Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fili ta furta “ina sonka Alfanso” karaf a kunnen Abba wanda yake shigowa,cikin kaɗuwar zuciya ya ce “uban wane ne Alfanso?” Ummah ta juyo a firgice sai dai ko kafin ta kai ga yi masa bayani ya rufe ta da duka,tun tana kaucewa har ta soma mayar da martani,ran Abba ya ɓace sosai ya fito waje ya ɗauki wuƙa yana ɓaɓatu “wato ni za ki dinga cin amana kina bin mazan banza sai na kashe ki yau” ita ma Ummah fitowa ta yi waje, Abba ya je zai caka mata wuƙa amma ta juya tsinin wuƙar zuwa ga Abba ta hanyar furta kalmar tsafi. Ihun Abba shi ya fito da ni daga cikin ɗakina,ban ida fita daga cikin mawuyacin hali ba na kuma shiga wani shock ɗin.Na ga lokacin da bakin Ummah ya motsa na kuma ji sarai abin da ta furta duk da kuwa kamar mai yin raɗa ta yi furicin.Babban tashin hankali a ciki kuma shi ne huda cikin Abba da wuƙar ta yi,nan take kuma jini ya soma yi masa zuba kafin ya faɗi warwas a ƙasa. Shigowar maƙwabta kuma kamar ƙyaftawar ido ce,ni ma wani furicin na yi wanda ya fito tun daga ƙasan zuciyata sai ga ni kusan Abba hannuna riƙe da wuƙar da ke soke a cikinsa har zuwa yanzu. Kururuwar Ummah cikin tashin hankali tana ambaton sunana shi ya ida jawo hankulan sauran maƙwabtan da ba su shigo ba.Raina ne nake jin yana ɓaci yayin da kunnuwana ke zuƙo mini munanan kalamai daga bakunan mutanen da suka shigo,babu jimawa kuma jiniyar motar ƴan sanda ta cika wurin.Sai da suka zo suka janye ni ne kawai na cire hannuna daga jikin wuƙar,tsakiyar ido na dubi Ummah ina yi mata wani kallo da ni kaina ban san ma'anarsa yayin da kuma ƴansanda suka maƙala mini ankwa suka fita da ni. Kamar wani kare haka wasu ɗaiɗaikun mutane suka fara jifata da duwatsu sai dai rasss nake kallon kowanne daga cikinsu .Har muka kai babban ofishin ƴansanda ban ce uffan ba,tun kafin a sauko ni daga cikin mota wani babban jami'i ya fito ya ce a wuce da ni kurkuku tun da dai an kama ni dumu-dumu cikin laifin kisan kai kenan babu buƙatar sai an shari'a. Ido kawai na rumtse tun da aka canza akalar motar zuwa kurkukun ƴan ta'adda.Motarmu na tsayawa suka fito da ni,sai da aka kai ni wani ɗaki aka canza mini kayan jikina zuwa na ƴan kaso aka kuma saka mini sarƙar ƙafa da ta hannu sannan aka kai ni masaukina.Wurin ko ta ina ƙwayaƙwayin lantarki ne manya-manya sun haska wurin kai ka ce rana ce,idanun mutane ƙur a kaina har aka buɗe ƙaton kejin da aka tunkuɗa ni na faɗi ƙasa warwas nan aka shiga yi mini dariya waɗanda suke masifafu suka shiga tsokanata suna yi mini waƙa.Cike da takaici na miƙe tsaye ina kallon kowanne sai na ga duk sun shiga hankalinsu suna wani ja da baya,daga can gefe na ji wasu masifafun IDON SHARRI(MRS SADAUKI) suna kallona ina waiga wa na ci karo da mamallakinsu,wani matashin saurayi ne da ba zai wuce shekara ashirin da bakwai ba.A kallon farko da na yi masa na ji a raina na samu aboki ,a hankali na cira ƙafata na fara tunkararsa kacar da aka ɗaure mini ƙafafu na fitar da wani irin sauti mai ƙarfi har na isa gare shi.Ina shirin zama ya dakatar da ni,“kar ka take mini yaro” wurin na duba sai dai ban ga komai ba,sai na ga ya kai hannu ya gusar da wani jaririn maciji ,tozali da idona suka yi da macijin shi ya bayyanar mini da wannan tururuwar da na taɓa gani a ƙafata,kamar ƙuda haka suka yaɓe macijin ba su barsa ba har sai da ya mutu.Nan take wanda na yi wa ɗaukar aboki na ga ya ɓingire ya faɗi babu numfashi,yayin da sauran cikin kejin suka fara yin ihun na kashe shi....... [18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 05 Cikin ikon Allah ni ma nake kallon gawar mutumin da ake ikirarin ni ne na kashe shi alhalin ko yatsansa ban taɓa ba.Tuni kururuwar mutane ta jawo hankali ƴansanda,suka shigo wasu suka fitar da gawar yayin da wasu ke tambayar ba'asi daga ƙarshe dai aka fito da ni aka kai ni wani keɓaɓen wuri wanda iskan shaƙa ma wuya yake yi tsabar matsatsi kuma ni ɗaya ne a ciki. Kamar wani kumurcin zaki haka nake hargowa ina jin wani abu daga can cikin ɓargon ruhina kamar yana son farkawa wanda hakan ba komai ba ne sai baƙin makamin iko da ke gudana yana rikiɗewa cikin jinina.Adadin fusatata iya adadin yadda inuwar ke daɗa luluɓe raunatacen ruhina mai ɗauke da ƙunci tun na yarinta.Kan kace wani abu na ji abun ya ɗauki mallakar komai nawa,tun daga gangar jikina,ruhina da kuma tunanina.Wani irin ɓacin rai da rashin imani ne nake jin yana tafasa ni yana fitar da tiririn zallar son yin kisa a duk mutumin da ya yi kuskuren shiga gonata. Ina nan a tsaye cikin sabon al'amarin da ya aure ni aka buɗe ƙofa haɗi da kunna hasken ɗakin.Wani babban jami'i ne ya shigo,kana kallon fuskarsa ka san bai da tausayi ko wasa a cikin aikinsa. “Ku cire masa wannan kacocin da kuka ɗaure shi da su” shi ne abin da ya faɗa yana mai kallona,ƴansandar da suka rako shi izuwa nan cike da tsoro suka ƙaraso jiki na yi musu rawa suka buɗe makullin da aka rufe kacar kafin su yi baya da sauri su ɓuya a bayan jami'in. Sai da ya yi mini kallon ƙurilla kafin ya ce “biyo bayana ” sai ya juya ni kuma na take masa baya har zuwa wani ofishi. Duk ƙamewa suka yi yayin da shi kuma cikin bayar da umarni ya ce “ku rubuta bayanin bogi ku ce an tura shi izuwa babban kurkuku don yanke masa hukuncin kisa,daga ɓangarena zan fitar da nawa jawaban” babu wanda ya yi masa gardama haka suka ƙame tare da yin biyayya ga umarninsa.Sai da aka bani wasu sabbin kaya na saka na cire na gidan yari. Cike da girmamawa kuma aka yi mana rakiya ni da shi zuwa bakin wata zuƙeƙiyar mota.A baya muka shiga ni da shi aka dinga sharara gudu da mu,har muka isa wani tabkeken wuri ban ce masa kanzil ba ina can cikin kogin tunanin dalilin da yasa Ummah ta kashe Abba da kuma shi nasa dalilin da ya so kashe ta. Hannuna ya riƙe,wani girrr ya ziyarce ni kamar na taɓa lantarki.Na juya na kai dubana gare shi,ya sakar mini murmushi kafin ya ce “mu fita” ban yi masa muso ba na buɗe ƙofa na fita nan na yi tozali da babbar hotel,ciki muka shiga yana mai yi mini magana “za mu kwana a nan zuwa ƙarfe uku na dare sai mu wuce” kai kawai na jinjina masa kafin mu shiga daga ciki,a reception aka bamu makullin ɗakunan da ya kama mana.Makullin hannuna na shiga juyawa ina jin wani abu na daban na ratsa ni,na ɗaga kai na kalli wanda ya bani key ɗin wato mai kula da hotel ɗin .A tattare da shi na hango zallar tsoro amma ban damu ba na share tare da yin gaba don nemo ɗakin da aka bani.Ina tsayuwa bakin ƙofar na ji wani irin iska na daban ya wuce shuuu,amma a haka na zura makullin ko kafin na juya shi sai na ji ƙofar na buɗe kanta handle na yin motsi kafin ƙiiii ƙofar ta buɗe mini ta bani hanya.Ƙafata ta hagu ita ce ta fara shiga,kamar na shiga wuta haka na ji jikina yayi tsammm wanda hakan yasa don dole na rumtse ido.Kamar walƙiya haka wani haske ya feso mini fuskar wata budurwa,sanye take da doguwar riga kanti kanta babu kallabi hakan ya bai wa doguwar sumar gashin dokin da ta saka bazuwa a kafaɗunta. Ba za ta wuce shekara ashirin da uku ba,tana da matuƙar kyawu.Yadda take tafiya cike da yanga shi ya ɗauki hankalin mutane da dama da suka zo wani wuri da ban san ina ne ba kawai dai na ganta tsakiyar taro.Kan kujera ta zauna,daga nan ne ta hangi wani mutum yana sanye da suit baƙaƙe tun na mutanen ƙarnin baya,ƙamshin jikinsa kamar na gawar da ta shekare a cikin rana madadin gidan sanyi.Kallonta yake yi cike da zallar maita,yayin da ita kuma ke jin tsikar jikinta na tashi wani irin sanyi na rufe ta maimakon kuma ta gudu a'a sai ma hakan ya tafi da imaninta.Miƙewa yayi daga inda yake ya zo ya miƙa mata hannu tare da yi mata magana ƙasan maƙoshi “taso mu tafi,na jima ina dakon zuwanki na tsawon shekaru masu yawa” ba tare da ta san dalili ba haka miƙe ta bi bayansa suka shiga wata mota har zuwa wannan hotel ɗin da muka zo ni da jami'i da aka basu key ɗin ɗaki kuwa wannan ɗakin nawa shi ne suka shigo. Da wani irin mugun ƙarfi na ja numfashi tare da yin baya na fito daga ɗakin ina fitar da gumi.Daga bayana na ji muryar jami'in yana cewa “zo mu je ɗakina” na juya na dube shi,ban yi masa muso ba nan ɗin ma na take masa baya. Muna shiga kamar wanda ya san irin abin da na gani sai cewa ya yi “Nadiya ƙaramar yarinya ce,ƴa ga shugaban ƴansanda wanda yayi ƙaurin suna wurin maƙiya.Duk duniyar nan babu abin da ya fi so irin Nadiya, wannan yasa ya killace ta ya haɗa ta da littatafai don ɗebe mata kewa.A wani dare ƙaddarar Nadiya ta canza ,bayan ta wuni tana karatu haka ta shirya ta tafi bikin shagalin ƙarin shekarar ƙawarta a nan ne ta haɗu da wani mutum wanda yayi daban da mutane.Duk da ta san haka amma ta bi bayansa,kaf ƙawayenta babu wanda ya iya ganin mutumin sun ce ita ɗaya ta fita.Hatta wannan hotel da suka zo masu kula da ita sun ce ita ɗaya ta shigo ta kama ɗaki,kuma da aka duba camara tsaro ta nuna iya ita ɗaya ce . Lokacin da suka shiga ɗaki sai ta kunna ƙwan lantarki,amma lokaci guda ya ɗauke daga nan babu abin da hoton bidiyon ya sake nunawa sai kukanta da kururuwarta haɗi kuma da wani yanayi marar daɗin ji da dukkan alamu tarayya ɓoyayyar siffar ke yi da ita.Sai bayan sati ɗaya sannan aka farga da mutuwarta saboda wari da ɗoyin da hotel ɗin ta ɗauka.An same ta a cikin toilet,jikinta babu sutura fatarta duk ta zagwanye.Fuskarta ta ɗauki wata irin mummunar siffa kamar ta zombie,babban tashin hankalin da aka fuskanta tattare da gawarta shi ne a cikin madubin banɗaki an hangi gangar jikinta na yin motsi wanda ke nuni da ba ta mutu ba tana raye.Can kuma aka ga bakinta ya motsa da aka bi didigin motsi laɓanta sai aka gane cewa ta furta kalmar “ga shi nan zuwa” wasu daga cikin ma'aikata suka gudu yayin da masu ƙarfin hali suka fito da gawar Nadiya aka binne ta.Tun daga wannan rana aka rufe wannan ɗakin ba a sake buɗe shi ba,amma ma'aikatan hotel ɗin sun tabbatar cewa duk dare suna jin sauti na fitowa daga cikin ɗakin wani sa'in kuma amon muryarta ne ke neman agaji ” yana kawowa nan sai yayi shiru. Na ce “to ni mene ne haɗina da duk wannan ɗin?” Ya bani amsa da “akwai haɗi sosai ma,yau bayan na kalli video ɗin da aka ɗauka a yayin kai ka can cikin kurkuku sai na ga shigen abin da ya faru ne da Nadiya ,sam babu wata alama ko shaida cewa kai ne ka kashe saurayin nan sai dai na ce wani abu da ke ƙunshe a ruhinka” ya faɗi haka tare da kunna mini video ɗin Nadiyar ta cikin ƴar ƙaramar system ɗinsa sai dai me zan gani? Fuskar Nelson ce shi ne wanda yayi tarayya da ƴar mutane.Sam ban san dalilinsa na yin haka ba,muryar jami'in na ji yana cewa “har zuwa yanzu da nake yi maka magana ba mu samo asalin wanda yayi wannan zaluncin ba,amma kai tabbas na san za ka iya gano wane ne saboda baiwar da kake tattare da ita” Idona na ɗauke daga kallon video ɗin Nadiyar na mayar da su kan fuskar jami'in,na haɗiye wasu yawu kafin na ce “wace irin baiwa?” “Je ka kwanta zuwa da safe za mu wuce” ya faɗa yana mai rufe system ɗin tare da nuna mini gado,wani kallo na yi masa mai cike da shakka kafin na je na kwanta ɗin.Ina lumshe ido na ji wani sabon al'amari kuma wanda ban yi zato ba,ruhina ne ke yin magana da esprit ɗina kan na kai ga tantance taƙamaimai abin da ke faruwa tunanina ya ɗan gushe sai tsintar kaina na yi a mutuware.Kamar kullum a zaune na tarar da Nelson kan banci yana shayi,gefensa na samu na zauna amma abin mamaki ya gane da wanzuwata har ma yana iya ganin ruhina. “Tun ɗazu nake zaman jiran ka ” shi ne abin da Nelson ya furta yayin da kuma ruhina ya ce “ni ma na zo ne mu yi wata magana ” “Abin da nake son sanar da kai ya fi muhimmanci kan wanda kai za ka faɗa mini” ya furta tare da miƙewa tsaye,sai na ga ya rabu gida biyu waninsa tsaye yayin da kuma waninsa ke zaune a take kuma na fahimci cewa shi ma yayi balaguron ruhi ne... ★UGANDA Tsugune take gaban wata ƴar ƙaramar rijiya tana leƙon baƙaƙen tafasasshen ruwan da ke ta zafir.Ba ta buɗe bakinta ba,iya idonta ne take juyawa wanda hakan shi ke ƙara hautsana baƙaƙen ruwan masu mugun kauri kamar narkakar dalma.Daga bayanta ta ji muryar Abbanta na kiran sunanta “ EZRA!” ba ta juyo ba sai da ta daidaita saitin idonta ya dawo normal,cikin wani irin rauni ta ga mahaifin nata na kallonta. Idonta ya kawo ruwa cikin amon muryartar wanda ya kasance da i'ina cikinsa wanda tun asalin haihuwarta da shi ta zo ta ce “Abiiih..kakkkar ka damu na ci alwaaa...shin zan nemo Ummi a duk inda take a faɗin duniyar nan” Abih ya kawar da kai kafin ya ce “ki tashi ki yi shirin makaranta kar ki makara ƙarfe bakwai ta kusa ” Cike da takaicin yadda mahaifinta a kullum yake ƙoƙarin ƙaryata abin da ke ƙunshe a zuciyarsa ta miƙe tsaye wanda hakan ya bai wa baƙar doguwar rigarta damar zubewa tana jan ƙasa.Kamar wata macijiya haka take tafiya sululu ba ka ma jin sawun takonta haka kuma kamar wata inuwa sam ido bai ganin lokacin da take cira ƙafarta. Tana shiga ɗaki ta buɗe wani akwati ta fiddo Bible wanda tsabar tsufansa har wasu takardun sun cire.Biro ta ɗauka da takarda ta rubuta wasu bayanai kafin ta rufe shi ,wani baƙin mayafi ta ɗauka ta yane dogon gashinta wanda ya zubo har gadon baya sannan ta fito. Har ta kai bakin ƙofa ta kuma cin karo da muryar mahaifinta yana cewa “ga wannan baƙin tabarau ki saka domin luluɓe idonki” Ta juya da mugun sauri tana kallonsa,sai ta ga sam Abih bai so suna haɗa ido yana kauce wa dubanta.Cikin saurin fushin da ya zama ɗabi'arta yasa ta yi amfani da idon nata ta fizgo tabarau ɗin ba tare da ta motsa ko da yatsan ƙafarta ba ne.Tana gama daidaita zaman tabarau ɗin ta fice cikin sauri,tana tafe tana furta wasu ɗalasimai da ita kaɗai ta san ma'anarsu har ta isa makarantarsu . Tun a bakin ƙofa kunnuwanta suka zuƙo mata gulmarta da ake yi a can ofis ɗin shugaban makarantar,cak ta yi tsaye tana mai kaɗa kunnuwan nata suna yin wani irin motsin rai haɗi da ɗan ƙara girma. “Ɗalibai da dama suna cutuwa saboda ita ,a ƙaf makarantar nan ita ɗaya ce Albino ta banbanta da students abin da ya fi shi ne kawai a sharanɗa mata saka safar hannu da kuma niƙaf ko kuma dai abin da zai rufe wannan ƙonanniyar fuskartata mai kamar zazzaɓin faɗuwar rana” shi ne abin da muryar wata mata ke faɗa kafin muryar wani mutum ta ɗora da “ya kamata kuma a lura da kyau a zuba mata ido,makin da take samu a kowace jarabawa ya wuce hankali duk ta ƙare tana amfani da baƙin tsafin gidansu ne”..... Yadda wani jinjirin Jemage yayi mata tsuwa a kunne ne ya janye hankalinta daga sauraren masu hana ruwa gudu.Ta ɗaga kanta sama tana mai kallonsa,babu shiri wani murmushi ya bayyana a fuskarta wanda haka ya bayyanar da haƙoranta masu kalar chocolat. A zahiri za ka ji kuka ne Jemagen ke yi,amma a baɗini magana ce yake yi mata.Idonta kawai take juyawa suna fitar da wani kalar haske kamar na wutar kyandir,tana a haka ta ji daga bayanta a rungume ta. “Koojal !” ta furta tana murmushi mai sauti,Jemagen ya ɓace kamar walƙiya yayin da kuma EZRA ta juyo tana facing ƙawarta Koojal wacce ta kasance makauniya ce ba ta gani. Cike da zumuɗi ta ce “EZRA yau dai za ki cika alƙawarin da ki ka yi mini” EZRA ta sake yin wani murmushin kafin ta ce “Yesu ya albarkaci rayuwarki Koojal ,da dukkan alamu kin ƙagu ki ga duniyar nan mai cike da ababen tsoro” Koojal ta ce “Ameine!(Tana nufin Amin kamar yadda in an yi wa musulmi addu'a yake cewa Amin !) Amma dai yau za ki buɗe mini ido ko?” “Ta buɗe miki ido kamar yaya? ” Malama Sharly ta faɗa wacce fitowarta kenan daga ofis ɗin shugaban makaranta.EZRA ta ƙure ta da ido tana mai juya su suka canza kala,cike da mugunta take haɗe fuska tana yi tana motsa bakinta sai ga Malama Sharly ta zube ƙasa,wanda ya yi daidai da tasowar guguwa iya inda suke ta luluɓe su tana wani laulaye su tana yin sama da su.Ita dai Kajool ba gani take yi ba kawai dai tana jin wani canji ne.EZRA ba ta tsayar da wannan guguwar ba sai da suka isa wani keɓaɓen wuri wanda ita kaɗai ta san ina ne. Cikin i'ina take kallon Madam Sharly tana cewa “tambaya kike ba? Ta ya zan yi na buɗe wa ƙawata Kajool ido? To idonki zan cire na saka mata” Kajool wacce ke tsaye kamar itaciya ta waro makafin idonta,yayin da kuma Madam Sharly ta yunƙura za ta gudu don kuwa tuni ta dawo hayyacinta.EZRA ta lumshe idonta ta fara karanta ɗalasima “akasubamatahe! Janukohiii! Jangooo! Jangooo! Jan...jan...jango!” wasu irin ƙananun baƙaƙen macizai suka ɓulɓulowa daga cikin ƙasa suka yi wa Madam Sharly sarƙa ta ko ina....... [18/12 13:06] MRS SADAUKI: https://chat.whatsapp.com/DINOgJaFqZuCh9dFNLLmp8?mode=ems_copy_t *INUWAR ALJAN*👻 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻 *FCWA*☀️ ________________________ 06 Wani irin murmushi ne EZRA ta yi wanda ba ka ganinsa sai ɗayan biyu,ko dai tana magana da masoyanta irinsu Jemagu,macizai ,kifaye da kuma ƙawarta Koojal, ko kuma in ta yi nasara ne akan wani abu da ta ƙudirta. Takardar da ta yi rubutu a kai ta fiddo kafin ta dubi Koojal ta ce “kar ki ji tsoro ƙawata,yanzu nan zan yi miki aiki idonki su buɗe” Kooljal ta yi ƙyaf-ƙyaf da idonta waɗanda suke farare tasss babu ɗigon baƙi ko ɗaya kafin ta ce “da gaske kuma na Madam Sharly ne za ki saka mini?” ba ta bata amsa ba,sai aikinta da ta fara tana karanto ɗalasimai kamar haka“marmaid nakhily bahee eyes! Kuncutacu habkur eyes ! Eyes” wata irin ƙara Madam Sharly ta soma yi ,yayin da kuma EZRA ta canza siffa daga mutum zuwa kifanyar ruwa,cikin zafin rai ta matsa kusa da ita tana mai sa hannu ta ciro idon Malama Sharly ɗin sannan ta dawo kusan Koojal ta shafi fuskarta nan take makafin idonta suka faɗo ƙasa kai ka ce dama na roba ne.Cike da ƙwarewa wurin tsafi EZRA ta ciro sanadarin ganin ta saka cikin gurbin idon Koojal sannan ta maida mata nata ɗin da suka zube ita ma Malama Sharly ta mayar mata da nata sai dai fa ba su da amfani. Tsaye ta yi gaban Koojal ta yi wani furicin a take ita kuma ta buɗe idon ta yi tozali da ƙawarta wacce tun tana makauniya take yawan shafar fuskarta sannan wani sa'in EZRA ɗin da kanta take siffanta mata yadda take wannan yasa ba ta yi mamakin ganin fuskarta fara ƙal ba irin ta Albino. “EZ..RA! ” ta furta murmushi mai haɗe da kuka yana kubce mata,rungume juna suka yi cike da murna kafin ta shiga yi mata godiya. “Ina Malama Sharly?” Koojal ta tambaya. EZRA ta ce“an mayar da ita makaranta” Koojal ta fara dube-dube ta ga manyan duwatsu ne ta ko ina ta ce “nan kuma ina ne?” “Farfajiyar Mermaid ce,an keɓance wannan wurin ne domin halittun ruwa masu rayuwa a doron duniyar bil'adama” EZRA ta bata amsa. Koojal ta ce “ko za ki iya zagayawa da ni? ” “A'a ba dai yau ba sai dai wani lokacin,yanzu za mu koma makaranta ne kafin a farga ba mu nan” ta faɗi haka tana mai kamo hannun ƙawarta,kamar tuntuɓe haka suka tsinci kansu a makaranta cikin kuma ajinsu.Wannan lamari ba ƙaramin burge Koojal ya yi ba,don ita a duniya tana son abin almara sai kuma Allah ya haɗa ta da matsafiya. Cikin ƙasa-ƙasa da murya ta ce “yanzu da nake gani mutane suna iya ganewa ?” EZRA ta girgiza mata kai,daidai nan malaminsu ya shigo ajin wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi gulmarta. Darasi ya fara yana tambayoyi amma babu wanda ya sani sai EZRA,duk da ya ga tana ɗaga hannu amma ƙin saka ta yayi ya juya ya ci gaba da rubutunsa. Koojal ta dubi littafinta irin wanda makafi ke aiki da shi mai kamar na'ura,shafa shi ta fara yi tana mai kallon rubutun sai ta ji tamkar wata murya na karanto mata abin da ke rubuce ba tare da ta san idanuwanta ke karatun ba. “Koojal?” malamin ya kira sunanta,cikin sauri ta ce “na'am malam” “In kin ga matsafi a gabanki mene ne farkon abin da za ki? Shin za ki guduwa ne ko yaya?” ita ce tambayar da malam ya jefo mata. Koojal ta basa amsa da “zan gaishe shi cike da girmamawa saboda babu abin da ya fi burge ni a duniya kamar tsafi da matsafi” Duk da ya ji haushin amsar haka ya ƙara jefo mata wata tambayar,“in ya yi ƙoƙarin cutar da ke fa wane mataki za ki ɗauka?” “Zan karanto addu'o'in kongosa na neman kariya Yesu ya taimake ni ” ta basa amsa.Sai ya saki murmushin jin daɗi ya ce “ta ya ake gane matsafi? Ina tambaya ne ga duk ƴan aji” Duk kowa shiru ya yi,can ya ci gaba da cewa “Maraton babban malamin Kiristanci ya ce duk wani matsafi ya tsani Bible da kuma Cross wannan ne yasa za ku ga da yawan mabiya addinin ke maƙale da Cross ko kuma ɗan ƙaramin icce mai hoton inda aka maƙala abin bauta Yesu Almasihu wannan babbar kariya ce.Sannan ya ƙara da cewa addu'ar Yesu Almasihu ka cece mu ta yi nauyi a bakin matsafi.Ku maimaita YESU KA CECE MU!” duk ƴan ajin suka furta amma banda EZRA sai kuma ya ci gaba da kawo wasu addu'o'in waɗanda suka saka kanta fara juyawa tana jin tamkar suna ƙona ta ne. Daga nan inda take zaune ta soma jin jijiyoyin jikinta suna wata irin kumbura suna ƙara girma,ta ware idonta waɗanda hucin azabar halin da take ciki ne ya haddasa suka rine suka zama kamar nunannen tumatur.Kan malam Rohan ta sauke su wanda shi kuma tsabar kaɗuwa da ganin lukutar masifa ya soma yin fitsari a wando ji kake shaaa kamar raƙumi na fitsari.Duk ƴan aji suka sa dariya,babu wanda kuma ya lura da halin da EZRA take ciki in banda shi wanda ya yi sanadiyar shigarta. Kamar wanda lantarki ya damƙe haka ya kasa yin motsi yana mai ci gaba da kallonta don dole don ita ce da kanta ta hana jijiyoyin jikinsa ci gaba da aiki.Cikin ƙaraji ta yi amfani da wata guragurbin murya mai matuƙar firgitarwa ta ce “wato so kake yi a lalle dole sai ka murƙushe baiwar tsafi da ke gudana a jinina da kuma ire-irena? Ka makaro domin kuwa na da ɗan lokaci tutar tsafi ce za ta dinga

Chapter 11 of 14