ne a baya.
Juyawa yayi ya nuli dakinsa, ni kuwa ina binshi a baya.
durowa ya buda ya dauko mani takardu da hotunan Halimatu, da
gani irin na sakandire ne, tare da miko mani kundin rubuta
maganganun asirinsa, "Diary, yace wai in karanta.
Halimatu kan ta yaudan yayana zance kenan, saboda rubutun
da tayi a kundin littafin asirinsa ya tabbatar mani sunyı alkawalin
yin aure da Halimatu, ficewa yaya yayi yana ta fada da yan surutai,
wanda tun a Kofar dakinsa nike ta bashi hakur, amma ya kıya.
Tashin hayaniyar yaya usman da yakewa Halimatu fada da
sauran surutai bacin rai, shi ya janzo Mamana da Daddy shigowa
habban falon da muke a tsaitsaye.
Da sharia' tayi nisa tsakanin Halimatu da yaya, wanda
Halimatu ta kasayin maganar komai, hakan yasa Daddy yace mu
fita inya gama, zai nemeta da ta shigo.
Allah kadai yasan abinda Daddy yacewa yaya Usman mu
kuwa munyi jugun jigum, a dakina sai ga yaya ya shigo ya zauna,
nesa da Halimatu," "Halimatu kiyi hakuri dan Allah, ban fahimci
komai ba, shi yasa har nayi maki haka, amma yanzun na gane,
kuskurena, nasan kuma shi aure Kaddarane, Allah ya baku zaman
lafiya."
Ganin sunyi shinı, yasa ni kuma na fice na barsu a dakin
nawa, a tunanina ko da wasu bayanai da zasuyi wanda basu shafeni
ba,
Ban fi inintina sha biyar da fita ta ba, suma suka fito, wanda
na fahimci fiskarsu ba wata walwala balle annuri ko annashuwa,
hakan dana fahimta yasa ban yiwa Halimatu maganar komai ba,
duk da nasan ina cike da al'ajabin abinda ya faru mintina hamsin
da biyar da suka wuce, zuwa awa daya.
Sannan ga cikina da zuciyata cike da tambayoyi kala-kala
wanda ya cancanci in samu amsarsu cikin lokaci mai sauri, amma
duk na hakura, tunanin kada in dawo mata da wani abu sabo a
zuciyarta,
*** *** ***
Har muka samu tsawon kwana biyu, amma ban tadawa
Halima da maganar yaya ba, amma kuma abinda ke neman f'aure
mani kai, shine yanda na ga yanzun kullum lalimatu na tare da
yaya, ko yaya fita yayi, to kuwa in ka bi shi da tambaya, zai
tabbatar maka gidan su Ilalimatu yajе.
Wanda ita kuma Halimatu, ba'a kwana biyu sai tazo gidanmu, in kuwa zata tafi, yayana ne direbanta mai mayar da ita
gida, lallai al'amarin nasu ya fara daure mani kai, wanda ni kuma
70
niyar yiwa lalimatu kamfai din Mustapha, sun sakani a kokontu,
da tunanin, ya halimatu zata mayar dani kamar yarinya.
Ranar cikon kwana na shida ne na tambayi Mamana zuwa
gidansu halaimatu, har na fita direba zai kaini sai ga yaya ya fito
da sauri," "ina zaki ki barni?, saboda tunda yaya ya dawo kullum
muna tare, in ina dakina zai shigo wai muyi hira, in kuwa dakinshi
na shiga, shima ya tsareni muyi hira, ba kuwa hirar kowa yake so
muyi ba, sai hirar Halimatu.
"Ni kuwa na ki bashi hasken komai akan Halimatu, "Yaya
gidansu Halimatu zanje yanzu zan dawo," "tsaya inzo in kaiki," ba
zanwa yaya gardama ba, saboda haka dole na yarda ya muka tafi
tare.
Ba abinda ya kaini gidansu Halimatu, bace in yi mata
maganar yaya Usman da ta Mustapha, saboda in san me ake ciki,
bayan mun gama gaisawa da mutanen gida, ba hirar da na farayiwa
Halimatu sai ta bugun cikinta game da yaya Usman.
"Halimatu da yaya muka zo yana kofar gida," tayi saurin
mikewa tsaye, "ina zuwa dan Allah Hamida, bari in je in kai mashi
ruwa," "nasa kai masa ruwa har da lemu, sannan da yaya Anas
'suke tare suna hira,
Ni ma yanzu abinda ya kawoni, shine maganar Mustapha,
kinga lokaci daya diba mani yayi shawara, saura kwana takwas,
ina son dama in shaida maki cewa da kwana takwas din ta cika ba
mamaki a satin a aiko da mutane neman aurankı daga gidansu,
saboda haka in sunzo, kisan dubarar da zaki gayawa su Abba."
Ni wallahi Hamida sai naji ma duk yanzu Mustapha ya fara
fita daga zuciyata, ni wallahi dama ce masa kikayi, na fasa da nafi
jin dadi, "nayi murmushi, "to sai kuma ki auri wa?," "yaya
Usman," "yace yana sonki?," "kwarai," "tun yaushe yace yana
sonki?".
"Amma in baki manta ba Hamida, ina yawan yi maki zance
ina da saurayin da nike mutuwar so, amma nace maki yayi mani
nisa, rashinsa ne ma ya janyo mani da kamuwa da son Mustapha,
dama shi wannan saurayi ba wani bane illa yaya Usman,".
"Me yasa baki gaya mani ba tun tuni sai yanzun da kika sani
naje na karyar da 'yancina, na wulakanta mutuncina duk akanki,
amma wallahi Halimatu kin bai mamaki..........." "Shin Hamida
71
me ya kawo wadannan zantutuka masu zafi haka, Allah huci
zuciyarki, kije ki karasa aikin ladarki ni kuma zan auri Mustapha,
ko dan darajarki ta daukaka.
Amma Hamida me zai hana muyı dubara mu samu wata
yarinya mai kyau mu ajiyeta da sunana ita Mustapna zai aura,
dama kinga bai taba ganina ba," nayi tsoki na mike, "ni kuma ga
Hamidar mahaukata ko?" ni zan koma gida na, ni duk kin bani
haushi," da kyar ta dan shawo kaina na dan kara zama.
*** *** ***
Na shirya jikina tsab, bayan na kammala komai na dakina, na
kalli agogon bangon dakina karfe goma da rabi na safiyar asabar,
wanda tayi dai dai da cika wata daya da Mustapha ya bani.
Ba wasu kayane jikina ba, bacc ruwan kasan yadi shadda na
wacce ya ciza da yawa, dinkin "I can't miss you", bani da fargaba
tambayar zan fita a wajasu Daddy, saboda ranar tayi daidai da
ranar yinin bikin kawarmu, Jamila Garba Sale Daudawa
Wanda mun samu kusan kwana biyar muna zirga zirga kan
sha'anin bikin, to balle yau, da yake ranar kai amarya.
Tunanina faya, shine ina zamu hadu da Mustapha inji wane
sharuddane za'. gindaya mani, wanda dai nasan basu wuce a kan
sufiyani ba,
a
Fashon- 'din' bakin takami ne a kafata, da jakarshi 'lappy
new year," mayafi baki, shine na yafa a jikina, farin gilashi ne
karami a fiskata, na fita naje na sanarda Mamana cewa zan tafi,
nan ne tace inyi gaba tananan zuwa bayan sallah a zahar, sai ta
taho mani da gudunmawar kayan da zan kaiwa amarya.
Ina isa falo, wayar dake da mazauni a gefan (ſaya na duguwar
kujera a dan karamin tebirin gefe, tayi kara, ban tsaya dauka ba
nayi gaba, anawa tunanin wani ya dauka a cikin gidan namu.
Amma har nakai kofa, sai naji ta karayi, har karo na uku,
nayi saurin dawowa da baya na dauka, miryarsa kawai naji, пa
gane kowaye, Mustapha kenan na amsa masa sallamar da yayi, he
tare da tsayawa bata lokaci ba, ya cigaba da magana,
"(I hope you remember what today is) nayi murmushi, "ban
manta ba amma kuma gashi ina neman dan excuse' na yau saboda
bikin da na gaya maka munayi na Jamila 'G' Daudawa," "to yanzu
ya zakiyi da ni ni kuma?" "wai da kayi hakuri sai gobe" "ko?"
72
"nayi murmushi, "rai ya bacine?" "ya kusa, saboda kinsan yau
kwana uku fa ban saki a idona ba ko kina son in hadu da ciwon
makantanc?"
"A rufawa Halimatu asiri, kada tace amarai da makahon
angonta, "yayi tsoki ya ajiye waya, ina ta magana, armma sai naji
shiru, hakan ya kara tabbatar mani ya ajiye wayarne,
Karfe sha daya na safe aka daura auran Jamila "" sha biyu
na rana mu kuwa muna ta shirye shiryen tafiya Walimar bayan
daurin aure, wanda nayi wanka na kara shirya jikina da "Cotton
lace mai kama da shikin (shaking) yadi mai rawa ruwan bulu mai
haske, da faful din mayati 'purple da jaka da takalmi.
Karfe uku na yammacin ranar muna 'Amusement park mune
manayn kawaye duk mun gaji saboda wahalar da muke sha, in da
ma muka ji dadi, fatin ya tsaru, gashi a natsi saboda ilimin da ya
wadaci wadanda suka halarci fatin.
Coil paper takardar nannade kaya, ita na samu na zuba
komai na fatin nan nace a kai mani but din motata, saboda
Mustapha da ke zuciyata, a nawa tunain zan iya cewa ya turo
yaronsa daya ya karba masa, ko bayan mun koma gidane, amma
ana kaiwa akace saina zo na bude but din, wai sun kasa.
Na mayar da hankalina waja bude but din matatą sai wani
yaro ya zo yace wai wani na magana da ni, ina daga kai ya nuna
mani ko waye, ko ba'a fada ba na gane ko wave, duk da va juya
bayanshı yana kallan wani bangaren, amma da gani kasan suine.
saboda gashin kansa ya bayanar da shi, Mustapha kenan.
Nayiwa yarinyar nuni da takai mani kayan dake hanunta.
wajan da Mustapha yake, sannan na bita a baya, ban tsaya gefe da
yake ba, sai na zagaya na taryi in da fiskarshi ke kallo.
"Bai dace kazo nan ba Yallabai, kasan dai ina tare da
Halimatu, nace kayi mani lamanin yau, in na gama, gobe da safe
sai ka fada in da zamu hadu sai in je, amma "iva
lamanin da zanyi maki kenan shi yasa na zo daukarki nima ki je ki
gama mani tawa bukatar.
Ko ni kadai zan maki lamanin amma ke ba zakiyi mani ba?.
ya bude gaban mota mazaunin dareba, ya zauna, ba sai yace in
shigo ba, ni kaina na fahimci abina yake nufi kenan.
73
Maimakon haka sai na fara bude baya nasa kayan ci da shan
da na diba masa, sannan na zagayo na zauna na mayar da kofa тя
na rufe domin in kara ba shi tabbacin zan mashi larnani nima.
"Bismila, ina sauraranka yallafai," "maganata lana nemau natsuwa, wanda ya nuna bai dace ayita anan ba," wai gawar da
zanyi sai naga Halimatu tana nufo motarmu, ban son lokacin-da na
ce, "Mustapha, Halimatu na shiga uku."
Abinka ga namiji banga ya tsorata ba, sai dai ya janye
mayfin kaina, ya dora a kansa, kamar ya dan lillefe kenan sai ya
dan kwanto kadan a jikina kamar yana mani wata magana, isowar
Halimatu, tasa na danyi kamar na tureshi, shi kuwa sai ya kата
janye mayafin ya rufe fiskarsa sosai.
"Sannu malam Sufiyanu, "inji Halimatu, Mustapha ya amsa
da "yauwa, ya gida Halimatu?, "ta danyi dariya, "kaji Suliyanu,
kaima ashe ka iya zaulaya, wai meye na rufe fiska ba matar ka
bace ba, saura kwana nawa Sufiyanu," "kai ni duk sai naji kunyarki."
Tayi dariya, ango kenan, ni ina sha'awarku, kaı kuma kana
jin k inyata, ni da Mustapha ma har yau ban sashi a idon ba, sai
dai hirarshi kawai," "kinsan,abun manya sai hakuri, yanz ın haka
in kin binkita, kilan ma baya kasar nan,""ta iya kasancewa tunda
rabon da mu samu labarinshi kusan sati biyu kenan."
"haka nc, amma in baya ga abinki kawarmu, ki canja wani
saurayin mana, ni in guje maki dana sani, kinsan masu irin
wadanna harkokin ba iya tsayawa suke suna kula da matansu ba,
tun da basu da lokaci," "da gaskiyarka, amma in ga shi Mustapha
ba za'a sameshi cikin wadannan mutanan ba, ni har ma ka kore ni,
kunya fa nike ji in a na yi mani wannan maganar.
"Tsaya! Tsaya!! Mana, tambayar alfarma zanyi wajanki da
amarya, a bani aron Hamida na awa daya in dawo maku da ita,
saboda tattaunawar karshe da nike son muyi, kinsan kuwa tana
neman natsuwa," "a'a'a rufa mani asiri, ni tawa da zan hanaka
Hamida sai kun dawo, zan sanarwa amaryar, har ma kwa dawo ku iskemu, a nan, tunda sai biyar na yamma za'a tashi, kaga kuwa
yanzu uku da yan mintina."
Tayi gaba, tana cewa ta tafi, sai mundawo, tana yin nisa ya tashi mota, tare da zame mayafin da ya rufawa kanshi ya dora a
74
cinyarsa, "ka banı in rufe jikna," ya miko mani tare da kallan nan
nasa na gefan ido.
Kai tsaye 'Asokoro muka nufa gidan Mustapha, wanda da
nayi mashi magana, ko kaltona bai yi ba, muna shiga shigewa yayi
ya barni babban falonshi, misalin minti goma sha biyar yayi, sai
gashi ya fito da duguwar rigar hutawar maza.
Ya iso ya zauna dan kusa da kujerata kofi ne a hanunsa
wanda da gani kasan lemo ne, "kinyi, kyau fa, "nayi dan
murmushi, amma ban ce masa komai, ta gefan ido ya kalleni,
yaushe nc zaku kai, amarya?" nayi yar dariya, "wacce amarya
kuma, ga ka na kawo."
Yayi yar dariya, 'au nine ma amaryar?, ka manta dazu, ni fa
sauran kadan kasani dariya yanda naga ka kudundune kai a
mayafi, da Halimatu ta gane........," "ya isa, don Allah bana son
kiran sunan nan fa kin sani," "Allah huci zuciyar yallabai, na
daina, amma kuma ina son muyi maganar da kace sai mun samu
natsuwa."
Ina sane da ita, shi yasa nima na samu na watsa ruwa, saboda
in kara samun naísuwa," mikewa yayi ya dawo kasan falo ya
zauna, sannan ya kalleni fiska a daure sosai,' "dawo nan kema, ya
nuna mani kasa, watau manufarshi, in zauna in kallanshi
Banyi mashi gardama ba, na dawo na zauna, kanshi
sunkuye, har tsawan kusan minti tara, sanna ya dago kai.
a
Hamida kalleni ido cikin ido, saboda maganar da zan yi mani
ba wasa a cikinta," na dago na kalleshi, "ni waye a gareki", "kai
saurayin kawatane," "ba wannan na tambayeki ba, nasan kinsan
abinda nike nufi."
"Kai babba nane," "ban dashi fa?" "kai mai sona ne," "a
kyau kin gane kenan," ki saurareni sosai zanyi magana da ke, ba
zancan wasa ko raha, ko kuma ban tsoro, ina son ki sa'a zuciyarki
komai ya fito daga bakina, to gaskiya ne,
Ya danyi shiru kadan, ni kuma na kawar da fiskata gefe
"amatsayina na mai kaunarki da zuciya daya ba zan taba yarda in
cutar da ke ba, saboda haka kada ki dauki maganata a matsayin
cutarwa ko takurawa.
Magana zamuyi ta gaskiya game da waccen yarinyar" "au
hali........." ya yi mani kallan da yasa nayi shiru dan dole, "in
75
mapana ta ki viyyuwa, to kamar yarda na fada a bava, yanzun ma
haka, watau ina da shariddana guda uku da zan gaya makı, a cıkı
sai ki zabl daya wanda kika ga ya liye maki.
Ya Kara hade fiskarsa, ina son kafin in fada sar na hiki ta
yarda kike so, shine don Allah in son ki janye maganar aurcna da
wata, in aurcki, ya kika gani?" "zancen in aurceka ma bata taso ba,
haka ma zancan janye maganar Halinatu, sai dai in mu dukan mu
ka bakura damu, wannan na amince.
"Na baki minti talatin kiyi tunani, kalin in fada makı ragowar
amma fa fiskarshi a daure take, "ni dai ka cigaba kawai tunda na
riga na fada, sai kiyi hakuri lokacin yayi, ni yunwa nakeji, abiner
zanci.
Ya mike ya barni nan zaune, hushi da takaici suka rufar mani
a lokaci daya, naji kamar in rufcshi da duka, amma nasan ba falın
yin haka, sai dai kallo na bishi dashi, har ya zauna tibirin cinn abinci
ya juyo ya kalleni bayan ya zauna.
"Kayan da kika sa a bayan motata nawane ko kuwa? na
dauke kaina gefe, ba tare da na bashi amsa ba, ina jinshi ya kara
tambaya'a a karo na biyu, amma shima nayi kamar banji sh ba,
banji ta!iyar sa ba, sai dai na ganshi tsugunc a gabana.
"Yanzun me zance maki ki fahimceni don Allah, in so kike
ayi magana, naji zamuyi magana, amma kiyi mani lamani in ci
abinci, tun safc har yanzu banci komai ba, kiyi mani hakuri in
samu in karya kumallo," na kalli agogon bango falanshi Karfe
hudu saura minti sha daya.
"Zamu gama komai zuwa karfe biyar, Kilama ba zamu kai ba,
in kaya nane a mota in sa a kawo mani in ci, watakilan na ficin na
wajanki tun daga hannunki suka fito, "Just see me go and cat"
please," "ni ka je ka ci ko ka gama dan Allah."
har yanzu bakiyi mani yanda zanji dadin ci ba" "ya kamo
hanuna nayi hanzari zan fizge hanuna, "bana so," "na tuba ba zan
kuma ba," ya mike yana yar dariya kadan, "Hamida my wife."
Na harareshi, "kinsan fa ban taba biyanki komai ba, akan
kallan nan naki mai saki kara yi mani kyau, kar ki sa yanzu in ce
zan biya," na kara harararshi, "Okey in zo kenan?, sai ya taho sai
kuwa na danyi kamar kukan shagwaban nan na yara daga zaune,
ya tuntsire da dariya, "I like you all Hamida."
76
Yanda vayı mani dazu yanzu ma haka, bayan da va gama сin
burns da samosa da dankalin da yan sauran cive civen da vavi,a
ya zo ya zauna kamar dazu, sai dai yanzu lemun kwankwanine
"Canned fruits a hanunshi wanda nima tuni va kawo mani nawa
gabana.
"Shawarar me kika yanke?" "ni dama na fada maka, bani da
wata shawara da ta wuce ka aun Halimatu, ko ka hakura damu
baki daya. "kalleni sosar dan Allah." na daga kaina fiskata a
daure na kalleshi.
Saitin idon Mustapha yakaru sosai, kyanshi va karu a lokacin
daya, wanda sonshi naji va Kara dirar mani azuciyata, navi sauri
na kawar da kaina gefe tare da runtsi idanu wana, na mayar da
numfashi a hankali.
"Me zanvi maka Mustapha?" "han taba jin wanda va kira
sunana yayi mani sanyi a zuciya ba, sat ke Hamida, ki daure ki
aureni kawai nike so," na bude idanuwana, "ba zai viyvuha.""ni
ma na mayar masa a cikin sanyin murya kamar yarda yayı manı
magana.
"yavi gvaran urya tare da kawar da idanuwansa daga
kallona, "in har na fa fi sharadina, ya zama dole fa ki zabi daya
daga ciki, sannan ina mai tabbatar maki da ba fashi ko in tausaya
akan ko wane sharadi da zaki zaba kin amince?
"Bani da zabl sai na amincewa vallabl," "ya juvo da kartinsa
ya kura mani ido, tare da hade fiskarsa, sharadına na tarko.
(SHINE KI JANYE MAGANAR Halimatu, 2 KO KUMA IN
KASHE MU NI DA KF) zabi daga ciki, in kuma ba ko daya, in
fada maki dayan wanda yazama dole ki zabeshi kenan."
"zancen janye maganar auran Halimatu ma bata tasoba sat
dai ko kisan in kana ganin shine alheri a garemu, "Hamida me yуе
dalilin kı navin taurin kai haka "saboda in cika alkawalhn da na
daukatsakanina da Allah, da ita kanta Halimatun."
"ya isa Hamida sharadina na Karshe, shine (SAI DALIN KI
BANI KANKI). Wanda in har kikayi mani haka, kinga a
kwatunancan na lefan da za'a kat gidan su lalimatu ne, har da
sadaki da komai da za'a nema.
"ban fahimci abinda kake nuti ba "ha ki san kankı ba
kenan?" "na san kaina mana, kenan in baka kaina ka yi tsati dashu.
77
ashe kai da matsaline ban sani ba, ka cuci kanka wallahi, me zance
maka, samo wuka ka yan
"Ya isa, ya isa!! Baki fahimce ni ba, ba ina nufin ki bani
kankı na saman wuyan ki ba, a'a ma'anata (sai na sanki da sunan
ya mace) gabana ya fadi hantar cikina ta kada, nana take sat naji
ini na daukata.
Na samu na ja da baya na mike da tangadina, na dinga ja da
baya, manufar hakan da nayi, shine in samu in gudu fiskar nan tasa
ba wani annun.
Nan take naji na tsini kaina, naji Allah wadarai da rayuwata,
nayi dana kafewa da na yi akan abinda ya nuna mani tun farko
baya so.
GGumi da sassarfar ja da baya, shi na dingayi a lokaci daya,
ganin ya cire rigar shan iskanshi ya wúrga saman kujera, shi ya
kara tsoratani, na juya a guje ina ihun azo a ceceni.
Hankalina ya kara tashi da na isa ga kofa najita a kulle, nayinayi taki budewa, ina cikin haka ya matso dab dani, na samu na
goce na ruga jikin tagogın gidan amma ko motsi basuyi ba.
Falon gidan Mustapha sai da na zagaya shi kaf; amma ban
samu mali a ba, ina ganin ga ni yayi na rikice, gashi zan bela
mashi lokaci, sai naga ya biyoni a gujc, wata fizga da yayi mani ya
hadani da bago ita tayi dai dai da wani rin ihu da na saki.
Wanda bai razana kowa ba sai ni da nayi kayana shi kuwa
idanuwanshi ma sun kada sunyi jajir, ya karaso ya hadani da
bango ya aitsi,gam, hakan ya yi dai dai da dago kaina da yayi ya
nufo bakina a day dai lokacin ni kuma naji karli ya zo mani, na
daddage na tureshi, na ruga.
Amma sai yasa kafarshi ya tadeni sai gani kasa wanwar, ina
jinsa, ya janyo kafaluna, wanda ni kuma hakan tayi, dai dai da
innalillahi wa inna ilaihir raji'un da na fada, tare da cewa, "na zabi
kashewar ka kasheni ina son kashewar."
Tsawa ya daka mani tare da niyar hayc ruwan.
Alhamdulillabi
Mu hadu a kashi na biyu.
Banyi littafin nan da sunan wani ko wata ba, ko wata manula
daban, nayi shine domin nuna girman alkawali da amana a
78
al'umna, ko ince yanda al'umma yanzu ta daukesu ahokan
wasanla
Saboda cin amana yanzu, ba'a daukeshi a bakin komai ba, karya alkawali kuwa, yanzu tamkar cin abinci ne, na zauna nayi
tunanin naga ba wata hanyar mafi girma da zan nunawa al'ummar
musulmi girman alkawali da amana, wacce zata girgizamu mu
koma ga Allah, sai ta wannan hanyar, Allah yasa mu gane amin.
Tarc da fadakarwa ga iyaye mata da maza, akan su dinga
kula da 'yayansu mata, su daina ganin sun girma ba wani abun da
zai iya faruwa a garesu, to wannan babban kuskurene, kulawa da
duk wani taku, ko maganar da zasuyi, shi zai tabbatar mana da
gaskiyar duk wata magana da zasu yi mana.
Sannan mu sani duk gaskiyar yaranmu da kwai inda zasu iya yi mana karya fa, saboda haka, a kula, iyayena mata, ko mai
girman 'yayanmu kuwa, "sannan da su yammatan kansu, ku dinga
hakuri, kuna jiran lokacin da Allah zai kawo maku mijin auranku
amma ba ku dinga wulakanta darajjarku ba, ga taryar mazan waje
kuma cewa kuna sansu, ku sani wannan zubarwa iyayenku
mutunci kukayi, da ku ka nku.
Ku sani Allah bai hıllicemu ba mu yan adam sai da ya halitta
mana abukan zaman mu, wala namiji wala mace, sai dai wadanda
ya halitto akan, su zo duniya su koma, ba tare da ya kadda masu
yin aure ba, saboda haka in muka jira, Allah zai kawo mana
mijinmu, komai dadewar da zamuyi.
Sannan sai iyaye, dan Allah su daina takurawa yara wai kan
basu fito da mijiba, mu tuna, komai kin auran da yarinya keyi, to
in mijinta ya zo, ko bata so, sai fa anyi, Allah ya bamu hakuri jure
jiran hakan.
Sai su 'yan mata, ku sani, duk wata soyayyar jin dadi da za
kuyi da namijji, to ta aikin banzace sai in mijinki ne, ku tsaya kuji
abinda baku sani ba, abin kuwa shine, kuna ragewa kanaku tsayin
amarci, da zakuwar so da kauna, in kunyi aure, saboda kuwa yalole dan dumin jikin naki tuna waje, a kiyaye, kada kuga mun dage da rubutawa kuma kuyi tunanin haka ake soyayya, a'a muna
rubutawa ne, domin kara armashin rubutun mu. a kiyaye, na gode.
Mai Kaunarku Anty Maryam 79
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels