Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daga baya suka kashe wayar. ************************************** Allah sarki Rayuwa yau kimanin satin Mustafa biyu a kulle cikin hotel yayi wani irin rama har duhu yayi ga wani ƙasumba daya cike masa fuska baida aikin daya wuce ya wuni yana Shaye-Shaye wasu ƙwayoyin ma Kamal da kansa yake zuwa ya kawo masa ya koma, amma fa sanda Mustafa ya hani Kamal daya sanar da kowa inda yake, kwata kwata yanzu rayuwar Mustafa ta sauya ga shi yanzu wani sa'in haka zaita aman jini ga tari dake damunsa amma tsabar taurin kai irin na Mustafa yaƙi fita yaga likita ko ya kira likitan yazo ya dubasa, kullum kuma cikin sambatu kiran *SHATUUN SA* Yake Rayuwar sa ta koma abin tausayi. Haka Habeeb yana cikin munguwar damuwa na rashin ɗan uwansa duk bincike da zaiyi yayi amma babu Mustafa babu labarin sa hankalin sa a matuƙar tashe yake, ko Maganar Auren nasa yanzu baya yi ɗan uwansa ne kawai a cikin ransa, haka ko kiran Indo a waya bayayi haka itama Indo bata kiran Habeeb ɗin domin kuwa kwanakin nan da Mustafa take kwana take tashi a zuciyarta ga wani irin tsinkewa da zuciyarta take yi, haka zata shiga cikin ɗaki ta yi kukanta ta goge hawayenta ta fito, RAUDA kuwa tafi kowa shiga cikin damuwa domin kuwa yanzu kuka shine ya zame mata abincin ta ta daina cin abinci, ta rame sosai tayi baƙi, ga yawan ciwo da cikin ta da ƙirjinta yake mata, duk wanda yasan RAUDA ya ganta yanzu sai ys tausaya mata, haka Momy itama tana cikin damuwa kullum cikin hawaye take tana roƙon ubangiji daya bayyana mata ɗanta, domin kuwa Habeeb ya sanar da ita gaskiyar Abunda yake faruwa ganin har yanzu babu labarin Mustafa, shine ya yanke shawarar sanar da Momy domin ta tayasa da addu'a saboda bakin uwa bashi da hijabi da UBANGIJI, wato yanzu tsabar tashin hankali Momy har mantawa take da Habeeb zai Auri Indo domin kuwa yanzu hankalin ta yana kan ɗanta, ko sanda Mamy ta kirata take sanar da ita Maganar zuwa wajen boka Momy cewa tayi ta rabu da ita kawai yanzu ba shi bane a gabanta, sosai Mamy taji haushin Abunda Momy ta gaya mata, domin kuwa bata so su tsaya iya nan ba taso ace tafi haka yagar kuɗi a wajen Momy. DADDY yana zaune a kasuwa gabaki ɗaya yau tunanin sa yana kan ɗannasa zuwa yanzu abun ya fara basa tsoro, ya juma yana tunani duk binciken daya kamata yayi yayi amma babu wani good imfomotion, jin kiran Sallah yasa Daddy tashi ya ɗauro alwala ya shige massalaci bayan sun idar ne Daddy yana zaune a massalaci Kamal ya masa Sallama, Amsa sallamar Daddy yayi kamal ya mikawa Daddy hanu sukayi musabaha sannan ne kamal yace. " Sunana Kamal ni abokin aikin ɗanka Mustafa ne, na kawo maka infomations ne akansa." Maida hankalin sa Daddy Yayi kan Kamal tare da cewa. " Bismillah ina sauraronka." " Alhaji Mustafa ba ɓata yayi ba yana nan cikin garin nan, a nan Abnur hotel ya kama ɗaki mai no 10 yana can ya mayar da Shaye-Shaye abincin sa, babu kalar ƙwayar da Mustafa baya sha na masa faɗa amma Mustafa yaƙi dainawa na ce masa ya dawo gida nan ma yaƙi, ban san dalilin sa na barin gida ba, amma dai nasan yana Abnur hotel." Ran Daddy yayi mungun ɓaci har wani duhu idanunsa yake masa Tabbas Mustafa yayi mungun raina sa ya ci masa mutunci, wato dan yaƙi aura masa Indo shine zai fita yabar gida, har ya koma Shaye-Shaye murmushin takaici Daddy yayi sannan ya cewa Kamal. " Na gode sosai Yaro na gode da sanar dani halin da ɗana yake ciki, zan kuma ɗauki mataki." Murmushin mungunta Kamal yayi tare da cewa Daddy. " Amma Alhaji dan Allah karka sanar dashi cewa nine na faɗa maka inda yake." " Karka damu yaro insha Allah bazan sanar dashi ba." Godiya Kamal yayi wa Daddy kafin ya tafi, Daddy ransa ya ɓaci sosai ya kuma yi alƙawarin cewa bazai sanar da kowa halin da Mustafa yake ciki ba, Abunda ya fitar dashi daga gida shine zai dawo dashi. ***************************************** Rana bata ƙarya sai dai uwar gijiya taji kunya, yau Alhamis gobe juma'a itace ranar daurin auren Habeeb da Indo, Momy yanzu ko Maganar Auren bata yi, saboda ba shi bane damuwar ta yanzu, yau da misalin ƙarfe biyu na rana Daddy ya dawo da akwati nan Auren Indo akwati shida Daddy ya haɗa mata Momy ko kallo kayan basu isheta ba, Habeeb kuwa babu nairar sa cikin kayan duka Daddy shiya haɗa da kuɗin sa, HASINA da RAUDA ce kawai suka ga kayan, itama RAUDA ƙarfin hali ne kawai ya sata ganin kayan turmi talatin Daddy ya sa mata masu tsadar gaskiya kaya fa masha Allah komai yayi. Daddy kuwa bai sanar da kowa labarin da yaji game da Mustafa ba, yayi shuru ya ƙyale maganar, haka kuma ya kwantar da hankalin sa. ***************************************** A can Dasina kuma sosai Mama suke hidimar su da ƴan uwanta, haka maƙota duk sun shigo musu, Lami kuwa tun safe take cikin gidan, Indo tana ɗaki sai sharɓar kuka take mussaman idan ta tuno gobe ne ɗaurin Auren ta kuma da wani daban ba ya Mustafa ba, zuciyarta na mungun bugawa idan ta tuno da wannan, jin kamar Muryar Zahra ne a tsakar gidan nasu ya sata saurin goge hawayen ta ta sauko daga saman gadon Mama ta fito da sauri, Zahra ce kuwa da gudu Indo taje ta rungume ta tana mata Oyoyo, gaggaisawa Zahra tayi da jama'ar wajen kafin Indo ta kama hanunta suka fice zuwa ɗakin Mama, sanda aka kawowa Zahra ruwa tasha bayan ta huta ne Indo tace. " Sannu da hanya, da ai nayi zaton bazaki zo ba da naga shuru tun jiya baki zoba." Murmushi Zahra tayi tare da cewa. " Ai kuwa da bazan zoba, saboda wannan cutar wai Abba babu ruwansa yana tsoron coronavirus gashi cikin jama'a zan shiga da ƙyar dai ummi ta lallashe sa Kafin ya barni na taho, Amarya amarya s gidan ya Habeeb sai ƙanshi fa kike hajiyata." Cikowa idanunta sukayi da hawaye kafin tace. "Zahra har yau ban ƙara jin labarin ya Mustafa ba, ina son sanin halin da yake ciki nasan yana cikin damuwa." Ta ƙarasa maganar hawaye na sauƙa a idanunta, Zahra kuwa tsuka taja tare da cewa. " Haba A'isha meyasa kika kasa ciresa a cikin ranki, karki manta fa wannan mutumin bashi zaki AURA ba gobe ɗaurin Auren ki, kuma yanzu nake jin cewa ya kamata ace kin ciresa a ranki ki yiwa kanki ƙiyamal laili karki je gidan wani da tunanin wani." . " Zahra kinsan dai............." " Karki ƙarasa wannan maganar kawai ki cire shi a cikin ranki, ni yanzu ba wannan ba, ina son ki haɗani da Baba muyi Magana, saboda Ummi na ta miki komi na saitin ɗaki har kayan kitchen ta Kuma sanar da Daddy, yanzu haka nabar Ummi sun tafi miki jere." Sosai Indo tayi farin ciki, bata yi ƙasa a gwiwwa ba ta ɗauki Zahra sukayi wajen Mama da Baba, suma sosai sukayi murna, daman kuma Baba bai sayi saitin ba, yana sone sai gobe idan za'a tafi da ita ya bada kuɗin aje birni a saya mata irin nasu na birnin. Rana bata ƙarya yau ne juma'a Ranar ɗaurin Auren INDO da Habeeb yayin da Indo take jin wani irin mungun nauyi a cikin zuciyarta sam bata murnar wannan Aure da za'a ɗaura ita Abunda yake ɗaga mata Hankali ma, yanda Habeeb ya daina kiranta a waya ko jiya da ta kirasa ma ƙin ɗagawa yayi kuma har yanzu bai biyo kiran ba, to me yake nufi da nine, tana maganar zucin ne tana kuka, Zahra da take gefe girgiza kanta kawai tayi, domin kuwa ko bata tambaya ba tasan damuwar ƙawar tata. MOMY kuwa yau baƙin ciki biyu ne ya haɗu mata na wannan auren da ya zama mata dole tayi haƙuri tana gani a ɗaura sa da kuma na ɓacewar ɗanta wanda yafi soyuwa a zuciyarta, tana cikin tunanin ne taga Daddy ya fito cikin manyan kaya, shida Habeeb kallon ta Daddy yayi tare da cewa. " To A'i mufa mun shige ɗauro auren ɗanki sai ki mana addu'a." A dole kuma cikin ƙarfin hali Momy tace. " Allah ya dawo daku lafiya, amma yanzu dan Allah Alhaji muna cikin wannan jimamin na rashin ɗan mu shine kai kuma kake ta tafiya ɗaurin Aure, kamar wanda baka damu da rayuwar ɗanka ba." Murmushi Daddy Yayi yace. " Karki damu ɗanki naji labarin sa, yana nan cikin halin lafiya, yama kusa dawowa kawai yaji ya muku saboda kun hanasa Auren Indo." Daga Habeeb har Momy kallon mamaki suke bin Daddy dashi kafin Habeeb yace. " What Daddy da gaske kasan inda ɗan uwana yake, pls Daddy ka sanar dani yanzu naje na ɗauko sa dan Allah." Murmushi Daddy Yayi yace. " Yanzu babu wannan lokacin muje muyi Abunda yake gaban mu idan yaso idan mun dawo sai mu ƙarasa Maganar, yauwa matar gwamma Hajiya Hari zata zo ita da ƴan uwanta za suyiwa Indo jere acan ɗaya part ɗina na baya." Ajiyar Zuciya Momy ta sauƙe kafin tace Allah ya dawo daku lafiya. Daddy basu wani juma ba suka isa cikin ƙauyen DASINA a gidan INNA suka sauƙa harda amininsa Alhaji Ahmed mahaifin RAUDA, su Uku suka je tarba kuma ta mutunci aka musu Daddy da kansa ya miƙawa Baba da amininsa Baba Abubakar sadakin Indo Naira dubu hamsin. misalin ƙarfe 2 na rana bayan an sauƙo daga Sallar juma'a aka shigo da goron ɗaurin Auren Indo cikin gidan nasu, Goggo Hali ce ta saka guɗa, tabbacin an ɗaura Aure, ai kuwa Indo tana jin wannan guɗar ta saka kuka sosai take kuka ganin da gaske ta rasa Mustafa a matsayin mijin Aure. Kuyi hkr fan's ban samu nayi editing ba zaku haɗu da typing error. *ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻* Ummu Nasmah ce [5/11, 12:52 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘💘💘 *S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽* *Cigaban* *(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)* 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 💘 💘💘 *Na* *r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸* *(մʍʍմ ηαςʍα)* 👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻 *Marubuciyar* *Sauyin Rayuwa* *Nasmah ko Nasirah* *Sara da Sassaka* *INDO A BIRNI* AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*. *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ *D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞* *Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa* Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake. Allah yabar ƙauna. *S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢* *AUNTY HAUWA MAMAN USWAN* Ina roƙar UBANGIJI daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya. _________________________________________ *P*••••••2️⃣9️⃣ ↗️ 3️⃣0️⃣ Sosai ta bawa Zahra tausayi Tabbas rashin masoyi akwai zafi sai dai ya zatayi ƙaddara ta riga fata, babu yanda zasuyi tunda Allah ya rubuta cewa Habeeb shine mijinta ba Mustafa ba, cikin tashin murya Zahra tace. " A'isha idan har kinyi imani da Allah da kuma ƙaddarar sa, to ya kamata ace kin Rungumi ƙaddara kin daina saka damuwa a zuciyarki, nasan akwai damuwa amma haƙuri zakiyi duk sanda ya taso miki ki dinga ambaton UBANGIJI, karki manta ko babu rabuwar rayuwa tsakanin ki da Mustafa to ki sani fa akwai ƙaddarar mutuwa, ko kuma idan ya mutu zaki bishi ne, yau ina INNA ta mutu duk son da kike yiwa Mustafa dole zaku rabu koba juma ko ba daɗe tunda akwai mutuwa, to meyasa ba zakiyi hkr ba yanzu ki godewa UBANGIJIN ki ki kuma Rungumi mijin da ya baki ki godewa UBANGIJIN ki A'isha domin kuwa ya miki ni'ima maɗaukakiya, tunda harya cireki daga cikin duhun jahilci ya haska ki a cikin hasken ilimi ta sanadiyyar fitar dake daga cikin wannan ƙauyen zuwa birni, ki godewa UBANGIJIN ki." Jikin Indo yayi sanyi ƙalau sosai nasihar Zahra ya shiga jikin ta shuru tayi tare da goge hawayen ta, Abokanan wasa kuwa sai shigowa suke suna tsokanar ta, can wajen ƙarfe Uku Mama da Goggo Asabe suka saka Indo a cikin ɗaki sosai suke mata faɗa akan zaman Aure, Mama ce ta dubeta tace. " Kiji tsoron Allah Indo ki yiwa mijinki biyyayah domin kuwa aljannar ki tana ƙarƙashin ƙafarsa, shi zaman Aure sai da haƙuri dole domin kuwa wahalar sa yafi daɗin sa yawa, duk abunda mijinki ya umarce ki dashi to kibi muddun bai sabawa UBANGIJI ba, ki sani cewa Rayuwar ki ta da babu Aure ba ɗaya bane da rayuwarki ta yanzu da igiyar Aure ya shiga ya zargeki, sannan kiso ƴan Uwansa tamkar yadda zaki so naki ƴan uwan, kiyiwa uwar mijinki biyyayah kamar yadda zaki min domin kuwa itace mahaifiya gareki yanzu." Sosai mama ta mata nasihar haka Goggo Asabe ma, kafin daga bisani suka turata wajen Baba shima sosai ya mata nasa faɗan Zainabu da Hansai sai Lami suma dasu akayi wunin juma'ar, shima ya Tanimu ya mata nasa faɗan, koda sukazo tafiya birni mutum huɗu ne zasu raka Indo, Goggo Asabe da Goggo Hali sai Lami da Innawuro Mama bata bar ƴartata ta tafi haka ba sai da ta kaɗata da ƴan kayayyakin su na ƙauye, haka ma ta haɗa mata da kayan gara mai yawan gaske, Indo tana kuka suka rabu da Mama. INDO har suka shiga motar aka tayar suka tafi bata saka Habeeb a cikin idanunta ba, hakan kuma ya mata zafi cikin ranta sai dai bata nuna hakan a zuciyarta ba har suka shiga cikin birni, part ɗin Momy aka sauƙe su, Indo ganin sun sauƙa part ɗin Momy sai da zuciyarta ta tsinke amma haka ta daure suka ƙarasa har cikin falon, su taradda Momy da Mamy sai ƙanwar Momy Aunty Zulai da kuma mahaifiyar Zahra, a wannan karon sosai Momy ta bawa kowa mamaki yadda ta saki ranta take fara'a tamkar tana son Auren da kanta Momy ta haura dasu bedroom ɗin Indo, abinci kuwa kala-kala aka shiga musu dashi tare da musu ban gajiya, Hasina kuwa ta bawa marar ɗa kunya domin kuwa zaka rantse da Allah ba itace akayiwa kishiya ba, mussaman ta zo part ɗin Momy ta tare su RAUDA kuwa tun safe tana ɗaki sai muƙurƙuso take yi sosai cikin ta yake mata ciwo, ko tashi bata iya yi, Hasina ce data lura da babu RAUDA ya sata zuwa part ɗin nata taga ko lafiya, ai kuwa cikin jini ta sameta cikin mawuyacin hali, da gudu tazo ta sanar da Momy halin da RAUDA take ciki, Momy batayi wata-wata ba ta ƙira Habeeb, cikin sauri aka saka RAUDA a cikin mota sai Hospital. Koda isarsu Hospital ɗin RAUDA ta galabaita sosai, babu sunan wanda take kira sai Mustafa, Emagency aka shige da ita DARECT, harda Habeeb cikin masu duba RAUDA, binciken da sukayi shiya tabbatar musu da haihuwa ce sai dai bata da ƙarfin da zata iya haihuwa da kanta dole sai dai a mata c's Habeeb ne ya fito ya haɗa Uban gumi ya dubi Daddy tare da cewa. " Daddy haihuwa ce sai dai bazata iya haihuwa da kanta ba dole sai an mata C's shine muke so ka saka mana hanu tunda shi Mustafa baya kusa." Cikin sauri Daddy yace " Habeeb meyasa sai ka sanar dani kaima zaka iya yanke ko wani hukunci akan RAUDA matar ɗan uwanka ne fah kaje kasa hanun a madadin ɗan uwanka, mudai burin mu ta sauƙa lafiya." Ai kuwa da sauri Habeeb ya koma cikin, a cikin mintuna kaɗan aka gama komai na shirin Cs amma RAUDA taƙi fir a shiga da ita ɗakin tiyata,tace dole sai taga Mustafa kafin ta shiga, Habeeb ne ya fito ya sanar da Daddy yace Daddy ya shiga ya mata Magana ko zataji nasa, koda Daddy ya shiga da ƙyar RAUDA ta ɗago idanunta ta kalli Daddy tare da cewa. " Ka taimake ni Daddy ka kira min ya Mustafa na gansa akwai Maganar da nake so muyi dashi kafin na shiga ɗakin nan, ka taimaka min Daddy naga mijina kafin na tafi." Sosai ta bawa Daddy tausayi bai ce mata komai ba ya juya ya fito cikin sauri tare da cewa Habeeb su jirasa yana zuwa yanzu, Daddy motar sa ya hau da kansa ya tuka bai tsaya ko ina ba sai Abnur hotel, yana zuwa ya samu ma'aikatan hotel ɗin yace su duba masa waye ya kama ɗaki mai number 10 suna dubawa suka tabbatar masa da cewa Mustafa Harun shine wanda ya kama ɗakin, har ƙofar ɗakin Daddy yasa aka kaisa da kansa Daddy yayi Nocking, Allah ya taimaka lokacin Mustafa ba'a shaye yake ba, daga cikin ɗakin yace. " Waye ne.?" Cikin ƙula Daddy yace. " Ubanka ne, nace Uban ka ne?" Jin muryar Daddy yasa zuciyar Mustafa tsinkewa, da sauri yasa hanu ya buɗe bedroom ɗin, tunda ya buɗe bedroom ɗin Daddy yake binsa da kallo yanda yaga ɗan nasa gabaki ɗaya ya sauya ya fice hankalin sa, ga wani uban ƙasumba daya tara kafin Daddy ya maida dubansa ga bedroom ɗin kwalaben Shaye-Shaye ne birjik zube a cikin bedroom ɗin girgiza kansa Daddy Yayi tare da saka hanu ya ɗauke Mustafa da mari har Uku kafin yasa hanu ya figesa da ƙarfi, har cikin mota, jan motar Daddy yayi da mungun gudu har cikin Hospital ɗin, kafin ya ƙara jawo hanun Mustafa shidai Mustafa bin Daddy kawai yake cikin Ransa kuma yana ayyana waye a cikin asibiti, Momy Mamy Hasina Indo Goggo Asabe gabaki ɗayan su tashi sukayi suna kallon Daddy da Mustafa, Indo gani tayi gabaki ɗaya Mustafa ya sanja mata shima kuwa Indo yake bi da kallo har Daddy yayi cikin ɗakin da aka ajiye RAUDA kafin ya sakesa, gabaki ɗayan su su Momy suma shigowa sukayi ɗakin ƙwarai sun tausayawa halin da RAUDA take ciki Mustafa kuwa da sauri ya ƙarasa gabanta ya tsugunna cikin tashin hankali yake cewa. " Me yake damunki RAUDA, meya sameki, kike kwance gadon asibiti.?" Ya mata Tambayar cikin tashin hankali, murmushin farin ciki RAUDA tayi na ganin mijin nata, tana cije leɓenta yayin da take jin munguwar azaba daƙyar ta buɗe bakinta tace. " Ya Mustafa kaine nake gani a gabana, ina kaje haka ka barni cikin tashin hankali, na shiga damuwa sosai na rashin ganin ka, kana lafiya ko ina kan babu abunda ya sameka.?" Wani irin sanyi jiki Mustafa yayi, har kunya yaji gashi dai shi ya tafi ya barta bai taɓa tunanin ta a cikin zuciyarsa ba ko sau ɗaya, Allah Sarki ashe ita dashi take kwana take tashi, kama hanunta Mustafa yayi tare da saka ɗayan hanun nasa ya goge mata gumin da take haɗawa kafin yace. " Kiyi RAUDA bada son raina na tafi na barki ba, ya zama min dole ne nayi nesa da ahalina domin samawa zuciyata sauƙin Abunda ke damunta ina mai baki haƙuri a karo na biyu daki yafe min.?" Murmurshi tayi tare da kamo hanun nasa ta ɗaura a cikin ta, kafin tace. " Kullum cikin yafiya nake gareka ban taɓa kwana ba tare dana yafe maka duk wani laifin da kamin ba, a yanzu nine nake buƙatar neman yafiyar ka domin kuwa ina ji a jikina cewa bazan fito daga ɗakin tiyatan nan ba da raina mutuwa zanyi ya Mustafa bazan tashi ba." Kaɗawa idanun Mustafa yayi yayi jajur hankalin sa yayi mungun tashi, gabaki ɗaya mutanen dake tsaye a wajen babu wanda bai tausayawa RAUDA ba, Indo kam ma uwar ƴan saurin kuka, sai sharɓar kukan take, ta maƙale jikin Zahra, hankalin ta yayi mungun tashi, domin kuwa shigen Abunda INNA tayi kafin ta rasu shi rauda takeyi yanzu, Mustafa cikin tashin hankali yace. " Bazaki mutu ba RAUDA bazaki mutu ba, ba tare da na nuna miki Soyayya ba da kulawa tare da tattali, A yanzu ina sonki ina sonki karki tafi ki barni ki tsaya mu raini ƴarmu tare karki tafi ki barta cikin maraicin rashin uwa." Murmurshi sosai RAUDA take mai haɗe da hawaye tana shafa cikin nata kafin tace. " Ƴata baza tayi maraicin rashin uwa ba, muddun HASINA da INDO suna raye na Tabbata bazasu bari tayi kukan rashi na ba, alƙawari ɗaya zaka min shine ka karka bari ƴata tayi kuka ina son ka nuna mata kulawar dani na rasa a wajen ka ko yanzu nayi farin ciki da furta min kalmar so, sannan na yafe maka kaima ka yafe min ina sonka MIJINA." Ta ƙarasa maganar tana danƙe marar ta dake mata ciwo, duban Mamy tayi dake gefe tana rausar kuka tace. " Ki daina kuka Mamy ki min addu'a sannan kice Daddy ya yafe min nima na yafe maku, ina sonki Mamy ki cewa kalit kar yayi kewata shima yamin addu'a, Momy kema ki yafe min kinji." Gabaki ɗayan su kuka suka saka Mamy gagara Magana tayi tsabar kuka yaci ƙarfin ta, RAUDA hanunta ta ɗaga tayiwa Indo alamar tazo, da sauri Indo ta ƙarasa gabanta tana hawaye, cikin ƙarfin hali RAUDA tace. " Ki yafe min nasan na miki kuskure a baya ina roƙon ki yafiya, sannan ga Amanar ƴata nasan ba lallai na samu damar ganinta ba bayan na haife ta ki riƙemin ita nasan zaki kula da rayuwar ta hanu ta miƙawa Indo alamun ta mata alƙawari." INDO kuka ta fashe dashi kafin tasa hanunta cikin na RAUDA tace na miki alƙawari kuma na yafe miki, insha Allah ma zaki tashi zaki RAYU da ƴarki bazaki mutu ba." Habeeb ganin da yayi Maganar RAUDA ba mai ƙarewa bane ya sashi tura gadon yayi tiyata room da ita, Mustafa da sauri yabi bayan su yana ajiyar Zuciya, tana kallon sa har aka shige da ita ɗakin Cs ɗin, jin gina Mustafa yayi a gefe sai famar ajiyar Zuciya yake sauƙewa, kowa dake wajen tsaye yake cikin tashin hankali, wajen awan su Huɗu da shiga Cs ɗin sannan Habeeb ya fito riƙe da jaririya a hanunsa jikin sa a matuƙar sanyaye, Indo ce ta tashi da sauri ta amshe jaririyar daga hanun Habeeb tana ƙare mata kallo, Mustafa cikin sauri ya k'arasa wajen Habeeb ba tare daya kalli jaririyar ba yana cewa. " Ina RAUDA ina fatan tana cikin halin lafiya ko?" Girgiza kansa Habeeb yayi tare da cewa. " Sai dai muyi haƙuri domin kuwa RAUDA ta amsa kiran mahaliccin ta, Allah ya mata rasuwa." Ja da baya Mustafa yake yana nuna Habeeb da hanu yana cewa. " Ƙarya kake RAUDA bazata mutu ta barmu ba, nasan zata tsaya ta rayu damu bazata barni nayi biyu babu ba, nasan UBANGIJI na bazai rabani da masoyana duka biyu a lokaci ɗaya ba ya barni cikin kaɗaici ba, ka daina faɗa min wannan maganar." Gabaki ɗayan su kuka suka saka, hankulan su yayi mungun tashi Daddy ne kawai yayi ƙarfin hali a cikin su ya ke kiran sunan UBANGIJI, turo RAUDA da akayi rufe da yadin tiyata, yasa Mustafa ƙarasawa da sauri ya yaye zanin, tana kwance fuskar ta rufe, sunkuyawa kanta yayi yana cewa. " Nasan bacci kike, ki tashi ki faɗa musu su daina miki kuka ke baki mutu ba da ranki ki tashi ki gaya musu, bazaki tashi ki gaya musu ba, nasan bazaki tafi ki barni ni kaɗai ba.?" Ganin da Daddy yayi Mustafa yana ƙoƙarin zaucewa ya sashi ƙarasowa gabansa tare da dafa sa yace. " Wanda ya mutu bazai taɓa dawowa ba, ka dawo cikin hankalin ka, ka yiwa matar ka addu'a domin kuwa ta rigaka gidan gaskiya, ita da ta

Chapter 12 of 14