kafin ya ce “amma ai da bari kika yi sai ranar da babu makaranta Mama”
Ta ɗan washe baki kafin ta ce “gaba za a kiyaye”
Abba wanda yake fitowa daga ɗakinsa duk ya ji abin da suke tattauna wa,har ƙasan ransa yake jin daɗin yadda ahalinsa ke mu'amulantar junansu amma duk da haka yana jin babu daɗi in ya tuna wani sa'in Grand-Maa na yin ƴar tsama da babban ɗansa mafi soyuwa a kaf ƴaƴan nasa.
Da sallama ya iso wurin,duk ƴar rige-rigen gaishe shi suka fara in ka cire Sheikh Rayyadeen da ya miƙe tsaye yana mai zuwa gun Abban ya amsa masa sallamar tasa tare da miƙa masa hannu suka yi musafaha.
Grand-Maa wacce ke zaune kan kujera ta ja tsuki tana mai cewa “in ba zuwan ƙarshen zamani ba da lalacewa ta ina ɗa zai tunkari ubansa ya miƙa masa hannu suna gaisawa sai ka ce wasu turawa,in kuma ka yi magana a ce ma ai shi ma addini ne”
Abba ne ya tanka ta don shi Sheikh ko kallon inda take bai yi ba.
“Maa wannan fa ba wani abu ba ne,ya ƙarfin jikin naki?” Abba ya tambaye ta cike da kulawa.
Kamar wata ƙaramar yarinya haka ta kwaɓe baki tana kukan dole haɗi matso ƙwalla.“Ta ya zan ji sauƙi alhalin kullum a gidan nan ni ce mai laifi,ka ga haka ɗazu uwarsa ta hana ni abinci wai ya kamata na dinga yin azumi tun da ban wani tsufa ba”
Abba ya dubi Ammy ransa a ɗan ɓace,ita kuma baiwar Allah sai ta fara ƙoƙarin kare kanta.
“Abban yara wallahi ban faɗa da wata manufa ba,gani na yi tun safe ba ta ci komai ba sai ruwan shayi shi ne na ce inda ma azumi ta yi ya fi ta zauna da yunwar nan ”
“Khadi a gidan nan wa yake sayen abinci?” Abba ya tambaye ta,idonta suka ciko da ƙwalla murya na ɗan rawa ta ce “kai ne”
“A kaf gidan nan wa yake da iko a kaina yayi mini faɗa har duka ma in ta kama?”
Ta basa amsa da “Grand-Maa”
“A ƙarƙashin wa kike a gidan nan?”
Kafin ta amsa masa tambayar Sheikh Rayyadeen ya tari numfashinta ,cike da nutsuwa ya ce “Abba don Allah ku bar maganar girma da ikon nan,cin abinci ya tara mu a nan amma kuma kuna shirin saka abincin ya fita ranmu ”
Abba ya ja numfashi tare da kawar da kai, Grand-Maa ta harari Sheikh kamar idonta za su faɗo yayin da ta yi wa Ammy mugun kallo sai dai suna haɗa ido da Mama sai ta sha jinin jikinta.Duk Sheikh na kallon komai ,har zuwa yanzu ya rasa dalilin da yasa Grand-Maa ke shakkar Mama amma kuma ta tsani mahaifiyarsa.
Ammy ce ta zuba wa kowa kamar yadda tsarin yake ranar girkinka kaina za ka yi haka.
Sheikh ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce “Aliya ke sai yaushe ne za ki fara taya iyayenmu aiki? Ko sai an kai ki gidanki ba ki iya komai ba?”
Duk sai suka kalle ta,Aliyu wanda ya kasance Yayanta uwarsu guda sai cewa yayi “wai wannan ce za ta yi girki mu ci? Allah ya tsari gawa da dariya”
Ammy ta yi ƴar dariya ta ce “Gadanga kar fa ka zo kana santi ”
Ya ce “haba dai Ammy wannan yarinyar ce za ta yi abinci mu ci? Ku dai barta da kwalliya da saka jan baki”
Ammy ta ce “in sha Allah duk ranar weekend tare da ita za mu dinga shiga kitchen ,zan sa kuma Saude ta koya miki girke-girken gargajiya”
Grand-Maa ta yi caraf ta ce “to sannu ƴar boko,ai gara na gargajiyar kan uwar fulawar da kike bamu kullum muna ci”
Ammy ta ce “yi haƙuri Ammy in sha Allah za a dinga yi miki girkinki daban,sai ki dinga faɗar abin da kike so”
Mama ta ce “haba dai Khadi wasa fa Grand-Maa ke yi miki amma tana son abubuwan da suka shafi fulawa ko Maa?” ta ƙarashe faɗa tana mai tsura mata ido, Grand-Maa duk da ranta ya ɓace haka ta daure ta yi murmushin yaƙe, Sheikh ya tsure ta da ido yana nazarinta kafin kuma ya ture plate ɗin gabansa ya ce “sai da safenku ”
“Tun yanzu za ka kwanta?” Ammy ta tambaye shi,sanin dalilin da yasa take tambayar tasa yasa ya ce “ban jin daɗin jikina ne Ammy,yau na gaji sosai”
“To ka sha maganinka kafin ka kwanta,in na tashi zan shiga na duba ka” Ammy ta faɗa cike da kulawa.
Ya ce “to Ammyna” sai yayi gaba,Abba ya dube ta ita kuma ta sunne kai tana jin fa ita ba ta ga dalilin da zai sa ta bar nunawa ɗanta kulawa ba.Duk shekarunsa ita a yaro take ganinsa,sauran ne suka tashi Aliyu da Aliya sai wurin ya yi saura Abba, Grand-Maa da Mama da Ammy.
“Mahmuda ya kamata ka yi wa matarka faɗa,shishigin da take yi wa mai gemu(cewa da Sheikh Rayyadeen) ya fara yin yawa,yanzu mene ne na tafiya duba shi? Ƙaramin yaro ne da za ta shayar ko me ? ”wannan ƙorafin na Grand-Maa ya fi shuren masaki da ta yi shi,don haka ba wani baƙon abu ba ne gun Ammy shi yasa ma ba ta wani damu ba.
Mama ce ta amsa mata madadin shi Abban,ta ce “Grand-Maa kin san tsakanin uwa da ɗa sai Allah,kamar ke ce da Abban yara kin ga duk da ya tsufa da ƴaƴansa haka wani zubin kike basa kulawa kamar ƙaramin yaro,in ba ki manta ba in ya jinkirta zuwa har cewa kike a kira miki shi a waya”
Cike da jin haushin katsalandan ɗin da take yi mata a lammuranta Grand-Maa ta ce “amma ai ni tsohuwa ce,ita kuma fa ba ki da sauran ƙurciyarta”
Mama ta ce “to mene ne aibu a ciki?”
Idon Grand-Maa ma suka kaɗa suka yi ja tsabar takaici,daga ƙarshe ta miƙe ta bar wurin.Mama ta ita ma ta miƙe da sauri tana cewa “ku jira kar dai a ce fushi Maa ta yi da ni ” sai kuma ta tafi da sauri,tana dab da shiga ɗakinta Mama ta ƙaraso tana mai cewa “wane sabon abu ne kuma kika tsiro Maa?”
Ta juyo cike da takaici ta ce “Ramma ki fita daga idona na rufe”
Mama ta zo ta ida tura Maa cikin ɗakin ita ma ta shiga ta dantse ƙofar kafin ta ce “me kike nufi? Kar dai ki ce mini zuciyar ƙurciya Sheikh Rayyadeen take so? Ke yanzu ba ki jin kunya cewa jikanki kike so? Wannan kuma wane irin salon tsafi ne?”
Grand-Maa ba ta bata amsa ba,sai shaƙe wuyan Mama da ta yi tana wani juya idonta suka rikiɗe kamar garwashin wuta yayin da akaifunta suka ƙara tsayi zaƙo-zaƙo.
Mama ta fiddo nata kayan aikin,wata ƴar siririyar tsutsa ce da ke cikin jijiyar wuyanta tana fitowa idon Grand-Maa ta cabka,babu shiri kuwa ta saki wuyan Mama ta yi baya tana dafe gun.
Mama ta shafi wuyanta tsutsar ta koma kafin ta ce “har abada ba zan bari ki cutar da Sheikh ba”
Ita kuwa Grand-Maa sai cewa ta yi “da ni da ke shege ka fasa” ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta fice,ko da ta koma can falo tuni kowa ya watse.
Sheikh Rayyadeen na zuwa part ɗinsa sai ya shiga toilet ya haɗa ruwan wanka masu ɗumi ya shiga cikin bahon ya kwanta tare da ɗan lumshe idonsa.Wata irin kasala yake ji ga wani yanayi kamar wanda zazzaɓi zai damƙa,a duk lokacin da fuskar Khadeeja ta faɗo cikin magijin ganinsa sai ya ji wani abu ya tsarga masa wanda hakan yake ƙara hura wutar kasalar da ta aure shi.Dakyar ya fito ya ɗauro towel ya fito,yanayin ɗakin ya fara canzawa ya kunna na'urar ɗumama guri sannan ya tsane jikinsa tare da saka kayan bacci masu ɗan nauyi.Kan bed ya kwanta amma bai kashe fitila ba saboda sanin Ammy ta yi masa alƙawarin za ta zo ta duba shi.
Babu jimawa kuwa ta buga ƙofa ya ce ta shigo,ta tura ƙofar da sallama da sauri shi kuma ya tashi zaune yana mai daɗa jan blanket ɗin sama yana rufe jikinsa.
Tana zuwa gefen wuyansa ta taɓa ta ji da zafi,cikin muryar tausayi take cewa “jikinka da zazzaɓi shi ne ka yi wanka? Ka sha maganin da na baka?”
Ido ya tsura mata na wani lokaci kafin ya girgiza kai,ta ce “ don me? Ai ko addini bai hana a sha maganin gargajiya ba,me yasa ba za ka sha ba tun da har ka ga na baka bai kamata ka yi sakaci da shi ba.A ina ka ajiye shi?”
Ya shagwaɓe fuska kafin ya ce “Ammy ba fa abin da ke damuna kawai ɗan zazzaɓi ne”
“Shi mugu da kake ganinsa wayo ne da shi,a sannu a hankali yake kama ka har ya damƙe ka duka” ta faɗa tare da soma duba inda za ta ga maganin.
Can kuwa ta gansa,da kanta ta kaɗa madara sannan ta zuba maganin ta basa ya sha ba don ya so ba sai don yi mata biyayya.Yana gama sha ya koma ya kwanta yana mai lumshe ido,nan take kuma yadda Khadeeja ta faɗa ƙirjinsa a bisa kuskure ya faɗo masa,da sauri ya cije leɓe yana jin kamar ya ƙurma ihu .
“Me sunan yarinyar ta ɗazu da ka fara yi mini magana?” ya tsinkayo muryar Ammy,a hankali ya ɗan buɗe idonsa da suka yi masa nauyi yana kallonta kafin ya mayar da su ya rufe ruf.
“Deeni!” Ammy ta kira sunansa,wanda wannan sunayen ya kasance keɓaɓe ba ta kiransa da shi sai in tana son nuna masa shi ɗin yaro ne ƙarami a idonta har yanzu bai wuce ta yi masa duka ko kuma wani abu da uwa ce kawai za ta iya yi wa ɗanta shi.
Kamar zai yi kuka ya ce “Ammy ba fa sonta nake yi ba”
“Na sani,amma ai ita ce silar ciwonka ”
“Wane ciwo kuma Ammy?”
“Deeni ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce,kar ka manta ni na ɗauki cikinka na tsawon wata tara,na haife ka sannan na raine ka.Babu wani hali naka da ban sani ba,hatta Maa da ke kakarka ta gane da yau ka haɗu da wata budurwa sai ni ce ba zan fahimta ba?”
Shiru ya yi kafin ya ce “Ammy na faɗa miki ba sonta nake yi ba,kawai tsautsayi ne yasa ta shigo hanyata”
“Na ji ba ka sonta mene sunanta?”
“Sunan mai darajata ne da ita” ya faɗa kamar zai fasa ihu,Ammy ta yi ɗan murmushi ta ce “takwarata ce kenan?”
“Eh!” ya bata amsa,idon Ammy suka ciko da ƙwalla tana mai yin addu'a a zuciya ‘ Allah yasa wannan ɗin ita ce abokiyar rayuwarka’ sai kuma ta fice ta barsa cikin duniyar tunani.
★KHADEEJA
Muna gaba buɗa baki na wuce sashena,sallar magarib na yi sannan na soma yin azkhar na maraice ina zaune kan sallaya lokacin isha'i yayi na miƙe na gabatar.Bayan na gama na yi wanka na saka kayan bacci pink riga da wando ne masu hulla,sai na ɗora ɗan madaidain hijabi a sama na fita zuwa falo.Soyayyen dankali na zauna na ci ina kallon Arewa24 da suke nuna shirin rayuwata,duk abin da jaruman ke yi sai nake hango kanmu ni da Sheikh wannan yasa na zauna ni ɗaya ina ta murmushi.
“Ke lafiyarki?” na ji muryar Yaya Hamza,da sauri na nutsu ina mai cewa “lafiya lau Yaya Barka da shan ruwa ka ga Daddy? Yau ba ka zo muka yi buɗa baki tare ba halan gidansu Mujahida ka sha ruwa?”
Ya ja dogon tsaki yana mai cewa “ke me yasa kin cika surutun tsiya ne,a yi mutum kamar Aku cacacaaa babu hutu sai zubo shi kike yi”
Na turo baki na ce “ai Mujahida ta koya mini” ya banko mini harara kafin ya ce “ba Mujahid ba?”
Na tuntsire da dariya kafin na ce “ka san kuwa haka ƙawata ta ce mini wai inda ma Yayanta Mujahid na aura shikenan mun yi masayar yayyu ”
Ya ɗan murmusa kafin ya ɗan dungure mini kai ya ce “ina mai tabbatar miki da cikin sati biyu kacal zai maido ki gida saboda ya tsani surutu”
Na sheƙe da dariya na ce “ai kuwa saurayina ma shi ma shiru-shiru yake kullum bakinsa a rufe kamar mai ciwon haƙori”
Yaya Hamza ya shiga yin dariya kafin ya ce “Allah ya shirye ki auta,kullum har tambayar kaina nake ko wane bawan Allah zai auri shirmamar ƙanwata?”
Na yi murmushi mai fiddo tsantsar farin cikin da ya fito daga zuciya sannan na basa amsa da “wani mai ilimi ne,mai nutsuwa, kyakkyawa ɗan gayu ,yana da cikar haiba da ƙwarjini.Bari na faɗa maka Yaya Hamza kaf makarantarmu kowa tsoronsa yake ji,hatta malamai fa ” sai kuma na tuntsire da dariya kafin na ci gaba da cewa “ɗazu fa malamin saura ƙiris zuciyarsa ta buga da Sheikh ya shigo ajinmu ” sai kuma na yi shiru ina tuna irin yadda ƙirjinmu ya haɗu da na juna.
Kamar wacce aka tsikara sai kuma na miƙe na nufi ɗakina ba tare da na yi wa yaya Hamza sallama ba.Ina shiga kawai na haye bed tare da jawo pilow na ƙanƙame na soma yin hawaye tuna cewa babu tabbas ya karɓi soyayyata.Ba tare da na shirya yin bacci ba na ji wani abu mai kamar rumfa ya luluɓe ni,kawai kwatsam sai na tsinci kaina a duniyar mafarki sai dai ba irin mafarkin da mutane suke yi ba a'a nawa na daban ne.
Cikin wani babban gida ne na tsinci kaina mai hoton ahali,ɗaya bayan ɗaya haka nake kallon hoton har idona ya sauka kan na Sheikh da na yi gaba kuma sai ya na ci karo da na wata mata,sosai suke kama da Sheikh tamkar ƴan biyu sai dai za ta girme masa.Ina shirin janye idona sai hoton ya soma yi mini magana.
“Kar ki tafi ba ki ji labarina ba” tana faɗa mini haka sai kuma na ƙara tsintar kaina wani wurin,sai dai wannan tare nake da ita.
“Ina ne nan?” na tambaye ta.
Ta bani amsa da “maƙabartar rayayyu ce”
“Rayayyu kuma?”
“Eh! Ni ma saura ƙiris na bi ayarin waɗanda za a binne da ransu” ta bani amsa tana goge hawayen jini.Kafin ta ci gaba da cewa “ni mace ce mai addini,na taso gidan malamai duk da ba su suka haife ni ba amma a can na girma tun ina ƴar shekara uku a duniya ƙanwar Mamana ta ɗauke ni riƙo.A can gidan aka yi mini aure,sai dai ban taɓa haihuwa ba.Farkon matsalata ta soma ne a wata rana da na bincika wayar mijina na samu shaidar yana cin amanata shi da wata mace a waje,da na tunkare shi da zancen sam bai yi mini gardama ba ya karɓi laifinsa tare da neman yafiya ni ma sai na haƙura na yafe masa.Sai dai a bisa tsautsayi ko na ce ƙaddara,sai na ƙara duba wayar tasa na ga dai ashe har yanzu bai goge komai nata ba sai na je can facebook na binciko sunanta tare da following nata.Na ɗauki tsawon sati biyu ina bibiyar duk wani abu da za ta yi posting a page ɗinta amma ko sau ɗaya ban ga mijina yayi comments ba,duk da cewa mafi akasari hotunanta ne masu bayyana tsaraici.Kwatsam wata rana sai ta wallafa zancen fyaɗe na wata yarinya da aka tozarta,kawai sai na yi mata magana pc na ƙirƙiro zancen ƙarya na ce ni ma da ina yarinya an taɓa yi mini fyaɗe,daga nan ne muka fara gaisawa fa har ta kai da mun yi masayar lambobin juna muka soma yin WhatsApp.Wata rana sai ta shirya mana haɗuwa a wani gidan cin abinci haka na kwashi jiki na je,a fili har ta fi kyau kan a zahiri tabbas ta yi haɗuwar da duk wani namiji mai lafiya zai so ya kasance da ita,tuni kishi ya turnuƙe ni amma na daure muka gaisa aka gabatar mana da abin sha da kuma abin motsa baki bayan nan kowacce ta kama gabanta.A wannan daren ne na ga ta saka video ɗinta a status jikinta babu wata suturar kirki,haka na kalla na sake kallo da na ji ban gaji da kallo ba kawai sai na yi saving nata.Tsabar yadda ta shiga raina yasa duk hankalina ya tashi,maimakon na je gun mijina a'a sai na ji tamkar wani baƙin ruhi na zuga ni a haka na yi amfani da kaina na biya wa kaina buƙata wacce a zahiri ni ɗaya ce amma a baɗini akwai sheɗani a tare da ni ” tana kawowa nan sai kuma ta dafe mararta tana cije haƙora,ina shirin yi mata magana alarm wanda ke tashina sallar dare ya soma ruri,na buɗe idona da suka yi mini nauyi kafin na miƙe dakyar na shiga toilet.Kan WC na hau na soma yin fitsari amma kamar abin tsiya haka na ji wani baccin na ƙara jana daga zaune....
[11/12 11:59] MRS SADAUKI: *MAFARKI*🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```
03
Da sauri na kamo ta,sai ta ɗago ta dube ni da idonta da suka soma canza launi suna komawa kore kamar na maciji.Murya na ɗan rawa ta ci gaba da cewa “tun da nake ban taɓa yin auren hannu ba sai wannan ranar,abin mamaki kuma shi ne gamsuwar da na samu ta sha banban da irin wacce nake samu a wurin mijina sam ban fahimci abin da yake faru da ni ba.Sai na yi istigfari har da ma azumi uku ina ɗauke da na huɗun ne kwatsam ta aiko mini video a WhatsApp wannan karon babu sutura ko ɗaya a jikinta ko ɗan kamfai,fuskarta kuwa duk ta ɓace da dukkan alamu sun gama mu'amula ne da namiji sai ta yi tabi'arsu ta ƴan kwalta.In taƙaice miki dai nan take azumina ya zama gurgu,na mance da istigfarin da na yi na ƙara biyawa kaina buƙata a karo na biyu.Sai bayan na gama ne na yi ta kuka tare da goge video na kuma ja mata kunne kar ta sake in kuma ta ƙara zan yi blocking nata.Ta bani haƙuri muka wuce wurin,sai dai ba a wani ɗauki lokaci ba kamar abin tsafi haka na ƙara tsintar videon a wayata alhalin na goge ta.Sai kuma na sake komawa ruwa duk da kuwa na yi ƙoƙarin hana kaina ƙara kallon videaon amma yadda kika san akwai wani baƙin ruhi mai zuga ni haka na buɗe na kalla .Na riga da na hallaka,karuwar mijina tuni ta yi galaba a kaina don har da link ɗin groupe ɗinta ta aiko mini na shiga ba tare da na san wannan shi ne takun farkona a cikin duniyar matsafa.Duka-duka mu bakwai ne cikin groupe ɗin,babu wata hira da muke yi sai ta sex da kuma videon batsa wani sa'in ma video call muke yi muna biya wa juna buƙata,a cikin irin wannan shiriritar ce muka fara yin gasar mazajen bogi ta hanyoyin biyawa juna buƙata da kanmu.Wata daga cikinmu ta bani wani abu wanda ba zan ce miki mene ne ba,ta ƙalubalance ni muddin na yi amfani da shi matsayin mijin tarayya na kwana ɗaya kacal to za ta bani 500k.Haka na yi ɗin duk da ina jinsa har cikin marata yana tokare ni haka na haƙura na cuci kaina akan kuɗi,yayin da su kuma suke tsaye a zahiri suna kallona.Bayan na gama kuwa ta bani kuɗin,ba tare da na san cewa duk don su ƙara kwaɗaita mini zama cikinsu ba ne mu ci gaba da sheƙewa” sai ta yi shiru tana mai ɗan lumshe idonta.
Na ce “mijinki fa ya sani?”
Kai ta girgiza mini kafin ta ci gaba da cewa “da na samu kuɗin dai na saya masa agogo sabuwa yayi murna sosai,ɓangaren auratayyarmu kuwa sai abubuwa suka canza na soma tsiro da abubuwan sheɗanci ina yi masa da sunan gamsar da shi,abin mamaki kuwa sosai yake jin daɗin haka ya kuma ƙara sona har yake mamakin yadda ban ƙyanƙyaminsa da nake kai bakina a wurin da yake bahaya” sai ta buɗe ido tana murmushi mai ciwo.Can ta ɗora da “wata rana kamar a MAFARKI haka na tsinci kaina wata duniya.Ƙawayen sharholiya suka ja ni wani gun don mu huta mu cashe,sai kuma tsari ya canza muka soma shiririta kafin kuma duk su tsaya cak suna masu haɗin baki su ce “lokaci yayi” duk sai suka zube ƙasa suka kuma roƙe ni na yi yadda suka yi ɗin,haka ni ma na zube gwiwana ƙasa ba tare da na san dalili ba.Babu jimawa wata tsohuwa ta bayyana,sanye take da baƙaƙen kaya,gashin kanta a buɗe yake wanda yayi fari ƙal,idonta kuwa sun shige sosai can cikin gurbi ko ƙyaftawa ba ta yi haka ta kafe ni da su tana kallona,ni kuwa zuciyata sai matsanancin bugawa take yi kamar zan mutuwa.
Cikin masifa take yi wa sauran faɗa tana zaginsu don me yasa ba su samo wasu members dayawa ba alhalin ta faɗa musu wannan karon mutane sosai take so.Kafin kuma ta juya ga karuwar mijina wacce ita ce shugabar groupe ɗinmu,ta tozarta ta sannan ta ce “me yasa ba ki sanar da ita tun farko ba? ” ba ta iya cewa komai ba,sai tsohuwar ta dawo kaina tana mai tambaya ta “me sunan mahaifiyarki?” na shaida mata sai kawai ta rufe ido tana kiran sunan Mamana,babu jimawa na soma jin kukanta haɗi da kakari.Ko da na koma gida kiran farko da na samu shi ne don a sanar da ni mutuwar Mamana,tun daga wannan lokacin kuma na yi alƙawarin ko mutuwa zan yi ba zan yi musu biyayya ba kin ji kuma inda farkon wata izayar ta soma yanzu haka ina jin motsinta za ta kawo mini ziyara domin amsa mata tambayarta a karo na ƙarshe na yarda na yi wa baƙin ruhi hidima ko kuwa na zaɓi ta binne ni da raina kamar sauran da suka bijire” tana gama bani labarin na farka.
Yadda na tsinci kaina a toilet yayi matuƙar bani mamaki,haka na yi tsarki na je kusan pampo na yi alwala.Da na fito na duba agogo sai na ga tuni lokacin sallar asubah ma ya yi,haka na yi nafila tare da farillar kafin na zauna ina lazumi ina kuma tunanin mafarkin da na yi.
Bayan na gama sai na fita,ɗakin Momy na je na gaishe ta tare da tambayarta abin da za a yi na breakfast ta faɗa mini sai na wuce kitchen.Tare da taimakon ƴar aikinmu na haɗa komai , lokacin da na gama tuni ƙarfe bakwai da rabi ta gota.A gaggauce na je na yi wanka na yi shirin makaranta,abicina ma sai cikin kula na zuba shi na wuce direba ya kai ni.
Ina sauka abu na farko da na fara yi shi ne duba inda yake parking motarsa,wurin wayam yake babu motar sai na ji babu daɗi.Haka na wuce ajinmu,bayan mun gaisa da Mujahida ne nake bata labarin mafarkin da na yi kafin na ƙara da cewa “ sosai fa na ji tsoro,kar ki so ki ga yadda na yi ta murna tare da yi wa Allah godiya da yasa mafarki ne”
“Amma abin da mamaki yake,kuma duk da kin farka bayan kin koma wani baccin matar ta sake dawowa ta baki ci gaban labarin?” Mujahida ta tambaya.
Na ja numfashi kafin na ce “shi ne abin da ya fi bani tsoro,kuma fa ina zaune cikin toilet.Haka kawai nake ji a raina wannan ba kawai MAFARKI ne ba”
Ta ɗan bangaje ni ta ce “dalla can matsoraciya wa ya sani ma ko Film ne kika kalla kawai kin manta ne kin yi dubin mafarki ne”
Na yi ƴar dariya ina mai cewa “in akwai wanda ya raina ni duniyar nan bayanki yake” ba ta kai ga cewa komai ba malam Ibrahim ya shigo.Abu na farko da ya ce mu yi shi ne raba mana takardun da zamu zana jarabawa haɗi questions ɗin.
Haka muka soma yi,duk wanda ya gama sai ya kai masa.Ina kammalawa na miƙe na kai masa,sai ya ƙi karɓa tare da cewa “ya jikin naki?”
“Alhamdullah!” na basa amsa tare da ajiye takardar kan teburi na fice.Idona na ƙara kaiwa wurin parking special amma har yanzu dai babu motarsa,haka kawai na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 14