Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce zai zo a makare a shaida muku ku fara yin karatu kamar yadda ya tsara muku” yana gama faɗar haka kuwa aka fara yin karatun sai dai yau ɗin ma Sadiya ce ke son lallai sai ta koyar da ni amma na ƙi. ★SHEIKH RAYYADEEN Tun bayan da ya fito daga gidansu Khadeeja ya nufi wata makaranta da yake bada karatun dare zuciyarsa fal takaici da haushin Deeja.Ya hau ya zauna kan cewa raina shi ne ta yi shi yasa har take basa umarni,umarnin ma na ya saɓawa Ubangijinsa yayi ƙarya.Sosai ma yayi mamakin cewa ƴar malam Ben Abdullahi ce,don su haka suke kiransa .Ya ja tsaki ya fi shuren masaki,yana jin inda ma da ta ce yayi ƙaryar kwashe ta yayi da mari.Yana isa makarantar kafin ya shiga ciki sai da yayi sallar isha'i sannan ya wuce ya koya musu bayan nan ya dawo gida.Yau ba tare da shi aka ci abincin dare ba wannan yasa bai san abin da ke faruwa ba sai da ya shiga babban falon sashensu ya tarar Ammy na zaune tana kuka idonta sun kaɗa sun yi ja sosai. Tun kafin ya ji dalilin kukan nata hankalinsa yayi matuƙar tashi,da sauri ya ƙarasa yana mai yi mata sallama tare da tambayar “Ammy lafiya me kuma ya faru?” Kamar wata ƙaramar yarinya haka ta jimƙe hannunsa gam tana mai ci gaba da yin hawayen da yake ɗaga masa hankali. Jijiyoyin kansa ne duk suka fito,ya ce “na sani yau ma Grand-Maa ce ta taɓa ki babu komai ni na san abin da zan yi, Please Ammy ki bar kuka” Ya faɗi haka tare da goge mata hawaye,ita kuma ta jinjina masa kai.Dakyar ya samu kanta ta shaida masa abin da ya faru,“Maa ta baiwa mahaifinka zaɓi ko dai ya sake ni ko kuma ita ta bar masa gidansa sai ya je ya canza uwa,shi ne shi kuma sam babu uzuri ko tambayar dalili ya hau ni da masifa har da cewa asiri na yi masa” ran Sheikh ne ya ƙara ɓaci sosai.Sai dai bai sanar da ita matakin da ya ɗauka ba,ɗakinsa ya shiga ya ɗauko mata maganin ciwon kai da na bacci ya bata ta sha babu jimawa kuwa bacci ya ɗauke ta. Babban falo ya fita ya je buga ƙofar ɗakin Saude mai aiki,bayan ta fito ya shaida mata yana son a yi masa aiki ne.Haka ya ja ta can zuwa sashen Ammy ta soma jera kayanta a trolly yayin da shi kuma ya kira amininsa Sheikh Laminu yana son a kawo masa babbar mota wacce za ta kwasar masa kaya,duk da shi ɗin bai ƙasar amma motocinsa ne haka yasa aka aiko mota biyu har da ma masu kwasar kaya.Sai ga shi abu kamar a mafarki ana kwashe kayan Ammy,hankalin Mama ne ya tashi duk da ta san abin da ya faru amma ba ta yi tsammanin gaske Abban yara zai iya sakin abokiyar zaman nata ba.Tambayar duniya ta yi wa Sheikh ya ƙi yi mata magana,ga Ammy sai bacci take yi sai bayan an kwashe abubuwan amfaninta kawai, ya tashe ta shi ma ba wai ta wartsake ba ne garas haka ya taimaka ya riƙe ta suka fita ya saka ta a motarsa,Rashida haka ya kai ta mota ita dama kayanta suna can gidan mijinta.A nasa ɓangaren ma kaf kayansa ya kwashe,motarsa ce a gaba yayin da na kayansu ke bin bayansa har suka isa babbar palace ɗinsa wacce ya gina domin matarsa da kuma ahalin gidansu sai dai kuma a dare ɗaya an rushe masa plan ɗin surprise ɗin da yake son yi musu. Duk wani abu da za a buƙata a cikin rayuwar ɗanAdam duk ya saka su.Lokacin da suka iso gidan ƙarfe ɗaya saura,amma tsabar yadda zuciyarsa ke tafasa haka cikin wannan daren ya narka musu kuɗi suka shiga jera masa abubuwansa da kayan jikinsa,na Ammy kuwa Saude ce ta fara shimfiɗa zanen gado suka kwantar da ita kafin ta soma aikin amma yadda bacci ya fi ƙarfinta haka ta haƙura ba ta yi shi ba. A ɓangaren Sheikh kasa baccin yayi,baƙin ciki ne iri-iri ke taso masa dakyar ya iya tashi ya nufi danƙareren benen saman da yasa aka gina masa duk don domin shi da matarsa ,amma ga shi an dawo babu ita a ciki.Haka ya soma ƙarewa ɗakin kallo tun daga kujeru har labulaye da capet sun machin,ba kuma sai an faɗa maka ba miliyoyin kuɗi ne aka kashe ba.A hankali ya taka ya shiga ƙaton bedroom ɗin wanda shi ma tsabar girmansa yasa sai da aka zuba masa kujeru sai dai wannan ɗin ɗaya ce mai katafaren girma kai kace ma wani gadon ne,a gabanta an ɗora capet mai taushi da ƙaramin banci na gilas .Shi kuwa gadon wasu labulaye ne farare tasss sun kai goma aka yi masa wata kwalliya da su ta yadda in mutum na ciki ba za ka sani ba. Wanka ya yi sannan ya shimfiɗa dadduma ya shiga jero nafiloli sam bai rumtsa ba ko kaɗan har aka kira sallah ya fita yayi,sai bayan ya dawo ne ya soma jin baccin kafin ya kwanta sai ya turawa shugaban makaranta saƙo.Sosai ya samu bacci mai daɗi ya ɗauke shi,ƴan magana na cewa abin da ka kwanta da shi a rai to shi kake mafarki hakan ce ta faru da Sheikh Rayyadeen ya yi mafarkin yayi aure sun tare a wannan gidan har da ma haihuwar yara biyu.Ko da ya farka kusan ƙarfe takwas na safe,wanka ya fara yi ya saka jallabiya ya sauko ƙasa amma da mamakinsa Ammy ya tarar a falon ita da mai aiki Saude. A hankali ya ƙarasa yayi musu sallama tare da gaishe su,yana zaunawa ita Sauden sai ta tashi yayin da shi kuma ya sunne kai yana mai cewa “yi haƙuri Ammy na san ranki ya ɓace da kika tashi kika ganki a wannan gidan” “Ko kaɗan raina bai ɓace ba Deeni,in akwai abin da ban ji daɗinsa ba shi ne ta yadda silata ka rushe plan ɗinka na sai ranar da za a kawo matar aurenka za ka shaidawa ahali su ma nan ɗin gidansu ne” Yayi wani ɗan murmushi wanda a cikinsa za ka iya hango damuwa ya ce “Ammy lokacin ina da burin auren Safara'u ne,na yi tunanin ita za ta ƙetarewa baƙar ƙaddarata sai dai ashe ita ce ma za ta rufe babin kwaɗayin yin aure a rayuwata” Ammy ta yi ɗan shiru kamar mai nazari kafin ta ce “ina yi maka kwaɗayin yin aure Sheikh Rayyadeen ɗina,kar ka taɓa yanke zuwan tsammani daga Ubangijin rahama”' Ya ce “na sani Ammy,ba wai na fidda rai ba ne a'a banda burin son ƴar kowa gudun kar na shafa mata kashin kaji ” “To ka auri Khadeeja” Ya wani dube ta da sauri kafin ya ce “Ammy ban sonta ” Ta ce “su ma ai sauran waɗanda ka yi burin aure babu wacce ka taɓa so Deeni” “Yunwa nake ji Ammyna,duk jiya ban ci komai ba” ya faɗa tare da jingina jikin kujera yana jin zuciyarsa na dokawa,tsoronsa guda ɗaya ne tak kar Ammy ta ɗaukin dogon buri ta ɗora kan sai ya auri Khadeeja.Bai so hakan ya kasance abu na farko da zai bijire wa umarninta,don shi kaɗai ya san matakin tsanar da yake yi wa Khadeejar.Sam zuciyarsa ba ta yarda cewa wannan za ta iya ma mata tagari ga mijinta ba ballantana uwar kirki ga ƴaƴanta,to ita kanta yarinya ce tana buƙatar a yi mata tarbiyya da kuma horon girmama manya,in son samu ne a bulalaye ta domin ta cire rashin kunya da tsaurin ido.Ya ja tsaki a fili tuna yadda jiya ta wani tsure shi da ido ko kunyarsa ba ta ji ba,tsabar iskanci kuma ko gaishe shi ba ta yi ba sai ma dai ƙawarta ce mai hankali ta yi haka. Ammy wacce ta zuba masa ido jin lokaci guda ya canza musu akalar zance,tana shirin tashi kuma ta ji yayi tsaki ita kuwa murmushi ta yi don tana ji a ranta tunanin Khadeejatu ne yake yi. Kitchen ta shiga ta haɗo masa abin da suka ɗan girka ta kawo masa,da mamaki ya ce “Ammy ina kuka samu gas ?” “Na mai gadi ne Saude ta karɓo ,shi kuma na aika ya sayo mini komai” ta basa amsa . Ya ce “in sha Allah zuwa an jima duk za a kawo komai na dangin abinci har da butalin gas ɗin” Ammy ta ce “Allah yi maka albarka ya kare ka,ta tsare ma dukiyarka ya kuma ƙara buɗi na alkhairi ” Ya amsa da “amin Ammyna na gode sosai” Bayan ya gama yin breakfast ɗin ya koma ciki,sai da ya sake yin wani wanka yayi brush ya fesa turaren baki sannan ya fito.Cike da nutsuwa ya shafa mai ya gyara saje da guminsa da kuma sumar kansa wacce take kwance luf irin ta larabawa.Yau ma fararen kaya ya saka,sai ya ɗora alkyabar maza mai ruwan ƙasa ya saka hirami ja.Tsadadiyar agogo ya ɗaura a hannun dama,ya saka takalmi ƙafa ciki irin rigarsa wani turaren ya ƙara feshe jikinsa da gemu kafin ya ɗora farin gilashi ya sauko ƙasa. A falo ya tarar da Ammy tana baiwa Rashida abinci,kusa da ita ya je ya tofa mata addu'a kafin ya yi wa Ammy sallama ya tafi.Tuni kuwa an wanke motarsa,ya shiga ya zauna bayan ya yi addu'a yana shirin tuƙawa Ammy ta fito tana tsayar da shi . Ta ƙaraso tana mai cewa “ga key ɗin motar Deeja ka kai mata” yadda ta game fuska babu hanyar yi mata gardama yasa shi ya karɓa kafin ya wuce. Ko da ya isa makaranta ƙarfe tara saura,sai da ya fara zuwa suka gaisa shi da malam Hafiz kafin ya je ya buɗe keɓaɓen ajin da yake tara malaman dukkan makarantar in yana son yin magana da su wanda su kuma ɗalibai suke yi wa lakaɓi da ajin hutun malamai. Yana buɗewa ya ga wani baƙin abu yashe a ƙasa,ya duƙa ya dauƙa sai ya ga niƙafi ce.Da mamakin ta ya aka yi ta zo nan ya je ya ƙarasa ciki,shaf ya manta da an kawo masa Khadeeja har na cikin babu lafiya.Cikin wata jakarsa ya cilla niƙafin sannan ya soma bincike har ya nemo littafin da yake so. ★KHADEEJA Ni ɗaya na buɗe alƙur'ani ina yin hadda,ban damu ba sam da ƙin zuwa a koyar da ni don ni ban ga wani aibun yin haka ba.Mujahidah kam an tafi ana ta yi mata gyara,sauran ɗaliban ma haka.A hankali na miƙe saboda yadda na ji zuciyata na tashi,bakin ƙofa na fito na tofar da yawu sai dai aka yi rashin sa'a suka sauka kan rigar Sheikh Rayyadeen wanda yake dab da ya shigo ajin,sam ban gansa ba .Na waro ido a tsorace ina kallon yadda ya wani ja burki yana kallon inda yawun nawa suka sauka...... Normal group 300, VIP 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 🚫 Waɗanda suka yi payment su yi mini magana na saka su group Please [16/12 07:55] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 08 Dukkan illahirin jikina rawa yake,yadda Sheikh Rayyadeen ya wani haɗe fuska kai ka ce bai taɓa yin dariya ba. “Biyo ni ” ya faɗa cikin tsananin fushi kafin ya juya,kamar zan faɗuwa haka na take masa baya har zuwa ajin malamai.Ya buɗe ya shiga ,kamar ba zan bisa ba sai kuma na ɗan shiga tare da tsayawa bakin ƙofa. “Ban san wane sheɗani ne a kanki ba da har yake yi miki huɗuba ki yi mini abubuwa iri-iri,to ko ma uban waye ya tsaya iya kanki saboda in kuka shigo gonata sai na yi mugun baki mamaki.Ban son rashin kunya da tsaurin ido,duk wanda ya yi mini ɗaya daga cikinsu zane shi nake yi” ya ida furicin tare da juyowa rai ɓace hannunsa na gani riƙe da bulala. Ko kaɗan ban taɓa tunanin zai doke ni ba,shauɗar da ya yi mini ita ta maido ni daga duniyar mamakin da na tsunduma.Na ƙara tare da sosa wurin,cike da masifar da ban san yana da ita ba ya ce “wato don kin ma raina ni ina yi miki magana hankalinki na wani wuri ,zaunaaa ” ya ƙarashe tare da sake shaɗa mini bulalar a karo na biyu.Babu shiri na zube kan gwiwaina,ya ɗaga zai yi mini ta uku na yi saurin kamo ƙafarsa cikin kuka na ce “don Allah Sheikh ka yi haƙuri ba zan sake ba,amma kar ka doke ni ban so” hannuwan nawa da na riƙe masa ƙafa ya shaɗe na sake shi da mugun sauri ina jin wani zafi yayin da shi kuma ya wani ja da baya yana jan numfashi kamar zai mutu.Ba tare da ya bani damar fita ba na tashi a guje na bar ajin na nufi namu inda muke karatu.Kamar an jefo ni haka na faɗa ciki ina matsanancin kuka, Mujahida da ke kusa da ni ce take cewa “a kullum ina faɗa miki ki rage wannan shagwaɓar taki nan makaranta ce ba komai ne za ki nuna ke ƴar Daddy ce ba amma ba ki saurarena.Waɗanda ke kusan window sun ga duk abin da ya faru,tun bayan fitarki ake cece-kuce don ma malam Hafiz ya shigo ya tsawatar ne da ƙila sun ta yi miki dariya” Kanzil ban ce mata ba don baƙin ciki,ita da ya kamata ta yi rarrashina amma ta zo tana yi mini surutu.Na ɗauki kamar minti biyar kafin na ji sallamarsa,duk aka amsa masa kuwa.Gudun kar na yi wani laifin na gyara zamana ina shafar ido,tambayoyi ya fara nan uwar iya yi Sadiya ta shaida masa ni kaɗai ce na ƙi zuwa a koyar da ni. Idonsa masu masifar tsoratar ni ya zubo mini,kamar daga sama na ji ya ce “zo ” kasa motsi na yi don duk a tunanina dukana zai yi.Duk ƴan ajin suka zubo mini ido,ina jin Mujahida na salalami “innalillahi!” Wani abin mamaki yana cewa na je ɗin ya ɗauke idonsa a kaina ya soma buɗe alƙur'ani.Zuciyata na ɗan dokawa na tashi ,kamar mai koyon tafiya haka na ƙarasa kusa da babban teburin gabansa na ja na tsaya. “Me yasa ba ki son yin karatun Alkur'ani? Ko ba ki iya komai ba kawai turo ki aka yi aji na gaba?” ya tambaye ni tare da ɗago kai,ni kuwa kayan jikinsa nake kallo yadda ya wani cire rigar sama kawai don na tofa masa yawu. “Kwashi kayanki ki koma tsohon ajinku ” ya faɗa a hankali amma kana iya jin feshin wutar da zuciyarsa ke yi. Sai a lokacin na yi magana “ka yi haƙuri na iya karatun ne” Hannuwansa ya game wuri guda ya ɗora haɓarsa tare da tsura mini na mujiya kafin ya ce “ina jinki Malama koyar da ni” Da sauri na sunne kai ina murmushi don na fahimci me yake nufi.Ya turo mini Alkur'ani wanda shi ne da kansa ya buɗe mini shafin,idona cikin nasa na jawo alƙur'anin tare da juyo shi gabana na soma karantawa cikin ƙira'ar da Daddyna ya koyar ni,sam ban taɓa sanin ainahinta ta Sheikh Rayyadeen ɗin ce ba saboda in banda cikin sallah ban taɓa jin yana koyar da karatu ba. Daga can baya na ji muryar A'isha tana cewa “ma sha Allah! Yau dai mun ji wacce ta iya bin ƙira'ar Sheikh ” duk sai wasu suka shiga yin murmushi mai sauti. Ni kuwa shi na kalla sai na ga ya ƙara haɗe rai kuma ko arzikin kallo ban ƙara samu ba haka ya dinga yi mini binciken karatun kamar wani makaho har ya kammala ya ce na je na zauna. Ƙin tafiya na yi na sake cewa “don Allah malam ka yi haƙuri ka bar fushi da ni, wallahi muddin ka ci gaba da yi to ba zan samu sukuni ba har abinci ba zan ci ba” Yadda duk mutane suka zubo masa ido suna kallo yasa shi cewa “na ji to tafi ki zauna” Na ɗan yi murmushi na ce “da gaske ka haƙura?” ya jinjina mini kai cike da murna na je na koma wurina na ci gaba da kallonsa cike da so.Shi kuwa Sheikh Rayyadeen karatu ya soma koyar mana, lokaci zuwa lokaci haka nake tsintar idonsa cikin nawa a haka har aka fita shan iska. Muna fita na rungume Mujahida tare da bata labarin yadda muka kwashi adashen tsiya ni da Sheikh bayan na tofa masa yawu daga ƙarshe na ƙara da cewa “wannan dukan da ya yi mini sosai na ji daɗinsa,kin ga yau zai wuni da tunanin abin” Ta ja tsuki tana mai cewa “ni dai wuce mu tafi mu yi sauri mu dawo kar lokacin dawowa aji ya yi mu kuma muna can” “Ina za mu tafi?” na tambaye ta,sai ta waro ido tana mai cewa “asibitin mahaukata ko kin manta?” ina shirin yin magana wani abu ya ɗauki hankalina yadda Sadiya da ƙawayenta suka tunkari aji alhalin Sheikh na ciki. Da wani mugun sauri na ja hannun Mujahida muka zagaya bayan aji don ta can ne zan fi jin abin da za su yi wurin nasa. Kunne na kasa ina saurare,ina jin lokacin da Sheikh ya ce “ina jinku me kuka zo yi?” Kame-kame suka fara kafin ɗaya ta ce “dama...dama mun zo ne mu sanar da kai ɗaya daga cikinmu ce ke sonka shi ne kawai” Na yi tunanin zai balbale su da masifa,zuciyata har wani bugawa ta yi jin ya ce “ita wacce ke son nawa ba ta da baki ne sai ke? ” “A'a malam ba haka ba ne kunya take ji” “To ku fita ku bani wuri” ya faɗa . “Sadiya ki faɗa masa mana” na ƙara jin wata ta faɗa ,ƙiri-ƙiri Sadiya ta canza harshe zuwa larabci ta shaidawa Sheikh Rayyadeen tana sonsa har da su cewa in bai aure ta ba mutuwa za ta yi. Ban san matakin fushi da kuma tashin hankalin da na tsinci kaina ba,sai da na ji ƙusoshin kaina na kwancewa yayin da wani abu ya soma yi mini motsi da mugun ƙarfi na ƙwala wata razananiyar ƙara wacce ta karaɗe dukkan makarantar.Duk wata bishiya da ke da kwai sai da ta kaɗa cike da razani, wannan karon hankalina bai gushe ba duka ina jin lokacin da Sheikh ya leƙo ta window yana tambayar Mujahida wacce ke faman riƙona. Can kuma suka zagayo su duka huɗun,cikin bayar da umarni yasa aka kai ni ajin malamai.Karatu ya soma yi mini su kuma suna tsaye a kaina, Mujahida kawai ce ta riƙe ni.Kamar zan mutuwa haka nake ji,shigowar malam Ibrahim ce yasa sauran suka fita iya ƙawata ce kawai ta tsaya. Wani abu ya shaƙa mini a hanci wanda ya kusa kai ni lahira ban shirya ba,wani irin ƙarfi ne ya zo mini na turo Mujahida zan gudu.Sheikh Rayyadeen ya riƙo ni da hannu ɗaya tare da mini wani riƙaƙen kamu wanda na kasa kubcewa,ci gaba yayi da karatun yana bugun tsakiyar bayana da hannunsa. Kamar ana ruwa haka na soma jin wani sanyi na rufe ni,yayin da wani abu mai zafi da ke cikin jikina ke yin ƙasa.Kamar wata ƴarsa haka yake ganin Khadeeja,shi sam bai ma taɓa ganinta matsayin cikakkiyar budurwa ba duk in Ammy na yi masa zancen ya aure ta har mamaki yake ji. “Khadeejatu?” muryar malam Ibrahim ta daki kunnena, lokacin tuni na ida samun cikakken hankalina.A hankali na sa hannuna kan na Sheikh Rayyadeen don cire nasa da yayi mini mugun riƙo don har wani zafi nake ji.Sai da ya kalli tsakiyar idona kafin ya sake ni,a hankali na miƙe kamar zan faɗi Mujahida ma ta tashi tana mai kamo hannuna. “Ya jikin naki?” ya sake tambaya ta,ban basa amsa ba sai ma ƙeya da na sa na fice. Sheikh Rayyadeen ji ya yi kamar ya haɗiye zuciya ya mutu don takaicin abin da ta yi wa malam Ibrahim shi kuwa da wani irin kallon so ya bi bayanta har ta fice. Yana maido hankalinsa ga Sheikh ya sha jinin jikinsa saboda irin mugun kallon da ya ga yana yi masa. “Khadeeja har yanzu yarinya ce,sai a hankali ” ya furta don ya ga da alamu ran Sheikh ɗin ya ɓace yadda ta tafi ba ta yi musu sallama ba haka kuma babu godiya. “Kana iya tafiya” Sheikh ya faɗa a takaice. Malam Ibrahim ya ce “don Allah ina neman alfarma ne,a yi haƙuri da ni son Khadeeja ya daɗe a zuciyata ne shi yasa na kasa controling kaina,na san haramun ne a bisa dokar makaranta yin soyayya da ɗaliba muddin dai ba a wajen nan ba ne za ku yi ta.Amma ina so ni dai a bani wannan damar zan dinga koyawa Khadeeja karatu duk in lokacin shan iska ya yi ta haka ne ƙila za ta yarda da ina sonta” Tun da ya fara zuba Sheikh ya tsura masa na mujiya har ya dire,da sauri ya juyar da kai yana mai cewa “ka tambayi mahaifinta ni malaminta ne kawai,sannan wurin shugaban makaranta ya kamata ka nemi izini ba wurina ba” Jikin malam Ibrahim ya yi sanyi kafin ya ce “to in sha Allah! ” sai ya juya ya fita, Sheikh ya bisa da wani mugun kallo kafin shi ma ya fita don lokaci ma tuni yayi. Muna fita direct aji muka nufa,yau ɗin ma haka mutane suka yi mini caaa suna kallo yayin da Sadiya ke hararena kamar idonta za su faɗo.Samun kaina na yi da mayar mata da martani tare da jan tsuki,na furta “marar aji kawai” yadda ta waro ido shi ya tabbatar mini ta canki abin da bakina ya furta.Ni kuma raina sai yayi fari ƙal kafin na ɗauki ruwa na leƙa ta window na wanke fuskata juyowar ga da zan yi muka yi ido huɗu da Sheikh.Da wani mugun sauri na je wurina na zauna,shi kuma rubutu ya soma yi jikin babban allon aji kafin ya soma yi mana bayani kan tarihin rayuwar Annabi.Tsawon lokaci kafin ya tsaya a wani wurin sakamakon lokacin tashi da ya yi,haka aka fara fita amma ni da ke a gaba ko motsi ban yi ba. “Tashi mu tafi Malama ni nan yunwa nake ji ban ci komai ba” cewar Mujahida. Na ce “to sannu acici uwar sakawa ciki abinci,ni me ki ga na ci?” “Na tafi don wallahi ba a gabana za ki sake yin wata tijarar ba” ta furta tare da ficewa,haka kowa ya fita aka bar ni a zaune ina kallon Sheikh Rayyadeen da ke faman latsa waya da dukkan alamu bai ma san ina nan ba. Murmushi na ga yana yi wanda ya fito tsantsar kyawunsa,muryar Ammynsa na ji tana cewa “yau yarona ya yi kewata har haka ne shi yasa ya kira ni video call?” A shagwaɓe ya ce “Ammy please kafin na iso a haɗa mini ruwan wanka kuma a sake gyara ɗakina don yau ina son na huta sosai” Ta ce “tuni fa Saude ta yi komai,sai ka zo” Ya shafi sajensa ya ce “ina jin yunwa kuma” “Oh! Ni Khadi Allah ya nuna mini dai ranar da za ka kawo mai yi ma girki don ni na kusa gajiya.Yawwa ka baiwa Khadeeja key ɗin motarta ” Ya dafe kai ya ce “ciwon kai dai,don Allah Ammy ki bar mini maganarta zuciyata ta tafasa take yi.Yanzu dai gani nan tafe yanzu in sha Allah ” yana gama faɗa haka ya kashe kiran,ni kuma da mugun sauri na yi kwance jikin table ina mai rera kuka a hankali. Inuwarsa da na gani a tsaye yasa na fahimci ya farga da mutum a ajin.“Ke?” ya furta,a hankali na ɗan ɗago kai na dube shi.Ya haɗe fuska tamau kamar ba shi ba ne ya gama zuba shagwaɓa,“me kike yi nan?” Ya tambaye ni,wani haushi ya rufe ni wato bai ma ga kukan da nake yi ba ballantana ya rarrashe ni.Ban ce masa komai ba,shi ma bai ƙara ba sai key ɗin motata da ya ajiye mini ya fice na bi bayansa da kallon mamaki kafin na tashi da mugun sauri na fita. Sadiya na tsinkayo can nesa kusan inda yake ajiye mota,da sauri na ga ta nufe shi tare da karɓar jakarsa ta kai masa har mota.Bayan ya buɗe ya shiga ya

Chapter 6 of 14