Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Da gudu Uwani ta bi bayan Shukra tana gurnani tana zabga mata igiyar a baya har Shukra ta fara kama ƙafar bene Uwani ba ta daina dukanta ba, tana hawa sai ga Shukra na rarrafe tana kuka saboda tashin hankali. Sai da ta ga Shukra ta shige sannan Uwani ta yi saurin ɗebe bokitan ta mayar da su wurin da suke, ta je ta ɗaga table ɗin ta mayar da ruwan jarkokin kai sannan ta koma ta kunna ƙwan fitilar harabar wurin ta wuce sashenta. A lokacin da ta shiga sashenta shiru babu motsin Jafar, ta zube a kan kujera kanta na matsanancin ciwo kamar zai tsage gida biyu. Uwar ɗakinta ta wuce don ta sauya kayan jikinta saboda rawar ɗarin da take yi, ɗrower kayanta ta buɗe tana shirin miƙa hannu ta yi ido biyu da Jafar tsugunne a cikin. Uwani ta basar kaman ba ta san abin da ya faru ba ta ce, "Kai kuma Ya Jafar mene ne haka?" Jafar ya fara wuri-wuri sannan ya ce. "Wai Uwani ke ce kika zama biyu ko ya aka yi?" Jafar ya wurga mata tambaya. "Wai me ka mayar da ni ne ya Jafar? Ni fa yanzu na gama yi wa saurayin Shukra wankin mota bayan na gama yi wa Mami wanki..." Cikin sauri ya katse ta. "Wankin me? Ke kika wanke wa Salim mota? To su waye na gani da bokiti a kansu suna ihu?" Uwani ta wara hannu ta ce. "Ni kam ban sani ba, ƙila dai mutanen gidan ne suke son buɗe maka ido." Jafar ya yi fakare yana nazari, abu ɗaya ne ya fi tsaye masa a rai wai Uwani ce ta wanke wa Salim mota. A fili ta ji ya furta, "Dole sai na ɗauki mataki a kanta." Uwani ta yi saurin tambayarsa. "Wace ce?" Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya furta. "Babu komai." Saboda tsabar gajiya Uwani na sauya kaya ta ɗauro alwalar Isha'i ta gabatar da sallah, a nan kan dadduma bacci ya yi awon gaba da ita. A yadda ya ga tana sauke numfashi sama-sama ba ƙaramin tausayi ta ba shi ba, ya ƙarasa ya cire mata hijabin ya ji jikinta ya ɗauki zafi zau! Cikin jakarsa ya duba ya ɗauko Paracetamol, ya jima yana tashinta sannan ta tashi ya ba ta magani. Duk yadda ya yi da ta tashi ta ci abinci ƙi ya yi, ya rabu da ita ya haye gado ya kwanta. Shukra da rarrafe ta ƙarasa falon Mami, babu ɗankwali ballantana mayafi ko takalmi, a razane Mami ta fara tambayar Shukra. "Ke Shukra lafiyarki kuwa?" "Mami ki ɓoye ni bokiti ne, wallahi bokiti ne ya danne mu ni da Salim." Da mamaki Mami ta ce, "Kamar ya bokiti ne Shukra? Shi bokiti mutum ne da zai iya motsi har ya danne ku. Wai ma ina ɗankwalinki?" Shukra fuska da ta gama jagulewa da makeup da hawaye ta zayyanewa Mami duk abin da ya faru, Cikin damuwa Mami ta ce. "Ni fa wallahi ina zargin yarinyar nan tana da Aljanu, mu dai tun da muka tare babu wani abin tashin hankali da muka taɓa gani. Amma tun ranar da yarinyar nan ta zo gidan nan masifar yau daban ta gobe daban, yanzu bala'in har ya kai kina hira ke da Salim ana razana ku? Gaskiya dole a san abin yi." Daga haka Mami ta shiga lallashin Shukra, da ƙyar a daren ranar Shukra ta yarda ta kwana a ɗakinsu. Da yake Daddy ba ya gari ya sa asubar fari Shukra ta koma ɗakin Mami bayan ta yi sallar asuba ta koma ta kwanta. Washgari Tun bayan sallar asuba Uwani da Jafar har sun koma bacci, suka ji bugun ƙofa. Jafar ne ya je ya buɗe da mamakin mai buga musu ƙofa da farar safiya. Karo ya kusa yi da Mami a ɗan duburburce ya ce. "Mami ke ce tun yanzu?" Mami ta ƙare masa kallo ta ce, "Eh ni ce, ina Uwani take?" Jafar ya ɗan sosa kai ya ce. "Tana ciki bacci take yi." "Ciki ina? Uwar ɗaki?" Jafar ya gyaɗa kai. Cikin sauri Mami ta ce, "To kai kuma a ina ka kwanta?" A ɗan kunyace Jafar ya ce, "Ni ma a ciki na kwanta..." "Laha'ilaha'illallahu Jafar tun ba a je ko ina ba?" Salatin Mami ya katse shi. A ɗan duburburce ya ce. "Am ai ita a ƙasa take kwana ni nake kwana a kan gado." A fili Mami ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi ta wuce cikin ɗakin. Yadda Jafar ya faɗa mata haka abin yake, bacci Uwani take sosai a ƙasa saboda gajiya. Mami ta ɗauki ruwan jarkar da ke kan mudubinta ta sheƙa mata, a zabure ta tashi tana waige Mami ta taɓe baki ta ce. "Ki zo ki wuce kitchen za ki taya Inna haɗa breakfast, kin saki baki kina bacci ai duk gidan nan babu bawanki da zai dafa miki ki dinga ci." Jafar kamar ya yi magana sai dai kuma ya yi shiru, tun da yake bai taɓa samun saɓanin da mahaifiyarsa da har za ta mare shi ba, don haka ya kawar da kai har Uwani da Mami suka fice daga ɗakin. Suna tafe Mami ban da masifa babu abin da take mata, kai tsaye kitchen suka wuce. A lokacin Inna har ta fara haɗa kayan breakfast, suna shiga Mami ta dubi Inna ta furta. "Inna daga yau Uwani za ta dinga zuwa tana ta ya ki haɗa kayan breakfast." Inna ta washe baki cikin jin daɗi ta ce. "Allah Ya taimaki Hajiya, ina matuƙar godiya. " Uwani da har lokacin bacci bai gama sakinta ba, ta fara murza ido. Ba ta yi aune ba sai jin ranƙwashin Mami ta yi a kanta ta furta. "Kin ga dai ta hanyar da na biyo da ke, wallahi kika kuskura kika bi ta ƙofar ciki daidai da rana ɗaya kika haɗa ni da Dadyn yara sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Cikin damuwa Uwani ta amsa mata, Mami har za ta fita ta juyo ta ce. "Idan kuma kin gama ki same ni a falo." Mami na fita Uwani ta jingina kai da bango, lokaci ɗaya hawaye ya fara ziraro mata. "Yarinya a wannan lokacin kuka ba na ki ba ne, shi wannan aikin da kika ga Hajiya ta kawo ki mu dinga yi gata ne take yi miki. Saboda duk macen da ba ta iya girki ba wallahi ta faɗo a wurin miji, ki ci gaba da haƙuri watarana sai labari." Inna ta yi maganar ƙasa-ƙasa. Kukan da Uwani take yi ya yawaita jin kalaman Inna ya sa ta furta. "Wallahi ni kam na gaji Inna, gara na koma wurin Dada ni ban saba da wannan wahalar ba." Sai da Inna ta ɗan leƙa bakin ƙofa sannan ta sake ƙasa da murya ta ce. "Ita dama rayuwar aure ai takan zo wa bawa da al'amura mabanbanta. Ni na ɗauke ki tamkar jikata duk abin da yake damunki ki dinga samuna a fakaice kina gaya mini, amma kada ki bari kowa ya fahimci haka don gudun mu samu matsala ni da ke." Uwani ta ji daɗin yadda Inna ta amshe ta hannu bibbiyu, don haka ta share hawayenta ta fara taya ta duk abin da ya dace. A cikin aikin da suke yi ne Inna ta fahimci sam Uwani ba ta iya wani girki ba, hatta aikin ma wani abin sai ta koya mata. Sai kusan tara saura sannan suka kammala komai, don har wanke-wanke babu abin da ba su gama ba. Uwani ce ta bi Inna dianing tana ganin yadda take yin komai, lokaci ɗaya Uwani ta nemi duk ƙuncin da take ciki ta rasa. Suna gab da barin kitchen ɗin ne Mami ta dawo tana bin Uwani da harara, ta dubi Inna ta ce. "Idan kun ƙarasa aikin ki ɗebo mata gero kwano ɗaya ta surfa, ta niƙe mini shi yau furar daka nake sha'awa." A sanyaye Inna ta amsa, Mami ta wuce ta buɗe tukwanen wurin, ganin abincin da Inna ta rage kusan na mutum bibbiyu ne ya sa Mami ta furta. "An kai wa Lado abincinsa ne?" Da sauri Inna ta amsa. Mami ta sake haɗe fuska ta ce. "Wannan abincin ai ya yi miki yawa Inna zuba mini a wancan plate ɗin." "Dama ni da Uwani na rage mana..." Mami ta yi saurin katse Inna. "Uwani idan ta gama za mu rage mata abincinta a wurinmu." Inna babu yadda ta iya haka ta ɗauki plate ta zuzzuba kamar yadda Mami ta buƙata, kusan shekararsu Takwas tana yi wa Mami aiki ba ta taɓa ganin ta yi mata iyaka da abinci ba sai yau, a ranta ta jinjina ƙarfin ƙiyayyar da take yi wa Uwani. Uwani tana kuka haka ta karɓi geron ta nufi harabar gidan tana dakawa, tun ba a je ko ina ba hannunta ya fara kanta ga turmin dakan ba shi da girman kirki don a surfe ma sai da ta raba shi gida huɗu sannan ta gama dake shi. Tun Uwani na cikin inuwa har rana ta same ta don sha biyun rana a lokacin ta kusa, tana nan tana daka su Shukra suka fito cikin shirinsu gwanin birgewa. Auta ce ta ƙarasa wurinta da sauri ta ce. "Uwani me kike yi haka ne?" Uwani ta share hawayenta. Tausayin Uwani ya kama Auta, a sanyaye ta ce. "Ki yi haƙuri Uwani In shaa Allah Mami za ta gane abin da take ba ta kyautawa, unguwa za mu yanzu wallahi da na taya ki." Uwani ta gyaɗa mata kai sannan ta wuce wurin su Shukra da har sun fita bakin gate. Fitar su Shukra ba jimawa ita ma Inna ta zo ta yi wa Uwani sallamar za ta je kasuwar Garu, Mami ta aike ta yin cefane. Ita kanta Inna ta so taya Uwani sai dai tana tsoron kar ta je ta yi abin da za ta bar aikinta, don da kuɗin albashinta take samun na rufin asiri. Lokacin da Uwani ta gama ta gama galabaita, ga yunwa ga kuma gajiya. Can kitchen ta je ta ajiye wa Mami garin geron saboda ba ta san yadda za ta sarrafa shi ba, ta fito za ta shiga ta ƙofar falo ta hangi wani tafkeken jangwalagwada. Har a fili sai da Uwani ta saki murmushi, ta ɗauko tsumma a kitchen da sauri ta ƙarasa wurinsa ta yi A'uzubillahi sannan ta damƙe shi da hannunta, a wannan karon ta ci alwashin yadda Mami ta azabtar da ita to ita ma sai ta rama. Har ta gama tsara komai koda ta kwaɓe mata tana gamawa Kura za ta yi wurin Dada, kuma ko kashe ta za a yi ba za ta dawo gidan ba. Cikin sanɗa take tafiya har ta shiga falon babu motsin kowa daga can ɗakin Mami ta fara jiyo muryarta sama-sama da alama waya take yi. Ta matsa a hankali da niyyar ta buɗe ƙofar ta zura mata ƙadangaren ta ji Mami na faɗin. "Haba Hajiya Karima kin gan ni fa na tuɓe kaya yanzu haka wanka zan shiga, don Allah ku jira ni. Kin san yadda nake bala'in son haɗuwa da matar DC kuwa? Kin san fa duk in da harkar manya take ba ma sanya da ita." Uwani ta saki murmushi da ta tuna tsiyar da za ta ƙulla wa Mami. A kan kunnen ta Mami ta gama wayar ta faɗa banɗaki, sai da ta tabbatar da wankan Mami ya fara nisa sannan ta buɗe ƙofar ɗakin a hankali ta shiga. Ƙofar banɗakin ta nufa sai ta fara murɗa ƙofar da sauri-sauri, daga ciki Mami na saɓa sabulu a fuska ta ji ana murɗa ƙofar. Mamaki ne ya kamata don ta san su Shukra ba sa nan, kuma ko suna nan ba za su buɗe mata banɗaki tana ciki ba. "Waye a nan?"Mami ta tambaya a hassale. Uwani ta kausashe murya ta ce, "Sarki ne ya zo da kansa ba aike ba." Da mamaki Mami ta furta. "Sarki wane iri? Kai waye da har za ka tsallake ko ina ka shigo ɗakin matar aure, kuma har ka nemi buɗe ni a banɗaki." "Sarautar ce haka! Kuma na aure ki daga yau, tun da na samu sukunin mai gidanki ba ya nan. Dama tun ranar da aka yi maganar auren ɗanki Jafar ni ma na kai kuɗin aurenki, yanzu haka kuma na biyo ki ne domin na ɓarje amarci." Uwani ta ƙarasa maganar dariya na son ƙwace mata. A hargitse Mami ta ce. "Kai malam wai waye kai ne ma? Ba ka da hankali za ka ce ka na son matar aure?" Uwani ta sake kausashe murya ta ce. "Ni dai babban burina ki ba ni haɗin kai domin ni matashin saurayi ne dal, soyayya ce kawai ta sa na tsaya a kanki. Amma kada ki yi mamakin kasancewa ta wata halitar da ba irin taki ba." Uwani na gama faɗar haka ta buɗe ƙofar a hankali ta wurgar wa Mami Jangwalagwadan sannan ta janyo ƙofar da ƙarfi ta rufe, da yake da key a jikin ƙofar nan take Uwani ta murza key ɗin ta cire shi ta ajiye a gefen gadon Mami. Lokacin da Mami ta ji abu ya sauka a kafaɗarta da sauri ta hau kiciniyar wanke kumfar fuskarta. Hannunta ta kai ta shafo kafaɗarta bayan ta wanke fuskarta, wani irin ƙadabarbar ta ji take jikinta ya hau karkarwa. Ta yi ta maza ta yi wurgi da shi, sai a lokacin idonta ya sauka akan tafkeken ƙadangaren. Da yake shi ma ya galabaita nan take suka fara 'yar tsere da Mami a banɗaki, duk yadda Mami ta so buɗe ƙofar sai ta gagara. Cikin Kuka Mami ta ce. "Wayyo Allah Lado, Jafar kana ina ka kawo mini ɗauki." Uwani ta gimtse dariyarta, ta sake matsa wa jikin ƙofar ta ce. "A yanzu babu mai iya taimakonki domin amarci na zo ci. Kuma daga yanzu ni fa zan dinga rikiɗa har zuwa surar mutane ina kawo miki ziyara." Uwani na gama faɗar haka ta sulale ta fice daga ɗakin, cikin sauri ta zagaya ta wuce sashenta. Jafar ta gani ya yi ɗaiɗai a falo yana bacci, da alama kallo yake yi bacci ya yi awon gaba da shi don ga remote nan a gefensa. A hankali ta wuce cikin ɗakinta ta faɗa kan gado tana sauke ajiyar zuciya, ƙugin da cikinta ke yi ne ya sake ankarar da ita yunwar da ke cin ta. Kitchen ta faɗa ta fara duba tukwane, ta ci karo da guntuwar Indomie da Jafar ya ci ya rage. Tukunyar ta ɗauko ya zuba shayi ta koma falo ta zauna ta ci, sannan ta buɗe bokitin dubulan ɗin ta ta ɗebo alkaki da dubulan na gararta ta baje a ƙasa ta ci gaba da loda wa cikinta. Tana cikin ci suka ji bugun ƙofa kamar za a ɓalle ta. "Ranka ya daɗe! Ranka ya daɗe akwai abin da yake faruwa a sashen Hajiya." Jafar shi da Uwani kusan lokaci ɗaya suka miƙe a zabure, da sauri Jafar ya buɗe ƙofar ya ga Lado da Baba tsoho, a ɗimauce ya ce. "Lafiya Lado?" "Ranka ya daɗe bugun ƙofa nake ji a sashen hajiya kuma idan aka buga bayan wani lokaci sai na ji shiru, kuma sama-sama nake jiyo muryar Hajiya kamar tana kuka." Jafar tun bai gama jin kalaman Lado ba shi da Uwani suka zuba a guje suka yi sashe ta, ganin haka ya sa Lado da Baba tsoho suka rufa musu baya. Jafar na zuwa ɗakin Mami ya nufa, abin mamakin komai tsaf yake babu wata hayaniyar tashin hankali. Wani rin numfarfashi suka ji a cikin banɗaki, da sauri Jafar ya dinga buga ƙofar yana kiran sunanta. Bugun da Jafar yake yi ne ya sake farfaɗo da Mami daga suman da ta yi, wanda ta yi suma a cikin banɗakin babu adadi. "Jafar! Wayyo Jafar ka shigo ka taimaka mini, wallahi ƙadangare ne zai haike mini." Mami ta yi maganar a galabaice don saboda wahalar da ta sha ko motsin kirki ba ta yi. Da ƙarfi Jafar ya dinga buga ƙofar amma a ƙame take ƙyam ta ƙi buɗuwa, "Ranka shi daɗe wannan ba shi ne mabuɗin na?" Lado ya ɗago key ɗin da ke kan gadon Mami. Da sauri Jafar ya karɓa ya buɗe yana buɗewa ƙadangaren ya yo bakin ƙofar a guje, ganin haka ya sa daga Lado har Jafar suka ɗiba a guje. Sai da suka ga ya shige ƙarƙashin gado sannan suka fara leƙowa, Mami da rarrafe da jan ciki ta fara tahowa Baba tsoho ya tunkari ƙofar banɗakin da niyyar taimaka mata, yana leƙawa ya hangi Mami tumɓur da sauri ya juya da baya yana faɗin. "Kai a'uzubillahi wannan lamari da muni yake." Baba tsoho ya nufi bakin ƙofa su Jafar na ganin yadda ya dawo jiki a sanyaye Lado ya je zai shiga da sauri Baba tsoho ya girgiza kai ya furta. "Ummm-ummm ku dawo Lado abin babu kyawun gani." Lado na zuwa ya ci karo da Mami na jan ciki, Mami da take a yunwace da neman taimako ta fara jan ƙafar wandon Lado tana faɗin. "Ku fitar da ni daga gidan, idan ba haka ba za su kashe ni." Ganin yanayin da Mami take ciki ya sa Lado ya fisge a guje yana faɗin. "Subhanallahi wannan lamarin ya munana Baba tsoho me ya sa ba ka buɗan aiki ba? Haka kawai zan ƙone idanuna." Jafar ya nufi wurin banɗakin, kamar haɗin baki Lado da Baba tsoho suka yi wata uwar sufa suka dafe kafaɗun Jafar suna faɗin. "Wallahi al'amarin akwai muni Jafar kada ka shiga." A ƙufule Jafar ya fisge ya ce. "Ni da uwata ne za ku yi mini iyaka? Duk halin da take ciki ni ba zan guje ta." Jafar ya fisge da ƙarfi ya tunkari wurin da Mami take. Cikin hukunci Ubangiji gobe ne za mu kammala Free pages ɗinmu, idan kina buƙatar ci gaba za ki biya 500 ta wannan Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar ta wannan lambar 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [23/06/2024, 12:50] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA BIYAR *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 Jafar na shiga da ya ga a halin da Mami take ciki turus ya yi, da sauri ya juya cikin damuwa ya dubi Uwani ya ce. "Maza ki shirya ta za mu wuce asibiti." Uwani da ke gimtse dariyarta ta wuce sumi-sumi kamar sabuwar munafuka ta ƙarasa wurin Mami da ke sharɓe a ƙasa. Baba tsoho shi da Lado dama tuni suka fito harabar gidan, suna nan tsaye Jafar ya fito abin duniya ya dame shi. "Kai Jafaru, wai ya aka yi ƙadangare ya shiga har banɗakin mahaifiyarka? Ko dai ture aka yi mata?" Jiki a sanyaye Jafar ya ce, "Wallahi Baba tsoho ban da masaniya, ka na gani dai kune kuka kira ni ina ɗaki." Daga haka gabaɗaya suka yi jigum-jigum. Abin ka da mai ƙiba Uwani da ta ɗago Mami sai dai ka ji ta sake komawa sharaf, kuma har lokacin idanun Mami a rufe suke. Da ƙyar Uwani ta samu ta ja Mami a ƙasa kamar rago, ta ƙarasa da ita bakin gado tana zaunar da ita a kai ta sake tafiya sharaf, kayan da ta gani a gefe wanda Mami ta ɗauko za ta sa su ta fara dubawa. Rigar maman Mami ta ɗauko ai kuwa Uwani tana ɗaga wa ta faɗi a wurin tana ƙyaƙyata dariya saboda girmanta, sai da ta yi mai isarta sannan ta miƙe ta fara kiciniyar saka wa Mami. Da ƙyar Uwani ta samu ta shirya Mami sannan ta leƙa waje ta kira Jafar, yana zuwa nan take ya kama Mami ita ma Uwani ta kama ta suka fita ita. A kujerar baya suka saka Mami, Jafar ya kunna motarsa suka wuce asibiti. Suna zuwa asibiti da sauri aka karɓi Mami aka shiga da ita, aka fara ba ta agajin gaggawa. Sai da Jafar ya ga Mami ta samu bacci sannan ya samu sukunin kiran Daddy ya sanar da shi halin da ake ciki, a nan take yake sanar da shi yana hanyarsa ta dawowa. Lokacin da Mami ta farka gabaɗaya iyalanta na wurin, Daddy ne ya matsa gaban gadon ya fara yi mata sannu. Da wani irin kallo take bin sa ta yunƙura ta cukumo wuyan rigarsa a zabure tana faɗin. "Wallahi ba zan aure ka ba, ni ina da aure har da 'ya'yana!" Da sauri Daddy ya riƙo ta, Mami ta ɗago kai tana ƙare masa kallo sai gani suka yi Mami ta sake tafiya luuuu a sume. Har rige-rigen fita kiran Likita suke yi, babu jimawa Dr Nura ya shiga cikin shigarsa ta likitoci. Sai da ya gama jin bayaninsu sannan ya ce gabaɗaya su fita, don yana son ba ta kulawa babu buƙatar hayaniya. Daddy ya so zama don ciwon na Mami ba ƙaramin tsoro ya ba shi ba amma Dr ya ce ya fita. Wata allura ya yi wa Mami ba ta fi minti ɗaya ba ta sake farfaɗowa, tana daga kwance ta ga Dr Nura tsaye a kanta cikin fararen kaya ga farin gilas maƙale a idonsa. "Wato wannan karon rikiɗe mini ka yi zuwa wannan surar kenan? Wannan fa idan ba da gaske na yi na ƙwaci kaina ba sai ya illata ni ya cuci iyalina." Duk waɗannan maganganun Mami na yin su a cikin zuciyarta ne, ta dai kafe Dr Nura da kallo ko ƙiftawa ba ta yi. Ta fara motsa baki a hankali tana biya Ayatulkursiyyu. "Sannu Hajiya! Yanzu yaya kike jin jikin na ki?" Dr Nura ya tambaye ta yana gyara tsayuwarsa. A hankali ta yunƙura ta tashi zaune tana ɗan dafe kanta, cikin shammata Mami ta suri dogon ƙarfen nan da ake maƙala ledar ƙarin ruwa a jiki ta shiga zungura masa tana kwaɗa masa. Idan Mami ta karanta Ayatulkursiyyu ta tofa masa sai ta ɗaga ƙarfen ta ba shi ƙwal. Hankali a tashe Dr Nura ya shige can kusurwar ɗakin yana faɗin. "Help! Help! Help!" Mami ta sake zungura masa ƙarfen tana faɗin. "Wato don ubanka har surar Nasara kake rikiɗewa ai wallahi yau ko ni ko kai." Dr Nura ganin neman agajin da yake yi da harshen turanci ba zai kai shi ba, ya sa ya taƙarƙare cikin ihun tashin hankali ya ce. "Wayyo Allah! Jama'a Patient ɗin nan za ta halaka ni." Su Daddy na daga waje suka jiyo ihun Dr Nura, da gudu suka taho za su buɗe ƙofar, sai dai da yake Mami na jingine da ƙofar tana jin alamun za a buɗe ta sake danna ƙofar da ƙarfi tana zungurin Dr. Ganin Mami na niyyar illata shi ya sa ya faɗa ƙarƙashin gadon asibitin, da ƙyar su Daddy suka turo ƙofar suna ganin ta da ƙarfen suka shiga kallon-kallo suma suna ja da baya. Daddy ne ya murɗe hannun Mami ya karɓe ƙarfen

Chapter 23 of 24