ya ɗauka ne yake tambayar sa, wani irin ƙwaya ranar yasa aka basa, murmurshi Kamal Yayi tare da sanar dashi sunan ƙwayar, kashe wayar gabaki ɗaya Mustafa Yayi sannan ya ɗauki wayar hotel ɗin dake cikin bedroom ɗin, ma'aikatan ya kira tare da bada umarnin cewa a nemo masa ƙwayar a kawo masa cikin mintuna kaɗan kuwa aka kawo masa tare da Pepsi karɓa Yayi ya jefa kwayar a cikin Pepsi girgizawa Yayi sannan ya ɓalle murfin ya kafa a bakin sa bai ɗaga daga bakin nasa ba sai da ya shanye tas sannan yayi wurgi da gorar gefe yana dafe kansa baifi 30 minute ba kuwa yaji ɗakin yana juya masa cikin wannan halin mayen bacci ya ɗebe sa, sosai yayi baccin shine bai farka ba sai 11am da salati a bakin sa ya furta yana duban agogon ɗakin, da sauri ya miƙe yana mamakin baccin da yayi, wani irin bacci yayi haka harya makara bai tashi yayi sallar asuba ba, tollet ya faɗa yana riƙe da kansa dake masa nauyi, alwala kawai ya ɗauro ya fito ba tare da ya tsaya wanka ba da Astagfurullah har ya ɗauki sallaya ya tada Sallah bayan ya idar ne yayi addu'oin sa, yana roƙar UBANGIJI daya mutu ya huta da baƙin cikin dake damunsa bayan ya gama addu'oin ne kuma ta faɗo masa cikin zuciyarsa, wayarsa ya jawo ya kunna tare da kulle layikansa ya sakasu a jirgi yanda kiran kowa bazai shigo masa ba, pic ɗin ta ya ƙurawa ido dake saman screen ɗin wayar tasa, hoton ta ne tun tana ƙauye, wanda Habeeb ya taɓa turo masa wani sonta ne yake ƙara fisgarsa, hawaye ne suka gangaro masa saman fuskarsa, goge hawayen yayi tare da jingina kansa jikin bango, wankan ma ji yake bazai iya ba, yana cikin wannan halin ne yaji ana masa Nocking ɗin ƙofa ko bai sani ba yasan ma'aikatan hotel ɗin ne, daga inda yake cikin nauyin Murya yace.
" Waye ne?"
Daga bakin ƙofar mahaukacin yace.
" Ma'aikacin hotel ɗinne."
" Me kuke buƙata?" Ya jefa masa tambaya.
" Breakfast ne daman muke so muji me kake bukata, sannan kuma muna son zamu gyara bedroom ɗin.?"
Cikin gajiya da maganar Mustafa yace masa.
" Kaje kawai bana buƙatar ko ɗaya yanzu idan ina buƙata zan kira ku, amma yanzu kam bani da bukata."
" Okey" ya furta tare da barin wajen."
Cigaba da tunanin sa Mustafa yayi shi yanzu Abunda yafi damunsa ma shine jinin da yake gani idan yayi tari ga wani zafi da ƙirjin sa yake masa ƙwayoyin da aka kawo masa ya ɗauka tare da ɗaukar ɗaya ya je frich ya ɗauko ruwa ya wurga ƙwayar a bakin sa domin gani yake kamar ƙwayar tana rage masa damuwar haka Mustafa ya wuni cikin maye.
RAUDA hankalin ta a matukar tashe yake tun daren jiya ta kira numbobin wayar sa yafi a ƙirga switch Off ake ce mata, koda gari ya waye a cikin wannan damuwar suka shirya breakfast ita da Mustafa a tunaninta idan gari yayi haske zai dawo amma ina shuru kake ji wai Mlm yaci shirwa babu Mustafa babu labarin sa, ƙara kiran layinsa tayi har yanzu dai switch Off, iya tashin hankali RAUDA ta shigesa, sai tayi yunƙurin tashi taje ta sanarwar su momy sai ts fasa ta koma ta zauna tana tsoro karta sanar musu kuma idan ya dawo yaci mutuncin ta yace ta haɗa sa da iyayen sa, dole yasa RAUDA ta hakura ta zauna cikin damuwa da tashin hankali, ita Abunda yafi ɗaga mata hankali ma numbobin wayar sa da suke rufe, hankalin RAUDA bai ƙara tashi ba sai da taga 11pm babu Mustafa babu labarin sa, wannan daren haka RAUDA ta kwana cikin tashin hankali, bacci kuwa gagarar ta yayi."
Habeeb kuwa tun 9pm ya shigo cikin gari Ganin kamar dare yayi shiya hanasa shiga wajen momy gara ya bari kawai sai da safe.
Habeeb daga masallaci bai koma part ɗinsa ba yayi na Momy tana lazimi ya sameta a bedroom ɗinta zama yayi ya jirata harta gama sannan ya gaisheta babu yabo babu fallasa Momy ta amsa bata Kuma tambaye sa ya dawo lafiya ba shima bai damu ba domin kuwa yasan Halin mahaifiyar sa mussaman ma idan akan abinda ya shafi Indo ne.
Suna zaune RAUDA ta shigo tana kuka, jikin Momy ta faɗa ta ƙara sakin kuka, dubanta Momy tayi tana cewa.
" Subhanallah RAUDA me yake faruwa ne haka na ganki cikin tashin hankali sai famar rera kuka kike, kuma kisan cewa mace mai ciki bata son damuwa."?
Cikin kukan tace.
" Ya mustafa Momy ya Mustafa ne."
Zabura Momy tayi tare da cewa.
" Mustafa kuma, me Mustafan ya miki faɗa kukayi ne dashi.?"
" A'a Momy ba faɗa mukayi ba, tun shekaran jiya, baya gida Momy idan na kira layinsa baya tafiya yau kwanan sa biyu kenan baya gidan Momy Hankali na yana tashe."
A zabure Momy ta miƙe tsaye cikin tashin hankali tace
" What kwanan Mustafa biyu baya gida, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un to ina yake me yake faruwa dashi na shiga Uku ni A'isha ina dana ya shiga, Allah ka rufa min asiri na kasa yana halin lafiya."
Habeeb shima cikin tashin hankali ya miƙe tsaye tare da cewa.
*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻
Ummu Nasmah ce
[5/9, 2:41 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘
*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*
*Cigaban*
*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*
AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*P*••••••2️⃣7️⃣ ↗️ 2️⃣8️⃣
" Yanzu ke RAUDA kwanan Mutum biyu baya gida amma shine kika zauna kikayi shuru baki sanar ba tuntuni, wannan kuskure ne."
Cikin kuka RAUDA tace.
'' Ya Habeeb tun jiya naso nazo na sanar sai dai kuma ina tsoro ne karya dawo yamin faɗa yace na haɗasa da iyayen sa, shiyasa ban faɗa ba amma ina cikin tashin hankali nima Momy."
MOMY cikin faɗan itama tace.
" Faɗan banza faɗan wofi sai me idan ya miki faɗa dukanki zaiyi, gashi yanzu bamu san wani hali yake ciki ba."
Habeeb wayar sa ya ciro ya kira layin Mustafa, amma Switch Off.
" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Momy layin sa baya shiga."
Hawaye ne ya zubo a fuskar Momy cikin sauri ta sauka kasa suma binta sukayi cikin sauri bedroom ɗin Daddy ta faɗa cikin tashin hankali Daddy dake zaune yana danna loptop dinsa ne ya dago kansa ya kallesu tare da cewa.
" Lafiya kuka shigo min a firgice.?"
Cikin tashin hankali Momy tace.
" Ina lafiya kuwa Alhaji Tun jiya babu Mustafa babu labarin sa kwanan sa biyu baya gida."
Ɗaga kai yayi ya kalli Momy yace.
"Yaro ne Mustafan da za'ace ya ɓata, ina ga kawai fushi yayi yabar muku gidan saboda bamu masa biyayya ba, mun basa Abunda yake so, dan haka karku ɗagawa kanku Hankali yanda ya tafi haka zai dawo."
Wani irin kallon mamaki Momy take bin Daddy dashi kafin tace.
" Kasan Abunda kake faɗa kuwa Alhaji Mustafa shi waye da baza'a saceshi ba, karka manta da cewa munafukai sunyi yawa a cikin wannan ƙasar tamu ta Nigeria, ga ƴan kidnapping da sukayi yawa a duniya, ka daina wannan tunanin Alhaji kawai ka tashi mu san yanda zamuyi ɗana ya dawo gida."
Murmushin manya Daddy yayi cikin kwanciyar hankali yace wa Momy.
" Babu inda zanje ba kuma zan ɗaga Hankali na ba, Saboda nasan Mustafa bai ɓata ba, babu abunda ya samesa dan haka kuma ku kwantar da hankalin ku, ku basa wasu lokutan zai dawo da kansa."
Allah sarki tsakanin ɗa da uwa sai Allah barema yanda Momy take ƙaunar Mustafa fiye da dukkan ƴaƴan da ta haifa, kwatakwata Momy taƙi yadda da maganar Daddy haka shima Habeeb hankalinsa ya tashi domin kuwa baisan wani hali ɗan uwansa yake ciki ba mussaman idan yayi la'akari da yanda ƙasar ta lalace a hallakar da mutum ba wani abu bane sun ɗauki ran ɗan Adam tamkar kiyashi Momy ce ta dubi Daddy cikin ɓacin rai tace.
" Meye hujjar ka na cewa bai ɓata ba yana halin lafiya, idan kuma har da gaske kasan bai ɓata ba, to ina ɗana yake ina farin ciki na yake.?"
Murmushi Daddy Yayi tare da cewa.
" Ko ɗaya ni bansan Inda ɗanki yake ba, kawai dai zuciyata tana bani yana halin lafiya ne, kinga A'isha, leave me a long ina lissafi ne karki ɓata min lokacin."
Cikin tsawa Momy ta buɗe bakinta zatayi Magana Habeeb yayi saurin tare ta da cewa.
" Dan Allah karki ce komai Momy ni zanje na nemo ɗan uwana, na miki alƙawari zan dawo dashi gida muddun yana raye kai koma ya mutu zan dawo da gawarsa gida, muje dan Allah."
Ficewa tayi tana ƙwafa tare da cewa.
" Barema ɗana bai mutu ba yana raye insha Allah."
Bayan sun dawo falo ne Habeeb ya dubi Momy yace.
" Zan fita Momy naje na fara binciko shi ki mana addu'a Allah yasa mu dace kuma yana halin lafiya."
Da addu'ar kuwa Momy ta bishi, hankalin ta yana mungun tashe, ta rasa inda zata saka ranta, alƙawarin da suka yi da Mamy ma na komawa gun boka ta manta dashi tsabar ɓacin rai RAUDA kuwa kusa da ita ta zauna tana cigaba da kuka.
Habeeb duk inda yasan zai samu Mustafa yaje amma babu wani labari kowa cewa yake rabonsa dashi yau kwana Uku, hankalin Habeeb bai tashi ba sai yanzu duk yanda ya ɗauki abun ashe Zafin sa ya wuce nan tambayar da yake yiwa kansa shine ina Mustafa yaje, shin yana halin lafiya, shin maganar Daddy gaskiya ne fushi yayi akan INDO yabar gidan Tabbas idan haka ta faru bazai taɓa yafewa kansa ba, domin kuwa zai kasance shine silar shigar ɗan uwansa cikin wani hali da wannan tunanin ya dawo gida, ya kuma shirya ƙaryar da zaiyiwa Momy dan ganin hankalinta ya kwanta, a falo ya tarar dasu Zaune sunyi shuru suna jiran dawowar sa, kusa da Momy ya zauna tare da ƙaƙalo dariyar dole yace.
" Momy Mustafa fa yana cikin halin lafiya, kinsan yanayin aikinsu, yanzu da naje office dinsu ogansu yake sanar dani cewa, sun tafi wani ƙauye bincike, tafiyar ta taso musu ne cikin gaggawa, yace kuma ƙauyen da suke babu network shiyasa ba'a samun wayan su, akan ma yanzu zaizo ya sanar daku sai kuma na rigasa zuwa."
Ajiyar Zuciya mai nauyi Momy ta sauƙe tare da cewa.
" Alhamdulillah! Sai yanzu naji Hankali na ya kwanta, amma kuma ai shi ogan nasu bai kyauta mana ba, kamata yayi ya sanar mana tuntuni amma tunda ansan inda yake ai arziki yayi, yanzu yaushe suka ce maka zai dawo."
Shuru Habeeb yayi sai can yace.
" Gaskiya Momy sunce babu rana dan sunce binciken da aka tura su yana da matuƙar hatsari dole sai sunbi a hankali, amma may be suyi one month."
Da Allah ya kaimu Momy ta furta sannan ne hankalinta ya kwanta ita kuwa RAUDA sam bata yarda da maganar Habeeb ba, zuciyarta taƙi amincewa da Maganar tasa tashi Habeeb yayi ya nufi bedroom ɗin Daddy da Sallama ya shiga Daddy amsa gefen Daddy ya zauna yayi shuru, ganin haka da Daddy yayi ya sashi rufe system ɗinsa ya maida dubansa ga Habeeb kafin yace.
" Habeeb akwai Magana ne naga ka nutsu."
" Eh Daddy akwai Magana."
" Okey ina sauraron ka meyake faruwa.?"
" Daddy akan maganar Mustafa ne, Daddy Mustafa fa baya kusa dan duk inda ya nasan yana zuwa Daddy naje baya nan, a duba lamarin nan Daddy yanzu haka ƙarya na yiwa Momy sannan hankalinta ya kwanta na ce mata daga Office ɗin su aka tura su wani ƙauye bincike kuma ƙauyen babu network shiyasa ba'a samun wayar sa, PLS Daddy."
Murmushi Daddy Yayi kafin yace.
" Shikenan Habeeb zan saka amin bincike, insha Allah komai zaizo da sauƙi jiya munyi waya da Mlm Musa mahaifin Indo akan Maganar kai kayan da za'ayi mu tattauna dashi mun tsayar da Magana cewa babu maganar kai kayan Auren saboda wannan cutar data addabi duniya coronavirus, SO taron Auren ma nace masa bazai yiwu ayi taron biki ba, idan an ɗaura Aure kawai washegari mutum Uku ko hudu su kawo ta ya isa in suka ga ɗakinta sai su koma, kasan sati Uku kawai auren ya rage so sai kaje kayi gyare-gyaren daya zakayi idan kuma akwai taimakon da kake nema a waje na sai ka sanar dani insha Allah zan taimaka maka."
Shuru Habeeb yayi sai can yace.
'' Daddy me zai hana a dakatar da Maganar Auren yanzu mun tunkari abinda yake gaban mu, na neman ɗan uwana, Daddy bazan ji daɗin wannan auren ba, muddun ba'aji labarin ɗan uwana ba, pls Daddy a ɗaga wannan Aure har sai munga dawowar Mustafa."
Haɗa fuska Daddy yayi cikin seriours ya yiwa Habeeb Magana.
" Babu Abunda zai dakatar da wannan auren sai dai idan mutuwa akayi bari kaji na sanar dakai ɓacewar Mustafa bazai sa na ɗaga wannan auren ba, zamu cigaba da neman sa duk da ina ji a jikina Mustafa bai ɓata ba, kawai yayi fushi ne akan ban basa Auren Indo ba, kafin ya tafi kwana nawa baizo ya gaishe ni ba, ka tashi ka tafi kaima ka bani waje."
Tashi Habeeb yayi ya fita yana cewa Allah ya huci Zuciyarka Daddy, sannan ya fice a falo ya samu Momy ya mata Sallama sannan ya fita da sauri RAUDA tabi bayan sa tana cewa.
" Ya Habeeb kawai ka faɗawa Momy haka ne domin ka kwantar mata da hankali amma ina ji a jikina baka samu labarin Ya Mustafa ba pls dan Allah ya Habeeb ka nemo min MIJINA."
Kallon tausayi Habeeb yake yiwa RAUDA kafin yace.
" Tabbas banji labarin Mustafa ba, amma ina nan ina bincike kuma Office ɗin su ma zasu taya mu bincike, sannan zanje police station na sanar karki damu insha Allah zai dawo gida cikin halin lafiya, ke dai ki cigaba da addu'a karki daga Hankalin ki komai zaizo ƙarshe."
Share hawayen ta tayi tace
" Shike nan ya Habeeb insha Allah zan cigaba da addu'a, Allah ya fito min da mijina."
" Ameeen" Habeeb yace sannan yace ta koma ɗakinta ta Zauna haka kuwa ta koma part ɗin ta amma har yanzu hawaye bai tsaya daga idanunta ba.
*****************************************
" Ke Indo wato ba zaki tashi ki je ki gaishe da Goggo ba ko, tunda kika zoki kinƙi fita ko nan da waje, yau kwanan ki Uku, ai ko ziyara kya fita, tunda dai sati Uku kacal zakiyi ki koma kuma da Auren ki maza ki tashi ki fita kije kiyi ziyara."
Tura bakinta INDO tayi tace.
" Mama wlh bana son fita ne naga gidan INNA hankali na yana tashi mussaman idan na tuno Rayuwata da ita a baya Mama ina son INNA sosai naso ace INNA taga Aure na ta kaini gidan mijina da kanta sai gashi mutuwa ta hanata ganin Aure na bare har ta kaini ɗaki na."
Ita kanta Mama sai da taji wani iri, yanda Indo ta shaƙu da INNA ko ita da ta haife ta basuyi wannan shaƙuwar ba, sai dai ya zasuyi dole suyi hkr domin kuwa shine kawai Abunda zasu iya, su mata Addu'a duban Indo tayi tace.
" Haƙuri zakiyi Indo bake kaɗai ba har muma muna jin zafin rashin INNA sai dai babu yanda muka iya dole muyi mu bita da addu'a shine kawai gatan da take buƙata yanzu a wajen dukkan masoyanta."
'' shike nan Mama zan shirya yanzu na tafi bari ma naje nayi wanka sai na fita."
Cikin murmurshi Mama tace.
" Yauwa maza shirya kije, tsaraba kam na raba na bawa kowa, sai dai na innar hansai ne zan baki ki tafi mata dashi, koda Ibrahim zan haɗaku ya ɗauki buhun shinkafar ku tafi tare."
Wanka Indo ta shiga bayan ta fito ne ta shirya ta ɗauki bag ɗin ta ta yiwa Mama sallama tare da cewa mama ta bawa Ibrahim tsarabar innar hansai ya kai musu daga baya.
Tunda ta fito Indo take ziyara duk gidan da ta sani da suna zuwa sai da ta shiga kowa yaga Indo sai yayi mamakin sauyawar da tayi, wasu kamma basa ganeta sai an musu bayani, tana hanyar ta ta zuwa gidan su Zainabu ne, ta hango kamar Garba abokin faɗanta, ƙarasawa wajen tayi ta tsaya, kusa dashi ba tare da tayi masa Sallama ne, zungure masa kai tayi tace.
" Kai Garba ɗan rainin wayo wai daman kana duniyar nan baka mutu ba.?"
Sai yanzu Garba ya gane Indo da tayi Magana yana dariya ya miƙe tsaye tare da cewa.
" Hegiya Indon INNA wai daman kece kika dawo balarabiya haka, aradu ban gane ki ba, kin dawo ƴar binni, nayi zaton ai bazaki ƙara dawowa ƙauyan nan ba, aradu tunda kika bar ƙauyen nan muka daina faɗa ahe daman kece mai jawo rigimar."
Dariya sosai Indo tayi mussaman tuno tsiyar data tsula a cikin ƙauyen, tace.
" Allah sarki yarinta kace su mai gari an huta da kai ƙara Garba an tsula tsiya fah."
Shima Garba dariyar yayi tare da cewa.
" Yanzu kam ai mun koma ga Allah, amma dai zaki wajen mai garin ki gaishe sa, naji ma ana cewa wai auren ki ya kusa, zaki Auri jikan INNA wannan ɗan gayen mai zuwa da mota, Allah sarki INNA, kamar ba azo duniya ba, Indo kema kinyi rashi aradu."
Ciccikowa idon INDO yayi da hawaye jin Garba ya ambaci INNA, kafin tace.
" Eh saura sati Uku ma Auren, ai Wlh bazanje na gaishe da mai gari ba mutumin da baya sona ya tsaneni tun da can Allah bazanje ba."
. dariya Garba yayi yana ƙara tuno rashin mutuncin Indo sun juma suna taɗin yaushe gamo kafin Indo ta wuce gidan su Zainabu, da Sallama ta shiga Goggo Hali dake tsugunne tana shara ne ta dago kanta tana amsa sallamar tare da bata wajen zama duk bata gane Indo ba sanda Indo tace.
" Sannu da aiki Goggo ya jikin Zainabu.?"
" Da sauƙin Goggo Hali ta amsa tana cewa, sai dai ban ganeki ba baiwar Allah."
Murmushi sosai Indo tayi tace.
" Haba Goggo Hali yanzu har kin mantani, Indon INNA ce fa ta wajen Baba Musa."
Salati Goggo Hali ta ɗauka tana tafa hanu tare da cewa.
" INDO wacce na sani fitinanniyar nan ƴar wajen Mairo kece haka kika koma jawur dake kamar ƴar Larabawa lallai kuwa kin samu duniya masha Allah."
Dariya Indo tayi tana cewa.
" Ehh nice Goggo yanzu Goggo Hali har nayi sauyawar da baza'a gane niba."
Ko kafin Goggo Hali ta maida mata da amsa tuni Zainabu ta fito daga ɗaki tana dariya ta zauna kusa da Indo tare da cewa.
" Mutanen birnin sai yau kika tuno damu kenan, tun shekaran jiya Lami tace min kinzo harma taje gidan naku."
" Eh tazo mun juma ma, yanzu ma haka daga gidan nata nake, na samu ma bata nan wai gaisuwar mutuwa."
" Ai Lami ba'a cika samunta a gida ba, yawon tsiya gareta, Indo munga tsaraba mun gode sosai Allah ya saka da alheri, ya haƙurin rashin INNA ban samu na miki ta'aziya ba gashi naji Lami na cewa kin dawo ne ayi bikin ki nan da sati Uku ko ki koma binni da Auren ki, Allah dai yasa da Mustafa za'ayi Auren."
Wani irin bugawa ƙirjin Indo yayi jin an soso mata inda yake mata ƙyaiƙyayi kafin tace.
" Alhamdulillah mun godewa Allah, INNA kwana ya ƙare, eh Wlh biki na ya kusa amma ba da Ya Mustafa bane, da ɗan uwansa ne ya Habeeb."
" Subhanallah kaddai ace har yanzu ya Mustafa baya sonki kece kaɗai kike haukar sonsa, amma gaskiya banji daɗin wannan labarin ba naso ace Mustafa kika aura, koda yake shi *AURE ƘADDARA CE* sai ku gama Soyayya da saurayi amma a ƙarshe sai ya kasance ba shi bane Allah ya ƙaddara mijin ka, Allah yasa haka shi yafi Alkairi."
Murmushin takaici Indo tayi kafin ta amsa da ameeen tashi tayi tace
Kinga bari na samu na gudu kar dare yayi ina son na shiga na gaishe da innar hansai kafin na wuce gida da Goggo Hali sukayi Sallama har zauren gidan Zainabu ta raka Indo, Kafin Indo ta wuce gida sanda ta shiga gidan su hansai, INNA Lami kishiyar mahaifiyar hansai ta samu zaune tana ɓarar gyaɗa kusa da ita Indo ta zauna tana ɗaukar gyaɗar ta kai bakinta kafin tace.
" SANNU da aiki INNA lami."
" Yau sannu" tare da dago kai tana kallon Indo lokaci ɗaya ta gane Indo bata yi mamakin ganinta ba domin taji labarin zuwanta yanzu ma kuwa Ibrahim ya fita ya kawo masu tsaraba, " Su Indo gidan fitina yanzu kuwa kina fitinar ko kin tuba."
Tuntsirewa da dariya Indo tayi kafin tace.
" Kai INNA Lami wato har yanzu baki manta da haura katangar banɗaki ba kenan, da ɗinma fa INNA Lami yarinta ce, kuma kinga ai yanzu na girma bazanyi ba, amma fa INNA Lami Ranar na tsula miki tsiya, Allah sarki yarinta mai daɗi."
Ta ƙarasa maganar tana dariya,
" Ta yaya zan manta da wannan Ranar da kika kusa sani fita waje tsirara, ja'ira yarinta ko tsiya, gashi kuwa ai yanzu birni ya gyara ki,."
Suna cikin hirar ne innar hansai ta fito gaisawa sukayi da ita sun juma suna hira kafin Indo ta musu sallama ta tafi, Indo har zata shige gidan su ta hango gidan INNA fasa shiga cikin gidan nasu tayi ta shige na INNA tun daga zauren gidan idanunta suka fara zubar da hawayen kallo take bin gidan dashi ta ko ina idanunta ne ya sauƙa a bedroom ɗin INNA ƙarasawa tayi tasa hanu ta tura ɗakin ta shiga ganan komai nata a ajiye komai yana nan babu abunda aka taɓa, gadon nata ta hau ta kwanta sai kuma ta fashe da kuka tana cewa.
" Allah sarki INNA kin tafi kin barni da kewarki, ganan komai naki a ajiye amma sai dai ke bakya nan, Allah ya jiƙanki INNA ashe barinki ƙauyen nan kin barsa kenan har abada bazaki dawo ba,"
Share hawayen ta tayi tana tuno Ranar data saka fararen kaya ta tsoratar da ita da mutuwa Allah sarki ashe kuma mutuwar taki tana kusa, Indo ta juma tana tuno rayuwarta da INNA, kamar wacce aka tsikara ta tashi da sauri ta ɗauki tsintsiya tahau shara, sanda ta gyara komai na gidan tana cewa.
" INNA gidan ki bazai wulaƙanta ba dan babu ranki zan cigaba da gyarawa har na bar ƙauyen nan."
INDO dai bata bar gidan INNA ba har magaruba sannan ta shiga cikin gidan su, daddare ma Sharifa ta kirata sun juma suna taɗi harta haɗata da Aunty Hindu ma suka gaisa sosai Aunty Hindu ta bawa INDO haƙuri na rashin samun halartar aurenta da bazasu yiba sakamakon bullowar wannan cutar ta coronavirus da ta tsayar da komai na duniya sun juma suna tattaunawa kafin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 14