yanda muka yi zato matan babansu Sa'a dukkansu Hama da
sauran matan Alhaji Ali, ita kanta Anti Hama iyaycnta sun zo ga kuma kawayenta data gayyata, gidansu Hakcem kuwa dama tun safe
a cike akc nan da nan aka karôesu hannu bibiyu aka saukesu cikin karramawa ni kam can cikin dakin Inna na kule na kwanta ita cc kuwa ta sani n ayi hakan wai amarya bata bari a rinka ganin fuskarta, can Anti llama ta sameni dada mun duka ta yi a cinya tana cewa
Allah sai na hadaki da Yayanki in ce mishi kai kana nan kana zullumin likita ya tafi da Suhaila ita kuwa tana can tana cin amarci
har tana kiba, tana kara fari, na ce Anti don Allah kar ki mun sharmi
36
wanc kiba zan kara ni da kullum nake cıkın tunanın Yaya Bashir? Ta
kyalkyale da dariya ta ce ai fa gashi nan na gani, ita ma Sa'a ta shigo
itama tsiyar takc mun me kike ci haka kika canza a kwana bakwai?
Na hararcta na ce to me zan ci kuwa wanda ya fi na gidanmu? 'Yan
mintoci muna bira tana bani labarin yanda hankalin Yaya Bashir ya
tashi da y aga har kwana uku ban dawo ba, na yi tsaki na ce sharrin
teacher ne kawai na rantse miki, ta ce to ai ya yi kyau don naga kamar
har an samu, na rike baki ina salati ita kuwa ta tashi zata fita tana
cewa ke Sa'a ki fito mun bar mutane da aiki, Hama ta shigo suka
gaisa da iyayen Hakcem ina can ciki na ji tana cewa ni ina amaryar
ne? Suka ce mata ta shigo tana shigowa ta harareni, ho 'ya mai abin
kunya, ashe dama shirywa kuka yi da mijinki, na soma yi mata rantse
rantse, da dai ta ga da gaske na damu sai ta yi dariya ta ce ke ni fa mijinki ya burgeni ya taimaki kanshi kema ya taimakeki don da Allah kadai ya san lokacin da Bashir zai ce ya shirya, yanzu kuwa ai kin gani ya biyoku da kayanku, na ce yaya aka yi haka Hama? ta ce ato ya yi waya Alhaji yana mitar wai kwanaku hudu baku dawo ba,
bayan ya cc biyu za ki yi kuma shi bai gaya mishi har dashi a tafiyar ba, sai daga baya ya ji labari shima ya taho, gida yanzu me ye abin yi? Shi ne Alhaji ya cemishi in dai gaskiya kake so to ka bisu da kayansu in kuwa ka fr so ya dawo maka da ita tayi renon ciki a
gidanka shí kenan in ta haihu ka ga sai ka hada garar biyu data aure data haihuwa, na ce kai Hama to ni wai daga an yi aure sai a soma maganar haihuwa ne? Ta bude baki a'a to me ye albarkar auren? Ran
nan tunda suka zo har cikin dare wai aikin jere suke yi ban dai sun me suke jerewa ba haka? Amma na ji kus kus wurin'yan uwan teacher
suna cewa kai mutanen nan suna aiki a dakin Inna na kwana abina.
Washegari wajen sha daya na safe su Hama suka ce su za su koma gida, Innar su Hakeem kuwa ta ce ai sam sai ka ce suna korarsu sai dai su bari sai gobe hakan kuwa aka yi Hakeem ya yi musu alheri mai
yawa har da wasika ya bayar a kaiwa Yaya Bashir ban dai san abinda
ya rubuta a ciki ba, kaya sosai Yaya Bashir ya yi mun har bai yiwuwa in tsaya kwatantawa bani ba hatta Hakeem da 'yan uwanshi sun yi
farin cikin ganin irin gatan da ya yi mun zamanmu a Girc bayan tafiyar iyayena zamane na cin amarci da morewa juna ga tarairaya daga ko ina kowa ji dani da Suhaila yake yi.
37
Hakcem agidansu dan gata ne ga mahaifiyarshi da kakarshi
wadanda baka raba bakinsu da ambaton Lamido gaba daya dangin
ubanshi ji dashi suke yi, na tambayi Hakeerm menene ma'anar Lamido
da yake amsawa bayan ni a sanina sunan babanshine ya yi dariya ya
ce Suhaila Lamido sunan shugabancine ni sunan mahaifina Ahmad ni
kuma tun ina yaro mutanen garinmu suke kirana Lamido don suna
fatan in gaji mahaifina, na ce to kana sha'awar gadon nashi, Hakeem
ya dan yi shiru jimawa kadan sai ya ce ba zai yiwu in ce ban son
gadon mahaifina ba a ko me ye dana san yana yi amma na fi sha'awar
in taimaki mutanen garina ta hanyar sana'ata kuma a yanzu ma
babana ne yake sarautar tunda kanin mahaifina ne ai na kai ki kin
gaisheshi kin ganshi ko? Na ce e, yayun Hakeem mata da kannenshi
wadanda suke gidajen mazajensu kullum baka rabasu da gidan in dai
har yana gari kowacce ta zo zaka ji tana cewa wurin Lamido ta zo,
mutanen gari kuwa maza da mata kowa ji yake yi kamar ya yi ta ina aka saka dashi, a dan zaman da na yi dashi na fahimci babu abinda
Hakeem yake so irin garinsu da mutanen garin bayan asibitin da ya
gina wanda komai da ake yi a ckinshi kyauta ne shi mutumne wanda
baya gajiya da hidimar jama'a komai dare in aka yi sallama fita yake
yi ba tare da ya nuna bacin rai ko gajiya ba, bashi ke sarautar garin ba
amma gidanshi ya fi na hakimin cika da jama'a mahaifiyarshi kuwa
na lura shigen irin hikimar Hama ne da ita tasa hannu biyu ta
rungumeni, ko 'yan uwanshi matane suka zo suka ce Inna mun zo
bamu samu Lamido ba in ya zo ki ce mishi kaza da kaza sai ta ce a'a
ku je ku samu matarshi ku bar mata wannan sallahun, Inna ai shirru
ne sai ka ji ta ce sirrun Lamido kuwa ai na matarshi ne in dai kuna
son gaskiya tunda ta zama taku zan iya cewa baiwar Allah nan ta
fifitani akan 'ya'yanta yanda Hakeem yake shugaba akan komai haka
nima ta shugabantar dani, nima na shiga taya Hakeem tattalin
mahaifiyarshi don kuwa shi mai son uwane komai dare in ya dawo
bai shiga wurinshi sai ya je jikin windonta ya ce mata Inna 'mi warti'
tun ban san me haka yake nufi ba har na gane cewa yake 'Inna na
dawo. In kuwa ya tabbatar ta yi barci kafin dawowarshi to baya
shigowa gidan da mota don a sashinta yake parking din motocinshi,
sai ya bar motar a waje ya taka ya shigo wai kar ya tasheta daga
barcinta, tunda na zo gidan Ilakeem bai cin abincin kowa sai nawa, in
38
a
kuwa zai yi baki masu aiki ko 'yan matan gidan yake sanyawa wai
kar in wahala ni kuwa kullum zan yiwa Ilakcem girki na kan yi ne
are da mahaifiyarshi.
Suhaila kuwa ta zama 'yar gari ko maganar gida bata yi sai dai ka
ji tana cewa 'yan matan gidan tunda dasu tafi har ka sunan babana na
Abuja biyu yayan Suhaila da baba Bashir, babana na gidan nan ma
sunanshi da yawa teacher, Lamido da kawu su yi ta dariya suna
zolayarta tana musu surutu tunda maganane d aita, mun yi sati biyar
ran nan a Gire cikin hutun Hakcem na watanni biyu hutun babban
ma'aikaci na kwanaki arba'in ban da asabar da Lahadi na wayi gari
ina hutun sallah a ranar tun safe ran Hakeem a бace yake wai ya ga
ina al'ada menene haka Suhaila ni fa na dauka daga wancan al'adar da
kika yi farkon zuwanmu shi kenan, sai kuma badi, na yi kamar ban ji
shi ba, ya sake cewa Suhaila ni fa yara da yawa nake son ki haifar
mun na ci gaba da abinda nake yi ban kulashi ba, ya biyoni har kicin
kunun nono nake dama mishi, abinda ya ce mun sai sha kenan ni
kuwa wurin mahaifiyarshi na koyi yanda ake damawa don ka'idane in
dai Hakeem yana gida to kullum zai sha kunun nono, ya matso kusa
dani., Suhaila ba ki ji ina magana bane, kika ki kulani? Ina gauraya
kunun wanda na riga na zuba mishi nono, na ce in na ji ka me zan yi
maka Lamido? A ganina duk abin baya hannuna in kuwa ina da wani
laifi to gaya mun sai in yi maza in gyara, ya yi dariya ya ce laifinki ba
kya tayani addu'a, Suhaila, kokarin da nake yi ina ganin da kina
tayani addu'a da mun yi nasara na ce to shi kenan zan fara daga yau,
ina kwance gadon Hakeem tausa yake mun har ina jin kamar barci zai
daukeni gashi kuma na riga na galaßaita a hannunshi don kusan awa biyu da suka wuce shi ke sarrafani ta yadda ya ga dama cikin zolaya
ya ce ni dai ina iyakacin kokarina Suhaila ke ce ina jin ba kya karba
na rufe idanuwana da tafin hannuna cikin jin kunya na ce kai teacher
ba ka jin kunyar irin wadannan maganganun ya jawoni jikinshi me yc
abin kunya? Idan na fadi gaskiya bana kokarin ne? Na yi shiru me ye
abin kunya, in na nuna ma matsu ina son ganin dan da zà ki haifar
mun? Ina so ne in fara ganin tukwicin kai kawon da na yi ta yi dake a
cikin zuciyata, na yi gwagwarmaya Suhaila kina makale a raina, duk
inda nasa kafa kina tae dani, ke ce tunanina a duk lokacin al'amura
suka mun sauki, duk wata mace da na gani in ba na surantata dake ba
39
bata burgeni balle bar ta bani sha'awa na yi mamakin yanda kika
mance dani gaba daya kika kasa tuna komai nawa sai da tuna miki
cewar ninc Hakeem Lamido na makale teacher na ce ban taba
mancewa da kai ba tcacher kaine abin tunawa na a duk lokacin da
wani alheri ya sameni, a ranar da muka ci gasar "MAN
COMPETITION" n ayi sha'awar ganinka a wurin, na yi kewar
rashinka a wurin liyafar da makaranta ta shirya mana, haka nan a
Bengazi kaine ka zamo abin tunawata a duk lokacin da bakin ciki ya
Rulleni in ji wani abu ya tokareni in rasa inda zan tsoma rayuwata in
ji sanyi wani lokaci in ji kamar in yi ta shur-shure babu hali, babu
wadanda zan yi wa wannan shagwabar ina tunaka teacher in yi
sha'awar ganinka don in gaya maka maraici ya sameni ga halin dana
tsinci kaina in tambaycka ko shi ne abinda ka yi ta kokarin
kwatantamun na kasa ganewa, sai da abin ya sameni shiruteacher ya
yi yana kallona cikin tausayawa, ya ce to ya ya aka yi kika kasa
ganeni? na ce na yi karfin hali na cireka daga cikin zuciyata daga
baya saboda nasihar da kakana ya yi ta mun cewar sanyawa zuciya
burin abinda aka san samunshi zai yi wuya shi ke karawa dan adam wahalar rayuwa.
Gaya mun zamanki a Bengazi Suhaila na kalleshi na yi
murmushi na cerayuwa cè da ban son funawa da ita, teacher amma
hakan ba zai hanani gaya maka ba tunda kana son ji na soma bashi
labarin al'amuran da suka faru dani tun rabuwarmu dashi a wurin
gasar cowbell yana kallona yana murmushi na gangaro har rasuwar
mahaifina teacher ya tayani kukan da nake yi na gaya mishi yanda
kakana MalamAhmad ya tafi dani Bengazi rayuwar dana tsinci kaina
a ciki na wayi gari cikin wadanda ake yiwa dukan tsiya a kowane
lokaci bayan ada ban taßa sanin yanda dukan yakc ba, zamana da
Malam Ahmad yanda muka shaku da juna muka so juna labarin
matan su Malam Ahmad, aurar da ni da Baba Hamza ya yi ga Sharif
irin dauki ba dadin da aka yi dani kafin a kaina gidanshi artabun da
muka rinka yi kafin wani abu ya hadamu yanda na samu ciki sau biyu
kawai da mu'amalar mu irin wahalar danatsunduma a cikinta da irin
mafarke-mafarken da na yi ta yi da Funke Farayc, haihuwar da na yi
rayuwata da yarinyar bayan ita ke debe mun kewa, ta zo itama la
rasu, zuwansu Yaya Bashir da mutuwar Malam
40
Ahmad, sakin da
Sharifya yi mu da dalilin sakin yanda Baba Hamza ya karbi maganar
mutuwar aurena, yanda na ke ta dajin nan ya iso tashar jirgi da namun
dajin da na gamu dasu shigana hannun Hajiya 6oyon da ta yi mun
bayyanar sirrinta na cewa itama muguwar ce shi ga hannun su Sharif
da ta yi da yanda mutumin nan ya zo ba tarc da na sanshi ba ya
kubutar dani ya kaini gidanshi ya nemar mun mota zuwa Sudan har
kawo mai tasin da ya kawoni gidan Yaya Bashir da yanda muka yi
dashi babu abinda ban gayawa teacher ba.
Ajiyar zuciya mai karfi teacher ya yi ya cc hakika kin wahala
Subaila, amma abin farin cikin shi ne wancan duk sun zama labari a
yanzu kina hannun masoyanki ne Hakeem mijinki da Yaya Bashir,
Suhaila ina sonki har ban san yanda zan yi in gaya miki ina sonki ba,
na kara lankwashewa jikinshi n ace ko dogon tabon da ya ratsa
bayana da kake yawan tambayata dalilinshi harna ce maka dashi aka
haifeni na boye maka ne kawai sauran tabon dukan Sharif ne saboda
gudunshi da nake yi ya zuga mun bulalar rakumanshi me ya sa su
Yaya Bashir suka kyale Sharif din nan Suhaila da suka je Bengazi?
Na yi murmushi na gaya mishi yanda Sharif da Yaya Ahmad suka
kwashe, na ce su Yaya Bashir da Yaya Ashiru ne kawai suka lallaba
suka ce a kyalesu kawai shi ya ci darajar auren da aka sagala a
tsakaninimu Baba Hamza kuwa shi da zumuncin da ya tozarta na gaya
mishi zuwan Baba Hamza da Sharif da yanda suka kasa ganeni har da
tsiyar da na yi musu ya yi ta dariya, muni sati bakwai a Gire muka
shiga shirye-shiryen komawa Abuja a wannan lokacin ni kaina na san
na canza saboda yanda nake jin nauyin jikina, shiri sosai aka yi mana
na tafiya, Abuja tamkar ba gida zamu ba, wani likeke rago Hakcem
ya bayar ya cc a yiwa Yaya Bashir kilishi dashi mu kai mishi tsaraba
mun isa Abuja ranar asabar da yamma washegari ranar Lahadi da
sassaſe muka yi shirin cikin kwalliya sosai ni kaina kwalliyar da biyu
na yi ta wai in samu in burge Yaya Bashir ya dai yarda da cewar
mijin nawa ba karamin kulawa dani yake yi ba, n da Suhaila sai
walkiya muke yi shima Пakeem ya yi ado cikin manyan kaya wanda
ba kasafai yake sanyasu ba a cikin motar Hakcem Combatable muka
isa gidan tun a kofar gida muka sha oyoyo wurin maigadi Anti Hama
kuwa da ta gamu ihu ta yi tana cewa yayan Suhaila ga amarc sun
dawo daga 'honcy moon' din da suka tafi ran nan ina zaune a gaban
41
Yaya Bashir kamar zai lasheni dadi ya kamashi ganin canjin dana
samu lafiya dai ko Suhaila? Abinda yake tambayata kenan in ce mishi
lafiya kalau, yaya ya ce to madallah shi da Hakeem I:uwa hira sosai
suke yi suka ci abinci tare teacher ya tafi ya barni nan ma Yaya
Bashir ya sake kirana kar fa ki boye min komai nine madadin mahaifi
a wurinki in kina da matsala rinka gaya mun in mijinki ya yi miki ba
daidai ba, ki zo ki gaya mun ina tace mishi to, sai dare Hakeem ya zo
Suhaila tana ganinshi da gudu ta dauko mun jakata tana cewa Yıya
Bashir baba mun tafi gidanmu, ya bita da kallo s,ai kuma ya juyo
gareni ki bar yarinyar nan agida Suhaila kar ki tafi da ita. Kasa yi
magana na yi na soma yi mishi kuka, teacher ya shigo yana rike da
hannun Suhaila ya zauna gcfe daya cikin nuna alamar girmamawa
Yaya Bashiryana mun fadan baya son rashin hankalin da nake so in
yi, ina kuka n ace mishi Yaya ni in dai an bani itan yanda ka fada
tunda aka haifcta to ka bar mun ita ta zauna inda nakc, kina so ki
nuna mun ba ki yarda damaganar da na yi bane? Na ce a'a zan yi
bayani teacher ya ce in shiga gida, na tashi na shiga dakin Anti Hama
ina kwance a kan gadonta ina kuka tare da tunanin yanda zan ji idan
Yaya Bashir ya hanani tafiya da Suhaila sai gata da gudunta Anti wai
ki zo mu tafi in ji Kawu da sauri na taso na zo na yi mishi sallama
muka tafi, a hanya Hakeem ya ke ban labarin wai da kyar ya bár
Suhaila ta dawo saboda wai dawainiyar da ake yi dani din zai yi
yawa mun koma hutun jami'a ina ci gaba da karatuna Suhaila ma na
ci gaba da kaita makarantar da dama take zuwa kullum ni ke kaita da
safe in je kuma in daukota teacher kuma ya daukar mata mai lura da
ita agida saboda wani lokaci dukanmu bama nan. Zamanmu gwanin
dadi ni da teacher shi mutum ne wanda kullum bai gajiya da hidimar
matarshi matsalarmu guda daya ce a kowanc lokaci ya ga ina al'ada
to shi kam a bacin rai yake na kasa ganc al'amarin ya ce mu je asibiti
mun je an ce dukanmu lafiya an kara mana da wasu magunguna
amma shiru in yana magana na kan yi kokarin kwantar mishi da hankali ta hanyar tuna mishí lamarin a hannun Allah yake shi ke
bayar wa idan ya so yin haka din in kuwa bai bayar ba sai ayi hakuri
daga baya sai na fahimci zargi ya shigo cikin maganar yana ganin kamar ni ke hana kaina daukar ciki don in samu in kammala karatuna
kafin in soma haihuwa, tashin hankalin teacher in ina al'ada ya fara
42
ח
a
a
Π
さ
damuna har na zama ina kokarin 6oyc al'adar tawa in samu in yi in
gama bai gane ba don dai a zauna lafiya to ran nan ma ya gane
saboda ya neme kasancewa tare dani da safe bani da yanda zan yi in
bijire mishi haka kawai babu dalili don haka na gaya mishi gaskiya
kawai bana sallah harya tashi ya fita sai kuma ya sake dawowa ba fa
za ki ko ina ba yau na ce ai dama babu inda zani ina dai da lacca ne
da karfe biyu da rabi, ya ce ba zaki ba, karo na farko dana ji ya ce ba
zani daukar lacca ba sai na bukaci snain dalili ya ce haka kawa, na ce
s'a to in haka kawai ne babu dalili zani ba zan fasa ba don kuwa ka
aureni ne bisa sharadin zan ci gaba da karatun nan da nan ya tunzuro
in na aureki bisa sharadin ci gaba da karatunki shi kenan sai ya zama
hujjar hana 'ya'yana zuwa duniya? Kina nufin karatunki ya fi haihuwa
muhimmanci a wurina? yanzu 'yar da matar Ahmad ta haifar mishi
mai sunan Inna bata kai wata biyarba? amma ni-a gidana kullum ana
cikin al'ada ko ina ganin kamar wata ya wuce sai kuma an san
hikimar da aka yi aka yi jikina ya yi sanyi na ce haba Lamido kana
nufin ina yin wani abu don haka kaina katseni ya yi in ba kya yi gaya
mun problem din mu Suhaila gaya mun ki ce.ga abinda ya hanamu
haihuwa zo ki gaya mun ya kamo hannuna ya samu wuri muka zauna
ya shiga maganganu na ce amma ai anan gidan bani da wani sirri da
zan rinka shan magungunan hana daukar ciki ba tare da ka gane ba
tunda a daki daya muke, a'a kar ki nemi yi mun wayo ina binki ne?
Na ce baka bina Hakeem ya ce bana binki za ki iya yin abinda kika ga
dama ban sani ba, na ce to babu laifi na gode, na ja bakina na yi shiru,
ya yi mita ya yi maganganu ya yi barazanar hana karatu, sai bayan na
haihu, ina jinshi cikin zuciyata ina tunanin meye abin yi a gareni? Ina
zuwa gaban Yaya Bashir da maganar zai ce abinda ya gudar mun
kenan da saurin yin aure gashi tun ban rufa shekaru biyu a gidan
mijin ba na soma samun matsala, in kuwa na je Jos ma duk dai ban
Isira ba don sai ya ji ina zuane ina kallon teacher yana shirye-shiryen
zuwa asibiti gun aikinshi nima ina tunanin abinda zan yi yana fita na
dauki waya na bugawa wani ma'aikacin airport wanda teacher yake
bulda dashi saboda zirga-zirga cikin sauri a jirgi na ce mishi akwai
jirgiņe zuwa Yola ya ce e, karfe daya zai tashi na ce to ayi mun bukin
ganin nan zuwa, ya cc to na tashi na shiga shiri na daidaici lokacin
lashin Suhaila a makaranta na fita ba tarc da na dauki mota ba shata
43
na dauka na tasi na je na daukcta a makaranta daga can na wuce
airport na samu jirgi zuwa Yola daga can na shige Gire ganina kawai
kwatsam suka yi ta yi mun tambayoyi kan wai ko lafiya suka ganni
haka ba tarc da mijina ba, na ce musu alyuka ne suka yi mishi yawa,
na budc wurinmu muka yi zamanmu cikin kwanciyar hankali duk
lokacin dateacher ya yi waya wai yana tambayata a ina nake? Kife
wayar nakc yi in ki sauraronshi kwana na biyu a Gire ran nan da
daddare sai ga tcacher, ban ma san ya iso ba sai da Inna ta aiko a
kirani na shiga falonta na sameshi yana zaune cikin nutsuwa da
alamar fada lake mishi na yi kamar ban ganshi ba na nemi wuri na
tsuguna na cemata gani Inna ta ce mun zauna mana Suhaila ai ni kin
burgeni wallahi Allah ya yi miki albarka ashe sabani kuka samu da
Lamido kika zo kika zauna anan baki gaya mana komai ba? Ban ce
komai ba gyara zama kawai n ayi ina sauraronta teacher ya gyara
cikin ajiyar zuciya ya ce Inna ba fa wani abu mai girma bane ta dai ga
damar zuwa nan din nene kawai ta ce kai Lamido ja bakinka ka yi mun
shiru kai fa baka san tana nan ba ka zo ne kana gaya mun cewar ka
nemeta a gidansu da kuma Jos bata nan kai kuma ka kasa gayawa
'yan uwanta cewar baka san inda take ba, shi yasa ka zo ka gaya mun
in san yanda za a yi a nemeta, ko ba haka ka ce mun ba, ya sunkuyar
da kai kasa ya ce haka ne Inna, ta ce to don kuma ka zo ka samu ta
rufa maka asiri sai ka ce ta ga dama ne? In da abinda ta ga dama take
yi ai da kararka ta kai gidansu me ke faruwa Suhaila gaya mun kawia
kar ki boye mun komai, ni kin burgeni tunda kin nuna mun ke matar
rufin asiri ce dama matar kirki a dakinta take yaji ba sai ta je tana
tonawa mijinta asiri ba, a wurin 'yan uwanla tana zubar mishi da
mutunci na dan yi shiru ta ce gaya mun Suhaila, na dan soma zan
gaya mata abinda teacher ke mun duk lokacin da nake al'ada na ji ta
soma salati tana tafa hannu na fasa kawai n ayi shiru duk da haka ba
karamin fada ta yi mishi ba, sai da ya ji ta natsa sai ya ce to inna ai
nima ta yi mun laifi saboda me da zata tafi da Suhaila ta barni ina
nemanta ta kuma katse mata karatunta ai ni Yaya Bashir ya baiwa
yarinyar tunda in banda na ce mishi ni zai baiwa rikonta ba Suhaila
ba da ya karbeta Inna ta ce ke Suhaila daga yau wannan yarinyar ta Lamido ce kar ki sake kaita wani wuri bada izininshi ba, na cc to a
dakinmu ran nan kudundune kaina na yi na ki sauraron teacher yana
44
fkarin cire rufata yana cewa haba Suhaila ba Inna ta sasantanmu ba,
ce ai ban gaya mata rabin abinda kake mun ba, balle ka ce na gaya
te duk laifinka ta ji ta ce in yi hakuri, to ai na gode miki Suhaila na
ki yihakuri kin ji, ya sakejawoni jikinshi na sake dunkulewa, na
a'a ni tunda in ba zan haihu ba bani da wani amfani a wurinka, sai
aika yi ta gaya mun bakar magana to gara abari kawai, cikin sauri
ya ce abar me Suhaila? Na ce a bar komai ma ai ba za a yi haka a ina
lika ga ana zama haka? Ke dai yi hakuri 'yan matana kin ji? Ya shiga
sumbatata. Tun daga nan na samu saukin al'amuran teacher sai dai kullum
idonshi a kaina yake in lokacin al'adata ta yi muna nan ai da teacher
kaina cikin zuciyata ina da damuwa ganin yadda shiru tun zuwana
gidan Lamido ban taba tsallaken wat aba, mutumin da yake matukar
son haihuwar kamar ya yi yaya? In tuna zuwana gidan Sharif cikin
(saütsayi kawai sai gani da ciki shi kuwa Sharif da ace matarshi ta
haihu gara mishi rakuminshi in gaji in ce to lamarin ba nawa bane na
Allah ne tilas kuwa a bar mishi kayanshi, ana cikin haka sai gawani
wata ya zo ina zuba ido in ga al'ada shiru wata ya zo ya wuce ban yi
bø nan da nan kuma na shiga laulayi iri-iri sai đai đuka na yi kokarin
shanyewa ban yarda teacher ya sani ba maganar al'ada ma da ya yi
mun cewa na yi n ayi bayanan yana Leğos inda ya je ya yi sati guda
na matsa mishi kwarai kan ni kam tunda ina cikin hutun zan tafi Gire
in je wurinsu Inna da kyar ya hakura ya barni saboda ya ga raina ya
6aci da ya hanani tafiyar ban tafi da Suhaila ba don ya cc in bar mishi
ita, a Gire na yi ta rashin lafiya iri iri Inna kam ta gane cikine dani
ban kuma 6oye mata ba, bana son Lamido ya sani don ina tsoron kar
a zo a nemi cikin a rasa