a dace." Tana aje wayar
na kwada sallama na shiga dakin, ina yi mata sannu
da gida ta amsa ni cike da fara'a, ban tambayc ta
hakurin da take ba wa Baba ba, itama bata yi min
zancen ba, don haka sai naji hankalina ya kwanta
don na lura ba zancena suke yi ba.
Bayan kwana biyu da faruwar hakan, dan
Gwaggo yazo gidan naji kuma sai rigima ake yi a
falon, ashe Tahir ne da iyalinsa ake shari'a, Gwaggo
ce Alkali, daga karshe dai naji an banko kofar,
matarsa ce ta fito cike da fushi ga masifa fal a
fuskarta.
Page | 93 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1)
Ni dai ina zaune ina son sanin (Current) din
abunda ke faruwa, amma babu hali dole na hakura
na shige dakina.
Da daddare muna cin abinci da Gwaggo, Tahir
ya shigo fuskar nan tasa kamar cabo don babu
annuri a cikinta. Ya sami wuri ya zauna, ni kam
banza nayi dashi don bai ishe ni kallo ba dama.
An kawo masa abinci amma ko kallon abincin
bai yi ba. Ya dora kafarsa kan dayar yana girgizata.
Ina kallonsa ta gefen idona, can kuma ya dauki
(Remote) din (TV) yana latse-latsensa. Sai da
Gwaggo ta gama cin abinci sannan ta ce masa.
"Dana ya ya dai ba za ka ci abincin ba ka shigo
ko sallama babu? Ka dauki komai da sauki mana."
"Gwaggo na riga da na yanke shawarar aure zan
kara." Ta ce, "Aure Tahir?" Ya ce, "Eh Gwaggo,
lokaci yayi da zan sami farin ciki a rayuwata. Haba
Gwaggo, ki duba ki ga aurena ya shekara kusan tara
amma in ban da tashin hankali babu abinda nake
ciki, a gaskiya Gwaggo aure nake so kuma ke za ki
zaba min mata."
Gwaggo tayi murmushi mai cike da nishadi. Na
lura abin yayi mata dadi, tunda naji ya soma
surutunsa sam ban yarda da maganar bai da
kwanciyar hankali ba, bayan duk halinsu daya,
shima namiji ne gashi da kudi, don haka ban ga
Page | 94 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
laifin Suwaiba da take gasa shi ba, kila ma sharri yake mata.
Sai sun tashi son kara aure sai su fara fito da
rashin kirkin matarsu, sai ka ce su basa yi, in auren
ma yake son ya yi me yasa ba zai fada (Straight to
the point) ba, sai ya fadi aibun matar? Ina tunani na
bar wurin don wani irin haushi ya bani, na isa dakina
na kwanta, dama ni bana wuce karfe tara nayi barci.
Bayan kwana bakwai da yin wannan abu,
Gwaggo ke tambayata randa zamu rubuta jarabawa
na wannan (Semester) din, na ce da ita nan da sati
uku. Naga ta saki fara'a sosai ta ce, ya yi kyau,
Allah ya nuna mana Ya kuma bada sa'a nayi wake.
Na ce amin. Sai dai ina ji a jikina kamar da wani abu
da ake shirya min da ban san da shi ba.
Ikon Allah! ji nake yi kamar ban da lafiya, tun
lokacin da Gwaggo tayi min tambayar hutunmu
abinci ma ya soma fita raina, gani nake yi auren dole
za'ayi min, don a koda yaushe za ka ji Gwaggo da
Baba suna waya, sannan Gwaggo taje Gusau har sau biyu na rasa ta inda zan fara tambayarta dalilin
zuwanta, amma saboda ina tsoron abinda zan ji shi
ne nake da kewa naki tambayarta. Itama bata ma
kula ina cikin damuwa ba, a kullum tana cikin nishadi.
Rannan ina zaune a falo sai wayar Gwaggo ta
fara ringing, da sauri na dauka. Babu suna lamba ce,
Page |95 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1)
na kara a kunnena na ce, "Hello!" sai naji anyi shiru,
na kara maimaitawa. Can naji an ce, "Ke!" sai da gabana ya fadi don ba karamin tsoro naji ba, sai ka
ce ina ganin mai maganar. Ban san lokacin da
Gwaggo ta iso guna ta amshi wayar ba.
Ji nayi tasa hannu ta karba ta ce "Hello!" wuri na
samu na zauna ina sauraren abinda Gwaggo ke fadi,
sai da tayi shiru na kusan minti uku sannan naji ta
ce, "Hajiya Basira bana da abinda zan ce da ke sai.
Allah Ya shirye ki ya ganar da ke, in ke mai ganewa
cc." Tana gama fadar haka ta ajiye wayar.
Na lura ranta a bace yake, na tashi na matsa kusa
da ita na ce, "Gwaggo me ke faruwa ne?" Na
marairaice fuskata kamar zan yi kuka sam bana son
in ga Gwaggo cikin damuwa, wallahi ina bala'in
tausaya mata shi yasa a kullum nake kara yiwa kaina
alkawarin ba zan taba saba mata ba, zan yi mata
biyayya a kan ko menene.
Ta dube ni ta sassauta muryarta ta ce, "Yar
kanwata, ina so ki bani hankalinki baki daya, ki
fahimci abinda zan gaya miki, ba wai nayi hakan da
wani manufa ba, sai don in aikata alheri, 'yar
kanwata nayi miki miji."
Baki nayi saurin budewa ina kallonta, sannan a
lokacin naji cikina yayi wani irin kuka tare da
murdawa, kulululu! Ka ke ji, idona kuma kan ka ce
wani abu hawaye zuba suke yi, wato a cikin zuciyata
Page | 96 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1)
kuwa wani irin zafi nake ji wanda ba na iya
misaltawa.
Ta ci gaba da cewa, "Yar kanwata ba zan yi abin
da zai cuta maki ba, ni na sani inshaa Allahu za iyi
dace da shi, yana da kirki ga hakuri yana da fahimta
tiye da yadda ki ke zato, don Allah kiyi hakuri nasan
na takura miki, amma insha Allahu alheri ne a gare
ki da mu baki daya.
Duk da tashin hanalin da ke tare da ni ban nuna
mata ba, sai dai kwallar da ta gani a fuskata. Na
soma magana a hankali.
"Gwaggo ba komai na fahimce ki, zan yi biyayya
gare ki in yi duk abinda ki ke so." Na mikc a
sanyayc zan wucc, ta rikc hannuna na juyo a hankali
na dube ta. Ta saki fuska ta ce, "Yar kanwata ba ki
tambaye ni mijin ba." Na kauda fuskata don wani
daci da ya taso min a baki da kyar na ce, ai ba sai na
san shi ba Gwaggo, duk abinda ki kayi yayi daidai,
ta ce ko nakasasshe nc? na dubeta da sauri naga tana
dariya. Ban iya cewa komai ba sai murmushin karfin hali da nayi mata. na ce, "Eh Gwaggo, ba komai zan
aure shi."
Ta jawo ni na zauna dab da ita ta ce"Dana ne
Tahir." Ai ban san lokacin da na kwanta a jikinta ba
ina rusa kuka, gaba ki daya na saki ukan sai ka ce
irin 'yan yaran nan 'yan shekara uku, ina fadin
"Gwaggo na shiga uku! Haba Gwaggo! Ki rasa duk
Page | 97 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
namijin da za ki hada dani sai wadannan mutanen
mara mutunci? Gwaggo na yadda ki hada ni da
kowane irin mutum amma ban da shi, ni ba zan iya
ba, ba zan iya zama da shi ba Gwaggo na tsani duk
wanda yake da alaka da Haj. Basira, wallahi
'ya'yanta ba su da bambanci da ita, dukkansu
halinsu daya, ni ba zan iya ba."
Gwaggo lallashina take yi tana bani magana,
amma ni fur naki, kuka nake yi kmar zan cire kayan
cikina. Tun tana lallashina har ta ture ni ta mike ta
soma fada. A kalla ta sami kusan awa biyu tana bani
hakuri, amma ko saurarenta naki, shi ne fa ta ture ni
ta mikc tana cewa, ke yarinyar nan ba ke jin lallashi,
to in ba ki sani ba komai an gama don har rana an
saka nan da wata daya in Allah ya kai..."
Ai ban bari ta gama ba nayi cikin dakina da gudu
ina ihu, tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, daga
karshe dai ta ce Allah shirye ki Dayyiba, dama ita ai
kullumk kalamanta kenan in kayi mata abinda ba
daidai ba.
Tun daga ranar na daina zuwa gun Gwaggo, ko
gaisuwa da nake zuwa musamman in yi mata na
daina, itama tayi kunnen uwar shegu dani ta share ni,
abinda yafi daga min hankali kenan, shi kenan
Gwaggo tafi ta ba tuna kenan, na shiga uku ai kan ka
ce wanina fita hayyacina, watan ni ba ma auren ne
yake tayar min da hankali ba, a'a share ni da
Page | 98 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1)
Gwaggo tayi har na tsawon kwana biyu, ai ba zan
iya kara kwana ba ban je na neme ta gafara ba.
Da yamma likis na dawo daga makaranta, na
shiga falon na iske ta zaune tana kallo, na karasa gun
ta in yi mata sannu da gida, abin mamakii cike da
fara'a ta amsa min. "Ya makaranta ya jarabawa?".
Na dan sassauta murya na ce, "Ai ba mu fara ba." Ta
ce, "To Allah ya ba da sa'a." da sauri na ce
"Ammin."
Na zauna sukuku kamr wadda aka fashewa
rubabben kwai a ciki, na ce "Gwaggo." Cikc da
shagwaba nake magana. "Don Allah kiyi hakuri da
abinda nayi miki, ni dai ban yi tsamamanin haka ba
shi yasa." Ta rungume ni ta ce, "Yar kanwata ba
komai, ni na san za ki yi dace da miji irin dana, don
ni nasan abuna na."
Na bata fuska sosai na ce, "Gwaggo na lura kin fi
sonsa da ni." Ta kyalkyale da dariya ta ce, "Kai wa
ya fada miki, ai ke na fara sani kafin shi." Na turo
baki na ce, "Gwaggo ni fa bana son shi, wallahi bana
Kaunar in hada wata alaka tsakanina da wadannan
mutanen saboda halinsu."
"Ka ji ki fa! Shi Tahir din an gaya miki halinsu
daya ne, shi fa daban yake da sauran yaranta,. Na
ce, "Ni dai Gwaggo ki canza min wani, wallahi bana
iya hakurin zama da irin wadannan mutanen..
Page | 99 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
"Ke wai wace irin yarinya ce da ba ki jin abın da
nake fada miki? To ai sai kiyı, miji ne an ba ki shi
da yake namiji ma bai damu ba sai ke?" kuka na rika
yi mata na kwanta a kan cinyarta ina kukan
shagwaba.
Tunda wannan magana ta fito sai naji ni tamkar
lokacin da Sa'id ya ci amanata, ba abinda ke min
dadi sai dai ikon Allah ban yi ramar da nayi a
wancan lokacin ba, amma nasa wa kaina tunani
sosai, babu abinda ya fi tada min da hankali irin idan
na tuna da matarsa da mahaifiyarsa, gashi mun fara
rubuta jarabawa, kuma auren sun saka shi kamar
bayan mun gama jarabawa da kwana hudu,
kwanakin kuwa sai gudu suke yi.
ASALIN WAYE TAHIR SHINKAFI
Tahir Moh'd Shinkafi tun yana dan yaye Нај.
Hauwa ta dauke shi daga wurin mahaifiyarsá. Ba
komai yasa mahaifiyarsa ta amince ba sai don wani
irin rashin lafiya da yayi lokacin yana dan shckara
daya da wata daya, to sai ya ki shan nono ya yayc
kanshi.
Ba ya cin abinci duk ya lalace gashi a lokacin
Haj. Basira tana zuwa makaranta, ita mahaifiyar tasa
a ranta ba ta zaton zai rayu, don yadda ya zama an je
asibiti anyi-anyi amma abin ya faskara.
Rannan da yamma Haj. Basira bata gida, Haj.
liauwa tajc gidan ta iske yaron yana ta kuka, mai
4
Page | 100 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
aiki itama ta gaji da rainon ko in ce lallashı, sai ta
ajiye shi a falo taje tana wani abun a daidai kuma
lokacin shima Alh. Muhammad Shinkafi ya shigo
gidan, shima kuka ya ishe shi, sai ya shiga sashen
Haj. Basira ya iske Yayarsa Haj. Hauwa tana fada,
shima ransa ya 6aci sosai. Ta dube shi ta ce,
"Muhammadu ina so ka ban: damar daukar yaron
nan, yana bukatar uwa, don Allah ka bani shi don
darajar Annabi (S.A.W)."
"Haba Yaya, har sai kin roka, ai abinda na haifa
kina da iko da shi, don haka na ba ki shi dama ai
danki ne." Bata jira komai ba ta shiga dakin da kayansa suke ta kwashi kayansa, zata fice kenan sai
ga Haj. Basira. Tana ganin Haj. Hauwa sai ta bata
fuskarta, tabi bayanta da yake Haj. Hauwa bata ma jira yi mata bayani ba, "Ke ar..." bata karasa ba Alh. Muhammad ya tsaida ita da hannunsa, ta hanyar
wani irin bacin rai a cikin idonsa, duk wulakancinta
in ta lura da yanayinsa sai tayi sanyi
Duk da mutane na cewa ta gama dashi, amma
shima wani halinsa ba ya gushewa don ba karamin kyalle ba ne idan tsiyarsa ta motsa, don haka ne dole
ta tsaya tana kallon ikon Allah.
Haj. Hauwa ta raini Tahir tamkar ita ta haife shi.
don komawa da yayi gunta cikin wata hudu ba za ka
ganc shi ba. Cikin ikon Allah da yake shi magani
dace ne, ta shiga kasuwa gun 'yan maganin
Page | 101 MARUBUCIYA: Sameera Museyhа
BAKI BIYU (1)
gargajiya, a nan tayi dace da magani takc ba Tahir
sai da ya kai shckaru uku sannan ta daina yi masa
wanka da ruwan dauri.
Jc ka ga yadda yaron ya zama, ya yi bul-bul, ga
rashin ji, yana da kuzari sosai sai ka ce ba shi ba,
yayi kyau sosai. Sam ba ta kai shi gun uwarsa
saboda wata kalma guda daya da Hajiya Basira ta
fada mata, ta ce in ita mayya ce to sai ta cinye shi
danye ba sai ta dafa ba.
Lokacin da ya kai shekara biyu tashin hankali
aka yi da ita, wai don rashin mutunci da cin fuska
irin na Haj. Basira ga rashin kunya, sai da taga yaro
ya warke yana ta hidima shi ne taje ta ce a bata
danta.
Shi yasa ita kuma Haj. Hauwa ta nuna mata
matsayinta, ta kore ta daga gidanta ta ce kuma Tahir
da ita sai ido.
Tahir ya girma cikin kulawa ta musamman da
tarbiya tagari, dama ita akwai (Displine), cikin ikon
Allah da ya girma sai Allah yasa masa son Haj.
Hauwa a ransa, duk da yasan mahaifansa. Duk
shige-da-ficen da Haj. Basira tayi a kan Tahir ya
dawo gunta, abun ya faskara.
Dama ita Haj. Hauwa yadda take nema wa kanta
tsari to haka ma take yiwa Tahir, a kan dole Hаj.
Basira ta kawo na Mujiya (idanu) tasa masu. Duk da
akwai lokacin da yaso ya koma gunta, shi da kansa
Page | 102 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
2
BAKI BIYU [1]
ya koma gun Haj. Hauwa sam ba ya son halin
mahaifiyarsa, inda ana canza uwa da ya canzata.
Da ya gama Makaranta (Secondary) cike da
sauki ya sami gurbin karatu a Jami'ar Danfodiyo,
wato (Usman Danfodiyo University, Sokoto), da
yake yana da ilimi (Sociology) ya karanta, ilimi a
kan rayuwar dan Adam.
Sau da yawa za ka yi mamaki idan Tahir ya fada
maka ra'ayin ka a kan rayuwarka. Kallon ka kawai
zai yi ya fahimci irin abinda ka ke tunani, Allah ya
kara masa wannan baiwar saboda dama shi đan
baiwa ne, saboda yana da natsuwa da hankali. Ba ya
da hayaniya, ba ya da surutu, gashi santalelen yaro
mai jini a jiki, shi irin samarin nan ne da suka sa
abinda ya dame su a gaba, bai da son shiga mutane
shi yasa ake kiran sa da (Gentleman).
Sam ba ya ra'ayin shashanci irin shaye-shaye da
neman mata, a kodayaushe yana gida abokinsa daya
ne Sahabi mijin Badiyya, dama sanadin sa ya ganta
har suka yi aure.
A kasar (London) ya yi (Masters) dinsa, yana
dawowa Alh. Muh'd ya samar masa aiki a (NNPC),
cikin ikon Allah ya buda masa fiye da yadda ake
zato, shi da kansa ya yi tunanin barin aiki don Allah
Ya ba shi sa'a, yana da (Connection) sosai. Lagos ya koma yana shigo da (Crude oil), wani lokacin kuma
ya shigo da (Petrol) ko kalanzir daga kasashePage | 103 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Kasashe, idan Allah Ya tashi baka ba ya kallon ko
kai waye yana baka abinda yaga dama.
Tahir dan shekaru talatin da biyu, gashi (Young)
amma akwai kudi. Shi yasa Haj. Basira ta haukace a
lokacin sai dai ya auri 'yar 'yar uwarta, a lokacin ko
maganar aure ba ya yi, don a ganinsa bai da lokacin
wannan. Tahir yana bukatar mace amma yana
Kokarin kame kansa, duk da kun san matashi, ba wai
bai taba harka da mace ba ne a'ah, kun san idan
matashi yana da abin hannu to in dai ba Allah Ya
kare shi ba komai kamun kansa sai ya fada tarkon
wata.
A can (London) yake da wata 'yar Baturiya da ta
amsa sunanta, Christiana sunanta, a makaranta suka
hadu. Tahir yana da ka'idojinsa da ya tanadar wa
kansa, yana da (Displine) sosai ma'aikatansa ma sun
sani, sam ba ya wasa da aikinsa, gashi dama yana da
ilimi gun fahimtar dan Adam.
Sau da yawa ma'aikatansa na mamakin hali irin
nasa, yana da kauda ido a al'amuran ka amma duk
randa abin ya taso masa ya fara zayyana maka irin
rayuwarka to abun sai kayi mamaki.
Tunda mahaifiyarsa ta matsa masa a kan auren
Suwaiba ya daina zuwa gunta baki daya. Ya dauke
kafarsa daga gidan, dama can ba zuwa yake yi ba
don sam ba ya ra'ayin irin halin mahaifiyarsa, amma
ya zai yi tunda haka Allah Ya shirya masa, shi dai
3
Page | 104 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
A
BAKI BIYU [1)
yana yin abinda ya dace. Yana kyautata mata amma
kullum bata gani tana hangen na Gwaggo.
Tabbas mijin Gwaggo yana da hali kuma yana
yiwa Gwaggo abinda bata bukata ba ma, yadda
amaryarsa ke jin dadi haka itama. Sau da yawa
'ya'yan suna zuwa mijinta ma suna zuwa mata hutu.
Mijin ya so kwarai ya bata daya daga cikin 'ya'yan
amma taki, ba don komai ba sai don irin wulakancin
da tasha a kan Tahir, shi yasa take taka tsantsan da
irin zaman su da kishiyarta, dama tunda suka hadu
da Haj. Basira suka zama abokan juna, shi yasa bata
karba ba, sannan dama Hausawa sun ce abokin
6arawo бarawo ne.
Tahir yaso kwarai ya ki amincewa auren
Suwaiba, sai dai kuma bai sami goyon bayan
Gwaggon tasa ba, dole ne yasa ya aure ta a cewarsa
bai ra'ayin irin Suwaiba, don yasan bata da kamun
kai, ita kuwa Suwaibar a (America) suka hadu, abin
ikon Allah ne, ya dan zauna da ita a can ba wai
zaman batanci ba a'a ita ce ta makale masa, sonsa
take yi sosai tun ba ya biye mata har ya fara
saurarenta, da ya dawo gida don dama kwas yaje
lokacin yana aiki da (NNPC) a nan Lagos sai itama
ta biyo shi.
Abin mamaki ashe 'yar uwarsa ce, don 'yar
kanwar Haj. Basira ce, tana Lagos ne da zama, da yake ita kadai ce 'yarta ta mace duk 'ya'yanta maza
Page | 105 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
SAKI BIYU [1]
ne shi yasa ta shagwabata, komai tayi daidai ne sam
ba a kwaba mata Babanta ma haka yake bala'in
sonta ba ya son yaga digon hawayenta, duk da ba ita
ce 'yar auta ba ita ce ta biyar a gun iyayenta da yake
su bakwai ne, amma ko autan baya yin abinda take
yi.
A (American) tayi karatunta na (Secondary), har
Jami'a, yadda taso Tahir ya kwana da ita ya ki, shi
fa ba sai an fada masa ba iliminsa kenan, duk irin
kwadayin da ta nuna masa ya ki amincewa. Ya dai
bar ta a matsay in abokiyarsa. To shi ne fa tana
dawowa tayi musu maganar Tahir, tayi mamaki
kwarai da gaske, ashe da gaske ne da ake cewa jini
daya duk inda yake aka hadu sai ya nuna.
Suna jin ta haukace a kan Tahir suka nemi
mahaifiyarsa, cike da murna ta amince, dama hakan
ya yi mata daidai. Ta shirya tafiya ta musamman don
suyi shirin da kyau, ita kanta ta san halin Suwaiba,
bata da tarbiya lo amma hakan yafi mata dama tana
neman yadda za ayi danta ya dawo gunta, asirin
duniyar nan tayi amma abun ya faskara. Ta rasa ita
Haj. Hauwa wane irin asirin take yi da yafi karfinta,
in da bukatarta zata biya da tuni ma ta nakasa Haj.
Hauwan, amma ta Allah ba tata ba, dole ta fita
hanyarta, to yanzu ta sami hanya me sauki da ta
amu damar kwato shi daga gare ta.
Page | 106 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1]
Ya kai sati hudu da liaj. Basira ke nacin taga
Tahir, amma ya ki zuwa, sai da tayi masa ziyarar ba
zata a Lagos. Sai ganinta kawai yayi. Bai yi mamaki ba, don ya lura wata bukata ce ta ke nema a gunsa, ta
nuna bacin ranta sosai, shi dai hakuri yake bata suka
zauna don suyi maganar. Tana fada mishi tayi masa
mata, tun kafin ya san Suwaiba ce hankalinsa ya
tashi, don dai shi bai shirya wa aure ba, ta kunduma
mai zagi ta ce don kaza-kaza ka inda Haj. Hauwa
mayya ce ta fada maka kayi aure za ka ki ne?
Ni na rasa maita irin na wannan mata, ta riga da
ta lashe ka tas ba ka jin maganata sai nata, to ko ka
ki ko kaso ni dai ce uwarka, sai dai ka kashe ni ka
huta, tun ma ba ka ji yarinyar da na samo maka ba, haka za ka je ka kwaso wadda bata da usuli ba 'yar
mutanen manya ba, irin yarannan na kananan
mutane wadanda ba su san su ci arziki ba..."
"Mama kiyi hakuri, ni ban ma nemi matar ba, ban tashi aure ba."
"Iye! Sai yaushe zaka yi auren? Haka marikiyarka ta shirya maka? Don na lura sai abinda
ta shirya maka ka ke yi, duk ransa ya 6aci shi baya
son yadda Mama ke zagin Gwaggo, itama tana so ya yi auren shi ne dai bai shirya ba.
A karshe dai ta fashe masa da kuka tana magiyar
ya taimaka mata yayi wannan aure don a rayuwarsa
Page | 107 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU 1]
bai taba yi mata alfarma ba, ita yanzu alfarmar da
take bukata yayi mata kenan.
"To shi kenan Mama, ki daina kuka zan duba in
gani.
"Au! Abinda za ka ce kenan, duk wannan
hawayen da na zudda ya zama na banza kenan?" Ta
Kara rushewa da kuka ta ce, "Oh ni Basiratu na shiga
uku! Matar nan ta gama da Tahir, ai kuwa zata ga
sakamako, don karfin hali kai da haihuwa wata da
kwatar maka da, ba ka da iko da dan nan sai..." Ya
katse ta, "Haba Mama, don Allah ki bari shi kenan
naji zan zo muyi magana a ina yarinyar take ne?"
Nan da nan ta kare kukan da ta kwakulo take yi, ta
washe bakinta a nan garin take itama 'yar Antinka се
Haj. Basira, ai ka santa sai dai ba ka da zumunci.
Tahir yau shckararka nawa ba ka je gidan ba, ai ta
fada min zuwanka biyu na karshen ma sako da na
baka kai baka ma shiga ba maigadi ka ba ka tafi,
dama tana da 'ya mace ne? ch mana, tana da ita ita
kadai ce kwal mace a gun iyayenta, tasa hannu a
jakarta ta zaro hoto.
"Ga hoton ta nan." Ta mika masa, ya karba ya
duba. Suwaiba ce da ya sani a (America), hankalinsa
ya tashi amma sai yayi ta maza ya cc, a'ah Mama a
ina take hala don ko zuwan da nayi gidan bamu hadu
da ita ba? uhum ai tana Makaranta ne a (Boarding).
A ina? Ta dan yi shiru tana tunanin abinda zata ce
Page | 108 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
masa, shi kuwa ya kura mata ido. Mits! Tayi tsaki ni
dai kaman a nan Lagos tayi karatunta, ya riga yasan
mahaifiyarsa da karya, ta saba yi masa, ta san shi
yana (Against) kai 'ya mace kasar waje karatu don
duk karatun da ka ke so mutum yayi ana yi nan
Nigeria.
Shi dai sam ba ya shalawar hakan don ko a
Nigeria ya aka kare ballantana a tura ta waje karatu,
har gara namiji duk abinda yayi ado ne a gare shi a
kan mace. Saboda lokacin Amina itama taso taje,
tare ma ne da Suwaiba. Tahir ne ya hana, don
mahaifinsa ma suna dasawa.
Shi dai ya kyale ta ne don babu yadda za ayi ya
ce karya take yi, kuma zancen ya ishe shi haka sai ya
ce, kawai da ita yaushe za ki koma Sokoto? Tayi
murmushi, ai akwai jirgin karfe shida na yamma, shi
zan bi. To shi kenan zan je in ganta, rungumarsa ne
kadai bata yi ba don dadi, ta rika cewa Allah yayi
maka albarka Tahir, na gode da ba ka watsa min
kasa a ido ba, Allah Ya yi maka albarka, shi dai so
yake su rabu lafiya, shi yasa ya ce mata hakan.
A ransa kuwa in ban da tir da yake yi da wannan
aure, ita dai Mama tana yin abu ne (With Interest)
shi yasa bukatarta kullum a baya yake. Lokacin da
Gwaggo ta koma Kaduna abin ba karamin dadi yayi
masa ba, don in ya shigo kai tsaye gidan yake zuwa
yayi kwana biyu ya koma.
Page | 109 MARUBUCIYA: Sameera Misapha
BAKI BIYU [1]
Bayan yaje gun Gwaggo da wannan labari, ta ce
Allah kara tun yaushe na ce kayi aure ka ki? To ai
kuwa dole ne kayi don dama ni ban ga amfanin
zamanka a hakan ba, gashi kuma na gida don haka
nima na bada goyon baya don ban ga-abinda ka ke
jira ba.
Gwaggo a dan bani lokaci, in samu ko kuma ke
ki samo min hankalina zai fi kwanciya, kai dai dama
haka ka ke duk aka yi ma zancen aure sai ka ki, ni
dai kaje ka aure ta don nima ina son in ga jikokina.
Murmushin takaici yayi ya rasa yadda aka yi,
Gwaggo taki ta fahimce shi koda yake ya karanceta,
so take yi yayi abinda mahaifiyarsa ke son don
kadda wata masifa ta taso sarai ya san halin
Gwaggo.
Bai samu goyon bayan Gwaggo ba dole ya koma
Lagos da sanyin gwiwa. Bai yiwa mahaifinsa
maganar ba, don ya san shima ba zai goya masa
baya ba, sai abokinsa ya samu Sahabi suke shawarar
inda za'a bullowa al'amarin, Sahabi duk
shashancinsa ya kan daina idan Tahir na tare da shi,
don yasan ba zai lamunta ba, in dai yana Kaduna to
yana gidan Sahabi.
Badiyya tana jin dadin zuwansa don a wannan
satin mijinta yana gida gashi da sakin hannu ga
tsaraba haihuwar da tayi ma bata iya sanin ainihin
alherin da ta samu ba, don har kullum in zai zo sai
Page | 110 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
ya kawo tsaraba. Mamana ya ke kiranta tunda ya san
matsayinta a gare shi.
An sami kusan wata uku Mama na son jin abinda
yake ciki amma ya ki, ko Gusau ya ki lekawa don
bai son maganar a kullum ta bugo 'masa waya ba ya
kin dauka sai dai ya ce mata ya