tura (Text) shi ma shiru.
Ina tare da Anti Badiyya ina fada mata halin da
nake ciki.
"Anti ya zan yi? Ni gaskiya Sa'id nake so, ya zan
yi tunda muka yi waya kwana bakwai da suka wuce
a kan ya turo in ya shirya saboda iyaycna sun fara
min zancen aure, wallahi Anti har gaya min yayi
shima dama iyayensa suna so yayi auren, don haka
ba matsala ba ce zai yi kokari ya turo, to tun lokacin
bana samun wayarsa. Wayyo Allahna Anti, ya ya
zan yi?".
Ta dafa min kafaduna ta ce, "Anya Dayyiba
Sa'id zai aure ki kuwa?".
Da sauri na dube ta na ce, "Don me ki ka ce haka
Anti?" Ta ce, "Saboda a gaskiya yadda ki ka bani
labarin halin da ku ke ciki, to Allah kadai Ya sani,
amma da alama akwai yaudara a al'amarinsa."
Tunda Anti ta soma magana gabana ya soma
faduwa, don ni ban taba kawo tunanin yaudara
tsakanina da Sa'id ba. Anti ta katse min tunanina.
Тa сe, "Ya kamata ki kwantar da hankalinki gu
daya, kiyi tunani a kan Sa'id, saboda a gaskiya ni dai
Page | 56 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1}
kin san ban taba ganinsa ba, sai dai yadda ki ke bani
labarinsa ina zarginsa."
"A'a Anti, Sa'id ba zai yi min haka ba, kin san
yadda yake kuwa? Yana da alkawari, ko abu yayi
min alkawari sau da yawa ina mantawa, sai dai in ga
ya kawo min shi..."
"To ai sai kiyi, ni dai shawara ce na baki kiyi
kuma tunani a kai."
Ta mike tana dauke da tsohon cikinta, na kuwa
tsurawa cikin ido don na lura tunda cikin ya samu,
Anti Badiyya ta koma mai fada, don haka na tashi na
dauki 'yar jakata na bar mata gidanta.
Gidan su Aisha na wuce na iske ta ita ma laulayi
ya sa ta gaba, sai amai take yi. Na tsuguna gefenta
ina yi mata sannu. Ta rike kan famfon da ke gabanta
tana wanke bakinta, na taimaka mata muka shiga
cikin falonta, na zo da niyyar muyi magana amma
dole na kyale ta saboda bata da lafiya, ni nayi mata
abinci kafin in koma gida.
A falo na sami Gwaggo Hauwa zaune tana duba
wata (News Paper), na karasa kusa da ita na zauna
tare da gaida ta. Ta amsa cike da fara'a.
"Yar kanwata kin dawo?".
"Eh, na dawo Gwaggo. Ya gida?".
"Lafiya kalau. Yau fa Babanki ya kira batun turo
wanda ya ce kiyi sati biyun da ya diba maki ya cika,
wai me ke faruwa ne?".
Page | 57 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1)
Na tsuke bakina cike da shagwaba, na ce,
"Gwaggo kin san fa yadda aikin 'yan Banki yake, sai
ana ta kokarin son ya zo sai dai aiki ne yayi masa
yawa...
Gwaggo ta amshe maganar.
"Shi ya fada maki aiki ne ya hana shi zuwa?".
Na dan yi shiru da kamar in yi karya, sai kuma
na kasa na ce, "A'a."
"To kin yi min shiru, ba ki san da yaron nan bai
da niyyar turowa, ba ki san dama ina hake da shi ba.
Tun yaushe ku ke tare da shi, ya taba shigowa ya
gaida ni? Sai dai mu gaisa idan na hadu da shi waje.
Don haka na san akwai matsala.
Yau shekararku nawa tarc? Kusan uku har da
rabi amma bai taba shigowa cikin gidannan ba,
kema ba ki taba tunanin ce masa ya shigo ciki mu
gaisa ba, da yake ba ki da hankali."
Sai a lokacin na soma tunani kala-kala. Anya ni
wace irin sakarai ce da nayi sakaci haka? To amma
ai ni ban yi tsammanin wani abu ba ne don bai shiga
gida an gaisa da shi ba, a tunanina gaisawar da suke
yi a waje ma ya wadatar.
To me yasa kowa yake masa shaidar mayaudari?
Ni kuwa sai naga ma wani sonsa ya karu a zuciyata,
saboda a ganina dabara ce ya yi wa 'yan uwana na
rashin bayyanar da halinsa, saboda ni nasan Sa'id
Page | 58 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
mutum ne adali, yana da natsuwa ga hankali da sanin
ya kamata..."
Gwaggo ta tsinka min tunanina da naji ta ce, "Тo
Mal. Sabi'u dai ya bani sako in ba ki, ya ce ya kara
miki sati biyu, idan yaronnan ya ki fitowa to zai yi
miki miji, nima hakan yayi min sai ki shirya.
Nayi murmushi na gamsuwa da tunanina, na zan
basu mamaki inshaa Allahu Sa'id ne mijina.
Ikon Allah! har na kara kwana hudu tun lokacin
da muka yi magana da Gwaggo, amma ban samu
Sa'id a waya ba, abun ya fara bani tsoro a dan
wannan lokacin kuwa har na fada.
Washegari muna Makaranta tare da Rahma take
ce min, an saka mata rana nan da wata daya. Abin ya
bani mamaki, sai dai ban nuna ba. Ban yi tsammanin
Rahma ta tashi aure ba, don ko zancen bata yi.
Sosai na nuna mata farin cikina, ni kuma na
kwashe duk yadda ake ciki da Sa'id na fada mata.
Ta tabe baki ta ce, "Allah Yasa ba yaudararki yake
yi ba, nima dai tun bana yadda da hakan har na soma
yarda.
Wayata ta ke (Ringing) na dauka ba tare da sanin
mai lambar ba, na kara a kunne na ce;
"Hello!" Sai naji muryar Sa'id.
Tuni na mike har jakata ta fadi, ban damu ba sai
na soma yi masa surutu.
Page | 59 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
"Haba Sa'id, lafiya kwana biyu ina ta nemanka
amma shiru, me ke faruwa ne? wai ka san halin da
ka jefa ni saboda rashin magana da kai na kusan sati
uku? Haba Sa'id!".
Daga can yake cewa, "To ki bari in yi magana
mana, ko gaisawa ba ki bari muyi ba. Ya ki ke? Ya
makaranta?".
Ban amsa ba, don tuni raina ya soma baci. Naci
gaba da magana.
"Sa'id so ka ke yi ka yaudare ni kamar yadda
mutane ke fadi?".
Yadda naji yayi shiru nasan tambayata tazo masa
a ba zata, sai da ya dau lokaci sannan ya ce min.
"Kiyi hakuri Dayyiba, ba ni da niyyar hakan,
amma...
"Bangane ba ka da niyyar menene ba? Haba
Sa'id!, ka bani mamaki. Kai ka sani ba wanda nake
so nake kuma bukata a wannan lokacin sai kai, don
me sai da abu ya kawo karshe ka ke son gasa min
gyada a hannu? Tun ina kawaici bana son in yi
magana har ka kai ni bango? Yanzu dai ina son jin
magana ta karshe, yaushe za ka turo saboda gida fa
suna son ganin magabatanka."
Bai jira wani abu ba ya ce, "Ranar sati suna nan
zuwa." Yana fadin haka duk wani bakin cikina ya
washe, nan da nan na sauke wata ajiyar zuciya. Na
Page | 60 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
tabbata shima ya ji sannan kuma a take hankalina ya
dawo jikina...
"Kina ji na Dayyia? Ranar sat..."
Wayar ta tsinke, sam ban damu da katsewar
wayar ba. Da murnata na isa gun (waggo na
rungume ta ina dariya. Ta ce, "Ni sakanni don Allah
kada ki kada ni, ke har yanzu da.. hankalin nan da
'yanmata ke yi ba ki yi ba, a kullum rawar kanki
karuwa yake."
Na ce, "Kai Gwaggo, in ban yi maki ba wa zan yi
wa? Na zo maki da albishir ne sai ku shirya ranar
Asabar magabatan Sa'id suna nan zuwa.
Gwaggo ta washe baki, farin ciki ne ya shige ta.
Та сe, "Тo Allah Ya kai mu, har naji dadi wallahi ba
ki ga yadda na damu ba."
"Kai Gwaggo, duk damuwarki har kin kai ni?".
"To uwar marasa kunya, za ki fara?".
Na rufe fuskata ina dariya.
Tun sadda muka yi magana da Sa'id, har gashi
yau Monday (Litinin) bai zo ba, bai kira ba, sannan
babu magabatansa, wayarsa ma bata shiga kwatakwata.
Tun ranar Lahadi dariya a fuskata ta kau, a lokaci
daya kuma na rame sai ka ce wadda aka tsotse.
Gwaggo kam don takaici magana ma ta kasa yi min;
gashi tana tausaya min, ita ba komai ya kona mata
rai ba sai irin shirin abinci da kuma gayyato
Page | 61 MARUBUCIYA: Sameera Mustaphs
BAKI BIYU [1]
Kawunnaina da tayi musamman suka zo daga
Gusau, haka suka koma babu karfin gwiwa.
Ni kam na rasa abinda ke min dadi, a ranar ma
Rahma tazo gidan ta ce muje kasuwa mu fidda
ankonta. Dolena naje ba don ina so ba.
Ita ta lura da yanayina, har muka yi maganar.
Sam hankalina ba ya tare dani, ba komai nake tunani
ba sai irin yadda nasa son Sa'id a raina da har
bangane mayaudari ba ne.
Tun daga lokacin ko abincin kwarai bana iya ci,
gashi Rahma taki kyale ni ta ce, ni ce babbar
Kawarta. Don haka dole nake biye mata ya zan yi. Ni
ba abinda ya fi tayar min da hankali irin yadda naji
Baba yayi shiru bai ce komai ba, shi kenan nasan
auren dole za ayi min.
Tun ina jiran wayar Sa'id har na saduda na
hakura, nemansa ma da nake yi dole na bari.
Cikin sati daya tal na zabge na rame sosai kai ka
ce mai maleriya da yaci ya cinye. Abincin gabaki
daya ya zama madaci a bakina, sai dai in sha abu
mai ruwa-ruwa, gaba ki daya na lalace.
Tun Gwaggo na kauda ido dole ta dawo tana
lallashina, ba abinda nake ciki sai zurfin tunani,
gashi har saura kwana biyar a fara bikin Rahma, na
shirya kayana zan je gidan Gwaggo ta ce, a'a sai dai
in rika zuwa ina dawowa. Na dai roke ta na nuna
Page | 62 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1]
mata ni ce mai gabatar da yawancin abubuwan
bukata.
An daura aurc ranar Juma'a, da daddare za a yi
(Dinner). Ikon Allah! kayan da zan saka ranar suna
gun dinki ba a gama ba, ga shi ban sami dama naje
karbowa ba sai bayan Magariba. Na isa gurin mai
dinki shi kuma ya kai min wai gida da yaga ban je
karba ba, don haka sai na kama hanyar gida.
Kawai nayi niyar shiryawa a gida tunda lokaci ya
riga yayi, koda na isa ma tuni an cika. A (High
Table) idona ya ganc min abinda bangane ba, Sa'id
ne zaune a gefen Rahma a daidai lokacin kuma naji
ana jawabin cewa ango da amarya su taso yanka
(Cake).
Abin mamaki, Sa'id ne da Rahma suka mike
suka isa gun (Cake) din, matar da take jawabi ita
tayi (Cake) din, don haka ita take ba da umarnin
yadda yankan zai kasance, matar ta ce in tayi
(Spelling) din (Love) sai su yanka.
Tabbas abinda matar ta tsara abin sha'awa ne ga
Jama'a, amma ni haka na rika tafiya a hankali idona
da bakina, kunnena har da hancina duk a bude suke.
Wallahi ban san lokacin da na isa gabansu ba, ina
kallon ikon Allah.
Jikina kuwa rawa yake yi, take kuma idona ya
cika da kwalla, fuskata tuni ta lalace da hawaye, sai
Page | 63 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
ajiyar zuciya nake ina bala'in tausayawa kaina,
zuciyata kuwa kamar zata fita saboda yadda take
bugawa, yawun bakina ya bushe.
Sam ban ji abinda mai jawabin ke magana a kai
ba.
"Don Allah 'yammata kije ki samu wuri ki
zauna, Ango da Amarya kuma su koma wurin
zamansu.
Ban iya matsawa daga inda nake ba, ina nan dai
tsayc a inda nake, jikina sai rawa yake yi, suma
kansu sun kasa tafiya sun yi tsaye suna kallona.
Can dai ban san abin da ya canza min shawara
ba, na juya na bar wurin da saurin gaske. Da na
karasa waje kuwa da gudu na karasa tsakiya wurin
na rika wani irin kuka mai sauti.
Ni dai ban san yadda aka yi ba, fitilar mota na
gani a gabana mai tsananin hasken gaske, ji kawai
nayi an buge ni gabb! Ka ke ji, daga nan ai ban kara
sanin inda nake bа.
Ina bude ido, abin mamaki a dakina na ganni. Da
sauri na duba jikina, ba ciwon komai a tare da ni, sai
na zauna a bakin gado da na fara tunanin ko mafarki
nake yi? har na soma kyakyatar dariya ina yi wa
Allah godiya.
Tuni zuciyata ta nemi daukewa da naga kayan da
na saka ranar dinar Rahma, na mike na nufi inda
Page | 64 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
kayan suke sai naji an taba kofar dakina, Gwaggo се
rike da kayan abinci.
"Alhamdulillahi, kin tashi?" Ta fada cike da
sakin fuska. Ta ajiye abincin ta riko hannuna muka
zauna bakin gado. Ta dube ni cike da kulawa.
"Ya jiki? Ba inda ke miki ciwo ko?" Na saki
idona ina kallonta. Na ce. "Gwaggo me ya same ni
hala?" Ajiyar zuciya tayi. Nan da nan kuma idonta
ya sauya zuwa bacin rai. Ta dai daure ta ce da ni.
"Ci abincin tukunna sai in fada miki..."
Na katseta, "Gwaggo kar dai da gaske ne Rahma
ta aure min miji...?" Kuka ya subuce min. Ta се,
"Haba dai! Yaushe ya zama mijinki?".
"Dama ba mafarki ba ne?" Na fadi hakan ina
kuka mai sauti.
"Haba 'yar kanwata, hakuri za kiyi kin san fa shi
mutum ba ya auren wanda ba nashi ba, Allah bai
kaddara Sa'id mijinki ba ne, shi yasa ya sauya al'amarin."
"Amma Gwaggo sun ci amanata su dukkan su,
koda wasa ba su taba nuna min akwai wata alaka
tsakaninsu ba, daga ita har Sa'id Allah Ya isa ban
yafe ba."
"Haba Dayyiba, ba ki san haka shi yafi zama
alheri ba? Duk abinda ki ka ga ya sami dan Adam, to
jarabawa ce a gare shi, kuma a karshe ya zama
alheri. Don haka ina so ki kaiwa Allah (S.W.T)
Page | 65 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
kukanki, Allah Shi zai biya miki bukatarki, kin ji
'yar kanwata! Kiyi hakuri tabbas ba mafarki ki ke yi
ba haka dinne, Rahma ta auri Sa'id, sai dai ina so ki
daurc ki kuma cije ki sa Allah gaba...
Na katse ta, "Allah sai Ya saka min tsakanina da
su, Gwaggo sun ci amanata. Ya zan yi da zuciyata da
take tashen son Sa'id? Shi nake so Gwaggo, don me
zai yi min haka? Don me ya 6oye min halinsa? Na
shiga uku Gwaggo ya ya zan yi da son Sa'id?
Gwaggo a ruhina fa yake.
Kaicona Gwaggo, dama wannan abu ba gaskiya
ba ne, dama mafarkin ne dai Gwaggo...?"
Gwaggo a katse ni da fadin.
"Wai Dayyiba ba ki ji abinda na fada miki ba? ba
ki san a rayuwarka baki daya Allah Ya shirya maka
ita ba? Ki dauka wannan abu kaddara ce." Ta tallabo
fuskata ta ci gaba da cewa.
"Karamin misali ma kaina shi ne, Allah Ya
shirya min rashin haihuwa na kuma hakura, ba wai
don bana so ba a'a, sai don na riga na yadda kuma
na amince haka Allah ya shirya min rayuwata."
Da sauri na rungume Gwaggo don kam haka
maganar take. Tun ranar gini tun ran zane, Allah Shi
ke shiryawa kowa rayuwarsa. Ji nayi nawa ma ba
komai ba ne, na Gwaggo shi ne babban abin
dubawa. A wannan dare da kyar na iya bacci, tare
muka kwana da Gwaggo a ranar. Washegari idona
Page | 66 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1]
kamar za su fadi don sun kumbura sosai, ina daki ba
inda najc, ko nan da kofar daki ban leka ba. Tunda
nayi sallah na koma kan gadona na kwanta naci gaba
da kokc-kokena, gani nake kamar ba zan iya hakura
da Sa'id ba, zuciyata shawara take bani a kan in san
yadda zan yi in auri Sa'id, ko don in rama
wulakancin da Rahma tayi min. Da wannan tunanin
bacci ya dauke ni.
Da na bude idona Aisha da Amina na gani a
gabana, ban san lokacin da na farke da kuka mai
ban tausayi ba. Tuni suma suka taya ni da kwalla.
Na dauki lokaci mai tsawo ina kuka kafin na
sassauta.
Suna ta lallashina tare da fada min maganganu na
kwantar da hankali, Amina ta debo abinci ta bani, ko kamshin abincin bana so, ai sai na fara yunkurin
amai. Sai da nayi aman kumallo saboda babu komai
a cikina.
Haba, nan-da-nan zazzabi ya shige ni. Na koma
na kwanta, ga wani irin ciwon kai na damuna, a
raina cewa nake yi dama in mutu da in yi rai, zuciyata suya take yi kamar an diba ruwan wuta an saka min.
Kai Allah Ya raba ka da (So) kalmar ita kanta
abin tsoro ce a gare ni, tabbas na yadda so na kisa. Daga jiya zuwa yau son Sa'id karuwa kawai yake yi
a raina, ni nasan halina ban iya son abu ba..."
Page 67 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Gwaggo ta tsinka min tunani da ta aza hannunta
akan goshina.
"A'a jikin da zafi sosai. Amina taya ni rike ta
muje asibiti, da mota ku ke ko?".
"Eh, muje Gwaggo mu kai ta".
Dolc aka kwantar da ni saboda da aka duba ni an
gano ma har da (Thypoid) dina ya tashi, ai tuni aka
sa min ruwa, ban san lokacin da su Aisha suka tafi
ba, don an yi min allurai gashi dama baccin baya
isata.
Gwaggo ce a gefena ta cc, "Sannu 'yar kanwata,
Allah Ya baki lafiya. Za ki ci abinci?" Na girgiza
kaina, ma'ana a'a. Ta ce, "To ga (Juice) ki sha."
"Dayyiba ki ci wani abu kada ki ba kanki
wahala."
A lokacin Alh. Shehu ya shigo ya zauna yana yi
min sannu, sai can cikin dare sannan ya wuce gida
tare da Gwaggo muka kwana.
Kwana biyu nayi ina fama da kaina har da allurar
jijiya ake min, a kalla sai da na samu kwana bakwai
a asibiti, a kullum kuwa sai Anty Badiya ta zo ta
kawo min abinci da kayan marmari. Sai da suka
tabbatar da na samu lafiya sannan aka sallame ni na
koma gida.
Kallo daya za ka yi min ka ji na baka tausayi,
kamannina baki daya ya canza, duk haskena ya
Page | 68 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
2
BAKI BIYU [1]
dishe, idona kuwa sun koma kamar tsokar nama don
tsananin kukan da suka sha.
Na kara kwana hudu Gwaggo ta shirya mana
tafiya zuwa Gusau, hakan yayi min dadi, ko ba
komai ina son in san matsayina gun Babana, ina son
in san hukuncin da ya yanke min. Da yake mun tashi
da wuri, karfe goma da rao: muna tare da su Baba
Mairo.
Na gani a cikin kwayar idona ta tausaya min da
sam bata nuna min wani abu ba, Baba ma da ya
shigo sai da ya ji tsoro. Ya kura min ido ya ce,
"Dayyiba ki kwantar da hankalinki, Allah ne bai
kaddara shi mijinki ba ne, kin san fa ita matar
mutum kabarinsa." Tuni nakc kuka na kara
tausayawa kaina.
Ban yi zaton Baba zai sauko ba, amma abin
mamaki sai cewa ya yi zai kyale ni ayi auren su
Zaliha tukuna, in yaso daga baya sai a san abin yi.
Gwaggo ta ce, "Haka shi ne daidai Malam Sabi'u,
Allah Ya ji da mu alheri."
Gwaggo ta wuce ta bar ni nan Gusau, yadda
iyayena ke yin nan-nan da ni shi yasa na dan sakí
jikina har nake cin abinci, sosai Baba ke kula dani,
komai za ka ji ta ce a kai min in ci. Sai dai fa daga
(Smiley) na koma (Bonny), don yawan dariyata na
daina, shisshigina da rawar kai ma na daina, sai kaje
Page | 69 AMARUBUCIYA: Sameera Musta
BAKI BIYU [1]
gidanmu ka wuni baka sani a ido ba, in har baka leka
dakina ba, sosai na canza na zama shiru-shiru.
A kowace safiya zan tashi in shiga dakin Baba da
Babah in gyara masu, to in na gama na shiga daki
kuwa ba ka sake ganina ko a tsakar gida sai ko ma
washegari sai kuma in ya zama dolen dolc.
Babah kuwa sam bata matsa min, a kullum dai
zata dan leko ta ce, "Kin ko ci abinci? Kin ci
wancan kin ci wannan?". Irc-iren haka dai, duk wata
kula na musamman na same shi a gun iyaycna, sai
hamdala.
Duk wani shirye-shirye na auren su Maimuna
tare muke yi da Babah, tare muke zuwa kasuwa mu
sayi kaya, nasan Babah tana yi min haka ne don in
saki jikina, ni kuma na rika yin kokarin danne
damuwata.
Ana saura kwana biyar a fara biki, gidanmu ya
soma cika da mutane. Su Anti Fiddausi da Badiyya
ba karamin kokari suka yi ba, don kayan kicin suka
yi masu, babu abinda ba su saya ba sai abinda ba a
rasa ba.
Ita kuwa Anti Nafisa (Electronics) ta saya ita ta
saya musu ma firij (Medium size), abin sai wanda ya
gani, 'ya'ya kam sun yi albarka, Allah Ya ba su
masu yi musu suma.
Ba su tsaya a nan ba, duk kusan abincin da za a
ci a bikin su suka tanadar dashi, mijin Fiddausi kuwa
Page | 70 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
har da gudunmuwa ya aiko wa Baba na dubu dari
uku.
A gaskiya Allah Ya rufa mana asiri, shi yasa
komai ya zo mana da sauki. Ni kam na sha kuka ni
kadai a bayi, don a ganina nima ya kamata in zama
daya daga cikin ma su yin wannan hidimar, sai dai
ni ban sani ba ko ni zakka zan zama a cikinsu, sai da
nayi mai isa ta sannan na fito muka zauna baki
dayanmu muna hira.
Faisal dan Anti Fidduasi ya yi wayo, 'ya'yan
Anti Nafiša su biyu nc, naga kuma ciki ne a gabanta.
Ita kuwa da Anti Badiyya sai faman jan ciki take yi,
cikin ya girma da yawa. Naji ta ce ma sun shirya ba
zata koma ba sai bayan arba'in.
Haka biki ya soma gwanin sha'awa. Ranar sati
aka daura auren su Zalihat da Nura, sai Maimuna da
Nasiru, a ranar aka yi walima da yamma. Amaren
sun yi kyau sosai, da daddare aka kai su gidajen
mazansu, su duka a nan Gusau suka tare.
Bayan biki da kwana biyu an watse ni da su Anti
muka je gidan Anti Nafisa, kafin mu isa tasa an
shirya mana abinci da ya ke itama a gaskiya mijinta
yana da abin hannu, yanzu haka a Abuja yake, amma
Karkashin (Nepa) dai ya ke, sai dai girman da aka
kara mashi. Ina daga kwance naji Anti Badiyya ta
cc, "Anti Nafisa ni kuwa ina son muyi wata magana,
Allah Yasa za ki iya taimaka min.
a
Page | 71 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Anti Nafisa ta ce, "Amin 'yar uwata. Mece cс
matsalar?"
"Anti, Sahabi (mijinta) shi ne, wallahi na soma
gajiya da halinsa."
"Wanne irin hali?" Anti Nafisa ta tambaya cike
da kulawa da maida hankalinta sosai ga Badiyya.
Nima bude kunnuwa nayi ina saurare, sai dai nayi
kamar T.V nakc kallo.
Ta ce, "Anti, Sahabi in ban da harkar 'yanmata
babu abinda yasa a gaba, babu abinda yafi damuna
irin idan ya fita tun safe ba ya dawowa sai karfe
shidda na yamma. Wallahi yana idar da sallar
Magriba kamar ina korarsa, za ki ga ya ci gayu daga
gani ka san inda za shi, duk da ban shaida ba, amma
irin (Text) din da nake gani a cikin wayarsa su suka
fi tayar min da hankali, gani bana iya gani in kyale
dole ne in ya shiga wanka sai na dauki wayarsa na
duba..."
Ko kafin ta gama idonta ya ciko da kwalla. Sai
da tayi ajiyar zuciya sannan ta ci gaba da cewa,
"Anti na gaji da halin nan nasa, na gaji ya ya zan
yi?".
Riko hannuwanta Anti Nafisa tayi ta ce, "Tabbas
a wannan lokacin mu mata muna fuskantar wannan
matsalar, to amma bari in fada maki kalma daya da
nasan ta ishe ki tunani, sannan ita ce kadai abun da
zan iya fada miki, kuma inshaa Allahu ita kadai ce
Page | 72 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
hanya in dai kin kula, kuma ki ka yi amfani da ita.
ita ce hakuri..."
Anti Fiddausi ta katseta, ta ce "Anti nima fa
matsalar da ke damuna kenan, duk da shi Mukhtar
ba ya fitar dare, don shi yana son yin bacci da wuri,
yana yin sallar Isha'i zai je ya kwanta, amma nima
ina cin karo da irc-iren (Text) a wayarsa.
Sau da yawa kuma suna kiransa ni nake amsawa,
idan na tambaye shi sai ya ce me yasa ban tambaye
su ba? wannan maganar ko kalma ba karamin bata
min rai yake yi ba, sannan kun san ya taba aure suka
rabu da matar, to wannan matar na gaji da abinda
take yi min, kun san tun safe zata yo masa (Text)
wai tana yi masa barka da asuba, sannan kuma ta
kira shi su sha hirarsu. Abin takaici wata rana ma
(Speaker) yake budewa ina jin duk irin hirar da suke
yi.
"To ai ke gara ke Badiyya tunda ba ya hira da su
a gabanki, me yafi takaici irin a rika hira gabanka?".
Ajiyar zuciya Anti Nafisa tayi, ta ce, "A gaskiya
a wannan zamanin mata da maza baki daya muna
fuskantar matsalolin aure, saboda rashin bin matakai
da addinin Musulunci ya tanadar, babbar matsalar
kuma ita ce, miji bai san hakkin matarsa a kansa ba,
itama matar ba ta san hakkin mijinta a kanta ba,
saboda wani lokaci mu mata muna da girman kan
daukar laifinmu, idan mijinki ya fada maki laifinki
Page | 73 ENMARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
sai ki dauki zafi, saboda ke kina ganin laifinsa yafi
naki shi yasa ba za ki saukar da kanki kasa ba ki
nemi gafararsa kamar yadda Allah ya ce mu yi.
Ina so ku gane cewa, aurc ba abin wasa ba ne, ku
dauka cewa ibada ku ke yi duk da soyayya na zuwa
a cikin sharudan aure, to amma a wani sashc na
zuciyarku ya kamata ku rika daidaita al'amuranku
ga zan yi wannan abu saboda Allah kawai, za ki fada
a zuciyarki kamar ke Badiya nasan idan kin sauko da
kanki ki ka bishi a yadda yake ki bashi hakkinsa
wurin kwanciya ko ya musguna maki, sannan ki ka
lura da cinsa da hansa, ki ka share shi, ina nufin ki
ka fita hanyar wayarsa, nasan akwai wahala amma
ina so ku daurc ku kauda idanunku a al'amarin
wayoyin mazajenku.
Ku rika tashi da daddare kuna kai kukanku ga
Mahaliccinku, ba wai a darc daya matsalar zata
wuce, ba a'a wai a dare daya matsalar zata wuce ba,
a'a wani ma har ya mutu yana rokon Rabbi bukata,
sai dai abun baya kasancewa har sai a lahira, sai
yaga sakamakon abinsa a can, wani kuwa tun a
duniya zai gani, wani kuwa yana roko Allah
(S.W.A) zai ba shi saboda Allah shi ya fi sanin
abinda ya fi dacewa da bawansa, kunga ina son ku
kwantar da hankulanku, ku natsu wallahi idan ku ka
kwatanta abinda na fada muku inshaa Allahu za ku
ga sakamako, kada ku taba jan su da fada, ku sa
Page | 74 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
musu ido kawai, kada ku