An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HAMIDA
1
AUNTY MARYAM KABIR MASHI
AUNTY MARYAM KABIR
MASHI
HAUSAВООК.COM
HAMIDA
NA
AUNTY MARYANARYAM KABIR MASHI
(MRS. UMAR ABDULLAHI)
ankalin jama'ar da ke tafiya akan titi duk ya koma H
ga kallon motocin da ke wucewa a gabansu, sauda
dama zaka ga in motocin nan zasu wuce duk jama'a
sun mayar da hankali akansu, na zaune ne. yarane. kai wani
lokaci ma har matan aure zaka ga suna lekowa ta saman
tagoginsu
Shin waye mai motocin nan? Wani mutum ne shi, wanda shi
ba shugaban kasa ba, ba wani gwamna, sannan shi ba wani banc а
Kasar nan tamu ta Nigeria.
Amma abin mamaki shine yarda mutanan gari ke kaunar shi,
saboda wata daukaka da Allah yayi mashi shi yasa ma na lura da
jama'ar garin Abuja sun fi son ganinshi fiye da acc masu ga
shugaban kasar su nan, ko me yasa? Na dai samu labarin cewa wai
shi mutum ne mai kyauta da daratta manya mutane, wai kuma
bashi da girman kai, sannan ga dukiya wacce jama'a sunce ba za'a
iya auna yawan dukiyarsa ba, a gida Nigeria to balle kasashen
duniya.
Ni abin yakan daurc mani kai saboda ni ma kaina ina son
inga na kara ganin wannan mutumin, saboda sau daya na taba
ganinshi, hakan ya tuna mani lokacin la naganshi, yau tsawan
shekara biyu da ta wuce kenan.
A lokacin da muka gama makarantar gaba da (primary)
firamare, shinc malamanmu suka gaiyaceshi bikin yaye dalibai yan
aji shidda (Send off), ni kuma ina cikin daliban da suka fi kowa
kwazo a makarantar mu, koma ince nice zakarar daliban shekarar,
Saboda a cikin darasi tara da ake mana ba wanda na fadi,
watau duk darussas nice (Over roll) banda ingilish Iinglish da
maths da aka kara bani kyauta a akansu, saboda shima ni na zano
Over roll a kansu,
A lokacin shine babban bako na musamman, saboda haka
shike mika mana kyaututtuka, inda yake gaisawa da wanda yaci
sannan ya mika mashi kyauta.
Kasancewar ni na zamo falibar da tafi kowa yasa ya kirani
bayan an gama ba dalibai kyauta, ya bani tashi ta musamman.
saboda yaba mani da yayi sosai, katuwar ambulan (envelope) mai
ruwan kasa ya bani a matsayin kyautar shi ta musamman, ni kuwa
2
yana bani na daga sama na nunawa sauran jama'ar da ke dakin
taron, dakin taro ya dauki tali.
Muna isa gida bayan taro ya tashı, a tsakiya babban falan
gidan mu Daddy na ya bude kyaututtukan da akayi mani, inda
Mamana keta yabaona, a haka har muka zo ga kyautar da yayi
mani la musamman.
Daddy na budawa sai muka samu littattafai guda goma na
rubutu da katukan yabo watau (Congratulation card) har guda
hudu ba komai a ciki sai kalaman yabo da taya murna, da kara
Karfafa mani gwiwa akan in dage gaba in fice haka.
Sai Babban katin hotonshi na cikin gilashi (Enlargement) mai
kamar irin na shugabannin nan na kasa, sai kyautar turare ga
ivaycna, ya rubuta a jikin turarirrikan, sai hankici masu dauke da
furannin turawa guda hudu da kyautar dubu dari
Daddy na yayi farin ciki sosai, sannan ya sa mani albnarka
kamar yarda namata ta keyi tunda aka fara bude kyautar, a lokacin
sai na fahimci Daddy ya danyi shiru, da alama tunanin yake, ban
tambayeshi tunanin da yake ba, ni dai na cigaba da murnata.
"Ke da Allah ki taho mu tafi kinga har zamu nakara," na
cwa kawata, aminiyata Halimatu, a lokacin da na kara sa tunanina,
amma sai na fahimci tunanin Halimatu yafi nawa zurfi saboda bata
maji maganar da nayi mata ba, har sai da nakai ga tabata tare da
cewa, "har yanzu lalimatu kina bani mamaki yarda har yau kinki
cire mutumin nan daga zuciyarki, wallahi in har kiua zurfin
tunanin haka, to zaki janyowa kanki cuta mai tsanani."
"Mhm, ke dai bari Hamida, tunanin bawan A!lah nan fa
yakan damar mani zuciyata," "wane mutumi ke nan?" na shareta
kamar ban fahimei abinda takewa tunaninba," "Mustapha mana,
"au Mustapha", nima,tunanin ranar da vaje yayi mana babban
bako na musamman nake yi, lokacin da muka gama makarantar
mu.
"Ai ni Hamida mamaki fa kike bani," "name kenan?" na
Allah ya baki dama ammna kin sa kafa kin taketa, da ni ke da damar
da Allah ya baki da ba zaki ganni nan ina fama da takarda da biro
ba," da tuni yanzu ina gidan aurena, yanda mutuman nan ya baki
katin gaiyatar auranshi,
3
7
"Katin gaiyatar auranshi?" na fada tare da dafe kirjina," "e
mana, ga dama amma kin yar da ita," "wai damar me Halimatu
"na kin kula samari da kike yi, ga wanan bawan Allah da nike yini
ina kwana tunaninshi, amma ke ya baki katin gayyatar auranshi
amma ko a kanki
"Wai yaushe ya bani katin gai yatar auranshi da har ban gaya
maki ba?" "ba ina nufin ya gaiyaceki bikinshi ba,tunda har ya
sanki ya kuma baki kyauta har da Babban katin hotonsa ya kuwa
gaiyace ni na in nemeshi, koda kuwa zan rasa raina, wallahi
Hamida da ni yaba kyautarki, Allah! Allah!! Allah!!! kinji dai ná
rantse, ko zan mutu sai na aureshi yanda zuciyarnan tawa ke
kaunarshi a kulum karuwa sonshi yakeyi a zuciyata........"
"Ke Halimatu, kina da hankali kuwa? Haka kawai mutum bai
san da ke ba, amma ke kullum baki da tunanin sai na shi dan hauka
har kina kiran salwantar da rayuwarki a kanshi."
"Hamida har yanzu fa ni ke nike gani mahaukaciya tunda har
yau ke baki san so ba, da kinsan so, shine zaki iya dan dana yanda
nike jin Mustapha a zuciyata, tunda kuwa nayi kokari na samu
hoton shi, wallahi da shi nike kwana da shi nik karya kumallo.
Hamida, tunda nike a duniya ban taba son da namiji ba
kamar yarda naji ina son Mustapha, nasan ina da saurayin da nike
mutuwar kauna a baya, to gannin ya yardani, yasa nima na hakura
da duk wata soyyaya sai gata yanzu na samu kaina ga soyayyar
daban Ta6a samun kaina a cikinta ba.
Kece shida ta Hamida, kinsan dai irin halin da nike ciki tun
ina yar aji hudu, amma gashi har yanzu ban samu ko ganinshi ba,
to balle in sa ran wata rana zanyi magana dashi har yasan halin da
nike ciki; tayi shiru, hakan yasa na daga kaina na kalleta, hawaye
ke fita daga idanunta, wani haushinta ya kamani nayi tsoki.
Wanda dama tun muna makaranta (secondary) in tana yi
mani hirar tashi nike in tafiyata in barta, nayi ajiyar zuciya "ni dai
maganata da na saba yi maki kullum yau ma ita zan mai maita
maki, itace kiyi hakuri ki cigaba da addu'a in har Mustapha
mijinki ne, to sai fa kin aureshi ko ma ta wane hali ne.
In kuwa Allah yasa Mustapha ba mijin ki bane, kinga anan
sai dai kiyi hakuri, ni dai shawarata daya shine ki dage addu'ar
neman zabi ga Allah, in Mustapha shine alheri ga rayuwarki, Allah
4
ya kaddara maki in kuwa bashi bane alherinki, Allah ya kawo maki
wanda yafi alheri a gareki, amma tunda naga har abin ya kai ga
zame maki tashin hankali har haka, to ni kuna nayi maki
alkawarin taimaka maki da addu'a Allah ya taimaka maki ya
tabbatar maki da manufarki ta alheri."
Na ja hannunta muka fara tafiya, hakan kurna yayi dai dai
da'a giyar zuciya da tayi mai dauke da sauti mai karfi, hakan yasa
mutanen dake kusa damu suka kallomu amma na fahimci Halimatu
ko a tsokar naman jikinta duk kallon da ta tara mana a kanmu sai
ma maganarta ta cigaba da yi.
"To Hamida na gode, amma ni a gani na ba wanda nike da
shi, wanda nike ganin zai taimaka mani sai ke" nayi saurin juyowa
na kalleta, "Me kika ce Halimatu? Ni? Ni ina nasan Mustapha, ina
ganin yarda na sanshi kema haka kika sanshi, kara ke ma ganinki
biyu da shi ido da ido, ni kuwa ma ganina da shi daya, a'a, ki ma
daina maganar nan Halimatu, saboda ban san ma inda zan kara
ganin shi ba, sai dai ban fita da rai ba ko a kiyama kila mu hadu da
shi, in ma Allah yasa muna cikin wadanda yayiwa rahamarsa".
"Ila san da haka Hamida, armma a tunanina, tunda ha nace
haka a ki tsaya ki tambayeni dalilin fadar haka ko" " na
tambaya Halinatu gaya mani inji"
"A irin bincikan da nayi na halaiyar Mustapha, jama'a da
dama sun sanar dani cewa wanda ya taba yiwa kyauta, ko ma shi
waye, to yana da hotansa yana kuma rubutawa saboda gudun wata
гапа, уaпа yin haka ne, saboda shi mutum ne wanda baya san yaga
ya wulakanta wani, sannan mutane sun tabbatar mani da cewa,
Duk wanda Mustapha ya tab baiwa kyauta to baya
wulaKantashi, kuna ko shi waye in har yaje mashi da uziri ya na
tsnyawn ya saurareka, kinga kuwa kina daya daga cikin mutanen
da ya taba yiwa kyauta in kin tuna kuma Hamida kyautar da
Mustapha yayi nıki mm iya kiranta ta musamman.
Saboda ni da farko da naga kyautar da yayi maki hankalina
ya tashi matuka sabuda sai nayi tunanin ko sonki yake da aure,
nali karli wata biyu bana iya barci, in har zaki tuna lokacin da mu
kayi (candy) finmu nayi wata rashin lafiya duk nabi na rame, to a
lokacin, abinne ke damuna a zuciyata, anuna daga baya da na
5
dinga binkı cankı sai na gano ba wani abu a tsakaninku, shune fa
hankalina ya kwanta.
Kuma sai hakan ya tabbatar mani kyautar da yayi maki irin
kyautar nan ce ta manya, in sun yaba da hankalin mutum, kinga
kuwa Hamida kece sa hun gaba ta wacce zata taimaka mani da in
auri Mustapha.
"Na dafa kafadarta saboda jikina kuma yayi sanyi akan
lamarin Halimatu, "kada ki damu Halimatu in har da raban nice
sanadiyar haduwarku da mustapha, to zanyi iya kokarina in
hadaku kuyi aure. In kuwa bani bace ba, dan Allah ina son kada ki
dauke ni awacce bata damu da halin da kike ciki ba, sai dai kuma
wani hanzari ba gudu ba.
Halimatu kada muje mu kai kanmu inda za'a wulakantamu,
kinsan fa namiji bashi da tabbas, kamar yarda muma mata wani
lokacin akan samu marasa tabbas a cikinmu. Gaskiya Halimatu
kinsan dai kin wuce kawa ko aminiya a wajena sai dai 'yar uwa ta
jini, saboda haka ba zan so in ga kunyi aure da Mustapha ya na
wulakantaki.
In kuwa haka ta faru, kin sanni Halimatu ba ha kuri gareni ba
zan iya cewa zan rama maki koda kuwa auren naki zai gutsure ni
ba ruwana.
Shin wai ma ba'a nan take ba kada fa son zuciya ya kaimu
(cin zaku bamu samu duron ba) ma'ana kuwa shinc Halimatu
muda ba.nu san halaiyarsa ba, muje mu kai kanmu ga aikin jana
sani daga baya sai dai jita jita da muke ji, kada ınuje mu fada
hannun 'yan mafia.
Saboda naji ana cewa ma ba dan kasarnan bane ba, ke kanki
Halimatu ki kalleshi sosai ai kyanshi yayi yawa, kamar aljani.
Kilama aljanne ya rikida ya dawo suffar mutane ya samu na kaiwa
Kasarsu
Halimatu tayi dariya "Hamida tsoro wa ya gaya maki dan
mafia ne? (mafia) ko aljani, mutum ne mai mutunci kamarki, ni
nan da kike gani Hamida nasan tarihin Mustapha daga farko har
karshe. "ke karya, ke dai kawai ki ce dan kina sonshi shi yasa baki
son a fadi haliyarshi maras kyau".
6
"ke wallahi Hamida," to nasan da jita jita to bada labarin shi
ko mutumin fakistan ne ko indiya ma aka ce, oho, har yau fa ba
wani mutumin da zaki tambaya ya baki cikakken tarihin Mustapha.
"Hamida na fahimceki ke da wasa kika dauki abin, to ni ina
mai tabbatar maki na je da kaina nayi bincike akan Mustapha,
kuma na gano wayc Mustapha, ni dai in kinyi niyya ki taimaka
mani Hamida
"Halimatu abin naki ma ya koma zauci-zauci hauka hauka sai
dai ince maki Allah ya baki sa'a....., wallahi Hamida ba wasa
muje makaranta in har muka gama (lecture) lakca kamin mu shiga
wata zan baki cikakken tarihin Mustapha "MUHAB", nace mata
"to kawai saboda ni har ma jikina ya mutu akan lamarin Halimatu,
tausayinta kawai ma ni ke ji ni.
Hankalina gaba daya yana ga kallan malamin da yake mana darasi
(lecture) a gaban allo, saboda malamin ya iya darasi sosai (lecture),
kamar ance in kalli Halimatu, sai na ganta tayi tagumi hannu
dukka biyun ta kurawa malamin dake gaban allo ido, amma kai da
ganinta kasan idantane kawai ke kallan malami, amma hankalinta
gaba daya b ga malamin yake na, na girgiza kaina kawai na juy
na ci gaba da kallan malam da ketsaye gaban mu.
Wata bishiya muka samu can nesa da inda jama'a ke geftawa,
muka shimfida daddumarmu ta zama, dama gashi mu da shiga
wata (lecture) darasi sai bayan awa biyu, hakan tasa da muka fito
mukayi nisa da jama'a sannan muka dauko kayan abincinmu muka
sa gefe, wanda direban gidan su Halima ya kawo mana, sannan na
mayar da hankali ga sauraran labarin tarihin Mustapha da
Halimatu zata fara bani.
*** ***
Mustapha Najib Bauchi dan asalin jahar Bauchi, ne ba wai
ina nufin a Bauchi akan haifeshi ba, amma ina son ki san
mahaifinsa ne dan asalin Bauchi, watau iyayensa da kakannin
mahaifinsa suna Bauchi.
A yarda na samu labari iyayen mahaifinsa suna zaune a
unguwar Jos Road can jahar Bauchi, amma kuma mahaifiyarshi
'yar kasar indiya ce. Hamida nayi kokari naga mahaifiyar
7
Mustapha da idona, amma ba wai magana nayi da it ba, dan dai
kawai in tabbatar da gaskiyar labarin dana samu na kuma tabbatar,
mahaifiyar Mustapha ba indiya ce cikakkiya.
Mahaifin Mustapha ya auro mahaifiyarshi ne a kasar
indiya a lokacin da yaje zama wakiltar Nijeriya a can
(Ambassador). A lokacin da mahaifinshi ya auri mahaifiyar
Mustaphawacce akace mani sunanta (Hindatu Alkishan Khan) tana
'yar shekara ashirin a duniya.
Amma in kinyi tunani ba girmanmu daya da su ba,
saboda haka tana aikine a karkashin ofishinshi jakadancin a can
indiya din amm fa iyakarta makarantar gaba da sakandire, dan dai
ta samu aikin ne kawai.
A yarda bincikena ya gano mani, na gano a hannun
mahaifin Mustapha ta ci gaba da makarantar gaba da sakandire.
Amma kuma labari ya tabbatar mani iyayenta musulmai ne
cikakku, a yarda naji labari, kakanta shine shugaban masulmai na
cikin kasar indiya, watau Sarkin Musulman Indiya. Sunce in ka
tambayi sunan (Khan Al-Salam) za'a kaika har gidanshi.
Iyayenta kuwa suna zaune a Kalcutta a cil in jahohin
ka sar indiya, saboda haka ance ba'a samu wata rig ma ba da
mahaifin Mustapha zai taho da ita Nigeria, sai dai 'yan dokokin ya
dinga kaita suna ganinta duk bayan dan lokaci, tare da tabbatar da
ba zaici amanarta ba, da cikakken adireshin inda za'a samesu a
Nigeria, yace ya amince.
Mahaifin Mustapha ba indiya kawai yayi Ambassador ba,
yayi wakilcin Nigeria ba, yanda naji labari, ance a kasashen duniya
biyar yayi bayan Indiya. Ance da (India, Switzerland, Netherland,
South Africa, France, Germany).
Sannan kuma abin wani mamaki, Mustapha kawai suka
haifa a duniya da ya gama yawan ambasadarshi, shine ya dawo nan
garin Abuja da zama a unguwar (Area3). Yana da manyan
kamfanoni da sa hannun jari kala-kala da hotal hotal da gidajc a
Kasashen duniya ma yana da sa hanuun kamfanoni.
Sanna kuma yarda na samau labari, ance shine mutumin
da ya sa hannun jari mai yawan gaske aka gina hotal din (Nicon da
Sheriton), sannan da kamfanin P.Z. ke da dai sauran kadarorin da
ban tsaya binciken su ba. 8
Ambassador Alhaji Najib Ahmad Bauchi, ya rasu tun
Mustapha na dan shekara ashirin da biyu a duniya a sanadiyyar
hatsanin jirgin sama, a hanyar dawowarshi daga indiya, inda ya kaı
matarshi gaisuwar mahaifiyartaa can indiya, yanda na samu labari,
ance har Mustapha ya shiga jirgin sai mahaifiyarshi tace
abannatashi wajanta domin ya kara sabawa da 'yanuwanta sosai.
Nan take Ambassador Najib yace fita, anma ayi gaggwar
mayar dashi Nigeria saboda makarantarshi, duk da ance ba kasar
yake karatu ba, a Switzerland, yana kokarin hada digirinsa na biyu
(M.B.A) duk da a lokacin shekararsa ta farko yake a karatun nasa.
Wannan tahowar ce Allah yayiwa Ambassador Najib Bauchi
rasuwa. Rasuwar mahaifinshi bata hanashi ci gaba da karatun shi
ba, a sakamakon wani aminin mahaifinshi Alhaji Nafi'u Sani.
yanda mutane ke bada shaida, Alhaji Nafi'u shi ya zauna kujerar
mahaifinsa ta taliyar da harkokin gida da na waje, an kuma bada
saidar ya rike mashi dukiyarshi akan amana.
Yanzun haka shike juyawa Hajiya Hindatu tata dukiyar, shi
kuwa Mustapha, yana Karasa karatunsa. Alhaji Nafi'u ya damka
mashi taga dukiyar, amma yanzun haka Alhaji Nafi'u yana kulawa
da Mustapha sosai, gashi tare da danshi suke, shine aminin
Mustapha, tun ma kafin baban Mustapha ya rasu tare suke da Jabir.
tare sukayi karatunsu a kasar waje, sai kace Jabir dan Alhaji Najib
ne.
Sai da ma ya rasu sannan mutane suka fahimci ba dan Alhaji
Najib bane, dan amininsa ne, yanzu haka magana, da nike maki
Mustapha shekarunsa na haihuwa sun kai talatin da shidda, tun ana
tilasta mashi yayi aure, har ma ansa masa ido, ba 'yammatan da
ba'a bashi ba turawa, indiyawa, hausawanmu ne, amma yaki
kodaya.
Kullum dai yace wai su tayashi addu'a in sha Allahu zai
kawo masu yarinyar da yake so, amma zancan nan da nike maki
amininsa Jabir yayansa uku, Zaharaddini, Nafi'u, Walid kenan, sai
yar mace Saddiqa"
"Ke kuwa Halimatu ya za'ayi yayi aure mutumin dake da
kudi, ko mace ashirin yace yana so lokaci daya za'a kawo mashi
su ya holewarshi da su, da safe ya fito ya nunawa jama'a shi
mutunmin kirki ne, ke ki dubi irin bakaken motocin da suke binshu
9
a baya tamkar wani shugaban Kasa, sai la kiga motoci gorma na
bınshi a baya, cikinsu kuma duk kwakwarki baki gane wacee yake
ciki balle ki sa ran ganinshi.
In ba yasan yana tabka abin kunya ba mai zai hana ya dinga
zuge gilashin motarsa ana ganinshi, amma kullum sai dai bakin
gilashi, ni fa har Daddy nace wa dama sun sa an kamashi an
bincikeshi ko dai banda kudin akwai mafiya.
Sai Daddy yace mani wai gwamnatin mu ta yarda da
kasuwancinsa, wai ma yana daya daga cikin wadanda Nigeria ke
takama dasu" Halimatu ta langwabe kai " Hanida na fahimci sam
baki son abinda nike so, amma ta wani bangaren bani ganin
laifinki tunda baki san soyayya ba, balle meye so, amma kuma
game sharhuliya da kike tsammanin yanayi, bazan musa maki ba
saboda in ma na musa maki zaki ga kamar dan ina sonshine.
Hamida a yarda shaidar jama'a ta nuna, bai taba ganin wata
budurwa yace yana soba to balle ta kaishi ga kwana da wata mace,
amma tunda ba tare dashi nike ba, ba zanyi saurin kareshi ba
amma dai dai gwalgwadon nayi bincike sosai a kanshi, amma duk
shaida daya aka bani. Yanda ma ake nuna mani harkokinshi ma
basa b rinshi wata soyayya, balle sakarci.
Bınkicena ya gano mani har gidanshi unguwar (Asokoro)
gidanshi, fa a tsayi yayi kilometa "biyu akace" fadi kuwa ma yayi
kilometa uku) ance daga get din gidanshi zuwa get na biyu sai ka
hau mota to balle shiga cikin gidanshi, ni dai dama hango get din
gidan kawai nayi, gidan mahaifiyar shi ne na unguwar "(arca3)"
din shine na taba shiga shima cikin wata kunya ta musulunci da
taje neman taimako wajanta, ita na samu na bi muka shiga na
ganta.
"Chabdi, wai duk ina, kika je har kikayi wannan binkicen ba
tare da na sani ba" "kina gidanku, ganin baki damu da halin da
nike ciki ba shi yasa ban damu da ki sani ba ni kuwa in gaya maki
gaskiya da in rasa Mustapha gara mutuwa ta," nayi saurin rufe
bakinta," Halimatu baki da hankali ne? sai kawai ta fada jikina
lana wani irin kuka.
A hankali na dago Halimatu sai naga ashe kuwa kukan gaske
take yi; "wallahi Hamida da gaske nakeyi ina son Mustapha dan
Allah ki taimaka mani, wallahi kome kika ce in baki zan baki in
10
dai zaki hada ni da Mustapha, mutuwa zanyi Hamida,
mutuwa
Na dafa kafadarta "Halimatu kalleni," ta kallni" ni Hamida
nayi maki alkawarin hada ki da Mustapha ko ta halin yaya ne ko
da kuwa rayuwata zata salwanta, ko da zan rasa iyayena da duk
wanda na mallaka, in har dai na cika wannan alkawarin to zan
zamo cikin farin ciki a rayuwata."
"Hamida ba zancen rasa rai ko iyaye, in dai haka ne, kara ayi
guda daya, gara ni in rasa nawa ni kadai," "a'a wannan alkawari
ne na dauka tsakamina da Allah, yanzu Allah ke bina bashin
alkawarin da nayi mashi ba ke ba, iyakata da ke ki tayani adduar
Allah ya taimakeni in sauke nauyin da na dauka, a wajan Allah.
Nayi alkawari cire tsoro ko shakko, ko tsoron ace mani yar
iska, ko wani abu maka-mancin haka, matsawar dai in nayi zan
cika alkawari da na dauka tsakanina da Allah, sannan daga yau mu
dinga addua'ar Allah ya tabbatar da alheri a tsakanin ku"
"Sannan Hamida dan Allah ki reke mani amanar kada ki
kuskura wani ya sani gidanmu da naku, dan Allah amana na baki,
ki daukar mani wanan amana da alkawari kirike" na daukar
maki Halimatu. Ni Hamida nayi alkawarin rikewa Halimatu
amanar data bani, tare da cika mata alkawarin da na daukar mata,
wanda yanzu sun koma tsakanina da kai Allah, Allah ka taimaka
mani."
Sai dai kuma akwai wani abu daya, shine ki rike mani nima
tawa amanar kada ki gayawa kowa, tunda kinsan yanzu dole ne in
saka takalmin yawar neman Mustapha kafin akai ga yakin neman
zaben ya yarda da abinda muke nema a gareshi in an tambaycki
gida ina nake zuwa, ki san abinda zaki fada" "in sha Allahu na
daukar maki alkawari nima”.
"Sai kuma ki dinga sawa zuciyarki samu da rashin samu
saboda kinsan fa duk kokarin mu, Allah ya riga ya rubuta komai
da zamuyi. Sannan ya riga ya gama rubuta ko waye mijinki dan
haka mu nan lalube ne zamu yi a duhu, saidai Allah (SWA) yace
rokonni in amsa maka dan haka mu ci gaba da addu'a ba dare ba
rana. Kiyamallailin tsakardare Allah ya bamu sa'a. In kuma
Mustapha ba alheri bane, Allah ya sauya zuciyatki ta so wanda
yake alheri a gareki, zan baki addu'o'i ki kema kiyiwa kanki"
11
"To na gode Hamida, (amına ni a ganina da in rasa
Mustapha nayi maki rantsuwa kara mutuwata Hamida) "to ni irin
wannan maganganun ne bana son kina yi, wallahi sai in warware
alkawarin da nayi maki yanzu yanzu" abin mamaki sai kawai naga
Halimatu ta tashi ta tsuguna gabana tana yafa hannuwa saman
kafadarta, wai ta tuba da hawayenta sharaf sharaf a fuska, nayi
saurin kamata na rungume a jikina nace mata shikenan da wasa
nake.
Lallai so babbar cuta inji Sulaiman din Ni'ima na karanta a
littafin So Babbar Cuta, gashi yau anayi a gabana. Haka muka
daura alkawari da amana da Halimatu, ni kuwa har muka tashi
daga makaranta tunani nake yi ya zanyi da wannan lamarin mai
wuyar gaske.
*** ***
Wai Hamida wa sunana? Hamida Haruna Masari shine
:ikakken sunana, wanda a yanzu haka muna zaune a Abuja
Babban bi nin tarayyar Nijeriya, amma fa aiki ya kowomu Abuja.
Asali ı garin iyayena shine Masari a karamar hukumar kour
dake cikin jahar Katsina. In an binkita anan za'a samu kafur
karamar hukumar jahar Katsina ce.
Mahaifina Alhaji Haruna Masari haifaffen cikin garin Masari
ne, auran zumunci ne tsakanin shi da mahaifiyata, abotakar wasa ta
shiga tsakaninsu, kenan dan mace da 'dan namiji suke.
Ina son Allah ya kaika Masari da ka taka kafarka