'yan shirye-shirye ne
da ta ce tana son yaje su gaisa da Suwaiban nan ma
kaucewa ya rika yi.
Suwaiba irin 'yanmatan nan ne da zasu iya yin
komai a kan da namiji, tunda dama a kasar waje ba
komai ba ne a tare namiji a tsakar titi ma ace ana son
fita da shi balle ita 'yar (Club). Ta sawa ranta tayi ta
koma gun Mama don yanzu dai an kai wata uku da
maganar amma ya ki zuwa a ganinta idan tana kusa
da Mama dole ne a matsa masa. Ta kuwa ci nasara
gun Mama don a kullum sai ta buga masa waya, daga karshe ta ce su shirya suje gun Malaminta, ya kira mata shi gida.
Sun shirya kuwa suka je dama Suwaiba, tana da kudi, don haka da su za ayi amfani don shirin da suka dauka ba na wasa ba ne. Da suka isa gun Boka Jilli, ya tarbe su suka fadi matsalarsu, ya ce ya gani ai a goshin Suwaiba akwai aure tsakaninta da Tahir
ta kwantar da hankalinta. Ya gaya masu abinda zai hada ya kuma basu kullin magani wai ta rika wanka da safe ta țurara da yamma, sun dauki kudi suka ba shi.
Page | 111 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
}
BAKI BIYU [1]
Ai kuwa da alama aikin Boka Jalli ya kama
Tahir, don ba suyi wata ba yaje Gusau, ba su san
Gwaggo ce ta matsa mashi yaje ba har sai da ta cc,
"Idan bai je ba, to kadda ya kara buga mata waya.'
Shi ne fa washegari ya shirya ya tafi.
Duk karambanin da Suwaiba ke yi, na
lankwashe-lankwashe da matse-matse yana kallonta,
miskilancinsa shi ke bata haushi. Tun da ya shigo
gidan in ban da gaisuwa babu abinda ya Каrа се
mata, ita ke kidanta take rawarta, shi dai ido yasa
mata. Kayan da tasa sun matse ta, amma saboda naci
da barikanci tsab take tafiya a cikinsu.
Ta nemi wuri dab da shi ta zauna tana yi masa
zance, to zance mana ita ta zama namijin shi kuma
mace, a ransa haushi da takaici ne cike da zuciyarsa,
ya rasa abinda zai yi da zai ba ta haushi.
Can ya mike tsaye yana tafiya yana magana zan
wuce, idan kin shiga ciki ki ce da Mama na shiga
cikin gari. Hawaye ne ya taru a idonta, ta daure ta
maida su ciki. Tayi saurin bin bayansa, da saurin
gaske ta sha gabansa ta kai hannayenta tayi sarka da
su a kan wuyansa, a shagwabe take magana, haba
Dolly (sunan da ta sa mashi kenan tun suna
Amerika).
Dalili kuwa shi ne saboda rashin duminsa, bai
cika magana ba, sai kayi magana goma shi bai yi
daya ba. To shi ne tun lokacinta ke kiransa Dolly, ya
Page | 112 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
ce yana kallonta cikin idonta me ki ke so? Sonsa ne
ya karu a zuciyarta, ga idonsa sun yi mata kyau,
idonsa wato kwayar idonsa ba baki ba ne (Brown)
nc, duk da fatar jikinsa ba wai farin nan ne tas ba a'ah shi wankan tarwada ne me haske sosai,
hakoransa ma abin kallo ne, don farare ne tas, dasashinsa kuma baki, dama familin baki daya Allah Yayi masu hanci, ko bai kyau zaga gansu dai dan hanci mai kyau.
"Tun yanzu za ka tafi? Komai ba ka ce min ba
fa?" Ya gyara tsayuwarsa ya ce, "Me ki ke son in ce maki, kin je kin yi abinda zai dame ki."
"Bangane ba Dolly, a dalilin me zai dame ni tunda muna son junanmu." t
"Ni na ce ina sonki? Ba ki san na tsani masu irin
halinki ba, bana son irin matan da ake kaiwa Turai
suyi karatu saboda tarbiyarku gurbatacce, ke kin
manta inda muka hadu a gun (Party) abokina kuma yadda aka shirya shi bai da bambanci da (Club Night) am against those taken their femal child abroad, ina son ki fita hanyata ki daina son takurawa
rayuwarmu, daga ni har ke."
Ta kura masa ido, sannan 'yar kwalla da ta
makale dama a cikin idonta ta zubo tayi saurin sauke
hannunta daga jikinsa ta share da hannunta a ransa ta
bashi tausayi, don ya taba (Expencing) din so a
Page | 113 MARUBUCIYA: Sameera Mstapha
さ
7
BAKI BIYU [1]
rayuwarsa rasuwa tayi bata rayu ba, da tuni har ya
manta yayi aure.
Zata wuce ya rike hannunta ya ce kiyi hakuri, ina
so mu hakura da junanmu, Allah ya hada kowa da
rabonsa. A'a ta fada tana ja da baya, a'ah ba zan
hakura ba, ina sonka kuma aure nake son muyi, ka
amince min zamu yi auren da jin dadi..."
"Jin dadi? Ban yi tsammani ba, sai dai in kina
son muyi zaman..." Ta katse shi "Maganganunka ba
suyi min dadi, don Allah ka bari sai da safe ta wucе
ciki tana kuka, shima wucewa yayi yana matukar
takaicin zuwansa, don dai bai amfana komai ba sai
bacin rai, wai yazo ne don ya bata hakuri, don a
gaskiya ko aurenta ya yi ya san zai cuta mata.
Tana shiga cikin gidan ta kwanta kan jikin Mama
tana rusa kuka na ban tausayi, ta ce Mama yau Tahir
ya wulakanta ni, ni mutuwa zan yi idan ban aure shi
ba ya zan yi, ban da amfani."
Lallashinta take yi, a ranta kuwa mamakin
wannan hali na Suwaiba take, sam bata jin nauyin
fada mata kowacce irin magana ce. "Kada ki damu,
inshaa Allahu kamar an yi an gama."
Tunda Tahir ya tafi bai sake ko waya ba, ya yi
kusan wata rabonsa da Gusau, mahaifiyarsa zafi
sosai ta dauka da shi, manzo ta aika har Lagos a kan
a ce masa tana nemansa, amma ba ya nan. Tuni ya
Page | 114 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
koma Abuja da zama tnda mahaifiyarsa tasa shiga
yana da gida dama a can sai ya koma.
Haj. Basira Kaduna taje gun Haj. Hauwa, kacakaca suka yi ita Mama a tunaninta ita ta hana shi,
bata san yadda take fama dashi ba a kan auren
Suwaia. Ana cikin haka kuwa sai ga Tahir ya shigo
gidan, ba wai yasan da zuwan Mama ba ne, shi dai
ya shigo ne kawai su gaisa, itama tun da ya bar
Gusau haka itama ya barta sai dai yana kiranta a
waya. Ai Mama na ganin ya shigo ta soma kunduma
masa zagi ta inda take shiga ba nan take fita ba, har
ta kai da cewa in dai bai zo aka daura auren nan ba,
to sai ya biya ta nonon da yasha, sannan zata tsine
mashi.
Tahir zufa yake zubdawa, wannan wace irin
masifa ce shi mace ne da za a matsa wa har ayi masa
auren dole? Abinda yake fada kenan a
zuciyarsa...Mama ta katse masa tunani da ta ce, "Kа
kara jin abinda zan fada maka, in dai ba ka zo aka daura auren nan ba, to wallahi ka biya ni nonon da
ka sha, sai ka nadawa kanka ko ka koma cikin
mayyar matar da ka maida ta uwar, aure nasa ranar daura shi ba nan da dadewa ba ne nan da kwana bakwai, in ka ga dama ka zo in ka ga dama kada ka
zo a ranar za a daura sai na ganka."
Har ta kai bakin kofar fita ta juyo ta ce, "Muna jiranki uwa, idan kin tashi zuwa don Allah kada ki
Page | 115 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1]
zo da shirin cin wani don duka muna 'sonsu." Ta
wuce abinta. Hawaye ya cika a idon Tahir, tausayin
Gwaggo ya ji, idanuwannan kamar an saka masu
tarugu sun yi jajir.
A ransa yana wadaran uwa irin tasa, ya mike da
kyar ya isa gun Gwaggo ya zauna ya riko hannunta
ya ce, "Gwaggo kiyi hakuri.." Ta dube shi cike da
fara'a ta ce, "Da me fa?". Ya dube ta ya ce, "Da
abinda Mama tayi miki a kaina, don ni ne sanadi da
take wulakanta ki, ki yafe min." "Ba komai Tahir, ka
sani ni va mai son tashin hankali ba ce, sannan duk
mai hali Allah ne daidai dashi, ni duk abinda tayi
min nasan akwai lokacin da ko an ce tayi ba za ta yi
ba. Lokaci ne kuma zai wuce wata rana. Ni dai ina
so kayi min wata alfarma guda daya a yanzu.
Ya ce, "Gwaggo fadi bukatarki inshaa Allahu
zan cika miki shi." Ta ce, "To ina so ka je ka auri
Suwaiba." Da sauri ya dube ta ya kasa cewa komai,
amma ya hadiye wani irin miyau mai daci da zafi a
zuciyarsa.
"Gwaggo bana sonta amma zan yi yadda ki ka
ce, zan yi saboda kin amince, amma ba don Mama
ba, ina so in zama mai biyayya a gare ki."
Ta ce, "Tahir a kullum kana yi min biyayya da
nake godewa Allah da ya bani da irinka, Allah Yayi
maka albarka yasa ka gama da iyaycnka lafiya. Ina
so duk abinda ya dace na aure kayi shi, kamar yadda
Page | 116 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
al'adar Hausa ta tanadar, ka kuma bi shari'ar Allah
ka zauna da matarka lafiya."
"Na gode Gwaggo, Allah Ya bamu hakurin
aiwatar da wannan al'amari."
"Amin." Ta fada tana godiya ga Allah da yasa
Tahir ya fahimci abinda ya dace. Da:.na ba zama da
mutum a'a fahimtar irin mutum da ka ke zaune da
shi.
Dole tasa Tahir yaje Gusau, bayan kwana uku da
farywar abinda Mama tayi, ba yadda bai yi ta daga
auren ba don akwai wasu shirye-shirye da yake son
yi sam taki, ta darje ta ce fa ranar sati za a daura
auren don har ta fada wa Alh. Muh'd Shinkafi bai ce
a daga ba sai shi? ba yadda zai yi nan ma dole ya
amince ya bukaci su fada nawa suke so har da lefe,
ba karamin kudi Mama ta fada ba, ya zari check ya
rubuta ya bata, duk da yasan abinda kekan. Ba yadda
Suwaiba bata yi ba don ta ganshi amma ya ki, a
ranar ya bar garin ya ce sai ranar daurin aure zzi zo.
ci
Zuwan da bai yi ba kenan, (Scotland) ta Kasar (British) yaje yayi zamansa, har aka daura auren aka
aka lashe ango bai zo ba, sai da ya tabbatar an gama komai sannan ya dawo. A lokacin sati biyu
kenan da gama komai. Yana dira Nigeria a Kaduna
ya wuce gun Gwaggo, tayi murna sosai da ganinsa sai dai ta nuna masa rashin dacewa abinda yayi naki
zuwa daurin aurensa.
Page | 117
KИPCPA MARUBUCIYA: Sameera Mustonha
BAKI BIYU (1]
Gwaggo na fada wa Mama ta bari a daga saboda
ina da uziri taki, to ya zan yi dole ne in kula da
aikina. To an dai yi an gama nima shekaran jiya na
dawo daga Gusau, don Allah kayi abinda ya dace ka
ji ko dana." Yayi murmushin jin dadi a ransa yana
son yadda Gwaggo take kiransa da wannan sunan
'Dana' tun yana karami haka take kiransa, sai can ba
a raba take kiran sunansa. Tsaraba sosai yayi mata
bayan ya kwana daya ya wuce Gusau.
A Gusau Mama tayi fushi da shi sai dai abinda
yasa tayi sanyi yadda taga ya dan fada, dole ta
hadiye fadan da ta shirya yi, ta ce ya dauki matarsa
ya tafi da ita.
Su Suwaiba sai rawar jiki ake yi ango yazo za а
tafi, tuni suka shirya ta cikin kaya na alfarma. A
gaskiya tayi kyau kun san fa mutum ko bai da kyau
in dai akwai kudi to kyau yake yi, to a gaskiya
mahaifinta ma ba baya ba don yana da nashi
wadatar.
Tun a mota take yi masa mitar ya tafi ko ya kira
ta bai ce da ita ci kanki ba, babu abinda ke fata mata
rai sai irin miskilancinsa. Ta tsani tana yi masa
magana ko kallonta baya yi sai dai ya rika saurarenta
kawai, amma zuciyarsa bata gunta, dole ta hakura ta
daina mitar.
A kaduna suka sami jirgi suka wuce Lagos, wai
ita ba za ta iya kwana gidan Gwaggo ba, abin ba
Page | 118 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Karamin haushi da takarci da wulakanci ya zama ba
agun Tahir, ba don Gwaggo ta ce su wuce Lagos din ba da ba za shi ba, cewa yayi sai dai ita ta wuce
amma shi ba za shi ba, da kyar Gwaggo ta lallashe shi ta tura shi suka wuce.
Ai kuwa itama ba karamin horo yayi mata ba,
don tunda suka isa Lagos bata kara sa idonta a kansa
ba sai bayan wata uku, shima din mahaifinta ne ya
kira shi ya same su tare a falon Babanta su duka har
da mahaifiyarta. Da aka tambayc shi dalilin yanke
wannan hukuncin ya fada masu ainihin abinda ya faru, ya ce kuma idan bata girmama mahaifiyarshi
ba to a gaskiya zamansu ba zai yiwu ba, sai dai ya sauwake mata kowa ma ya huta.
Mahaifinta Alhaji Mudassir yayi tur da halin rashin mutuncin da 'yarsa tayi, sam bai goyi bayanta ba. Itama mahaifiyarta bata ji dadi ba, har dukanta
taso tayi a wurin amma da yake tayi saurin barin wurin ta dace ta bar falon ba tare da an doke tan ba.
A ranar ta bishi gida, amma bata sami yadda taso ba, gashi ko zaman gidan baya yi, idan ya bar gida baya dawowa sai tayi barci haka suke har suka sami
wata biyar da aurc. Rannan dai da abin ya ishe ta,
dole ta iske shi gun aikinsa ta shiga wurin cike da
sauko duk wani girman kanta kasa ta nemi wuri ta
zauna.
Page | 119 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Shi dai kallonta yake yi, ta fara magana. KРАТ
hakuri ina son muyi magana, naso kwarai muy
maganar a gida amma ba ka yarda in san fitarka ba
ballc dawowarka."
Shirun da tayi yasa ya ce, "To ba komai tashi
muje gida muyi maganar." Ta mike a sanyayc suka
kama hanya. Ya lura ta sauko dama abinda yake jira
kenan, da suka isa sai da ya ce da ita ta kawo masa
abinci da saurin gaske ta shiga kicin ta dibo abincin,
sai dai bai ci da yawa ba.
Sai da suka nutsu ya ce, "Fadi maganarki ina
saurarenki." Ta сe, "Dolly, don Allah kayi min
adalci ka bani hakkina." Ya gyara zamansa ya ce,
"Abinda ki ke bukata kenan kawai ba ki bukatar
zaman jin dadi tsakanina da ke?"
Ta washe baki ta ce, "Ina so, abinda nake fatan
samu kenan daga gare ka." Ya girgiza kansa "Ok,
ina da sharuda da nake son ki bi kafin ki samu
abinda ki ke so."
Dawowa tayi kusa da shi ta ce, "Wallahi fadi ko
menene zan yi, zan yi abinda ka kę so."
Mu hadu a littafi na biyu domin jin wanne irin
sharudda ne zai gindaya mata?
Taku,
Samira Mustapha.
Page | 120 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
SALAMABOOXSHD
No.650 J2, Katsina Central Market
Tel: 08062929660,
Littattaran marubucivar.
BAKIBIYU
SILA
LADABI
FITINAR MULKI
YADDA ALLAH YA SO
KAIDIN MACE
BAKI BIYU KATIN MACE
RAGEAST SAMIRA MUSTACHA
Cover Graphics AGF Computers Fagge
07030319787
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels