fasa kyautata musu ba don
halinsu ba a' a sai don Allah sai don kuma kuna
bauta kun san kuma duk abin da ku ka yi saboda
Allah, to Allah shi zai saka maku.
Ke kuwa Fiddausi ki godewa Allah ma yana hirar
a gabanki, kin san abinda yake ciki, to in kina so ki
daina damuwa da al'amarinsa, ki sa masa ido kada ki
kula shi ko ma dai ai ya rabu da ita tunda saki uku ne
tsakaninsu, me ruwanki da su, kafin ki shiga ita ta
shiga. Ke dai kiyi abinda na fada miki, wato hakuri
da sa ido, kiyi masa biyayya ki roki Allah mafita da
na tsari daga sharrin duk wani sharri."
Da naji Anti Nafisa tayi shiru, sai na saka masu baki na ce, "Kai Anti ni ina ga ma aurc ba zan yi shi ba, don babu abinda ke cikinsa sai cin amana.
Wallahi a yanzu ba wanda nake ki nake jin takaici
irin da namiji, bana da makiyi irinsa, su dukkansu mayaudara ne don halinsu daya..."
"Ki ka ce ba za kiyi aurc ba?".
"Ba zan yi ba Anti, na hakura da auren."
"Wacce irin magana ki ke yi, ba ki son lada
kenan ba ki son ki raya sunnar Manzon Allah
(S.A.W) kenan?".
"Eh! Gaskiya na fada Anti, ai an ce in ka zabawa
kanka rashin aure sai kayi ibada, don haka ma ni
ibada zan yi, in yi karatu duka boko da Islama,
sannan in yi aikina in kuma karc mutuncin kaina."
Page | 75 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
A daidai lokacin maigidan Anti Fiddausi ya ke
kwada sallama. Tayi saurin mikewa.
"Ba dai Mukhtar ba ne?". Anti Nafisa ta isa
wajen kofa tana amsa sallam, ai kuwa shi na. "A'a,
mutanen Kano ya hanya? iso mana."
Ni kam bar masu gidan nayi don a gaskiya sun
kara min ilimi a kan wanda na sani, tuni bakin cikin
Sa'id ya dawo saboda a zuciyata na kuma Kara
tsanar da namiji, dukkan su halinsu daya ba su da
banibanci.
Idar. sun aure ka in ban da su nemi su kashe ka
ba su da buri a zuciyarsu, ga su sun iya hora mutum
su kuma maida kai bayinsu. Allah Ya kiyaye, ni kam
ai sai dai ayi ta yi, amma aure kam sai a Aljanna
inshaa Allahu.
Na isa gida na iske 'yan Allah sanya alheri suna
zaune suna hira da Baba, na shigo na gaida su na
wuce dakin Babah, nayi sallahr La'asar sannan na
kwanta duk raina a bace yake.
Daga can falo naji wata kawarta tana bata labarin
wulakancin da mijin 'yarta yayi, wai da 'yar tata
bata da lafiya. Da yake rashin lafiyar ya yi tsanani
kuma mijin ba wani hali ne da shi ba.
A gaskiya yayi nasa kokarin amma suma ba su
huta ba, da su ake ta dawainiyar ciwon ya kai har
Page | 76 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
mun ma cire rai, don ciwon har jinin jikinta yake
tsotsewa.
"Wallahi Mairo muna asibiti da yarinyar nan a
lokacin, ma jini ake sa mata, ba ta ma san inda take
ba, sai ga mijin ya shigo mana cike da rashin
mutunci, ya mika wa kanwarta takarda tarc da katin
יי daurin aurensa.
"Kai Habiba, amma wannan mutumin da karfin
hali yake, aurc ya yi?".
"Hum! A lokacin bukatarsa aje a kwashe kayanta
zai sa amaryarsa, sannan ya saki Binta saki har uku."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kai maza na
yin abinda suka ga dama a wannan lokacin, Allah ne kadai maganinsu. Allah Ya saka wa wannan yarinya.
To ya yarinyar tayi?".
"Ya zata yi Mairo? Dole ta rungumi kaddara,
don baki dayanmu mun kasa sanar da ita abinda ake ciki, har sai da ita da kanta ta lura ba avi met
zancen komawa gidan mijin ba, sannan ta zo ta same
ni ta ce, "Mama yaushe zan koma gida, hala na fa warke."
Na dube ta na ce, "Mijinki ya rabu da ke, duba
wancan dakin da ke kulle kayanki ne a ciki. Ba kin
san abin mamaki abun bai bata mamaki ba, cewa
tayi, "Alhamdulillahi, ai dama ta gaji da zaman da
suke yi." Ni kam kunnuwana na rufe da tafin
hannuwana don kada in ji Karshen labarin, to me ke
Page | 77 RMARUBUCIYA: Sameera Mustanh
BAKI BIYU [1]
shirin samuna ne? duk inda na zauna babu labarin da
ake yi sai matsalar da namiji, shin duka maza sun
zama shaidanu kenan? in ban da gasa mata babu
abinda suke yi. Ni kam duk yadda za'ayi da ni ba
zan yi aure ba, don halin maza sai su, gara in zauna
haka ba sai nayi auren ba.
Kiyayya sosai nasa tsakanina da da namiji, na
tuna lokacin da zan gama 'yar dilana ta "kan da
namiji (GP) na yayi kasa na fito da (Pass). Tabbas
namiji da ne da yake yin abinda yaga dama a
wannan zamanin, sai abinda yake so za ayi masa,
sannan su kuma matan sun manta da Allah a cikin
al'amuransu, don haka ni nayi alkawari da kaina.
zan zama mace mai mutunci amma ba zan yi aure
ba. Tare da Anti Fiddausi muka wuce Kaduna, ta
ajiye ni sannan ta wucc. A lokacin Gwaggo ta shirya
mana tafiya zuwa umara. Murna a guna ba a
magana, sannan na kara sayan (JAMB) in rubuta
saboda nasan zaman gida zan yi tun da (Poly) ba za
su dauke ni ba sai nayi shckara biyu a gida saboda
na fito da (Pass).
Mun je kuwa mun yi aikin Umurah sosai muka yi
addu'a ba na wasa ba, sosai nayi addu'a a kan Allah
Ya kare ni daga sharrin da namiji.
Allah kuma ya bani ikon kare kaina da
mutuncina. Muna dawowa muka rubuta jarabawa.
X
Page | 78 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Cikin ikon Allah kuwa da ya fito na sami (Point)
din da ake bukata, har (Point 210), na kuma saka
(University) na Kaduna baki dyan (Choices) din
cike da sa'a. A wannan lokacin na sami (Admission)
suka bani (Economics).
A saukake naje nayi (Registration) na fara zuwa
Makarantar, abin mamaki sai muka hadu da Amina
Aminu, sam ban san tayi (Appling) ba kuma
(Caurse) din mu daya ba, sosai nayi farin ciki da
hakan, ko ba komai mun saba tun can dama.
A wannan lokacin ne Anti Badiyya ta haihu ta
sami 'yarta sai dai ni ban sami zuwa suna ba, don
muna karatu sosai itama Aisha cikinta har ya fito
sosai, muna haduwa a Islamiyya.
Muna zaune ni da Amina, a makaranta muna
jiran (Lecturer) ya shigo aji, na lura kamar tana tare
da damuwa.
"Yar uwa me ke damunki ne? na lura yau You
are not in the mood."
"Uhm!." Ta fada tare da maida hankalinta guna
ta ce, "Yau kam gaskiya ina cike da damuwa
wallahi, kin san uwargidata mace mai dumbin
hakuri, tana da imani daidai ita, don wani lokacin
ma ganin nake yi ta fini.
Matar nan 'yar aljanna ce, sai dai in ta canza
daga baya da yake kin san dan Adam ajizi ne,
wallahi kin san lokacin da nazo gidan nan a zatona
Page | 79 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
zaman zamu yi har na soma yi mata ganin gari, sai
daga baya na gano shirme nake yi.
1
1
Sosai muke zaman lafiya da ita, sai abinda ba a
rasa ba, shima din sai dai ni in dauke shi da zafi
amma ita kam tuni har ta manta ma mun yi, shi yasa
in tana cikin matsala ji nake kamar ni ce a cikinta.
Danmu, wato babban danta shi nc babba a gida,
sunansa Abdulkadir, ba ya jin magana, shayc-shaye
yake yi Dayyiba, amma cikin ikon Allah ba wanda
ya fahimci hakan sai ni.
Ina tunanin yadda zan fada mata, gashi duk gidan
daga ita har Baban sun bala'in yarda dashi, sun sakar
masa da yawa. A tunaninsu yana da hankali da
natsuwa.
Tabbas yana da natsuwa don ba ya da raini, ko ni
Anti sama Anti kasa haka yake kirana, don in gaya
miki ma ya girme ni da shckaru hudu. Ya ya zan yi
in fadi wannan mummunar maganar ga
mahaifiyarsa, sannan yana bin 'yan aikinmu da yakc
muna da wata yare ce ita mai suna Monica, ita ke
mana reno da 'yan gyare-gyarc.
'Yar aikita ce jiya da daddare na fito kenan na
same su tare a nan dai kofar (Kitchen) dina ta baya
yana (Kissing) dinta...na rasa matakin da zan dauka
a kan wannan al'amari."
Ajiyar zuciya nayi ina girgiza kaina don nayi
(Shock) sosai da wannan labari, a kullum kam
Page |80 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIT0 [1]
Aruba sai ta yabi kishiyarta, ba ta taba fadan
cbunta ba, dolc ne ta shiga damuwa tunda sun zama
dava. ko ba komai kai ma kana da yaran, to dole ne
ka shiga damuwa don kana tunanin abinda ya faru da
dan wance kai ma fa ba wai kafi karfin hakan ya
יי
same ka ba ne, Allah Ya shirya mana amin.
Shirun da tayi, nayi tunanin tana jiran shawara
daga garé ni ne, sai na gyara muryata na cc, "Yar
uwa kema ai mai imani ce, don haka dole ne ki san
hanyar da za ki bi ki fadawa mahaifiyarsa abinda
ake ciki, sai kuma ku tashi tsaye ku nema masa
taimako kuma kuyi addu'ar Allah shi ne mai
shiryarwa ku kai masa kukanku zuwa garc Shi.
Amma kafin ki sanar da ita ina so kiyi hikima da
dabara da Allah yayi maki ki zauna da shi, ki fara
jawo shi a jiki. Na tabbata ba ya samun haka daga
mahaifiyarsa, saboda shi dan fari ne kin san
Bahaushen mutum da kawaici, duk yadda za ki yi ki
jawo shi zuwa gare ki, ki maida shi tamkar abokin
shawararki irin kin gane? Ki dai san yadda za ki yi
ki hada wata alaka ta musamman tsakaninku.
To ba mahaifiyarsa kadai ba, Allah ma yasan
abinda ki ka yi, don idan yaron nan ya shiryu
sanadinki to kin yi jihadi, kuma za ki daukaka a gun
iyayensa. Ina so ki cire son kai a zuciyarki, kiyi
saboda Allah ba wai don a biya ki a nan duniya ba,
a'a shi Allah yasan sakamakon da ya dace da ke.
Page | 81 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Kin san sau da yawa yanzu dan Adam yana abu
ne don a rama masa abun da yayin, saboda son kai
irin namu. Don haka nake ba wa dukkan mu mata
mu shawara mu aikata alheri ba wai don mutum dan
uwanmu ya maida mana ba, a'a sai don Allah Ya
biya mu. Allah Ya shirye mu amin."
Amina taji dadin shawarar da na bata. Ta се,
"Dama kuwa wallahi haka nake tunani a zuciyata,
duk da ban jawo shi a jiki ba, amma inshaa Allahu
haka zan yi. Zan yi kokari in yi hakan, Allah Ya
barmu tare Dayyiba, kin bani shawarar da ta dace
dani, Allah Ya barmu tare amin.
Bayan na koma gida ne, na iske Gwaggo cikin
tashin hankali, na isa gunta da sauri tana zaunc ne a
falo dirshan a kan kafet, idanunta jajir da alama kuka
tayi.
Na sassauta muryata na ce, "Gwaggo lafiya, me
ya faru? Ba ki da lafiya ne?"
Ajiyar zuciya tayi kafin tayi magana. Tayi
magana a sanyaye ta ce, "Jikata ce ta rasu." Na zare
ido na ce, "Kar dai Nana Asma'u?"
"Ita kuwa." Ta amsa min.
Tuni nima idona ya cika da kwalla ina fadin,
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un!". Don yarinyar
tana da shiga rai sosai, sau daya na taba ganinta, a
take kuma naso ta don kwarjininta...
Page | 82 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Gwaggo ta katse min tunanina. Ta ce min "Zan je
Abuja yanzu nasa a yanka min (Ticket) zuwa Abuja,
kafin su wuce Sokoto in yi musu gaisuwa."
A raina na so zuwa amma ban san dalilin da yasa
Gwaggo bata tsąra tafiyar dani ba, don haka dole na
hakura na zauna. Da karfe hudu da rabi na rakata
(Airport) suka wuce.
Mutuwar yarinyar nan ya shige ni ba kadan ba,
don ina bala'in son yarinyar. Sam bata biyo halin
iyayenta ba, ita daban ce.
Allah kadai yasan dalilin da ya dauke ta, gata ita
kadai ce gun iyayenta, wai su Turawa! To ta Allah
ba tasu ba, don gashi dai 'yar guda gudan ta tafi sai
suyi saurin neman wata, babu wanda zai iya
shiryawa kansa rayuwa sai Allah.
A ranar sukuku na yini, don wallahi mutuwar
yarinyar nan ya shige ni. Allah Ya jikan wadanda
suka riga mu, mu kuma Allah Yasa mu cika da kyau
da imani, amin suma amin.
Wannan (Semester) ta dan yi dadi saboda ta
zama kamar (Rivision) ce gare mu. Mun yi sati biyu
da hutu Aisha ta haihu, ta haifi namiji. A ranar muka
je mata barka, yaron sak Babansa. Ni dama ban
damu da daukar jariri ba don ba sha'anin yaro nakc
so ba, ko daukar ban iya ba. Sam babu ruwana da
yaro.
Page | 83 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Sau da yawa Baba nayi mın fadan hakan, ko
'ya'yan su Anti ba ruwana da su, kai ni fa duk
abinda zai zama aiki gare ni bana so.
Har da Gwaggo taje yiwa Aisha barka, a lokacin
take cewa "Aisha anya kuna wa kawarku fada ta
fidda miji tayi aure?."
"Wallahi muna yi Gwaggo, cewa tayi ita ba za ta
yi aure..."
Da saurina na rufe mata bakin ta kasa ida
maganarta, Amina ta caбe ta ce, "Da gaske ne
Gwaggo haka ta ce." Ai sai nayi tsuru-tsuru ina
rantse-rantse na rashin gaskiya, na ce "Kai don
Allah, karya fa babu kyau. Ai Gwaggon kin san
bana ce haka ba."
"Humn! Lallai da gaske ne wannan al'amari, da
Babanki ya fada min sam ban yarda ba. Menene
dalilinki na fadar irin wannan maganar da babu ko
dadin ji? To wallahi kiyi wa kanki fada, wannan ba
rayuwa ba се.
Tun a nan Gwaggo ke ta yi man fada, ni kuma na
rasa dalilin fadan, don dai rayuwata ce bana son
matsala. Da muka isa gida kuwa har daki ta same ni
ta ce, "Shin maganar nan da gaske ne ko wasa? Ni fa
ina so muyi magana 'yar kanwata."
Na turo baki na ce, "Gwaggo don Allah ki
taimaka min, so nake in gama karatuna kafin in yi
auren.
Page | 84 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
と
BAKI BIYU [1]
"Lallai kuwa yarinya da wasa ki ke, don yaron
nan ya ki aurenki shi ne za ki ce ba za kiyi aure
ba?".
"Ba haka ba ne Gwaggo, wallahi ni gani nake ba
zan iya rayuwar aure ba, shi ne kawai dalilina."
"Za ki iya mana, me zai hana ki yin rayuwar aure
ke kuwa? Lamarinki akwai ban mamaki,
shekaranjiya Babanki ya bugo yake fada min abinda
ya ji yayinki na fada, ashe da gaske ne? To da sake,
dole ne ki fidda miji kiyi aurc.
Ka ji min yarinya da shirme, in ba don aure ba za
ki zo duniya ne? To ki kiyaye ni bari ganin ina ba ki
goyon baya a al'amurranki, a gaskiya ba zan ba ki
goyon baya a maganar kin aure ba, sai ki canza
zanin dauri don wanda ki ka dauko bai dace da ke
ba." Fuuu! Ta fita daga dakin rai a басе.
Tunda nake a rayuwata da Gwaggo ban taba
ganin bacin ranta ba sai yau. Nan da nan hankalina
ya tashi, nabi bayanta muka isa falonta. Naje har
gabanta ina kuka na ban tausayi.
Na ce, "Gwaggo kiyi hakuri ba wai na ce ba zan
yi auren ba ne, sai dai ina tsoron da namiji da cin
amana ne, ni kuma a tunanina idan na zauna ba aure
sai in ga kamar zan fi şamun kwanciyar hankali."
"Wanne in kwanciyar hankali za ki samu a
duniya? Dama mun zo ne don mu samu kwanciyar
hankali? Duniya in ban da ibada me muka zo yi? So
Page | 85 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
ki ke a nuna mu mutuncinmu ya zubc, iye?
Tambayarki nake yi.
To bari kiji in fada miki, duniya ba wurin zama
ba ce, kin san yadda ki ke karatu don kiyi jarabawa
ki ci to haka muke a duniya, sam bata da dadi sai
wahala.
Idan ki ka yi ibada Allah zai saka miki 'yar
kanwata, ba ki burin ki samu gidan Aljanna ne
abinda kowa ke burin samu?"
Kuka nakce yi sosai saboda a gaskiya duk na
manta da hakan. Tabbas duniya jarabawa cc, kowa
abinda ya rubuta ita zai kwasa...
Gwaggo ta tsinka min tunanina ta cc, "Kiyi
tawali'u kiyi tawakkali ga Ubangiji Allah (S.W.A),
ki bashi rayuwarki, ki bauta masa kamar kina
ganinsa. Ki sani Allah yana biya wa bawansa
bukatunsa na alheri na mutum ya naka ko na sharri,
ki roki Allah bukatunki Shi zai biya miki
bukatarki."
Na sassauta kukana na ce, "Gwaggo kiyi hakuri,
wallahi a da da gaske ne matakin da na dauka, amma
yanzu na canza ra'ayina amma ina so ki taimaka min
Gwaggo in dan yi nisa da karatuna, ki tuna abinda
ya same ni a baya, ku dan bani lokaci in samu wanda
nake so ba don halina ba Gwaggo saboda Allah nake
rokonku Gwaggo."
Page | 86 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Ajiyar zuciya tayi ta ce, "Babu komai, amma da sharadi idan har ki ka ki fitar da miji duk matakin da
muka daukar miki za ki amincе."
Shiru nayi na ce, "A'ah Gwaggo ni dai ku bani lokaci in samu wanda nake so don Allah.”
Marairaicewa nayi sosai don Gwaggo ta tausaya
min, kallona take yi sai ka ce yau ta fara ganina,
amma ba ta ce min hanzil ba ta mike ta ce, "Allah
Ya bada sa'a."
Murna, nayi sosai sannan na wuce dakina ina
tunanin ta inda zan fara, ko fuska bana bayarwa, sau
da yawa an sha tare ni amma ko ci kanka bana ce
maka, haka za kai ta zancenka ni dai nawa ido, kai
ke kidinka kai ke rawarka, zagina ko su koma yi min
habaici, ni dai nawa ido.
Don na dauki maza dukkansu al'amarinsu daya
ne, duk labarin da ma suke badawa daya ne. To don
mene zan ansa su in batawa kaina lokaci in yi asarar
yawuna. A da nayi wannan yanzu kam nima gwana
ce gun iya takuna, in dai a harkar namiji ne.
Haka dai iyayena suka hakura da maganar auren
naci gaba da zuwa Makarantata, hankalina kwance
zuciyata zaune. Haka kuma lokaci yake ta tafiya, gashi har na shiga (Two Hundred Level), kannena
da suka yi aure abin kamar hadin baki tare suka
haihu, kwana biyu ne tsakaninsu.
Page | 87 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Ikon Allah sai kallo! Baki dayanmu muka hallara
a Gusau, dukkanmu mun hadu. Na lura Baba da
Babah ba karamin farin ciki suka yi ba, gashi
iyayenmu sun yi iyakar kokarinsu nima a wannan
lokacin na dan tabuka wani abun, na sai wa Babah
turmin atamfa da turare shima Baba shadda ce na
saya masa da turaren, sosai suka yi godiya, don
gaskiya ban taba yin hakan ba, abinda ya kara sa na
saki jikina sam ba ayi min zancen aure ba.
Sun kauda kai, sai dai Anti Fiddausi da take cikin
damuwa, don kishiyarta zata dawo gidan, hankalinta
ya tashi sosai. Fada Babah take yi mata a kan kada
tasa ma kanta damuwa, gata da juna biyu. A raina na
ce, Su Anti kenan! ita ko dan (Planning) din nan da
ma'aurata ke yi yanzu bata yi ba, ni kam ai yara biyu
sun ishe ni zaman rayuwa ba don komai ba sai don
bana son wahala.
Ni ban ki ba ma idan nayi aure in shekara bakwai
kafin in haihu ba... Baba ta katse min tunani da ta
ce.
"Ke Dayyiba dauki Ikram ki wanke mata kashi."
Na bata fuska sosai na cc, "Kai Babah!". Nayi
magana cike da kyama, na ce "Wallahi ni fa wankin
kashin nan amai yake sa ni."
Duk wanda ke cikin dakin dariya yayi, suna min
tsiya. Ni dai a kan bakana nake, ba zan wanke
kashinnan ba. Babah kam abin itama dariya ya bata.
Page | 88 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
こ
BAKI BIYU [1]
Ta ce, "Yarinya za ki gane kema ai kina kan hanya.'
Daga karshe dai ita ta tashi ta wanke wa takwararta
kashin, sunansu dama daya amma ake kiran yarinyar
Ikram.
Da muka dawo (Second Semester) abun mamaki
na dawo gida sai na iske Rahma, ba idona kadai na
saki ba har da baki da hanci, ina kallonta. Abin
mamaki ko digon bakin ciki ban ji a raina ba, sai ma
naji dadin ganin nata, da alama ciki ne ma da ita.
Ta rame sosai, gashi tayi duhu. Na karasa inda
take na ce, "A'a su Rahma manya! Saukar yaushe?".
Na zauna dab da ita, sai na hango kwanciyar kwalla
a idaniyarta.
Jikina yayi sanyi, nasan ba komai ya kawo ta ba
illa ta bani hakurin abinda ya faru, tuni har ta fashe
da kuka. Na dan kai hannuna a bayan da yake ta
duka kan cinyarta ina lallashinta a hankali.
Na ce, "Haba Rahma, nasan dalilin kukanki, kada
ki damu dama haka nan Allah Ya shirya, kin san fa
dukkan dan Adam tara yake bai taba cika na goma,
don haka ki kwantar da hankalinki, ni ya riga da ya
wuce a guna, don dama matar mutum kabarinsa."
Ta dago idonta da yayi jajir ta ce, "Dayyiba ban
isa in ce ki yafe min ba saboda ni nasan naci amana
ce, don abinda nayi maki nasan ba za ki taba
yafe..."
Page | 89 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1]
Nayi saurin katseta na ce, "Haba Rahma, na fa
gaya miki ni ya wuce a guna, na kuma yadda da
kaddara, inda Allah Ya yi ni matar Sa'id ce da
komai rintsi duk wuya zan aure shi, to da yake ni ba
matarsa ba ce ba zai taba faruwa ba."
Ta sassauta kukanta ta ce, "Kin san Sa'id ya sake
ni!" Gabana yayi bala'in bugawa, nan da nan
idanuna suka yi ja na ce ina girgiza kaina.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un! Me ya yi zafi
haka 'yar uwa? Wallahi a raina nayi bakin cikin
wannan lamari, sam bana son in ga ko in ji kalmar
saki ga 'yan yara mata. Dududu auren yaushe aka yi
shi, yafi wata goma kuwa? Na rasa dalilin da yasa
yanzu saki ta zama abun wasa, a arewa ko menene
dalili oho! Sai ga anyi aure har ma akwai 'yan wata
biyu to Allah Ya shirye su ya ganar da su.
Koda yake sau da yawa ba a nan take ba, irin
yadda ka daukar wa kanka tun farkon haduwarku shi
ne ke gabatar da irin rayuwar auren da zaku yi, tun
faro sai ka ga namijin da na macen dama ba don
Allah za suka auri juna ba. Ko shi ne ke son samun
wani abu daga gun iyayenta ko kuma ita yarinyar
dama tana sonsa ne don kudin da yake da shi.
To dole ne a samu matsala tunda ba son juna
suke yi ba saboda Allah sai don wani biyan bukatar
mai shi...ta tsinka min tunanina da naji ta ce,
"Dayyiba tun farko wallahi bani na kawo shawarar
Page | 90 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1]
auren ba, shi Sa'id din ne yazo ya same ni ya ce shi
ya ji ya gani muyi aure, dama ai shi ba sonki yake yi
ba, yana tare da ke ne kawai amma dama shi a
matsayin abokiya ya ajiye ki, ba wadda zai aura ba,
shi ne yake sona tun ranar da ya aza idonsa a kaina,
na ce dashi to ya za mu yi da ke don ni na san ke
kam sonsa ki ke yi.
Ya nuna mini ai sam ba hakan ba ne, to a gaskiya
tun ranar da ki ka kawo shi guna I have a sexual
fantasy on him, ko in ce I had a crush on him shi
yasa idona tuni ya rufe na amince da bukatarsa..."
Nayi saurin katseta na ce, "Kadda fa ki damu ya
riga ya wuce a guna, sai dai a tari gaba. Sannan
Allah Ya ba mu wadanda za mu zauna da su."
"Na gode da addu'arki 'yar uwa, bari in tashi in
tafi dare ya soma yi." Na ce "Gaskiya kam, don har
shida ta wuce, zan zo jibi inshaa Allahu." Nayi shiru
ina tunani, muka soma tafiya har bakin (Gate) din gidanmu, sannan na dubeta na riko hannunta cike da
fara'a na ce da ita. "A gaskiya Rahma kiyi hakuri,
amma ba sai kin kara zuwa ba, don na riga nayi ma
kaina wasu sharuda na musamman, don haka nake
fatan alheri tsakaninmu, sannan tabbas wata rana ko
ba jima ko ba dade zamu iya haduwa zan yi kokari
mu gaisa, don Allah kiyi hakuri idan na bata
maki..."
Page | 91 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Ta rike ni gam ta ce, "Babu komai, na fahimce ki
saboda hakan shi ne daidai da mai irin halina sosai
na gano kuskurena, kuma naji dadin yadda ki ka yi
min, don haka nake yi miki fatan alheri nima, sai
mun hadu."
Ta wuce nima na shigo cikin gida ina tunanin
rashin imani irin na da namiji, shin wai me ke sa
muke yin kuskure ne gun fidda gwani? A lokacin na
kara bala'in tsanar da namiji a raina.
Ni nasan mu ma muna da laifi sosai, to amma ai
hankalin namiji da na mace ba a hada shi, me yasa
namiji ke biye wa mace ne har a rika wulakanta su?
Allah Ya ganar damu hanya madaidaiciya baki
dayanmu, amin.
Naje ina ba Gwaggo labari, ta ce ai da farko
korarta naso in yi sai dai na kyaleta.
"Bata fada miki dalilin sakinta da aka yi ba?".
"Gwaggo ni na hana in ji, ni na gaji da jin
matsalar da namiji. Saboda wallahi Gwaggo na tsani
namiji saboda halinsu."
"Kin ji ki fa! An fada miki duka aka taru aka
zama daya? Ko mu mata haka ba shaidanu ba nc, ko
ko shekaran jiya ba ki ji wadda ta kashe mijinta ba
ne?".
Na zare idona na ce, "Gwaggo mace ta kashe
mijinta?". Nayi tambayar cike da mamaki. "Ki rika
sauraren gari ya waye a Alheri Radiyo ko ki kalla a
4
Page | 92 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
D.I.T.V za ki sha kallon abubuwa iri-iri na tsoro da
na ban mamaki, Allah ya tsare mu daga sharrin
zuciyoyinmu amin.
Abin ba wuya dama sai in ba ka shiga ba, gashi
muna (Three Hundred Level). Na dawo daga
Makaranta na shigo gidan duk na gaji, yunwa ma
nake ji sai da na shiga daki nayi wankan nayi sallar
La'asar, sannan na fito na wuce dakin Gwaggo don
da na dawo ba mu hadu ba.
Ina dosar dakinta da alama waya take yi, naji
tana ta faman bada hakuri, sai na saurara in ji da
wanda take yi, Babana ne. Naji kuma tana cewa,
"Nima na bada hadin kan hakan."
"Yayi daidai, Allah Yasa