Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya ajiye, sororo ta yi ta fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan ta ce. "Daddyn yara da gaske kune? Ina ne nan?" Kafin Daddy ya ba ta amsa tuni Dr Nura ya yi wata irin sufa irin ta jaruman indiya ya fice daga ɗakin, glass da takalmansa kusan lokaci ɗaya suka yi tsalle sama suka zube a tsakar ɗakin sai dai hakan bai sa ya tsaya ko waige ba ballana ya ɗebi abin sa. Kan gado Daddy ya zaunar da ita yana yi mata sannu, sai ji suka yi ta fashe da kuka tana faɗin. "Daddyn yara ni dai daga nan ka wuce Kura da ni, har abada ba zan sake kwana a gidan can ba." Kamar ƙaramar yarinya Daddy ya shiga lallashinta sai da ta yi shiru sannan ya tambaye ta ainihin abin da ya faru. Tiryan-tiryan Mami ta sanar da shi abin da ta ji da kuma shigowar ƙadangaren, don ita ko shigar su Jafar ba ta sani ba saboda ta yi suma ya fi bakwai a cikin banɗakin. A yanzu shi kansa Daddy ya fara yarda da cewar gidan ba su kaɗai ba ne, saboda ya sake kwantar mata da hankali ya ce ya amince za su koma can da zama. Uwani na rakuɓe a gefe ta yi zuru tana ƙarewa fuskar Mami kallo, tana mamakin yadda Mami ta zabge ta zuƙe a wuni guda, suna haɗa ido ta doko mata harara ba shiri Uwani ta janye idonta gefe. Daddy da kansa ya koma kiran likitan da zai sake duba Mami duk da ya lura ciwon ba na asibiti ba ne, da ƙyar ya samu Dr Samira ta je ta duba Mami ta saka mata ƙarin ruwa da allurai bayan wani lokaci aka sallame ta. Su Shukra ko kaɗan ba su so komawa Kura ba don dai babu yadda suka iya ne, ita kuwa Uwani murna fal ciki. Daddy ne ya kwashe su suka ɗebo kayan sakawarsu. Mami kuwa fir ta ƙi yarda ta shiga gidan sai a mota suka bar ta. Su Shukra sun ɗauki hanyar Kura babu jimawa Salim ya kira ta a kan zai je ya ɗauki motarsa, bai dai gaya mata ba amma a cikin ransa ya ƙissima ba zai sake zuwa gidansu ba har zuwa lokacin da za a ɗaura musu aure. Adaidaita sahu ne ya sauke shi a ƙofar gidan Daddy, gaban Salim ne ya fara faɗuwa a hankali ya yi ta maza ya ƙarasa jikin gate ɗin ya fara ƙwanƙwasawa. Daga cikin gidan Lado ya furta. "Waye nan?" "Lado ni ne." Zuro kai Lado ya yi yana ganin Salim ya washe baki ya ce, "Allah Ya taimake ka, yau kaine da rana tsaka." Salim ya miƙa masa mukullin motarsa ya ce. "Shiga ka tuƙo motata ka fito mini da ita." Sororo Lado ya yi ya furta. "Ranka ya daɗe ni da ko mashin ban iya tuƙawa ba, ina ni ina tuƙa mota?" "Lado amma gidan nan ba ku kaɗai ba ne a ciki, ka na gani dai rannan aka so tafiya da mu a bokiti ban da ƙarfin addu'armu da ta iyaye da tuni wani zancen ake ba wannan ba." Lado ya yi jim sannan ya ce. "Ranka shi daɗe naka ai mai sauƙi ne." To yau dai in faɗa maka tik da ka sani haka ƙadangare ya tarfa Hajiya tumɓur tana wanka. Kai yanzu haka ma suna can hanyar Kura don gabaɗaya Hajiya ta rikice, ban da sha'anin iska ina ka taɓa jin ƙadangare ya auri mutum? Wai ƙadangare ne fa yake ce mata amarci zai sha da ita, ina ka taɓa ganin ƙadangare na magana?To Kai kuwa ma a shekarun Hajiya ban da neman cika wa da imani me take nema a wurin namiji ballantana ƙadangare? To ɗazun nan sun zo ɗiban kaya za su wuce Kura Uwani ta kwashe komai ta faɗa mini." Take cikin Salim ya sake kaɗawa, ganin ya ɗan fara ja da baya Lado ya ce. "Ni ma fa Baffa nake jira ya zo a yi wacce za a yi, idan har ƙadangare zai auri Hajiya ni waye da ƙangaruwa ba za ta aure ni ba. Haka kawai ina zaune ta murƙushe ni cikin dare babu mai ceton rai." Salim ya zaro ido ciki a tsure ya ci gaba da ja baya. Lado ganin haka ya sa ya ce. "Ranka shi daɗe ina za ka je ne? Ka shigo ka ɗauki motarka mana." Salim ya zabura a razane ya furta. "Allah Ya tsare ni wallahi, zan aiko a ɗaukar mini ita daga baya don ita kanta motar kafin na fara hawa sai an yi mata sauka biyar." Daga haka Salim ya juya ko sallama bai yi wa Lado ba yana zuba sauri. Da zuwan su Mami Kura ba a ɗauki lokaci ba, labarin abin da ya faru da ita ya watsu cikin gidan gabaɗaya. Facalolinta sai zuwa suke duba ta, wanda yawanci zuwan da suke yi da biyu suke yi. Domin masu yi mata dariya a bayan fage sun fi yawa saboda irin habaicin da ta dinga yi musu a lokacin da za su tare. Sai daga baya Dada ta shiga a lokacin yawancin mutane sun watse daga Daddy sai su Jafar, Uwani kuwa dama tun da ta shiga gidan ta yi sashen Dada daga nan ta wuce wurin turken awakinta. Sannu a hankali jikin Mami yake ƙara samun sauƙi, ganin yadda Mami ta yi laushi ya sa Uwani ta yi tsammanin ko Mami sauya halinta ne. A haka sai da suka shafe kusan kwana goma a cikin gidan, kuma a wannan kwanakin kullin sai Daddy ya sa an yi saukar karatun Alƙur'ani. Wannan saken da Uwani ta samu ya sa hankalinta ya kwanta, ta manta da matsalar Mami gabaɗaya. Don tun da suka koma Kura sau biyu ta shiga duba Mami, kuma ba wata kyakkyawar fuska take samu ba. Su Mami ba su suka koma gidansu ba sai bai fi saura sati guda bikin Shukra ba, da ƙyar Mami ta yarda ta koma kuma kafin ta koma sai da suka yi musayar ɗaki da Daddy, ita ta koma ɗakin Daddy shi ya koma ɗakinta. A kwalemar fitar da kayan ne aka fitar da Jangwalagwadan da ya shiga ɗakinta, don shi kansa ya galabaita. A lokacin da za su tafi ne Uwani ta saka kuka don cewa ta yi fir ba za ta koma ba, sai da Dada ta lallaɓa ita da Daddy ta amince amma sai cewa ta yi sai dai idan da awakinta za ta koma. Ba musu Daddy ya amince ya ce zai yanki wani wuri a cikin farfajiyar gidan a yi wa awakinta wuri, amma sai bayan bikin su Shukra. Cikin farinciki Uwani ta bi Jafar suka wuce duk da shi ma ba wata fuska take samu a wurinsa ba, amma ba ya zagin ta ko cin zarafin ta. Shirye-shirye sun fara kankama a wurin su Mami da wurin iyayen Salim, da yake Mami na zirga-zirga sai tsangwama da takurar da take yi wa Uwani ta yi sauƙi. Haka kuma Uwani ta fara gogewa da aikin da suke yi da Inna, don wani lokacin ma idan Inna ta gaya mata yadda za ta sarrafa abu ita take yi. Tun ana gobe kamun bikin Shukra hankalin Mami yake a tashe sakamakon wayar da suka yi da mahaifiyar Safna, a kan cewar za su zo ranar Juma'a da safe su tafi ranar Lahadi bayan ɗaurin aure. Sakamakon biyo jirgin da za su yi daga Lagos zuwa Kano. Tun da suka gama wayar gumi yake keto wa Mami. Ganin ta rasa mafita ya sa ta kira Shukra ɗaki. "Shukra ina tsoron asirinmu ya tonu, ina gudun duk plan ɗin da na shirya ya wargatse. Kin san dai matuƙar Safna da mahaifiyarta suka zo gidan ko yaya ne za su iya fuskantar Jafar na da aure, alhalin ni kuma ban sanar da kowa ba bayan Hajiya Falmata." Shiru Shukra ta yi sannan ta ce. "Hanya ɗaya ce, mu nemo abin da zai sa Yaya ya sake ta kawai." "Ta wace hanya kenan?" Shukra ta zuba tagumi tana nazari, da sauri ta dafa Mami ta ce. "Na samo mafita, kin san me za a yi Mami?" Mami ta girgiza kai da sauri. "Sata kawai za mu laƙa mata, ba kin ce Daddy ya ba ki ajiyar wasu kuɗi masu yawa ba? To da su za mu yi amfani." Shukra ta yi ƙasa da murya tana tsara wa Mami yadda za su yi, lokaci ɗaya suka saki dariyar samun mafita. Suna gama tattaunawa Mami ta ɗebo damin kuɗin ta damƙa wa Shukra, Shukra ta ɓoye su a cikin jakarta kai tsaye ta nufi sashen Uwani ita da ƙawarta Fatima. Kuma ko Fatima ba ta san da plan ɗin su Mami ba. Tun da Uwani ta tare sau ɗaya Shukra ta taɓa shiga sai a wannan ranar ta yi na biyu. Shiru ta ji falon babu kowa, sallama ta rangaɗa daga cikin ɗaki ta ji Uwani ta amsa. Ita ma Uwani dawowarta kenan daga sashen Mami don tun da Dada ta zo kusan wuni guda a cen take yi, idan ta dawo ɓangarenta sai dai ko wani uzurin ne ya dawo da ita. Uwani na fitowa Shukra ta ɗan saki fuska tana murmushi ta ce, "Ki je Mami tana kiranki. Sannan kuma ƙawata Fatima za ta yi Sallar Walha, sashenmu hayaniya ta yi yawa shi ya sa na ce ta zo nan." Uwani sakato ta yi tana mamakin yau rana ɗaya da har Shukra ta sakar mata fuska, a sanyaye ta amsa mata sannan ta wuce kiran da aka ce Mami tana yi mata. Uwani na fita Shukra ta faɗa ɗakin Uwani bayan da Fatima ta fita yin alwala, ta janyo drowar madubin ta saka kuɗin a ciki ta mayar ta rufe. Ba su wani jima sosai ba suka fice daga ɗakin bayan Fatima ta idar da Sallah, a ɓangaren Shukra dama kuma buƙatar maje Hajji Sallah tun da buƙatarta ta biya ba ta ga amfanin zaman nasu ba. Uwani na zuwa ta samu Mami a falo ta tsugunna har ƙasa, a lokacin Mami zaune take da matan Baba Mustafa sai ƙawarta Hajiya Falmata. "Uwani ku je ke da Auta ki taimaka mata ku ciro mini wayata ta faɗa bayan gado." Babu musu Uwani ta yi wa Auta magana suka shiga ɗakin Mami, sun sha wahala sosai kafin su samu damar ɗauko wayar tun da can ƙarshen gado ta faɗa. Abu ɗaya ne ya tsaye wa Uwani a rai, a iya sanin ta tun ranar da ta zo gidan Mami ba ta taɓa saka ta aiki tare da Auta ba. Amma sai ta sa a ranta ko don ganin mutane ne ya sa Mami ta yi hakan, don kar a ce har yanzu ba ta ƙaunarta. Wurin sallar Azahar bayan Mami ta yi sallah ta fito falo ta fasa kukan an sace mata maƙudan kuɗin da Daddy ya ba ta ajiya har kimanin raina miliyan biyu da rabi, nan da nan hankulan mazauna gidan ya tashi. Dada na jin haka ta fara sababi rai a ɓace. "A gaskiya ni kam idan aka kwashe kuɗin nan an cuci Mamman, saboda Allah a tara mutane domin harkar arziƙi su ɓige da harkar tsiya? Shi dai ɓarawo bai ji daɗin halinsa ba, ba don sai Hajji zan je Saudiyya ba da babu abin da zai hana na kai ƙarar ɓarawon nan wurin Ubangiji a ɗakin Allah ba." Haka dai kowa da abin da ya dinga faɗa, daga ƙarshe aka ce su waye suka shiga ɗakin Mami a ranar su za a bincika, nan take aka bada shedar Uwani ce da Auta suka ɗauko waya. Kiransu aka yi aka tambaye su kowacce ta ce ba ta ga kuɗi ba, Mami ta bada shawarar a duba ɗakunan kowaccensu, haka aka kasu gida biyu wasu suka yi ɗakin Auta wasu suka wuce ɗakin Uwani. Falonta aka fara dubawa har da ƙasan kujeru, sannan suka wuce ɗakinta, masu duba drower saka kaya na yi, wasu kuma har da leƙa ƙarƙashin gado suke. Kwatsam ana duba drower madubi sai ga kuɗi, nan take mutane suka ɗauki salati. Aka wuce wurin Mami da kuɗi, saboda tashin hankali Uwani jikinta har karkarwa yake yi. Duk yadda Uwani ta so fitar da kanta abin sai ya gagara, ta yi kuka ta yi rantse-rantse babu wanda ya yarda da ita. Hatta Dada a wannan karon ba ta yarda da ita ba, Uwani ta rarrafa gaban Dada tana kuka cikin takaici Dada ta wanke ta da mari sannan ta hankaɗa ta gefe. Daddy ne kaɗai da ya zo ya lallashi ta, a ransa yana wasu-wasin wannan abin da ya faru. Lokacin da Jafar ya dawo ya ji labari ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, nan take kuma Mami ta birkice a kan sai Jafar ya saki Uwani a cewarta ba za ta zauna a ɓata mata tarbiyyar yara ba. Shi kuma Daddy ya sake jaddada wa Jafar umarninsa na ko bayan ransa bai amince ya rabu da Uwani ba. Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗe wa Uwani don haka ta koma sashenta, ta faɗa kan gado ban da rusar kuka babu abin da take yi. Lokacin da Jafar ya shiga ya same ta kallon tsana ya wurga mata sannan ya ce. "Wallahi ni dai an gama cutata, a ce wai matata ta rasa wa za ta yi wa sata sai mahaifina, me aka rage ki da shi ci ko sha? Ƙanƙanuwar yarinya da ke ko a ina kika san kuɗi da har za ki sa hannu ki kwashe miliyan biyu da rabi. Ni kam na yi dana-sanin aurenki, ni dai aurenki wallahi bai amfane ni da komai ba sai tsiya. Ya zame mini dole na yi gaggauwar auren Safna, don ba zan zauna ɓacin rai da takaicinki ya kashe ni ba. Shashasha ɓarauniyar banza da wofi." Jafar ya yi tsaki ya fice daga ɗakin. Uwani ta ci kuka kamar babu gobe, tana nan ɗaki Auta ta je ta same ta. "Uwani Allah Ya sani har yanzu ba na jin ke kika ɗauki kuɗin nan, tare fa muka yi komai muka gama." Rai a ɓace Uwani ta ce. "Auta fice mini a ɗaki kada na sauke fushina a kanki." "Don Allah ki saurare ni kada ki yi mana jama'u..." Cikin tsawa Uwani ta katse ta. "Ki fice mini a ɗaki na ce." Auta ta tsorata sosai da yadda ta ga Uwani ta birkice lokaci ɗaya, bayan fitar Auta Uwani ta fara nazarin shigowar Shukra da kiran da Mami ta yi mata. Murmushi ta saki ta share hawayenta a fili ta furta. "Wallahi wannan ƙwallar da na zubar ba za ta tafi a banza ba. Ni Uwani za ku laƙa wa sharri, ai ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka." Daga haka Uwani ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta, ta koma can sashen su Mami. Yadda mutane ke bin ta da kallo ita ma Uwani sai ta murje idonta ta fara bin su da kallo, hatta Dada fushi take yi da ita don haka ita ma ta yi kamar ba ta san da Dada a wurin ba. Duk in da Uwani ta gifta sai dai ka ji ƙus-ƙus na tashi. Auta ta nema ta ba ta haƙurin abin da ta yi mata, ita ma dama Auta ba ta ga laifin Uwanin ba don idan ita ce ma za ta yi fiye da haka. A cikin dabara Uwani ta tambayi Auta Event ɗin da za a yi kamu, Auta ta nuna mata ai sai su tafi tare tun da ba ta san wurin ba. Yamma liƙi jama'ar gidan ana ta hada-hadar tafiya wurin kamu, Uwani ma atamfarta ta saka da mayafi sai dai tun rana Auta ta hana ta yin wannan ɗige-ɗigen kwalliyar. Ita ta biya musu kuɗin make up aka yi muku kwalliya sai ga Uwani ta fito shar kamar ba ita, lokacin da Uwani ta saka ƙafa a cikin hall ɗin ne ta saki murmushin ƙeta da mugunta. Ta zura hannu cikin aljihun doguwar rigarta ta ji fakitin sabuwar rezar da ta saya tana ciki a fili ta furta. "Uwani ce fa 'yar ƙashin gwiwa, ai yanzu za mu fara wasan da ku tun da haka kuka zaɓa." AlhamduLillah a nan free pages na wannan labarin ya ƙare🫠 idan kina buƙatar ci gaba za ki turo 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar biya ta wannan lamber 07062062624 Sai mun haɗe a shafin gobe idan Allah Ya kai mu domin mu ji tsiyar da Uwani za ta shuka, Fakitin Reza a cikin Hall ɗin kamu na san akwai ƙura.😂 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 24 of 24