gashi wainar shinkafa da wata
irin miya mai dadin gaske, ni kaina nayi mamaki ace kamar
Mustapha da yake ba cikakken dan kasa ba, amma ya iya ci waina.
Nay sauri na bude jakata na zazzgo fauda na shafa a fisk ta,
gudun ka la a gane nayi kuka, yayi sallama ya shigo ya zama
kujerar tibirin cin abinci wacce ke kallona.
"Alhamdulillahi, mun gama lafiya, sai muyi magana mai
kyau bismilla," "na riga na gaya maka komai kenan tun dazu, sai
dai tunda ka nemi in karayi maka bayani, zan iya kara yi maka, ni
Hamida nazo neman alfarmar a wajanka na ka auri aminiyata
Halimatu, Halimatu, aminiyatace, tare mukayi Primary tare
mukayi sakandire anan Abuja.
Zumuncin da ke tsakanina da Halimatu yasa va koma
zumunci na tsakanin iyaye da iyaye, har ya zamana yazu zumuncin
iyayen mu yayi karli sosai, ba dan komai ba saboda mahaifin
Halimatu dan kasuwa ne, hakan yasa Daddy ya kutsashi a harkar
gwamnati, yana kawo kayayyaki daga Kasashen waje.gwamnati na
biyanshi.
In ba na gaya maka ba, ba zaki taba tunanin ciwa zamunci ne
kawai ya hadamu ba, sai dai kace diyar wa da diyar kane, Na
daukarwa Halimatu alkawalin zan hada ku kuyi aure, saboda halin
da naga tana shiga a kan sonka, in kuma ka karbl wannan taimako
33
da na nema a garcka, zanfi kowa farin ciki a duniya, nagama
dai in da tambaya ko kana nerman karin bayani, zaka iya yi a shirye
nike in baka amsa duk wata tambayarka."
"Naji bukatar ki, Hamida, arnma kuma sai kika same tawa
bukatar sabanin taki, saboda nima na samu kaina cikin son auranki
yau shekara biyar kenan, tun a lokacin kina yar aji uku.
ka Na ganki ne a wajan wani fati nc da aka gaiyaceni naji,
kuwa ince dinner,dina ta manyan mutane, ban taba tunanin zanga
yara a wajan ba, amma sai kawai na ganki kun shigo tare da
mamanki, da aka gama taron nasa aka bincikita mani, sai aka c
mani ke yar Haruna masari ce, a lokacin yana a(G.M) awan
kamfani ya aiki.
*** ***
Tun daga lokacin Hamida nasa ake gadinki, duk inda kafark
ta taka, to ki tabbatar da yarana suna biye da ke, domin gudun kad
wani ya rigani, tun a łokacin baki taba fita daga cikin zuciyata be
sai dai naki nuna kai nane a lokacin, saboda ganin ki yariny
arama.
Duk wata tsarewa da kika ga malamai nayi maki a makarant
suce maki (Extra lesson) za suyi maki, nine nan nake biya ar
koyar dake, ina son kiyi tunani akaina ni ma ki tuna yarda kil
tunani wacca yarinyar zata shiga wani hali nima haka zan iy
shiga, yarda kike tunani tausaya mata, kamata yayi nima ki tausay
ınani,
"Yallabai ka tuna girman alkawari, ba zan taba yarda
karya mata alkawari ba, ni dai har yanzu ina nema alfarmark
Yallabai Halimatu kykykyawace, ga gashi, fara ce itam
makaranta daya mukayi da ita, yanzun haka tare muke zuw
makaranta da ita
Halimatu ta fini hankali da natsuwa, mahaifin lalimatu y:
Daddy kudi, Halimatu. " Nayi shiru, saboda kar
hannuna da yayi wanda ke kan tebir ajiyc, ya daga kai yayi m
kallan kasan gira.
"Duk wannan bata daneni ba, Allah yasa ita aljanace sabe
kyau, ni ke nagani, ke kuma nike so, daga yau kada ki karayi m
maganar wata 'yarinya, in har ke kinsa bakya sona, ki gaya m
34
gaskiva kawat, in samu wata, mata da yawa a duniya, har sai na
Jira An zaba mani
Na janyc hannuna, na mike, ban tsaya jin wani karin dogon
surutu ba, na rataya jakata, tare da saka takalma na, domin
mayafina na akaina na neni hanyar fita, har na kai kofa na juyo Mustapha na zaunc a inda na barshi, ko juyowa bai yi ba.
A zuciyata nace tabdijam, yau na hadu da sarkin milki ga takama, ni da ya kamata inyi mashi yarda naga dama, amma shi ke
yi mani, na Itabtawa Halimatu ashar a zuciya, nace duk ita ta janyo mani wannan siyar da mutunci, nayi gaba abina.
Ni nasan ko da kudi aka hadani ba zan kara hawa wannan
abar ba, wacce nasawa suna liptar kasa, na kwammace in tafi a
kafa, duk da nasan da tafiya sosai kafin in isa kofar fita.
Tafiya nake, amma ko alamar kofar bangani ba,ni sai naji ma
tsoro tsoro ya fara kamani, saboda yarda wajen ke amsa takun
takalmana na, sunkuya na cire takalmana na rike a hannu, wata
zuciyar tace kin zama ba kauya.
Kukan wani abu naji a bayana, na tsaya na waiga banga kowa
ba, sai na karaji a gabana, nan take sai jikina ya kama rawa, saboda
sai naji kamaı kukan damisa naji, tafiya sosai a bayana, amma in
na waiga bana ganin komai,
Babu zancen tsayawa shawara, sai kawai na auna da gudu, sai
naji an biyoni, me zanji? wani abu ya gifta ta saman kaina,
innalilıahi, kuwa a bakina tafi dubu, har ya zamanto na koma salati
tafiya kiyama.
Mai zanji a bayana a lokacin da kafata ta kara tsayin zirin
gudun da take, sunana naji ana kira ana cewa kada ki karasa,
"Hamida kada ki karasa kofar nan, dawo baya, dawo baya, na
tsaya cak, amma na kasa waigawa, tsoro ma yasa na zame na
zauna jiran koma meye ya zo ya karasani in huta.
Ji nayi an tsugna kusa dani, "Hamida," na dago da sauri
zansa ihu, sai naga Mustapha tsugune, ban san lakacin da na
chukumeshi ba, ina kiran ka fitar dani, so kake ka kashe ni dama
nasan kai dan mafiyane.
Yasa hannu ya rufe bakina, "ke ke, ba komai, kasan da kika
lafi ya janyo haka, masu gadin wajan ne, ba,a tafiya kasa a wanan
wajan sai in tare da ni kike, sunyi zatan wani abu kika yi a ciki,
35
shine kikagudo," ya dago fiskata, kallarsu suna kallanki," na waiga
sai naga Aku da wani tsuntsu katu gaske, sai wani kata kare sai
wani zazzalo halshe yake, idanunshi kuwa kamar kwallan dan
kadanya saboda ja da ginna.
Baku bata hakuriba,' sai naji akun yana cewa, sorry, sorrу,
mama," shi kuwa dayan tsuntsun sai naga ya kawnta yana wani
kuka, kare kuwa ya daga hannayenshi sama yana zazzlo harshe,"
to ku tafi ta hakura kada ku karayi mata haka, ku kalleta sosai.
Sai naga ko wannanasu ya kuro mani ido, to ku tafi ya isa
haka nan, a kara bata hakuri suka kara yin irin na dazu su
dukkansu, tukuna suka juya, suka tafi,"ya tun tsire da dariya ya
lakaci hancina, "sarkin tsoro,yayanki ne fa, da kin kuskura kin kai
kofar fita harbeki za'ayi da kofar ta bude"
Na mike tsaye, ina mayar da numfashi sama sama,
"alkawali ko Hamida?" na harareshi, na juya zan tali, "na gaya
maki ba'a tafiya a kasa, sai in na bayar da izinin haka, na tsaya zo
mu bau na rikeki har mu kai," "ni ba zan hau ba, sai dai ka fada
cewa a kafa zan tafi."
"Naji zanyi maki duk abinda kika ce in yi maki am na nima
ina: on in kin koma gida kiyi shawara da zuciyar ki, da at niniyarki
ki janye maganarta" "ba zai taba yiyyuba,""to shikenan naji zanyi
shawara nima, ina bukatar nambar wayar ki."
Na bude jaka na dauko katin gidan mu na bashi, shima ya
mik mani nashi, "Complimentary card" talfon din hannu na ga ya
dauko daga aljihunsa, ina jinshi yana jaddadawa yaransa cewa
gamunan fitowa amma a kafa, ya kashi ya mayar aljihu.
Muna tafe, amma wai ni Mustapha zai jawa aji, sai wata irin
tafiya yake a hankali, ni kuwa bukata ta in fita in bar mashi
gidanshi, saboda hankalina ya tashi, akan gidan
Har zan fita, ya dan waigo ya kalleni, kisa takalmanki
mana," a lokacin nema na tuna ashe fa bani da takalmi a Kafata, na
kalleshi, wai tunanin ko zanga yayi yar dariya, anıma sai nagama
kallonshi ba a gareni yake ba, gefe daya kawai yake kallo, wani
haushi ya kamani, na sunkuya na saka takalmana, na mike kawai
da sunan in tafi
"Kamata yayi ace kin fita cikin natsuwa, saboda kare ginnan
ki a idon yarana, baki sani ba ko wata rana kece uwar dakinsu, in
36
kuwa bake bace, nasan zumunci zai hadamu tunda mun riga mun
hadu yanzu, kinga in kin zo nan gaba, zai kasance sun girnamaki,
kinga har abada raini ba zai shiga tsakaninku ba.
Amma fa ba dole, shawara ce na baki?" ya daga riga yasa
hannunshi a aljihu, ya tsaya daga gefe, tare da yi mani kallan da na
lassara kallan jan aji, watau kallan kasan gira, mai kama da za'a
lumshe ido
Muje mana kayi tsaye," "kin gama kintsawa?" nace masa
"I,' hakan da na fada yasa nayi gaba, yayi saurin janyoni," jirawa
zamuyi, ya kuma zamu kin saki fisakarki, alamar kina cikin farin
ciki, "na lizge hannuna, tare da sakar masa hararar wulakanci,
Yayi munnushi, "ba mamaki tunda yanzu kujera milki da
takama tana hannunki, in ma kina so, na hada maki da takobin
yakin zinari, sai muga wanda zai yaki wani tsakanina da ke," sai
ya cigaba da tafiva, dole tasa na bishi da sauri na jera da shi ina
yaken baki.
Kofa na budewa, gaba dayan kartin nan majiya karti, ga
bakaken kayan rashin mutunci sun saka a jikinsu, sai suka mike
tsaye da saurinsu, suka taho garemu, a cikin layi, wai gaisuwa suke
kawo mani,
Wani mugun haushi ya kamani, katin in isa ga motata kuwa
har an bude Kofofin gabanta, da yaken fara'ata na amsa masu
gaisuwa yan kudin da ke jakata, dubu uku ne na bude na mikawa
daya daga cikinsu, har da wata kankan bar basu hakuri wai ban
fito da kudi da yawa ba, sai kace su ke gareni,
Na fahimei wani daya daga cikinsu da gani shine dan gaban
goshin sa, ina kuma kyauta ta zatan shine shugabansu, saboda
ganin sun jero tare da Mustapha bayan na danyi gaba kadan, ganin
har murmushi yake, yasa nasan shine dan gaban goshin Mustapha.
Ni kuwa har na shiga mota na zauna, gudun kada in tayar in
tafi, su gane cewa bamu shiryaba da ogansu, yasa nayi sakato ina
jiran isowarshi,
Tare suka iso da wannan Katon, saboda ba zan kırashi yaro
ba, ina ji suka bude but din motata, suna yan surutaı, sannan suka
mayar suka rufe ya zagaya ya shiga gaban motata shima, katon ya
mayar da Kofa ya rufe ya zagayo ga tawa Kofar ya rufe (madam to
37
miji ki dinga surutu, har ya kai ga jin haushinki, Hamida jan aji
abune mai fadi da girma, in dan nace zan fassara maki shi sai mu
kwana a zaune, ban gama ba.
A dunkule dai su wadannan abubuwan da kika lissala mani,
shine nuna wa koma waye ke fa macece ba halittarku daya dashi,
ragowar Hamida sai mun samu natsatan lokaci zan warware maki
su daya bayan daya."
"momi in na je na gwada in yayi inzo in gaya maki," ta
tuntsure da dariya, "to shi kenan jeki ki gwada mu gani lamida.
Dama ai irin wadannan abubuwan, inu iyaye mata mu ya kamata
mu dinga koyawa 'yayanmu mata, saboda su tsira da mutuncin su,
amma yin shiru garemu, yana haifar da babbar illa, tunda ita
yarinya bata san yarda zata yi ba in ta hadu da saurayi da ya fita
wayau.
Wai mu kunya, kunya ta wuce ki saki yarki ta lal un
kamin kiyi mata aure, ai wannan shine babban abin kunya Allan ya
kiyaye amin. Allah ya baki sa'a ki sauke nauyi akawali da kika
dauka, karin baya nı kuwa, sai kin kusan aure." "kai momi ni fa ba
aure zanyi ba."
"Dafaki zmuyi a tukunya mu cinye, in ba aure zakiyi ba, kin
san dai ba zai yiyyu ba mu dinga kallanki kina sintiri a cikin gida,
gamu ga ki, "kai Momi wallahi ni ban san aure," sai me kike
SO.... ?" "sallamar da Halimatu tayi ita ta katse maganar
Momi,
muna shiga daki Halimatu ta cukumeni, "yaya lamida an
dace?" nayi dariya an dai kusa," "yanzu ba zance maki komai ba
sai gobe ki sameni gida tunda ba lacture sosai, sai mu hakura da
zuwa makaranta, tunda kinga yanzu nayi yamma."
"Ni dai lamida gobe tayi mani nisa, in zo yau da dare inji
bayanin mana," "to shikenan ina jiranki, ni zan koma gida, hudu ta
wuce yanzu Daddy ya dawo," ta rakoni har motata, bayan nayi wa
momı sallama.
karfe takwas na dare Halimatu ta iso gidan mu, bayan ta
gaisa da Mamana, ne muka wuce (dakina, in da nayi dubarar kunna,
abun daukar maganar wani a rediyo ta. wanda dama tuni nayi
mata, saiti da sabon kaset.
42
Muka zauna, har da dukan cinyata da dan zagin nan na
kawayc yan makaranta, wai in fara bata labari.
"sai kin bani goron albishir tukuna zan gaya maki," "me kike
so, Hamida gaya mani wallahi ko meye zan baki in dai har ina
dashi," nayi dariya, "to tsaya in fara, kema dariya kike bani, lallai
Hamida har yanzu da sauranki."
"Naga Mustapha, munyi magana da shi, amma da farko yace
mani shi ba yanzu zaiyi aurc ba", "ni ko nan da shekara nawa ne
zan jirashi, in dai har ya amince," nayi tsoki," "banza mai zubar
mana da mutunci, Allah yau ba karamin haushi kika bani ba, kin
sani ina ta bin namiji, kamar wani mijina, shi kuma sai wani
kankanba yake yi mani.
Na danyi shiru, wai shi dan ance ana sonshi, dan girman
Allah Halimatu ki hakura da wannan mutumin ki samu wani ki
aura, sai ma yaga ko dan yana da kudi, ko dan yanda ruwan indiya,
shi yasa muka ce muna sonshi,"
in
"Hamida, yace baya sona ne?"tafada asan yaye a'a cewa yayi
bashi lokaci yayi shawara," "Alhamdulillahi, nayi zatan cewa
yayi baya sona da sai ince mki ajalina ne ya matso," "kinji,ki kan
namiji zaki ce zaki mutu," "! Iamida ina tsoron ranar da zaki fada
tarkon so, so bala'l ne kinji,"
sai kuka, Hamida gani kike wasa nike ko? Hamida kina ganin
Mustapha zai aureni," "in nace maki e nayi maki karya Halimatu,
haka in nace a'a, sai dai mu dage da addu'a kawai, ni wallahi
Halimatu bacin kin kafe, da kin hakura da Mustapha, saboda sai in
ga ko ya aureki, anan gaba zai iya wulakantaki, tunda ke kika fara
cewa kina sonshi.
Karki damu da soyayyar da kike yi mashi ki dogarashi da
Allah, Allah sai ya misaya maki wani, ni bazan so inga ana
wulakanta ki ba, zuciyata ba zata so ba,"
"Hamida ki yi hakuri ba shawararki naki bi ba, na gode da
shawarar da kike bani, ba yau ba kawai, harda ta baya, amma ina
son ki sani, ni Halimatu tsakani da Allah nike son Mustapha, ba
don kudi ba, ko wani yanayin fatar jikinshi ba.
A'a, domin raya sunar Manzo (SAW) ko da Mustapha ya
aureni ya wulakantani, dai dai da shine, tunda shi miji nane, in har
da cin zali tsakanina da shi, sai in danganashi ga Allah ya saka
43
mani in munje gobe kiyama, ni dai ai buri na ya cika tunda na auri
wanda nike so, zuciyata ma naso
Komai zaiyi mani, tunda ina sonshi, ba zanga laifinsa ba, in
dai har kinyi niyyar taimaka mani, ki taimaka mani sai Allah ya
hiyaki kema, in kuwa kina ganin ba zaki iya ba, ki hadani da shi ki
bamnu, ni na janyo hankalinshi har ya soni."
"Halimatu tunda nayi maki alkawalin, kinsan ba abinda zai
hana in cika shi, wai dama shawarace, insha Allahu zanyi iya
hakin kokarina, amma duk da haka, ki cigaba da addu'a Allah ya
tabbatar da wanda yafi alheri a gareki ya cire maki son shi a
zuciyarki."
"Amin Hamida, ni dai duk da haka na danka maki amanar
komai a hannunki," "ba komai in sha Allahu zaki sameni mai rike
maki amanarki, "a haka mukayi sallama na rakata,
In dawo wa daki na kashe rediyo na tariyo kaset din baya na
karajin hirar da mukayi da Halimatu, nan take na dauko jakata, na
dauko katin Mustapha na dadda mashi waya nambar sallularsa.
Nayi murmushi jin ya kama sunan a waya, hakan bai bani
mamaki ba nasan a jikin salular sa ya ga sunana "barka da dare
yallabai." Kamar 'a zai amsa ba, cen kuma sai naji yace "ina
mika gaisuwata, ya mutanan gida, nace masa "lafiya kalau, amma
hasu gaisheka, tunda basu san zanyi wayar ba, "zasu sani ne kinsan
komai yana da lokaci."
"Haka ne, dan Allah yallabai ina son yaro daya gobe, wajan
karfe goma na safe, zan ba shi sako ya kawo maka, amma
makaranta zai sameni, "to ranki ya dade, amma "why not" in zo da
kaina in karba."
"Ka rufa mani asiri, yarinya karama kamata, in ce ka zo
kasan abinda ba zai taba yiyuwa ba kenan," yayi ımurmushi da ya
dan daga sautin da har naji a waya, "Ilamida ke nan, sai anjima,
"ya kife kan waya.
Lallai yau ni Hamida naga tasku, wai ni namiji ke jawa aji,
yana neman wulakantani, kan wata, kai alkawalin nan da wahala
yake, na ajiye kan waya nima na shige bandaki abina domin
watsawa jikina ruwa inji sanyi a zuciyata,
Me zai neme takura mani zuciya? Wai da na kwanta barci, sai
na samu kaina da tunani abubuwan da suka faru yau tsanina da
44
Mustapha, wai sai na samu kaina da jin da din tunanin da nike,
kamar dai yarda budurwa ke tunanin saurayin da take matukar
Kauna.
Me nike nufi ni lamida? Ina son Mustapha ko yaya kenan?,
nayi tsoki na juya na cigaba da addu'a ta ta kwanciya barci, amma
abin ikon Allah, sai kuma naji zuciyata ta karra kamo mani tashar
tunanin Mustapha.
Na tashi zaune tare da kara rungume filon hannuna, na tallbe
kumatuna da shi, a take kuma na lumshe idona hade da murmushi
na da na tuno ni a kwance jikin Mustapha, dazu, gaskiya ni dama
zuciyata tafi son irin su Mustapha, yana mutukar birgeni, saboda
irin yaukinshi da yatsina kamar angon sarki.
Ga jan aji na karshe, gashi duk maganar da za kayi bata
girgizashi, ko kuwa dan yana cikin gajiyar kudi?, nayi tsoki,
bude idona, sam bana son Mustapha, Mustapha sai Halimatu,"a
fada a fili, da naji tunanin zaiyi mani yawa a zuciyata.
ASP
S
Na koma da baya na kwanta, tare da sa dariya, ba wani abı
ya sakani dariya ba, illa tunoni da nayi dazu a gidan Mustapha d
na zama bakauyiya, na tuna irin tallan kasan idon da yake yi mani k
na girgiza kai, Halimatu zata shı miskilanci wai, ace mutu baya
kallan dan 'uwansa da ido, sai dai kasan ido.
Nayi tsoki kuma, "kai ban son Mustapha, na juya na kwan
sosai a take anan nayi tunanin cire Mustapha daga zuciyata kada
tabka abiu kunya kan son zuciya, atake anan na tuno maganganu
da mominsu Halimatu tayi mani nan take na kudıri niyvar sai
rama jan ajin da Mustapha keyi mani, ni har kuka masai na sal
shi.
Tare da nuna masa nima fa na iya, gannin yarda zuciyata
ke ta yi mani sake-sake, yasa na yanke shawarar yin sallah Nafil
in dogara komai ga Allah, haka akayi kuwa ban tashi daga k
sallayata ba, sai karfe uku na dare, ina kwanciya kuwa sai barci.
Karfe goma na safe ne aka kirani a dakin daukar karatu, w
inje nayi bako, da jin haka nasan dan aiken Mustapha ne, na fita
samu wannan. wanda naga a yaran Mustapha, kamar shine d
gaban goshinsa, wanda naji ya cewa Abdul Rashid
har kasa ya tsuguna ya gaisheni, ni kuwa na amsa tare da
masa, daga yau kada ya kara yi mani haka bana so, nan na dau
45
S
1
takardar sakon da zai kaiwa yallaba dinsa ya karba, na kara da cе
masa, in yaje yace ya bashi amsa ya kawo mani yanzu, yace to, na
bude jakata na dauko bandir din dubu biyu na mika mashi, sai
yaki karba sai da nace masa in yaje yace ni na bashi
Kaset din hirar da mukayi da Halimatu ne na aika mashi,
domin samun wata hanyar shawo kanshi, da ya guntauwar takarda
kamar haka.
Assalamu alaikum.
Ina fatan ka tashi lafiya, dama na rubuta maka wannan
takardane, domin ka kara sanin da gaske muke fa, ga kaset nan kaji
dan Allah,
Sai anjima daga Kanwarka Hamida Haruna masari.
Awa daya tsakani, aka kara aikowa kirana, na bi malamin a
baya har zuwa wani ofishin malamai, yana zaune nayi sallama na
shiga, amma ko dago kanshi bai yi ba, balle in samu sannu da
shigowata, Mustapha Najib Bauchi kenan.
Na shiga na zaura kujerar nesa dashi, nima na dan dauke
kaina, sannan nace, "sa ınu ko," yayi shiru kamar bai jini ba, nima
sai na share na janyo wani littafi dake gefena a kan wani tebir, na
bude na kama karatu.
Ba tare da na daga kaina daga karatun da nike ba, nace "ina
kwana? na sauri da Allah, saboda ina cikin lecture na fito, in
kuwa ba wata matsala ce ta kawo ka ba, zan iya ce maka, kayi
hakuri da Allah sai wani lokacin ka iya tambaya izini sai ka zo,
Yayi murmushi da fitar sautinshi kawai naji, ya dura wani
abu akan tebir,ban kalleshi ba, balle in san me ya (fura, "lafiyata
kalau ni, ga kaset dinku nan naji komai amma da wuya abinda naji
yasa ni in fasa abinda ke zuciyata, ya mike tsaye, daga yau ni dan
Allah bana son ki kara fadar sunan wannan yarinyar a gabana,
balle ta kaiki ga yi mani hirarta.
Na rufe littalin hannuna na ajiyc, nima na mike tsaye "ina
son nima daga yau kada in kara jin sunana a bakinka, balle kayi
tunanin kana sona, ni Hamida Haruna masari, nace bana sonka,
bana kaunarka, balle wauta ta kaini ga auranka, saboda na lura,
46
koma wautar ta kaini na aurcka, ba zaman lafiya zamuyi ba, tunda
tun a yanzu ka nuna baka son abinda nake so,
Na danyi shiru tare da taku uku, kaga kuwa hakan ya nuna
mani cewa kai namiji ne wanda sai abinda yasa kanshi zaiyi, ban
isa ka tausayawa rayuwata ba, kaso abinda nike so, a matsayina na
mace, kuma matarkа.
Saboda haka, daga yau ni Hamida na barka har abada, tunda
kafi son in shiga kamun Allah fiye da kai danuwana mutum ka
taimaka mani, ni Hamida nace ko zan mutu, Halimatu ta mutu, ba
zan kara ko kiran sunanka ba.
Kada kuma in kara jin ko miryarka, ta ambaci sunana na juya
zan tafi, yayi saurin taryar gabana, yasa hanuwa a aljihu, ya dago
ido sosai ya kalleni, kallan da zai iya sa budurwa ta kamu da son
saurayi a take, na kawar da kai na gefe.
"Meye na taryar gabana? Kasan dai da ganina ni yar gidan
mutunci ce, saboda haka, ba namijin da ya isa ya ce zai
wulakantani, ko da kaga muna neman alafrma a wajenka, kada
kayi tunanin kudi, ko kyau ko wani milki ya kawomu, sam, Allah
ne ya jarrabemu da son hada zuriya dı kai ta sunnan aure.
Bai wai ta shashanci ba, sanna in sanar da kai wani sabon
abu, Halimatu ma da kaji tace tana sonka ni nasan sharin shedanne
kawai, amma Halimatu na da samari na gaske, wadanda ma suka
fika komai.
Sannan ni nan da kake gani, na isa in sa Halimatu kuma na
isa in hanata, saboda haka, ka sani daga yau Halimatu bata sonka,
dama girmamawa da nike maka, ita tasa na 6oye maka duk wata
halaiyata kunya tasani nasunkuyar da kaina dama ga maganar tawa
a hankali nike yinta yarda zata shiga ko ina na dakinshi.
Ni nan da kake gani maza 'yan uwanka ma shakkun yi mani
magana suke, balle su iya budar baki suce suna sona.
"Hamida duk maganr bata kai ta zafi haka ba, tunda nace ki bani
lokaci inyi shawara, ki bani mana, ni yawan zancen ne bana so,
kona mani zuciya yake yi.
Ni kuwa tawa zuciyar ta buga kenan tunda ni kiri kiri ka
nuna baka kaunata kwata-kwata "Hamida yaushe na fada?
"karya nayi maka?" tun da ka nuna baka son abinda nike so, ka
kuwa nuna mani kiyayya a fili."
47
"Ya isa, na, ki banı lokact zanyi shawara, in na gama
shawarata, zan aiko maki da ko mai, shi kenan ko, an hucc?, na
Kara daure fiska, tareda harareshi, ya dan kauce kadan, "Allah
huce zuciyar gimbiya, har yanzu dama kujerar milki na hannunkı.
navi gaba ban tsava bashi amsa ba, shi kuwa ina jinshi yana kırana
amma ban ko juya ba.
*** ***
Tun shirun da Mustapha yayi, bata damu na, gashi yanzu har
ta kai ni ga zama na musamman domin in tunaninshi, hakan ta
farune sakamakon, daukewar kafa ko wani,aike ko wata waya a
tsanina da msutapha, yau gashi har tsayin sati biyu dai dai.
Wannan shirun da Mustapha yayi mani yasa zuciyata ta fara
raunana tana son ta kamu da kaunar shi, gani nima wai jan aji da
vake yi mani shi nike son in dinga ramawa, anya kuwa zuciyata
bata karanto mani karya, ko ban tamabayi kowa ba, nasan zugani
zuciyata keyi in so Mustapha ko dan ta raba zumuncin da ke
tsakanina da Halimatu.
Na samu na mike bna haye gado na domin in ga ko zan iya
komawa barci bayan sallat asuba da mukeyi gidan mu, ranakun
asabar da lahadi, maimakon in komawa, sai na samu zuciyata da
karanto mani, abinda nasan ba zai ma taba yiyyuwaba a kaina, sai
dai ko a kan Halimatu, shine ai yano na auri Mustapha.
Na kwanta har da Kokarin rintsi idanuwana, wai ni a dole bari
nike son yi, amma abin mamaki, sai ma na samu idanuwa na, da
Kinyin bukatar da na nufesu da yi mani.
Nayi tsoki na mike zaune, tare. da kallon, agogon dake ajiye
gefen gadona, karfe shidda da minti uku, nayi imanin sai takwas
na safe ake fita falo gaba dayan gidanmu, ko ince motsi ma ba
zaka samu ba, sai karfe takwas na safe.
Hakan yasa na janyo littafin 'RISALA na bude na soa
karantawa, amma sai na samu zuciyata da aiyano mani, ta wacсе
hanya zanbi in ga Mustapha, donin Karasa zancen Halimatu,ko
zuciyata ta daina yaudara ta.
Gaskiya nasan ba zan iya bin Mustapha har gidansa ba,
saboda ina ganin zubarwa kaina da mutunci ne, na dinga tuno,
maganganun da mukayi da momi su halima, kenan momi tana
48
nufin in ja Mustapha a jikina ya sone, so na gaskiva a cikin son da
vake yi mani sai in cusa son Halimatu a zucivarshi.
Na tashi kawai na shige bandakı navi wankana, na fito