da Mustapha, amma ban gaya mata nice
yarinyar da yake so ba,na dai ce mata, yace yana da yrinyar da zai
aura.
Waı abin bakın cikın da haushin, sai tasa mani kuka narna
rasa da me zanji da marin da nasha, ko tabawar jikin da yayi mani,
ko kuwa da bakin cikin kukan da tasakani gaba tanayi mani?.
Nan take na tureta na mike abina, tana kirana tana ta magana,
amma ban ko tsaya saurarenta ba, da gudunta ta biyoni har bakin
motata, dai dai lokacin da nake shirin tashin ta, "Hamida," nayi
saurin daga mata hannun "Halimatu nayi iya kar kokarina na kasa,
in kinsan har zaki iya da kanki, bisimilla.
Ni kam na gama zuwa wajan namiji ya na wulakantani daga
yau mani zumuncin namu ya kare in har sai na yi maki abinda kike
so, mari! Mari, wai ni Hamida ce namiji ya mareni akan wata."
Na ja mota abina nayi gaba, "ina isa gida wajan karfe biyu da
rabi na rana, maman na daki, na shiga da katunayen kwalaye biyu
na ajiye gabanta, "mama tsaya in dawo, zali nike ji wanka zan
danyi in ji sanyi."
Nayi gaba zuwa dakına, ni wai duk gudun kada ta gane nayi
kuka, bayan na kammala shiryawa, nasa riga da wando, dinkin
ganah, na fito zuwa dakin Mamana.
Bayani nayi mata cewa na kyautar da na samune yau da na
kammala gwajin abincinmu, tayi mani murna, sannan tace in ajiye
sai dadday na ya dawo, a haka na dinga hira ta da Mamana.
Karara waya naji ta dauki yi da karlin gaske, kamar wacce ke
amfani da wayar lantarki? Nayi saurin dauka saboda zuciyata ta
bani, cikin mutum biyu, to daya ne wala Mustapha, ko lalimatu.
Ina dauka, na kanga a kunena, sai naji anyi sallama, miryar
Mustapha naji a kunnena, ban amsa ba, na kife kanwayar nace, "ta
58
tsinke mama," na ajiye kawai, muna fara hira naji ankara bugo
wata, nayi saurin dauka. "muryar Mustapha dai na karaji а
kunnena.
Ban tsaya mayar masa da sallanarsa ba, na ajiye wayar
nacewa Manana, "wayar bata da kyau, ta kara tsinkewa" minti
biyar tsakani aka Kara bugowa, "muryar dazu dai itace, gudun
kada maman ta gane, yasa na gaisa da shi,.
Magiyar inyi hakuri ita ya dinga vi a cikin wayar, ni kuwa sai
na wayance da cewa bata nan, e, a'a, wai dan dai Mamana ta
dauka da gaske wayar nake yi da wani.
A haka na ajiye kan wayar, ba tare da na bashi wata
kwkwarar amsa daya ba, hakan kuwa yayi dai dai da shigowat
Halimatu dakin mamana, tare da sallamarta, kamar gaske na washe
mata baki, bayan sun gaisa da Mamana, na mike navi dakina.
kamar dai nace zo mu koma dakina kenan.
Ina shiga bandaki na shige na kulle, ina jinta, tanata dukan
kofa a hankali tana hadani da Allah in bude, ko motsi banyi ba, ta
kuwa yi wajan awa daya a haka, ina ji ta gaji ta tafi.
Wanda yayi mani dai dai da fitowa da nayi da sauri ta dauki
waya da ke ta ihu a dakina, ban tsaya jin ko waye ba na hau
masila a waya, "kaga Mustapha bana son wulakanci, wallahi zan
gaya ma Daddy in ce kai dan iska ne," "to Hamida in kinga ya
dace ki fada ki fada."
"kaga wallahi ko ka kyaleni ko kasa in gaya maka maganar
da har ka mutu ba zaka manta da ita ba, banda cutata da kaso kayi
Allah bai baka sa'a ba, na son ka mayar da ni mai ido daya," nayi
saurin kife kan waya, na haye gadona.
Kukan me zanyi kuma?, na tambayi kaina, hakan yasa na
mike na lito zuwa dakin mama, ina shiga na sameta tayi barci, ni
ma sai na dawo nawa dakin, mai makon in kwanta ni kuma, sai
nayi alwala nayi sallata raka a hudu, na dinga rokon Allah ya yafe
mani akan alkawalin da na kasa cikawa, wanda na dauka sakanina
da shi.
Bayan na gamane ni ma barci ya daukeni kan abin sallata.
ban farka ba, sai shidda da rabi na magariba, hakan vasa na shiga
bandaki na Kara watsa ruwa a jikina domin in samu jikina ya dan
warware mani. 59
Bayan nayi sallah magariba ne, na fita falo, ni ma kamar yanda muka saba, ina fita Mamana tayi mani maganar idona, da
yayi jajir, nan na sanar da ita da cewa ciwo yake kawai, hakan yasa
ita kuma tace mani in shirya dadare in je asibiti, na amsa mata da
to kawai?
Bayan sallah isha ne Daddy ya kirani, fiskarsa a daure yake
tambayata, "wai me ke tsakanina da Mustapha?, gaskiya gabana yayi mummunan faduwa, amma sai na dake kamar ban fahimce shi ba.
"Daddy wata magana aka gaya maka a kan haka?" "gani nayi
wancen lokacin yayi mak kyauta mai yawan gaske, gashi yanzu
ma ya kara yin wata shine nike tunanin ko da abinda ke faruwa ne?," "ba komai Daddy dan dai shine babban bako shi yasa."
Na samu yabo sosai a wajan iyayena, bayan mun kammala
ganin kyaututtukan ne, nace da Mamana zanje asibiti da tace in je
Bayan na fito daga Specialist Hospital ne na ga motocin
Mustapha a tsaye gefen titi, da hanzarina na kara jan motata sai gida, har muryar Mustapha naji yana kwalla mani kira, amma ban
tsaya saurarenshi ba.
Bayan na baiwa Mamana magungunan da likita ya bani ne naji karar wayar falonmu, duk da nasan gidan mu gidan jama'a ne,
saboda dan milki da mahaifina ke da shi, zamu iya samun waya a
kai kai,, amma sai naji wannan wayar kamar tasha ban ban da ta
kowa, hakan yasa nayi saurin daukar wayar.
Tun daga gaisuwa na gane muryar Mustapha, amma gudun
kada Mamana ta gane, sai na tsaya muka gaisa, "lamida ina son
magana dake yanzu, yaya zamuyi mu hadu a yanzu?, ni yanz.un
haka ina get din gidanku a tsaye in har kin amince, zan shigo
yanzu.
"Ni yanzu ina da abubuwan yi, saboda haka ina son ayi mani
hakuri wani lokaci, ina fatan ka gane?" "karki ajiye wayar, wallahi
kika ki saurarata, zan shigo kaina tsaye in samu Daddy inyi mashi bayanin komai .""to shi kenan ina zuwa, "nayi saurin katsi shi.
Ina ajiyewa nacewa Mamana Halimatu ce ta bugo mani wai
in bayar a kaimata littattafai na da mukayi aiki a satin nan na
60
dauko littattafan Karyata har guda uku, na zo na wuce ta gaban
Mamana izuwa kofar fita.
Duk harabar gıdan mu, sai da na waiwaiga, amma hanga
kowa ba, hakan yasa nayi tattaki zuwa wajan mai gadi domin in
tambayeshi, ko munyi bakin mutane a gidan namu Mai gadi ya
amsa mani da anyi baki amma suna wajan get fin gidan nan.
Ban tsaya jin wani ba'asi daga bakin mai gadi ba, na wuce
zuwa wajan get Mustapha ne zaung saman motarsa, ya daga kansa
sama, anawa tunanin bulu bulu din samaniya yake kallo, saboda
yanayin damana da muke ciki.
Har na iso na tsaya bai dawo da kallanshi gareni ba, duk
kuwa da uwar sallamar da na rabka, "zuwa nayi in bayar da hakuri
akan abinda na aikata na rashin sani ina fatan zaki yafe mani?".
"Ba wani laifin da kayi mani, saboda ni na janyo wa kaina da
na taka har gidan ka, kaima ya dace in baiwa hakuri. na juva na
tafiyata cikin gida, ina jin kiran da yake mani kasan kirane na
nadama, mai kuma dauke da miryar dana sani mai yawa.
Hakan ni kuma da naji, shi na karayin gaba ban tsava yasa
ba, saboda tausayi da Kaunar Mustapha da ya dirrar mani a zuziva
a nana ta c.
Ban fi minti sha biyar da shiga gida ba. ina zaune gefe
Mamana, muna hirar da wani abin ma banajin abinda take fada.
saboda hankali na naga Mustapha, Daddy ne ya fito daga sashensa.
yace in zo yana kirana.
Ban tsaya yin komai ba, na nuli sashin Daddy na, na nawa ne
dan mayafin daguwar rigata na rufe kaina dashi, shigar manyan
matane ta ruwan tokar boyel, gabana kam ya fadi, amma, han nuna
nasan Mustapha ba, halle Daddy ya gane faduwa gaban da nayi.
Tsugunawa nayi har Kasa na gaishe da shi. kamar dai na
samu Daddy na da hakinsa, sannan na zauna sosai a Kasan kafet
nace. "gani Daddy," "ke kinsan wannan" injı Daddy na, tare da
nuna mani Mustapha da dan yatsansa.
"I na sanshi Daddy, wannan ne wanda ya bani kyauta da na
gama makaranta, kuma shine wanda yake son Halimatun gidan
Abba (Ghana, shine yanzun yake dan bina, wai in yi mashi hanyar
auranta, ni kuma bana son yana zuwa wajena, tunda Halmatu dat
'yar uwata ce shi kenan dama inda na sanshi Daddy."
61
"To kai ka gaya mani gaskiyar zuciyarka, kana son Halimatu
ko kuwa?, ni nan da kake gani zan iya auradda Halimatu ga duk
wanda naso, kuma a zauna lafiya, saboda haka, kayi magana, in
bar da gaske kake.
"Yallabai ni bamuyi haka da ita ba, asalima ban san
Halimatun ba, ban ma. ...,""Daddy shine fa yace yana sonta
zai aureta, shine kuma yanzun zaka ce. .""Daddy ya daga
mani hannu, "shikenan, naji, wannan maganar ba lawa bace ba,
kun shirya zancen gaskiya, maga yan aike," Daddy ya tashi ya fice
abinsa.
in
Yana fita na fara yi masa masifa, "yanzu Mustapha me kakc
nufi ne da kazo har wajan mahaifina?, kasan dai ko kazo wajan
iyayena, sai nace ina sonka, zasu aura mani kai ka riga ko sa
cewa ni Hamida bana sonka, tunda ba kason abinda nike
11 SO.
Tsugunawar da yayi kusa dani ita tasa nayi shiru ba tare da na
gama maganata ba, "Dago ki kalleni lamida? ni Mustapha in har
da gaske kike baki sona," na dago muka hada ido, ya lumshe mani
idon da yasa, naji duk gashin jikina ya tashi.
Nayi saurin sunkuyar da kaina," "in har da gaske baki sona,
ki tsaya inyi maki wani abu daya, shi zai sa in gane baki kaunata,
"me ye shi?" na tambayeshi,' fago ki kalleni so sai sai inji maki
abinda zan tabbatar da gaskiyar maganarki.
In kuwa har na gane gaskiyar cewa ba ki kaunata, wallahi zan
yi maki duk abinda kike so," "to naji kayi mu gani," "me zan ga
Mustapha zaiyi mani?" sai naga ya tallabe kumatuna, yana shirin
kai bakinsa ga nawa, nayi saurin kwace fiskata,
"Kana da hanakli kuwa Yallabai?" na mike zan tafi, ya kira
sunana, cikin wata yanayin mirya, baice in juya ba, ni da kaina na
juyo na kalleshi, yayi wani murmushin da saura kadan in mayar
mashi da amsar nawa murmushin, son Mustapha ya wani karu a
zuciyata, hakan yasa na dawo na durkusa gabanshi?
"Gani yallabai," na fada, "me kike son inyi maki Hamida kiji
dadi a rayuwarki?, ka so Halimatu,ka aurcta, ka aika gidansu, ka
cire hotunana daga gidanka," ya dago muka hada ido, "ke bakya
sona?, na daga mashi kai.
62
Yayi murmushi mai fitar da sauti, a ya matso da fiskarsa dab
da tawa, "naji duk zanyi maki, anma nima sai kin bani amsar
tambayata daya, da fada maki sharuddana, in har kinyi mani su, to
zan kuwa yi maki duk abinda kike so.
Ya janye fiskarshi daga sunkuyowar da yayi" "kin amince da
abinda na fada in cigaba da fada maki?" na daga kaina alamar E.
Na farko sai kin tabbatar mani da gaskiyar baki sona, har a
zuciyarki, nayi murmushi, "ya za'ayi ince bana sonka kana
musulmi dan uwana, "ni ba son musulinci ba so na aure nake
maki magana," "dan Allah yallabai kabar wannan tamabayar ba
yanzun ba, kaga dare nayi.
"Ba zanyi maki gardama ba, ko mai kikace inyi zanyi,
magana ta biyu, itace ba zan so waccan yarinyar ba, sai dai zan
aurela a bisa sharudda uku, ki bani wata daya, anma kafin wata
dayan ta cika kema ina son kiyi saurayi.
Amma da sharadi ba zaki dinga zance da shi ba, dalilina nace
maki kiyi saurayi kuwa, shine ina son in wata daya ta cika na fada
maki sharadi na guda uku kika amince da su to tare za'a daura
auran mu da 'e da saurayin na ki.
Ki sani ba zancan ki tsaya hira da shi, amma ban hanayin
hirar waya ba, ki sani ina da mutanen dake kula mani da duk wani
taki da zakiyi a garin nan, saboda haka ki kiyaye, ba zancan
tsayawa da shi balle ya tsaya kusa da ke, ko ta kai ga taba jikinki,
in kuwa na samau daya daga haka, zan iya daukar babban ruatakin
da zan iya kashe shi.
Na biyu dole ne ki dinga jewa waccan yarinya hira wajena,
saboda ni ba zan iya zuwa wajanta ba ni ma, tunda ke zaki zamo
madadinta kenan, aınma wani sharadin nawa kuma shine, bana son
in kin zo mata hira wajena ki ambaci sunanta ba, sai bayan wata
daya, kenan bana son in ji kin ambaci ko sunanta, sai bayan wata daya."
"Amma ai yallabai kasan dai makaranta nike yi, kaga ba
yarda za'ayi in dinga jewa Halimatu hira, in ka anince yarda ba
zanyi hira da kowa ba, kaima kayi hakuri da yin hira da ita," "ni
dama ba da ita zanyi ba, da ke, saboda haka ba ruwana, ni dai
nasan sai anyi mani abinda nike so zan aure wacce ake son in
aura. 63
"yallabai iyayena ba zasu barni in dinga yawan fita ba," "ni
ba ruwana, amma ai kin san da haka kikayi mata alkawalin hadata
da ni ko? To yanzu ma ki san yarda zakiyi kina zuwan mata
hira........" "kullum ko yaya?""ta yiyyu kullum ta yiyyu, sai na
nemi son ganinki, saboda haka ki dai shiga saurarata waya in har
ina son a zo mani hira.
"Ina jiranki gobe," haba gobe kamar ba yau ka zo ba," "ina
ruwana, ni dai dole azo mani hira," "a ina zan zo kasan dai ba zan
zi gidan ka ba," "aamma ai kina da katin Naicon a hanunki,"
"gaskiya ba zan dinga zuwa naicon ba, saboda kada in hadu da
abukanan Daddy, kaima kasan wajan mayan mutanc ne,"
"Gobe zan bugo waya in sanar da ke in da zamu hafu sarkín
cika alkawali, ni zan tafi na bar mutane suna jiyarana a waje?
wallahi kaji tsoron Allah ka daina wahalar da su dan kana da
kudi." svital sb ка
"Ai kuwa ni a ganina ina kulawa dasu dai dai gwargwado
amma duk da haka zan kara kiyayewa na gode, banayi masu haka
wallahi, yanzun ma uwargida tace tayi mani fishi, shine muka tahó
biko da su, na danyi murmushi "to sai da safe, nasan Diddy na cen
ya na jirana in sha jerin tambayoyi.я в вау ла rin
Ganin bashi da niyyar tafiya yasa nayi mashi sallamar dole
nima na shige cikin gida, ina isa falo, Daddy da mamana suna
kallan labaran Karfe tara, hakan yasa na kalli agogon falon 'mu,
naga goma saura minti sha takwas, na koma daga gef nima ha
zauna, ism Tamilnug 3 06/0
Jikina har rawa yake yi daga zaune saboda zaman jiran
tsammanin Daddy ya jefo mani tambayoyi nike yi, amina har'ya
shiga sashinshi, bai yi mani magana ba, wanda hakan yayi dài dai
da karfe goma da minti sha biyar ha dare АиЯ
Mamana ta kalleni, "ina kika j6? "mama Sauráyin Hammatü
ne yazo muka gaisa," "wacce irin gaisuwace haka niar dadewaoh
"mama shine bai tafi ba shinc ni kuma na Kasa ce masa ya tafi.
shine sai yanzun ya tafi?.
"Ki dai kiyaye mutuncinki, kullum dai ina gaya maki wallahi
in har kika tsaya yaudarar kanki to kin yiwa kanki," ta mike ta nuli
nata dakin, nima hakan yasa na kashe talabijin din da sauran yan
kayayakin wuta na shege nawa dakin.
64
*** ***
Sati biyu kenan da yin yarjejeniyar mu da Mustapha, da
motata nike tafe a hankali har na karya ta izuwa ,Amingo stor"
domin siyen kayan da Mamana ta aikeni wanda haka yayi dai dai
da rabuwata da Mustapha minti ashirin da suka wuce
"Amingo na shiga zagayawa domin tsintar kayan da naje
siye, ba'afi minti uku da fara daukar kaya siyena ba ina zubawa a
dan kwandon da nike zuba kaya, sai naji ance mani, "(sannu,
turaran ciki bakar kwalbar mai wahalar gane kala,)" na dan waga gefena kadan.
Ba tare da na cigaba da kallansa ba, na danyi murmushi, haba Alhaji sufuyanu, kaine ba'a yi maka kirarin kana wahalar gani ba.
sai ni da nike yawo kullum a titi, ina neman dan ilimina,
"Hamida kenan, ya gida? Na amsa da lafiya kalau, haka muka cigaba da tafiya ko wannan mu yana daukar abinda yaje siye.
Gudun kada yace zai biya mani kudin siyayyar da nayi, vasa.
ban karasa siyayya taba, nayi saurin zuwa na biya kudi, amma sai
ya zamato na ts ye gefe daya na jira shi,
Bayan ya 'iya nasa ne, aka daukar mana kaya zuwa matocin
mu, amma sai naga yasa a kawo leda daya mai kaya a ciki wajan
tawa mota, hakan yasa na nunawa mai daukar kayan cewa, ba
nawa bane, bayan mai daukar kayan ya koma wajansane, sai suka
taho tare wands hakan ya tabbata mani da Sufiyanu siya mani kayan yayi.
Bayan yar guntuwar mahawarar da ta shiga tsakaninmu.
wacce dole ni na hakura ba sifiyanu ba, sai muka tsaya yar hirar
wajan minti sha biyar, wanda a wajan hirar ne yake kara dawo da gabatar mani da kanshi a matsayin mai son ya aureni.
Banyi mamaki ba, saboda nasan Sufiyanu tsohon masoyinane, tun ina yar aji biyar sakandire, sai dai a lokacin ni ban daukeshi wani masoyi ba na dai mayar dashi abokin wasana ma,
tunda in yazo gidan mu ni tsokanarshi muke yi ni da Halimatu.
Samun fiska da kumatu da Sufiyanu yayi wajena, shi yasa ya ke sanar dani cewa zaizo a daran karamar wajan takwas na dare.
saboda yarjejeniyar da mukayi da Mustapha, ita tasa na amsa masa
da ina jiran babban bakona. 65
Amma kafin mu rabu, sai da na dan daure na tambayeshi
cewa yayi aure?, ya amsa mani da har yanzu dai yana jiran wacce
uyi dai dai da rayuwarshi ne, shi yasa bai yi ba, amma yanzu a
shirye yake da yi in har na amince masa.
Yar dariya nayi kadan irin tamu ta mata, duk da irin kallan da
yake yi mani yana hanani sakewa sosai, wanda irinsa na baro
bayan mintuna hamsin da wani abu da suka wuce, wanda
Mustapha ya sani a gaba yanayi mani, koma ince yafi na Sufiyanu
razana mani jikina.
Nasan shigar da nayi yau zata iya janyo mani kallo ga
jama'ar gari, to balle masoyana, ba wata shiga bace illa bakar
shadda dinkin Good morning momi, da farin mayafi, farin takalmi
ga farar jakata ratayc a kafadata.
Wanda fashon din 'yankune ne a kunnena da wuya na masu
kalar baki da ratsin fari suma, hakan yayi dai dai da bakin jan
bakin bakina, da yayi kwance a leban farar mace kamata, wanda
bakin kwalli kajal ya dira a dunduniyar tudun idanuwana ya kayata
mani fararen idanuwana,gá bakin cikin idon shima yau kamar an
tura nani shi.
Karin kyan jiki irın na yarda gashin kaina ya kwanta bayana,
kitso daya rak akayi mashi, Mustapha ya yaba mani matuka da
kwalliyar da nayi duk da dama jama'ar duniya suna cewa
kwalliyar yar babbar makaranta, tasha banban da ta yan kanana
yaran yan mata.
Nayi mumushi tare da yin sallama da Sufiyanu na bude
nuwan tukar motata mai duhu, tamkar kayi kallo daya kawai yace
mata baka karka tacan yafə mayafin da nayi ya su bace a dai dai
lokacin da na záuna matukin direba, zan tashi motata.
"Sannu Hamida" haka, naji Sufiyanu ya fada, a dai dai
lokacin da yake kada makullan motar da ke hannunsa, ban amsa
masa ba, amma nayi murmushi, na ja mayafina tare da ce masa
"ina jiran babban bako fa". Wanda hakan yayi dai dai da tashin
motata da nayi, nadan jata kadan sannan ya amsa mani da "to
karfe takwas fa".
Karfe takwas saura minti goma sha uku na dare ina jikin
madubi ina kara gyara fiskata, ni nasan ba son Sufiyanu nike ba,
66
amma nayi hakan ne domin in'tursasa zuciyata ta so Sufiyanu dan
kawai Mustapha yaga da gaske nike yi, maganar Halimatu.
Nasan ban saba ba, amma yan kwanakin nan da nike tare da
Mustapha, na dan fara saba iya mayarwa da saurayi amsar
tambaya, ko yi masa magana.
Hakan yasa banji komai ba da Sufiyanu ya zo, Sufiyanu kam
ya samu karbuwa, saboda hirarmu abin sha'awa dashi, muna cikin
haka "Aina'u ta shigo, har kasa ta durkusawa ta gaishe da
Sufiyanu, sannan tace in zo in dauki waya a cikin gida in ji
mamarти.
Da annashuwata na fita daga baban falan baki na kusa da
shashen Daddy, tare da cewa Sufiyanu, ina zuwa, tun a kofa nayi
tsaye chak da na hango Mustapha, tsaye dan nesa da ni kadan, yayi
taku uku domin na taho in da yake.
Wanda hakan yasa shi kuma ya tsaya, ni kuwa nayi hakane
gudun kada Sufiyanu yaji abinda ke faruwa tsakanina da
Mustapha, shima yajanye ya barni ba a kowa ba.
"Sannu yallabai," waye ciki?", maganar da yayi mani kenan
wanda ko sannunt bai amsa mani ba. Wace tambaya ce wannan
kuma haka?" "inji naki tambaya, sannan ki dawo mani da ita, nace
waya a cikin falan?" "bako nane," "waye kuma haka?" "baka san
ko meye bako ba?"
"ina sauraranki ki sanar dani ko wayeshi," "bako na, shine
mutuman da nike saran zan aura nan da lokacin da za'a daura naka
auran kaima," "amma in kinyi tunanin sai da na gaya maki ban
amince kiyi hira da kowa ba, kamar yadda ni ma ba zan yi da ita ba.
Ya juya ya taka kamar sau uku, tukuna ya tsaya, ba zan
hanaki ba, amma kuma duk abinda ya biyo baya akanku kiyi kuka
da kanki, "amma yallabai kaine kace in yi saurayi ko?".
Bai tsaya ba, balle ya bani wata amsa, ni kuwa hakan tasa na
juya zuwa falon da Sufiyanu yake zaman jirana, cikin hirar mu da
Sufiyanu ne nayi masa dabara, cikin hikimar cewa jibi zan yi
tafiya, saboda haka sai dai a waya zai dinga samuna.
Nayi mashi alkawalin buga masa waya kullum mu gaisa da
shi, wanda a karshe nace masa gobe yaya na usman zai dawo daga
spean saboda haka zai iya samun sako ta waya cewa ya turo da
67
iyayonsa da kayan aure da komai in har aka nemi daga gıda in
kawo wanda nake so.
Yayi murna kwarai da gaske, wanda na fahimci shi,
uciyarsa, fis take tamkar nace ya koma ya turo da mutanc a (faura
mana aure dashi a yanzu.
Nayi haka ne, gudun kada wani abu marar kyau ya faru a
kanshi, saboda ganin yarda Mustapha ya hasala da yawa, Karfc tara
da kwata Sufiyanu yayi sallama dani, ni kuwa rakiya har bakin
motarsa, abin kuwa sai naga ya bani sha'awa.
Wanda zuciyata ta fara amincewa da in aure shi, ko dan
hankalinsa da natsuwa da suka gama jikinsa.
Halimatu nayiwa waya daga shiga ta gida, na sanar da ita
gobe karfe tara na sake ko takwas da rabi, ta zo muyi abincin
taryar bako yaya Usman, wanda in mun gama zamu isa filin jirgin
Abuja Intel-Air port mu taro shi karfe biyar da rabi na yamma.
Ba tantama yaya Usman ne na hango yana saukowa daga
jirgi, duk da na samu shekara uku kenan baganshi ba, amma sai
gashi ta farat daya na ganeshi.
Tun daga nesa nake daga masa hannuwa, har ya hango ni,
ganin ba bari isa in da suke yasa, na dinga tsallan mur ıar
gashinan zuwa, amma yana tsowa in da zan iya zuwa in taryeshi
ban san lokacin da na ruga a guje ba na taryoshi.
Yanda yaya ya ware hannuwa, a manufarshi in shiga ya
rungumeni, amna saboda gırma da nayi, sai naji na kasa yin haka,
sai dai nayi saurin rike hanunwansa duk biyu, ina dariya, amına
abinka da zama turai da yaya yayi.
Da muka tafi zuwa wajansu Daddy sai da ya rungumeni a
gefan kafadarsa, da murnarsa ya durkusa ya gaishe da Daddy,
wanda yana zuwa wajan mamarmu, sai naga ya kama hannunta,
sannan ya durkusa ya gaishcta,
Mamarmu ta amsa tana dariya ta murnar katan danta ya
dawo, wanda tuni 'Aina'u ta dare shi dan murna, shi kuwa ya
rungumeta yar kanwarsa, ya gaishe da mominsu Halima, sannan
Halimatu ta gaishe shi.
Dan rashin kunya ta irin wanda ya dan zauna tare da turawa,
yasa yaya ya tambayeni, wai har yanzu ba'ayi mana aure ba, ni da
Halimatu?, kuma a gabasu Daddy, wanda momi da take ita
68
69
тясесс тai wayayyan kai, ta bashi amsa da ko saurayı bamu da
shi.
Hakan yasa ni kuma, "momi' Halima tana da wanda zata
aura, har sun kusan dai daitawa, ba mamaki a aiko maku da mayan
mutane nan da dan wani lokaci.
Yayane yace in gaya mashi gaskiya, ni kuwa har da rantsuwa
ta, da kara tabbatar masa da gaske nake yi, anan iyayenmu suka
zama 'yan kallo, saboda nasan basu san komai ba na game da wani
abu na Halimatu.
Amma abin mamaki sai na ga yaya Usnan yayi wa Halimatu
wani kallo da ban fahimci mai yake nufi ba, hakanan kuma sai
naga yasa Halimatu tayi saurin sunkuyar da kanta, kamar wacce
bata da gaskiya.
Tun daga lokacin sai naga yaya Usman ya dan canja fiska ba
kamar farko ba, haka muka shiga mota, amma banga yaya ya canja
ba.
Daddy da Mamana sashen Daddy suka wuce kai tsaye ni
kuwa da Halimatu da yaya cikin gida muka nufa, wanda Halimatu
tayi saurin shiga kicin, hakan yasa nima na bi bayanta, domin a
tunanina kayan abinci ko sha zata daukowa yaya.
Muna kicin ni da lalimatu yaya ya shigo, tambayar da yayi
mani itace ta bani mamaki, wai in gaya mashi gaskiya Halimatu na
da wani saurayi wanda bashi ba?, na dago da dan hanzarina.
"yanzu nan yaya dama kai saurayin Halunatu ne, ni ma na mayar
masa da wata tambayar.
Ya bani amsa da, "IE mana, yanzun da bata taba gaya maki
ba?" "wallahi ban taba ji ba, yayi dan munmushi, "dama ance mata
baku da tabbas, kamar yanda kuma kuke ce mana maza bamu da
tabhas ya juya ya kalli lalimatu.
Yanzun haka kika yi mani Halimatu? "yaya karfa ka zama
dan runto da kai saurayin Halimatu ne, nayi imani da ta fada
mani," "to zo muje ki gani in nuna maki tabbacin cewa ni babba
masoyin Halimatu