An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
BAKI NIYU
HNL
by samira mustapha
HAUSAВООК.СOM
1
BAKI BIYU
SAMIRAA MUSTАРНА
BAKI BIYU [1]
BAKI BIYU - 1
na daga bakin kofar sashenmu, daga nan in da
nake ina hango mutumin da nake jin shi a
raina. Ni na san sonsa nake yi, yana bala'in burge ni.
Tabbas na san ina kaunarsa saboda irin zubin da
Allah ya yi masa, duk da shi ne mutumin da ya zam
zakka a gidan, saboda irin halayyarsa da nake jin ana
fadi, sam ban taba yarda ba, saboda ni a hakan ya yi
min saboda a gaskiya ya san darajar mutum.
Yana da sakin fuska, sannan ga wasa da dariya.
Ko kai ba sa'an yinsa ba nc. Sau da yawa ina jin ana
cewa ba ya jin magana, ko kuma ya cika rashin ji, to
ni ba na ganin hakan saboda ni duk abinda ya yi
daidai ne a guna, yana burge ni.
Hada idon da muka yi da shi ya saki fuskarsa
3
yana daga min hannu yasa nima na saki murmushi
ina mayar masa da martani, a raina kuwa wani irin
dadi ne ya kama ni, don ina kara sonsa in ya yi min
hakan. Duk da ni karamar yarinya ce 'yar shckara
goma sha biyu, na san na kamu da son Ameer,
sunansa kenan. Amma da yake kannensa da muke
tare da su suna kiransa Yaya Ameer, don haka nima
ko in ce duk yaran gidanmu ma haka muke kiransa.
Abin da yasa nake kara son kallonsa a
kodayaushe, saboda shi dangayu nc, kullum za ka
gan shi ya shiga motarsa ta 'yan gayu ya daga sauti,
in zai iso wuri to sautin kidan da yake saurare shi za
Page | 3 ARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKIBIYU1[
ka fara ji. Sau da yawa mutane na ba ni haushi idan
suna zaginsa, meye laifinsa don Allah? ai lokacinsa
ne dadin mutum ya ci lokacinsa, don nima in da na
samu gatansa ban ga dalilin da zai sa in ki jin dadina
ba.
Ya Amir ba wai kyau gare shi ba, amma saboda
koshin lafiya da shiga na alfarma, shi yasa yake da
shiga rai. Ba ya da jiki sosai, yana da tsawo sannan
sumarsa baka ce wuluk kamar sauran 'yan uwansa.
Sai dai kuma duk Yayinsa da kannensa sun fi shi
kyau, amma ba za ka ganc hakan ba sai ka ganshi
tare da su. Da alama yana da farin jini sosai a gun
Jama'a, saboda sakewar fuskarsa, ga sakin hannu.
Yana da kyauta don sau da yawa in mun hadu zai
miko min hamsin.
Suna da kudi sosai iyayensa, sai dai shi ya fita
daban da 'yan uwansa, ko don ina kaunarsa ne nake
ganin haka? oho.
Alh. Muhammad Sani Shinkafi, dan asalin jihar
Zamfara (Gusau) kenan, shi ne mahaifin Amir. Yana
da matar aure daya da 'ya'yanta biyar, da ya ke
garin sun fi albarkar gona (Noma) da siyasa, yasa
Alh. Sani Shinkafi yana daya daga cikin hamshakan
masu kudin garin, a yadda nake jin labarin
kadarorinsa, har ba zan iya fadan adadin dukiyarsa
ba.
Page |4 ARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Yana da gonaki da za ka ga an rubuta (Shinkafi
Farms), sannan yana cikin siyasa. Saboda a yanzu
haka ma shi ne mai baiwa Gwamna shawara, wato
(Permanent Secretary), kana a gonakinsa kuwa babu
abin da babu. Irin su shuke-shuken kayan abinci da
na kayan gina jiki, duk ana shukawa.
Sannan ga na kiwon kaji na noma da na kwai, su
kifi. Kai! ba abin da babu na dai harkar
(Agricultures), duk yana yi. Don haka ya shahara, ba
a Zamfara ba ma kawai dukkan Nijeriya.
Matarsa Hajiya Basira, mace ce mai kirki, ga ta
ita ma da zuciyar kwarai. Shi yasa ma in nayi
tunanin irin kirkin Amir bana mamaki, don
mahaifiyarsa tana da mutunci fiye da tunaninka.
Tana da kyauta, don a idona na sha ganin irin
kyaututtukan da take yi wa jama'a, ba 'yan uwanta
kaďai ba, mu da muke zaunc da ita mu muka san
hakan, saboda yawancin kayan da za ka ga muń sa
masu tsada, to ita ce ta ba mu su.
Ya'yanta kuwa, babban danta sunansa Yaya
Idris, tuni yayi aure yana da matarsa daya da
'ya'yanta biyu, sai na biyu sunansa Yaya Tahir, shi
kuma yana karatu a kasar (London), nan da wata uku
zai dawo. Sai gwanin nawa Yaya Amir, shi ma
karatunake yi a nan Jami'ar (A.B.U Zariya),.
saboda naji labarin kamar an koro shi ne daga kasar
(America) saboda irin rashin jin da yasa a gaba a
Page | 5 ARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
can, shi ne suka turo shi gida, a cewarsu wai har da
shayc-shayc yana yi, muje Makaranta mu dawo
dakin yana a yadda yake har sai Yayyaina sun gaji
sun gyarа.
Mahaifina Mal. Sabi'u Mamman, dan usulin
Katsina ne, mahaifansa 'yan Ruma ne, don haka duk
wani labarin kyau ba ta taso ba, don bata bakina zan
yi idan na ce zan fadi yadda yake da kyan.
Kowa ya san asalin 'yan Rumawa, mutane ne da
kamar su suka halicci kansu don kyau, duk da ba
dukkansu ba ne dole a samu wanda bai kai wani ba.
sai dai yawancinsu gaskiya ba a maganar kyansu,
duk fadin jihar Katsina kuwa.
Don haka mahaifina fari ne tas tamkar dan
Balarabe, yana da tsawo da jiki, don zaka iya kiransa
mai jikin saboda har yaso yayi masa yawa.
Matarsa daya duk da yayi auren har sau uku ya
rabu da matan ne sannan ya auri mahaifiyata Baba
Mairo.
Yana aiki ne a karkashin mahaifinsu Ya Amir,
wato Alh. Muhammad Sani Shinkafi, zama ne ya kai
shi jihar Zamfara, Allah kuma ya hada shi da shi.
Da farko direban Baban Falo ne (haka muke
kiran Alh Muh'd Sani), tun yana saurayi duk da ba
wai Alh. Muh'd Sani ya girme shi ba ne sosai. sai
dai saboda shi ya yi saurin aure, sannan yana da
Page | 6 ARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
wadata, in ka ga Babana ka ce ya girmi maigıdan
nasa.
Sun hadu da mahaifiyata ne lokacin ma yana da
matarsa ta uku, sai dai bata taba haihuwa da shi ba,
sanadin auro mahaifiyata ta fita, a cewarta ya auro
"yar masu arziki gashi dama zaman hakuri take yi
don ba ya haihuwa.
Tabbas Babah danginta masu kudi ne, don 'yar
uwar Alh. Muh'd Sani Shinkafi cc, duk da
dangantakarsu ba mai Karfi ba ce, a can Shinkafi
kamar yada naji gun Kakani suka hada 'yan
uwantakar tasu.
Mahaifiyar Babah ita ce Cousin mahaifiyar
Baban falo. Da yake gidansu babban gida ne, matan
mahaifinsu hudu ne da wadanda ya saka kuwa
takwas. Kuma hudun da ba ya tare da su ma yana da
'ya'ya sosai tare da su.
To mahaifiyar Babah itama ba ta gidan, tana da
'ya'ya shida tare da Kakan su Baban falo, da suka
rabu kuma sai ta tafi da Babah Mairo can Ghana.
Da yake usulinta kenan, a can Ghana ta girma sai
dai ba tayi makaranta mai nisa ba a can din, tunda
suka tafi ba su dawo Gusau ba, tun Babah na da
shckara uku suka tafi.
Rayuwar Babah a Ghana ba wai ta jin dadi ba ce,
saboda talla take yi, neman kudi suke yi sosai ita da
mahaifiyarta. Sai da suka sami shekaru ashirin da
Page | 7
ARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
barin garin sannan suka sami labarin mahaifin Babah
Mairo ya rasu.
Duk da haka mahaifiyarta ba ta so dawowa ba,
har sai da aka mata manzo (dan aike) tun daga nan
Zamfara, da kyar da sudin goshi sannan ta amince
suka zo saboda sosai ta dauki zafi da Alhaji Sanin
Shinkafi, dalilinta kuwa shi ne, ya share ta bayan
tasan tana hakki a kan 'ya'yanta biyar da ta bari
gidan, bai taba tura su su ganta ba.
a
Da suka zo garin Gusai kuwa, tuni har an gama
zaman makoki, shi yasa ma Babah bata hadu da 'yan
uwanta ba, bata san su ba kuma bai hana da
mahaifiyarta tashi tafiya ta ce za su wuce tare ba.
A wannan lokacin 'yan uwa da yayyen Babah
suka durje a kan ba za a tafi musu da 'yar uwarsu ba,
gata duk ta fita daban da 'yan'uwanta. Bata da ilimin
Islama ballantana boko.
Hayaniya sosai aka yi da ita, amma taki hakura.
Hatta 'ya'yanta sai da suka yi mata alkawarin za su
rika tura ta Ghana su suna ziyarar ba ita kadai ba ma
su dukansu amma sam taki.
Su kuwa ba wai sun so su raba su ba ne, a'a
wasiyyar da mahaifinsu ya bar masu a kan suyi
alkawarin daukota ta kasance tare da 'yan uwanta ne
kurum, in ba haka ba su meye nasu? Don haka ne
suka zauna musamman don ganin wannan matsalar
tazo karshe.
Page | 8 ARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU (1]
Da yake Baban falo yana daga cikin manyan
jikokin a zuriyar kuma kun san in mutum na da abun
hannunshi ya ba da shawarar a daura wa Babah
Mairo aure in anyi haka shi ne kadai zai sa Innarta ta
barta.
Nan aka dinga shawarar wanda za'a ba aurenta.
A nan ma shi din dai ya bada shawarar a hadata da
yaronsa, don a cewarsa ya san halin mahaifina, yana
da karamci don duk mutumin da zaka zauna da shi
fiyc. da shekaru ashirin to ana kyautata zaton
mutumin kwarai ne, gashi a wannan lokacin ma
aurensa na tangarda aka yi maganar rashin
haihuwarsa, ya ce matarsa ta karshe ce kadai bata yi
ciki a gidansa ba, sauran sun yi ciki har daya daga
cikinsu ma ta haihu, sai dai dan bai zo da rai ba.
A karshe dai shawarar Baban falo aka dauka,
washegari suka daura mata auren. Mahaifina ba a
samu matsala da shi ba, don shima dama yana
bukatar hakan.
A kan dole mahaifiyata ta koma Ghana, duk da
'ya'yanta sun yi iya kokarinsu a kan ta zauna tare
dasu taki, sai da Babah Mairo ta haifi 'yarta ta hudu
sannan mahaifiyarta ta rasu itama.
Ni dai ban taba jin Babah ta fadi rashin kirkin
Hajiya Basira ba tunda nake, na kan ji Yayycna na
fadan bata da mutunci, ni da mahaifiyata kam
kirkinta muke gani sosai, har dai ni da na kan ce Ya
Page | 9 ARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Amir ma ita ya biyo da kyauta. Haka kurum zaka ga
ta aiko min kayan sawa, sai dai na rasa dalilin da zai
sa Babah bata bari mu shiga gidan, meye dalilinta
ban sani ba. Amma haka na tashi na iske iyakarmu
tsakar gidanmu.
Haka yaran gidan wato 'ya'yan Haj. Basira, in
ban da Amina da take shiri da Yayata Nafisa, itama
din don tana shiga cikin gidan ne aiki.
Mahaifinmu yana yi mana hidima daidai
gwargwado, saboda muna zuwa Islamiyya da boko,
yanzu haka yayata ta kusa karewa, tana aji shidda a
(Sccondary), sai mai bi mata tana aji hudu ita
sunanta Fiddausi, ta uku tana aji uku, sunanta
Badiya, ta biyar din ta rasu sunanmu daya da ita.
Daga ita sai Mujahid, shi yana aji daya sannan ni
sai Nafi'u, daga shi sai Maimuna da kuma Zalihat ita
ce auta mace daga ita sai Hassan da yake aji hudu na
(Primary).
Ajinmu daya da Nafi'u saboda tare aka saka mu
makaranta, don nayi nauyin baki ban yi magana da
wuri ba. Maimuna da Zalihat su kuma shekara daya
da wata biyu ne tsakaninsu, Babah ta haife su
kurkusa don haka ma sau da yawa mutane ke cewa
su 'yan biyu ne, suma ajinsu daya.
Mu takwas ne gun iyayenmu, duk a cikinmu
kuma ba wadda ta biyo mahaifiyarmu, don kun san
yadda jinin farin mutum yake, dukkanmu maza da
Page | 10 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
matan jajir muke sai dai wani ya fi wani farin ko
kuma kayi yanayi na kama da ita.
Cikinmu mata ba wacce ke kama da Babah,
dukkanmu da Babanmu muke kama, sau da yawа
ana cewa ba ita ta haife mu ba saboda ita bakа се
gamu ba suma, sau da yawa ana cewa shuwa ne
wasu kuwa kan ce mu buzaye ne, gashi ko daya a
cikinmu 'yan usulin Katsina ne, amma kuma ikon
Allah ba mu taba zuwa garin da yake, mahaifinmu
bai taba zuwa ba tunda ya auri Babah Mairo, ba
yadda bata yi ba ya ki kuma ya ki fada mata
dalilinsa, gashi suna da kusan shekaru ashirin da
aure.
Da tunanin nan na gama duk aikin da nake yi, har
da kayan da na jika na wanke su, a lokacin kuma a
ke kiran Sallar Magriba. Don haka alwala nayi nayi
sallah, na nemi wuri na zauna. Ina kallon yadda
Babah ke kai-da-kawo tana faman shirya abincin
dare. Baba ba ta gajiya da aiki, na rasa inda na gado
rashin son aiki, hatta Zalihat ta fi ni son aiki, itama
da take karama a gida ta iya ta dafa abinci amma ni
ban iya ba, tun Babah na tuhamata har ta gaji ta sa
min ido.
Washegari a makaranta na hadu da abokiyata
Ummu Kaltume, muna shiri sosai da ita, tun muna
aji uku a (Primary) muka hadu har gashi zamu je aji
daya na (Secondary) tare.
Page | 11 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
A cikin gidanmu ba wacce ta taba zuwa
(Boarding School) sai ni, nima din Babah ta bada
goyan baya, don a cewarta in na tafi can dole nc in
yi aiki.
Muna zaune muna jiran direban su Umma ta ke
bani labarin anyi haihuwa a gidansu, kishiyar
Mamanta. Ni dama harkar yaro bata gabana, don ban
ma shiga harkarsu. Ko Babah ce ta haihu ban
damuwa da yaran ballantana a ce in wanke wa yaro
kashi, ai an kashe ni. Don haka ban ma yi niyyar
zuwa ganin bebin ba, sai dai na fara tunanin naje
gidan nasu a ranar zan samu sassaucin aikin da
Babah kc sa ni.
Da yamma na dawo gida, a kofar gidan na iske
Ya Amir zaune a kan benchi shi da dan Direba suna
hira. Yayi min kyau a ido, fuskata na saki sosai
kamar wadda aka yi wa alkawarin zoben zinari.
Da na karasa kusa da shi sai na dan rusuna na ce,
"Yaya ina wuni?" Ya dube ni cikc da fara'a.
"Daga ina ki ka fito haka Dayyiba?" Ya fada
yana kallona.
"Gidan Kawata naje."
Ya kara fadada murmushinsa.
"Zo ga wannan." Ya fada yana tura hannu a
aljihun rigarsa. Naira ashirin ya zaro sabuwa ce dal,
na washe baki tare da mika hannu zan karba, sai ya
maida hannunsa baya. Na daga dara-daran idona na
Page | 12 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
dube shi, har lokacin fuskarsa a sake take. Ya сe,
"Me za ki saya da ashirin? Na maida idona kasa ina
murmushi da har kumatuna suka lotsa.
Ban ce komai ba, amma na san kallona yake yi.
Na kara kai hannu zan karba sai naji daga bayana an
ce Dayyiba, Babah na kira.
A tsorace na dubi bayana. Nafi'u ne ke yi min
magana. Da sauri na sauke hannuna zan wucc. Amir
ya ce "Dayyiba kin yi mantuwa." Na dube shi tare
da kallon hannunsa da ya miko min kudin.
Sai dai kuma na kasa karbar kudin, na ruga a
guje cikin gida. Ina isa na iske Baba a tsakar gida da
bulala a hannunsa, a take na fara kyarma. Duk
ilahirin jikina rawa yake yi.
Tambayar da ya jeho min yasa na razana. "Daga
ina ki ke?" Na soma kuka, nan da nan fuskata ta cika
da hawayc ina kuka. Ya matso har inda nake ya
zabga min bulalar sau biyu, ihu na saki don azaba
ina fadin.
"Don Allah Baba kayi hakuri..."
"Sai kin fada min in da ki ka je yau."
"Wallahi ina gidan su Ummu, kishiyar Mamanta
ce ta haihu, shi ne naje ganin baby."
Ya kara tsula min wata har sai da na saki fitsari.
"Wa ki ka tambaya da za ki?" Ya tambayc ni
cike da daga murya. Kuka nake yi sosai, don a
Page | 13 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
rayuwata ta duniya ba abin da na tsana kamar duka.
Hakuri nake ba Baba, sannan ya daina dukan nawa.
Ya ce, "Haka kuma ki ke rokon maza kudi, ba na
hana ki ba?
"Wallahi Baba ban roke su ba, shi ne ya bani
kawai. Na fada cikin kuka. Ya cc, "To kada ki
karfa mana, ko ko matse ki yayi ya ba ki?" Na
girgiza kaina cike da tsoran kada Baba ya kara min.
Na ce. "Wallahi na daina karba, yi hakuri Baba.
Wucewa yayi ya yar da bulalar gefena yana
fadin, "In ki ka sake sai na karya ki a gıdannan.
Haka na kwana ranar ina fushi, dama na saba duk
lokacin da aka duke ni ko aka yi min fafa, to na
dinga fushi kenan.
Washegari bai hana Babah ta bani aikin da zan yi
ba, bata kuma lallashe ni ba, dama mun saba. Nima
na san kaina, na cika fushi abu bai taka-kara-yakaraya ba zan rinka fushi, duk 'yan gidanmu sun san
halina. Shi yasa ba mai shiga sabgata.
Gia ni da tsiwa, a duk lokacin da muka yi fada da
su sai sun ce min mai kazanta, ga yanga ga iya yi
amma kai ba kintsi. Da yake ina da saurin kuka shi
yasa ma Nafi'u yake saurin bata min.
Rayuwata ta kuruciya daban ce da ta 'yan uwana,
saboda irin yadda na dauki kaina. A wannan lokaci
ne muka fara rubuta jarrabawar (Common
Enterance) din mu.
Page | 14 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
A wannan hutun ne nayi wani rashin lafiya da
tunda nake ban taßa ba, thypoid ne. Don haka a koda
yaushe zaka ganni a kwance na zama kamar auduga
don tsabar langabewa.
In ka kalle ni dole ka tausaya min, don yadda na
zama cikin lokaci kadan. Na rame sosai, duk da ba
wai ciwon ya yi yawa a jikina ba ne, wurin yi min
allura kuwa tun suna lallashina har suka gaji suke
danne ni aka yi min.
Nayi kusan kwana shidda ina fama da jiki, amma
yadda nake vi kya ce nayi wata biyu ban da lafiya, a
koda yaushe ina kan Katifarmu ina barci, ko ba
baccin nake yi ba, za ka ganni dai a daki, dama gani
bana son aiki, koda naji sauki ma naki nuna hakan
don na san Babah dama jira take ta sa ni aiki.
Ni dai a rayuwata sam bana son wahala, a
gaskiya ni kaina na san son jikina yayi yawa, don ko
magani bana sha. A da Babah ba ta gane ba sai ta
nika min magani in sha, to gaskiya bana sha sai dai
in yi dabara in zubar, tunda ta gane sai take sa ake yi
min allura.
Kafin ayi allurar kuwa sai an ji haushina, don
sosai zan 6ata masu lokaci, dole sai an nemo mutum
kamar uku ko hudu sun danne ni kafin ayi min.
Yanzu kuwa da na kara girma maza ke danne ni, a
kullum idan Babah zata yi min fada sai ta zage ni a
kan ni raguwa ce, haka din ne kuma nima na san
Page | 15 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
haka. (Gashi in ban ga dama ba ko abinci aka yi
wanda bana so to ba zan ci ba, sai dai in sha kunu
shi yasa nake kamar in karye. Sam abinci bai dame
ni ba, har dai irin su tuwon dare. Ba laifi na kan ci
dumame shima din ba kodayaushe ba, ina ga dalilin
rashin jikin nawa ne yasa 'yan gidanmu ba su damu
da rashin son aikina ba.
Komaina a hankali nc, kai ko tafiya nake yi
tamkar ina jin tausayin kasar, shi yasa ake cewa wai
na cika yanga ni kuwa ba na ganin hakan illa iyaka
tafiyar ce da ta zame min tamkar dole.
Ina zaunc a tsakar gida ina yanka alayyahun
girkin rana. GGwaggo Hauwa tayi sallama, da gudu
najc na rungumeta, tunda ita kadai ke sona. Tana da
saukin kai sosai, yar Babah ce sai dai ba fakin
mahaifinsu daya ba, ita 'yar dakin mahaifin Baban
falo cc. Tana da kirki sosai, itama a nan garin take
na Gusau.
Sai dai sun yi kusan tashi su koma Kaduna, don
maigidanta an yi masa (Transfer) zuwa Abuja, dama
yana zaune a Kaduna ne da amaryarsa, ita kuwa tana
Gusau.
Ba yadda ba a yi da ita ta koma Kadunan ba ta
ki, dalilinta kuwa shi ne, dama ita ba ta da yara ba ta
taba haihuwa ba. Tun suna sa rai ita da maigidanta
Alhaji Shehu Magaji har abun ya zama abin magana
Page | 16 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1)
gun 'yan uwan maigidan nata, a kan dole ya sake
aurc.
Shi kuwa sai da suka sami kusan shckaru sha
biyu kafin ya yi auren, yana auren kuwa ko shekara
ba a yi ba amaryar ta haihu.
Ba yadda ba a yi da ita suje asibiti ba a taimaka
masu ta ki, ta ce ita fa haihuwa ta yarda Allah ke
badawa, in da ita mai haihuwar ce da tayi tunda ai a
da sun nemi taimakon amma abin yaci tura, don
haka ita ta hakura.
Ta kuma ki zuwa Kadunan ta ce ita Gusau takc
son zama, a kan dole maigidan nata ya hakura ya
barta, duk da ya kan dauki lokaci bai je ba, yawanci
sai ya sami hutu yakan je yayi mata sati uku.
Da yake maigidanta yana da wadata sosai. ya
zamto bata da matsala ta dauki 'ya'yan 'yan uwanta
masu shi da wadanda ba su da shi tana renonsu,
kamar dan Alh. Muh'd Sani Shinkafi na biyu, tun
yaye da ta karbe shi bata maido shi ba, kuma bai ce
a maida shin ba. Gashi yanzu har ya gama Jami'a
yana aiki. Tsakaninsa da gidanmu sai dai yazo duba
'yan gidan.
Gwaggo ta rungume ni tana fadin, "Ke kuwa me
ya same ki haka duk kin rame? Dama ga ki ba jikin
gare ki ba?" Duk da zaman yata a guna Gwaggo
nake kiranta saboda yaran da take reno, dukkansu
Gwaggo sukc kiranta. "Gwaggo ina wuni?" Na fada
Page | 17 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
cike da jin dadi, ta amsa tare da kwalla wa Babah
kira.
"Mairo!"
"Na'am!" Ta amsa cike da zumudin ganinta. Та
fito daga kicin tana yi mata maraba.
"Ke me ya sami Dayyiba haka ne duk ta jeme?"
"Hauwa kenan, kema kin san fa yadda take!
Dama wani jikin gare ta hala."
"Haba Mairo, ke kin ga yadda yarinya duk ta
Kare, naga ko a jikinki."
"To me zan yi Hauwa? Kin san fa dama ba wani
jiki ne da Dayyiba ba."
"Ni dai wallahi a kula yarinyar nan sai ka ce ba
'yar gidannan ba, dama tun shekaranjiya naso in zo
ban samu dama ba, ai idan ma bata cin abincin ne ba
sai a saya mata maganin cin abincin ba."
"Yanzu kamar Dayyiba 'yar shekaru sha biyu ce
sai an bata maganin cin abinci sai ka ce 'yar shekara
biyu?"
"Eh mana, ana ba dawa mana kamar yanzu ma da
tayi rashin lafiya ana iya a hada mata a
magungunanta a bata mana.
Da sauri na bata fuska na ce, "Ni Gwaggo bana
son magani." Babah ta dungure ni ta keyata ta ce,
"Kin ji irinta ai, Dayyiba bata son magani ko kadan,
in kin san yadda muke yi da ita gun shan magani
wallahi har na gaji yanzu allura ake yi mata."
Page | 18 MARUBUCIYA: Sameera Mustapha
BAKI BIYU [1]
Haj. Hauwa ta dube ni ta cc, "Kyale ta 'yar
kanwata, Allah kara sauki."
Duk hirar da suke yi Gwaggo ba ta bari na bar
wajen ba, zaunar da ni tayi in da take zaunc suna
hira da Babah.
"Wai Mairo me ya hada ki da Gimbiyar ne yau
na shiga gidan naji ana yi da ke?"
"Humm!" Ajiyar zuciya Babah tayi ta cc, "Kc
dai bari Hauwa, na gaji da matsalar Basira. Tun satin
da ya shige take son in tanka ta muyi rigima naki,
shi yasa ta nemi ta wulakanta ni, don haka ma a yau
dinnan