na hakura da shiga cikin gidan."
"Habawa Mairo, tun ba yau ba nace ki daina
shiga kin ki, to ga irinta nan. Duk kokarin da kike yi
na ķauda kai a al'amarinta, duk ta rage ba ko don
darajar Alhaji ma ai ya kamata ta rika..."
"Ni kuwa a ganina don ma ina 'yar uwar Alhajin
ne yasa take yi min haka." Ta katse Gwaggo, "Kin
san abinda ya hada mu ta fada miki?"
"A'a ba ta fada ba, ni dai Alhajin ne ya ce in zo
in ba ki hakuri kafin ya shigo gari."
"Daga fa na dauki naman kajin da na soya na ba
Nafisa, da yake tare muka yi aikin, wallahi ni ko
bakina ban sa naman nan ba, ina mika mata tana
shigowa, shi ne da sauri ta fizge naman ta maida
tukunya, ta kuma ture ni yadda ki ka san 'yarta. Ta
rika nuna ni da dan yatsanta har dungure ni take yi
Page | 19 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1)
tana ci min mutunci a kan fiffiken kaza da na ba
Nafisa, ai ban san sadda hawayc ya zo min ba, itama
Nafisan sai ta fashe da kuka.
Mun yi kusan minti ashirin Basira na cı min
mutunci kafin ta bar ni ta fita daga kicin din tare da
ja min kunne a kan in kiyaycta, dama mun riga da
mun asirance Alhaji, ita kuwa an yi kadan ayı da ita.
Ban taba maida mata martani ba, duk irin abinda
tavi min ni nasan akwai ranar da zan rama.
"Ai gara da ki ka kyaleta, kin maida ta
mahaukaciya. Ni da son samu ne ma Alhaji ya samo
muku haya tunda ya ki gina gidan da ya yi alkawari
tun ba yau ba.
"Ai tuntuni yaso yin haka Hauwa, Baban Nafisa
ne ya ki. Kin san halinshi ba sai na ba ki labari ba."
"Haka ne. Ba komai, Allah Yaga zuciyarki
Mairo, Allah Shi zai saka miki." In ji Hauwa.
"Haka nc Hauwa, babu komai."
"Kin san tunda Alhaji ya jawo Sabi'u a jiki nasan
sai an yi haka, tunda yanzu duk vawancin tafiya in
zai yi tare suke zuwa."
"Nima nayi tunanin haka Hajiya Hauwa, ban dai
furta ba ne, don bana son tashin hankali."
A ranar nayi bakin ciki da wannan labari da naji,
don sai naji duk na tsani Haj. Basira. Ban taba
tunanin haka takc ba, ban taba tunanin tana da
:
Page | 20 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
makamancin hali irin haka ba, don ban taba jin
Babah ta fada ba, ashe Babah hakuri take yi da ita.
To ya aka yi ban taba sanin halin da ake ciki ba?
koda yake gaskiya kwata-kwata bana shiga cikin
gidan, tunda na so shiga Babah ta dake ni, dama ni
ina da gudun zuciya, saboda bana son abin da ya
taba ni, don haka duk abinda ne an za a taba jikina
to zan nisanci wannan abu.
Duk wata daraja da nake gani na Haj. Basira ya
fice min, don a gaskiya nasan wannan abu da tayi wa
Babah ba yanzu ta soma ba, dama tun can tana yi.
Sannan tun da aka yi a kan kaza da ba wani abu ba,
to nasan anyi mata ma a kan komai...
Ji nayi Gwaggo Hauwa ta shafa min gashin kaina
ta ce, Dayyiba ni zan wuce fa! Don Allah ki rika cin
abinci kin ji ko?"
Na ce, "To Gwaggo zan ci." Sannan suka yi
sallama ta wuce, har waje gun motarta nayi mata
rakiya, ta zaro Naira dubu ta miko min.
"Ungo ki sai abin dadi kici, kiyi hakuri ban sai
miki komai ba." Na karba ina godiya sannan ta
wuce.
Da zan shiga gida naga Ya Amir, ya fito da
motarsa yana taje kansa. Sosai na tsaya ina kallonsa,
da yake ban da nisa dashi. Sai a ranar na lura sosai
da bakin bakinsa. Ya kara min kyau a ido, ban
ankara ba muka hada ido yayi saurin sakin
Page | 21MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
murmushi tarc da miko min hannunsa da ya
dunkulc, na isa gun ina kallon hannun nasa. Tafin
hannunsa baki ne shima.
Ya ce, "Kin san rannan ba ki karbi ashirin dinki
ba." Ya fadi haka tare da bude hannunsa. Ashirin
biyu na gani, ya mika min na dan juya na duba
haguna da dama sannan na kalle shi na girgiza kaina
ina nufin a'ah.
Sakin fuskarsa ya karu, ya ce "Me yasa?" Na cc,
"Haka kawai bana so." Ya ce, "Amma ban taba ba ki
kudi ki ka ki amsa ba,."
"Haka ne. Kayi hakuri, amma ba zan kara karba
ba." Cikin rashin damuwa ya daga kafadunsa ya се,
"Ok, ba damuwa tunda haka ki ka cc." Ya ja motarsa
ya wuce.
Ya kara burge ni saboda da wani ne nasan sai ya
ji haushina. Na shiga gida ina tunanin abinda naji a
kan mahaifiyarsa, "To Allah kadai Yasan wanda ya
biyo a kirki." Na fadi hakan a zuciyata.
A haka muka cinye hutunmu har jarabawarmu ta
fito, na samu (admission) a (Boarding school) har
guda uku (F.G.G.C Zaria), Gusau da kuma (F.G.C
Sokoto). Baba da kansa ya zabar min Zaria don haka
can zan tafi a take a ka soma shirye-shirye a
gidanmu ba wacce taje (Boarding) amma ni Baba ya
ce ko don saboda son jikina dole ne ma ya kai ni
Page | 22 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
(Boarding). A lokacin kuma Alh. Muh'd Sani ya
ware mana motar da mahaifina zai rika yin nashi
hidimar da yake ya ce ya daina yin Direba a gidan,
vana zuwa daya daga cikin gonakinsa yana aiki ana
biyansa albashi. Carina II aka ba wa Baba a ranar
kamar ya zuba ruwa a kasa yasha, mu ma mun yi
murna sosai.
Lokacin da za'a kai ni Makaranta ma da ita muka
tafi. Cikin sauki aka gama min komai na makaranta.
Da su Baba za su tafi nayi kuka kamar raina zai fita,
sai dai daga baya dole na hakura.
Cikin sati na dan saba har na samu kawa sunanta
Aisha Mansur, dakinmu daya da ita, ita ce a saman
gadon da nake. Nan da nan muka shaku saboda tana
da hakuri.
Abin ya bani mamaki. Tabbas bana son aiki
amma sai naga na fara kula da kayana na makaranta,
sannan ina wanki sai dai basa fita. Sau da yawa sai
Aisha ta karba ta sake wankewa, da yake tana da
kirki. Daga baya ma hada wankin muke yi muyi
tare, ni in yi sabin farko ita kuma sai tayi na biyun
muyi shanya tare. Nayi dacen abokiya, don cikin
Karamin lokaci muka shaku sosai.
Baba kuwa da yake ni kadai ce 'yar (Boarding).
sai ya zama kuma kayan abinci wato (Provisions)
yana min shi sosai, musamman kuma Gwaggo
Hauwa ke zuwa min (Visiting) da (Provisions)
Page | 23 MARUBUCIYA: Sameera Mustaphr
BAKI BIYU [1]
itama. Sai a lokacin na san lallai Gwaggo ba
karamin sona take yi ba.
Rannan muna hutu har na koma gida na iske ana
shirye-shiryen auren Anti Nafisa, ta sami miji a nan
Gusau, yana aiki a Nepa na nan Gusau. Mun sami
sati biyu aka soma biki, ranar Juma'a aka daura
auren, ranar kuma aka kaita.
Sai a lokacin na kara yarda da irin bala'in Hаj.
Basira, sam ta hana ayi taro a gidan, dole aka je
gidan Gwaggo Hauwa aka yi walima, daga can ma
aka kai Amarya. Sosai na kara tsanar Hajiya Basira,
saboda a gaskiya bata da mutunci.
Ina mamakin duk kwarjini da rashin saukin da
nake zaton Alh. Muh'd Sani Shinkafi yake da shi
amma ya kasa tankwasa matarsa, to Allah ya
sauwake.
Gidan Anti Nafisa yayi kyau sosai, don ba abinda
ba a sa mata ba, daidai gwargwado gashi dama
family din Baba da yayinta sun taimaka don haka
tubarkallah kawai zan ce.
An gama biki da kwana uku muka koma
makaranta, sai dai kam nayi kuka sosai har Baba na
sa kwalla.
Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya har gashi
muna rubuta jarrabawar kare aji daya ta
(Secondary). A wannan hutun ma dan Baban falo na
biyu yayi aure, ya auri wata diyar 'yar uwar Hajiya
Page | 24 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Basira, auren gida yayi. Biki aka yi sosai saboda a
gaskiya yafi wansa wadata, don shi a (N.N.P.C
Kaduna) yake aiki, shi yasa duk a cikin 'ya'yanta
tafi ji da shi, da da kanwarsa aka so a hada ama sai
aka fasa don saurayinta bai shirya ba, naji kuma ana
cewa Haj. Basira ce ta ki saboda yaron bai da kudi
dan Makaranta ne.
Da muka koma ne muka shiga (J.S.2), ni nasan
ba wai ina da kokari na azo a gani ba, amma sai
Aisha tayi ta cewa wai ina da kokari, a gida ma ba a
cika matsa min ba kamar yadda ake wa Nafi'u, don
haka zan iya cewa ni (coverage) cc, a ganina
shakuwa ta musamman ta shiga tsakanina da Aisha,
ko ina muna tare da yake ajinmu ma daya. Hatta
(Visiting) aka zo are muke a dalilin haka muka hada
iyayenmu, sai dai su Aisha a Kaduna suke, amma su
asalin 'yan Maiduguri ne.
Kwanci-tashi gashi har muna (J.S.3), abun ba
wuya. Da muka zana jarabawar, Gwaggo Hauwa ta
roki Baba a kan zata zo ta dauke ni in yi hutu
wajenta Kaduna. Baba bai musa ba, don haka ma
hutar da ita muka yi na bi Aisha.
A gaskiya naji dadin hutun, saboda yadda nake
zato na iske, ni dai bana aikin komai sai dai ayi min.
Ina ma a ce gun Gwaggo nake, nayi kyau sosai fatata
kuwa har da sulbi take yi, sai da hutunmu ya kai
Karshe sannan muka je Gusau ni da Gwaggo,
Page | 25 MARUBUCIYA: Sameera M
BAKI BIYU [1]
(Provision) sosai tayi min a wannan zuwa ne want
abun al'ajabi ya faru.
Ni na sani cewa na soma zama cikakkiyar
budurwa, saboda kirjina duk ya ciko, sannan kyau ya
soma bayyana sai dai ban da kibar dai.
Ina zaune tsakar gida kamar yadda na saba ina
hutawa, kamar an tsungule ni na mike na nufi
lambun gidan da yake a kusa da sashenmu yake, na
sami wuri na zauna ina sauraron kukan Tsuntsaye
daga cikin lambun.
Ji nayi an yi min darr a bayana, wtaon an sa
hannu a kasan hammatata. Da sauri na dago kaina na
dubi mai yi min wannan abu, Ya Amir ne, duk da
nayi bakin cikin abin da yayi ban nuna masa a
fuskata ba, na dai dan bata fuskata cike da tsarguwa.
Na cc, "Kai Ya Amir, har ka bani tsoro. Da
sauri ya nemi wuri kusa dani sosai ya zauna. Sam
bai ji dadin hakan ba, saboda kamar zamu shafi
junanmu. Ya dubc ni kuma kaina a kasa ya ce.
"Mamana ya ki kc ne?" Na kara sunkuyar da kaina
kasa ina murmushi na cc, "Yau kuma na zama
Mamanka?"
Ya cc, "Ai dama ke uwata ce tunda dai ke
kanwar Alhajin falo cc." Na сс, "Haka ne, to amma
ai ni na dauke ka wa."
Ya cc, "Da ki ka dauke ni wa ni kuma na dauke
ki mata.
Page | 26 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1]
(rabana ya fadi ras! bai sau uku. Sai naji kamar
har da jikina rawa yake yi, na kasa kallonsa. Cikin
raina kuwa farin ciki ne sosai ya kama ni, ni a guna
wannan abun al'ajabi ne, don ban taba tunanin haka
zai faru ba.
Ni nasan abu ne mai wuya hakan ta faru, to
amma gashi abunda nake buri ya faru cikin sauki,
ashe ba ni kadai na kamu ba..."
Ya tsinka min tunanin da nake yi, ko ke ba ki
sona a matsayin mijinki? Nan ma shiru nayi.
Dayyiba tun ba yau ba, tun kina 'ykar
Karamarki nake sonki, don Allah ina rokonki da ki
amince ki karbi soyayyata.
Naji abun ne kamar a mafarki, na rasa inda zan
sa kaina don dadi, don Allah kada ki cc a'a my love.
ni na sani ba tun yau ba ke matata ce. Ya kara
dubana.
Ni dai har lokacin kaina a kasa yake, kunyarsa ce
ta kama ni. Sai na sake kama jikina.
"Kin amince min 1Dayyiba? Ina so in ji amsarki."
Ji navi ina ce masa "Eh, na amince." Ina kallonsa ta
gefen idona naga ya daga hannuwansa baki daya
yana fadin.
"Alhamdulillah! Nayi wa Allah godiya." Sannan.
ya kara dubana ya ce, "Ina son mu yi soyayyarmu a
boye saboda 'yan sa ido, gashi kin ga ba ki gama
Makaranta ba, ko da za mu yi hira sai mu rinka
Page | 27 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
haduwa nan." Nayi saurin amincewa da abinda ya
fada min, saboda ni ma ba zan so a sani ba yanzu
saboda da sauran lokaci.
Muna nan zaune a wurin muna hira har aka kira
sallar Magriba, sannan muka rabu.
A ranar ruwa ne kadai ban zuba a Rasa na sha ba,
saboda farin cikin da nake ciki, a wannan daren har
sar da nayi nafila saboda murna, na roki Allah yasa
hakan yafi zama alheri a gare ni.
Mun shiga aji hudu cike da nasara, ranar visiting
Baba ke fada min an sanya ranar daurin auren Anti
Fiddausi da Anti Badiya, da yake ita Anti bata fitar
da miji da wuri ba, shi ne har Badiya ta gama a ka
hada bikin nasu. Dadina daya da sai mun samu hutu
za ayi bikin.
Soyayya tsakanina da Ya Amir kuwa mun shaku
sosai, sonsa kullum karuwa yake yi a cikin zuciyata.
Ranar da muka fara rubuta jarabawa ne Mallam
Tanimu Kaita, mutumin da naki jinin ganinsa, ba tun
yau ya furta yana sona ba amma saboda tsana da
nake yi masa duk yadda zan kwace wa ganinsa to
zan yi shi, don haushinsa da nake ji.
Da yamma lis muna komawa (Hostel) da yake
Masallacinmu da dan tazara muna tare da Aisha da
wasu 'yan dakinmu da muka fito Masallaci tare,
Salima take bamu labarin kanwarta da ta karyc a
hutun da muka dawo.
Page | 28 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Daga bayanmu muka ji ana fadin, "Don Allah ku
tsaya an aiko mu gun ku." Mu duka muka tsaya
kuma muka kalli mai maganar, na kula idonta a
kaina ya tsaya. Ta ce, Dayyiba Sabi'u, Malam
Tanimu na kiranki, wai ki same shi a (Staff Room)."
A take nayi tsaki tare da wani irin bakin ciki.
Suwaiba Alhassan ta ce, "Kc kuwa wallahi wannan
mutumin na sonki, ki duba ki ga rannan da muka yi
lattin zuwa (Assembly) da ya lura kina tare da mu
sai ya ce mu wuce, da ba don ke ba da mun ci duka
wallahi."
Na kara jan tsaki "Mitss!" Aisha ta ce, "Hakuri
za ki yi kije ko don ku rabu lafiya." Salima ta dube
ni ta ce, "In kin san yadda 'yammatan Makarantar
nan ke sonsa, wallahi kin yi sa'a."
Saboda takaici ban iya cewa komai ba. Na kalli
Aisha na ce, "Don Allah zo ki raka ni."
Mun isa bakin kofar sai kuma muka tsaya daga
wajc. Ya ce "Ku shigo mana." Aisha ta fara shiga
sannan ni, yana zaune yana rubutu.
Malam Tanimu shi ne (Displine Master) a
Makarantar, yana da cin zalin yara, abinda yasa nake
hakuri da irin damun da yake min kenan, sannan irin
mazajen nan ne masu nacin tsiya...
Ya katse min tunani da ya ce, "Yammata kuna
lafiya?' Aisha ce tayi saurin amsawa. Ya ci gaba
"Ku zauna mana." Ba musu muka zauna. Ya dubi
Page | 29 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Aisha, "Ke Aisha ke ce 'yar rakiya? Kina sa min
baki a kan Kawar taki kuwa? Ko wasikar da na ba ki
ki bata ba ki bata ba?"
"Na bata Mallam." Ajiyar zuciya yayi. "Haba
Dayyiba, nayi iyakacin kokarina a kan neman
soyayyarki, ya ki ke so in yi da kaina?"
a
A zuciyata ni ban da tafasa da zuciyar take yi
babu abinda take kulawa, tsanarsa ce ke kara yawa
tare da ni, ko kallonsa bana yi, idona a kasa yake ina
wasa da 'yan yatsuna.
"Dayyiba!" 2
Ya kira sunana tare da kai hannunsa kan tebur
din da ke gabansa, ya tsura min ido na kusan sakwan
uku. Ajiyar zuciya ya kara yi kamar mai tunani. Ni
dai ban kalle shi ba ina nan a yadda nake.
Can muka ji ana buga kararrawa ta lokacin cin
abinci. Zumbur! Na mike na ce, "Malam za mu je
cin abinci."
"Ashe dama yunwa ki ke ji ki ka kasa cewa
komai?". Ni kam tuni na kama hanyar fita.
A hanya Aisha ke ta tsokanata, nayi mata dundun
wasa. Haka dai nayi iya gwargwado don 6oye kaina
daga Mal. Tanimu, tun daga wannan term ya kare.
Mun koma gida da kwana shidda aka fara bikin su
Anti.
Mijin Anti Badiyya yana zama ne a Kaduna, don
haka can za a kaita ita kuma Anti Fiddausi Kano,
Page | 30 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
biki yayı armashi sosai. Dukkan su rana daya aka
wuce da su.
An shirya mota dai-dai zuwa gidajensu, a
wannan bikin naga naci gun Ya Amir, a cewarsa ana
iya ayi masa snatching idan bai yi hankali ba, da
kyar muka rabu don tsabar son da muke wa
junanmu.
Ni motar Kano na bi don akwai wadanda za su
wuce Kaduna tare damu. Anti Fiddausi an sha kuka.
ni kam dariya nake tayi mata, ban san mijinta na da
kudi ba, kai kowa ma yayi mamakin irin gidan da ya
shirya musu. Gidan flat ne amma na gani na fada,
itama cewa tayi bata san yana da kudi ba, don bai
taba nuna mata ba.
Ta samu gurin zama kam, Allah Ya ba su zaman
hakuri kawai za a ce. Kwana daya muka yi muka
wuce Kaduna, itama gidan Anti Badiyya ba laifi,
don dai kawai gidan ba nasa ba ne amma shi ma
gidan ya hadu duk da su gidan sama ne suna kuma
flour na uku a gidan. Ita kam ba mu kwanan mata ba
a gidan Gwaggo Hauwa muka yada zango.
An gama biki da sati biyu muka koma
Makaranta, duk da ban je Gusau ba a nan Kaduna
Gwaggo tayi min komai na siyayya.
Tun daga wannan lokacin na gano na cika
budurwa sosai, don kirjina ya cika gashi na daurawa
Page | 31 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
kaina wata akida na rashin rayuwa da kowane da
namiji in ba Ya Amir ba.
Kowa kuma ya shaide ni da kunya sosai, ba wai
don ina saka hijab ba ne a'a, sai dai a koda yaushe za
ka ga na yafe jikina da gyale (Pashmina), in kuwa
kayan Makaranta na saka to zan tabbatar na sauko da
shi ya rufe min kirjina, don a yadda na lura kamar
nafi duk kawayena cikar kirjin.
Hatta gun wanka ban taba yarda a ga tsiraicina
saboda nauyin da nake ji shi yasa ma bana wanka sai
na davo daga class irin da rana din nan. Tun ana
tsokanata da akidar har aka sa min ido.
A wannan hutun na second term dinmu a Gusau
nayi shi, sai dai ba ma tare da Ya Amir, saboda a
lokacin suka je Ummara da shi da mahaifiyarsa, duk
da irin hali irin na Maman su Ya Amir bai hana ni
son dan nata ba, so da ban taba yi wa wani da namiji
shi ba.
Sai dai Allah bai hada mu ba, wannan zuwan har
muka koma school ba su dawo ba. A haka na koma
Makaranta cike da damuwar rashin ganin Ya Amir a
Makaranta kuwa karatu muke yi sosai don muna
third term ne.
Cikin wata uku muka rubuta jarabawarmu, mun
koma gida da sati daya kuma kura ta tashi gida.
Dalili kuwa shi ne, ranar Talata naje gidan kawata
Page | 32 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
da yake makotanmu ne, sunanta Amina. Yawanci
dama tare muke idan na dawo hutu.
Na dawo na shiga gida sai kawai na wuce kai
tsaye gidan kiwo, dama a cikin gidan akwai lambu
gidan kiwon kuwa yana daga bayan lambun daga
can na shiga lambun nayi zaune ina shakatawa cike
da nishadi.
Ji nayi an kai hannu kan kafaduna, cike da tsoro
na mike tsaye gabana kuma yana faduwa kamar zai
fita. Raina a bace na dubi dan rainin wayon da yayi
min haka. Ya Amir ne saboda 6acin ran abinda yayi
min yasa nayi tsaki, na kuma banka masa harara, sai
dai ban ce komai ba na tsare girar sama da ta kasa.
Sam fuskata babu annuri, takaicinsa da naji a
wannan lokacin ba kadan ba ne. A rayuwata ban
taba tunani ko shafa namiji yayi min ba saboda irin
cin amana irin wadda nasan wasu mazan suke yi.
Tun ba yau ba nasha jin labarin irin mazan da ke
cewa su in dai ana soyayya ba a taba juna, to ba so a
tsakani.
Ni kuwa na dauki alwashin da namiji ko shafata
ya yi to na tabbata bai da bambanci da irin mazan da
nake zargi...
Ina cikin tunanin Ya Amir ya tsinka min tunanin
nawa, inda ya kara riko hannuna. Wallahi ban san
lokacin da na ware hannu na kai masa wani irin
Page | 33 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
wawan mari ba, tas! Ka ke ji. Na kuma nuna shi da
dan yatsa na ce da shi.
"Ashe kai ma dan iska ne kamar sauran mazan
da nake zargi masu irin wannan halayen? To bari ka
ji, tabbas naso ka amma a yau wallahi na tsane ka!
na tsane ka!! kuma bari in fada maka between me
and vou is over...
Na juya zan wuce, dama tsaye ya yi galala kamar
dan shckara biyun da ya yi kashi a wando, rike da
kuncinsa ya cc, "Ke kin san abinda ki ka yi kuwa?
Marina fa ki ka yi? an gaya miki ke kin kai irin
matan da za su mare ni in kyale su?"
Ina jin ya fadi haka na ruga a gujc, ya biyo ni da
gudun tsiya, saura kadan ya kama ni. Allah Ya bani
iko na shige gidanmu. Ai kuwa har cikin gidan ya
shiga.
Muka iske Babah na zaunc a tsakar gida, naje
bayanta ina ihu. Da sauri ta mike tana fadin "Lafiya?
Lafiya Amir?" Bai tsaya saurarenta ba ya kai hannu
zai kamo ni sai ta rike hannunsa.
"Haba Amir! An cc fa ko mutuwa na kunyar idon
mahaifi..." Rai bace ya nuna ta da yatsa cike da
fushi yana cewa, "Ke ba ruwanki, ki fita hanyata
mara mutunci."
A daidai lokacin Baba ya shigo gidan, ya shiga
tsakaninsu da Babah ya ce, "Haba Amir, me ya yi
zafi haka?"
Page | 34 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1)
Hannu ya daga wa Baba ya cc, "Kai! kaima
munafuki ba ruwanka..." Tas! Tas!! Tas!!! Ka ke ji,
Baba ne ya mare shi. Ai kuwa nan shima ya daga
hannu zai rama sai Sahabi maigadi ya rike hannunsa
ya fitar da shi waje, sai zage-zage yake yi, har da
gori. Wai dama Baba ya mallake Baban falo shi yasa
ya samu gindin zama, sannan dama shi bai ga laifin
Mama da take wulakanta wadannan kaskantattun
mutanen ba.
A waje yake ta fadin wadannan maganganun da
ba dadi, ya zage su Baba tas!. Ni kam kuka na dinga
vi ba sassauci, don ni na jawo akc zagin su Baba
haka. Ban taba tsammanin Ya Amir haka yake ba,
dama ashe dukkan su haka suke ba su da mutunci?
Lallai Baban falo yana da aiki gabansa.
A ce duk cikin 'ya'yansa ba mai halin kwarai?
Dama duk abinda aka ce suna yi saboda ba su taba
yi ba ne a gaban idona ba, ashe dukkansu nc haka?
kai Allah ya waddaran naka ya lalace..
A cikin tunanin naji muryar Mama tana zagezage, ita ce har tsakar gidanmu tana ta faman fadar
ashar, har da cewa tayi, yau shi ne zai zama rana ta
Karshe da zata sakc zama da mu, ta shiga fitar mana
da kaya tana football da su.
Daga Babah har Baba ba wanda ya ce da ita ci
kanki, suna zaune cikin daki Baba suna sauraren irin
Page | 35 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
cin mutuncin da Mama ke yi masu, ai tuni naji duk
na tsani kaina, don dai saboda ni ake al'amari.
Da gaske ne fa gida ba lafiya, yanzu haka ga ni
tarc da Malam Sabi'u yana so ya bar gidan." Tayi
shiru tana sauraren abinda yake fada. Sai kuma ta
amsa da "To." Tana kuma mikawa Baba wayar.
"Ungo Alhaji na son magana da kai." Sai da
Baba yayi ajiyar zuciya sannan ya amsa. Bai dai ce
komai ba, bayan sallama da ya yi. Sun sami kamar
minti ashirin yana sauraren abinda Alhaji ke fada
masa, sannan ya amsa da "To ba komai, Allah Ya
saka da alheri." Ya mika wa Gwaggo suka yi
magana kadan sannan suka yi sallama.
Ta dubi Baba ta cc, "To ka ji yadda aka yi Mujc
gidan da ya fada maka ku zauna can."
"A'a Hajiya Hauwa, ni da kin bar wanhan
maganar. Ni wallahi na hakura da wannan zanman,
Katsina zan wuce." A take Gwaggo Hauwa ta żaro
ido ta ce, "A'ah ba za ayi haka ba, ya ka cc da Alhaji
ka amince da zuwa gidan da ya ba ka halak-malak?
Baban Dayyiba hakuri za ka yi, ni nasan kun yi
hakuri kowa ma ya sani, sai da aski yazo gaban
goshi sannan zaka yi fushi? Haba dai wannan gida
ma dama sunanka aka gina shi don Allah, don
darajar Annabi (S.A.W) kayi hakuri muje gidan, wa
ke maida hannun kyauta baya? Sai shaidan. Haba
Baban Dayyiba!."
Page | 36 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
3
BAKI BIYU [1]
Wata ajiyar zuciya Baba yayi, ita kuma Gwaggo
sai hakuri take faman ba Baba. A kan dole Baba ya
hakura muka wuce sabon gidanmu. Na juya nayi wa
gidanmu kallon karshe, a raina nayi alkawarin ban
sake shiga gidannan.
Baki dayanmu mun yi mamakin sabon gidanmu,
flat ne ya sha fenti, gashi ya tsaru sosai. Sashe uku
ne duk da dayan ba girma ne da shi ba, shi ne sashen
maza sai na Baba daga wajc, na Baba kuwa shi ne
daga ciki, sashen Baba katon falo ne hade da
dakinsa, sai aka shirya dakin baki daga gefe.
Ba abin da ba a saka ba, maganar tsaruwa ma
bata taso ba, duk wani bakin ciki ya gushe, dadi
sosai muka ji. Gwaggo ta zaga damu ko'ina gefen
Baba kuwa bedroom uku ne kowane da bandaki a
ciki, sai katon falo da kicin. Abin dai sai wanda ya
gani, ba abin da ba a saka ba hatta (Kitchen) an saka
su (Freezer, freign, Gas cooker da blander), komai
an yi shi cikin tsari.
Sai da muka natsu muna zaune baki dayanmu a
falo sannan ne Gwaggo ke tambayar abinda ya
haddasa rigimar, Babah ce ta nuna ni da dan yatsa ta
ce, "Kin ganta nan ita ce mafari, ina zaune tsakar
gida ta shigo gidan a guje tana ihu.
Page | 37 MARUBUCIYA: Sameera Musiapia
BAKI BIYU [1]
Baba ya mike a fusace ya сс, "Ja'irar yarinya,
dama