yaran gdianshisai in zai yiwa nawa yaran wani abu ne
zaka ji yana kirgata a cikinsu ina zuane agida ko a oflico sai kawai in ganshi tare da yara ya ce wai ya san n aji marmarin ganinsu sai dai
ban samu lokacin zuwa ba don haka sun zo in gansu tun ina jin kunya
in ya yi mun hakan har na saba na wartsake in ya zo dasu kawai sai in
yi ta murna ina ina naka saka dasu mu'amalata da Yaya Bashir da
iyalinshi ta mamaye mun gurbin komai da nake bukata ina ganin
yana daga cikin dalilan da suka sanya na ma kasa yin wata kawa da
zan yi kut da kut da ita.
Sai dai kawai abokan wasa da dariya sai ko matan abokan Dr
wadanda kuwa mu'amalace irin ta matar abokai, sai dai har a yau din
nan n akan tuna Funke Faraye in tambayi kaina ko tana ina oho? Ina
zaunc a office dina ina fama da aikace aikace aka sanar dani isowar
Yaya Bashir cikin hanzari na mike naje na tarbeshi muka dawo muka
zauna me zan kawo maka Yaya? Na tambayeshi cikin girmamawa ya
ce bani ruwan sanyi kawai na nufi na'urar sanyaya komai na dauko
mishi robar ruwan swan tare da kofi na ajiye a gabanshi na zuba
uishi ruwa na mika mishi ya karba ya sha ya ajiye ya yi korafın zafin
rana da ake fama dashi muka yi magana akan hakan sai na
lambayeshi yaya ka yi hakuri wallahi ko jiya sai da Suhaila ta mun
magana wai kun dawo daga Bengazi ba muje munji labarin mutanen
Bengazi ba, ya yi murmushi ya ce na san abinda kike ciki, kuma ita
Suhailar ta yi mun waya shekaranjiya ai ta ce mun Bashir bashi da
lafiya ko? Na ce e, amma zazzabine kawai ya kuma ji sauki sosai
yaya kuka samu su Baba Hamza ya ee lafiyarsu kalau yana gaisheki
Sharif kuma ya ce ayi miki godiyar aiken da kika yi mishi kuma wai
tunda baki manta dashi ba to ki aika ya daukar miki'yarshi da take
tayaki kwana lokacin da kike gidan na yi dariya na ce Allah sarki
Sharfi ai kuwa bari Lamido ya dawo zan rokeshi sai mu je tare in
daukota Mabaruka yake nufi na sani Yaya Bashir ya ce c, haka na ji
ya fadi sunanta Yaya Bashir ya dan sosa kanshi na gane zai yi wala
magana na kara nutsuwa na tattara hankalina wuri daya ina
sauraronshi sai kawai na ji ya ce mun Baba Hamza fa ya bani aure
hannu biyu na saka akina na mishi ihu wayyo Yaya Bashir zaka yiwa
Anti 1lama amarya? Ya yi murmushin karfin hali na soma yi mishi
57
kuka, nan da nan ya sha mur tare da zare mun ido na yi maza na share
hawayen da koma cikin nutsuwata ya bata rai ya ce kina hauka ne
kina nufin saboda Hama sai ba zan yi mata hudu ba idan ina da
ra'ayin yin haka? Na cc ka yi hakuri Yaya Bashir na yi rashin hankali
ya cc gara da kika gane rashin hankali kika yi, mun je Bengazi mun
tarar dasu Baba Hamza tsufa ya kamashi ga rashin lafiya, ko dayake
gaskiyar magana ita ce tun da muka je gidan na ga 'yan matan gidan
na yi tunanin cikinmu wani ya auri wata daga cikinsu saboda hakan
zai kara karfafa zumunci a tsakaninmu ba zai zamo sai an yi shekaru
kafin mu tafi ba, ga 'yarshi a gidanmu dole ne mu kara kulawa da
iyayenta da 'yan uwanta dake can komai rashin kirkin Baba Hamza da
muke gani kanin mahaifinmu ne ayau bamu da wani wanda ya fishi a
duniyar nan shi kađai ne suke uba daya damahaifinmu haka ne ko ba
haka ba? N ace haka ne kuma ma ai ya yi nadamar abinda ya yi ya ce
yauwa to to sai kuma shi Baba Hamzan ya ce yana so in auri daya
daga cikin 'ya'yanshi ban yi mishi gardama ba Suhaila gaskiyar
magana ita ce 'ya'yan nashi kyawawa ne na yi murmushi n ace e,
wallahi tun ma ba Fadima ba, illar dai kawai bai damu da sanyasu a
makaranta ba, wacce ka daba Fadima ko Salma? Ya yi murmushi ya
ce Fadima na ce kai madalla yaushe ne daurin auren? Ya ce ai sai da
aka daura muka taho yanżu dai zan gama shírya mata inda zata zaune
ne a gidana na Jos, zan karasa ta tare a can, na ji dadin hakan har
cikin zuciyata dama Inna tana maganar ya dace ace Bashir ne a kusa
da ita to gashi zai kai iyalinshi can kenan zai raba zamanshi tsakanin
Abuja da Jos, na saki jiki sosai muka yi ta hira da Yaya Bashir na
kuma tabbatar mishi da cewar na ji dadin auren Fatima da ya yi, na се
to amma in Anti Hama ta ce ta fi son zama a Jos fa? ya ce shi kcnan
amma zan gaya mata zan rinka yin kwana hudu ne a Abuja uku a Jos
don a nan mafi yawan harkokina suke, yanzu so nake ki je ki samu
Hama ki san yanda kika yi kika shawo mun kanta tunda na gaya
mata ta ki cewa komai na kasa sanin ind ata dosa ta ki furta ko da
kalma guda daya ne kin gane? Na ce nagane in na je na dauki Suhaila
a makaranta zamu je gidan ya ce to, muka yi sallama ya tafi na yi
maza na gama abinda zan yi na đauki Suhaila daga can na wuce gidan Yaya Bashir a dakinta na sameta tana kwance nace haba Anu duk sallamar a muka yi shiru kamar ba kya nan? Ta juyo ta yi mun
58
wani irin kallo da ban taba ganin ta yi min irinshi ba na ce wayyo
Allah na kar ai laifin yayana ya shafeni na juya na kalli Suhaila na ce
mata maza shiga kicin ki samarwa kanki abinda zai taimakeki, ta juya
da gudu na samu Anti Hama akan gadon na zauna na shiga yi mata
maganganu ina rarrashi ina ban baki, ina gaya mata matsayinta wurin mijinta da yanda yake ji da ita, kusan awa biyu ni kadai nake magana
bata ce mun komai ba, sai jimawa can na yi sa'a ta çe haba Suhaila ai
ban san akwai 'yar haka tsakanina da Bashir ba, na rike baki na ce lah
sunanshi kike fadi yau la soma sakin maganganu na bacin rai da kishi
ina bata hakuri har dai na samu na shawo kanta ta hakura na ce haba
Anti Hama in kika bari Yaya Bashir ko wani ma ya gane kin ji zafin
auren nashi ma ai kin bada kanki yanzu shirun da kika yi bai fi tayar
mishi a hankali akan ace da surutu kika yi ta yi ba? Wacce mata Yaya
Bashir zai aura ta kaiki? Kowa ya san irin son da ya yi miki yake
kuma yi miki 'ya'yanki shida kin aureshi auren saurayi da budurwa
kin zauna da 'yan uwanshi lafiya tun kina ke kadai kina jin inna ma
da suka gaya mata maganar auren cewa ta yi lallene abi al'amura ta yadda ranki ba zai baci ba to meye kuma za a yi miki bayan haka? Та
soma lissafi to za a canza mun komai na cikin gidan nan, za a canza
mun mota, ban yarda ya soma tafiya da mata tafiye-tafiyenshi da yake yi zuwa waje ba dama Ahmad ne mai yi mishi rakiya, na yi
murmushi na ce ran uwargida ya dade in dai kin yarda da zama lafiya
ai magana ta kare, Yaya Bashir ya dawo ya samemu mun hadu dukanmu a falonshi har da Anti Hama don ta sauko muna tattaunawa
na gaya mishi dalilan Anti Hama ya yi murmushi ya ce ni duk abinda
ta ce na yarda har ma zan yi mata albishir daga yau duk inda zani da ita zan tafi don amarya zata bata shekaru tana hidimar karatun lana
isowa makaranta zan jefata.
Wata guda Yaya Bashir yana shirin isowar amaryarshi Fatima
wacce daga ganin irin shirin dayake yiwa zuwan nata kasan ya riga ya
mato akan yarinyar, duk da Hakcem bai kammala karatun da ya tafi yi ba ya halarci bikin Yaya Bashir dashi muka ta fi Bengazi ba karamin biki aka yi ba a can, har ma Engineer Muhammad shima ya kara amarya ya auro daya daga cikin 'ya'yan Baba hamza Dr Hakeem
ya sameni a masaukinmu bayan sun kammala daurin auren Engineer
ya ce Suhaila ki yi maza ki daukeni mu bar garin nan in ba so kike
59
nima in je in ce baba liamza ya sakc bani wata a cikın 'ya'yan nashi
ba, na kyalkyale da dariya na ce Baba Hamza ai ya baka ni don haka
ba zai yarda ya yi maka kari ba, mun dauko amarya mun iso Jos nima
na zo da Mabaruka 'yar gidan Sharif,. mun yi biki ya kayatar har bai
yiwuwa ace za a yi ta bayani an kammala komai kowa ya koma
gidanshi lafiya, shekaru biyu bayan tarewar Fadima ta haifi danta
namiji, Yaya Bashir ya sanya mishi sunan Hamza yana zaune lafiya
shi da iyalinshi har ni ma wani lokaci cikin zuciyata ina sha'awar in
da ace hakcem zai mun amarya da sai mu zame mishi kamar yadda
Anti Hama da Fadima suka zamewa Yaya Bashir, ina zaune kusa da
Dr. Hakeem Lamido so nake wai ya saurari maganar da na zo mishi
da ita shi kuma ya lasa yayanshi a gaba wai in yana hidimarsu baya
sauraron kowa fama yake da Aisha wai yana rarrashinta ta yi shiru na
ce da ka bani ita teacher in saka mata nono a baki sai ta yi shiru in
samu mu yi magana, ya harareni ya ce ke tafi ta gaji da shan nono
rarrashi take so na kuma fi ki iyawa, na zobara baki na nufi wayar
dake ta kara na dauka Fadima ce daga Jos na ce a'a ran amaryarmu ya
dade ta ce kai do n Allah marya shekara uku? So nake ki bani aron
'yarki ta yi mun rakiya? Na ce ina za ki? Ta ce'zan yi wa maigidan
rakiya zuwa birnin Paris zai je hutun wata guda na zaro ido n ace ina
Anti Hamar? Ta ce ai anti Hama ta janye daga wadannan dokokin
nata ta ce ta amince ta yarda Yaya Bashir adalin shugabane don haka
kan komai ma ya yi adalci don haka daga yanzu zmau rinka yin tafiya
canji-canji na ce kai madalla da Anti Hama ta zamo Musulma ta
kwarai mai sowa 'yar uwarta abinda take sowa kanta, zan shirya miki
Suhaila zan turo miki ita sai dai kuma in an je kar a yi wasa azo mana
da tsarabar 'yan biyu a makale, ta kyalkyale da dariya, ta ce kin kuwa
san shima yayan naki abinda ya gaya mun kenan jiya, na ce to ai ba kokarina bane kaine sai ka bada himma, muka yi sallama, cikin zuciyata ina tunanin wato shi dai namiji a gaban matar da yake so kullum yaro ne!
Sai an jima
HAFSAT SODANGI
60
HASSAN BOOKSHOР MIGA
Bayan Masallacin Abacha
Kasuwar S/Gari Kano.
Cover by:
AGF GRAPHICS FAGGE
C/O ANKA-GRAPHICS FAGGE
08028182666
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels