Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙirjinsa,ruwan gemunsa suka ɗiga kan fuskata da wani matsanancin bugawar zuciya na yi baya saura ƙiris na faɗi Mujahida ta taro ni sai muka yi cirko-cirko muna ƴar kallon mu da Sheikh Rayyadeen..... Group biyu ne normal 300 , VIP kuma 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 .Kamar tun a talla na faɗa muku wannan sabon salo ne sabuwar sheƙa to haka take,nan duk shimfiɗa ce ba mu ma fara labarin ba. [14/12 15:15] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 06 Ban san me yasa yake yi mini ƙwarjini ba a duk lokacin da babu gilashi a idonsa,sai na dinga ganinsu tsirararsu girma da kyawunsu ya ƙara fitowa uwa uba wani abu da nake gani kwance a cikinsu mai ɗaga mini hankali da kaɗa hantar cikina. Mujahida ce ta yi ƙarfin halin gaishe shi “barka da warhaka Sheikh ” Bai amsa ba sai ni da yake kallo,ƙila gaisuwar tawa yake jira.Kai na sunne ina mai ƙara jimƙe hotonsa da ke hannuna.Bai ce mana kanzil ba saboda kiran sallar da aka ƙwala a masjid ɗin gidansu,yayi gaba yana jifata da mugun kallo yayin da ni kuma na ja wata ajiyar zuciya ta murna ina mai shigewa cikin falon . Ko ina tsaf yake sai ƙamshi ke tashi,kamar wacce ta san gidan haka na bi na tafi wancan sashen na jiya sai a lokacin ma na farga da Mujahida ba ta biyo ni ba.Zan juya kenan Ammy ta fito tana cewa “wa ke nan?” da sauri na juyo ina kallonta,a kunyace na gaishe ta ita kuma ta amsa mini da murmushinta tana ambaton sunana daga ƙarshe,babu wata magana don duk a daburce nake na ciro hoton Sheikh ɗin na miƙa mata.Sai ta karɓa ta duba tare da kallona da mamaki,“ina kika samu wannan hoton?” ta jefo mini tambayar. Shiru na yi,sai ma a wannan lokacin na ga wautata.Kame-kame na fara kafin daga ƙarshe na shaida mata mafarkin da na yi,duk illahirin jikinta ne na ga yana kyarma kafin ta ce “ MAFARKI?” Na jinjina mata kai,sai ta ja hannuna ta kai ni ɗakinta ta zaunar da ni tana mai cewa “zauna na yi sallah” banda wani zaɓin haka na zauna,yadda ta jima a sujidar ƙarshe yasa na ji ina ƙaunarta don na tabbata addu'a ce take yi. “Ammy?” na ji muryar Sheikh daga can falo,bai tsaya da kiran sunan nata ba yadda na ji amon muryarsa na tunkaro nan shi yasa na tashi da mugun sauri na buɗe wata ƙofa na shige ina dafe zuciya da tunanin na tsira sai dai nan ɗin ma wani tashin hankali na ci karo da shi .Fuskar tsohuwar nan Grand-Maa ce zaune raɗam a mirror ɗin toilet,babban tashin hankalin shi ne iya kanta ne kawai ya bayyana kuma a gundile babu gangar jiki. “Yiiiii!” ta girgiza gashin kanta tana bani tsoro na fasa ihu tare da banko ƙofar na fito,sam idona sun rufe da tsoro ban gansa ba haka na je na faɗa jikinsa tare da ƙanƙame shi gam ina kuka tare da rumtse idona ina cewa “aljana! Aljana!“ Kiciniyar hakice ni yake yi,sai dai sam na ƙi basa wannan damar don ba mugun riƙo na yi masa.Sai da Ammy ta yi magana ne sannan nutsuwata ta fara dawowa,“Khadeejatu?” ta furta tana mai jawo ni ta baya,na ɗan jan numfashi kafin a hankali na buɗe idona akan gemun Sheikh suka sauka,zuciyata na ɗan bugawa na soma sassauta riƙon da na yi masa ina mai ɗaga kai na dube shi.Idonsa ne na ga sun kaɗa sun yi ja,sai na ƙara ruɗe na ƙi sakin gefen cikinsa da na cikuikuye,kamar wani wanda bai da hankali haka yasa tafukan hannuwansa kan ƙirjina ya wani tura ni baya,saura ƙiris na faɗi amma Ammy ta tare ni.A zuciye ya fita ko sakan biyu bai ƙara ba,wani kuka ne ya zo mini wanda ban san na mene ne ba. Ammy ta fara rarrashina sai bayan na yi shiru sannan ta kamo hannuna ta ce “zo mu je ki nuna mini daidai ina ne kika tukunyar ” haka na bi bayanta muka je can bayan ɗakunansu na nuna mata wurin.Ta ja numfashi tana mai cewa “ Khadeejatu kin san wani mafarkin gaskiya ne,ta hanyarsa ce Allah subhanahu wata'ala yake nunawa muminai abin da ke faruwa a rayuwarsu.Ban san me lokaci ya tanadar muku ke da Deeni ba da har ƙaddararsa ta faɗo a tafin hannunki,ga shi ke ce za ki zamo silar warware wani baƙin ƙulli na rayuwarsa” Saurarenta kawai na yi amma ban ce komai ba,sai ta ci gaba da cewa “ki tsaya nan bari na je na dawo” kai na jinjina mata ta tafi ta bar ni nan. Tuna wa na yi yadda hannuwan Sheikh suka sauka a ƙirjina,duk da na san a bisa kuskure ne amma haka nake jin haushi .Ina nan tsaye Ammy ta dawo da abin haka rame,da sauri na karɓa na buga daidai wurin da aka nuna mini a mafarki.Bugu guda ne na yi amma sai ƙasar ta soma buɗewa da kanta, Ammy ta duƙa ta sa hannu ta soma janye sauran ƙasar da ke bakin rame cm.Hannunta na rawa ta ciro tukunyar tana mai ambaton sunan Ubangiji ,a gabana ta buɗe ta a ciki mun samu wandon Sheikh tun yana ɗan yaro sai kuma wani ƙwai mai kamar na jimina sai wasu tarkacen. Ƴar kallon-kallon muka soma yi ni da Ammy kafin na ji wata idea haka kawai ban san daga ina ta fito ba,“ki ƙona komai ni kuma ki bani tukunyar da kuma ƙwan na tafi da su” wani abin mamaki shi ne ko kaɗan Ammy ba ta yi gardama ba hakan kuwa ta yi ta miƙo mini tukunyar wacce ƙwai ke ciki na ɓoye ta a hijabi ,a haka muka rabu na fita waje sai dai babu key ɗin mota a hannuna kuma ban san inda yake ba. Don dole na koma can cikin gida,falon Ammy na shiga na kuwa same ta tuni ta zuba tarkacen a cikin kasko ta ƙyarta musu ashana. “Ammy makullin motata” na furta,haka aka ta bincikensa amma ba a gani ba. Ta ce “bari na kira Sheikh ya sauke ki” ba ta ma bari na furta wata kalma ba ta fita. Ammy na shiga ɗakinsa ta same shi a kwance gorar ruwan sanyi a hannunsa,yana jan numfashi duk da ta san abin da ke saka shi a wannan halin amma wannan karon sai ta ƙi nuna damuwarta ta ce “ka taso ka sauke Khadeejatu gida” Ya ɗago da sauri yana kallon Ammyn wacce ta haɗe rai ,kamar wani maraya cike da tausayin kansa ya ce “to” Sai ta fita ta barsa yana jin kamar ya kama da wuta ko kuma ya fasa ihu ƙila zai ji sassauci.Ya miƙe yana masifa yana cewa “ke ɗin ba masifa ba ce a gare ni a'a ke kanki matsala ce,a kullum banda fitina babu abin da kike kawowa a rayuwata duk in mun haɗu daga kina gudu sai kin faɗo jikina mtswww!” ya ja dogon tsaki kafin ya ci gaba da cewa “na tsane ki!” haka ya fita can farfajiya ya buɗe motarsa ya shiga yana jiran fitowarta. Ina nan tsaye Ammy ta shigo ta kama hannuna muka fito,sai ta sa key ta rufe ɗakinta kafin mu fito babban falo.Karo muka ci da Grand-Maa,cike da girmamawa Ammy ta gaishe ta amma tsabar munafurci irin nata sai cewa ta yi “Khadi wannan fa wace ce?” “Ƴata ce Maa ta kawo mini ziyara ne za ta koma gida” Ammy ta bata amsa. “Amma kamar na ganta a jiya” Ammy ta dube ni kafin ta ce “eh ta zo” “Tun da ta zo jiya ,yanzu kuma me ya maido ta? Munafurci ko me?” Ammy na jin haka ba ta ƙara tankata ba ta ja ni zuwa waje,idon Grand-Maa ƙur kaina tana kallon hijabina da dukkan alamu so take yi ta san mene ne ciki. Muna zuwa kusan motarsa Ammy ta buɗe mini gidan gaba,kasa shiga na yi na girgiza mata kai tare da buɗe baya na zauna.Ta yi murmushi ta ce “sai da safe Deejar Ammy ki gaishe mini da mamarki” A hankali na ce “to Ammyna” wata irin waigowa Sheikh yayi da sauri yana yi mini kallon mamaki mai cike da tsana kafin ya soma jan motar. Sai da muka hau kan titi ya ce “wace unguwa?” maimakon na basa amsa sai na soma leƙen fuskarsa,rai a ɗan ɓace ya sake tambayata sai a lokacin na shaida masa.Da muka shigo layin kuma na soma nuna masa har muka iso ƙofar gida,gabana ne ya faɗi rasss ganin duk ahalin gidan a waje har da masu gadi. Murya na rawa na cewa Sheikh “don girman Allah ka fita ka yi wa Daddyna bayani ko ƙarya ce ka yi masa ka ce daga makaranta nake motata ce ta lalace shi yasa ka ɗauko mu ni da Mujahida ” Wani irin rumtse ido Sheikh yayi yana jin zuciyarsa na azalzala,shi da yake hukunta ɗalibai akan in sun yi ƙarya amma yau shi ne ɗalibarsa ke son ya yi ƙarya.Fita ya yi ya je ya gaishe da su Daddy,ban san me ya faɗa musu ba sai na ga duk sun shiga cikin gida.Sai a lokacin ya buɗe mini na fito,na yi tsaye ina kallonsa yadda haiba da ƙwarjininsa suka fito.Motarsa ya rufe sannan ya yi gaba na dinga take masa baya,cike da mamaki nake kallon yadda yake sa kai ciki.Muna shiga falo sai na ga Momy har wani rawar jiki take yi wurin kawo ruwan sha,yayin da shi kuma Daddy ya nunawa Sheikh wurin zama .Ban wani jinkirta ba na haura can sama inda ɗakina yake,ƙarƙashin bed na ajiye tukunyar kafin na cire hijabina.Toilet na shiga na haɗa ruwan ɗumi na yi wanka na canza pad,yunwa nake ji amma kasa fita na yi ƙasa don na san bai tafi ba,har yanzu kuma ban bar mamakin dalilin da yasa Daddy bai ce mini komai ba alhalin yana da zafi sosai. A can falo kuwa cike da mutunta wa suke kula da Sheikh Rayyadeen,wanda shi ɗin ba ɓoyayye ba ne a wurinsu musamman ma Daddy wanda suke cikin association Islamic ta ƙasar Nijar shi da Sheikh ɗin.Ammy ita kuwa ta san shi a tv da kuma bakin mijinta in yana yi mata hirar addini,ko kaɗan Daddy hankalinsa bai tashi ba da Sheikh Rayyadeen ya fito ya shaida musu cewa ya kawo Khadeejatu ne gida a bisa umarnin mahaifiyarsa,sai dai yana mamakin meke haɗin Deejar da Ammy ɗin. Ummah dai na zaune tana kallon Sheikh Rayyadeen don ita ba ta san shi ba,amma sosai take mamakin ta ya babban malami kamar shi yake ɗauke da ƙulli-ƙulli na asiri a jikinsa.Hirar addini kawai suke yi kafin ya miƙe ya ce “ni zan koma” Daddy ne ya yi masa rakiya har zuwa ƙofar gida sannan ya dawo ciki, ya dubi Momy ya ce “je ki kirawo mini Ummita” Ina kwance ina wasiƙar jaki Momy ta shigo,da sauri na sunne kai ina jin gabana na faɗuwa.“Ki taso Daddynki na kira” shi ne kawai abin da ta faɗa ta fice,jiki babu ƙwari na zumbula hijabi na sauka.Kusa da Ummah na zauna ina mai kwantawa a jikinta,“daga ina kike? ” Daddy ya watso mini tambayar da ta tabbatar mini cewa Sheikh bai sanar da su komai ba.Wannan yasa na gyara zama na shararo ƙarya,“daga makaranta muke Daddy,motar da na ɗauka ce ta lalace ka san an kai mu ajin ƙarshe shi ne Mujahida ta zo muka tafi can don mu yi exercises ” “Amma shi Sheikh ce mini yayi Ammynsa tasa ya kawo ki gida” “Eh suna tare ne lokacin da suka haɗu da mu a hanya,ka san wani abu Daddy Ammynsa nada kirki sosai ” na faɗa ina murmushin ƙarfin hali don zuciyata cike take da fargaba. “Ina motar take yanzu?” “An kira mai gyara ya tafi da ita ,Ammy ta ce in an gyara za a kawo mini har gida” na basa amsa.A yadda na ga Daddy ya gamsu da hujjojina shi ya kwantar mini da hankali har na nemi abinci na ci. Ummah ta miƙe ta nufi ɗakinta tana mai cewa “ƙawali ki zo ki yi mini tausar ƙafa” Sarai na san halin Ummah babu wata tausa da zan yi mata ,tambayoyi ne za ta yi mini amma saboda ban jin tsoro ko shakkar sanar da ita sirrina kawai na miƙe na bi bayanta. Ina shiga kuwa ta jawo ni ta zaunar tare da tsura mini ido,na ja ɗan numfashi kafin na ce “gidansu ne na tafi Ummah ,kin san kusan shekara uku kenan nake ciwon son Sheikh Rayyadeen amma ban taɓa furta masa ba.Jiya kuma na yi wani mafarki da ya tsorata ni shi ne na je na shaidawa Ammynsa ” Ta ja numfashi kafin ta ce “ƙawali ba ki ganin mutumin nan yayi miki girma? Dube shi fa gudan dattijo da me Daddynki ya girme masa?” Na turo baki na ce “to ni ina ruwana da girmansa tun da ba goya shi zan yi ba na yi yawo?” Ta yi ƴar dariya kafin ta ce “lokaci yayi za ki fahimci abin da nake nufi.Matansa nawa?” “Bai taɓa aure ba” na bata amsa,ta ce “amma hotonsa ne na gani a hannunki ko?” na jinjina mata kai,ba ta ce komai ba sai jakarta da ta jawo.Magani ta kaɗa mini ta bani na sha,kafin na fita na koma ɗakina.Wayata na ɗauka na kira Mujahida,tana ɗauka na soma yi mata masifa.Ta sheƙe da dariya ta ce “ke ba fa zan tsaya ba Sheikh yayi dambuna ah to,kin ga yadda yake hararenmu kuwa?” Na ja tsuki ina mai cewa “to ai shi ya kawo ni gida” cike da mamaki ta ce “da gaske?” nan fa na bata labarin duk abin da ya faru. Ta ja numfashi ta ce “yanzu tukunyar na nan wurinki?” “Eh bari duk ranar da kika zo zan nuna miki ” na faɗa ina mai jingina jikin pilowe da na ɗora a baya,haka muka yi waya sosai ni da ita kafin mu yi sallama.Na cije leɓena na ƙasa ina mamakin maganar da na furtawa babban malami kamar Sheikh Rayyadeen,sai yanzu ma na ji kunya na rufe fuskata da tafin hannu ina mai cewa “ oh Khadeeja me ya shiga kanki da har za ki cewa Sheikh ya furta kalaman ƙarya?” sai kuma na ji tsoro kar ya ɗauke ni wata iri wacce ba ta da tarbiyya.Karon farko da na ji cewa ya zama dole na samu lambarsa,sai dai duk iya binciken shafinsa ban ga inda ya taɓa ɗora lambar ba a dole na haƙura na shiga rungume pilow ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba ya kai ni duniyata ta MAFARKI. Yau kuma cikin wata asibiti ce na tsinci ruhina,ina tafe ina dube-dube kamar wacce ta ɓata kafin kuma na soma shiga ɗaki bayan ɗaki har na isa wani mai lamba uku.A can ƙarshen gado na hango ta tana kuka,gashin kanta duk ya cunkushe haka ma kayan jikinta duk sun yage,yayin da fatarta ke fitar da jini saboda yagar kanta da take yi da manyan akaifunta. Ina yin tsaye bakin ƙofar ta tsaya cak da kukan da take yi tana kallona,a zahiri mahaukaciya ce amma a baɗini da hankalinta rasss. “Me yasa ki ke zaune a asibitin mahaukata alhalin da hankalinki?” ita ce tambayar da na jefo mata. Jikinta ta ƙanƙame tana mai cewa “alhaki ne! ” tako biyu na yi kawai amma na ganni a gabanta,hannunta na kama na jimƙe sosai sai ta soma magana kamar an kunna rediyo. “Ƴar talakawa ce ni,na auri talaka na rayu da shi na tsawon shekaru har na haifa masa ƴan mata biyu.Amma rayuwarmu na nan a talauce,ƙarfin babu ta sa na soma yin aikatau don ciyar da yarana saboda mijina ya koma cima zaune.Yawan aikin da nake yi yasa cikina ɓarewa ina tsaka da gugar tiles,nan na zube jini na bin ƙafafuna ina murƙususu.Na ɗan fita hayyacina na wani lokaci kafin na dawo normal,nan na yi tozali da abu ma fi girman ɗaga hankali.Uwar mai gidan da nake yi wa aiki ce na yi tozali da ita ta kwashe ɓarin da na yi ta saka shi a kwalba tana siɗar yatsunta da suka yi kace-kace da jini.Ƙwala-ƙwalan idonta kuma suna juyawa babu sirki kamar na ƴar tsanar roba,wagegen bakinta ta buɗe mini tana wani irin murmushin ajali kafin ta ce “ni da mai ciki ba mu iya zama wuri guda,yawuna tsinkewa suke yi ” wani tashin hankalin ne ya sake rufe ni,don kuwa na fahimci ita ɗin mayya ce na yunƙura da niyyar maƙure mata wuya shi ne ta cire igiyar da ke saita tunanina ta haɗiye a bakinta,kin ji dalilin zuwana a nan ɗin ” ta ƙarashe faɗa tana mai janye hannunta yayin da kuma idonta suke canza kala zuwa kore kamar dai na Rashida. Ina gama jin labarinta na fito daga cikin ɗakin,cikin wani lungu mai tsananin duhu wata mata ta bayyana a gare ni tana mai yi mini wani jawabi mai kamar bushara.“Duk wasu matsalolin da muke faɗa miki a MAFARKI don su nusar da ke ne gidan da kike son kutsa kanki ciki.Hadiza(cewa da Ummah mahaifiyar Daddy) ta yi wa duniyarmu hidima wannan yasa muka yi alƙawarin kare bayanta, wannan ɗin haƙinmu ne.Ungo wannan ruwan ki zuba su a cikin baƙar tukunyar da kika ɓoye a ƙarƙashin gado” ta ƙarashe tare da miƙo mini wata ƴar mitsitsiyar kwalba na karɓa tare da jimƙe ta gam cikin tafin hannuna.Daidai nan na farka,wata irin ƙirshiwa ce nake ji ina shirin dirowa daga kan gado na ji wani abu cikin hannuna ko da na duba sai na yi tozali da kwalba.Nan take kuma mafarkin da na yi ya dawo mini cikin kai,sauka na yi na jawo tukunyar na buɗe ta tare da zuba ruwan ciki wani abin mamaki shi ne yadda ɗigon ruwan da ba su wuce biyar ba amma suka kusan cika tukunyar .A sannu a hankali na ga ƙwan na ƙara girma yana yin motsi,kafin kuma ya soma tsagewa .Ido kawai na zuba ina kallo har ida buɗewa duka,wata ƴar jaririyar halitta ta fito mai kamar mutum kamar kuma aljana,tana da manyan ido da kunnuwa faka-faka sai ɗan ƙaramin hanci.Wani tsalle ta yi tare da yin suka kan jikina,na buɗe murya cincin ƙarfina na ƙwala razananiyar ƙara da mugun sauri ta sauka daga gare ni ta yi suka ta haye gadona tana mai zubo mini idonta da suke wasar canza launi.... Normal group 300, VIP 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [15/12 09:13] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋 🦋🦋🦋 🦋🦋 Mallakar : 🦋 Chamsiya Laouali Rabo ```MRS SADAUKI 💫✍️``` 07 Ban taɓa shiga tashin hankali ba irin na yanzu,kuka nake yi na rashin mafita.Ga shi dai ni ce da kaina na binciko wannan baƙin sirri amma kuma sam ban ji zan iya zama tare da aljana ba a ɗaki guda,ita kuwa shegiyar halittar sai ci gaba take da kallona tana juya ido kafin ta ce “ sunana Nina halittar prophecy,na rayu a wasu ƙarnikan baya,yanzu kuma kin sake haifata kin raya ni ” Jikin ƙofar toilet na ƙara matsawa na riƙe ta gam,jin kuma wata lukutar masifa wai ni na haife ta.Wani tsallen ta sake ta diro ƙasa kafin ta ci gaba da cewa “kar ki ji tsorona,aikina shi ne nusar da ke hanyar da za ki bi don cimma burinki na samu Sheikh Rayyadeen ” Ambaton sunansa da ta yi shi ya ɓarar mini da dukkan tsoronta da nake ji,kan gwiwaina na zube ina mai cewa “da gaske za ki taimaka mini na samu Sheikh Rayyadeen?” Ta jinjina kai kafin ta ce “bani hannunki na dama” a tsorace na miƙa mata su,caraf ta saka yatsana manuniya a baki ta dantse da haƙoranta wani abu ya shige ni mai kamar lantarki ya soma caza ni kafin wani lokaci na tsinci kaina kwance a kan capet Daddy da Momy da kuma Ummah kewaye da ni.Ɗaya bayan ɗaya na kalle su kafin na ja numfashi na ce “meke faruwa da ni kamar ni kamar ba ni ba?” “Alhamdullah tun da kin farka,je ki haɗa mata wani abu ta samu ta ci” cewar Daddy yana mai kallon Momy,amma Ummah ta yi karaf ta ce “a'a bari na haɗa mata” sai ta fita. Tashi na yi zaune ina mai ɗan lumshe ido haɗi da sauraren yadda jijiyar gefen wuyana ke wani bala'in harbawa.Babu jimawa Ummah ta kawo mini abinci,amma kallo guda na yi masa na san da ta saka magani amma haka na ci kafin in shiga toilet na yi wanka da ruwan ɗumi.Ko da na fito babu kowa ɗakin,kimtsawa na yi na saka sabuwar pad tare da uniform ɗin makaranta.Ina saukowa ƙasa duk sai suka yi murnar ganina,sai a lokacin na gaishe su Daddy ya ce “mu je na sauke ki makarantar a motata ” cike da jin daɗi na yi masa godiya kafin mu fita,yau a gaba na zauna kusan Daddyna sai da ya fara tuƙi a babban titi sannan ya miƙo mini wayata wacce ban san yaushe ya ɗauke ta ba kuma ni kaina da na tashi ban ma neme ta ba. Ina karɓarta sai na ga an ɗora mini hoton Sheikh Rayyadeen kan fuskar wayar,hakan ya tabbatar mini yanzu Daddy ya san mene ne burina wata irin kunya ce ta kama ni,sai kawai na sunne kai ina shafar screen ɗin da ke ɗauke da haske yana nuno mini abincin ruhina. “Tun yaushe kuka fara soyayya Ummita?” Daddy ya jefo mini tambayar. A kunyace na ce “Daddy ba soyayya muke yi ba,hasali ma bai san ina sonsa ba” “Don me? Ai sai ki sanar da shi” da sauri na ɗago kai na dube shi jin abin da yake cewa,ya jinjina mini kai kafin ya ce “manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kansa ya yi mana nuni da hakan,ya ce duk wanda muka ji muna so mu faɗa masa” Na rufe fuska na ce “ni dai Daddy kunya nake ji” yayi ƴar dariya kafin ya ce “duk da cewa ba zubar da aji ba ne mace ta furtawa namiji kalmar so,amma kuma na ji daɗin haka daga gare ki .Na san ba ke ce ta farko da kike sonsa ba,ƙila ma har wasu sun taɓa furta masa to ke ina so ki zama daban da sauran.Duk namiji in dai malami ne shi to yana ƙaunar ɗalibarsa ko ɗalibi mai ƙwazo,to ke yi ƙoƙarin kasancewa haka” A shagwaɓe na ce “Daddy tun tuni fa nake ta ƙoƙarin hakan,amma a cikin ajinmu fa har da mahadatan Alkur'ani akwai” “Ke ma ki haddace Ummita ” “In sha Allah Daddy” na furta daidai nan kuma muka kawo makarantar,har ciki ya shigar da ni na yi masa sallama na fita.Daddy na tafiya na kai dubana inda ake parking amma ban ga motarsa ba,jiki a sanyaye na nufi sabon ajinmu sai na tarar da wani sabon tsari wai layin da za mu zauna daban.A gaba na zauna,babu jimawa Mujahida ta zo ita ma bayan mun gaisa take cewa “yau kuma mafarkin me kika yi?” shiru na yi kafin na tuna matar da na gani a gadon asibiti,bayan na gama labarta mata ta ce “ko mu je can asibitin mahaukata ɗin mu gani?” Na ce “har mu tashi daga makarantar safe,amma kin san muddin na ganta har azahiri to wallahi zan sa a raina ba wai kawai MAFARKI ba ne akwai wani ɓoyayyen lamari da ke faruwa da ni” Shiru duk muka yi sakamakon shigowar malam Hafiz wanda ya kasance shugaban makarantar. “Ku fitar da littattafai ko kuma alƙur'ani ku yi karatu yanzu Sheikh ya kira ya

Chapter 5 of 14