tashi tabar wajen domin a yanzu taji ta fara tsanar Mustafa cikin rayuwarta muryar sa taji cikin tsawa yana cewa. " To munafuka me kike nufi Allah ya isa kika jamin ko meye, munafuka da kike cewa akwai Allah yana ji yana gani Kuma shine mai sakayya, to daman ai shine mai sakayya, kuma nine zai sakawa da kika cuceni aka aura min ke dole ba tare da ina sonki ba, nine ya kamata na ja miki Allah ya isa domin aurenki cuta ce a gare ni, kuma bari kiji daman ni da Sa'a ta nake yawo da ita nazo duniya so bana buƙatar Addu'ar ki tunda ba uwata bace ke, idan kinga dama ki tayar da hankalin naki wannan damuwar kice ba nawa ba, ni wlh da zaki tafi gidan naku ma da kin taimake ni, dan zanfi sakewa nayi walwala idan babu ke cikin gidan nan *NA MAIMAITA MIKI INDO ITACE NAKE SO KUMA ITACE ZUCIYATA ITACE RAYUWATA GABA ƊAYA* Tashi ki ɓace min da gani mtsss." Ya karasa maganar tare da tsaki. Shuru RAUDA tayi hawaye na gudu a kuncinta ta shige cikin ɗaki, zama tayi gefen gado tayi tagumi sai yanzu taji ta fara danasanin Auren Mustafa domin ƙiyayyar da yake mata ya fara yawa, wayarta ta ɗaga ta dannawa Zaliha kira ƴar baffan ta wanda suke ciki ɗaya, tana ɗagawa RAUDA tace " kizo gida na ki sameni ina cikin matsala Zaliha" tana gama faɗin haka ta katse kiran ta kwanta, can taji shigar text message cikin wayarta dubawa tayi taga Zaliha ce ta turo mata cewa. " Bazan samu zuwa yau ba, amma gobe zanzo da yamma." Allah ya kaimu RAUDA ta furta tare da kwanciya cikin tashin hankalin ƙalubalen da yake gabanta hawaye na cigaba da zuba cikin idanunta. 💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢 Ta juma sosai a gidan su zarah kafin drivern gidan ya dawo da ita gidan Aunty Hindu da Sallama ta shigo cikin falon muryar sa taji ya amsa mata da cewa. " Ameeen Wa'alaikimussalam farin ciki na barka da dawowa." Turus ta tsaya tana duban sa jin ya ambace ta da wani sabon suna wai *Farin ciki na* taɓe bakin ta tayi tuno da zancen Aunty Hindu na ɗazu da take cewa Barrister yana sonta, duban sa tayi ba tare da ta sanja masa fuska ba tace. " Barrister Umar kaine tafe da la'asar haka, sannu da zuwa" ta furta masa tare da zama tana fuskantar sa. Shima cikin happy yake kallon ta kamar zai haɗiyeta yace. " Wlh kuwa nine tafe na jiraki harna fara ƙosawa ina kikaje haka tun ɗazu nake zaman jiran ki?" Murmushi Indo Tayi ba tare da ta nuna masa wani sauyawa cikin fuskar ta ba tace. " Naje gidan su Bestie nane kace kasha jirana, to sorry." Murmushi Barrister Umar yayi cikin zolaya yace. " Sorry for what Hajiya?" Murmushi itama tayi kafin tace. " Sorry for waiting me, naga kamar ka gaji da yawa na jirana dama gashi rago ne kai ɗin Allah dai yasa Ummi ta baka ruwan sanyi kasha nasanka da son ruwan sanyi." Cikin dariya ta ƙarasa maganar tana duban sa. Murmushi Barrister Umar yayi yace. " Ke kuwa ina kika taɓa ganin inda uwa ta hana ɗanta ruwan sanyi ai ina zama ummi na tana kawo min ruwa, kinga aiki zan tafi nasan yanzu haka Oga Mustafa yana can yana jira na, daman na biyo na ganki ne kawai na wuce." Jin sunan Mustafa da Indo tayi Habeeb ya ambata sai da gabanta ya faɗi, murmurshi kawai tayi tace. " Na gode Barrister Allah ya bada Sa'a a dawo lafiya." " Ameen bye." Murmushi INDO tayi itama ta tashi tayi ɗaki wajen Aunty Hindu. " Ina kika shiga A'isha? nayi zaton gida kika dawo nazo na tarar bakya nan." " Ummi gidan su Zarah naje." Girgiza kanta Aunty Hindu tayi ba tare da tayiwa Indo maganar Mustafa ba da Barrister Umar tace " Daddyn ku yace bazai yiwu ki bimu Egypt saboda baya son kiyi nesa dasu yace ma gobe ki koma gida, dan haka ki haɗa kayan ki duka gobe da yamma zaki koma can." Shuru Indo Tayi idonta ya ciko da hawaye tace. " Yanzu Ummi tafiya zakuyi ku barni, Ummi bana son zaman gidan Momy PLS Ummi ki tafi dani dan Allah nafi son na zauna tare dake." " Kiyi hkr Indo bai kamata muyi musu da Daddyn kuba, ki koma gabansa ki zauna ki ɗauko hakuri da juriya ki sa a cikin rayuwarki na tabbata wata rana zaki ci ribar haƙuri ki musu biyayya tamkar yanda za kiyiwa iyayenki hakan shi zaisa ki shiga ran kowa." Sosai Indo taci kukan rabata da Aunty Hindu da Daddy Yayi amma babu yanda ta iya haka taci kukanta tayi shiru ta ɗauƙi dan gana. Da sallama ya shiga office ɗin nasa, yana jin sallamar tasa yayi banza dashi kamar bai jiba, sanda yayi sau wajen uku kafin ya amsa da ƙyar, ƙarasowa Barrister Umar yayi ya zauna yana miƙawa Mustafa hanu, amsa yayi sukayi musabaha sannan Barrister Umar yace. " Sorry Oga nayi let na biya wani waje ne amin afuwa, na haɗa duka infomations ɗin da kake buƙata sai dai ......." Dakatar dashi Mustafa Yayi ta hanyar ɗaga masa hanu yace. " Ba wannan bane a gaba na, so nake ka fara sanar dani *MENENE YAKE TSAKANIN KA DA SHATUU IDAN BAKA GANE BA INA NUFIN INDO*.?" Shuru Barrister Umar yayi yana kallon sa Kafin ya buɗe bakin sa yace............... *Muje zuwa yanzu aka fara wasan*🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀ *Vote* *Share* *And* *Comments* *Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻* *(Ummu Nasmah ce)* [3/31, 10:00 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘💘💘 *S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽* *Cigaban* *(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)* 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘 💘💘 *Na* *r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸* *(մʍʍմ ηαςʍα)* 👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻 *Marubuciyar* *Sauyin Rayuwa* *Nasmah ko Nasirah* *Sara da Sassaka* *INDO A BIRNI* AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA* *D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞* *Aunty fauza ƴar Amana* Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake. Allah yabar ƙauna. *S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢* *Aunty Hauwa Maman Uswan* Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ *P*••••••5️⃣ ↗️ 6️⃣ " Meyasa kamin wannan tambayar Barrister? Barrister Umar ya jefowa Mustafa Wannan tambayar cikin mamaki. Murmushin gefen baki Mustafa Yayi cikin isgili ya cewa Barrister Umar. " Wai kai a haka lauyer kake ɗaukar kanka ko? Hmmm su malam lauyer manya, a matsayinka na lauyer akwai dokar da ta ce ka maida tambaya cikin tambaya kafin amsar tambayar farko, na tambayeka baka bani amsa ba shine kake kuma jefo min wata tambaya robbish lauyer kenan kake ƙoƙarin maida kanka, da a gaban Shari'a kake tabbas da ka faɗi, ya kamata kake aiki da doka a matsayinka na Barrister, answer Question meye tsakaninka da *INDO*?" SHURU Barrister Umar yayi na wasu lokuta dan ya ɗan ji zafin maganganun Mustafa kafin ya dubesa cikin ɓacin rai yace. " Oga banda amsar tambayar ka ta biyu, a yanzu, sai dai ga amsar ka ta farko, ina zaton cewa zuciyata ta kamo da matsanancin ƙaunar ta, wacce take tafiya tare da ko wanni bugun numfashina Rayuwata ce ita ɗin.?" Runtse idonsa Mustafa Yayi yana jin maganganun Barrister Umar cikin ƙwaƙwalwar sa da kunnen sa tamkar ana masa feshin wuta, buɗe idanunsa yayi waɗanda suka kaɗa suka koma jajaye lokaci ɗaya, ya fara maidawa Barrister Umar Magana son ransa. " Ya kamata zuciyarka tayi gaggawar cire INDO cikin ta, domin kuwa Indo bazata taɓa sonka ba, kayiwa Zuciyar ka faɗa tun kafin lokaci ya ƙure maka ta kasa amfanan ka, ka tausashi numfashinka tun kafin ya fara neman ɗauke maka kana jawosa yana ƙoƙarin barin jikin ka, domin kuwa Indo ba matar Auren ka bane ina sanar dakai wannan shawarar ce a matsayina na abokinka domin ina tausayawa zuciyarka kamuwa da mungun ciwon Soyayyar wacce bazata sameta ba domin ta maka zarra." Wani irin kallo Barrister Umar yake bin Mustafa dashi mai cike da alamomin tambaya, cikin tashin hankali Barrister Umar yake tambayar Mustafa. " Me kake nufi da wannan maganar taka, shin Indo tana da wanda take so tuntuni ko me kake nufi.?" Murmushi Mustafa Yayi yana duban Barrister Umar Kafin yace. " Yes ka amsawa kanka tambayar ka, tana da wanda take tsantsar so wanda bazata taɓa iya rayuwa babu shiba, ba zata iya ciresa cikin Zuciyarta ba, wannan mutumin shine rayuwar ta, shine duniyar ta, shine farin cikin ta, dan haka ka cire kanka cikin niyyar shiga tsakanin masoya dan zakayi danasani ne a gaba marar Amfani amma shawara ce idan ka ɗauka." Murmushi sosai Barrister Umar yayi kafin yace. " Na fahimce ka, na kuma fahimci shi wanda kake kira tana so, sai dai kuma banga Soyayyar wani cikin Zuciyarta ba, tunda gashi na fara hango soyayyata cikin idanunta, karka damu da wahalar da zan shan indai akan Indo ne na shiryawa hakan zan iya shiga ko wani irin hali ne saboda farin cikin zuciyata, zan kuma iya karawa dashi wanda kake kira duniyar ta, *ITA MACE AI ALLURAR CIKIN RUWA CE MAI RABO SHIKE ƊAUKA* dan haka ina yiwa mai rabo fatan Alkairi, mu zuba muga wanda zai ɗauka nasan ina tafe da nasara ta a ko yaushe." Barrister Umar yana gama faɗin haka ya sarawa Mustafa tare da juyawa ya fice daga cikin office ɗin ba tare daya ƙara sauraron Mustafa ba. Murmushi mustafa Yayi yana yiwa Barrister Umar kallon tausayi dan yana da tabbacin cewa muddun yana raye Indo bazata taɓa son wani Namiji ba, tashi yayi ya kwashi Key's ɗinsa ganin an kusa fara kiran sallar magaruba, bai shiga cikin gidan sa ba, sai da yayi sallar magaruba sannan ya fara shiga part ɗin Momy domin kai mata hira. Habeeb kuwa suna zaune da HASINA yaji ringine ɗin wayar sa, dubawa yayi yaga kiran Aunty Hindu ne, kallon HASINA yayi yace. " Aunty ce take kira bari muji Allah dai yasa lafiya" Da "ameeen" Hasina ta amsa shi kuma Habeeb ya ɗaga wayar basu wani juma ba ya katse kiran yana duban Hasina yace. " Kira na Aunty take, tace nazo yanzu bari naje na dawo.'' Duban Habeeb tayi tace. " Allah yasa dai lfy Ummi take neman ka yanzu kaje Allah ya dawo da kai lafiya." " Ameen" Habeeb yace tare da ɗaukar key ɗinsa ya fice, tunda Habeeb ya fita ƙirjin Hasina yake bugawa domin kuwa tasan dole zai haɗu da Indo a can, dafe ƙirjin ta tayi tana lumshe idanunta tare da jin wani kishin Indo yana taso mata. Cikin mintuna kaɗan Habeeb ya shiga cikin gidan Aunty Hindu, a falo ya tarar da ita tasa Indo a gaba ga akwati a gaban su Indo sai famar sharɓar kuka take, cikin sauri Habeeb ya ƙaraso wajen nasu yana cewa. " Subhanallah! AUNTY meya faru take faman kuka haka?" Duban sa Aunty Hindu tayi tace. " Ko kaima ka tambaya, kiran dana maka kenan, gata nan dan kawai nace ta haɗa kayan ta, Anjuma driver ya maidata gidan ku shine take rusar wannan kukan ita dole bazata koma ba, kuma kasan Daddyn ku cewa yayi gobe tayi sammako ta dawo, shine ta koma kawai yanzu yafi tayi sammakon, tace ita dole saita jira Abban Hasina ya dawo daga Abuja kuma shi dawowarsa babu lokaci, dan wata ƙilma nice zanje canna samesa mu wuce Egypt." Murmushi Habeeb yayi tare da zama yana duban Indo yace. " Barni da ita Aunty jekiyi Aikin ki kawai." Tashi Aunty Hindu tayi ta wuce bedroom ɗin ta tana yiwa Indo sababi. Haɗa ransa Habeeb yayi yana duban Indo da itama ta maida dubanta garesa yace. " Da a ina kike kafin Aunty Hindu tazo kasarnan okey na gane wato bakya son gidan mu saboda ba'a biya miki bukatunki ko? Ba'a miki Abunda kike so babu mai kula da lamarin ki ko okey ba damuwa wata ƙila mu bamu da Abunda zamu baki shiyasa zaki gujemu yanzu." Zaro ido Indo tayi tana kallon Habeeb cikin yanayin tashin hankali tace. " Me kake faɗa haka ya Habeeb babu ko daɗin ji, ya Habeeb ni kuwa ina inke da gatan daya fi wanda kamin kaida Daddy, koni butulu ce bazan ce wani gida yafi na Daddy ba, kawai na shaƙu da Ummi ne shiyasa nake ji kamar bazan iya rabuwa da ita ba, amma dan Allah ka daina faɗin wannan maganar." " Bakya san rabuwa da Aunty Hindu amma kina son ɓacin ran daddy ko?" Muryar Indo kamar zata sake fashewa da kuka tace. " Ya Habeeb ya za'ayi naso ɓacin ran Daddy haba ya Habeeb ka daina faɗa min wannan maganar haka, na yadda ka tashi kawai mu tafi ka daina faɗamin." Murmushi Habeeb yayi cikin ransa ganin harya samo kanta cikin sauƙi kafin yace. " Jeki kuyi sallama da Aunty Hindu sai kizo mu tafi." Tafiya Indo tayi bedroom ɗin Aunty Hindu ta sameta Zaune bakin bed ɗinta tana ninke kayan ta zama tayi gefen ta tace. " Ummi zamu tafi da ya Habeeb zai sauƙe ni a gida." Kallon tausayi Aunty Hindu take yiwa Indo har Zuciyarta taso a bata Indo sai dai babu yanda ta iya fadan daya fi ƙarfin ta dole ta maida shi wasa, ko zuwa ƙauyen DASINA ma ta fasa daman saboda Indo zata tunda kuma bazata ba ta fasa duban Indo tayi tace. " Kiyi hkr Indo Babu yanda na iya ne naso na riƙeki har na aurar dake da hanuna, sai dai Allah bai ƙaddara hakan ba, Indo kullum nasiha ta ɗaya ce gareki shine ki kasance mutum mai haƙuri a duk inda kika tsinci kanki, domin shi haƙuri yana kai mutum zuwa ga matakin babban nasara, tabbas kuma haƙuri haske ne, karki damu da duk abunda mahaifiyar su Mustafa zata miki, zai zama tarihi wata rana ki mata biyayya karki gaza dan tana hantarar ki kice bazaki bita ba, kiyi hkr ki mata duk wata biyayya da ƴa zata yiwa mahaifiyar ta, nima kuma kafin na tafi zanzo" kuɗi Aunty Hindu ta ɗauko ta danƙawa Indo a hanunta tace. " Gashi 10k ne ki riƙesa ko data zaki dinga saya dashi ki gaishe da su Daddyn naku." " Karɓa Indo tayi cikin sanyin jiki ta yiwa Aunty Hindu godiya har bakin mota Aunty Hindu ta rako Indo ta shiga mota shima Habeeb sallama yayiwa Aunty Hindu sannan yaja motar suka bar gidan Aunty Hindu tana ɗaga mata hanu, sunyi nisa da tafiya babu wanda ya cewa wani komai Habeeb lura da yayi da ran Indo a ɓace yake yasashi samun gefen titi yayi parking ya dubi Indo yace. " *HABIBTY NA* cire tagumin haka ko na juya na maida ke wajen Aunty Hindu." Zaro Ido Indo tayi tana kallon Habeeb tace. " Ya Habeeb *HABIBTY* kuma meyasa ka kiran da wannan sunan yau kuma?" Murmushi Habeeb yayi yana duban ta yace. " Bakya sone na kiraki da hakan ko kuma ban dace na kiraki da sunan ba ne?" " A'a bawai baka dace bane gani nayi saurayi ne yake kiran *BUDURWAR SA* da wannan sunan Kuma baka taɓa kirana da sunan ba shiyasa na tambaya." Murmushi sosai Habeeb yayi tare da cewa. " Okey to ki ɗauke ni a matsayin *saurayin* idan har kina ganin na dace da hakan, ni kuwa ina maraba da hakan *HABIBTY NA*" Dam! Gaban Indo ya buga maganganun Zarah ne suka fara yawo cikin ƙwaƙwalwar ta *ƙawata yaya Habeeb yana sonki da gaskiya mutumin kirki ne ya soki tun kina cikin ƙazantar ki bai taɓa nuna miki ƙyama ba*." Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un take furtawa cikin ranta ashe daman maganar Zarah gaskiya ne ya Habeeb sona yake kai anya kuwa ina ga dai yanzun ma zolayata yake, tabata da Habeeb yayi yana dariya tare da cewa. " Tunanin me kike haka *HABIBTY NA* Kodai na saki cikin searching ne?" Murmushin dole Indo tayi tare da haɗiye yawu dakyar tace. " A'a babu wani tunanin da nake yaya Habeeb ai nasan hakinka da zolaya" kawar da maganar tayi ta hanyar cewa. " Ya Habeeb yaushe zamuje Dasina, ina son zuwa naga Mama." Murmushi Habeeb yayi tare da tayar da motar ya harba titin yana ce mata. " Wannan ba maganar yanzu bane ki bari sai mun sami zama, keda zaki fara zuwa makaranta ina ke ina zuwa ƙauye, amma zamuyi maganar daga baya." Indo bata sake magana ba haka shima Habeeb har suka isa cikin gidan parking Yayi kusan tare suka fito suka nufi cikin falon Momy suna zaune gabaki ɗaya suna hira Momy Mustafa Sharifa Ishaq Sharif, da Sallama suka shiga Sharifa ce ta amsa, Mustafa kuwa wani Shu'umin kallo yake bin Indo dashi yana lumshe idanunsa Momy kuwa wani ƙazamin kallo take bin Indo dashi tare da tsantsar tsana cikin idanunta, Ishaq da Sharif kuwa da gudu suka tashi suka nufi Indo suna mata Oyoyo, akwatin nata Sharif ya karɓa yana ƙoƙarin kai mata cikin ɗakin su suka ji muryar Momy ta daka masa tsawa tana cewa. " Dan ubanka bata akwatin ta, jakinta ne kai shegen shishshigin tsiya nifa bana son kuna shigewa jikin wannan abar ƙyamar zan ci muku mutunci wlh idan baku fita harkarta ba daga ku har yayun naku." Ajiye akwatin Sharif yayi ya koma gefe yana fushi Habeeb kasa magana yayi ya tsaya yana duban Momy domin kuwa yasan koya mata magana bazata fahimce sa ba, sai dai ma ta zagesa, Mustafa kuwa Sarkin rashin haƙuri tuni ya fara yiwa Momy Magana. " Haba haba! Momy wai meye Indo ta ci miki haka kika tsaneta, ya kamata ki sassauta wannan ƙiyayyar da kike mata karki manta da cewa itama mutum ce kamar kowa kuma tana da Iyaye suna sonta kuma kamar yadda kema kike son naki ƴaƴan Abunda bazaki ji daɗi ba idan an miki bai kamata kiyiwa ɗan wani ba, itama fa Momy tana gata da Asali kamar yadda ƴaƴan naki suke dashi, ko mummunan laifi ta miki ya kamata ace kin yafe mata ki kuma mata fatan shiriya barema babu abunda ta miki pls Momy ki sassauta ƙiyayyarki gareta karki manta da cewa zata zama surukar ki nan gaba kaɗan." Shuru Momy tayi tana sauraron Mustafa bata katsesa ba harya gama sannan ta fara magana. " To ubana ka gama min faɗanne, to banji ba dan ubanka, na RANTSE DA ALLAH Mustafa zan iya rabuwa da kai na yafewa duniya kai muddun baka janye Maganar Soyayya da wannan abar ba, bare harta kaiku ga Aure idan kana neman zaman lafiya dani kana kuma neman albarkata to ka rabu da wannan YARINYAR domin na tsaneta bana ƙaunar ta cikin Rayuwata." Gabaki ɗayan su cikin tashin hankali suke kallon Momy mussaman Mustafa da yake jin bazai iya rayuwa babu Indo ba Habeeb kuwa suman tsaye yayi yana jin maganar mahaifiyar tasu kamar sauƙar aradu, juya kawai Habeeb yayi ya fice daga falon ganin hawaye na neman zubo masa, Indo kuwa tuni hawaye ya wanke mata tata fuskar kuka take harda sheshsheƙa Abunda take gudu kenan shiyasa taƙi dawowa Aunty Hindu ta tilasta mata dole sai ta dawo yanzu ga irinta nan, jan akwatin ta kawai tayi ta shige bedroom ɗinsu, Mustafa kuwa ranshi idan yayi dubu to ya ɓaci idanunsa sun kaɗa sunyi jajur ya dubi Momy ya fara faɗin mata maganganu. "Da farko kin min Auren dole kinsani na amshi matar da ban taɓa sonta ba a matsayin matar aurena na kuma miki biyayya na amshe ta a matsayin ki na mahaifiyata, duk da raina baya son ta, sai gashi yanzu nayi tozali da matar da nake so na Aura a matsayin zaɓina a karo na biyu kince baki yarda da hakan ba, anya kuwa Momy wannan karon zan iya miki biyayya anya Momy ina sonta fiye da yanda nake son komai na rayuwata ciki harda Numfashina, na daɗe da Soyayyar ta cikin Raina, meyasa Momy zaki tarwatsa Soyayyar Shekara da shekaru karkiyi wannan ɗaukar alhakin Momy domin..............." Sauƙar marin da yaji ne yashi kasa ƙarasa maganar da yayi niyya yana duban Momy da jajen idanunsa wacce ta sauƙe masa mari magana Momy ta fara cikin tsawa wanda yasa Sharifa fashewa da kuka tana duban Momy. " Na isa da kai! Shiyasa nayi maka katanga tsakaninka da ita, kuma dole kamin biyayya idan kuma kace bazaka min biyayya ba to kajeka babu ni babu kai karka sake takowa inda nake har abada ɓace min da gani." Bai cewa Momy komai ba ya taka ya haura sama bedroom ɗin su Indo ya shiga ya sameta tana zaune ƙasan tayels sai riskar kuka take harda majina sunkuyawa yayi ya kamo kafaɗarta ya ɗaga ta tsaye, sannan ya kama hanunta yana ƙoƙarin janta su fita, ƙwace hanunta Indo take ƙoƙarin yi amma ina Mustafa ba riƙon wasa ya mata ba, janta kawai yake tana cijewa har suka isa gaban Momy hanunsa riƙe dana Indo ya tsaya a gaban Momy yana kallon sa, Indo kuwa tsabar tsoron Momy rufe idanunta tayi tana jiran taji sauƙar duka......... *Vote* *Share* *And* *Comments* *Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻* *(Ummu Nasmah ce)* [4/2, 11:01 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘💘💘 *S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽* *Cigaban* *(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)* 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘 💘💘 *Na* *r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸* *(մʍʍմ ηαςʍα)* 👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻 *Marubuciyar* *Sauyin Rayuwa* *Nasmah ko Nasirah* *Sara da Sassaka* *INDO A BIRNI* AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA* *D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞* *Aunty fauza ƴar Amana* Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake. Allah yabar ƙauna. *S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢* *Aunty Hauwa Maman Uswan* Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻 *بسم

Chapter 2 of 14