masa.
Da ƙyar ya miƙa hannu ya karɓe shi, har zai shiga gida abokinsa Sani wanzan ya zo wucewa. Ya kalli Baba Saleh sai kawai ya tuntsire da wata irin dariya, wacce shi kaɗai ya san manufar yin ta. Haka kawai gaban Baba Sale ya faɗi, amma sai kawai maze ya wurga masa harara ya shige gida.
Ɗan Bushir ban da yage baki yana kuka babu abin da yake yi. Yana zuwa ya kwantar da shi a kan gado, ya sa gefen rigarsa ya share hawayen ya ce.
"Ɗan Bishiririna! Ɗan Bishiri ka yi haƙuri ban kyauta maka ba ko? Yanzu me kake so na sayo maka?"
Ɗan Bishir ya kalli gabas da yamma, ya kalli mahaifiyarsa da ke gefe a zaune kalli mahaifinsa. Sai ya sake ɓarke baki ya saki kuka.
Ƙirjin Baba Sale ya buga da ƙarfi ya jikinsa yana rawa, ya rungume Ɗan Bishir ya dubi Uwale fuska shaɓe-shaɓe ya ce.
"Uwale tsoro nake ji, wallahi ina cikin tashin hankali."
Uwale ta sauke ajiyar zuciya, saboda ta san za a yi haka ko ma fiye da haka.
"Me ya faru mai gida?"
Baba Sale ya ja gefen ɗan kwalinta ya share hawaye ya ce. "Ina tsoron ko dai an guntule Ɗan Bishir gabaɗaya, Uwale kada fa Bala wanzan ya nakashe mini ɗan ɗaya-ɗayana..."
Kuka ya ci ƙarfinsa.
"Yanzu mai gida duk yaran da ka dinga yi wa shayi, iyayensu ba su ce za ka nakasa musu 'ya'ya ba sai da abin ya zo kanka? Kamar ba ka san yadda Bala yake da ƙware a harkar wanzanci ba? Kar ka manta shi fa ɗan gado ne."
A hassale Baba Sale ya ce.
"Kowa ai nasa ya sani, ni gudan jinina kuma magajina na sani don haka a kansa zan yi magana..."
Ita ma Uwale ta katse shi.
"To ai ɗa na kowa ne, shi ya sa ɗa da dukiya ba a yi musu mugunta. Kuma hausawa suka ka ƙi naka duniya ta so shi, ka kuma so naka duniya ta ƙi shi. Wallahi wannan zazzafar soyayyar da kake yi wa Ɗan Bishir ba za ta kai ka ba. Don ba zan ɓoye maka ba a cikin gidan kowa haushinsa yake ji, ko kaɗan ba shi da farin jini a wurin yara da manya."
Wani irin kallo ya shiga wurga mata, yana jin a ransa yadda ta caɓa wa Ɗan Bishir baƙaƙen maganganu da ace ba a yi masa kaciya ba, babu abin da zai hana bai kora ta gidansu ba. To don dai ya san idan ta tafi babu mai jinyarsa.
"Baaabaaaa!"
Ɗan Bishir ya furta a shagwaɓe, da sauri Baba Sale ya amsa masa sai ya ce.
"Zan ci abincin Rahina, daɗi gare shi. Ni ba zan ci komai ba sai abinci ko shayinta."
Zumbur Baba Sale ya miƙe ya ce, "Ai kuwa yanzu zan karɓo maka, zauna Ɗan Bishiririna ga ni nan zuwa." Ya ƙarasa maganar yana zuwa bakin ƙofa, ya waigo yana jifan Uwale da harara ya ce.
"Shi Ɗan Bishir dai ya zama kabewar kan kabari baƙincikin mai taushe, duk wani mahassadi sai dai ya gan shi ya ƙyale."
Daga haka ya fice daga ɗakin.
Kai tsaye sashen Labaran ya wuce, daga bakin ƙofa ya tsaya yana sallama. A lokacin Rahina ta tsakar gida a zaune tana shan iska, Labaran yana wanka a ta bayan kitchen ɗinsu don ya ce kafin ya samu kuɗin da zai rufa musu banɗakin sashensu, a nan za su dinga wanka saboda abin da ya faru da Rahina.
"Wa alaikassalam."
Rahina ta amsa sallamar tana yunƙurin miƙewa domin ta saka hijabinta, daga can gefe ta ji Labaran ya ce.
"Kada ki sake ki ƙara magana."
Shiru ta yi saboda ta san zafin kishinsa, shi kuma Baba Sale jin an amsa ya saki murya ya ce.
"Amarya mai daɗin tuwo da miya, angon na ki yana ciki?"
Wannan yabon da Labaran ya ji ana yi wa Rahina ya sake ɓata ransa, don haka ya zura gajeren wandonsa ko kunfar jinsa bai wanke ba ya fita fururu ƙofar gida.
"Lafiya Labaran me yake faruwa?" Baba Sale ya furta fuska ɗauke da mamaki.
Labaran ya yarfe kumfar fuskarsa ya ce, "Ita ta kawo haka! Ka san dai abin da ka aikata haramci ne ko? Ka zo ƙofar gida ka zage muryarka kana magana iyalina tana sauraronka, ba ka tsammanin ta ji muryarka ta yi mata daɗi?" Ran Baba Sale ne ya ɓaci, amma da ya tuna Ɗan Bishir ya zo nemarwa abinci sai ya wayance.
"Labaran kenan, yanzu dai duk ba wannan ba. Wallahi Ɗan Bishir ne yake son cin abincin Rahina, saboda zaƙin girkinta kasan na daban ne."
Tun Baba Sale bai gama magana ba Labaran ya hau huci, rai a ɓace ya ce.
"Allah Ya isa, wallahi ba zan yafe maka ba, da wannan yabon. Yanzu saboda Allah abincin Rahina ne wani zindiƙin sankacecen ƙato yake yabawa haka?"
Zuciya ta fara ciwo Baba Sale ya ce, "Kai Labaran kada ka faɗa mini maganar banza da wofi, ban da aska da tasha jinin Ɗan Bishir ka isa na tako wurinka neman abinci ne? Ka faɗa mini ko nawa ne zan biya ka, ka sayar mini abincin nata."
Labaran ya buga tsalle kamar mai shirin tashi sama, saboda yadda kishi ya tirniƙe shi ya ce.
"Ba askar kaciya ba Allah Ya sa abba-tuwa ce a kansa, wallahi ba zai ci abincin Rahina ba. Yanzu ni kake kallo ka ce na sayar maka da abincin Rahina? Ko kasan sayar maka da abincin nan daidai yake da na sayar maka da wani tsagi na daga baiwar da Allah ya ba ta?"
Haush ya sake mamaye Baba Sale sai kawai ya zuciya zai faɗa gidan, da sauri Labaran ya suri wani ƙaton itace. Ganin haka ya sa Baba Sale ya fice, shi kuma ya rufa masa baya yana faɗin.
"Jama'a ku tare ga baƙin kwarto mai lasisi nan."
Baba Sale yana faɗawa cikin gida ya danno ƙofar ya saka sakata, Labaran ya yi bugun duniya bai buɗe masa ba.
Ganin yadda Mahmud ya yi zuru yana nazari ya sa Mudassir ya taɓo shi ya ce.
"Wai me yake faruwa ne?"
Mahmud ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi Mudassir na haɗu da wani iftila'i a cikin wannan ƙauyen, ina cikin damuwa kuwa matuƙar Mai gari ya gano ni."
Mudassir ya bi shi da kallon mamaki don a iya saninsa da Mahmud, wannan ne zuwansa garin na farko, saboda har yana kan hanya shi ya dinga yi masa kwatance. A tsorace Mahmud ya kwashe duk abin da ya faru tsakaninsa da Laraba ya ba shi labari, tun bai rufe baki ba Mudassir ya dinga sheƙa masa dariyar ƙeta. Haushi ne ya kama shi, ya dube shi rai a ɓace ya ce.
"Ka ma mayar da ni ɗan iska wato ga mahaukaci ko?"
Cikin dariya Mudassir ya girgiza masa kai ya ce, "Wallahi a garin wannan tsoron naka watarana sai ka halaka kanka. Yanzu kai Mahmud aljanu ne za su kai ka su baro? An ma kuwa aljanar gaske ce? Ace aljanu su nemi ya yanka musu zabi su tafi da su? Gaskiya akwai ayar tambaya."
Jiki a sanyaye Mahmud ya ce.
"Wallahi a wannan dajin ba na jin za a samu bil'adama a cikinsa, kai ganin idona na fahimci ba mutum ba ce. Yanzu tun da ka ce dole mu gabatar da kanmu wurin mai gari sai dai ka wakilce mu."
"Kai ka san yadda mutanen ƙauye suka ɗauki mai gari kuwa? Ai dole sai mun haɗu mun gabatar da kanmu ya san da zamanmu a garinsa, wallahi yadda ka ci ubansa shi ma haka zai ci na ka idan ya gano ka."
Mudassir ya furta yana gimtse dariyarsa.
Wata dabara ce ta faɗo wa Mahmud ya saki murmushi a fili ya ce. "Mu je gidan da ka ce za mu sauka, na san yadda zan yi da su."
Mudassir ya shiga kwatanta masa hanyar, suka sauya akalar hanyar zuwa wani ɗan madaidaicin gida mai ɗaki biyu wanda babu kowa a cikinsa.
Mudassir ne ya ɗauko mukulli ya buɗe musu ƙofar suka shiga da kayansu, a kan wani ɗan ƙanƙanin gas da Mahmud ya taho musu da shi suka ɗora ruwan wanka. Sai da suka yi wanka suka sha ruwan tea da Mudassir ya dafa musu, sannan ya ce su shirya zuwa wurin mai gari.
Mahmud shadda ya saka fara ƙal, ya ɗauko hula ya saka. Sai kuma ya saka face mask a fuskarsa idonsa yana sanye da glass. Mudassir kuwa ya saka ƙananan kaya sun yi kyau sosai, duk hanyar da suka bi sai abi su da kallo ana ganin 'yan birni sun shigo garin. Lokacin da suka ƙarasa ƙofar gidan mai gari shiru suka ji shi kamar babu mutane, a ƙofar gidan suka tsaya duk da Mahmud ya rufe fuskarsa amma gabansa faɗuwa yake kada Mai gari ya gano shi.
"Salamu alaikum!"
Mudassir ya yi sallama yana zura kai soron mai gari. Shiru suka ji ba a amsa ba, da yake ɗakin Mai gari a soro yake yana jin duk abin da suke faɗa.
"Na yi mamaki da na ji ba a amsa sallamar ba, ɗazu fa da na zo a kan idona ya shiga gida."
Mahmud ya furta a hankali, shi kuma Mai gari jin haka ya sa cikinsa ya sake kaɗawa, don ya yi tunanin hukumar kare haƙƙin aljanun ce ta sake turo wakilanta. Yana daga cikin ɗakinsa gumi ya shiga keto masa, wani ɗan matsakaicin matashi da ya zo wucewa ganin su Mahmud a tsaye ya ce.
"Wai Mai gari kuke nema?"
Mudassir ya gyaɗa masa kai, don yaron ya yi musu magana da biyu ne saboda ya birge abokansa da ke can labe suna kallonsu. Ko babu komai dai ya san ya yi wa 'yan birni magana.
"Idan kuka yi magana bai amsa ba, yana nan cikin ɗakinsa ku ƙwanƙwasa masa."
Yaron ya furta yana niyyar wucewa, Mudassir ya ce masa.
"Don Allah zo ka shiga ka yi mana sallama da shi, ka ce baƙi ne suka zo akwai muhimmiyar maganar da suke son tattaunawa da shi."
Gaban Mai gari ya sake faɗuwa, nan take jikinsa ya shiga karkarwa. Jin furucin saurayin da kuma baƙin da suke ƙofar gidan, ya sa shi sake firgicewa musamman da ya kallo ƙauren ɗakinsa ya karye ba shi da damar rufewa duk abin da zai faru sai dai ya faru da shi. Doguwar rigar shaddar jikinsa ya cire, ya zame dogon wandonsa daga shi sai gajeren wando. Don haka ya wala ƙafafuwa ya saita bakin ƙofa, cikin shirin ko-ta-kwama. Don ya ci alwashin sai dai ya fice a guje amma ba zai zaune hukumar kare haƙƙin aljanun ta sake hukunta shi. Musamman da ya san idan suka ritsa shi a ɗakin babu mai ƙwatarsa sai Allah.. Cikin murna yaron ya shiga soron gidan Mai gari yana sallama, ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin zai yi magana sai ji ya yi Mai gari ya fito a guje ya baje shi a ƙasa. Ya tattakura ya fita da gudu, a daidai lokacin, yaron ya fasa ihu saboda zafin buguwar da ya yi. Su kuma su Mudassir ganin yanayin da Mai gari ya fita a guje su ma sai suka rufa masa baya suna gudu, don a tsammaninsu wani abin ne ya koro shi daga cikin gidan. Saboda yadda Mahmud ya fi tsorata shi ne yake biye da Mai gari, hularsa da glass ɗinsa sai da suka yi kusa tsalle uku sannan suka faɗi a ƙasa. Abin da ya sake ɗaga hankalin mai gari, yadda ya ga duk waigen da ya yi sai ya ga su Mahmud suna biyo shi a baya. Don haka ya tattakura ya ce.
"Jama'a ku kawo mini ɗauki, hukumar kare haƙƙin wancan jinsin za su halake ni."
A madadin a samu wasu su fahimci maganar Mai gari, sai dai duk majalisar da suka wuce su ma sai su rufa musu baya saboda tun da suke ba su taɓa ganin Mai gari da gajeren wando yana gudu ba.
Sai da Inno ta bari jikin Malam ya sarara masa da zafi, sannan ta sake aikawa ɗaya bayan ɗaya ta kira iyalanta. Tun da suka shiga ɗakin suka fahimci ran Inno ya gama ɓaci, Malam kallo ɗaya ya yi wa Yaya Inu ya ji gabansa ya faɗi, don haka ya sauke kansa ƙasa.
"Gabaɗaya na tara ku ne domin na yi muku godiya a kan cin mutumcin da kuka yi mini. Ba malam kuka wulaƙanta ba, ni kuka wulaƙanta. Idan har saboda na ce za mu yi aure da Malam ne kuka yi haka mu zuba ni da ku, a yau ba sai gobe ba zan yi wa Malam Liman magana bayan sallar Magriba a ɗaura mana aure."
Gabaɗaya shiru suka yi Baba Ibrahim ya ya ce, "Har ga Allah Inno ni ban san abin da ya faru ba, hasali ma ba na gidan a lokacin da abin ya faru."
"Dama ni ban ce kai ba ne Iro, jikina yana ba ni Inusa ne saboda na yanka zakarunsa na dafawa malam."
Malam da ya tuna gargaɗin Yaya Inu ya yi sauri ya ce, "A'a Inno ba na jin Inu zai aikata mini haka."
Inno ta sake ba wa Malam haƙuri, ta kuma ba su umarnin da su ba shi haƙuri tare da biyan kuɗin sadaki dubu hamsin. Babu yadda suka iya haka suka ba shi haƙuri sannan suka fice. Suna fita Inno ta aika aka kira mata Malam Liman, bayan sun gaisa ta kawo kuɗi ta damƙa masa na sadaki. Ta yi masa bayanin duk abin da ya faru, Malam Liman ya yi mata Allah sanya alheri sannan ya tafi.
Bayan sallar Magriba kuma aka ɗaura auren Inno da Mai Yasin a kan sadaki naira dubu hamsin. Lokaci ɗaya gari ya ɗauka a kan maganar auren Inno, baƙinciki ya mamaye su Baba Ibrahim.
"Magana ta gaskiya hankalina bai kwanta da wannan mutumin ba, na ɗauka maganar auren nan za ta kwana biyu har na yi musu gwajin jini saboda muhimmancinsa. Gaskiya duk kun jagula al'amarin nan."
Baba Ibrahim ya furta cike da takaici.
"Uwar me gwajin zai yi ne da ka addabe mu da zan can nasara, da tun can da ake yin aure babu gwajin me ya faru da mutanen baya? Ko shi Baffa lokacin da zai auri Inno an yi musu gwajin ne? Kai ni ba wannan ne agabana ba, fargabata kada tsohon nan ya sake gangancin taɓo garkena."
Yaya Inu ya faɗa. Baba Ado ya tuntsire da dariyar ƙeta ya ce, "To garkenka kuma ai sai dai kar a kuma, ba ka ji labarin Inno ta sa an fita da matashin ragonka ba? Ɗazu nan fa aka wuce musu da shi wai Ali mai tsire ne ya gasa musu..."
Tun bai gama magana ba Yaya Inu ya shaƙo wuyansa jikinsa yana rawa ya ce.
"In ji uban wa?"
Baba Ado ya zame hannunsa yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya, jikin Yaya Inu ne ya sake sanyi don ya san Ado da miskilanci idan ka ga dariyarsa to wata ƙetar ya samu.
Bai iya tankawa 'yan'uwansa ba ya faɗa cikin gidan da sauri, kai tsaye ɗakin Malam ya nufa don a can yake jin muryarsu sama-sama. Kamar wanda aka jefe haka ya faɗa ɗakin, Yaya Inu ya yi turus ganin wani shimfiɗeɗen gasasshen nama a gaban su Inno suna reɗa da wuƙa. Ta ci sabuwar atamfa sai murmushi take, Malam da bai san naman ragon Baba Inu suke ci ba, ya sake yanko wata shimfiɗeɗiyar tsoka cikin gadara ya tura a baki.
Yaya Inu da ya rasa mafita sai kawai ya zauna a bakin ƙofar ya fashe da kuka, Sai a lokacin Inno ta lura da shi. Ta washe baki ta ce, "Kai Ɗan Inuna, a duniya me za ka yi wa kuka tun da kana faranta ran iyaye. Wai dama haka ragon nan ya kiwatu, ni fa lokacin da ka ce mini an taya shi dubu hamsin na yi mamaki. Ashe-ashe rabon mu sharɓi ganimarsa a daren tariya ta da babanku ne."
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻
SHAFI NA TAKWAS
Duk maganar da Inno take yi babu ɗaya da Baba Inu yake ganewa, saboda wata irin juwa da ya ji tana ɗibansa. Hankali a tashe Mai Yasin ya furzar da naman bakinsa, gabansa yana bugawa ya dubi Inno ya ce.
"Inno kina nufin wannan ragon da aka gaso mana muke ci ragon Inusa ne?"
Cike da son birgewa Inno ta saki murmushi ta ce, "Ragon Inusa ne, ai sau biyar ana taya shi yana ƙin sayar da shi, mutumin ƙarshe da ya zo ko sati uku ba a yi ba dubu saba'in ya taya shi." Inno ta kalli wurin Yaya Inu da har lokacin kuka yake yi kamar wanda mahaifiyarsa ta mutu, ta kalli Mai Yasin da ya gama firgicewa ta ce.
"Na jima ban ci gashin nama da ya yi daɗi kamar wannan ba, ai wallahi Inusa Allah ne kaɗai zai biya shi saboda ko lokacin da na sa aka fita da ragon ba ya gidan..."
Kukan da Mai Yasin ya saki ne ya katse furucin da Inno take yi, hankali a tashe ta dube shi haɗe da faɗin.
"Malam lafiya kuwa?"
Mai Yasin ya girgiza mata kai cikin kuka ya ce, "Babu komai Inno, kawai ina taya Inusa jimamin rashin ragon da ya yi. Gaskiya Inno ba ki kyauta masa ba, me ya sa ba ki nemi jin ta bakinsa ba kafin a yanka."
Mai Yasin yana gama faɗar haka ya sake ɓarkewa da kuka. Sororo Inno ta yi jin abin da ya faɗa, saboda yadda ta san shi da son nama ba ta taɓa tsammanin zai faɗi haka ba.
"Malam ai saboda wancan karon na ga ya ji haushin zakarun da aka yanka masa shi ya sa na ɗauki rago, yanzu da a zo duk bayan kwana biyu muna yanka zakaru ba gara mu yi mai gabaɗaya ba."
Mai Yasin yana haɗa ido da Yaya Inu ya ga ya yi masa wani mugun kallo, mai ɗauke da manufar za mu haɗu da kai, sai kawai ya cusa kansa cikin cinyoyi kamar ƙaramin yaro ya sake ɓarkewa da kuka. Shiru Inno ta yi ta rasa bakin magana, kukan Yaya Inu da na Mai Yasin ya cika ɗakin. Jiki a sanyaye Yaya Inu ya miƙe yana dafa bango, don ji ya yi wata hajijiya tana yunƙurin taɗe masa ƙafarsa. A daddafe ya fice daga sashen su Inno ya wuce sashensa, su Baba Ibrahim suna wurin da ya bar su amma saboda halin da ya shiga ya sa har ya wuce bai tanka musu ba. Zazzafan zazzaɓi ne ya rufe shi don haka ya shige ɗakinsa ya ja bargo ya rufa, domin kusan a ƙasa da shekara goma sha biyar wannan ce asara mafi muni da ya tafka.
Bayan Yaya Inu ya wuce sashensa, Baba Ibrahim ne ya shiga sashen Inno ya yi sallama daga tsakar gida, Inno ce kawai ta amsa masa ya yi gyaran murya sannan ya ce.
"Inno dama wata 'yar magana gare ni idan babu damuwa."
Daga can ɓangaren Inno ta ce, "Na taso ko za ka shigo ciki?"
Baba Ibrahim ya ji daɗi yadda ya ji muryar Inno wasai, don haka yake fatan Allah Ya sa ta ba shi haɗin kai a game da buƙatar da zai je musu da ita. Ya matsa bakin ƙofar sannan ya ce.
"A'a zan shigo ma, da yake maganar da ku duka za mu tattauna."
Sai da Inno ta amsa masa sannan ya shiga cikin ɗakin ya zauna daga gefe, ganin har lokacin Mai Yasin bai daina kuka ba ya sa mamaki ya kama Baba Ibrahim don haka ya ce.
"Inno lafiya? Me ya samu Malam?"
Inno ta ɗan canza fuska ta ce. "Wai fa don ya ji na ce ragon Inusa na saka aka gasa mana, shi ne yake taya shi kukan jimami!" Baba Ibrahim ya yi ƙuri yana kallon Malam, saboda haka kawai ya ji bai yarda da hujjar yin kukansa ba.
"Inno magana ta gaskiya ba a kyauta wa Yaya Inu ba, ina laifin ma ki sa a ɗebi kaji amma a ce rago guda ai kuma ya yi muku yawa."
Baba Ibrahim ya furta, don ya san fiye da jinya ma ɗan'uwan nasa yana iya yi saboda soyayyarsa da abin duniya.
"Mu ajiye wannan zancen a gefe Iro, yanzu me yake tafe da kai."
Baba Ibrahim ya yi jim sannan ya ce.
"AlhamduLillah! Haƙiƙa ina godiya ga Allah (S W.A) da Ya sa haɗuwarmu da kai Malam da zamo mana alheri. Tun da aka ce harka ta auratayya ta shiga tsakani, to kuwa ta wuce komai. Amma wani hanzari gare ni ba gudu ba Inno da kuma Malam!"
Baba Ibrahim ya ɗago ya ɗan dube su sannan ya cigaba da cewa.
"Dama maganar gwajin jinin da na yi rannan ita ce na zo zan sake maimaitawa. Don Allah ina son ka fahimce ni Malam, ba ina son a yi wannan gwajin don wata manufa ta ko saboda ba mu yarda da kai ba ne. A'a ina son a yi muku wannan gwajin ne saboda a tantance lafiyarka da ita Inno, saboda kada a cutar da ɗaya daga cikinku ko kuma gudun samun wata matsalar da ba ma fata a nan gaba."
Tun da Baba Ibrahim ya fara magana Mai Yasin ya haɗe rai, Inno ta dube shi sheƙeƙe ta ce.
"Kai Iro fita daga idona na rufe, yadda yahudanci ya ratsa ka so kake ni ma ka ribace ni ko? Wallahi tun ranar da na ji kana yi wa Inusa faɗa, a kan yawan haihuwa na fara zargin ka karɓo kwangilar yahudawa. Kai Iro ka ji tsoron Allah, yanzu lokacin da na auri ubanka akwai wani tsirfar gwajin jini kafin aure ne? Ni za ka haramtawa sunnar Annabi ina zaune ƙalau?"
Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin damuwa, don dama ya san za a rina an saci zanin mahaukaciya. Shi kuwa Malam zuciyarsa fes, duk da ya san lafiyarsa ƙalau amma shi kansa bai yarda da sabuwar al'adar da ta shigo ta gwajin jini kafin aure ba.
"Wallahi Inno ba ni da wata alaƙa da Yahudawa kamar yadda kuke zargi, shi wannan gwajin jinin yana bayyana rukunin jinin da kika ɗauke da shi. Gwari-gwari bari na yi miki bayani, nau'in rukunin lafiyar jini na gado shi ake kira da Genotype. To kamar yadda muka sani Inno kowanne ɗan'adanm da Allah Ya hallita, yana tare da wasu ƙwayoyin halitta da suke gudana a jikinsa, kuma waɗannan ƙwayoyin halittar gadonsu ake yi. Misali idan iyaye suna da nau'in jini mai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 24