ke ce silar rigimar ban sani ba?" Ya nufo ni
gadan-gadan zai duke ni, ai ban san lokacin da nayi
tsalle na je gun Gwaggo ba, ina kuka ina ba da
hakuri itama Gwaggo hakurin take badawa.
Та сс, "Нaba Malam Sabi'u! abinda ya riga ya
wuce, kayi hakuri." Ta rike ni ta ce, "Ke me ya hada
ki da rigimar?" Ai kuwa ina kuka ina fadi masu
abinda Ya Amir yayi min, nan fa jikinsu yayi sanyi.
Gwaggo Hauwa ta gyara zamanta ta ce, "Wannan
abu bai yi kyau ba, amma ai komai ya wuce. Tunda
Allah Ya raba, yanzu haka da nake fada maku Alhaji
ya saki Hajiya Basira saki daya, dama saura biyu
tsakaninsu.
Kowa ido ya zaro, nan Babah ta ce mu tashi
muyi cikin gida. Suka ci gaba da hirar.
Ni kam dadi naji a raina, ko ba komai an nuna
wa Mama matsayinta, tunda ga lokacin nasan lallai
yarinta ciwo ne, dama haka Haj. Basira take, wallahi
na tsane ta fiye da yadda mutum kc zato. Ji nayi har
da duka 'ya'yanta halinsu daya, dama a da nake
cewa Ya Amir mutumin kirki nc, ashe shima
shaidani ne.
A lokacin Gwaggo Hauwa ta nemi alfarmar Baba
ya bata ni in zauna gunta, tunda dama ai yanzu saura
shekara biyu in gama Makaranta.
Page | 38 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Ba yadda Baba zai yi, ya ee "A'a, saboda ko ba
komai Gwaggo Hauwa tana da mutunci, duk da dai
ransa bai so hakan ba saboda yana da son yara, gashi
dama sai da ya wahala har ma ya cire rai kafin ya
same mu, shi yasa bai iya musa wa Gwaggo Hauwa
ba, yasan irin yadda zata ji har ya ce a'ah.
Don haka ne ya ce, "Ai babu damuwa, dama
gashi Makarantar tana kusa da ku, sai dai kuma kin
zabi raguwa da dai Maimuna ce da take son aiki."
"A'a, ni ina sonta a haka, kasan tun can dama da
Dayyiba muke shiri, kasan tunda Tahir yayi aure shi
kenan gidan yayi min girma, ba kowa a tare dani,
dama dalilin zuwana kenan na iske wannan Kurar."
Haka kuwa aka yi, kayana tsaf! na kwashe ban
manta da ko kyalle ba, murna a guna tamkar za a sa
ni Aljanna, don dama ina ta addu'ar hakan ta faru.
Ranar Litinin tunda safe muka wuce Kaduna. Na
sami yadda nake so don bana aikin komai, hatta
kwai ban iya soyawa ba, don bana ma gwadawa.
Masu aikin gidan har takaicina suke ji, don komai
bana tashi in yi sai dai in kira ayi min, dan zaman da
nayi ma sai da Gwaggo ta sallami 'yan aiki biyu.
Gwaggo Hauwa tana da son yara, don haka ne
dole ma ka shagwabe idan kana gunta. Ba aikin da
nake yi a gidan, hatta (Under wears) in na ga dama,
jika su nake yi kamar dai yadda na saba yi a gida.
Page | 39 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Uwale ita ce matar da ke kula da dakina, ita ke
wanke su. Da yake tana da hakuro sosai, sam bata
damuwa da iskancina, hatta abinci sai an bini daki
an kai min, don haka ne na murje sai ka ce irin
'ya'yan sarauta, 'ya'yan sarautar ma na fada a gani.
Navi kvau sosai, har ma da muka koma
Makaranta sai abokaina su rika tambayar man da
nake shafawa, ni kuwa tunda na koma Kaduna
Gwaggo la saya min (Oil of Olay) ina shafawa, a
gaskiya man ya karbe ni sosai.
A wannan (Term) din nc su Anti Badiyya da
Fiddausi suka zo min, murna a guna kamar zan yi
hauka. Ni dai nasan na zama 'yargata ta ko'ina, cike
da murna da jin dadi muka shiga aji biyar, wannan
shekarar ma haka nayi ta cike da nasara.
Kowa a lokacin samari suka rika kunno kai suna
sona, sai dai ni bana kula su, don ma ni haushi sukc
bani sai in ta ganin kamar duk halinsu daya da Amir.
A kullum ina bakin cikin abinda ya faru
tsakanina da Amir, shi yasa sam bana yadda in tsaya
da kowa. Ba wai bana son yi ba ne, a'a! ni fa bana
son namiji wawa, bana son ire-iren maza masu
sanyi, ina nufin irin wadannan masu saukin, ko
shiga ba su iya ba.
Nafi son namiji gaye, gayen ma mai sakin hannu,
irin wadanda suka san (WhatApps), ai kun dai gane
abin da nake nufi. Sannan bana son kananan mutane
Page | 40 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1)
duk da ni karamar yarinya ce dududu ban wuce
shekaru goma sha shidda a lokacin ba, amma nafi
son maza da suka fi karfina. Ni ba wai abun hannun
mutum ke burge ni ba, a'a ni dai ina son in ga namiji
mai kudi kuma yana more abinsa. Yana shiga irin na
'yan gayu masu ji da kansu, sannan suna da aji. Sam
ban son (Gentleman), nafi son darjeje in na fadi
hakan a raina na kan yi murmushi saboda ni kadai
nasan abinda nake nufi.
Ni nasan na taso ina da bala'in rawar kai, ga
surutu, ga son abokai. A tunanina a set dinmu bakı
daya ba wanda ban sani ba, don saboda tsabagen
surutu, sai dai bana da fada amma akwai taurin kai
zan iya zama da mutum ko kai wane iri ne saboda ni
bana da wai sai na zabi aboki, a'a kowa ma abokina
nc.
Shi yasa a Makarantar ake kirana (Smilcy) a
kullum ina cikin dariya da sakin fuska, kamar Kwai
ko (Laughing gas), saboda haka ne ma sunana ya
bace a ke kirana (Dayi Smiley).
Da muka shiga (SS.III) a lokacin kam na batse,
don ni a ka ba wa (Social Prefect) saboda iya yi na,
dama tun can ina cikin iya rawa ba (Night) din da za
ayi ba a sani ba, saboda irin rawar kaina.
Makarantarmu tana daya daga cikin Makarantun da
ake ji da su a Arewa na Gwamnati, ba ita kadai ba ce
amma kun san kowa nashi ya sani.
n
1
Page | 41 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Tunda na koma gun Gwaggo Hauwa, wata irin
wayewa da kaifin ilimi ya shige ni. Ni kaina ina
mamakin hakan.
Koda yake dama in dai kana zaunc a Kaduna
dole ne ka samu kanka haka, har dai in kana tare da
masu halin, sannan in kana tare da masu wayewar.
Lokacin da muka kai (Third term), da yake muna
shirye-shiryen rubuta jarabawar gama Makaranta ne,
a ka ba mu hutun sati biyu, in mun koma Makaranta
ba zamu dawo ba sai mun gama rubuta jarrabawar
baki daya.
Muna isa gida Direba ya ajiye ni, sai na lura da
baki a gidan, don (Jeep) ce kirar (Land Rover 2010
Spootware)din (Parkc). Na san motocin Gwaggo
Hauwa daga (KIA) sai (HONDA) Judgement Day.
wadda mijinta ke hawa, sai kuma (Honda Jeep)
itama (2010). Koda yake dama na saba ganin baki
irin wannan ba tun yau ba.
Da na shiga gidan, na iske wata mata a falo tana
da kiba, wai! Kibar da ta baci ba tana da haske
sannan hasken nata na hutu ne saboda kayan da ma
ke jikinta abun kallo ne.
Tayi shiga ne na alfarma, gata ta iya shigar. Tayi
min kyau sosai, don ta iya (Dressing), kayan da ta
saka (Ash) ne da baki (Material) ne me bala'in kyau.
Page | 42 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1)
Daga gani matar manya ce. sai dai bata da sakin
fuska don tunda na shigo muka hada ido da ita.
Kallo daya tayi min ta ci gaba da abin da take yi.
Waya ce a hannunta tana latsawa. Sai da na kai
kusan tsakiyar falon sai na dan risina na cc, "Ina
wuni?" Ba tare da ta kalli inda nakc ba ta amsa,
yadda ka san dole ce ma amsa gaisuwar.
"Lafiya." Ta fada tare da kara wayar a kunnenta.
ta fara magana. Ni dai ina jinjinawa wannan bakuwa
tamu don ina ga 'yar gidan sarauta ce, na kusa da
Kofar falon Gwaggo naga wata yarinya mai kyau ta
fito, anyi mata kwalliya sosai.
Ina ganinta nasan bata wuce diyar bakuwar nan.
don itama an shirya ta sosai. Na kai hannuna na shati
gashin kanta na ce, "Yar baby ya dai? Me sunanki?"
Take ta saki fuskarta da murmushi ta ce, "Asma'u,
amma Nana ake kirana."
"Nana How old are you.?" Tayi fari da ido ta ce,
"Am five years old." "Da kyau!" Na fada ina kara
son yarinyar a raina saboda wayonta. Na karasa
cikin falon nayi saurin isa gun Gwaggo na
rungumeta na ce "Kai Gwaggo yau ko tarbana an ki
saboda an sami wasu 'ya'yan ko?"
Та сс, "Кai 'yar kanwata ba haka ba nc, ai jikata
ce ba ki waye su ba ne?" Na zare ido na ce, "Kaddai
yarinyar
W
Idris ce?"
Wane Idris kuma? 'yar Tahir dai."
Page | 43 MARUBUCIYA: Sameera Mustaphа
BAKI BIYU [1)
"An yi haka Gwaggo, ashe wannan matarsa ce a
falo."
"Ita ce, ke da ashe ba ki santa."
"Ni kam ban san ta ba sai a hoto shima din
lokacin tana Amarya, sannan duk zuwan da suke yi
ina Makaranta, hala wani zuwan suka yi da
Dayyiba?"
Kwata-kwata zuwansu na biyu kenan, tunda
Tahir yayi aurc, shi kadai yake zuwa ya yi kwana
daya ya wuce bayan kowane wata biyu. Kai amma
shi kuwa wane irin namiji ne da ba zai iya tursasa
matarsa tayi zumunci ba?
Gwaggo ta saki fuska ta cc, "Ni kuwa ba ki san
wani abu ba 'yar kanwata, duk a cikin 'ya'yan da na
rika babu wanda yafi kyautata min irin Tahir,
haihuwarsa ne kawai ban yi ba, amma ni kam nasan
dana ne, don yana da mutunci, ga shi yana da kula.
Ke a rayuwarsa baki daya babu abinda yake yi
bai fada min ba, dole sai da amincewata sannan zai
aikata wannan abun. Da ne gun liaj. Basira, amma
rayuwarsa baki daya a gidannan yake, shi yasa take
adawa da ni sai dai ni bata ishe ni kallo ba, babu
yadda ba tayi ta raba mu ba amma Allah ya kare ni
daga sharrinta mai dunbin yawa.
In fadi miki abinda ba ki sani ba, wannan matar
tasa Suwaiba ba karamin rigima aka yi ba kafin ya
Page | 44 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
yada ya aureta, sai da na nuna fushina sosai sannan
ya amincc.
A lokacin babu cin mutuncin da Basira bata yi
min ba a kan auren, hár cewa tayi na wanke na bashi
yasha ba ya ganin kowa da gashi sai ni, ni kuwa
wallahi ban ga dalilin da zai sa in yi wa dan mutane
asiri ba, don dai ko ba komai na rike yara sama da
goma sha biyar, Allah kuma ya bani abin da zan
taimaka musu da shi, suma kuwa suna nasu
Kokarin..."
"Ai Gwaggo ba sai kin fada ba, wallahi kowa ya
shaida hakan. Allah nc zai biya ki." Nayi saurin
katse ta ne saboda na lura ranta yana baci, idonta
take ya sauya kala, har da kamar kwalla za su fito
daga idon nata.
"Kai mata irin Haj. Basira Allah ne kadai zai iyaа
da ita, amma shaidan ce. Allah Ya shirycta in mai
shiryuwa cс."
"Amin." Gwaggo Hauwa ta katse ni, ta ce "Duk
da ban taba haihuwa ba, wallahi ina da kwanciyar
hankali tunda Allah Ya hore min baiwa ta zama da
'ya'yan mutane. Ina alfahari da hakan ko 'ya'yan
sun butulce ballantana' ma Alhamdulillahi baki
dayansu na aurar da su..."
Na sake katse ta.
"Gwaggo ke uwa ce da ba ki haifan ba ma nayi
miki alkawari Giwaggo inshaa Allahu zan yi miki
Page | 45 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
biyayya tamkar mahaifana a kaina, ina so in zama
'ya a garc ki, kuma inshaa Allahu za ki zama mai
alfafahari da ni.
Fara'a ta saki sosai da har hakoranta suka
bayyana, sannan na lura a cikin kwayar idonta akwai
wani nishadi na daban da ya shige ta. Tasa hannu ta
rungume ni tare da shafa min gashin kaina, tana sa
min albarka tarna kuma hamdala ga Allah, ni kuwa a
raina kara daukar wa kaina alkawari nakc yi, zan
zama mai cikakken biyayya gare ta.
Muna cikin haka sai muka jiyo sallama daga
bakin kofar falon, Gwaggo Hauwa naji ta ce, "A a!
Tahir har ka dawo?".
Murmushi ya saki wanda bai kai ciki ba, ya
Karaso yana cewa, "Gwaggo na dawo an wuni
lafiya?".
"Lafiya kalau."
Har sai da ya zauna sannan ya ce, "Gwaggo
madarata nake bukata."
"Ai ko na manta da shi a can (Gardiner), bari in
kira Babale ya dauko maka."
Sai a lokacin na gaida shi, ya amsa ba tarc da ya
dubi inda nakc ba. "Umm!" na fada tare da mikewa
tsaye. A raina kuwa ina tunanin hali na masu
wulakancin nan daga shi har matarsa ai halinsu
daya, sam basa da bambanci, saboda dai dukkansu
Allah Yayi masu girman kai, duk da rawar kaina
Page | 46 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
sam ban nemi in shige masu ba, don na yi wa kaina
alkawarin ni da 'ya'yan Hajiya Basira sai dai ido,
don dukkan su halinsu daya ba su da bambanci da
uwarsu...
Gwaggo ce naji tana cewa, "Anya Tahir ka san
'yar uwarka Dayyiba?" A daidai lokacin kuwa muka
vi ido hudu da shi. Sai da gabana ya fadi, saboda
idanunsa suna da wani irin abu da ban san ko
menene ba.
Da sauri nasa idona kasa, naji ya ce, "Ok, ita cc
Kanwar taki da ki ke bani labari?"
"Haba dai Tahir, ka ce ba ka san 'yar Malam
Sabi'u ba ce? Uwa ce fa gare ka."
"Haba dai Gwaggo, ta ya za ayi ta zama uwata,
sai dai in a Hausance ko?"
"A'a wallahi ana iya kiranta uwa a gare ka,
saboda kanwa ce a gare ni da kuma Baban falo, ko
ka manta mahaifiyarta Gwaggonmu ce, tunda
Kanwar su Babanmu ce."
Ya ce, "Ikon Allah! ashe haka dinne dai uwa ce a
gare ni:
Ni dai ina jin su amma na riga na karasa daki,
nan kuma ya canza hirar zuwa ga ta (Business). Can
naji Gwaggo na cewa.
"Wai Tahir na ba ka shawarar ka kwantar da
hankalinka, ka ki ko? Dubi yadda ka fada sai ka ce
ba kai ba, shin zaman duniyar nan nawa take da zakа
Page | 47 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
sa wa kanka tunani kana ba wa kanka wahala, ka
duba ka gani babu abinda ka rasa, Allah Ya hore
maka a duniya shekaran jiya nan Babanka ke bani
labarin ka sami kwangilar da ka ke nema ta harkar
mai, to menene naka wai iya ka ci ka kwantar da
hankalinka kaji dadin dukiyar da Allah Ya baka."
Shiru yayi yana saurarenta, Gwaggo duk yanayin
zamana da Suwaiba kin sani to ni wallahi na gaji da
matsalarsu daga ita har Mama, wai cewa tayi in
rinka tafiya da ita gun aiki duk garin da za ni sai naje
da ita, shin Gwaggo domin za a takura ni a kan
abinda ban yi niyya ba, ni shi kenan bana da ikon sa
doka a gida sai Mama ta shirya min yadda zan yi?".
"Hakuri za ka yi, yarona dan albarka. Wata rana
sai labari zai wuce..." a daidai lokacin Suwaiban ta
shigo, sai naji Gwaggo tayi shiru.
Can kuma naji ta ce, "Ashe ba barci kike yi ba,
dama kina falon kenan? sam ban ji amsar da ta ba
wa Gwaggo ba, duk da kasa kunnenta da nayi. Hum!
Lallai matar nan tana da jin kai, ko magana wato
dole ce ta zama mata, kai mulki dadi, Allah ba mu
wanda zai amfanc mu amin.
Haka na gaji idan ina son jin gulma sai dai
bukata bata biya ba, don falon suka bari daga nan na
shige bandaki don in yi wanka in yi sallah.
Ban Kara yadda na hadu da ko dayansu ba,
saboda na lura mulkin nasu sai su, ban ma fi kwana
Page | 48 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
biyu ba na wuce Sokoto, don dama na kan je lokacin
hutu amma ba kowanc ba.
Kwanana tara na koma gida Kaduna, a can
Gwaggo ke bani labarin ai da kyau Suwaiba tayi
kwana hudu, sai da suka yi rigima da Tahir,
karshenta ma sai ita cc ta wuce ta bar shi a nan.
Ni dai bai ko taba bani tausayi ba saboda ai hali
shi yake ja wa mutum, halinsu ne. Don haka sun
dace da junansu.
Kwana biyu na kara na koma Makaranta, muka
hade da Aisha takc bani labarin an sa mata rana.
Muna gama (Graduation) da wata biyu za ta yi aure.
Nayi mata murna kwarai, don dai tayi sa'a ta auri
wanda take so, ba tun yanzu suke tare ba, tun muna
aji biyu yake sonta har gashi Allah Ya nuna mana
mun gama.
A gaskiya duk da rashin biye wa abokai Aisha
daban ce, saboda muna shiri sosai da ita, tun
haduwarmu muke tare gashi mun gama fara
jarabawa. Cikin wata biyu kuma muka gama har da
Neco, muna gamawa a ranar muka wuce Kaduna.
Tunda na koma gida ba inda nake zuwa a koda
yaushe ina gida tare da Gwaggo, a lokacin wata
shakuwa ta musamman ta karu tsakanina da
Gwaggo, in ban da shagwaba da iya yi ba abinda
nake yi, sam bana shiga (Kitchen) balle in koyi girki,
hatta taliyar (Idomie) zan ci to dafa min za ayi.
Page | 49 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Ana saura kwana shidda za'a fara biki, Aisha ta
hada ni da babban abokin mijinta. Abin mamaki sai
naga kamarmu daya da shi. Ita kanta Aisha abin da
ya bata mamaki da sauran wadanda muke tare da su,
sunansa Sa'id.
A gaskiya tun bai furta yana sona ba naji a raina
ya yi min, don yadda nake son suffar da namiji haka
yake. Yana da tsawo, ga shi ya iya shiga, shigar
Kananan kaya yake yi, sannan ga shi da sakin hannu
saboda shi ya dauki nayin (Dinner) din su Aisha ma.
A gaskiya ya kashe ni da birgewa, don duk wani
mafarki a kan da namiji da nake burin samu yana da
shi. Motar da yake shiga ma abar kallo ce. (Ford) ce
kuma (Jecep) mai fadin gaske, in ka shigeta sai ka се
kana cikin Jirgi.
Da bai furta yana sona ba da ban san yadda zan
yi da rayuwata ba, sau da yawa in na tuna irin halina
na kan dantanshi da 'yar karya, saboda irin rayuwar
da na daukar wa kaina abun mamaki Aisha tana
hakurin zama da ni, donni komai nawa nafi son
hadadde.
A kullum idan ina bata labarin irin rayuwar da na
zaba wa kaina ta kan cc min in dai bi a hankali don
duk mai irin halina a karshe burinsa baya dacewa da
shi, sau da yawa irin rayuwar da ka ke so ita ce bakа
samu gara dai kai ta addu'a, ai maganar da nake yi
Page | 50 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
ina yiwa kaina baki ne don in sami hakan а
rayuwata.
Ni nasan ba karamin kyau nayi a wannan auren
na Aisha ba, don a gaskiya Gwaggo bata wasa wurin
sai min kaya da kayan kwalliya, shi yasa sam Sa'id
ya ki yadda in yi nisa da shi, in dai taro ya hada mu
da shi mu kan samu kamar kusan awa muna hira, sai
dai duk da haka bana gajiyawa da ganinsa.
Gidan Aisha a Malali G.R.A yake, muna kusa da
su, don mu muna Unguwar Rimi ne a Inuwa Wada,
shi yasa na ce da ita sai ta gaji da ganina.
Mun bala'in sabawa da Sa'id, a cikin raina kam
ban san dalili ba, ina sha'awar ganin sa ko don yana
kawo min kayan dadi ne oho, amma ba wai nasa
harkarsa ne a gabana ba, saboda ina tsoron in so shi
yayi min irin na Amir, sai dai ni na sani tuni na
kamu da sonsa.
Mun sami kamar wata goma a gida kafin
(Admission) ya fito, ikon Allah ni ban sami
(Admission) ba shi ne fa mijin Gwaggo Alh. Shehu
Magaji ya bada shawarar a nema mini (Polytechnic
Kaduna), sam ban ki ba saboda zaman gidan ya ishe
ni, gashi Baba ya soma maganar aure, Gwaggo ta
nuna masa ai aurc za'ayi shi sai da wanda nake so ne
bai fito ba amma in sha Allahu za a zauna da shi ayi
magana. Cikin ikon Allah kuwa na sami (Period) a
nan (Poly Cabs) na sami (Business Admin).
Page | 51 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Soyayyarmu da Sa'id kuwa a kullum karuwa
take yi, ni dai ban taba yi masa maganar aurc ba, sai
dai shi a kodayaushc bai da magana sai na in ya aure
ni zami yi kaza zamu yi wancan, to shi ne dalilin da
yasa na saki jiki da shi sosai, kuma na kara sa wa
raina shi ne dai zabina.
A nan Makaranta (Poly) a gaskiya duk da rawar
kaina ina kokarin kama kaina, don wata rayuwa ce
ta daban, na samu kawa Rahinatu, ita 'yar Lagos ce
a nan ta sami Makaranta sanadin Kawunta, don haka
ma a gidansa take zaune. Itama kyakkyawa cc, fara
ce sosai tana da kyau. Kawancenmu ya yi karfi
saboda kusan halinmu daya, sai dai ita tafi ni iya yi,
har a raina na kan yi mamakin ashe akwai wadda tafi
ni rawar kai. Ga ta da shisshigi, komai kuma aка сe
a kan wani abu ta ce miki ta fiki saninsa. To haka dai
muke zaune da ita, da yake ni kuma halina ne duk
yadda halin mutum yake ina iya zama da shi ba tare
da na matsa wa kaina ba.
Haka mukai ta zuwa Makaranta har muka gama
(First Semester), Allah Ya taimake ni bana da (Spil
over), Rahma ce ma take da guda uku. Ni na san
haka na iya faruwa, don Rahma in ban da karya ba
abinda ta sa a gaba, ga son hira da maza kala-kala, in
yau ka ga wannan to gobe wani za ka gani, ba abinda
yafi bani haushi da ita irin shisshiginta, ta fiye
shisshigi.
Page | 52 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Sau da yawa wani abun in tayi ni nake jin kunya,
gata dai Allah ya bata duk wani abu da cikakkiyar
'ya mace take son samu, ita tana da shi. Koda yake
dama an ce mutum bai taba cika goma ba, a taba
halittar mutum cikakke.
A wannan hutun ne suka hadu da Sa'id har
gidansu muka je nayi (Introducing) din Sa'id ga
Rahma, a matsayin wanda zan aura. Sosai ta jinjina
min na samun gwarzo irin Sa'id, itama sai da ta gaya
min irin kamar da muke yi da shi.
Ban sami zuwa Gusau ba wannan hutun, ban
kuma damu in je ba saboda na lura Baba ya soma
matsa min da zancen aure, ni kuwa ina son samu ne
so nake ko 'yar (Diploma) in samu, sai dai naje gun
Anti Fiddausi da ta haihu ta samu Faisal, nayi kwana
hudu na dawo.
Mun koma makaranta, Rahma dai tana nan da
halin nan nata sai dai ma abinda ya karu, haka kuma
nake tare da ita, to ya zan yi tunda haka nima na
zabawa kaina, sai ka ce dole.
A wannan (Semester) din karatu yayi mana
yawa, don ta shiga (N.D.I) ce don haka dole ne ma
na fidda komai a gabana, karatu nake yi sosai. Sa'id
kuwa kusan sau biyar yana shiga Makarantar in ya
shigo gari ya ke ina (School) sai kawai ya wuce
can. Mun gama wannan (Semester) sai hutu,
Gwaggo ta ce min inshiga makarantar Islama, a take
Page | 53 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
na amince na shiga (AL-AMANAR ARABIC
SCHOOL), na kuma yi sa a (Pre Basic) suka bani,
duk da ina da izifi talatin suka ce ai makarantar ta
arabic ce, don haka dole in soma daga farko. Shi
yasa na rage fita sosai don na maida hankali sosai.
Ina zuwa Islamiyya, ga shi ina jin dadin karatun
sosai, a nan kuma na hadu da Aminatu Amin, ita
kuma 'yar asalin Kano ce, ita kusan halinta daya da
Aisha, shi yasa na nace zan haďu da su. To da na ba
Aisha ma labarin Makarantar sai ta ce zata shiga
itama da yake nima na matan aure na shiga.
Cikin sauki kuwa itama ta shiga muka hadu mu
uku, ita Aminatu tana da kishiya tare ma suke zuwa.
Sai dai tana gaba da ita, ga shi tayi dacen kishiya
sam ba sa da matsala zaman aminci da yadda suke
yi, don a kullum tare suke zuwa kuma tare suke
tafiya, duk da kowace na da motarta, amma ba za ka
taba fadan wacece ta wancan ba, kowace shiga suke
yi har na maigidan nasu.
Mun koma makaranta, Alhamdulillahi nayi
(Passing) ina da (Lower Credit) a (GP) dina, don
haka muka ci gaba da karatu, ita kuwa Rahma ta
sami matsala, amma tana da (Pass), don haka dai
muna tare.
A wannan lokacin ne ganin Sa'id ya soma yi min
wuya saboda (Transfer) din da ya samu zuwa Lagos.
Sai muyi sati uku har wata ma ba muga juna ba,
Page | 54 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
waya ma mun rage sai ya ce aiki ne ya yi masa
yawa. Na yadda don karin girma ya samu, don haka
dole ne yanayi ya canza. Ya ce min in ya fita tun
safe ba ya samun kansa har sai karfe tara na dare,
don haka ne muka koma yin wayar dare shima din
bai wuce na minti sha biyar zai ce don Allah in yi
hakuri yayi bacci ya gaji da yawa.
Ina tausaya masa sosai, don dai mutum ya
kasance yana aiki tun safe har dare, gashi sonsa yayi
ambaliya a raina, ina bala'in sonsa. Su Aisha har
cewa suke yi da alama ni na fi son sa a kan yadda
yake sona, ni dai ban yarda ba, gani nake yi shi din
ne yafi sona ni tausayinsa ne kawai yayi min yawa.
Haka rayuwa ta rika wucewa har gashi muna
(Final Year) dinmu na (Diploma), har ma mun yi
nisa don mun kai kusan wata biyu da rabi da karatu a
(Final Year) din.
A wannan lokacin nc Baba ya matsa sai dai in
fito da miji in yi aure, saboda su Maimuna da Zalihat
sun fitar da wanda suke so, suna gama Makaranta za
suyi aure ba za su fi wata biyu da gamawa ba, don
haka in fitar da wanda nake so don a hada ayi biki
gaba daya.
Hankalina ya tashi sosai, don kwata-kwata yanzu
sai muyi kusan sati ma ba muyi magana da Sa'id ba,
Page | 55 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
tun abun bai damuna har na fara damuwa, gashi
Gwaggo ma ta bi bayan Baba, ta ce in yi wa Sa'id
magana ya fito. Na rasa inda zan sa kaina. Tun da
satin nan ya kama nake ta faman neman Sa'id a
waya bana samu, sannan na