Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ra'ayin ki, ita Soyayya ba'a dole idan ban miki ba, zan ɗauki ƙaddara domin ita Soyayya haka ta gada kije kiyi nazari, ki koma ciki Hasina na jiranki nima zan shige." "Na gode" Indo ta furta sannan ta juya ta shige cikin gida, a falo ta tarar da Momy da Hasina da Aunty Hindu sai Sharifa Zaune, kusa da Hasina Indo ta zauna Momy kuwa harara ta zabgawa Indo sunkuyar da kai Indo tayi ba tare data ƙara haɗa ido da Momy ba, kama hanun indo Hasina tayi suka haura sama har bedroom ɗinsu, kallon Indo Hasina tayi kafin tace. " Alfarma nazo nema a gareki Indo Wannan shine karo na farko dana fara neman alfarmarki ina fatan zaki min wannan alfarmar." Kallon Hasina INDO tayi sannan tace. " AUNTY HASINA niko me zaki tambaya a gareni wanda bazan iya miki shiba ki tambaye ni koma menene zan miki shi muddun ina da halin haka." Murmushi Hasina tayi tace. " Sanin kina da alfarmar da zan tambaya a gareki yasa nazo nementa gareki." " Ina sauraron ki Aunty Aunty Hasina ki faɗa min abunda kike buƙata a gareni na samu na miki shi cikin gaggawa." " *So nake ki Auri MIJINA* ki Auri Habeeb ceto rayuwar MIJINA daga halin da Soyayyar ki take neman jefa shi na gaji da ganin shi damuwa ina son gani farin ciki a idanun MIJINA wala Allah ko nima zan samu farin ciki daga garesa." Tunda Hasina ta fara maganar Indo take binta da kallo tana girgiza kanta cikin Ruɗani tare da tsantsar mamaki take duban Hasina kafin tace. " Kinsan me kike faɗa kuwa Aunty Hasina, Ya Habeeb kike kira na Aura keda kanki kike wannan maganar, Aunty idanma kinzo ki gwada nine to ki sani cewa nikam ba maciya amana bace bazan taɓa Auren mijinki ba, ki daina wannan tunanin cikin ranki." Murmushin ƙarfin Hali Hasina tayi tace. " Nasan Abunda nake faɗa Indo, ba kuma gwadaki nake ba da gaske nake miki wannan maganar Tabbas MIJINA nake so ki Aura ba kuma haramun bane dan kin Auri mijina bamusha nono ɗaya ba bare kice akwai haramci a ciki MIJINA yana tsantsar sonki soyayyarki har nema take ta masa illa Soyayyar ki tana neman ta wargaza min farin cikin gidana dan Allah ki taimakeni ki Auri MIJINA ko zamu samu cikakken farin ciki a cikin gidanmu domin kece kaɗai wacce zata dawo min da farin cikin MIJINA nikam na kasa amma ina da tabbacin ke zaki iya." Hawaye ne ya gangaro a Idon Indo tace. " Bazan iya ba! Bazan iya ba Aunty Hasina bazan iya auran mijinki ke Tamkar ƴar uwata ce wacce muka fito ciki ɗaya keda ya Habeeb kun jawoni jikinku a lokacin da nake buƙatar ƴan uwan da zasu rarrasheni kun ɗauki damuwata damuwarku kun min komai cikin Rayuwata Aunty Hasina ki faɗa min taya zan iya Auren mijinki dan Allah ki daina wannan maganar." " Murmushi Hasina tayi itama idanunta na ƙoƙarin zubar da hawaye, tayi saurin mayar dasu saboda kar Indo taga rauni a tattare da ita tace. " Hakanne yasa nake son ki sakawa Habeeb da alkairin da ya miki ta hanyar Auren sa, karki damu dani har abada kina matsayin ƙanwata dan kin Auri MIJINA matsayin da kike dashi a zuciyata bazai taɓa goguwa ba, sai dai ma ya ƙara ninkuwa MIJINA yana sonki fiye da yadda yake sona kullum da tunaninki yake kwana yake tashi yana mungun jin dadi idan yaji ana hirarki ya kan ji farin ciki a duk sanda yake kallon Soyayyarki har kuka ta sashi" tsayawa da maganar Hasina tare da ɗauko wayarta ta dannawa Indo recording d'in da tayi ɗazu sanda suka gama ji sannan ta cigaba da cewa " Zaɓi ya rage gareki ki ceto rayuwar sa ko ki barsa cikin damuwar da komai zai iya faruwa dashi, sai dai ki sani muddun wani abu ya samu MIJINA a dalilin ki bazan taɓa yafe miki ba." Tashi Indo tayi cikin tashin hankali cikin kuma tsawa da tsantsar tashin hankali take cewa. " Wai me ake nema da rayuwata ne, ya kuke so nayi da rayuwata ne wai, kowa *SO SO!* Duk kanku kuka sani ke kince mijinki ya Mustafa yace kansa shima Barrister yace kansa ki faɗa min ta ina kuke so nasa kaina gabaki ɗaya kun sani a tsakiya." Murmushi Hasina tayi ta tashi tace. " Kije kiyi tunani ki yankewa kanki Hukunci *WAYA KAMATA KI AURA A CIKIN SU* tana gama faɗa ta juya ta fice daga cikin bedroom ɗin........... *Vote* *Share* *And* *Comments* *Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻 *(Ummu Nasmah ce)* [4/11, 10:54 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘💘💘 *S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽* *Cigaban* *(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)* 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘 💘💘 *Na* *r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸* *(մʍʍմ ηαςʍα)* 👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻 *Marubuciyar* *Sauyin Rayuwa* *Nasmah ko Nasirah* *Sara da Sassaka* *INDO A BIRNI* AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*. *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ *D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞* *Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa* Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake. Allah yabar ƙauna. *S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢* *AUNTY HAUWA MAMAN USWAN* Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya. _____________________________________ *P*•••••••1️⃣5️⃣ ↗️ 1️⃣6️⃣ Sosai hankalin Indo ya tashi wunin Ranar haka ta yishi sukuku bata jin daɗin Zuciyarta ko kaɗan Ko bacci ba tayi wani ishashshe ba washe gari kuwa da safe ta sake shiga cikin wani sabon tashin hankali na tafiyar Sharifa Egypt sun rabu cikin kewar juna domin ita kanta Indo tasan tayi babban rashi na Sharifa cikin gidan mussaman idan ta tuno cewa daga ita sai Momy zasu zauna a cikin gidan Zuciyarta na mungun tsinkewa idan ta tuno da hakan, a ranar da sharifa ta tafi itama Indo bata wuni cikin gidan ba Daddy ta tambaya taje gidan su zarah sun tattauna sosai da Zarah game da Habeeb inda Zarah tayi murmurshin tana tuna mata maganar data gaya mata cewa Habeeb yana sonta haka zalika ta bata shawara cewa Habeeb shiya dace ta Aura ita dai bata nunawa Zarah cewa ta amince da maganar ta ba har suka rabu Indo ta koma gida. Lokaci na tafiya yayin da satittika suke shuɗewa, Indo dai ta fara zuwa makaranta cikin Nasara yayin da Itama Zarah tayi joining ɗin school ɗin sosai alaƙa mai ƙarfi ta daɗa ƙarfi tsakanin Indo da Zarah ƙullu haka kuma Habeeb tana sauraronsa kamar yadda suke a da amma ko a fuska bata nuna masa cewar tasan yana sonta ba, haka har yau bata bawa Hasina Amsa ba asali ma bata yarda sun haɗu ba kusan zance wasan ɓuya suke haka kuma Barrister UMAR ta sallamesa ta hanyar sanar dashi gaskiyar zuciyarta a cewar ta bata da ra'ayin Soyayya yanzu cikin aminci kuwa Barrister UMAR ya haƙura Mustafa ne dai kullum suke cikin dabi haɗuwa goma faɗa ashirin Momy kuwa kullum cikin ƙara tsanar Indo take gashi yanzu tsabar tsana harta dawo tana mata mugunta duk wani aikin daya shafi gidan itace take yinsa karatunta kuwa sosai take yi kuma tana ganewa sosai sai dai duk muguntar da Momy take yiwa Indo bata hana ta zuwa makaranta ko aiki take mata tana ganin time ɗin makarantar ta yayi zata karɓi aikin ta, a haka rayuwar take tafiya Daddy kuwa a wannan satin yaje shi DASINA ya sanar da Momy cewa akwai abu mai mahimmanci da zai kasa ta masa addu'a Allah yasa ya samu Abunda yaje nema Daddy da yaje da niyar ya dawo a ranar haka bai samu ba saida yayi kwana ɗaya washe gari ya juyo ya dawo cikin dutse. 💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢💢 Yau tun safe ta tashi da tashin zuciya ga wani jiri da yake damunta ga kuma kasala daya sata a gaba, tashi tayi ta ruga da gudu banɗaki sai amai take ta famar kwararawa, Mustafa dake Zaune ne ya tashi yabi bayanta domin kuwa tun jiya yake lura da yanayin ta, a bakin tollet ɗin ya tsaya yana kare mata kallo ta juyo da niyar fitowa ne tayi taga-taga zata faɗi saurin tare ta yayi ta faɗo jikinsa har bakin bed ɗinta ya ajiyeta tare da cewa. " Wai me yake damunki ne kam tun jiya ina lura da yanayin ki.?" " Nima bansan me yake damuna ba, sai dai ina yawan jin murɗa ga jiri da yake damuna sai kuma yanzu da nayi amai." Taɓe bakin sa yayi yace. " Okay Allah ya baki lafiya" sannan ya juya ya fice, yana fita RAUDA ta fashe da kukan baƙin ciki, ganin mijinta bai damu da lafiyar ta ba sosai da tasha kukanta tayi shuru dan kanta. Yana zaune yaji ƙiran Daddy ɗagawa yayi bayan sun gaisa Daddy yace yazo ya samesa yanzu a gida, amsawa yayi da to sannan ya ƙatse wayar yana rufe system ɗinsa ya fice daga part ɗin nasa ya nufi kiran Daddy. Zaune Indo take a bedroom ɗinsu ta gama aiki ta gaji ta ɗauko assignment ɗinta tana dubawa Ishaq ya shigo bedroom ɗin kusa da ita ya zauna yace. " Aunty Indo kina assignment ne.?" Kallon sa tayi tana murmurshi tace. " Eh assignment nake Ishaq har kayi wankan ne, ina Sharif.?" " Eh nayi Aunty, Sharif kuma yana falon ƙasa, Daddy ne yace wai kije yana ƙasa." Ajiye LITTAFIN Indo tayi tace. " Okay tashi muje to, idan na dawo na ƙarasa assignment ɗin." Tashi Ishaq yayi suka sauƙa tare a gefe Indo ta zauna tare da cewa gani Daddy, tana hararar Mustafa dake zaune gefe murmurshi kawai yayi tare da kanne mata Ido Habeeb Kuma yana kusa da Momy suma Daddy ne yayi kiran su. Duban Habeeb tayi tace. " Ya Habeeb wai ina ka shige ne tun safe ban ganka ba." Hararar ta Habeeb yayi tare da cewa. " Da baki ganni ba kuma ai baki nemeni ba." Dariya tayi sosai tace. " Kai ya Habeeb meye abun jin haushi kawai fa cewa nayi bari na gani zuwa dare idan baka zo ba saina kira ka, sai kuma gashi yanzu kazo." Murmushi Habeeb yayi yace. " Kaji Sarkin wayo uwar iya kare kai kekam da low kika karanta jama'a sun banu." " Dariya Dukan su sukayi sannan Daddy Yayi gyaran murya ya fara magana yana maida hankalin sa ga Indo yace. " *A'ISHA INDO* Tambayar ki nake son nayi shin kina da wanda kika ajiye a matsayin miji ma'ana wanda zaki Aura, lokaci yayi daya kamata ace kin fitar da mijin Aure mahaifin ki yamin magana akan hakan kuma kinsan al'adar garin namu na Dasina 12 to 13 years ake yiwa yara Aure kinga ke kuma yanzu kina da 18 years ya kamata ki sanar dani idan da wanda kika fitar.?" Shuru Indo tayi kanta na ƙasa ta rasa me zata cewa Daddy domin dai ita yanzu babu wanda zata ce ta tsayar a matsayin mijin da zata Aura, Habeeb kuwa Shida Mustafa gabaki ɗayan su zuba mata Ido sukayi suji me zata ce, dukansu zuciyoyin su dukun uku-uku suke yi kowa yana tsoron yaji wa Indo zata fitar a matsayin miji, Daddy Kara maimaita mata Tambayar yayi a karo na biyu ganin tayi shiru ta kasa cewa komai, a sannan Indo ta kaɗawa Daddy kai alamun babu wanda ta tsayar, hamdala Habeeb yayi cikin ransa yana kuma sawa a zuciyarsa a yau zai sanar da Indo Soyayyar da yake mata domin ya gaji da ajiyar Cuta cikin zuciyarsa dole ya sanar da ita ko zai samu sauƙin nauyin da ƙirjinsa yake masa, Mustafa kuwa Sarkin rashin haƙuri har zaiyi magana Daddy ya ɗaga masa hanu duban Momy yayi sannan ya kalli Indo yace. " Alhamdulillah! Daman na tambaye kine domin na baki damar ki *A'isha* kiyi hkr da hukuncin dana yanke akanki koda bai miki Daddy, Aisha akwai wasiyyar da *INNA* ta bar mana daf da zata rasu wannan wasiyyar nake son cika mata shi yanzu, Inna ta bar wasiyya cewa kar wani daban yazo ya Aure ki idan ba tsakanin Mustafa ko Habeeb ba, hakanne ya sani nayi dogon nazari tare da fahimtar ku sai nake ganin kamar akwai alaƙar Soyayya tsakanin ki da Mustafa shiyasa na ɗauki ƙafata da kaina naje DASINA wajen magabatan ki da kuma nawa iyayen na sanar da mahaifinki cewar na haɗaki Aure da Mustafa mun tattauna sosai da mahaifinki dare da ƴan uwa kuma alhamdulillah! Kowa yayi na'am da wannan haɗin a taƙaice dai ban bar DASINA ba har saida aka saka shartin aurenki da Mustafa Wata biyu kacal aka saka, ban sanar da kowa wannan maganar ba har mahaifiyar ku gata nan sai yanzu, na kuma gama haɗa kayan Auren ku yana kasuwa jibi za'a kawosa, Allah yasa ban muku katsalandan cikin rayuwarku ba." Wo ho ho kuzo kuji daɗi wajen Mustafa ji yake tamkar Daddy ya masa bushara da gidan aljanna wani irin farin ciki yake ji cikin ransa ganin ya samu Abunda yake so cikin sauƙi, Habeeb kuwa wani irin bugawa Zuciyar sa tayi zogi take mata ta toshe cike da tarin baƙin ciki, jin maganganun Daddy yake tamkar sauƙar aradu a kansa wai har anyi baiko tsakanin Mustafa da Indo, dafe ƙirjinsa yayi yana jin wani mungun baƙin ciki duk abunda Habeeb yake Indo tana ganinsa ta ƙasan ido ta kuma tausaya masa ainun Tabbas idan akwai wanda ya dace ta Aura to Habeeb ne, a yanzu ta fahimci halin da yake Tabbas zata faranta masa kamar yadda ya faranta mata bata gama tunanin nata ba taji sauƙar muryar Momy cikin kunnuwan ta tana cewa. " What! Alhaji kasan me kake faɗa kuwa aure tsakanin ɗana da wannan abar, Allah ya sawwaƙa, Abunda bazai taɓa yiwuwa ba kenan, tun wuri Alhaji kamar yadda kaje ka haɗa wannan maganar Auren to kaje ka sunce domin alaƙar da bazata taɓa ƙulluwa bane." Zabura Mustafa Yayi zaiyi Magana Daddy ya katsesa tare da ɗaga masa hanu duban su yayi yace duk su tashi su tafi saboda baya so yayi hayaniya da matarsa gaban ƴaƴan sa duk da basu gama maganar da suka fara ba, tashi Habeeb Yayi yana tangal-tangal ya fito bayan sa Mustafa ya biyo yana dariya tare da dafa kafaɗar sa yace. " Alhamdulillah! Bros mafarkina zai cika zan mallaki shafukan Indo a matsayin matar da na daɗe ina mafarkin samu gaskiya yau DADDY ya faranta min raina ina cikin farin ciki yau." Murmushin mai ciwo Habeeb yayi cikin danne damuwarsa ya miƙawa Mustafa hanu yace. " Congratulation Bros kayi dacen mata Allah ya sanya Alkairi." Murmushi mustafa yayi tsabar daɗin da yake ji yasa ya kasa gane halin damuwar da ɗan uwansa yake ciki amsa masa yayi da. " Ameeen bros yau zan wuni cikin farin ciki." Murmushin ƙarfin hali kawai Habeeb yake har suka rabu da Mustafa kowa yayi part ɗinsa, Habeeb zama kawai yayi a falo ya dafe ƙirjin sa yau tsabar baƙin ciki yasashi kukan ma ya kasa, a jiyar ZUCIYA kawai yake shi kaɗai yasan Abunda yake damunsa. Can kuwa Daddy duban Momy yayi yace. " A'ishatu ki fita a idona na rufe, ina sanar dake cewa idan kika kuskura kika kawo min matsala cikin wannan lamarin to Tabbas kisa a ranki cewa zamu samu mummunan saɓani, ranki zaiyi mungun ɓaci kina ji ko." " Ina ji Alhaji sai dai ka sani bazan taɓa lamunta da wannan haɗin ba, bazan taɓa yadda ɗana ya auri wannan fitsararriyar YARINYAR ba wlh komai zai faru sai dai ya faru." Tana gama faɗin haka ta juya ta haura sama kaɗa kansa Daddy Yayi yana yiwa Momy kallon rashin Hankali sannan shima ya wuce nasa bedroom ɗin. INDO kuwa tun shigar ta bedroom ɗin nasu ta kasa sukuni tausayin Habeeb kawai take ji cikin zuciyarta, Tabbas ya mata Alkairi, to meyasa ita bazata saka masa da Alkairi ba, idan har ta bar Habeeb a cikin wannan halin Tabbas ta cika cikakkiyar butulu, idan da akwai wanda ya dace ta Aura to Habeeb ne, Mustafa sam bai dace da rayuwar ta mutumin daya dinga wulaƙanta rayuwarta mutumin daya ƙyamace ta, mutumin da kullum yake ciki hantarar mutumin da baisan darajata ba to akan meyasa zata auresa duk abunda ya mata yaci banza kenan, shi kuma ya Habeeb ya yiwa rayuwar ta Hallaci kuma har gobe a cikin mata Hallaci yake dole ma ta Saka masa, Indo takai kusan 11pm tana tunani ta kasa bacci kamar yadda haka yake shima Habeeb a garesa ya kasa sukuni muƙurƙusu kawai yake yau da wuri ya rufe bedroom ɗinsa SABODA baya so Hasina ta shigo ta samesa a Halin da yake ciki, yasan hankalin ta zai tashi sosai ita Hasina daman ta fuskanci halin da yake ciki shiyasa ma bata tunkaro bedroom ɗinsa ba, Habeeb yana cikin wannan halin ne yaji wayar sa tana ringine dubansa yakai ga screen ɗin wayar sunan Indo ya Baiyana tashi yayi tare da ɗaga wayar ba tare da Sallama ba yace. " Meya hanaki bacci a wannan lokacin.?" Share hawayen ta Indo tayi tace. " Abunda ya hanaka bacci nima shiya hanani bacci, ka fito ka sameni ina tsakar gidan ku." Cikin mamaki Habeeb yace. " What! Tsakar gidan mu kuma taya kika fito har kika shigo nan." " Yanzu ba lokacin Tambaya bane ka fito kawai ina jiran ka." Katse wayar yayi ya sauƙo daga bed d'in sannan ya nufo waje A tsaye ya ganta tana jingine jikin part ɗin nasa tsayuwa yayi yace. " Meya fito dake cikin wannan daren?" Kallon sa tayi Ido cikin ido sannan ta fara magana cikin raunin murya. " Ya mutuwa zanyi zan mutu ya Habeeb." Cikin tashin hankali ya dubeta yace. " Wacce Irin magana kike wannan waya ce miki zaki mutu.?" " Ya Habeeb kasani cewa muddun ka bari jibi aka kawo kayan aurena da ya Mustafa to ka sani mutuwata ce aka kawo domin a ranar zan haɗiyi zuciya na mutu." Murmushin baƙin ciki Habeeb yayi yace. " Babu Abunda zai kasheki karki manta da mustafan ki kika samu to me zai kasheki bayan kin samu burin ki na shekara da shekaru." " Bana son ya mustafa kai nake ya Habeeb kaine zaɓina kuma na tabbata kaima kana sona ya Habeeb kaje ka ware Aure tsakanina da ya Mustafa ni kaine zaɓina." Murmushin rainin hankali Habeeb yake yiwa Indo kafin yace. " Baki taɓa ji daga bakina nace ina sonki ba, dan haka kije ki riƙe zabin iyayen ki." Yana gama faɗin haka ya juya zai bar wajen sai yaji muryar ta tana cewa. " Ranar Litinin itace ranar da za'a sallaci gawata domin itace ranar mutuwata Ranar da za'a kawo min bakaƙen akwati a matsayin na aure na, ka tanadi likkafani da igiya domin kaine nake son ka kaine makwancina." A firgice ya juyo idanunsa sun sauya kala cikin firgici yake cewa. " Bazaki taɓa mutuwa ki barni ba, ba gawa za'a sallata ba gawawwaki za'a sallata domin bazaki ke kaɗai ba sai dai mu mutu tare, ki sani duk abunda nima ya sameni idan Gurguwa kika zama to ki sani nima zan sa adda na sare ƙafafuna duka mu zauna idan kuwa tsautsayi ne afka idanunki kika makance to ki sani ba ɗan jagora zan zame miki ba, zan nemi kara ne na tsokane nawa idanun muyi dai-dai ki daina ambaton mutuwa domin kuwa kina ɗaga min hankali idan kina ambaton sa." Murmushi Indo tayi hawaye na gudu a idanunta tace. " Idan har baka son ganin mutuwa ta to ina so a wayewar safiya kaje ka sanar da Daddy muna son juna idan ya kirani zan tabbatar masa da hakan." ______________________________________ Tirƙashi yau ake yinta ko ya waɗannan ƴan uwa zasu kasance wai me yake shirin faruwa ne tsakanin wannan family? Ku biyoni domin warware muku.😄 *Vote* *Share* *And* *Comments* *Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻* *(Ummu Nasmah ce)* [4/12, 11:57 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘💘💘 *S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽* *Cigaban* *(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)* 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘 💘💘 *Na* *r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸* *(մʍʍմ ηαςʍα)* 👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻 *Marubuciyar* *Sauyin Rayuwa* *Nasmah ko Nasirah* *Sara da Sassaka* *INDO A BIRNI* AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*. *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ *D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞* *Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa* Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake. Allah yabar ƙauna. *S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢* *AUNTY HAUWA MAMAN USWAN* Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya. ________________________________________ *P*•••••1️⃣7️⃣ ↗️ 1️⃣8️⃣ " Da wani Ido kike so na kalli ɗan uwana, bana son ganinsa cikin damuwa, gara kawai ni ki barni cikin damuwata bana son abunda zaisa ya ji haushi na." " TABBAS ya Habeeb baka ƙaunar Rayuwata na tabbata da kana ƙaunar Rayuwata da zaka ceci rayuwata, na gode amma ka sani muddun baka sanar da Daddy Soyayyar mu ba ka sani babu makawa sai na mutu idan kuma na mutu sai kai ka rayu da ɗan uwanna ka kuma kaine sanadi na." Tana gama faɗin haka ta juya a guje tabar wajen a hankali ta bugawa mai gadi get buɗewa Yayi yana cewa. " Hajiya ai ɗazun na gaji da jiran kine shiyasa na taho Saboda kar wani abu ya faru kiyi sauri ki shige a hankali kar wani ya ganki." Godiya Indo ta yiwa mai gadi sanna ta wuce a hankali harta shiga ɗakin sannan ta rufe a hankali tasa key still a hankali ta haura sama ta shige bedroom ɗinta, faɗawa tayi saman bed ta saki kuka mai cin rai tana cewa. " Ina SONKA ya Mustafa Tabbas Soyayyar ka a jini na yake sai dai ka wulaƙanta rayuwata ka ƙyamaci ni ka tsangwame ni baka taɓa nuna min ƙauna ko kulawa ba a sanda nake gigin sonka duk da a lokacin ban gama sanin meye Rayuwa ba, sai dai nasan zafin Soyayyar ka duk da ƙanƙantar shekaru na, sai yanzu dana zama mutum zaka ce kai lallai kana sona, ya Mustafa ina sonka amma dole zan danne Soyayyar ka zanyi ƙoƙarin ganin na cireka a rayuwata, domin kuwa ya Habeeb shine wanda ya dace da rayuwata ina da tabbacin zan samu ingantacciyar rayuwa a wajen sa Tabbas zai kula dani zai riƙeni bisa Amana, Ya Habeeb kaine wanda zan aura insha Allah zan soka koda a gidan kane Tabbas kaine ka dace da na bawa soyayyata." Ta ƙarasa maganar tana sakin kuka harda majina sam bata saka Abunda Momy tayi ba a cikin ranta domin kuwa idan da sabo ta saba da tsanar da Momy take

Chapter 5 of 14