ji hankalina ya tashi.
Ina nan tsaye Mujahida ta fito tana mitar cewa ta gaji,ban kula ta ba sai ma zancen Sheikh da na ɗauko mata.“Yau mutumin bai zo ba Allah sa dai lafiya”
“Wane mutum?”
“Ke banza dubi babu motarsa” na faɗa tare da bangazarta.
Ta ja tsaki tana cewa “uban ƴan takura za ki ce,ashe bai zo ba shi yasa na ji makarantar ko ina hayaniya”
Na ɗan murmusa kafin na bata labarin abin da Yaya Hamza ya ce,sai da ta ci dariya kafin ta ce “kuma fa zamanku zai yi wuya kin ga dai shi bai son yawan magana,ke kuma ga ki kamar Akun kuturu” na dake ta na ce “ni ce Akun kuturun?” ita ma ta rama ta tabke ni sosai tare da rugawa tana cewa “eh ke ɗin” da gudu na bi ta don na rama ɗin wanda ya yi daidai da shigowar Sheikh Rayyadeen a ƙafa yake babu mota.Cak na tsaya ina mai kallon tsakiyar idonsa da suka yi ɗan ja,shi ne ya fara ɗauke kansa kafin ni kuma na juya masa baya ina dafe saitin zuciyata.
Daga bayana na ji Mujahida na cewa “to sai ki juyo don kuwa tuni ya tafi da dukkan alamu dai bai da lafiya don na ga abin ƙarin ruwa a hannunsa”
Na juyo ,na fara rama dukan da ta yi mini ina mai cewa “babu wani nan,so kike yi dai ki ɗaga mini hankali”
“Wallahi gaske don me zan yi miki wannan wasar,kin ga waccan ita ce ƙanwarsa” Mujahida ta faɗa tana yi mini nuni da wata budurwa wacce za mu iya yin sa'anni ko kuma ta girme mini da kaɗan.
“Amma ya na ganta ita baƙa?”
“Oho ni za ki tambaya,bari in Sheikh ya kai ki gidansu sai ki tambaye ta” ta faɗa tare da yin gaba,na tsayar da ita ina mai cewa “na fa kawo abinci daga gida yana can aji”
“Na sani ai,ruwa zan nemo” ta bani amsa,sai na take mata baya muka je ta samo ruwa muka dawo.Bayan kowa ya gama zana jarabawa muka shiga aji don cin abinci amma sam na kasa cin na kirki saboda tunanin abin da ke damun Sheikh .Wunin nan dai haka nan na yi shi duk babu daɗi,da na je gida ma haka sai da aka ga canji.
Abu kamar wasa sai ga shi wajen kwana uku Sheikh bai ƙara takowa makaranta ba,ga shi kuwa tuni an kai mu aji na gaba wanda ya kasance ajinsa.Ga baƙunta ga kuma tunani sai duk suka taru suka ramar da ni,yau ta kama Lahadi bayan mun fito shan iska tsoffin ƴan ajin Sheikh suka yanke shawarar zuwa duba shi haka ɗaiɗaiku daga cikinmu mu ma muka runguɗa muka bi ayari kasancewar da ƙanwarsa a ajin wannan yasa ba mu da damuwa ta fannin sanin gidansu.
Babu wani nisa sosai,tafiyar minti goma sha muka isa ƙaton gidan wanda ya ninka namu sau biyu.Tun da na ɗora ƙafa a ƙasar gidan jikina ya ɗau rawa zuciyata ta soma bugawa kamar za ta faɗo tsabar lugude.
Ita ƙanwar tasa mai suna Aliya ita ta yi mana iso zuwa babban falon gidan,kan lafiyayyen capet duk muka zubo sai wasu su biyu ne wanda alamu ya nuna ƙawayen Aliyar ne suka hau kujeru.
Babu jimawa ta sa aka fara kawo mana lemu mai sanyi,kafin ta ce “bari na je na kira shi” wani irin dam na ji zuciyata ta buga .
Can kuma ta dawo ita da wata mata wacce kallo ɗaya na yi mata na gano inda Sheikh ya samo kyawunsa,wato daga gare ta ne.Cike da girmamawa duk muka shiga gaishe ta,ita kuma tana amsawa cikin kulawa kafin ta ce “ku taso ku ƙaraso” haka duk muka miƙe muka take mata baya,wani falon muka ƙara ratsawa kafin kuma ta ƙara kai mu can cikin wani.Ido na lumshe jin yadda duk ƙamshinsa ya cika ɗakin,sai da Mujahida ta ɗan bangaje ni sannan na buɗe idona sai na ga tuni har sun zauna sai ni ce a tsaye kamar haure .Jikina ne ya hau rawa saura ƙiris na faɗi Allah ya gyara na samu wuri na zauna, Ammy ɗin ce ta kira sunansa “Sheikh Rayyadeen? Tashi ga su nan sun shigo”
Ta ƙasan ido na kalle shi,yana kwance kan kujera mai zaman mutum uku ya luluɓe da blanket.A hankali ya tashi ya zauna yana mai yi mana sallama,ni dai ban amsa ba sai ɗan kallon fuskarsa da na yi wacce ta ƙara yin haske .
Ƴar rige-rigen yi masa ya jiki suke yi shi kuma yana amsawa,tare da tambayar sabbin fuskokin da bai sani ba su kuma suna yi masa bayani ɗaliban da aka kawo ne sabbin zuwa.
A bisa tsautsa yi na ɗaga kai da niyyar satar kallonsa,karaf idonmu ya sarƙe cikin na juna da wani irin mugun sauri na sunne kai ina mai kama yatsuna ina wasa da zobena.
Ammy wacce ke tsaye duk tana kallon komai,dama burinta bai wuce ta ga wacce ta jefa ɗanta cikin wannan halin ba.Amma don sake tabbatarwa sai cewa ta yi “ma sha Allah nan dukkanku ajinsa kuke ?”
Cikin murna suka amsa da eh,Ammy ta ce “ina ga dai tun da shi malamin naku bai da lafiya ni zan je na ci gaba da koyar da ku” duk sai aka soma murna tare da nunawa eh ana so ta koya ɗin,ita kuwa Ammy sai cewa yi“ke ya sunanki?”
“Sadiya” ta bata amsa tana wani sunne kai,na dube ta ina mai cewa a zuci ‘ kina da kunya amma shi ne kika haye kujera daga zuwa gidan mutane’ haka Ammy ta dinga tambayar sunaye har ta kawo kaina ta ce “ke kuma me sunanki?”
Na ɗan dubi Sheikh kamar ba zan yi magana ba sai kuma na ce “Nana Khadeejatu” ina ganin lokacin da ya kawar da kai kamar na ambaci sunan kashi.Bayan ta gama jin sunayenmu cikin tsokana ta cewa Aliya “ke kuma fa?” duk sai aka sa dariya,nan dai ta fita Aliyar na take mata baya.
Sheikh Rayyadeen kuwa tambayoyi ya soma yi wa ɗaliban nasa suna basa amsa yadda ajin ya kasance bayan tafiyarsa .Duk da kaina na sunkuye amma lokaci zuwa lokaci ina jin kaifin idonsa a kaina,a hankali na kai hannu na taɓa Mujahida ta juyo ta dube ni tana mai tambayar “ya dai?”
“Ki tashi mu tafi” na furta kamar zan yi kuka,don wani irin yanayi ne nake ji yana ratsa ni ga kuma kallon Sheikh da nake ji a jikina.Hararar wasa ta yi mini tana shirin juyawa na ce “please ki zo mu fita waje to” kanzil ba ta ce mini ba sai ma yadda kusan kowa ya maido dubansa kaina sai na ji duk na tsargu,cikin ikon Allah Aliya ta sake shigo wa hannunta riƙe da faranti an yanka ƴaƴan fruits sai ta soma tsokanarsu tana cewa “yau dai za ku ci abinci a gidan malaminku duk wacce ta ƙi ci kuma bulala goma” hakan da ta yi ne yasa sai hankalinsu ya koma can.
Uwar iya yi Sadiya wacce na lura kamar kanta na rawa sai cewa ta yi “duk wanda ya yi habaici dai a kasuwa ya san da wanda yake” ɗayar ce wacce suka hau kujera a ɗazu ta karɓe da cewa “ai ban so kika kula ta ba Diya ”
Yadda suke raha a gabansa abin yayi matuƙar bani mamaki,ko da yake kawar da kai yayi gefe yana latsa waya.Ko kunya ba su ji haka wasu daga cikinsu suka sa hannu a faranti suna ɗauko fruit suna ci.
Aka yi sallama, Ammy ce da tare da wani mai farar rigar likitoci.Gaishe shi aka fara yi kafin shi kuma ya tambayi jikin Sheikh ɗin kamar wanda bai son yin magana ya ce “alhamdullah!”
Hannunsa ya kama don saka masa sabon tiyon ƙarin ruwa amma samun jijiya ya gagara sai sokarsa yake yi jini na zuba.Duk in ya tsake shi sai na rumtse ido don takaici,da na ji na kasa haƙuri ban san ina na samo jarumtar miƙewa ba na ce “kawo ka gani”
Ba Sheikh ba alamun mamaki ne ya bayyana a fuskokin kowa,duk yadda kuwa Mujahida ta so riƙe mini ƙafa ina tuni har na isa gabansa na karɓe allurar .Sai kuma a lokacin na dawo hayyacina,yadda Sheikh Rayyadeen ya kafe ni da ido shi ya saka jikina soma rawa.
Mahaifiyarsa ce ta matso tana cewa “bari kallonsa yi aikinki” sai da na ƙara kallon tsakiyar idonsa kafin na sunne kai,a cikin ledar magunguna na zaro safar hannu kafin a hankali hannu na yi mini rawa na soma jan hannun jallabiyarsa sama.Ɗaure damtsensa na yi gam ba a ɗauki lokaci ba kuwa jijiyarsa kore ta bayyana,da Bismillah na soka allurar ina mai ɗan ɗagowa na dube shi idonmu ya sarƙe cikin na juna kafin kuma ya kawar da kai gefe.Na ja numfashi ina mai kwance ɗaurin da na yi masa tare da cewa likitan “na nemo jijiyar”
Ya saki ɗan murmushi kafin ya zo ya ƙarasa aikinsa,ni kuwa ji na yi ban iya zama cikin ɗakin na nufi ƙofar fita ina shirin ficewa muka yi kaure ni da wata,da sauri ta yi baya ni ma haka kafin kuma mu ɗago muna kallon juna.Zuciyata ce ta wani buga darammm sakamakon ganin fuskarta,ba kowa ba ce sai matar da ta zo mini jiya cikin mafarki.....
[12/12 18:35] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```
04
Da wani sauri na ƙara ja da baya ina mai ci gaba da kallon matar wacce idon nata suka ke kore kamar dai yadda na gani a mafarki.Ita kuwa ban sani ba ko ba ta gane ni ba ne oho,haka ta bi ta gabana ta ƙarasa shiga falon.Na bi bayanta da kallo sai dai kafin ta ida sa wurin Ammy ta zube nan tana wani abu kamar wacce ta aka yi wa allurar hauka.Duk aka kwashi salalami kafin Ammy ta zo tana kiran sunanta haɗi da jijiga ta,“Rashida? Rashida?” sai dai babu wani canji zai ma ƙara hauhawa ciwon yake,tuni ɗaliban suka fara fita a bisa umarnin Sheikh Rayyadeen da ya miƙe tsaye kamar ba shi ne ke yin ciwo ba.Duk kowa ya fita hatta likitan da ya zo yi masa magani,Mujahida ta zo ta kama hannuna amma kamar gunki haka na ƙi motsawa.Sheikh wanda ke tsaye ya zubo mini idonsa kafin cikin wata murya ya ce “fita”
Na ɗan girgiza masa kai saboda wani furici da zuciyata ke jadadda mini ‘ Khadeeja ba banza ba ne Allah ya nuna miki matar nan a cikin mafarki ƙila ke ce za ki cece ta’ haka Mujahida ta fita ta bar ni saboda yadda Sheikh ke banko mana wani mugun kallo kamar idonsa za su faɗo.
Daga nan inda nake tsaye na ce “a yi mata turaren habbatu sauda ” Ammy ta ɗago ta dube ni kafin ta cewa Sheikh “je ka ɗauko,ke kuma je ki nemo garwashi ” sai a lokacin kawai na fita zuwa can falo,babu kowa da dukkan alamu ɗaliban sun tafi.
Waige-waige na fara don duba ina ne kitchen,kwatsam idona ya sauka kan hoton ahali shi ma sak irin yadda na gansa a mafarki ne.A hankali na soma takawa na isa gare shi,abu biyu ne suka ɗaure mini kai yadda na ga kaf mutanen cikin hoton an yi musu wani mugun ɗauri daidai wuyansu in aka cire Sheikh da kuma wata tsohuwa wacce nake kyautata zaton kakarsa ce.
Hannu na kai na shafi hotonsa,ina taɓa na tsohuwar na ji wata murya a bayana.
“Wace ce ke?” ita ce tambayar da aka yi mini cikin wata baƙar murya mai tarwatsa hankali.Da mugun sauri na juyo nan na yi arba da tsohuwar,ina shirin yin magana sai ga Aliya tana mai cewa “Grand-Maa tun ɗazu fa ke nake nema kin Rashida can ta zo babu lafiya” ta faɗa tana mai kama hannun wacce na ji ta kira Grand-Maa.Take musu baya na yi,su ke gaba wannan yasa suka rige ni shiga da wani mugun sauri na ga Grand-Maa ta fito tana tari kamar ranta zai fita.
Wani kallo da ta yi mini da jajayen idonta kamar na tsohuwar mayya shi ya tsorata ni ,da gudu na baro wurin na kama hanyar fita daga gidan gaba ɗaya.Ko da na fito ƙofar gida sai na hangi Mujahida can gaba tana zaune kan dakali tana waya.Na ƙarasa ina mai zama kusa da ita,da sauri ta yi sallama ta kashe wayar kafin ta zuba mini na mujiya.
“Me?” na tambaye ta.
Ta waro ido ta ce “yaushe kika koyi ƙarfin hali Khadeeja? Kin ga kuwa yadda ran Sheikh ya ɓace amma ke oho ko a kwalar rigarki,kuma a haka ne kike so ya amince ya karɓi soyayyarki”
Na ce “ni fa ban ga abin laifi ba”
“To a wane dalili za ki tsaya alhalin kowa ya fita?”
Sai da na kamo dukkan hannuwanta sannan na ce “Mujahida matar nan da ta shigo ita ce wacce nake baki labari na yi mafarki da ita,kuma wallahi yanzu ma idonta sak irin na macijin na gansu”
Mujahida ta ƙwace hannuwanta kafin ta ce “kin ga tafiyata babu ni cikin hikayar nan,ta ya daga ganin mata yau ki ce wai ita ce ta zo miki a mafarki”
Na ce “ki yarda da ni,wallahi hatta hoton da na ce miki na ahali to yau ɗin nan ma sai da na gansa”
Shiru Mujahida ta yi kamar mai nazari kafin ta ja numfashi ta ce “ni ma na ga hoton amma sai na yi tunanin ko dai ƙila kin taɓa ganinsa ne Sheikh ya ɗora”
Na girgiza kai kawai ina jin wani tsoro na luluɓe ni,haka muka runguɗa zuwa makaranta.
Yadda ajin ya kancame da hirar Sheikh Rayyadeen ana haɗa sunansa da na Sadiya sai abin yayi mugun ɓata mini rai.Mujahida wacce ita kaɗai ta san sirrin da ke ƙunshe a birnin zuciyata sai cewa ta yi “kar ki wani damu kanki wai don tana rawar kai, wallahi ina da yaƙinin ita kaɗai ke kiɗanta take rawarta.Ke yanzu ki dube ta kin ga ta yi kama da macen da Sheikh Rayyadeen zai so?”
Idona ya ciko da wasu hawaye kafin na ce “na sha ji a labarai cewa baƙar mace na ɗauke da wata irin baiwa Mujahida,kuma malamai sun fi kowa sanin sirrikan da ke tattare da mata to ƙila ita ma Sadiyar tana da shi”
Ta ja tsaki kafin ta ce “waccan fa da kike gani tsohuwa ce don ta haura shekaru talatin da biyar yanzu kuma yayin ƴan shila ake yi” sai kuma ta yi shiru tare da yin wata muguwar dariya kafin ta kawo bakinta daidai kunnena ta raɗa mini “amma fa ƙawata za a sha gwagwarmaya don an ce tuzurai sun fi kowa zalamar mata kuma alƙur'an yadda Sheikh yake da ilimi na san akwai kallo duk ranar da kuka keɓe”
Wani irin yammm na ji a jikina,na ɗan bangaje ta tare da yi mata hararar wasa na ce “ta ya aka yi ma har tunaninki ya kai can? Ni fa ko sau ɗaya ban taɓa hango mu a wannan matakin ba”
Ta yi wani ƙayatacen murmushi kafin ta ce “ Khadeeja ko kin san da ina sonki ne domin Allah? Ganinki cikin farin ciki shi ne abu mafi tsada a rayuwata,silar ƙaunar da nake yi miki shi ne dalilin da yasa har na karɓi Yaya Hamza matsayin wanda zan aura amma kin san ba irin kalar namijin da nake so ba ne”
Na ja numfashi na ce “amma Mujahida a wane dalili ne ba ki son farin namiji?”
“Ni dai bai yi min ba” ta bani amsa a takaice.
“Yaya Hamza fa shi ya yi miki?” na jefo mata tambayar.
Ta yi murmushi ta ce “jininki ne fa ai ke ma kin san dole na so shi”
Na kama hannunta na ce “don Allah kar ki yi wasa da zuciyar ɗan uwana yana mugun sonki”
“Na sani,don yana faɗa mini kusan kullum ”
Ina shirin yin magana amma ɗaya daga cikin manyan ɗaliban ajinmu ta yi magana kan a yi shiru sai ta soma jawabi “da farko ina yi muku sallama irin ta addinin musulunci,abin da yasa na buƙaci na yi magana shi ne dama don na ce mu yi wa kanmu faɗa .Don Sheikh bai da lafiya ba shi zai sa a ce an ƙi ci gaba da karatu ba,a cikin ajin nan akwai mahadatan Alkur'ani har biyu Sadiya da kuma A'isha da wannan nake kira a gare su don Allah su taimaki sauran wurin koyon karatu na san in kun yi haka sosai Sheikh zai ji daɗi in ya dawo” wannan shawarar da ta bayar duk kowa sai yayi amanna da ita,yayin da kuma aka fara zuwa suna koyar da karatun haka kawai na ji kishin Sadiya duk da tana yin karatu mai daɗi sai dai ba ta fi ni iya ƙira'a ba.
Ko motsi ban yi ba ballantana na je ta koyar da ni kasancewar ita A'isha ɗin an tsara waɗanda suke yin hadda take yi wa gyara.A gabana Mujahida ta je aka koya mata tana zaunawa ita Sadiyar ta ɗago kai tana kallona,na kawar da kai gefe ina kallon Mujahida wacce zungurar mini ƙafa.
“Ke?” ta furta duk da na san da ni take amma ban ko waiga ba,“ke kin iya karatun ne?” wannan karon a gabana ta zo ta tsaya tare da buga table.Na ɗaga kai na dube ta,a girme ta girme mini don ta kusa ninka shekaruna biyu amma da yake shi kishi babu ruwansa da shekaru sai cewa na yi “ai masu ra'ayi ne za a koyar to ni banda shi”
Tana shirin yin magana malam Ibrahim ya shigo da sallama,aka amsa masa cikin ladabi kafin shi kuma cike da murna ya ce “na ji daɗi sosai yadda na ga kun mayar da hankali kuna karatu masha Allah ”
“Malam ita wannan ta ce ba a isa a koyar da ita ba” cewar Sadiya tana mai nuna ni da yatsa.
Malam Ibrahim ya dube ni da kyau kafin ya ce “Khadeeja yaushe kuma kika ɗauki wannan hali?”
Na turo baki gaba ina cewa “ni ban so ta koya mini ne don ban saba yin karatu wajen mace ba in ba Momyna ba”
Kusan ajin dariya aka shiga yi mini wasu na tsokanata da sunan ƴar Momy,sai da malam ya tsawata musu kafin ya cewa Sadiya “tun da ba ta so ki bar ta kawai,ci gaba da koyar da sauran”
Sai da ta banka mini mugun kallo kafin ta gusa daga inda nake.Mujahida ta ce “ban so kika yi haka ba yanzu sai ki sa ki yi baƙin jini wurin mutane a yi dubin girman kai ne gare ki”
“To sai me? Su suka sani” na faɗi haka ina mai ɗaukar jakata na fice daga ajin,wayata na fiddo na kira direba na ce ya zo ya ɗauke ni.Kusan mintin sha biyar kafin ya iso,na shiga baya na zauna kafin na ci gaba da latsa wayata ina aikin da na saba.Shafinsa na facebook na shiga na duba ai kuwa na ci karo da wani sabon hotonsa da ya ɗora.Kamar wata mahaukaciya sabon kamu haka na yi ta dariya ni ɗaya har sai da direba ya juyo ya tambaye ni sai a lokacin na nutsu.
Ina isa gida na tarar Daddy na nan,sallama kawai ya amsa mini ya jefo mini tambayar “me kika dawo yi gida?”
“Malaminmu a bai da lafiya shi yasa,yau muka je ganinsa har na saka masa ƙarin ruwa.Wallahi Daddy sai na ji na matsu a koma Makarantar boko don na ƙara ci gaba da karatuna daga inda na tsaya,ka ga shi kenan in Sheikh bai da lafiya ni ce zan dinga duba shi” yadda Daddy ya kafe ni da ido ko ƙyaftawa bai yi shi ya fargar da ni kan kwabsawar da na yi.
Sai na rufe bakina da hannu ina mai waro ido.Ya ce “kafin ki amsa mini tambayoyin da zan jero miki da farko fara bani amsar me yasa yanzu kika bar saka niƙafi?”
Na ɗan kwaɓe fuska kafin na ce “Daddy ta ɓata ni ma ban san inda take ba,kuma ita kaɗai gare ni duk na yi kyauta da sauran saboda na yi wa Momy alƙawari wacce ta saya mini kawai zan dinga sakawa”
“Na ji! Yanzu yaushe kika zama likitar malaminku?”
“Daddy ba fa abin da kake tunani ba ne,kawai mun je ganinsa ne sai likitansa ya gagara samun jijiya shi ne na nemo” na basa amsa ina mai sunne kai ƙasa zuciyata na dakan uku-uku saboda ganin kamar ran Daddy ya ɓace.
“Wane Sheikh ne za ki dinga yi wa magani in bai da lafiya?”
“Ƙanena wanda Momy za ta haifa mini” na basa amsa ina mai yin wani murmushi duk a tunanina zan iya yi wa Daddy wayo,shi ma martanin murmushin ya maido mini kafin ya ce “to je ki in kin huta ki gyarawa Umma ɗaki yau da maraice in sha Allah za ta zo”
Wani irin tsallen murna na yi ina mai cewa “a ɗakina za ta sauka Daddy”
Ya ce “kin sani sarai da Ummah ba ta iya hawan sama ciwon ƙafa take”
Na soma kukan sangarta kafin na ce “a'a Daddy kar ka bari ta ji haka please ka bari na sauke ta a ɗakina”
Kai kawai ya girgiza,ni kuwa ina haurawa sama na ƙara gyara ko ina duk da kuwa mai aiki ta gyara shi.Toilet na shiga,ina cire sutura ta sai na samu kaina da tsayuwa gaban mirror ɗin da ke manne a bango.Na yi murmushi ina jin wata irin kunya ganin surata a ciki,sai nake ganin tamkar mirror ɗin idon Sheikh ne.Da sauri na gusa na je na yi wanka na ɗaura towel na fito,kafin na kimtsa sai da na ƙara shiga shafin Sheikh Rayyadeen na yi bincike a nan ne na ga nan da sati biyu yake birthday na cika shekara arba'in da biyu.
Ina shafa mai ina tunanin irin gift ɗin da zan basa,a haka har na shirya na sauko ƙasa.Daddy tuni ya tashi,motsin da nake ji a kitchen yasa na nufi can yau ma kamar kullum Momy ce ke a tsaye tana girki Baba Laure na taimaka mata.
Kusa da ita na ƙarasa ina mai jingina kaina a kafaɗarta tare da kallon abin da take dafawa cikin tukunya.
“Momy kan rago za mu ci?” na faɗa ina haɗiyar yawu.
“Na Ummah ne” ta bani amsa tana yin murmushi mai sauti,na ce “to ai tare za mu ci”
“Na sani! Je ki ma ki dama fura na can kan dinning ”
“Momy na gaji please ki saka Baba Laure ” na faɗa a shagwaɓe ashe rabon a yi mini faɗa ne,nan ta soma balbale ni da masifa har da su cewa “wato duk yadda na tsaya kai da fata ina yi wa ahalina hidima ke ba za ki iya yin koyi da ni ba? Dama furar shi ne kin gaji? An faɗa miki zama mace raggonci yake nufi? To gara ma ki jajirce don in kin yi aure babu wanda zai yi miki aikin gida ke za ki yi abinki ”
Ina turo baki ina ƙari na fita na je na ɗauki furar na dama,bayan na gama na saka ta a frigo don ta yi sanyi.Sai kuma na koma kitchen na soma kama mata aikin,ina kallon yadda Ammy ke sakin murmushi.Bayan mun gama komai muka jera a dinning kafin mu yi sallah,duk yadda Momy ta matsa mini kan na ci abinci ƙin ci na yi don na yi alƙawari tare da Kakata za mu ci.
Sai yamma lis sannan Ummah ta zo,tuni lokacin yunwa ta gama galabaitar da ni amma ina ganinta na neme ta na rasa na je da guduna na rungume ta.
“Haba Deeje ya isa haka kar ki kayar da ni ” Ummah ta faɗa tana dariya,na yi baya ina turo baki ina mai cewa “ni dai wallahi ba Deeje ba ke dai ce sunanki ke haka”
Ta yi dariya ta ce “ ai sunan dai nawa ne ubanki ya ara ya maƙala miki”duk aka yi dariya,bayan gaishe-gaishensu ita da Momy aka gabatar da abinci har za ta je ta yi wanka amma na hana ta ina mai cewa “ƙawali wallahi in har sai kin yi wanka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 14