bakin garin
zaka tsaya cak saboda sai kayi tunanin kyawawa duk sun kare sai a
garin Masari kawai, saboda kyawawan fuskokin da zasu yi maka
sannu da zuwa.
Kada kayi tunanin matansu zalla, mazan garin da yaransu duk
haka suke in kuwa kaga baki a garin samoshi akayi, ko kuma
mahaifiyarshi aka auro wani gari ko taje ta auri na waje. kokannina
wajen uwa sun rasu sai dai 'yan uwanta da kuma dangin
mahaifinta, amma kakannina na wajan uba suna nan da ransu,
wanda Yakubu shine sunan kakanmu da matarsa Adama, sai kuma
kishiyoyinta har biyu.
12
'Yaya kuwa kakarmu ta uba nada biyar, duk kannan Daddy
ne, mata biyu maza biyu, Hassana da Usaina ke bi masu, sai
Aminu sai Tanimu na karshe. Mahaifiyata kuwa su biyu ne kacal
itace babba, sai kanwarta Kilishi sai kuwa 'yan uba da dama.
Bashira sunan mahaifiyata kenan, yaya Usman ne babbanmu,
sai ni Hamida, sai kanwarmu Aina'u. yaya Usman yanzu haka
yana karatu a Spain, yana dauko digiridinsa na biyu duk da nasan
ya dan girme mani sosai, saboda sai da ya shekara biyar tukuna
aka haifeni yana karanta Water Enginering. Kanwata kuwa yanzu
ajinta biyar a primary.
Ni kuwa nayi Girls College abuja, gashi yanzu ina karatun
digiri akan (Home economics) watau akan harkar girke girke, duk
da yanzu shekaruna goma sha tara kenan aduniya.
Alhaji Haruna Masari (Minister) minista ne a ma'aikatar
hulda da kasashen waje. Ba laifi alhamdulillahi Daddy yana da
rufin asirin arziki, hakan yasa ya gina gidan kanshi a unguwar
'maitama'.
Bai dace in bayyana irin kyawo na ba, sai dai in jira jama'a
su bayyana maku amma duk da haka zan iya kiran kaina fara mai
dan siririn hanci ga tsin, karamin bakina ya biyo bayan hancina.
'yar gajeriya habata ita ta biyo bayansu.
In ka daga kanka sama kuwa zaka ga idanuwa fararan gaske
anma fa akwai kwayar ido, wacce zan iyacewa ta kawata fuskata,
irin kyawan habata yasa na zama zan iyacewà ta kawata jama'a,
sannan da gani kasan fulani ne na asali. lakan yasa in ka wuce
idanuwana zaka iya ganin gashin saman idona kamar anyi caka da
na kanti.
Girar saman idanuwana kuwa tamkar irin layin jagira babba.
samanta kuwa bakin gashine a kwance, saman kaina kuwa zamu
iya kiranshi irin gashin kowace mace, amma sai shi kuwa yayi
Isayi tamkar jilar sa wacce ta kwanta bayanshi, hakan yasa nikan
hadashi in daure kayana, dama kuma gani mace maison kitso, sai
dai kam 'yan kanti gyaran gashi suna samun aikin gashina saboda
kullum kafata na wajan su.
Wankewa duk sati yin shamfo kuwa wata dayane, inkuwa na
gota bai li sati ba, ko kwana goma. in kuma ka dawo da idanka
kasan wuyana, alhamdulillah, komai yayi amma fa banda tsiya,
13
inka kalleni daga sama har kasa zaka iya ganin cikakkiyar mace,
'yar doguwa mai dirin gaske, sufar kwanciyar farce na, kamar
tsayin farcan kanti, damma ya zamana gida an hanani tara farce,
tunda na gama makaranta.
Ragowar bayanina kuwa kayi dariya kawai irin dariyar nanU IR
sabon farin ciki wanda baka fi minti daya da samun labarinsa ba.
*** ***
Wai me ke shiri faruwane a kaina? Saboda tunanin alkawarin
da na daukarwa Halimatu ya na damar mani zuciya, tun daga ranar
kuwa har yau lahadinnan bana samun barci sosai, saboda sallolin
tsakiyar dare da na dorawa kaina su, na Allah ya taimaka mani in
cika alkawarin Halimatu, amma gani yau har kwana ashirin da
aganarmu, amma ban samu ko labarin hanyar da zanbi in ga
lustapha ba, balle in ce zan fara sauke nauyin da ke kaina.
tar Daddy na samu na dan tambayarshi akan Mustapha
amma sai yace mani shi kanshi ba zai iya fadar taka maimai inda
za'a samu Mustapha ba, saboda shi ba mazauni bane so sai. in
ma yana gar, to ofishin nashi ma suna da yawa.
Ni kuwa a nawa tunanin ganin nike bai dace ina 'ya mace in
afi gidan Mustapha nemanshi ba saboda ina son mutuncina nima,
tunanin hakan da nike yi yasa Aina'u ta dinga sallama banji ba, har
sai da takai ga shigowa ta dan tabani, aunty kije inji mama.
Ban tsaya sauraron komai ba na mike na bi Abashiyya.
Maman na samu a falo na isa gabanta na zaina tare da dura
hannyena akan cinyoyinta, ganin mama, "wai ke yaushe zaki
girmaner, ke dai kullum ki kwanta jikin mutum kamar mage, ni
dagani dan Allah ko in turcki, kai mama nice fa" maman tayi
dariya.
To tashi ki gano mani kofar gida ko da dircbobi ki zo zan
aike ki nasan yanzu yamma tayi ta yiyyu ko direbobin sun tashi
aiki,"na mike na nuli kofar fita amma ban samu direba ko daya
ba, har mai gadi naje na tambaya amma sai yace mani duk sun tati.
Na dawo falo na sanarwa Mamana, tayi shiru, da alama aiken
nata yana.da mahimmanci a gareta, "mama in ja mana in tafi,
yanzu na dawo kafin Daddy ya dawo," "a'a, karki janyo mani
14
fada, kina sane dai ya hanki tuki, to balle yanzu yamna tayi kuje
ku hade a hanya ince me, dama da safe ne, har ki dawo, amma
yanzu ina, lokaci ya kure,
"To in shiga tasi mana," a'a sai dai ki shiga bos, saboda kin
ga yamma tayi tasi din nan tsoronta nikc, gara dai bos cikin jama'a
ne, karki dadfe dan Allah, zan aikeki gidan Hajiya Mabaruka.
Dauko mayafinki ko," na wuce sai dakina,
A yanda garin yayi kyau, samaniyar, garin ta fitarda wani
yanayi mai kara sa dan adam ya jishi cikin nishadi, ga iskan
damana yana kadawa a hankali mai ratsa jiki cikin kwanciyar
hankali, na kalli agogon hannuta a dai dai lakacin da nike tafiya
bayan na sauka daga bos, karfe biyar da minti sha shidda.
Na samu na tsallaka titi, na shiga hanyar unguwar Zone 4:
korayen ganyayyakin shukakkun fulawa da na ratsa sai rausayawa
suke yi a hankali, da alama ko suma bishiyoyin suna jin dadin
iskan da yake kadawa a wannan yanayi, ga,tafiya nike a natse,
saboda sashen da nike tafiyar ba wasu mutane, sai dai daya da ke
geftawa.
2
Ba wasu kaya bane a jikina illa atamfa yar ingila budadden
dinkine sai kawai naji na tsinci kaina da tunani kala-kala, wani
inyi murmushi wani kuwa inyi tsoki, "sannu maļama," naji ance
bayana, gabana naji ya fadi, hakan da naji yasa ban waigaba
ballantana ta kaini ga tsayawa, sannan yanda na nuna ma kamar
banji abinda ake fada ba.
Me naji an ambata? Wai Hamida, rugawa zanyi ko kuma insa
ihu kawai? Amma sai naji zuciyata tace mani kada kiyi ko daya ki
juya kawai kiga ko waye ni kuwa har da wani dakewa, wai ni a
nufina ban tsorata ba,
Kamar wani biri na ji ya dirar mani a kai dai daı lokacin da
na juya, saboda ganin aljanin mutame da nayi a tsaye yana dan
alamar murmushi kumatu, duk da wando da rigane irin namu na
hausawa watau kufta da wando na ruwan kasan bayaga bakin
gilashin fuskarsa, amma hakan bai hana inga gashin kanshi ba
kaınar gashin kan turawa saboda ba hula a kanshi.
Alamun haka da na gani ya kara tabbatar mani cewa aljani
nayi gamo dashi ba dai mutum ba wannan kyawan fiskartashi, duk
da gilashio ya rufe wani bangare a fiskarsa, amma da ganin kasan
15
ba kyawan dan adam bane, to balle inn wannan bakrl da
kyau haka, sai Baba Aljani.
Ya fitar da gılashin fiskarsa a lokacinda munmishin tiskarshu
ya karu, cikina ya kara juyawa yayi wanı kuka mai kama da kukan
in gudawa ta riskeka a motar haya ba kuma datnar tsayawa kayi
"Hamida baki gane ni ba ko?" kallanshi da na tsayar da idona
nayi sosai, shi ya dan so ya tuno mani in da na taba ganin aljanar
fiskarshi, ya sunkuyar da kai alamar jimami, na Kara dalle
idanuwana na Kura mashi ido, cikin sakan goma sha takwas na
gano fiskar da Babban katin hoton ta ke falon Daddy na.
Nayi sauri na tsuguna, "dan Allah yallatai kayi hakuri
wallahi a farko ban gane ka ba, ina yini kayi hakuri yallabai,
Kanshin turaran da naji dai dai hancinsa shi yasa na dago kaina
nayi saurin kawar da fiskata, saboda hada ido da na miji kamar
wannan, faduwar gaban matane, balle ni da nasan ba samun irat
shi zanyi ba,
Ni ya kamata in tsuguna in gaishcki Hamida kiyi hakuri
rashin hankali nayi Babba, amma gaba ba zan maimaita hakan ba
"a'a ni ya cancanci in gaisheka yallabai, saboda nice kasa da kai,"
nafada a dai dai lok acin da na mike tsaye saboda tsugunniyar sa da
tayi kusa dani soasi.
"Amma in baki manta ba, kinsan mata na da darajja ta
musamman wacce Allah yayi masu, tunda kinsan kuke haihuwar
mu, hakan yasa ni Mustapha ni ke ganin ba wanda ya cancanci in
girmama irin mace, ina fatan kinsan labarina a bakin mutanan
gari? In kuwa baki sani, ba zan fan gaya maki kadan yanzu.
Kinsan dai bani da kowa a Nigeria, ko ince a duniya ma,
wańda ya wuce mahaifiyata, ita kadai nake takama da ita, saboda
haka, dolene in ga darajjar kowace mace a duniya, ko nayi kuskure
ne? nace masa "a'a, amma yanda kuke manyanmu, kamata yavi
ace kun hakura mu yara mu cigaba da gaisheku, ko ya ka gani?
Yayi munnushi ya mike tsaye, "Ilamida abar wannan
maganar, akanta yanzu sai muyi mahawara dake mai tsayi, in kina
so muyita, ki jira lokaci kalilan, zamuyita atsanake, yanzu dai ina
zaki haka, a kafa?, ko da yake na lura dake ba ruwanki da takanmar
nan ta 'ya'yan masu fada aji, tun da ana yawan kai mani labarin
cewar an ganki a kasa, kwanakin baya ma, na ganki da wata tsaye
16
a baki titi, da safe wajan bakwai da rabi, amma ina jin makaranta
zaku a lokacin ko?"
Nayi mumushi nace masa, ta yiyyu, yanzu ma kuma da ka
gannı, Mamana ce ta aikeni, nan ciki," "ina direbobin gidan naku?,
"sun tashi daga aiki da yau da wure shi yasa," "amna fa babban
hadarine a dinga barinki kina fita ke kadai haka, don Allah daga
yau ki daina, bana so, ina jin haushin haka,"" in sha Allahu na
daina"
Ba maganar da ke zuciyata tunda na gane Mustapfa, sai
maganar Halimatu, hakan yasa nayi godiya ga Allah da ya kawo
mani Mustapha har gabana a yau, amma tun farko sai naji ba zan
iya yi mashi maganar ba, ganin yanzu na lura da mutum ne mai
saukin kai, sai naji zuciyata ta aiyano mani in yi mashi maganarta,
"Hamida kwana da yawa?, "mhm' kawai na iya cewa, kai a
sunkuye, 'nayi tunanin ko zaki nemeni ko a waya ne, kiyi mani
godiya, ta musamman akan abinda kika gani a ambulan dinki
shekaru biyu da su ka wuce, amma naji shiru, ko kuwa kayan
nawa basu baki mamaki ba ne?," bance komai ba, shima kuwa
naga alamar yalura daba abinda na aiyana a zuciyata, hakan yasa
naji ya cigaba da maganar shi "ni kuwa tun lokacin nike ta
Kokarin inga mun kara haduwa, amma Allah baiyi ba sai yau.
Saboda duk inda zan ganki, to cikin mutane ne, ni kuma
kinsan shigata cikin mutane, ba zai mani dadi ba, kuma sai nayi
nıyyar ballawa gidanku, sai wari abu ya taso mani na gaggawa,
yau ma Allah neya Kaddara haduwar mu, saboda har munwuce
akayi mani waya cewa, gaki nan kin sauko a bos, shine nayi
umurnina dawo dani baya, Allah kuwa ya bani sa'a na sami ki ke
kadai."
Nayi dan murmushi, "ki kayi murmushi, ko baki amince da
maganata bane? "a'a na maince, nima mamakin ganin ka kai
daya nayi yanzu,"waya gaya maki ni kadai nike, zagaye nike da
jama a, ko kina son ganin su?" "nace a'a, na gode
Gashi na fahimci sauri kike, ni kuma ina dauke da
maganganu, bama magana ba, to ya kenan?, ko in bullo gidan ku
ne yau da dare?" "ni ma kuwa kasan ina da mganganu, anuna ni
neman wata alfarma zanyi garcka, Allah yasa ta samu shiga a
wajanka, ka san ku manya,"
17
"Hamıda kenan, tsakanına da ke wave babba?, kar da n
neman agarcka?" "amma dai kin san dat ke ce babba, "anм
kuma ni ke neman alfarma a gareki, ko da vake kada in katsıkı.
Kara na barki kinyita amma maganarki ki sant Harmda, duk
duniyar nan, ba abinda zaki nema a gare ni inu ba zan iya baki ha.
sai dai in ya kasance ba mallaki na bane, in kuwa har ana siyar da
shi, zanyi amfani da dan abinda Allah ya hore mani in siya makı,
ko da kuwa zan koma yawo da riga daya nc.
in kuwa rai nane, abu ma mai sauki kenan,"nayi saurin dago
kai, "kina shakku ne?" "na isa, mamaki ne va kama ni "ki cire
duk wani mamaki, yanzu dai ya zamuyi mu hafu, ko in zo gidan
naku ne da yamar?" "a'a gidanmu fada za'ayi mani, tunda Daddy
ya hana namiji yazo waje na yace sai na gama karatuna, kaga
kuwa in kaje, za'a tambayeni kai waye?"
"To meye, ba sai kice masu ni Mustapha ne, kuma nazo
neman alfarmar a mallaka mani Uamida ne a matsayin abokiyar
rayuwata in kuma ke ba zaki iya fada ba, in na zo ni na gayawa
Daddy din,"
"Innalillahi wa it na ilaihr raji'un" na fada a cikin zuciyata,
wacce ta fito tare da laduwar gaba, a take kuma ta aiyano mant
halin da Halimatu zata shiga, in har ta samu labarin Mustapha yazo
gidan mu.
"Kinyi shiru, ko ban samu karbuwa ba a zuciyarki?," han
nuna fargabata,ba fili, sai na dan dake," yallafai sai ma naj
kunyar ka ta kamani, saboda a nawa tunanin ina jin nauyin kamar
ka ka nemı wani abu z wajena in hanaka, koda kuwa ace bani da
shi zan iya iyakar kokari in satmar maka shi, to balle nu gaba dayа
na, amma ina fata kalmar da zan gaya maka, ba zata zamo
sanadiyyar bacin ranka ba, in kuwa kadan ji sosuwa a zuciyar ka.
ina mai neman afuwa agarcka,
Dan Allah kayi hakuri yallabai ni anyt mani nyi, ko in ce
nayi alkawalin aure da wani, anma in fatan wannan ba zata ruguza
zumuncin da nike son inga ya karfala a tsakanin mu ba, ko
haduwar da nike so muyi yanzu,
Mutum natsatsan gaske, dan haka ko nuna alamu wata
magana ta fito daga bakina ma bai yi ba, balle ta kai ga sashi ya
rude, sai dai dan murnushin Kasan kumatu da na lura yanayi.
18
"naji dadin maganarki Hamida, amma fa ki sani, ni Mustapha
na riga nasan ke ko wacece, nasan me ke tafiya a gidan ku, amna duk da haka ni ma ina son kamar yarda kika roki a cigaba da zumunci, to nima ina son haka, tare da zaba mana inda zan sameki
domin ki gaya mani alfarmar da ki kayi niyar fada mani,saboda gaggauta yi maki ita, ko dan zumuncin da ya fara shiga tsakaninmu
a yanzu.
"gaskiya bani da wani wajan zuwa, sai dai kai ka zaba mana,
amma fa banda gidanka," yayi yar dariya irin ta manyan," zaki yarda da zabina kuwa?" "zan yarda mana, yasa hannu a aljihu ya dauko wani kati, "ga wannan ki sameni a naicon Hotel," "haba yallabai, ina ni ina zuwa Naicon kamar wata karuwam ka dai sake waje,"
Ya dago yayi mani kallan gefan ido, "amma fa Hamida kin yi
mani mummunar fahimta, ko kin ganin nayi maki kama da mai ajiye karuwa ne?" "ba haka nike nufi ba " "haka ne
mana, ni kuma dalilin ce maki mu hadu a can, shine dan naga waje
ne na jama'a sannan ban ambata maki cewa ki sameni wani daki
ba a hotel din, sannan kuma ki tunı ke ki ka yi mani kashedin
cewa banda gida na, ban da naku, tc ina zan kaiki kuma in kuma, kin amince muje gidan mahaifiyata."
Nayi saurin kama baki, "ka rufa mani asiri don Allah, so kake
tace mani 'yar iska," "Hamida ni fa tsaya in gaya maki, ba wanda
zai ganni dake garin nan yayi mani zargin ke wata abuce wajena,
sai dai yace mani wacce zan aura," "shikenan naji, kamar wacce
rana kenan zan zo?" "anjima," "yayi kusa, sai dai ko nan da sati
daya," "ba zan iya ba a rage kwanaki" "kwana biyar," "mutuwar
kenan," "mutuwa?" "of course," "kinsan dai yanzu tunda mun fara
hada zumunci daga yau, ba zan iya daukar lokaci mai tsayi ban
ganki ba,
Ki yar da gobe to, karfe goma na safe," "bai yi safiya ba?"
"saboda ke nace haka, domin da yamma jama'a za sunyi yawa а
wajan, da safe kuwa, ba mutane sosai, ko ya kika gani aminiyata,"
"na danyi murmushi, "shikenan sai goban in sha Allahu zanzo,
amına ko zuwa sha daya ne zaka ganni, ka sanmu mata da aikin
safe," "to shikenan" 19
Amma da kinzo get din ki nuna wannan katin, guda kada ki
dan girgiza da nasa an taryoki, ko da yake ma bana son in jeda
kowa, gudun surutun su, kada suji har Hajiya taji, nayi murmushi
"to sai nazo," yasa hannu a aljihu ya dauko wani dan karamin
akwati, "ga wannan ko dan zumunciu ko," "haba tun yanzu?" "sai
yaushe, ai zumunci ya fara tun daga mintunan da suka wuce: to
ajiye mani sai gobe, "nazo" "to shi kenan Allah ya kaimu,kin gansu
nan yayi shekaru a hannu na dan kwana daya ai mai sauki ne.
Mu kayi sallama na juya na tafi, ban fi minti biyu da fara
tafiya ba, sai naji gudun motoci a kusa dani, na tsaya na waigo, sai
naga motocin nan da muke gani a titi suna wucewa, ina kallo suka
fito da sauri suka bude wa Mustapha kofa, har ya sunkuya zai
shiga, sai naga ya dago kai, yayi mani murmushi, tare da daga
mani hannu.
Ban mayar masa ba, ya sunkuya ya shiga, har sun zo
wucewa, naga gilashi na sauka a hankali, sai na ganshi ya dan leko
kadan, tare da fadar wata kallama a hankali, wacce tayi mani
kamar yace (Ilove you), amma ban tabbatar ba, suka ja motocin su
sukayi gaba.
Ina komawa gida safon mamana kawai na bata na shige
dakin na bugawa Halimatu waya, nayi mata albishir da naga
Mustapha har ma nayi magana dashi, amma ina son gobe ta tanadi
goron albishir dinta, domin zan zo mata da kyakkywan labari da
ihun murnar ta" "tace sai nazo, da kyar kuwa na samu mukayi
sallama da ita,saboda ta tsareni sai na bata labarin Mustapha.
Asubar fari na mike nayi alwala na dinga lazimi da nafila
kafin ayi kiran asalatu, addu'a Allah ya bani sa'a ita na dingayi
bayan na gama sallah asuba.
Karfe tara na safe bayan na gama komai na gidanmu, duk da
ba wani aikin kirki nike yi ba, saboda masu aikin da mike da su a
gida, amma nasan nikan gyarawa Mamana dakinta da bandakinta,
haka ma nawa dakin, wani lokaci kuma nike gyara sashen Daddy.
Nayi wanka na gyara jikina, amma har lokacin ban samu
wata dabarar da zanyi in fita ba, ina zaune ina tunanin hanyoyi
kala-kala, amma ko wace hanya na zuba a fai fai na tsince, sai inga
batayi ba, ma'ana za'a gane ni a gida ina cikin kule kullena sai
20
wayar dakina tayi kara, ina dubawa sai naga sunana a jikin wayar,
hakan ya tabbatar mani ni akayiwa waya,
Da saurina na dauki waya, a tunanin na ko Mustapha ne duk
da nasan ban bashi nambar wayar gidan mu ba, "Yauwa Halimatu,
dama cikin tunani nike akan yarda za'ayi in fita, abinda nike so
kiyi mani yanzu shine zan cewa Mamana kece kika bugo waya ki
kace mamarki na kira na in rakata unguwa, dan haka in aka zo
nema na gidan ku kisan yarda za'ayi ki kareni kema, kin san fa
tunda zamu fara aiki, dole ne sai kin hada da taimaka mani ni
kuma zanyi kokari in dawo da wuri."
"To shikenan Allah ya taimaka, ko in zo mu tafi tare?" "a'a,
ba yau ba, sai mun samu shiga ko?" mu kayi sallama da ita da
sunan in na gama zan biyo ta gidansu
Mamata na samu a dakinta na zauna tare da gaya mata sako
mamarsu lalimatu, na hada da tace kuma in tafi da Motata da ita
zaıu tafi, Mamana tayi shiru, "kin dai san Daddyn ki ya hanaki
tuki ko?" "Mamana na sani, kinga yanzu ma ai ba laifina bane,"
"to shikenan jeki kishirya, bani in gayawa Alhajin, in ya anuince
to, in yaki sai ku tafi da dircba,"
Kai mama kika sani ko abin asirire, tunda kika ji tace ni,
kinsan dai gidan Mamy ba za'a rasa direna ba, ke dai mama kiyi
kokari ya bari dan Alah," "to je ki ki shirya ina zuwa
("Cotton) lace kwatin lasn fink mai hade da ratsin ruwan,
Kasa na saka a jikina, da takalma na suma masu ruwan kasa, masu
suna (How are you beby) tare da jakarsa, mayafi fink mai suna (1
go to London) ita kanta rigar'yar budaddiyace ma iya kiranta da
suna (iam okey)
Na gyara gashina na daure tare da sakin shi bayana, na mayar
da mayalina na rufe shi, tare da dan goga turaran, Home sweet
home" a kayana, durowata na janyo na dauki yan kudi na zuba.
gudun faruwar wani abu a hanya.
Ina fita Mamana na shiga dakinta, na shigo na zauna gefenta.
"mama na shirya, ba tare data bani amsaba, ta janyo durowa ta
miko mani makullin tare da 1,00 wai in rike in ji Daddy saboda
matsalar mai, da murnata na karba nayi waje.
Mota honda civic na karya kwanar ta zuwa get din hotal din
naicon, ina isa na mikawa masu gadin get din katin da Mustapha
21
ya bani, "okey madam he is inside waitin foryou" ma'anar abinda daya daga cikin mai gadin ya fafa shine, yana ciki yana jira na, na
amsa da "okey thanks) ni ma,
Rumfar ajiyc motocin hotal din na nufa kaina tsaye, na je na faka tawa motar, tunani daya ya fado mani, shinc ina zanga Mustapha yanzu, Amma duk da haka wannan tunanin bai hanani kashe motata ba, na zuge gilassanta,tare da yunkurin fita daga
motar, abinda zuciyata ta bani amsa kuwa, shine in je (reception) in tambaya, wata kilan na samu wanda zai nuna mani shi Hakan yasa na fito tare da kulle motata, na cigaba da tafiya tamkar wacc bata san taka kasa, yan tsirarin mutanen da ke harabar
kuwa, kallabu duk sai yadawo a kaina, sam banji komai ba, saboda
da sabo da jama'a da yaba a makaranta
Sam ban mayar da hankalina wajan kalle kalle ba, saboda
gudun kada a daukeni ba kauya, "sannu da isowa" naji an fada a
baya na, ban waiga ba, balle in kai ga amsawa, ko wata alamar
tsayawa," nayi zaton ba zaki zo ba," nan take sai naji na gane
muryar da tayi mani magana, hakan yasa na mayar da amsa kawai,
ba tare da na juya ba,
"Nayi maka kama da masu karya alkawaline?" "ni na isa in
fadawa gimbiya wannan maganar," ban mayar mashi da amsaba,
sai ma jerawa yayi muka cigaba da tafiya, kujeru biyu da tibir a
tsakiyar su muka nufa, amma kujeru ba irin wanda naga sauran
jama'a na zaune bane ba,su sunfi kama da zubin sarakuna, nan
take nace a zuciyata, abun manya sai manya yaro kuwa sai dai ya
dora hannu akai ya sha kallo.
Sai da ya janyo mani kujera na zauna, tukuna, ya zagaya ya ja
tasa ya zauna shima, a lokacin ne idona yaga shudiyar shadda
kubta sanye a jikinshi, amma kanshi ba zancen hula, agogon dake
hannunshi, ita ta kayata silim hannunshi ya haska saman tabirin da
ya dura hannun na shi
"Ina kwana yallabai?"" lafiya, amma fa ba kalau ba," me ya
faru kenan?," "kamata yayi ki tambayi yana kwana jiya," "nasan
ka kwana lafiya, tunda ga ka gabana ayanzu," ya dan kawar da
kai,"to naji,amma dan ya zamana ba zan iya yi maki gardama ba,
da sai in ce maki, karfin hali nayi na zo maki yanzu."
22
Na danyı murmushi, kamanta abinda ya hadamu wajan nan
ne?" nayi haka ne saboda gudun jan doguwar magana "na isa in
manta Hamida, ko me kike tunanin, nima yana zuciyata, Amma
saboda ke ce Babba, ina son ki fara fadar taki maganar," haka tayi
dai dai da daga kwalin lemo da yayi ya tsiyaya mana, a kofunan,
na daga nawa na dan kurba kadan na ajiye.
"Yallabai ina mai bakin cikin gaya maka maganar da zata
fito bakina, amma in har ka karbeta da hannu biyu, to ka tabbata
nafi kowa farin ciki a duniyar nan, yallabai ba abinda zakayi mani
ka nuna mani kai musulmi ne dan uwana, kuma mai jin kan
alumma, to balle ni mace wanda da bakin ka kace kana girmama
mata nayi farin cikin da ka furta wannan maganar da bakin ka,
Saboda sai tayi dai dai da mace tazo neman alfarma a gareka
ina fatan ba zan samu wukanciba ko an fiska, ko rushewar
zumuncin da ya kullu a tsakaninmu sannan don Allah ina nemana
alfarmar da cewa ko da maganata zata bata maka rai, ka yafe ni,
kuma kayi hakuri ka tsaya mu tattauna cikin natsuwa, kamar yarda
muka fara yanzu,"
Ya dauki kofin lemonsa ya kurba, sannan ya dago ya
kalleni," "ina sauraranki Hamida,"ba wani abu da zan iya hanaki a
duniyar nan, ki sani, komai nawa ya zama nakı dama tun shckaru
da dama da suka wuce saboda haka, ki daina shakkun fada mani
abinda ke cikin zuciyarki.
Kinsan nima fa zan nemi alfarmar gareki, saooda haka, imani
in maka zamuyi da ke, dan haka bismilla."
"Yallabai dama zuwa nayi gareka akan wata matsala da ta
damar mani zuciya, ina ga in ba kai ba, ba wanda zan samu ya
taimaka mani ya karbe kukana, in kuwa ka taimaka mani zaka
sameni mai yawaita yi maka addu'a har ina mutu," "kada kiji
komai Hamida, fadi ina jinki, tare da baki cikakken lokaci."
"Yallabai, wata yaya, Aminiyata, kawata ce ta dade tana son
ka da aure, yau wajan shekara hudu kenan, ganin yarda muke tare
kullum, naga yarda take wahala a kanka, alhalin kai baka san
tanayi ba, shine na daukar mata alkawarin zan hadaku kuyi aure,
domin samun lada gareni, gashi a iya nawa binciken, na binkito
cewa kai mutum ne mai jinkai da tausayin al'umma gashi ance
23
mani baka san ganin wani a