Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kike so zan sanar da shi Bin Abdullahi ɗin ya nemo miki miji” ya furta yana mai miƙe wa ya fita ya bar ni cikin ɗumbin tashin hankali.Dakyar na samu jarumtar tashi,zuciyata a cunkushe na je na shiga mota dakyar nake driving ikon Allah ne kawai ya kai ni gida.Ina fita na shige ciki,Daddy da Momy duk suna falo amma ban gaishe su ba.Kan bed na zube ina mai fashewa da sabon kuka,a haka Momy ta shigo ta same ni. “Auta lafiya meke damunki?” ita ce tambayar da ta yi mini tana mai zaunawa bakin gado.Rungume ta na yi gammm kafin na ce “wata ƙawarmu ce ta rasu” “Ayya! Allah ya jiƙanta ,ke kuma addu'a ya kamata ki yi mata mamaci bai son ana yi masa kuka” Momy ta faɗa tana shafar fuskata,kai na jinjina mata kafin na miƙe na shiga toilet.Iya hijabi kawai na cire na je na tsaya ƙarƙashin shower na sakarwa da kaina ruwa,na lumshe ido ina jin zuciyata duk babu daɗi. Kalaman Sheikh Rayyadeen tamkar cida haka suka dinga kutso kwanyata suna firgita ni.Na toshe kunnuwana kafin na zube ƙasa dirshen ina yi wa kaina tambayoyin da babu mai bani amsarsu “shin mene ne laifina don kawai ina sonsa? Ni kaɗai ce nake da irin gurɓataccen tunanin na kasancewa da wanda nake so ko kuwa duka masoya haka suke ji?” ganin wannan ba za ta fishe ni ba na miƙe na cire kayan jikina,tsarkake jikina na yi sannan kuma na haɗa ruwan ɗumi na shiga na kwanta kamar daga sama haka na soma jin yanayin nan yana fizgata na son lulawa duniyar da ban san taƙaimaimai ina ne ba amma na bata suna kawai MAFARKI domin a cikinsa ne kawai nake tsintar kaina. Yau kuma cikin wata ƴar ƙaramar buka ce nake mai ɗauke da wasu tarkace irinsu;ƙaho,ƙaton kan bijimin sa,fatun namomin daji daban-daban,kwari da baka na ƙashi,wasu abubuwan ma ban san sunansu ba. A kwance nake kan baƙar fatar akuya,an yi wani circle da kyandir duk sun zagaye ni.Kusan kaina Nina ce a tsaye sai manyan idonta take juyawa,can kusan ƙafafuna kuwa Ummah ce Kakata riƙe da wata ƙwarya. “Lokaci yayi” cewar ita Nina ɗin.Sai kawai Ummah ta soma zuba mini ruwan da ke cikin ƙwaryar tana bin duk illahirin jikina tana zubawa duk ɗigo ɗaya in sun taɓa fatata wani irin shock ne nake ji kamar lantarki ya kama ni.Ana zuwa daidai kaina ji na yi kamar raina zai fita ,ana gama wankan kuma sai aka kunna wani turare wanda bai da hayaƙi sai dai ƙamshinsa wasu kalamai Ummah ke furtawa waɗanda ban san mene ne ma'anarsu ba. “Barka da shigowa wannan duniya!” Nina ta furta tana mai kwantowa jikina,kamar yadda ruwa ke shiga ƙarƙashin ƙasa haka Nina ta ɓata a cikin ɓargona.Na ja wani dogon numfashi wanda ya yi daidai da wanzuwata a wani wurin,ƙofar wani gida ce ina tsaye daga gefe ina kallon abincin ruhina Sheikh Rayyadeen tare da wata budurwa .Na ƙarasa kusa da su ina mai ɗauke budurwa da mari tare da yi mata kashedi “ Sheikh Rayyadeen nawa ne ni ɗaya,ba kuma zan yi sharing nasa da wata ba” “Ni kuma ba ni sonki,kuma ba zan taɓa aurenki ba” Sheikh ya furta mini yana jifata da kallon tsana,hawaye suka soma bin kumatuna daidai nan na farka .Wani abin mamaki kuma da kuka na tashi kamar wata yarinyar goye,na yi saurin tashi na fito daga cikin ruwan na yi alwala kafin na ɗaura towel na fita. Kayan bacci na saka,na yi sallar magarib da isha'i sannan na sauka.Falon babu kowa sai Ummah a zaune ta saka tv a gaba tana kallon India Film ,na ɗan yi murmushi ina mai cewa “ƙawali kallo ne ake yi?” Ta dube ni kafin ta ce “sai yaushe za ki sanar da shi kina sonsa?” Mai shirin kuka an jefe shi da kashin awaki,kawai sai na faɗa jikinta ina hawaye.“Akwai wacce take so tun tuni” “Shi ya faɗa miki hakan ?” “A'a a gabana ta sanar da shi” “Je ki ci abinci to” ta furta tare da miƙewa tsaye tana yi mini wani irin kallo,da sauri na kamo hannunta ina mai cewa “na yi miki alƙawari gobe zan sanar da shi” sai ta yi wani murmushi tana shafar kaina,sai dai fa ba normal shafa ba ce a'a ina jin wani ɓoyayyen sirri na ratsa ni wanda ya mantar da ni duk wata damuwata. Da hannunta ta bani abinci mai magani,a ɗakinta kuma na kwana a wannan daren.Wanda a cikinsa abubuwa da dama sun faru,Ummah ta koya mini abubuwa da dama duk da cewa cikin MAFARKI ne amma gaskiyar magana ita ce komai reality ne. Washegari da wani irin ciwon kai na tashi,sai dai ban san dalili ba don duk mafarkan da na yi na manta su. Bayan na yi sallar asubah kitchen na shiga na taya ƴar aiki girka abin da za a yi breakfast kafin kuma na haura sama na yi wanka tare da shirin makaranta,karon farko a rayuwata da na ɗauki turare mai ƙamshi na fesa a jikina shi ma ɗin ina son bar wa Sheikh Rayyadeen aiki ne ina son ya riƙe ƙamshin turarena ta yadda ko ina zai ji shi sai ya tuna da inda ya fara jinsa kamar dai yadda ni ma ya zautar da ni da nasa turaren. Ko da na fito sai Ummah kawai a falon tana tsaye tana kallon saman ɗakina da alamun ni take jira.Ina zuwa ta jawo ni tare da dangwala mini wani abu a tsakiyar goshi sai kuma baƙin kwalli da ya kasance ban ɗauke shi abin ado ba ban saba shafa shi fa.Wannan yasa sai da aka sha daga sannan na bari ta shafa mini shi,na turo baki gaba ina cewa “haba dai ƙawali kamar dai abin tsafi” “Soyayyarki tsabtatacciya ce ƙawali babu wani tsafi da zai shigo ciki, wannan fa kwallin Momynki ne na karɓo .Kuma tsaya ki gani yadda zai yi matuƙar tasiri kin san ido na ɗaya daga cikin abin da ake amfani da su don isar da saƙon so” Ummah ta faɗa . Na ce “kenan ba da baki zan furta masa ba?” Ummah ta ɓata rai tana mai cewa “au da kin zata ki furta masa nake nufi?” Ban ce komai ba na wuce,yau dai direba ya sauke ni .Na kai dubana a parking special,babu motarsa duk sai na ji babu daɗi.Da na shiga aji Mujahida na gani,ta taso kamar kullum za ta rungume ni amma na ture ta tare da yin gaba na bar ta tsaye. Zaune na yi tare da fiddo littafi na soma dubawa amma a zahiri ba karatun nake yi ba. “Ki yi haƙuri don Allah wallahi banda wani zaɓi ne shi yasa na sanar da shi” Mujahida ta faɗa tana mai yin zaune kusa da ni .Ban ɗago ba haka kuma ban ce mata komai ba sai ita ce ta ci gaba da cewa,“wallahi tun jiya da na tafi gida na kasa sukuni na so ma kira ki sai kuma aka yi katari banda kuɗi a layina ga kuma Ya Hamza bai kira ni ba ballantana na sanar da shi” Miƙewa na yi a hankali na fita na bar mata ajin,can wajen wasu shuke-shuke na nufa na zauna ina kallon yadda ruwa ke faltsa suna zuba kan ciyayi. ★SHEIKH RAYYADEEN A ɓangarensa kuwa sosai ya ji zafin yadda ƙanƙanuwar yarinya irin Khadeeja har za ta iya yin gurɓataccen tunani a kansa.Zuciyarsa har azalza take yi yana jin kamar ya kama da wuta don baƙin ciki,yana isa gida yayi parking tare da bai wa masu kula da gidansa key ya ce a wanke motar. Yana shiga falo da kukan Rashida ya soma cin karo, wannan yasa ya nufi ɗakinta da sauri.A takure ya same ta wuri guda tana ƙanƙame jikinta ga Ammy a tsaye riƙe da kofin ruwa. “Malamin da Abbanku ya ce zai yi mata karatu yanzun nan ya fita,shi ya bada ruwan nan a bata ta sha” Ammy ta faɗa kamar za ta yi kuka. Sheikh ya karɓi kofin,ya je a gabanta ya tsaya kanta ya kamo yayi Bismillah ya soma bata ruwan idonta ta zuba masa waɗanda da a ce ya lura da kyau da zai gane sak na Grand-Maa ne don ba su bar komai daga siffarsu ba. Abin da Sheikh Rayyadeen ɗin kawai ya iya tsinta cikinsu shi ne zallar sonsa,ya yi saurin kawar da kai kafin ya janye kofin daga bakinta don tuni ta shanye.A nan ta ɓingiri ta shiga yin baccin wahala. Sai a lokacin suka gaisa da Ammy kafin su fito,ta ce “ɗazu Mamarku ta zo nan har sun fara kawo kaya” Ya ce “babu damuwa zan shiga daga ciki” Ammy ta yi saurin tsayar da shi tana mai cewa “amma ya na ga kamar ranka a ɓace?” “Babu komai Ammy kawai gajiya ce” ya bata amsa kafin ya wuce sama.Kayan jikinsa ya rage ya shiga toilet don yin wanka saboda magarib ta gabato.Bayan ya gama wankan gaban mirror ɗin da ke cikin toilet ya ja ya tsaya yana ƙarewa faffaɗan ƙirjinsa kallo,yayin da kuma rashin kunyar Khadeeja ke keta tunaninsa.Da ya ji ransa na shirin ƙara ɓaci sai kawai ya fita,ya shirya cikin jallabiya ya fesa turare tare kuma da ɗaukar dadduma ya fita don tuni an soma kiran sallah .Ba shi ya dawo ba sai bayan isha'i,yau kwata-kwata bai da ra'ayin cin abinci abu mai ɗan sanyi yake so hakan yasa iya zoɓo kawai ya sha ya wuce ɗakinsa,ita ma Ammy ba ta wani takura masa ba sai kallon tausayi da ta bi ɗan nata da shi. Kan bed ya hau tare da kunna system ya soma yin bincike kan madu'in da zai yi wa'azi a wannan juma'ar.Duk yadda yake son ajiye hankali wuri guda abu ya cuttura kalaman Khadeeja ne kawai ke yi masa yawo,can kuma saƙon text ya shigo sai ya ga sunan Maryama.Sallama ce ta yi masa tare da gaishe shi,a duniya ya tsani mace marar aji shi yasa kaf ƴan matan da ke kawo masa tallar kansu yake jin ba zai iya soyayya da su ba. Ya ja tsuki a fili kafin ya danna kiran Sheikh Laminu,ringung biyu ya ɗaga yana mai yi masa sallama.Bayan ya amsa ne yake cewa “aboki kenan sai da ka bai wa yarinyar can lambata?” Sheikh Laminu ya tuntsire da dariya ya ce “Maryama ce yarinya? Fatan dai ba shirme ta yi maka ba? Ɗazu na shaida mata yadda muka yi da kai shi ne na tura mata hotonka da kuma lambarka ” Sheikh Rayyadeen ya yi shiru kafin kuma ya ce “okay!” sai ya kashe kiran,bai yi mata reply ba sai aikinsa da ya ci gaba da yi har kusan ƙarfe biyun dare kafin ya rufe system ɗin ya je yayi alwala yayi nafiloli.A nan kan dadduma yayi bacci mai cike da mafarkin Khadeeja,abin da ta faɗa ɗin dai ne ya faru wato yana rungume da ita ya saka ta a ƙirjinsa suna kwance kan bed sai faman manne masa take yi tana ƙara dagula masa lissafi wanda hakan ta kai shi da raba su da suturar jikinsu har suka raya daren da soyayyar baki da kuma ta gangar jiki. Da ya farka ji yayi kamar ya kama da wuta,ga lokacin sallah tuni yayi don wasu masallatai har sun fara ga kuma yadda wanka ya hau kansa.Duk da sosai ya ji daɗin mafarkin amma kuma bai hana takaici kama shi ba yana daɗa jin tsanar fitinaniyar yarinyar wacce ta addabi rayuwarsa. Cikin woshin mashin ya saka kayansa da dadduma kafin ya tsabtataccen jikinsa,ko da ya tafi masjid iya raka'a ɗaya ya samu sai bayan an salamce ya miƙe ya kawo cikon sannan ya zauna yayi azkhar.Bai dawo gida ba sai da rana ta fito sosai,jikinsa duk a sanyaye don rabon da ya rasa sallar asubah tun yana ganiyar ƙurciyarsa. Sai da ya shiga kitchen ya gaishe da Ammy sannan ya je ya dubo Rashida yau tana zaune kan dadduma da alamu kamar hankalinta ya ɗan dawo jikinta. Sallamar da yayi ta amsa kafin ta ɗago ta dube shi cike da rauni,shi kuwa Sheikh sosai ya ji daɗin ganinta haka. “Ya jikin naki?” ya tambaye ta. Ta ce “da sauƙi Ya Sheikh ” kasancewar haka take kiransa saboda tun suna yara ta bar masa girman. Ya ɗan murmusa ya ce “Allah ya ƙara miki lafiya ƙanwata” Ita ma murmushin ta yi kafin ta ce “amin!” addu'o'in da ya saba yi mata ya yi kafin ya juya,har ya kai bakin ƙofa ya ji muryarta tana cewa “ina ɗalibarka wacce na gani ranar nan?” Da wani irin sauri ya juyo ya dube ta,kafin ya ce “wace ɗaliba? Ai suna da yawa” Ta girgiza kai ta ce “ka san wacce nake nufi Ya Sheikh ” ta ida furicin tana mai yin kwanciya,kafin ma ya kai ga yin magana tuni Rashida ta yi bacci. Da wannan abin al'ajabin Sheikh ya nufi ɗakinsa,sai da ya sake yin wanka sannan ya shirya cikin fararen kaya yau kuma baƙar alkyaba ya saka da jan hirami ya feshe jikinsa da turare sannan ya sauko. Ammy ta tarbe shi tana mai cewa “ga abincinka nan na kawo ma tsakiyar falo ” “Azumi nake yi Ammy ” ya bata amsa. “Yau fa Laraba ce” ta faɗa da ɗan mamaki. Ya ce “eh na sani Ammy,na tafi sai na dawo” “Amma Deeni...” yayi saurin katse ta da cewa “Ammy na makara ƙarfe takwas saura kuma sabbin ɗalibai ne da ni ” “To a dawo lafiya” “Amin” Haka ya fice ya shiga motarsa,yana gudu yana ta nazarin maganar Rashida sai mamaki yake yi kan cewa da ta yi wai ya san wace ɗaliba ce yake nufi.Yana shigowa harabar makarantar ya ga yadda ruwa suka fara ɓullo shuke-shuken suna shigowa har inda babu su.Sai da ya fara yin parking ɗin motar kafin ya fito ya nufi can. ★ Ruwa na ɗaya daga cikin abin da ke bani sha'awa,yadda suke faltsar ba ƙaramin burge ni hakan ke yi ba.Wannan yasa da mai gadi ya kashe pampon sai na ji haushi,yana gusawa na je na sake kunnawa tare da tsayuwa ina kallo daga ƙarshe ma jakata na ajiye na je ina saka hannuwana a ruwan ina wasa. Ba zan iya ƙa'ide lokacin da na ɗauka a wurin ba,na shagala sosai a wasar kafin na soma ganin wata narkekiyar tsutsa tana fitowa na miƙe da sauri ina mai yin wata irin razananiyar ƙara na yi tako ɗaya ƙafata ta zame na yi tuntuɓe tare da yin gaba,sai dai ban faɗi a ko ina ba sai kan ƙirjin Sheikh Rayyadeen wanda ban san me ya zo yi kuma a nan ba .Tsabar ruɗewar da na yi shi ya mantar da ni tsoronsa da nake yi,ƙanƙame shi na yi gam igiyar numfashina na soma cirewa,“maci..ma .cijiii!” na furta,ina jin lokacin da yake bubuga fuskata cikin ɗimuwa yana cewa “kar ki rufe idonki! Kar ki some mini” idon nawa na soma ƙoƙarin buɗewa ina ɗan juya su,sai dai firgicin da ya kame mini zuciya shi ya hana ni yin yadda yake so ɗin.Ba zan ce na suma ba,haka kuma ba zan ce ɗari bisa ɗari ina cikin hayyacina ba sai dai ina ɗan tsintar maganar mutanen da tuni hankalinsu ya kawo gare mu. Ina jin lokacin da yake cewa “ku zo ku kama ta kuka wani tsaya kallona” sai kuma na ji an ciciɓe ni ana tafiya da ni yayin da kuma amon muryar Sheikh ke ratsa kunnena yana yin masifa.Daga nan ne na ji ɗif,ban san kuma wane lokaci aka sake ɗauka ba kafin na ja ajiyar zuciya na buɗe idona Sheikh Rayyadeen na gani riƙe da kaina yana yi mini karatu. “Ta buɗe idonta” muryar Mujahida ce wannan karon,sai ya saki kan nawa tare da tashi ya wani juya mana baya.Na tashi a hankali ina kallon ƙawata wacce idonta suka yi ja da alamun ta sha kuka,hannuna ta kama ta miƙar da ni sannan muka nufi ƙofa na ɗan juya domin satar kallonsa daidai shi ma ya juyo idonmu suka sarƙe cikin na juna.Daidai nan free page ya ida duk mai son ci gaba zai iya biyan 300 kuɗin normal group,ko kuma 500 na VIP group via 2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBANK DM +22795045822 *NB:* Yanzu nake rubuta shi banda complete ɗinsa,in kina da niyyar shiga group ki tura kuɗinki kai tsaye ki bani receip Ni kuma zan saka ki group.Daga lokacin da book ya kammala zai koma 1k. 18 Disamba 2025. [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 01 Sakacin iyaye na ɗaya daga cikin abin da ke jefa rayuwar yara yin mu'amala da aljanu tun suna ƙananu ba tare da an ankara cewa wannan illa ne ba. Sunana David,ɗan farko gun wasu shagalalun iyaye waɗanda suka mayar da sa'insa abin ado,cin amanar juna ruwan sha,wasa da tarbiyyar ƴaƴansu tabi'arsu.Shekaruna ashirin da biyar kacal a duniya amma in aka ganni za a iya bani shekaru talatin saboda yadda ƙwanjina ya buɗe silar aikin wahala.Tun ina ɗan yaro mahaifiyata ta rataya mini nauyin kula da ƙannaina,tun daga yi musu tsarki,wanka da kuma basu abinci a baki madadin ita ta yi.Komai tsawon dare in ƙanena yayi bahaya ni ne ke zuwa na wanke masa na kuma kai banɗaki na zubar,babu wata addu'ar neman kariya ko wani furici da zan furta domin gusar da wani abin cutar wa a irin haka ne na haɗu da wata baƙar siffa wacce duk da ƙanƙantar shekaruna bai hana na fahimci wannan ba bil'adama ba ce. A tsaye nake tsakiyar banɗaki hannuna riƙe da fo ,yayin da kuma siffar ke tsugunne kan inda mutum ke hawa don yin buƙatarsa.A lokacin wani irin tsoro ya ziyarce ni,sai dai tamkar itaciya haka na kasa motsi sai ma ido da na ƙanƙance ina ƙarewa siffar kallo.Mace ce a zubin halitta don ga dogon gashinta nan ya zubo har yana jan ƙasa,fuskarta baƙa ƙirin ce mai ɗauke da wasu ƴan ƙananun ƙahonni daidai gefe da gefen hanci,bakinta a buɗe yake wanda hakan zai iya baka damar ganin dogayen haƙoranta biyu da suka zarce sauran.Duk a cikin duhun daren idanuwana suka bani ikon ganin wannan ikon Allahn,a hankali na ga ta taso ta zo gare ni ba tare da ta ce komai ba ta karɓi fo ɗin hannuna sai ta ɗora babban yatsanta a tsakiyar goshina wani irin abu na ji mai mugun zafi ya ratsa ni wanda yasa na fita hayyacina.Ko da na farka Ummah na gani gefena tana jiƙa wani zane a ruwa tana ɗora mini yayin da kuma idonta suka yi ja alamun ta yi kuka.Muna haɗa ido da ita ta ce “Davido?” a cikin muryarta na tsinto tsantsar tausayina,a bakinta kuma na ji cewa an same ni a yashe ga ƙasa daidai ƙofar banɗaki . Mahaifina ya matso yana cewa “har yanzu jikin nasa da zafi?” “Eh kamar gawarshi har wani tiriri ke tashi,dubi hatta ruwan da nake tsoma zanen sun ɗauki gumi” Ummah ta faɗa tana matsar ƙwalla. Abba ya ce “ki goya Joy mu tafi mu kai shi gidan mai magani” ba ta ce komai ba haka ta ɗauki ƙanena Joy wanda bai rufe murfin shekara biyu ba,ni kuma Abba ne ya saɓe ni zuwa gidan mai magani. Tun da muka shigo farfajiyar gidan idona suka soma yi mini gane-gane.Abin da ido bai kamata ya gani ba ni ras nake ganinsa,duk mutanen da suka zo babu lafiya kallo ɗaya na yi wa kowanne daga ciki na hango matsalarsa.A bisa bangunan gidan mai magani kuwa kamar yadda ƙadangaru ke yawo haka ko ta ina aljanu ne ƙanana da manyansu.Lokacin da muka shiga cikin ƴar bukarsa kuwa muna haɗa ido da shi na ga ya ɗan tsorata,amma sai ya ɓoye tsoron tare da bada umarnin a kwantar da ni kan tabarmar da ake shimfiɗe majinyata.A ido tabarma ce,amma a baɗini bijinmi wani dodo ne,bai tambayi iyayena abin da ya faru ba amma sai ni ya tambaya shi ɗin ma ba ta baki ba a'a ta ido. “Wane ne kai? Me kake so a gare ni har ka bari aka kawo ka wurina alhalin ka fi ƙarfina?” su ne tambayoyin da idonsa suka watso mini amma ni sam ban basa amsa ba,kuma ban san dalilina na yin haka ba.Ƙila shi kuma ya fahimci har zuwa lokacin ƙarfin ikon da ke jikina ban fara yin aiki da shi ba ne ko kuwa tasirinsa bai bi jikina ba ne oho,sai ya ɗauko wata ƙatuwar laya ya ɗaura ta a damtsena tare da cewa “zuwa saukowar zazzaɓin rana duk wannan zafin jikin nasa zai sauka zai kuma samu lafiya” Abba ya basa kuɗi amma ya ƙi karɓa a haka muka dawo gida.Kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa haka ta faru,ina warware wa kawai sai na fara walwala tare da mantawa da wannan siffar da na gani .Yayin da kuma Abba da Ummah suka dasa rashin mutumcinsu daga inda suka tsaya,dama iya na ɗaya rana ne ba su yi masifar da suka saba ba da yi wa juna gori wasu kalaman sam ba su dace ba. A lokacin da na shiga zangon shekara goma sha biyar a duniya na soma yin aikin ƙarfi don ciyar da ƙannaina biyu Joy da kuma Joyel wacce ta kasance autarmu.Tamkar mahaifi haka suka ɗauke ni,da zarar na shigo haka suke zuwa da gudu su tarbe ni da murna iya wannan annushuwar da nake gani a tattare da su shi ke wanzar da nawa farin cikin har izuwa yanzu da nake ganiyar shekara ashirin da biyar. “Ba ka da aikin yi kullum sai shan giya da bin mata a hakan wai kai miji ne” “In ba miji ba ne ni ai ba zan baki yara har uku ba” “Uwar me kake yi wa yaran ? ” “In ban yi musu komai ke da ke uwarsu ai ina yi miki wata tsiyar da har ta sa kika kasa barina kika manne mini” “Zancen banza yo kar ka sake yi,ka zata kai kaɗai ne namiji a duniya?” “Kenan dama abin da nake zargi gaskiya ne kina cin amanata?” Wannan ita ce sa'insar da iyayenmu suka tashi da ita a safiyar yau duk sun cika mana gida da surutunsu da babu daɗin ji.Cike da ɓacin rai na tashi daga kwancen da nake ,tun ina haƙurin saurarensu har na kasa jura na tunkari ɗakinsu.Ban ɗaga labule ba,a bakin ƙofa na ce “don Allah ko za ku iya yi mana shiru ko mun samu mu yi bacci cikin salama?” Daga can cikin ɗaki Ummah ta ce “kan ubanka! Haifarmu ka yi da za ka bamu umarni?” Shi kuwa Abba wata irin dariya ya yi kafin ya ce “ai shi ne daidai ke tun da ke ma ɗin ba mutumci ne da ke ba ga shi nan kin haifi ɗan daba ” “Ko ma dai mene ne babu ruwanka da ɗana ” “Ni ma ai nawa ne ina ce ni ne ubansa ko?” “Wa ya sani abu cikin duhu!” Ummah na faɗar haka na gusa daga gurin.Ƙofar gida na fita na zauna kan dakali ina jin zuciyata duk babu daɗi. Wani irin yammm! Yammm! Na soma jin ƙafata na yi mini ko da na duba sai na ga tururuwa ce duk ta yaɓe mini ƙafa kamar ta samu wani suga.Girgiza ƙafar na yi amma ko ɗaya ba ta faɗi ba kamar ma an sa super glue ne a manne su.Da sauri na kai hannu don kakaɓe su sai dai wani abun mamaki bayan na shafa ƙafata sai na ga wayam babu komai kuma ba su zuba a ƙasa ba.Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya ziyarce ni,dole na miƙe na koma cikin gida na cika bokiti da ruwa na kai banɗaki .Ina tsaka da yin wanka na soma jin wani irin yanayi wanda tun da nake zan iya cewa sau ɗaya tak na taɓa samun kaina a cikinsa shi ɗin ma a mafarki a lokacin da na shiga zangon balaga. Idona a rufe suke na goga sabulu ban wanke ba,yayin da kuma nake jin tamkar ana shafar duk illahirin jikina ana yi mini abin da ban taɓa jin makamancinsa ba.A wannan lokaci ba zan iya tantance ina cikin hayyacina ne ba ko kuwa ya gushe,abu ɗaya zan tuna shi ne na samu kaina a matsayin namiji har na samu nutsuwa,sai dai da wa? Ban sani ba.Ina dawowa cikin tunanina na ida yin wanka,na fito na je ɗakina na shirya .Ciwon kan da ya sauko mini tuni na neme shi na rasa,na fito kenan zan fita neman kuɗi sai ga su Joy sun fito su ma cikin

Chapter 8 of 14